INAAYA CHAPTER 1

INAAYA CHAPTER 1

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yarinya ce yar kimanin shekara sha shidda tana tafiya kaman tana tausayin kasa sanye take da abaya baka tasha stones ajiki ta yafa gyalen abayan ta, kafarta sanye take da slippers inta na hermès brown color ga jikarta rataye a kafadar ta kirar channel black color  hanunta na dama kuma sanye yake iwatch ce series 3. Fara ce batada tsayi sosai kuma ba guntuwa bace, sannan siririya ce tanada shape daidai mai kyau, fuskarta doguwa ce da dan karamin bakinta ga lips in ta pink shade da dogon hancin ta ga idanunta farare tas tanada hazel brown eyes. Kyakyawa yarinya ce dan saboda kyawunta baya misaltuwa she’s an epitome of beauty itace yarinyar da ake kira da INAAYA.1

Tafiya take cike da natsuwa kaman batasan taka kasa hannunta rike da wayarta iphone 8 da wata leda da aka rubuta shoprite a jiki, hannunta na dama rike da makulin mota tana tafiya harta isa wurin wata mota hyundai elantra 2018 ta bude ta shiga ta tada motar ta fara tuki a hankali. Cike da natsuwa take driving har ta isa bakin wani babban gate tayi horn  sai wani dattijo ya fito da murmushi a fuskarsa ya bude mata tazo shiga ta sauke glass tace malan aminu an wuni lafiya da murmushinsa ya ce lafiya kalau mamana me sunan yan gayu da murmushi ta ida karasawa wurin parking ta ajiye motar ta fito ta karasa zuwa wurin wata kofa babba ta bude ta shiga falo ne mai girma sosai amma ba mai tarkace ba kujeru ne ash color sai curtains navy blue da katuwar tv a jikin bango sai a tsakiyar falon centre table ne na glass mai kyau. Da sauri tana murmushi ta karasa cikin falon inda wata mata ke zaune tana kallo fadawa tayi jikinta tana dariya ta kama kunnenta tana cewa “sorry

mamii’am wallahi traffic ya tsaida ni” murmushi matar tayi mai kama sosai da inaaya  dan dai ita tanada dimple tace naji tou ki je ki ga abinci a dining ki ci tace ok my mamii i will freshen up first. Upstairs ta hau ta bude wani daki wanda yake mallakinta ta shiga daki ne mai girma hade da walk in closet da bathroom a ciki dakin dauke yake da Queen sized bed navy blue color da ash curtains sai wani standing mirror daga gefe da dan karamin fridge sai a dayan bangaren kuma study table ne da chair ajiye jikarta tayi da ledan datazo dashi a kan gado ta isa wurin fridge ta bude ta fiddo ruwa ta sha sannan ta tube kayan jikinta ta daura towel ta shiga bathroom wanka tayo tare da dauro alwala ta fito closet inta ta shiga ta ja stool ta zauna gaban dressing mirror ta fara shafa man ta ah hankali ta gama ta fesa turarukanta masu dadin kamshi ta shirya cikin doguwar riga me laushi ta dauko doguwar hijab ta saka tayi sallah ta zauna nan ta gama addu’a sannan ta dawo daki ta dauke ledanta da chocolates ne a ciki tasaka a fridge da daura dankwali a kanta ta fita parlour wurin mamii.

