IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 8 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 8 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

lokacin Sulaiman ya karya kan motar ya shiga school of management studies domin daukar Iliyas. Tunda suka gaisa da Iliyas tayi shiru bata kara cewa komai ba sai kalle-kallen titi. Ta rasa dalilin daya saka Iliyas din yake yi mata kwarjini, sam bata iya sakewa matukar yana tare da su.
Hira sai ta koma tsakanin Sulaiman da Iliyas, sai dai duk rabin hankalin Sulaiman yana kan Safina wacce yake lura da yanayinta ta madubi, bai so shirun da tayi ba, ya so ace sun ci gaba da hirar da suka faro da ita, ya fahimci yanayinta ya sauya sabanin yanda suka tawo.

Kasa hakuriya yi ya juya yace mata “Akwai wata damuwa ne Safina? Kin san bana son ganin ki cikin rashin walwala”. Zuciyarta tayi sanyi saboda kulawarsa a gareta, ta yi niyyar ce masa babu komai amma sai taga ko ta fada masa haka ba yarda zai yi ba, akan haka sai tace “Wallahi wani Assgment aka bamu kuma gobe za a karba amma ni ko bincike ban yi ba balle har na rubuta”.
Sulaiman ya dan lumshe ido yace “Kin tabbatar wannan ne kadai damuwarki?”. Kai kawai ta kada masa alamar “Eh”. “Amma duk kika sa hankalina ya tashi?”
Inji Sulaiman.Tana dariya tace “Tuba nake yi, ban zaci zaka damu haka ba”.
Shima ya yi dariya yace “Kin kuwa san matsayinki a wajena? Ai da naga damuwa a wajenki ji nayi tamkar an yankeni da wuka kuma kice baki zaci zan damu ba”.
“Ai hakuri ba zan kara maimaita hakan

Www.bankinhausanovels.com.ng
ba”.”Serious?”. Girgiza kai tayi alamar amsawa “Serious”.”Wannan wane irin Assigment ne yake neman wahalar min dake bari muje gida sai mu tarar masa domin muga bayansa”. Tayi murmushi “Karka damu ai ba mai

wahalar bane, nima dan ban zauna masa bane amman yanzu dana zauna zan gamashi”. Iliyas ya tabe baki yace “Iska na wahalar da mai kayan kara” A cikin ransa amman a zahiri bai ce musu komai ba har suka kaita gida, sai a lokacin ne ya yi mata sallama suka juyo suka taho gida.
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, watanni shidan da aka diba na bikin Rahama sun cika, makwanni uku kacal suka rage a daura aurenta da agonta Idris. Tuni shirye-shiryen suka yi nisa a wurin Safina uwar son bidi’a tsare-tsaren yanda bikin zai kasance take yi tamkar bikinta za ayi.
Lefe aka fara kawowa duk da dai lefen bai gamsar da Safina ba amma sai murna take yi domin ita kwata-kwata bata iya hassada ko kyashi ba, tana matukar dokin bikin saboda shi ne bikin ‘ya mace na farko da za a yi a gidansu gashi kuma tana ji da Rahama domin ta hakkake duk duniya ba ta da kamarta.
Ranar juma’a bayan sun tashi daga lakca Nafisa ta biyo Safina domin taga lefe. Akwati uku ne da kit kayan cikin akwatunan madaidaita ne lefen ya yi daidai a wajen duk wani mai wadatar Zuci. Sun tarar da wata kawar Rahama, Fatima itama ta zo ganin kayan, tana ta ganin kayan tana ta yabawa, ita kuwa Nafisa dagawa take yi tana tabe baki tamkar wacce aka yiwa dole, Nafisa tagama gani sai tace “Ina sauran kayan?”.
Rahama tace “Ai suke nan”.Fatima kuwa data gama dubawa sai tace”Kaya sun yi kyau, Allah ya samu a danshin ku”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nafisa ta yi farat tace “Ya sakı a danshinta dai, ki daina hadawa da mu kar mala’ikun amin su amsa”. Maganar Nafisa ta zowa Fatima da bazata inda ta saki baki tana kallonta, Nafisa kuwa ko ta kanta bata sake bi bata maida dubanta da Rahama “tace “Ke kuwa Rahama me ya yi miki zafi kamar wadda tayi kwantai ake neman kai da ita? Gaskiya ki sake tunani kar kije kiyi abinda zai dawo ya dame ki daga baya, haka kawai ance aure hutu me zai kai ki gidan wahala? Ni wallahi naji kunya yanda Safina take zuzuta bikin nan tana cewa naga kayan lefe. Gaskiya ni har jikina ya yi sanyi”. Tana rufe baki Safina ta karbe.
“Nima babu yanda banyi da ita ba, nayi iya yi akan ta rabu da Idris din nan amman taki, dan haka na rabu da ita taje ta karata”. Cikin kunar zuciya Rahama tace “Abin ma har da cin mutunci?”.Safina tace “Babu wani cin mutunci Rahama maganaçe ta gaskiya kuma kin fi kowa sanin tsakanin mu babu boye-boye, idan ban fada miki ba wa kike son ya zo ya fada miki?, gaskiyar Magana da sake domin ba zamu gayyato kawayen mu a zo ana jin kunya ba, kin tsaya wata soyayya kamar in an yi auren soyayyar za a ci”.
Rahama tace “To me akai da idan muka yi aure ba zai iya rike niba?”. Ai alamar karfi tana ga mai kiba”Inji Nafisa.
“Ni dai na ji na gani, sai ku barni da
ra’ayina” Tana gama fadin haka ta fice daga dakin. Da aka tashi sayen kayan daki Safina ce akan gaba wajen fadawa Babansu irin kayan da ake ya yi, da ita aka je sayen kayan dakin,kayan masu kyau na burgewa aka saiwa Rahama duk abinda taga ya burgeta sai tace a saya, da kudinta ma ta sayi wasu abubuwan burinta kawai bikin ya yi armashi. Inna kuwa ji take kamar ta shake Safina dan haushi saboda rashin zuciyar da take nunawa da irin gandokin da rawar jikinta akan bikin ita ko kunya bata ji.
Kawayen da Safina ta gayyata har sun fina amarya yawa, shi yasata shiryawa karya sosai a bikin. List tayi na irin abubuwan da suke bukata da total din kudinsu a takarda ta baiwa yaya Isma’il tabaiwa yaya Abbas sauran ta baiwa Ango idris tace sune abubuwan da suke bukata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kuwa Ango nunawa ya yi babu wata damuwa zai basu kudin da suka bukata din, a ranshin ya san wannan shirin Safina ne kawai amma amaryarsa Rahama ba haka tace masa ba, walima kawai za su yi kuma makarantar Islamiyyarsu ceta shirya, amma a ransa babu wata damuwa tunda duk dominsu za a yi komai.
Rahama kuwa kasa Magana ta yi, banda tana gudun kunyata ‘yar uwarta data karyata abinda ta fada da yawunta, ganin idanun abokansa ne kawai yasa ta daga mata kafa, ko babu komai dai ai duk dan ita take ta wannan rawar jikin, ta hakikance babu wanda ke yi mata son da ‘yar uwarta tata take yi mata, bambancinsu daya ne kawai sabanin fahimta, fahimtarsu da rayuwa ta sha bambam.
