KASAR WAJE CHAPTER 4 BY MARYAM DATTI
KASAR WAJE CHAPTER 4 BY MARYAM DATTI
Bayan Yusuf ya gama aikin yamma na pool sauri ya ke yau ya dawo gida yaga hayfa gashi gobe bufday d’insa na 27yrs gashi gobe hayfa zata fara aiki zaiyi kokari suyi celebrating ko yaya ne+
********
Tunda ya tashi da asuba bayan yayi sallah yana tsaye kanta yana tunanin abinda zai had’a musu na karyawa kafin yasir ya iso ta fito d’aki ya juya yana kallonta
Tana sanye da doguwar rigar Sheraton dark pink ta matseta kmar da fatar jikinta aka auna d’inki tayi d’auri ta d’an bar gaban kanta gashin a kwance sosai tayi kyaw na fitina ga k’irjinta a cike dam hayfa akwai baiwar k’irji
Wani irin yawu Yusuf ya had’iye, ita yunwa ya fito da ita!
Fitowa yayi daga kantar yazo har gabanta ya d’ago fuskarta ya fara mata wani zazzafan kiss
Itama batasan ya akayi ba ta fara tayashi hannunsa ya rik’o nata ya had’a yana ci gaba da kissing d’inta na fitina kai sai gashi ya mannata da k’irjinsa sosai hannunsa na k’ugunta
sunyi nisa suka ji Yasir na k’ok’arin bud’e k’ofa da d’an sauri hayfa ta janye jikinta ya shiga d’aki
Zama tayi gefen gado ta rik’e kanta tana tanbayar kanta “mai yasa ta fara biyewa wannan talakan da ba zama tayi da shi ba”?
d’an ajiyar zuciya tayi tace in kuma bana sakar masa jiki bazan samu damar sanin kasarnan ba bare har na samu na tafi a lokacin dole ya bani takarda na nema kamal mu shirya na fara karatuna da wannan tunanin taji nutsuwa a zuciyarta tana zaune taji yasir na cewa to ka yiwa ogan café visarta ya k’are?
Yusuf yace eh kasan ana d’an d’aga k’afa wai bayan wata kafin hukuma ta shigo ciki kuma IA zan nema wani aiki gobe bayan pool wanda kaga in na had’a da café da pool da shi zan samu na ansar mata visar ko yaya ne
Yasir ya ce gaskiya tayi dace sosai da samunka a matsayin miji inama da Hamdiyya ce ta samu miji kamar ka
D’an murmushi Yusuf yayi yace meyasa kace haka?
Ita kanta hayfa ta nutsu tana saurarsu
Yasir yace ka duba yadda auren nn yazo maka babu shiri amma duk da haka baka tab’a danasanin auren ba sannan dukda nauyi da matsaloli da kake dashi kullum burinka sauke nauyin matarka da bata hakkinta kana burgeni sosai ba don nasan yadda wannan gimbiyar ya saye zuciyarka ba da na baka hamdiyya nasan ko bana raye ba zata tab’a kukan auren miji kamar ka ba!
Ajiyar zuciya hayfa tayi
Shima Yusuf ajiyar zuciya yayi yace “nagode”
Yasir yace yau wai me za muyi ya kamata muyi celebrating ko yaya ne
Yusuf yace eh ina tunani IA
Yasir yace ni zanyi komai sabida dama ban bada gudunmawar bikinku ba, wai ita madam da zata fara aiki yau ya za kuyi?.
Yusuf yace ay ita nata kamar tym d’in Gizela ne 4:pm zata fara ta tashi sai lokacin tashinmu d’aya
Yasir yace gaskiya ka fiya son yarinyarnan yanzu aikin nn da zai sosai kudin zai taimaka maka amma ka bar mata Allah yasa tana sonka kamar yadda kake sonta
Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace munyi latti muje
Fita suka yi duka!
Yayinda hayfa ke zaune duk jikinta ya mutu jin hirarsu
STORY CONTINUES BELOW
Toh shi yaushe ya santa ya ke sonta haka?
Batada ansa ta mik’e ta duk jiki ba k’wari ta fito ta hada tea da bread ta zauna tana karyawa tanata tunanin hirar yasir da Yusuf. A Nigeria ammah ta sayar da waya 310k kash aka biyata a kasuwar makarfi plaza ta wuce taje ta tsaya conditions road kabala ta saya kujeru 150k ta biya ta saya generator 45k tayi d’an cefanen gida domin mijinta gyaran computer yake a kasuwar royal wataran ya dawo da kudi wataran babu dama ita ke rabin hidimarta shiasa duk burinsu kada hayfa ta shiga irin rayuwarsu
Bayan ta dawo gida tayi wanka tana falo yara suka dawo laraba ta cire musu kaya suka yi wanka suka ci abinci gaz ma ya k’are ta bawa laraba kudi taje refiling
Tana falon masu kawo kujeru suka iso kujerun sunyi kyaw sosai tana kallonsu tana k’arawa auren hayfa da yusuf albarka tana cewa tunma auren baije ko’ina ba kujerun masu L ne da 1sitter aka jera falon yayi kyaw bayan tafiyarsu ta fara tunani duk wata in hayfa Tana turo mata kud’i da ita da iyayenta da y’ar uwarta sun kusa fita wahala har abada
d’an murmushi tayi a ranta tana tunani wannan na d’aya daga cikin dalilinta na k’in kamal sabida yadda mutane zasu saka musu ido a gane daga jikinsa suke samu su da iyayensu amma Yusuf kuwa basu da matsala ba d’an Kaduna ba ne gashi babansa ya rasu shi yake jan ragamar arzikinsa ga shi ance danginsu ma can da nisa har sokoto
Sosai amma ke k’ara godewa Allah da samun Yusuf a matsayin wanda zasu cika burinsu da shi
Wayarta ta d’auka ta yiwa hayfa msg mai cike da nasiha da rarrashi akan ta rik’e Yusuf shine cikar burinsu da fitarsu kunya a idanun duniya.
Hayfa na d’aki a kwance ta gama gyaran gida tanata tunanin aikin da zata fara wannan aiki kuma sai asar ba safiya ba wane irin office ne wannan
d’an tsaki tayi tace ko da yake komai na turai daban da na Africa tana cikin tunanin su Yusuf suka shigo gidan
Yasir ya d’an kishingid’a falo inda Yusuf ya wuce d’aki direct
Ganin tana kwance yayi sallama muryarsa kamar ba ta namiji ba
Ansawa tayi a hankali saidai bata tashi daga kwancen ba
Tura k’ofar d’akin yayi ya kulle ya jingina bayansa da k’ofar yace “ki shirya muje kada muyi latti”!
a hankali ta mik’e yana kallonta doguwar riga ce jikinta kamar ko yaushe ya d’ameta ta shiga bayi ta wanke fuskarta dama tayi wanka ta d’an gyara fuskar ta d’ora abaya mai bud’ad’en gaba ta saka flat lopas tayi kyaw sosai
Kallonta Yusuf ke yi cike da so zata shafa humra taji muryarsa “ah ah kada ki saka”
d’an sakin baki tayi tana kallonsa ya rik’o hannunta ya jawo ta jikinsa yana mata wani irin kallo da nan da nan yasa gab’ob’inta suka fara sanyi
Yusuf ganin abinda yayi ya d’anyi yayi d’an tasirin sata saduda yayi murmushi yace “mu je” yana rik’e da hannunta itama ta kasa cire hannun suka fito falo