Tana zuwa tazauna kusa da mamii tana cewa “mamii kizo muci abinci tare ” kallonta mami tayi tace A’a ci ke kadai ni sai daddynku ya dawo turo baki tayi kaman zatayi kuka ta nufa dining inda aka jera abinci taja kujera ta zauna ta bude kula taga fried rice ta tabe baki ta rufe da bude dayan kulan da masa ne a ciki sai ta saki murmushi ta zuba guda uku a kan plate tasa miyanshi dayaji kayan hadi a hankali ta fara ci ta gama ta dauka plate in ta taje kitchen ta wanke shi saboda inaaya ba me son ba masu aiki wahala bace dawowa tayi parlour ta zauna tace mamii wai yaushe su aneesah zasu dawo nayi missing nasu gidan is so boring without them yar dariya mami tayi tace ai hutu ya kusa karewa sun kusa su dawo tsalle tayi tace yaaay! Dan harararta mamii tayi tace kefa bakisan kin girma ba kike tsalle haka turo baki tayi tace sorry mamii’am ta tashi tace bara naje na duba wayana sama ta hau ta shiga dakinta ta hau kan gado ta dauka wayarta taga 20missed calls from besty murmushi tayi ah hankali tace this girl is crazy sannan ta danna mata kira ringing uku tayi ta dauka tace inteeeee you crazy girl naga kin kirani har so 20 meya faru ne? ah dayan bangaren kuma cewa tayii you useless girl i have good news for you shiyasa guess what? Are you getting married cewar inaaya mtsww mumuu not that i am coming to Nigeria next week ihu inaaya tayi ta tashi tana rawa tana tsalle tace are you for real dariya inteesar tayi tace for real amma there’s a bad news two weeks kawai zamuyi saboda abba nada aikin yi to ai sai abba ya barki nigeria tunda yanzu hutu mukeyi cewar inaaya ko baya barinki murmushi inteesar tayi tace bansaniba sai munzo dai I’ll ask him then shiru inaaya tayi sai tace tou shikenan can’t wait sukayiyy dan fira tasu ta kawaye kafin tace ki gaida su ammah bye ta kashe wayar tana sauri ta fita da gudu ta sauka kasa tana ta ihu mamii! Mamii!! Da sauri mami ta fito kitchen tana lafiya inaaya me ya faruu mamii next week su inteesar zasuzo nigeria murmushi mamii tayi tace ai kece baki sani ba dama tace mamiii dama kin sani baki gaya mani ba tace eh dama inteesar tace a bari ta gaya maki dan turo baki inaaya tayi sai kuma tayi murmushi.

Asalinsu*
Alhaji abubakar geidam haifaffen dan garin yobe ne asalinsu fulani ne da matarsa da haj. Fatima wadda itama iyayenta yan garin yobe ne, suna da ya’ya shidda maza hudu mata biyu Alhaji usman shine babban cikinsu ana kiransa da BAFFAH da matarshi haj sa’adiya da yaransu biyar mata hudu namiji daya fareeha ce babba tana da kimanin shekaru 29 tayi aure da yaronta daya sai abubakar(abby) yanada shekaru 26 ya kammala karatunsa inda yake aiki a abuja yanzu sai maryam(aleesha) tanada shekaru 23 ta gama karatunta tana serving a abuja sai khadija shekarunta 19 tana karatunta a nile university tana karanta economics sai autarsu amina(mimi) tanada shekaru 16 yanzu tagama secondary school suna hutu wannan iyalan gidan baffah kenan da yake zaune a garin abuja da matarsa inda yake running business inshi successfully. Alhaji sulaiman shine na biyu wanda ake kira da BABA yana zaune a garin kaduna a inda yake aiki  da matarsa haj.hadiza tun bayan aurensu haj hadiza ta jima kafin ta fara haihuwa yaransu uku biyu yan maza sai mace daya sameer ne babba yanada shekaru 27 ya kammala karatunshi yana aiki a garin kano saura watanni biyar aurenshi sai ishak wanda yake shekaru 23 ya kammala karatunshi zai yi joining masters sai autarsu hanifa wadda a yanzu shekarunta 18 tana karatu a kaduna state university (kasu) tana karantar bsc biology.sai na uku shine alhaji ibrahim wanda ake kira da ABBA baya a nigeria tun bayan aurensa yake switzerland an kaishi aiki can da matarsa haj.salma yaransu hudu babban shine aliyu yanada shekaru 29 ya gama karatunshi yana zaune a london can yake aiki sai nasir  me shekaru 26 har yanzu yana karatu a nan switzerland inda mahaifinshi ya dawo da shi saboda yaki karatu duk inda aka kaishi bayan shi mahaifiyarsu ta jima bata sake haihuwa ba har ta fitar da rai sai tasamu ciki ta haifa yara yan biyu mace da namiji Ahmad da zainab(inteesar) wanda sukeda shekaru 16 yanzu sun gama secondary school daga su bata sake haihuwa ba.sai Alhaji umar wanda ake kira da DADDY  a garin abuja yake yana aiki da matarsa haj.Aisha yar maiduguri ce kanuri by tribe da yaransu biyar sai’d ne babba yanada shekaru 24 ya kammala karatunsa yana masters a us yanzu sai fatima(INAAYA) tanada shekaru 16 ta gama secondary school tana jiran admission yanzu sai kanwarta aneesah tanada shekaru 13 wadda take js3 yanzu a great heights academy a abuja sai yan biyu maza ammar da ayman shekarunsu 10 yanzu suna js1  suma a great heights academy. Sai haj. Fai’za wacce suke kira da AMMI tana zaune a bauchi wanda mijinta dan gamawa ne a garin bauchi alhaji isah sani gamawa suna zaune cikin kwanciya hankali da yaransu biyu adnan me shekaru 30 wanda yake a gombe yana aiki da matarsa fareeda yar gombe ce ita suna da yara biyu yen mata hayfaah da hayraah shekarunsu 4 yanzu sai kanwar adnan me shekaru 23 fatima(aleena) wadda take serving yanzu ta gama karatu. Haj. Rabi itace karama a gidan alh. Abubakar geidam ana kiranta da MOMMY tana aure a garin kano yaranta hudu duk yan mata Allah bai bata da namiji ba nafeesah(feenah)ce babba shekarunta 25 wata biyu da suka wuce akayi aurenta sai aisha(ummi) me shekaru 23 tagama karatu tana serving a garin kano sai farhana shekarunta 19 tana karatu a BUK kano tana karantar bsc nursing sai autarta saleema tanada shekaru 13 tana js3 a crescent international school kano wannan kenan.
+
Cigaba*
Inaaya ce zaune da mamii a parlour suna fira tace “mamii wai wa zaya dawo da aneesah daddy ne zaya tura driver? Kinga mamii idan driver ne inaso muje sai mu dawo tare saboda nagaji da abuja kuma na dade ban ga favorite anty ina ba” murmushi mamii tayi tace to masu favorite anty sai ki gayama daddyn naki idan ya dawo tace to mamii. Suna zaune suna kallon series a zee world har aka kira sallahn magrib tashi mamii tayi ta nufa daki sama tace inaaya tashi kije kiyi sallah tace to mamii tashi tayi tabi bayan mamii suka hau upstairs a tare daki kowa yawuce inaaya na shiga daki ta fada toilet ta dauro alwala ta fito a dauka prayer mat ta shimfida ta kabbara ta fara sallah tagama ta zauna tana karanto azkar in ta Ta gama ta koma kan sofa dake a dakin ta kwanta ta jawo wayanta ta kunna data ta shiga duba messages ta whatsapp taga messages dayawa from her other Besty sultana wacce suka gama same school da ita wadda take zaune a abuja da iyayenta itama.
Sultana~
Heyy
Bestfriend
Where are you?
I have gist for you
Keeeee
Inaayatuuuu
This girl your phone is useless
Idan help mutum ke nema har ya mutu kina can
Ineeeeeee
Ohhk ya sarah’s wedding date have been fixed💃🏻
Can’t keep calm ooooo
December ne bikin💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Byee.
Inaaya~
Heyy sweetheart
Sorry wlh ina tare da mamii muna fira tun dazu
Woooww are you kidding me
Yaaaaaaay💃🏻 can’t wait Allah yasa Alkhairi sai nazo
I have good news for you too inteesar is coming to nigeria next week💃🏻
STORY CONTINUES BELOW
Haka inaaya ta ci gaba da duba whatsapp messages from her friends and cousins tana replying ta gama ta kira ya sai’d ta face time ringing hudu tayi yayi picking sai ga fuskar wani kyakyawan saurayi ta bayyana a screen in inaaya fari ne da hancin sa dogo yanada beard da gashin kansa kaman na larabawa murmushi yayi dimple inshi ya lotsa sissy how far naa dariya tayi tace “ya sai’doooo nayi fushi you can’t even call your sister shikenan” hade fuska yayi kaman bashi yayi murmushi  ba yace keee waye sai’doo kin rainani ko yarinyar nan pouting tayi tace Allah ya baka hakuri bye dariya sai’d yayi yace scaredy cat hade rai inaaya tayi kaman zatayi kuka bai bar murmushi ba yace sorry sorry lil sis bazan sake ba sorry kinji sakin fuska tayi kadan tace to promise you’ll get me new phone idan zaka dawo smiling sai’d yayi yace done ma’am itama smiling tayi tace best bro ever i love you yace i love you too sissy, shiru tayi sai kuma tace so bro how’re you and your studies yace Alhamdulillah sis yasu mamii da daddy hope they’re all good tace mishi yeah we’re fine just that the house is boring without you especially now that aneesah and the twins are not around yace eyya sorry sis ai sun kusa su dawo and i’ll also come to visit very soon bude idanu tayi tace really yace of course dariya ta fara yi tana clapping kaman wata karamar yarinya tana cikin dariya aka yi