RAINON Y'AN HUD'U BY Khadijat M Abdullahi

RAINON Y’AN HUD’U CHAPTER 3 BY Khadijat M Abdullahi

RAINON Y’AN HUD’U CHAPTER 3 BY Khadijat M Abdullahi

Www.bankinhausanovels.com.ng 

_____________Umar ne ya shigo hannunsa niki _niki da kaya, Goggo Na washe baki ta ce” A’a Ummaru har an fara yin hidimar, Ai ban sani ba ,da mun tafi tare ” Umar na dariya ya ce” Haba Goggo, ai yanzu na manyanta ,tunda na zama Baba, Abba dai bai ce Komi ba, Momy kam dariya tayi ta ce” Goggo!!! 

    Goggo na murmushi ta kalli Hanne ta ce” Mi kike so nayi, kamar y’an Hud’u ?

    Momy na dariyar mugunta ta ce” Goggo Dama zan fada maki ne, mu zamu koma dani da Abbansu, gobe Insha Allah Sai mu dawo, tunda dare ya fara yi ”

    Goggo bata yi musu ba, saboda nama da taga an siyo min “Nan dai Momy suka koma ita da Abba, aka bar Aunty Bilki…

Zama Goggo tayi tana tande baki ,ta ce” Uwar y’an Hud’u, ya jikin ?

  Banza nayi da ita, na fara cin nama, ina satar kallon Goggo, Jarirai kam Sai kuka suke tsallarawa, Umar ne ya ce” Sahibata in kingama, ki basu abincinsu ?.

    Kukan shagwa6a Na fara yi na ce” Haba Habibi, taya zan shayar da yara har guda hud’u, lallashina ya farayi, na kam tirje idona na ce” Ban San wannan ba, Goggo najin muna rigama, ga yara sun damemu da kuka, ta ce” Dan Allah Farida ki taimaki yaran nan ?

    Zun6ure baki nayi na ce”Haba Goggo ni gaskiya bazan iya ba,ga C.S in da akai min ina Jin zafinsa, ga rigimar wa’yannan yaran, a gaskiya na gaji…..

    Umar ne ya fara marairaice min ya ce” Sahibata !!! Ni ma Na ce” Sahibina 😂😂😂

Kallona yayi da Yarinya a hannunsa, ko daukaf jarirai bai iya ba, ya ce” ki taimaka min,Goggo ta ce” Haba Farida ke ki ka haufe su fa ?

  Gajiya nayi da maganar don haka, Na ce”Goggo ke ki basu susha mana ?

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE