MALIKA MALIK BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 12 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 12 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Abangaren gidansu Zahra ne Shirye Shiryen yafi yawa saboda itace uwar gayyah,Tun ana saura sati daya biki Hajiya Saratu momi ta dauko hayar wata Falmata mai gyara amare daga maiduguri,wacce zata gyara Zahra ciki da bai kafin ranar bikin yazo,Hakika bakaramin burgeta momi tayi ba,haka takasa boye murnata afili dama ita burinta taje ta rikita Saleem wanda zai manta da kowa da komai sai ita shalele Fatimatul zahra’u.

Bangaren gidansu Saleem kuwa Abbi shima ya saki aljihu ana ta Shiryen shiryen biki,Tunda daga kano Abuja za’a kawo zahra sai ta kwana washegari su Wuto zamfara da ita,wannan Auren na musamman ne,domin yazoma Saleema akan gaba,sun gama Final Exams dinsu ta tararro ta dawo gida aka Shiga shagali da ita tayi alqawari sai ta chusama Malika haushi Sosai da sosai,Balle ma Da Sadiq ya sanar da ita itama Zahran ba baya ba akwai kyau ga iya kwalliya da Iya tsara kalamai,Kawai sai taji lokaci ta burgeta saboda neman suna harda karban nombarta ta kirata suka gaisa.

Itako Zahra an samu nayi ai sai aka zare an samu kanwar miji abagas,abun takaichi ma Saleema bataji kunya sanar da Zahra duka sirranka auren Saleem da Malika wanda batasan dasu ba,yazamana Family issues ne,itako zahra kanta ya fashe harda daukan ma Saleema alqawarin sai inda karfinta yakare game da mallakan Saleem,harda ikirarin sai malika ta barmata gidan🤔.,Saboda munafuncinsu yazo daya,sai ga Saleema ta Shirya kayanta tsab tatafi kano gidansu zahra tace chan biki zai fi dadi,Allah barshi in Za”a kawota sai ta biyosu su dawo tare,Ummi da Abbi basu zargi komai ba sun zata dama kila chan kawayene suna da kyakyawan alaqa duba da itama Saleema zamanta yafi yawa akano,basu san ko kullewan ta munafunci bane.

Duk wannan Abun Saleem bai san dashi ba don babu wanda ya sanar dashi,Dayake ma Saleema yanzu bata gabanshi Tunda sukayi karon nan da ita agida yadaina mata dariya,gabda bikin yaga kiranta ammh sai ya Shareta bai daga kiran ba kuma bai calling dinta back,sai ana gobe biki yana Shirin tahowa Abuja inda zasu hadu anan gidan Abbi su Tafi daurin Aure,Zahra ta kirashi tana rokonshi don Allah ya iso kano yau ya hallarci Dinner dasuka Shirya,kawai sai yaji kamar muryan Saleema cike da mamaki yake tambayan Zahra murya wa yakeji kamarta kanwarsa Saleema..?Zahra na mirmishi ta sanar dashi itace,gabansa ya fadi hannunsa bisa bakinsa,yana jinjina al”amarin na Saleema   tsoro ya darsu ranshi rai bace yace zahra tabata waya nan akaba Saleema waya ta karba tana gaisheshi bai iya amsa gaisuwanta ba ya kira sunanta a kakkaushe..

   “Saleema,Don ubanki uban me kikazo yi gidan su Zahra..? Tana tabe baki tace”Yo laifi ne don nazo gidansu matar da zaka aura,Don mutaru muyi shagalin biki tare..? yana Numfarfashi ya tare ta yana Fadin”Ke rufemin baki munafuka,kinsan Allah Saleema kinsan dai nasan halinki wlh tallahi in naji wata mgana ta Fito to nasan daga bakinki ne,Kuma sai naci ubanki na kakakkrya ki shegiya Mai dogon baki kawai..”Yafada yana huci ya yanke kiran,Tabe baki Saleema tayi kafin tace acikin ranta”Ni ba munafuka bace..”Tafada tana murguda baki kamar tana gabanshi,Nadira ce ke tambayanta ko lafiya,sai ta barsa tace bakomai..,”

Abangaren Malika ma,Joda da Maman Abba suna ta gudanar da Shiryen Shiryen zuwa amarya ta ango,Maman Abba da kanta ta karbi kayan Malika wajen kala biyar taba telanta ya tsaro mata dinkuna na gani na fada,kuma saleem yabada kudin da kanshi,kuma zahirin batu dinki sun Fita sosai,Gashi yayi mata masu yalwar saboda cikin jikinta.