knocking kofan dakinta waye tace da karfi bude kofan akayi yarinya ce da bazata wuce tsararsu aneesah ba ta shigo bakinta dauke da sallama tace yaa inaaya mamii na kira tace to fauziyya kice mata gani nan zuwa tace to ta fita juyawa tayi kan wayarta tace ohhk yayaaaa can’t cwait to see you talk tomorrow mamii is calling me byee yace ok sissy bye regards to mamii,daddy,aneesah and the twins tace InshaaAllah ya sai’doo hade da winking ya hade fuska ta sa dariya ta yi saurin kashe wayan chargi ta saka shi ta fito ta sauka kasa mamii na parlour tace mamii gani tace yauwa inaaya dama ce miki zanyi kinsan gobe za muje gidan baffah ki kwanta ki yi ta baccinki da kika saba kinji ko smiling tayi tace no mami bazanyi ba InshaaAllah tana rufe baki sukayi karan bude gate da rufewa tace mamii ga daddy nan ya dawo nasan shi ne ta tashi da gudu ta nufi kofa ta tsaya,tana nan tsaye sai aka bude kofan da sauri ta fada jikinshi tana hugging inshi daddyy na smiling mutumin yayi yace ohhh ni mamaana bata girma dariya tasa tace kaii daddy am just a baby fa yace to shikenan my baby na gaji muje parlour kama shi tayi suka shiga parlour mamii na zaune ta juyo tana kallansu gwanin burgewa ta tashi tsaye tana cewa daddy an dawo sannu da aiki ya gajiya smiling yayi yana kallon matarsa cike da so yace yawwa mamii gajiya kam akwai shi sai na yi freshening up naci abinci sai na huta tace to sannu yace yawwa haka ya nufa sama mamii ta bi bayanshi inaaya zamanta tayi parlour tana kallon indian film half girlfriend haka har su daddy suka fito ya canza kaya zuwa jallabiya ya fita ya nufi masallaci domin gabatar da sallah isha su ma inaaya da mamii yin tasu sukayi cikin gida suka gama.Bayan wani lokaci suna zaune parlour saiga daddy ya dawo nan suka hau dinning cin abinci shiru kakeji sai karan spoons da forks suna cin abinci saida suka gama fauziyya tazo ta kwashe plates in ta nufa kitchen dasu ta wanke suka koma parlour daddy ya canza channel zuwa news yana kallo yana shan fruit salad in dake gabansa sai inaaya tace daddy na kallonta yayi yace mamaana me ake so dariya tayi tace erm… dama daddy inaso idan za aje daukan aneesah kano mu je da drivern sai mu daukota mu dawo kallon ta daddy yayi na wasu seconds kafin yace ke kadai zaki bi driver mamaana tace eh daddy ai tare da aneesah zamu dawo plss daddy na wlh nayi missing mommy na dade ban ganta ba to daddy yace mata yace sai nayi tunani tace yawwa my daddy that’s why i love you smiling yayi mata mamii kam dama batace komai ba tana zaune tana kallonsu har suka gama.tashi inaaya tayi tace to mamii daddy goodnight natafi nayi bacci a tare suka ce mata goodnight ta nufa sama ta shiga daki, tana shiga taga wayarta na haske indicating kiranta akeyi saboda a silent take sultana ce ke kiranta tayi sauri ta daga hello babyy girl daga dayan bangaren sultana cewa tayi hello sweetheart ke kam kinyi wuyan samu I’ve been calling you tun daxu oops sorry ina can dasu daddy shiyasa dariya sultana tayi tace yayi yar daddy dariya suka sa gaba daya sai inaaya tafara cewa ehen! Wai ina ya sarah kince mata sai nazo Allah yasa Alkhairi tace eh yaushe zakizo its been long da mukayi hanging out you know i mish you awwn! You know i also mish you cewar inaaya “yeah I know you miss me so when are you coming inji sultana” I’ll come on Sunday InshaaAllah, but why not tomorrow no babe gobe gidan baffa zamuje to shikenan can’t wait for Sunday we’ll have fun sosai yesso inji inaaya soo intee is coming to Nigeria sultana ta fada da karfi eh manaa am so so happy we’ll enjoy this holiday to the fullest haka sukayi ta firan yanda zasu yi ta enjoying holiday nasu har 11 na dare sannan inaaya tace am sleepy Besty goodnight ohhk best goodnight ki gaida su mamii and yeah my regards to mimi gobe idan kunje gidansu ok InshaaAllah bye sweetheart ta kashe wayan sai ta dan shiga instagram tana scrolling tana liking pictures kadan kadan sai taga hoton wani saurayi mai kyau anyi posting a wani page northern blog wai wata ta tura picture nashi a taimaka ko handle nashi a sama mata she’s in love with him tabe baki inaaya tayi bata ko yi liking ba ta kashe data ta aje wayan side drawer ta kashe wutan dakin tayi addua cikin few minutes bacci ya dauketa.
