ZAFIN RABO BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 11 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 11 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ko da ya shigo parlor d’in baiga kowa ba, ba sakeena, ba kausar ba kamila, baisan me ya saka abun yayi mishi dad’i ba dan yau baya san had’uwa da matar shi, bedroom dinshi yayi, yana shiga ya fara cire kayan shi tare da fad’awa bathroom sai da yayi wankan shi sosai sannan ya fito, k’ugun shi d’aure da towel, yana fitowa yaji hayaniyar su a waje, gabanshi ne yayi wani irin fad’uwa, barin ma jin muryar sakeena da yayi, a hankali kamal yayi wurin closet d’inshi ya samu jallabiya ya zura bayan ya gama gera jikin shi da feshi shi da turare masu mugun k’amshi, sai da ya d’aure fuskar nan tashi tamau sannan ya fita daga d’akin.

+

Dukkan su na zaune tv a kunne, murmushin da ya gani a fuskar ta ne ya saka shi tsaywa cak, binta ya fara yi da kallo yana mamakin kamar ba ita bace jiya hawaye suka cika fuskar ta, yafi mintina yana kallanta, suma na parlor d’in basu san yana wurin ba, sai can kamar daga sama kamila ta juya ta ganshi,

“Lah ya kamal yaushe ka dawo?”

Maganar da tayi ce ta saka sakeena da kausar saurin kai idanunsu kanshi, suna had’a ido da ita tayi wani mugun had’e rai kamar bata tab’a dariya ba, sannan tayi saurin kwada idanunta, ya d’an yi sakwanni yana kallanta, sannan kuma ya maida hankalin shi kan kamila,

“Ban dad’e da shigowa ba”

Yana maganar yayi wurin su tare da d’an rankwashin kausar a kai yana jin ta fara mita, banza yayi da ita yayi wurin sakeena da take kan two seater idanunta nakan yatsun hannunta, tsugunnawa yayi a gaban ta a hankali, ya k’ura mata ido, sannan can ya kamo hannunta, yasan ta mishi kashaidin da ya daina tab’a ta ba da izinin ta ba, amma jikin shi ya gaya mishi baza ta tab’a tona mishi asiri ba duk abinda zaiyi mata, har lokacin bata d’ago ta kalle shi ba,

“Are you still angry?” A hankali yayi mata tambayar,

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE