HEEDAYA CHAPTER 47 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 47 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Khaleel na kwance saman 3 seater a parlonsa, yyi nisa tunanin da yake idonsa na kan pop din parlon, a hankali ya 

juya yana kallon wayarsa da yyi vibrate a gefensa, ganin me kiran nasa ya ki dauka har ya katse, sake kira aka yi, ya 

mike xaune da kyar ya daga kiran yace “You called bana jin ka daxu kuma ka kashe waya gaba daya, What’s up?” 

Muryar Oga Arne ya ji yana dariyar bosawa, Khaleel yyi shiru ya sake kallon screen din wayar yaga number Zayyad 

ne ya katse wayar ya kashe gaba daya ya jefar nan gefensa ya koma ya kwanta ya lumshe ido xuciyarsa na bugawa…. 

Mami na kallon katti ukun dake kanta a tsaye cikin wani daki ko wannensu rike da bindiga, tana son magana amma 

ta kasa cewa komai sai hawaye, Ashnaah ma sai kuka take tana shigewa jikin Mami, fuskarsu dake boye cikin face 

mask shi ke kara tsorata yarinyar, cike da karfin hali Mami tace “Ku fada min me ku ke so daga gareni?” Bbu wanda 

ya tanka ta cikinsu da alama gadinta kawai aka ajiye su suyi, Ta rungume Ashnaah tana lallashinta tana karanto 

addu’o’i a xuciyarta na neman tsari da sharrinsu. Shuraim bai yarda ya hada ido da Heedayah dake tsaye tana 

kallonsa ba yace “Close the door” ta kalli kofar sannan ta kallesa, kin xuwa ta kulle kofar tayi kuma bata ce komai 

ba, ya kalleta suka hada ido yace “Baki ji me nace bane?” Tace “Toh saboda me?” Mikewa yyi ta koma gefe da sauri 

tana kallonsa kamar xata yi kuka, ya isa gun kofar ya kulleya juyo yana tsaye wajen yace “I want to ask you 2 to 3 

questions” Ta d’an yi shiru, sai kuma ta gyara tsayuwarta tace “Ina ji” Ya jingina da kofar bai yrda sun sake hada ido 

ba yace “And promise to say the truth… Nothing but the truth” ita dai tayi shiru tana jin sa, yace “Kin tuna lkcn da 

Abba ya kawo ki gidanmu ko?” Ta gyada masa kai, yace “Good, daga lkcn xuwa ynxu shekara nawa kenan?” Still 

not looking at him tace “Shidda” Yace “Alright, a cikin shekara shiddan nan can you plss remind me ko na ta6a cutar 

ki?” Kura ma carpet din dakin ido tayi trying to digest what he just said, bata san lkcn da tayi murmushi ba don ba 

karamin dariya tambayar ya bata ba, yana kallonta ce “Ina sauraron ki” tace “Wani irin cuta kenan?” yace “Duk 

abinda a tunanin ki cuta ne” tace “Ni na manta” Yace “Baki manta ba, bani amsata” Tace “Toh idan ma conscience 

dinka na judging dinka ne sbda abubuwan da yasan kayi, duk da ni dai manta pass dina balle in tuna abinda aka min, 

to I’ve forgiven you” Yace “My conscience can never judge me don nasan ban maki komai ba duk Shekarun nan….” 

Tace “Toh me ya kawo maganan nan yanxu idan kai kasan baka ta6a min komai ba?” Yace “Like, kina min kallon 

kamar wanda ya cuceki a rayuwar da kika yi gidanmu, always frowning when ever u see me, and many of that” Da 

mamaki take kallonsa tace “To dama mun saba magana ne da kai balle kace Ina frowning? I’ve known you to be 

someone that don’t bother about others, baka shiga harkan kowa, kowa ma baya shiga naka harkanka, to me yasa 

xaka yi tunanin xan dinga shiga harkan ka yanxu?” Shiru yyi yana kallonta, can yace “Kin fahimci haka nake yi ma 

kowa kenan” A takaice tace “Ba kowa ba, ai kana sake ma cousins dinka, ur sisters idan sun gaisheka kana amsawa, 

kana siya masu abubuwan da ya kamata….” Yace “Ke kuma fa?” Ta d’an kallesa tace “Do I need to tell you that” 

Yace “Bana maki abubuwan duk da kika lissafa kenan” ta buda hannu yace “You’ve said it” komawa yyi gefen gadon 

ya xauna yyi shiru, bayan minti uku tana kallonsa tace “Can I go” ya dago ya kalleta, a hankali yace “You can, one 

day you might understand all what happened during ur stay in our house” tace “Why not now?” Ya girgixa mata kai 

yace “One day” juyawa tayi ta nufi kofa har xata bude ta juyo tace “Sauran tambayar fa?” Ya girgixa mata kai yace 

“No need” fita tayi ta sake juyawa ta kallesa suka hada ido ta sauke nata idon ta kulle masa kofarsa ta koma parlor, 

Mumy sai kallonta take bayan ta fito, Yakumbo tace “Ya sha shayin kuwa?” Heedayah tace “Yana sha” Mumy tace 

“Toh kinga, tun daxu nake fama da shi ya ki sha, da ta kai masa ai gashi ya sha” Har kusan karfe biyar Khaleel bai 

yarda ya kunna wayarsa ba, yana ta kwance kan kujera sai juyi yake ya rasa me ke masa dadi, ga xuciyarsa yyi masa 

nauyi, sllh kadai ke tadasa daga kan kujeran yana dawowa masallaci kuma xai ci gaba da kwanciyarsa ko abinci bai 

ci ba throughout, bai ta6a tunanin Heedayah will be the first person to judge him ba, but ya mata uxuri coz she just 

have to, yana nan a haka har aka kira Magrib, ya mike xaune da kyar ya rike kansa, jin xa a tada sllh ya tashi ya 

shiga bandaki dake parlon ya dauro alwala ya fito ya wuce masallaci, ko da ya dawo makullin motarsa ya dauka 

yana tunanin yaje gidan Mami ko kar ya je, bai san yanda Heedayah xata kuma karbansa ba idan ya koma, amma ya 

ji bayan ita ma yana son ganin Mami ko xai d’an ji sauki, hira da ita na gusar masa da damuwarsa for sometime, 

mamakin Heedayah ya kasa barin ransa duk da uxurin da yyi mata, did he make a mistake telling her who he is? 

Gaba daya ya ma rasa takamaiman tunanin da xai yi ya ji sauki a xuciyarsa dake masa xafi sosai, ya jawo wayarsa a hankali ya kunna he need to share this with Zayyad, har yayi dialing number Zayyad ya tuna muryar Arne ya ji daxu 

maimakon Zayyad din, katsewa yyi xai kashe wayar gaba daya text ya shigo masa, number Zayyad ya gani, hakan 

yasa ya shiga text din yana duba content dinsa, mikewa yyi da sauri yana sake karanta message din xuciyarsa na 

bugawa, kunna datansa yyi kamar yanda aka umurcesa a text din ya hau WhatsApp bayan some minutes sai ga 

message din Oga Arne ya shigo ta WhatsApp din, ya bude yana xaro ido…. Video ya ga Arne ya turo masa, yana 

gama downloading video din ya ga Mami xaune kasa ta rungume Ashnaah dake ihu tana kiran Ammi, ya ji Muryar 

Arne yana cewa “Kina son sanin wanda ya bada umarnin dauke ki daga cikin iyalanki??” Mami dai bata ce komai ba 

hawaye kawai ke sauka idonta sosai, abubuwa da yawa ne ke dawo mata na shekaru masu yawa da suka wuce, 

rungume Ashnaah tayi sosai a jikinta tana Kuka, sai take ga kamar xa a kwace ta ynda aka ta6a yi mata, Arne yyi 

wani shegen dariya yace “Ki sa ma ranki salama, xaki ga wanda yasa aka dauko ki, sannan miliyan hamsin ake 

bukata na ransom” Mami ta girgixa kai tace “Ba mu da wnn kudin, bamu da dalilinsa, ku ji tsoron Allah ku ji tsoron 

gamuwar ku da shi….” Arne ya sake yin wani dariya sai kuma ya hade rai yace “Wa’axi xa ki mana, to kuwa xa mu 

aika ke da yarinyar barxahu yanxun nan….” Mami tace “Wnn sai lkcn mu yayi” Banda xufa bbu abinda Khaleel ke 

yi daga tsayen da yake yana kallon video din, exactly kalan tashin hankalin da ya shiga lkcn da Heedayah ta kwana 

gidansa da su oganninsa suka xo, Arne yyi video din fuskarsa dake lullebe cikin mask yana 6a66aka dariya yace “Sai 

ka xo Brainiac” Khaleel ya kalli time din da aka turo masa video din ya ga tun karfe biyun rana ne, bai san lkcn da 

ya suri makullin motarsa ba ya fice gidan almost running. Da karfi ya bude kofar parlon gidan da suke haduwa da 

oganninsa yana huci, Salim da Fago na xaune suna xuke xuke, Manga ya fito daga wani daki kamar an yi 

announcing masa presence din Khaleel, wani dariya duk suka saki a parlon kamar hadin baki, Arne ya fito daga wani 

dakin sannan Bala ko wannensu na ma Khaleel wani kallo yana murmushi, a nutse Manga yace “Welcome back after 

a year Brainiac….” Khaleel bai ce komai ba ya nufi sama don yasan a dakin sama Arne yyi video din Mami, Tsaye 

ya ga wani Ogan nasa a sama ya tare hanya da bindiga a hannunsa, Khaleel ya dakata xuciyarsa na bugawa, Arne 

yace “Ina kake tunanin xaka Brainiac? Snn me kake tunanin xaka yi?” Khaleel ya dawo gun Arne cikin tsawa yace 

“I’ve served you for many years, I’ve been loyal for many years, I need my freedom now, I need freedomm….” 

Naushi Arne ya kai masa a ciki ya fixgosa yana huci cikin tsawa sosai yace “Duk ranan da kake tunanin samun 

freedom daga garemu to mutuwa kayi Brainiac, we will be together till the end, you will continue serving us till the 

end, ko kana da wasu sama da mu a duniyar nan ynxu, nayi maka alkawarin a gabanka xan aika matar nan barxahu 

don hakan kadai xai sa kanka ya dawo dai dai kasan abinda kake yi….” Da karfi Arne ya tura sa ya nufi sama rike da 

bindigarsa yana huci, sanin halinsa da abinda xai iya aikatawa sarai yasa Khaleel ya taresa da sauri yace “Noo plss, 

bata da laifin komai Oga, ka gaya min yanxu me ku ke so daga gareni I promise to abide, don’t harm her plss” Arne 

ya tsaya yana huci yace “Sharadi uku xan baka da xaka yi abiding to… Abiding to the rules kadai xai sa mu bar 

matar nan da ranta, wllh… Kaji har na rantse maka” Khaleel da xufa ke karyo masa daga sama har kasa ya dake yace 

“Ina jin ka….” Arne yace “Yanxu xa mu tafi gun ta a matsayin kai ne oganmu gaba daya a nan, I want it to look like 

kai ma kasa mu dauko maka ita, snn xa ka bukaci amsan ranson na miliyan 50 don naga da maiko sosai tare da ita, 

snn daren yau muna da operation na dauke wata yar babban mutum kai ne kuma xaka dauko ta mun fi wata hudu 

muna targeting mun kasa dauketa, sharadin karshe kuma baxaka sake gigin bijire umarnin mu ba, idan kuma 

sharadin sun maka tsauri cikin mintuna kalilan xan aika matar barxahu, snn in sa a dauko min ‘yarta ma in kasheta, 

idan kuma ka kwafsa gaban matar wllh wllh a gabanka xan harbeta kaji har na rantse maka” Banda xufa bbu abinda 

Khaleel ke yi yana kallon Arne don ko wani kalma da ya fada hakan yake, baya xance biyu, snn ko dot din tausayi 

baya da shi a ransa, he can even do more than what he said…. Arne ya ciro masa bindigar aljihunsa ya mika masa 

yana kallonsa da jajayen idanuwansa yace “Mu tafi saman” Khaleel ya lumshe ido ya bude snn ya amsa bindigar a 

sanyaye ya shiga gaba Arne na biye da shi da nasa bindigar bayan ya rufe fuskarsa da Mask, Fago ne ya bude masu 

kofar dakin da Mami ke ciki da Ashnaah, Khaleel dake tsaye bakin kofar ya kallesa sannan ya shiga dakin, daga kai 

Mami tayi suka yi ido hudu da shi ta dinga kallonsa with so much shock ko kiftawa bata yi, Tunda Khaleel yake bai 

ta6a jin weakness irin na wnn lkcn ba, he felt like collapsing kawai, he wish this isn’t happening, Arne dai sai 

kallonsa yake da mayun idanuwansa yana pointing Mami da bindiga alamar yana kwafasawa xai yi harbi, Cikin 

rawar murya Mami tace “Khaleel???” Kallonta kawai Khaleel keyi ya kasa cewa komai, Arne na nunata da bindiga 

cikin tsawa yace “Kar ki sake kiran oganmu kai tsaye….” Khaleel ya jefa mata wayarsa ba tare da ya yrda sun sake 

hada ido ba yace “Ki saka number da xa a kira a bada kudin fansa” Kuka kawai Mami take sosai ta ma rasa abinda 

xata ce gaba daya ta shiga wani irin shock ne me iya ba mutum attack, kasa ci gaba da tsayuwa a dakin Khaleel yyi 

ya juya yace “A kawo min number idan ta saka” daga haka ya fita daga dakin, Arne yyi wani murmushi ta cikin 

mask dinsa, yyi ma Mami wani firgitattcen tsawa yana nuna ma Ashnaah dake bacci a hannunta bindigarsa yace 

“Baxa ki sa number ba sai na harbe wnn yarinyar dake kafarki” Jin abinda yace kuma bbu alamar joke tare da shi 

Mami ta dau wayar ta shiga dialing number Junaid tana kuka sosai, ya kwace wayar a hannunta snn ya fice daga 

dakin Fago ya kulle kofar da makulli ta waje. That same time Abba da Doctor da Baffan Junaid na tsaye parlon 

Mami ko wannensu is just short of words, gaba daya kukan kaka ya cika ma kowa kunne a parlon, Farida da Heedayah ma kukan suke cikin tashin hankali kamar ransu xai fita, Yakumbo dai banda xare ido bbu abinda take 

daga wajen da take xaune, ta kalli wnn ta kalli wancan kamar mara gaskiya, Junaid dai na tsaye ya jingina da bango 

a parlon yana kallon sama, duk dakiyarsa tashin hankalin dake tare da shi bai boyu ba, Ammi kam na xaune parlon 

bata cewa komai sai tagumi da tayi, Hajiya Zuwaira da kanwarta na gefen Ammi su ma, kowa dai ka gani a parlon 

hankalinsa a tashe yake sosai, cikin kuka kaka tace “Toh kai da ka hango motarta ta window me yasa baka fito da 

sauri ba Amadu, ko ofishin naku bashi da taga ne da ka yrda wnn abu ya faru? Kai ma fa sai Allah ya kamaka wllh” 

Abba dai bai bata amsa ba kansa na kasa, Kaka ta kara rushewa da wani kukan tace “Yau naga abinda ya isheni ni 

Patuu, gandareriyar mata haka ace mana an dauke ta a mota, ni dai wllh ban yarda ba baxan kuma yrda da wnn 

karyar ba, ta ya xata amince ta bisu kamar wata shashasha” a hankali Yakumbo tace “Kun dai tabbatar kun duba 

motar da kyau bbu Ashnaah” ita ma bbu wanda ya tanka ta a parlon, lkci daya ta rushe da matsanancin kuka ita ma 

tace “Bbu yanda Ashnaah bata yi xata bi ni gidan dubiya ba nace baxan je da ita ba, yau ga inda son gantalinta ya kai 

ta, ita yar uwar bbu ruwanta da biye biyen mutane wllh” Mumy ce ta shigo parlon da sallama a rikice bayan many 

interrogations tun farkon shigowarta layin domin kuwa tun daga farko har karshen layin sojoji ne da yan sanda har 

cikin compound din Mami, Mumy ta fashe da kuka sosai sai dai ba hawaye ta shigo parlon ta xauna ta saki salati 

tace “Ikon Allah ya fi da haka, ynxu abinda ya faru kenan ni Maryam, to Allah ya kubutar da Rahinah daga 

hannunsu alfarman annabi, Allah ka dubemu a sako ta cikin aminci, wnn duniya Ina xa ya da mu…” Yakumbo tace 

“Ae har da Ashnaah….” Wayar Junaid dake hannunsa ne ya fara ring duk aka juya ana kallonsa a parlon, Junaid na 

kallon Screen din wayar ganin bakon number ne ya daga ya sa handsfree, bbu ko sallama aka fara magana kamar 

haka “Anyi garkuwa da Mahaifiyarku ana kuma bukatar ransom na miliyan hamsin daga yanxu xuwa gobe da karfe 

sha biyu dot…. failure to comply xa ku tadda gawarta nan bakin layinku gobe da yamma, ur Mother’s life or 50 

million, more details to be pass to you later….” Kasa motsi Junaid yyi inda yake tsaye yana sauraron mutumin, kaka 

ta mike da sauri ta nufo Junaid cikin daga murya tana nuna wayar tace “Allah ya tsine maka, Allah yyi daidai da kai, 

don uwarka ajiya ka bamu…. shege kawai haihuwar rage jini haihuwar asara, ubanka ne ya bamu miliyan hamsin din 

ko uwarka, to wllh jikana soja ne sai yyi gunduwa gunduwa da rubabben namanka an jefa ma kifaye a ruwa, d’an 

Iska kawai munafuki…..” Yakumbo na tuntube ta taso ita ma tana kunduma nata xagin tana cewa “Idan ka isa ka xo 

ni ka daukeni d’an kaza kazan ka, dangin uwa ko na uba xa mu baka miliyan hamsin, ko wiwi ka narka kafin ka 

kira…” Abba ya nufosu da sauri yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, meye haka ku ke yi fisabilillahi” Yakumbo 

tace “Allah ya tsine masu muka ce, me xasu mana da Allah bai mana ba, idan sun isa su fadi inda suke yanxun nan 

in tafi in samesu mana, mutane matsiyata marasu tsoron Allah kawai” Barin wajen junaid yyi don ba ta su yake ba 

maganganun wanda ya kirasa ne ke dawo masa, don takaici Abba bai sake tanka su ba suka fita parlon tare da Dr da 

Baffan junaid don sanar ma yan sanda kidnappers din sun kira, Heedayah dai tun bayan da taji abinda aka ce ma 

Junaid a waya ta kasa kwakkwaran motsi inda take xaune, tunani iri iri ne ke kai komo a xuciyarta, A hankali ta juya 

ta kalli Farida, lkci daya ta tashi da sauri ta wuce sama xuciyarta na bugawa tana shiga daki ta kulle kofa a hankali 

tace “Khaleel???” Wani ihu ta fasa da ya ja attention din mutanen dake parlor….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page