Sound in alarm ne ya tayar da inaaya daga bacci ta tashi ta zauna kan gado na wasu seconds kafin ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, dogon hijab inta na sallah ta ciro tayi spreading prayer mat a kasa ta kabbara sallah tayi nafiloli sannan ta yi sallah asuba ta zauna a kan mat in tana karanta azkar inta har ta gama ta dauko al Quran tafara karanta suratul yasiin ta gama ta karanta suratul mulk cikin kira’ar ta me dadin gaske rufe Quranin tayi bayan ta gama karantawa da jawo wayarta taga karfe 6:30 komawa tayi kam gado ta kwanta har bacci yayi gaba da ita.karar buga kofa ne ya tashe ta daga baccin data koma ta tashi tana turo baki baccin bai ishe ta ba hakanan ta tashi ta bude kofa don ganin waye ya tashe ta da safen nan tana bude wa mamii tagani tsaye ta bata fuska tace sannu fatima kin kyauta sai ta juya ta wuce sai lokacin yayi mata occurring mamii tace zasu je gidan baffah ta tashi da safe, da sauri taje tana duba wayanta don ganin time tana dubawa taga past twelve da sauri ta fada bathroom ta yi brush da wanka ta fito ta shiga walk in closet nata taja stool wurin dressing mirror ta zauna tana shafa mai a jikinta da sauri take shafawa amma cike da natsuwa har ta gama ta fara neman kayan da zata saka wani lace ta ciro wanda akayi ma dinkin doguwan riga A line shape wani red sai daga kasan rigan anyi wani embroidery da black color saka shi tayi ya mata kyau sosai a jikinta ta shafa powder da khol kadai sai tasa lip gloss a bakinta daura dankwalinta tayi irin na zamani sannan ta dauko wata hand bag black ta louis vuitton a bag hanger dake cikin closet in, ta ciro takalminta na gucci shima black color sannan ta feshe jikinta da wani turare mai cool kamshi na cartier fitowa tayi daki ta ajiye hand bag inta da shoes ta sauka kasa tana sauri.mamii ce zaune kan kujera ta shirya cikin wani blue and silver lace dinkin doguwan riga yayi kyau sosai zama tayi kusa da mamii tace ina kwana mamiii shiru tayi mata sai ta kama kunnen ta tace “sorry mamii’am wallahi I overslept bansan time ya wuce haka ba but kiyi hakuri bazan sake ba”
Kallonta mamii tayi tace “naji ai sai ki wuce kici abinci mu tafi ” to tace sanna ta nufi dining table ta zauna tana hada tea bude food warmers in tayi taga fries ne da plantain sai peppered chicken kadan ta zuba tana ci a hankali har ta gama. Parlour ta koma wurin mami tace nagama mamii sai tace mata to muyi sallah sannan ko? Tace eh tare suka hau sama kowa ya nufa daki domin gabatar da sallah zuhr,bayan inaaya ta gama sallah ta gyara dankwalinta ta fiddo black medium sized veil inta ta sa shi a right shoulder inta ta zo ta dauki wayanta da wallet tasa cikin jakan ta zira takalmanta ta fito parlour ta zauna jiran mamii batayi ten minutes ba sai ga mamii ta fito suka fita tare wurin mota inda driver ke jiransu gaida drivern inaaya tayi ta shiga gaba mamii na back seat suka tafii.Tafiya ce mai nisa daga gwarimpa gidansu inaaya zuwa sunnyvale estate inda gidan baffa yake haka suketa tafiya shiru babu mai magana sai karatun Quranin dake tashi a motan har suka isa.
