MALIKA MALIK CHAPTER 11 BY JANAFTY
MALIKA MALIK CHAPTER 11 BY JANAFTY
Karfe 10 da wani abu suka isa anguwan su Malika,wanda Tundaga farkon layin har karshe jerin gwanon motoci ne na gani na Fada,anguwan tacika makil,Malika ko Tunda suka baro Zamfara take kuka har zuka iso katsina,Tun Saleem na bata baki har ya gaji ya kyaLeta.
Bai samu damar Shiga da motar ciikin haraban gidan ba,sakamakon yadda aka wangale get din Mutane sunyi Dafifi kowa nata daura alwala saboda lokacin Jana’iza ya kusa,Malika dataji kanta na sarawa ta dago kanta tana bin ko”ina da kallo,Zuruf tayi zata bude Murfin motan sai taji hannun Saleem bisa nata ya damke,waigowa tayi tana kallonshi wasu hawaye suna zubomata Kara damke hannunta yayi yana kallonta kai tsaye kafin yace.
“Kiyi min wata alfarma plz..? Girgiza kai tayi tana Kokarin kwace hannunta,shiko yaki sakinta ganin haka yasa ya Bude baki yana Fadin”kada ki yi kuka sosai,kinga fa Tundaga Zamfara kike kuka,har muka iso nan,don Allah in kika Shiga ciki ki tararro juriyanki kada kiyima Daddy kuka,ayanzu haka yafi bukatar addu’anki Fiye da na kowama..”Runtse ido tayi hawaye suna kwaranyomata kai ta gyada mai alamun taji,mirmishin yake ya saki kafin ya Kai hannun nata bakinshi ya sakarma wani light kiss,kafin ya saketa ta bude murfin motan da hanzari Ta fice tana Rufe Fuskarta da Gefen hijabinta kuka na kwace mata.
Shi kuma ya Fito daga motan ya nufi haraban gidan inda su Abbi ke tsaye shida sauran yan”uwan Daddy na Malumfashi,gaisawa sukayi yana kara musu gaisuwa,kafin shima ya koma gefe yasamu buta yafara daura alwala domin har an kammallah yima Daddy Sutura ana jiran lokaci ne ya cika a sallaceshi zuwa gidansa na gaskiya,kowa ka kallah awajen Fuska babu Annuri kowa yayi tagumi yana alhinin wannan Rasuwa ta Alhaji Abdulmalik Dankasuwa….
Itako Malika na Shiga Falon gidan ta tsaya cak tana bin kowa da kallo,gabadaya dangin Daddyn natane yan malumfashi suka cika Falon suna koke kokensu,wanda ada sune in ta gansu sun zo gidansu tayi ta fadan cewa sun zo maula sun cika musu gida,sai gashi yau sune suka zo su taru suyi kukan rashin da kuma Faduwar bango garesu gabadaya.
Nan idanuwanta suka kai kan Hajiya binta dake zaune gefe da dogon Hijabi ta carbi tana ja,Fuskarta ta kumbura saboda kuka,gefenta kuma Joda ce itama sanye da hijabi tana Sharan kwallah,Shigowar Malika shiya sa Falon ya dau Shuru kowa ya juyo yana kallonta cike da tsausaya domin ansa babu wanda akama mutuwa kamar ita.
Hajiya ta kalleta idanuwanta da suka sukayi jawur cike da kuka tace”Malika..”Takira sunanta cikin raunin da karayan zuciya,ai da gudu malika tatafi gareta ta Fada jikinta tana Fashewa da kuka,Rumgumeta hajiya tayi itama kukan take tana Fadin”Mun rasa Alhaji malika,mun rasashi lokacin da da ni dake muka fi kowa bukatarshi,wayyo Allah mutuwa tamana yankan kauna ta daukemana Alhaji lokacin da muke tsakar bukatarshi..”Take Fada tana kuka,Malika dake jikinta ta kara fashewa da kuka,cikin muryan kuka wacce ta Dishe take Fadin.
“Dama da gaske mallam yake Daddylove ya tafi ya barni..? Why..? meyasa zai min haka ? zai tafi ya barni cikin wannan Duniya mai cike da kunci ni kadai,ya rayuwata zata kare,wayyo ni Malika dama Allah ya dauki raina,nima na mutu abinne gawata kusa data Daddyna,domin babu Abunda zan tsinta aduniyar indan na zauna ba ni da kowa sai shi,gashi yanzu Babu shiii..”Tafada tana kara kife kanta akasa tana kuka harda jijjiga.
Wata wacce take kanwa ga Daddy tataso daga inda take ta riko Malika itama tana hawayen tace”Ashh malika bar Fadin irin wannan kalaman basu dace ba sam,ki na zaton Allah daya bamu shi bai Fimu sonshi bane? karki Manta gawan Mahaifinki na cikin gidanan kuma sai ki sakamai da mganganun banza da koke koke,yanzu ne fa zamu nuna mai mu masoyanshi ne ta hanyar neman masa gafaran Allah,gashi kema baki da lafiya ko so kike kijama kanki mtsala muna alhinin rashin Mahaifinki mukoma alhinin shiganki wani hali..? Girgizamata kai Malika tayi tana toshe bakinta da hannun kada kukanta ya Fito,Zaunar da ita tayi tana zama kusa da ita carbin hannunta ta mika tana Fadin”,Yita salati acikin ranki,Kibar kukan nan hakannan kada kijama kanki wata mtsalan Abdulmalik tashi ta kare ,sai dai mune muke cikin kila wa kalan Yaushe zamu mutu? yau ne gobe ne? bamu sani ba..”Take Fada tana Share kwallah.
Gabadayan Falon sai da kalamanta yasasu ta kwallah,itako Malika batayi gaddama ta karbin chasbawan tana karanta innalillahi bakinta na motsi ammh hawaye sun gaza daina gudu bisa kuncinta,haka Hajiya binta ma ana ta bata baki,ana mata Fadan tadaina kuka ita da zata Tallafin Raunin malika,ammh itama ta koma tana biye mata suna kukan da bashi da amfani,dole suka hadiye kukansu ammh fa zukata sun Raunana,gabba sun yi rauni suma.
Tashin hankali bai kara ziyartansu ba sai da akace Hajiya da Malika su fito su zo Falon waje inda aka shirya Daddy,domin sumai addu”a da ganin karshe,lokacin da Malika taci karo da gawan Daddynta kasa control din kanta tayi haka ta fada kanshi ta kamkameshi tana kuka mai taba zuciya kamar zata Shide,hajiya ce kadai ta samu daurewar yimai addu”an Fatan dacewa da kyakyawan mtsayi.
Malika kin sakin Gawan Daddy tayi Fadi take ita, Daddynta bai mutu kada su Fitar dashi,gashi ta rike makaran dakyau taki saki,sai da Abbi ya fita waje ya kira saleem yazo da karfi gaske ya bambareta jikin makaran yana lallashinta,ammh ita hankalinta ya bar jikinta,ganin tana Fizge fizge ne yasa ya Kara tsaurara rikon dayayi mata,har sukayi baya suna neman Faduwa,neman kwatan kanta take ita sai taje ta riko daddynta kada su Fita dashi,ammh Saleem bai barta ba sai da ya tabbatar da sun Fita da gawan waje kana ya Sausauta rikon nata yana Fadin”Haka mukayi dake..? Haba Malika stop don Allah baki ganin halin da kike ciki ne?”…Yafada yana kallonta cike da tsausayinta.