Duk da Malika na boye kishinta bata bayyanashi ammh yau kam takasa control din kanta,balle dataga Saleem ya Shirya kayansa Zai Wuce Abuja bazai dawo ba sai jibi in sun taho da amarya,tana zaune agefen gado sanye da doguwar rigar Atamfa cikin dunkunan da Maman Abba ta dinkomata,tayi mata kyau sosai balle da cikinta yakara tsufa,sai ta dan kumbura kadan fuskarta ta cika sai takara kyau,tagumi ta zabga hannu biyu tana kallonshi yana kokarin saka botir din gaban wani yadinsa Fari ammh Shara shara ne,domin hatta Farar vest dinsa ana gani,Hulansa ya dauko xanna bukar,mai adon baki ajiki domin aikin jikin rigar baki ne,Yadorata akai agogonsa baki na fatar damisa yake daurawa kafin hankalinsa ya koma kan Malika wacce idanuwanta suka fara cika da kwallah.

Yadade yana kallonta kafin ya saki ajiyar zuciya ya karisa kusa da ita,har ya durkusa gabanta bata Sani ba,sai da sanya hannu ya ciremata hannuwan datayi tagumin dasu,kana ta dago tana kallonshi ido cikin ido, Kwabe Fuska yayi yana kallonta yace”Why…? Haba Amanata meyesa kikeson Allah ya kamani ne? ehe kina tagumi abunda kikasan babu kyau meyasa kikeyi..? Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi dukar da kai tayi saboda bazata jure kallon kwayan idonshi saboda suna dauke da wasu sirranka wanda suke haddasamata wasu irin yanayi atare da ita.

Kanta na kasa tace”Na daina..”Ta fada tana sosa hanci dan mirmishi yayi kafin ya saka hannu ya dago habarta yana Fadin”Mejego..Uhmmm..Menene fadamin naji..? Yafada yana shafa lebenta da hannunshi guda daya,rikemai hannu tayi tana kokarin maida kwailarta tace”Katashi katafi kada kayi dare a hanya..”,Kwayan idonta yake son gani,ammh sai taki ta rinka kauda kai,shikuma yana binta da ido,ganin haka yasa yatashi tsaye yasa hannu ya dagata tsaye yana Kallonta cike da kulawa,bai bata zarafin mgana ba, ya budemata hannuwanta tafada,lokaci daya ta saki kukan data ke rikewa Tun dazu..”matseta yayi yana shinshinar Wuyarta cike da salo,lokaci daya yana Shafa cikin jikinta,Tunda dama ta gefe ya Rumgumeta,saboda cikin daya yi mishi shamaki.

Sai da tayi kukanta ya isheta kana tayi Shuru tana Ajiyar Zuciya,tare da sauke Numfashi,Mirmishi yayi yana Kara gyara mata daurin dankwalinta bayan ya bata Sumbata asaman tsakar kanta yake fadin”Kamar kada natafi Amanata,inaji ajikina zanyi kewarki sosai..”Da sauri ta dago kanta tana kallonshi kafin tace cikin sauri”are u Sure zaka yi kewata mallam..? Yana kallon cikin kwayan idanuwanta yace”Very Sure..Kefa zaki kewata..?Bata iya bashi amsa ba,sai kawai tayi dage ta kama lebenshi tana tsotsa da sauri rike kanta da hannu daya yayi,hannu daya kuma yakara mtseta cikin maranshi cike da salo Malika take sumbatarshi har sai da suka gaji kama suka saki juna suna maida numfashi,bisa kirjinsa ta lafe tana Fadin”Zanyi kewarka sau ba adadi mallam,kariga ka zama jinin jikina,rayuwata bazata iya tafiya ba sai da kai,ina nace maka bani son zama dakai akoda yaushe wlh nayi karya mallam,i so much luv u,don Allah karka bani ko bayan kayi aure..”Tafada hawaye na wanke mata Fuska.

   

Wani sanyi yaji ya Shiga cikin ransa,cike da farinciki ya damki Fuskarta da hannu biyu yana kallonta yace”Da gaske kina sona malika..”?Gyada mai kai tayi hawaye suna kwaranyomata,Bakinta ya sumbata kafin yace”Duk da yadda na lalata rayuwarki na toxartaki keda mahaifinki..? Hannayenshi ta damke tana Fadin”Da shine ma nakejin ka mamaye duka raina,kayi sanadiyar Chanza malika zuwa wata malikar dabam,in ko hakane ka taka muhimman rawa arayuwata mallam,ka koyar dani abubuwa dama,wanda ni banda bakin godemaka sai dai nayita maka addu”an Allah ya saka maka da gidan aljannah Firdausi..”

Bai samu zarafin mgana ba,illah matseta dayayi ajikinsa yana shakan kamshin Turarenta,cikin wata murya yake fadin”kinsa me? bai bata zarafin mgana ba ya cigaba da cewa”Nima sai daga baya nadinga jin Abunda na aikata gareki ban kyauta ba,mussama ranar danaje daukanki agidanku naji matukar kunyar yadda Daddy ya karbeni batare da yayi Duba da irin Tozarcin dana miki ba ya karbeni hannu bibbiyu kuma wani karin nadamar tawa yadda yabani ke batare da Gaddama ba,ranar naji kunya sosai..”Mirmishi tayi kafin tace”Ni kuma abu daya ke ban haushi a abunda kayi min in na tuna..? 

Dago kanta yayi yana Fadin”Menene shi..? Gira ta matse tana Fadin”Har ka manta..”Tafada tana hararanshi,ware ido yayi kafin yace”Srry gayamin don Allah..”Yafada yana Shafa dogon hancinta zuwa karamin bakinta,Shagwabe Fuska tayi kafin tace”Yadda ka karbi Virginity na da karfin Tsiya mana..”Tafada tana Wulkamai ido cike da salo,Mirmishi ne ya Subucemai wanda sai da duka fararen hakoransa suka bayyana awaje,hannunta ya riko yana Shafawa har zuwa saman kirjinta yana mirmishi kafin ya gangaro zuwa katon cikinta,cikin husky voice yace”Ni kinga wannan daren D Unforgtable Night and moment kenan bazan taba manta wannan Daren ba..”Yafada yana Shafa cikinta yana wani munafikin dariya.

Fuska ta kwabe tana kallonshi kafin tace”Saboda mene…? Hannunsa ya dora bisa lebenta yana zagaya babban yatsanshi dashi yace”Baki sani ba..? ta gyada kai tana kallonshi Yar dariya yayi kafin yace”Dare ne mai cike da Tarihi ,dare ne da kika Shayar dani wata zuma mai dadi wanda banta zaton akwaita ba,Wlh tallahi i can Explain buh abu daya na sani ke ta dabamce domin Haryanzu kina kan Shayar dani wannan zumar,sai dai na ranar is so Sweet and special..”Yafada yana kanne mata ido daya,Dariya da kunya suka kamata,sai takaimai duka Kirji tana mai kukan Shagwaba dariya yake yana Fadin”Allah am Serious,ko zaki karamin ne,sai na kara tabbatarwa..”Wata uwar harara ta makamai kafin ta warci hannunta tana kallonshi,Juyawa tayi ta dauki yar jakarsa wacce ya sanya kaya ta rataya tana Fadin”Ni..? ai yanzu mun tsufa abari amarya tazo sai tabaka sabuwar zumar,muje na takamaka kaga dare nayi kuma,sadiq karya ga kamar ni na tsaidaka..”

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE