MISBAH CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI
MISBAH CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI
A wannan sati biyu mama tayi dukkan iyawarta da dagewarta akan Shamsu da farida,taga sun saki jiki da juna ,da kokarin nuna musu su rungumi kaddara suyi ibadar aure,su manta komai. In sunyi haka tabbas basu yiwa Allah butulci ba ,kumansun yarda da kaddara kamar yadda ake so kowane musulmi na kwarai ya yi. In sun haka kuwa Allah zai sa albarka a rayuwar su,ya daga darajar su a duniya da lahira.
Da irin wannan maganganun na mama yasa suka saki zuciyar su,musamman ma dai farida ta riga ta saduda,ta daura damarar manta baya,ta kuma cusa soyayyar mijinta da Allah ya kaddara mata a zuciyar sa.
A satin biyin ta koyi abubuwa da yawa ,don haka tayiwa mama godiya sosai,gami da mata alkawarin zama mace ta gari,saliha ga Shamsu,zata yi kokarin kawo farin ciki da kwanciyar hankali tare da nutsuwa a rayuwar Shamsu ,ta riga da ta amince,ta karbe shi matsayin mijinta.
Wannan magana tayiwa mama dadi matuka da zancen da farida ,tayi ta saka mata albarka.