Kwanaki biyu a tsakani Idris ya kawowa Safina kudin data bukata ba tare da gazawar ko kobo ba, har ma abinda basu nema baya yi musu domin kuwa ya kama musu hall din da zasu shirya dinner har ma ya biya kudin, hakan ba karamin dadi ya yi wa Safina ba. Biki ya tafi cikin tsari kamar yanda ta tsammata, kuma Idris ya fitar da ita kunya, haka shima gwaninta Sulaiman ya fitar da ita, ya shiryo tashi gudunmawar ya aikowa amarya wacce ta zamo abar alfahari a wurin Safina ace ga gudumawar saurayinta Sulaiman.Ranar dinner kawayenta suka yiwa
Rahama kwallıya ta garari, leshine golden colour da gwaggwaro mai ruwan zuma irin adon jikin leshin, sai takalmi da wata masifaffiyar purse suma ruwan zuma, sun fito da ita amarya sosai. Safina da kawayenta kuwa nasu leshin sky blue ne mai fararen filawa da kuma fararen gwaggwaro masu zaiba, takalma da jakankunan su ma fararen ne masu zalba, sun haskaka wajen sosai, kowa ya kalle su dole ne su burge shi.
Haka aka kwashi shagali, an yi biki lafiya kuma an gama lafiya, Safina kan ta sha yabo a wurin ‘yan uwa da abokan arziki bisa irin gagarumar rawar data taka a sabgar duk da dai da ma can an san mai yice amma bata taba yin wanda yakai wannan ba. Haka aka tattara amarya aka kaita gidan mijinta kowa ya watse cikin farin ciki.
Duk tsawon lokacin da suka shafe suna soyayya da Sulaiman, Safina bata taba zuwa gidansu ba sai a wannan sallar ya matsa mata lamba akan taje ta gaida mahaifiyarsa, yanzu da babu Rahama sai ta nemi rakiyar Nafisa, sabo tirken wawa, tayi kewar Rahama sosai, sun saba komai tare suke fadi tashi, suyi fadan su kuma su shirya duk a loikaci guda, itama bata so Rahama ta rigata aure ba, dan dai kawai har yanzu bat agama yanke shawarar abinda ya dace da ita bane.Da zata tafi Inna ta hada mata kayan arziki ta kaiwa mahaifiyar Sulaiman din, domin Inna tana matukar kaunar Sulaiman ba ta da gwani sai shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sulaiman ne ya zo ya dauke su a motar Iliyas, a bakin titi ya yi parking domin mota bata shiga lungun nasu, tun anan Nafisa ta ware ido tana kallo Sulaiman ya yi musu jagora har cikin gidan, gidane na gargajiya amman babu laifi da anga yanayin gidan ansan gida ne na masu rufin asiri, kofar gidan a shafe take tas-tas da sumunti, dakali biyune a kofar gidan, bayan an wuce soraye biyu za a iske makeken tsakar gida wanda aka rufe fiye da rabin shi da rumfa, a cikin rumfar akwai dakuna guda hudu jere reras, komanne daga dakunan cikin da falone, a can soro na biyu dakin su Sulaiman yake da sauran matasan gidan.
Tarba ta arziki da girmamawa aka yi musu, saboda kara a dakin kishiyar mahaifiyar Sulaiman aka sauke su, kannenshi suka rika zuwa suna gaishesu daya bayan daya, haka abokan shi suka rika shiga suna gaisawa, Safina sai mamakin yadda akai kowa yasanta, to ai daman duk wanda yasan Sulaiman yana da labarin Safina domin bashi da buri sai ita, duk sun santa a hoto a zahiri ne kadai basu taba ganinta ba, akan haka suke ta nan-nan da ita.
Ita kuma Nafisa ta kasa sakewa sai takurewa take yi guri guda sai kallon kowa dai-dai take yi a kaskance, duk abubuwan da aka tara agabansu babu wanda ya isheta kallo, da alama dai gidan da mutanen gidan basu yi mata ba. Sulaiman ya zazzagaya dasu gidajen yayyensa maza dake cikin unguwar tasu, duk inda suka je aka yita ina kasa ina ka aje da su, kowa yasan labarin Safina. Bayan azahar kuma ya kaisu gidajen ‘yan uwanshi mata a makwarari da hanga duk a cikin birni, daga karshe kuma ya kaisu gidansu Iliyas domin su gaisa da Hajiyarsa, sai aanan Nafisa ta saki jikinta har tasha lemo kasancewar gidansu Iliyas gidan bene ne ginin zamani kuma ‘yan gidan ‘yan book ne wayayyu, duk da cewar suma ba masu kudi bane amma sun fi su Sulaiman karfi nesa ba kusa ba.
Anan ma an nuna musu karamci da girmamawa fiye da yanda suka zata, ko ina faram faram ake da su ga alherin da ake cikasu da shi, da ace Safina mai zurfin tunani ce wannan kadai ya isheta ta daga hannu ta yiwa Allah godiya tare da yin farin ciki samun surukai nagari, amma ita sam bahaka ta so ganin su Sulaiman da danginsa ba, gaba daya taji jikinta duk ya yi sanyi gashi ta lura da yanda Nafisa ke kallon komai a kaskance, haka ne ya kara karya mata gwiwa.
Suna komawa gida Nafisa kamar jira take su shiga dakin Safina, cikin yankwana tace “Wai dama Sulaiman dan cikin wannan surkukin lungun ne?”. A kokarin Safina na sharewa tace “Eh”. “Amman gaskiya bai dace da zama a irin wannan lungun ba, yanzu haka zai aureki ya kai ki lungun dako mota ba ta shiga?” Ta dan tsahirta ko Safina zata ce wani abu amma shiru bata ce komai ba, daga nan ta dora da cewa “Wai sana’ar me Sulaiman din yake yi?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“A kwari yake”. Safina ta amsa a takaice. “A kwari?” Nafisa ta yi tambayar cikin mugun mamaki tamkar wacce aka ce mata dan fashi ne “Wai wane shi Sulaiman din nan domin ba haka na zace shi ba?”
Safina ta sanar da Nafisa duk abubwan data sani game da shi, tana rufe baki tace “Kuma kin san haka kike tare da shi? Gaskiya bai dace da ke ba, ai kamata ya yi ki auri dan bako wayayye ba irin wadannan kananan ‘yan kasuwar ba, ajinki da kimarki duk sun wuce nan, gaskiya nama raina wayonki Safina”.
“Wai me kike nufi ne? so kike in rabu da
shi kenan?”. Nafisa tace “Aa ni bance ki rabu da shi ba, amma dai ya kamata ace kin san abinda ya dace da ke”.
Safina tace “Amma kin fi kowa sanin cewar
Sulaiman ya dade yana sona?”. “Nifa bance dole ki rabu da shi ba, amma zama da saurayi daya ba naki bane tunda dai ke ba karamar yarinya bace, kullum bukatar ki karuwa take yi, wannan kasuwanci na Sulaiman ba zai dauki hidimominki ba, dan haka kiyi amfani da damar ki kawai, a ki dinga yagar rabonki a jikin duk wanda ya zo wajenki kina kashe gararin gabanki”. Safina tace “Ya kike tunanin Sulaiman zai ji
idan yasan ina kula wasu samarin?”. “Bari za ki yi ya gane? Ke sai kace ba mace ba? Duk kawayen nan namu da kika ga suna
fantamawa aka ce miki saurayi daya suke kulawa?”
Da wadannan shawarwari Nafisa ta
sauyawa Safina tunani ta amice zata fara kula samari duk da dai ba soyayyar gaskiya zata yi da su ba, zata biye musu ne kawai dan ta amfana da abin hannunsu amma gaskiya lamari babu wanda zata so kamar Sulaiman a cikin ranta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Har kullum matsalar Safina ita ce dogon buri, zarmiya da kuma son abin duniya, gata da daukar zugar kawaye ko yaushe ba ta da ra’ayin kanta, duk son da take yiwa abu da zarar an zugata nan da nan sai ta sauya ra’ayi, mace ce mai raunin gaske.
Haka al’amarin karatun Safina ya ci gaba da mirginawa cikin nasara, babu abinda ke gagararta, kwakwalwarta na da yalwa fahimta duk abinda ake koyar dasu kuma tana da kishin karatu, bata fashi saida wani dalili mai karfin gaske, yanzu haka sun yi nisa a second semester suna dab da fara jarrabawarsu ta end of session.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page