+
Da sallama suka shiga gidan baffah babu kowa a parlour sai kamshin turaren wuta dake tashi da Ac sallama suka kara yi sai ga mai aikinsu janette ta fito daga kitchen gaishe su tayi ta nufa sama ta gaya ma ummi parlourn gidan su inaaya da mamii suka zauna saiga ummi ta sauko tana murmushinta mai kyau ahhh yau su mamiin aneesah ne muke gani mun dade bamu ganku ba dariya mamii tayi tace ai kuwa dai gidan naku ne da niisa “wlh bari haj aisha akwai nisa” cewar ummi kenan pouting lips inaaya tayi tace “bara naje inda zaa yi noticing ina” dariya ummi tayi tace habaa inani ina manta diyata ai fushi nike dake shiyasa ko kizo mana hutu sai tace toh ummi ai zanzo su aneesah basa nan shiyasa tafada kaman zatayi kuka “to shagwaba ce ta taso inee smiling tayi tace to ai kece ummi sai kuma tayi dariya tace “uhmm kar fa nayi rashin hankali ummi ina wuni ban gaida ki ba ya gida” dariya sukayi gaba daya su ummi da mamii tace lafiya lau daughter ya hutu tace Alhamdulillah ta tashi tsaye tana ummi ina mimi “mimi na daki bacci take daughter” sama tayi da gudu bata jira ummi ta ida magana ba ta bude dakin mimi da khadija ta shige fadawa tayi kan gadon mimi ta na mata ihu a kunne mimzzzzzzz get up am here tashi wadda aka kira da mimi tayi tana hararan inaaya tace come on ineee why are you a kill joy ina dream me dadi kinzo kin tada ni dariya inaya tayi tace “uhh hakanan ake cewa inasan bacci mimz you’re x20 of me wurin son bacci” smiling tayi tace “na u sabi”ta tashi daga kwance ta zauna kan gadon yarinya ce kamar inaaya a tsayi dan ita ba fara bace black beauty ce da dogon hancinta da lips inta yan kanana da manyan idanunta mashaAllah da shape inta mai kyau wani irin gashi gareta mai tsayi sosai tayi parking inshi in a messy bun,tashi tayi tsaye ta nufa hanyan toilet nasu dake cikin dakin ta gama abunda zatayi tafito ta zauna kan sofa dake dakin tana cewa ineeeee oya kin tada ni what’s up meye labari ahhh intee is coming next week fa zaro ido mimi tayi tace please da gaske kike? tace of course dear! Ihu ta sa ta tashi tana tsalle biye mata inaaya tayi sai da suka gaji suka zauna suna sakin ajiyar zuciya sai mimi tace “dama abba ya barta a nan ta ida holidays wlh da abuja will be too small for us sai mun hada da kaduna and kano infact har yobe sai munje”
Hmmm! Wlh can’t even start thinking of crazy things in da zamuyi OMG! So much fun Allah ya sa abba ya yarda dai Amiin sukace a tare sai inaaya tace “ke na manta ma sultana na gaishe ki kuma ansa bikin yaya sarah” ohh my dear sultana mun dade bamuyi magana ba kinsan tunda wayana ya lalace komai seems not so good kuma gashi baffah yace am a destroyer sai nayi learning lesson zaya bani wani
“Owww sorry sweetheart its not  good gaskiya to kije ki sama ya abby ki ta mishi pity face har ya siya maki”
“Hehhhhehe this girl you’re such a darling haka zanje nayi ma cux everything is boring without my phone”
“Ke if we continue talking we’ll talk for the whole day ina ya khadija da ya leesha?
“Uhmm wa in nan ki barsu kawai am so angry at them wai suna kara encouraging baffah a bar ni nakoya lesson first instead of them to be helping me shiyasa na sharesu fa” dariya inaaya tasa tace ina bayansu ta fita da gudu daga dakin don tasan sauran idan ta tsaya.
Dakin dake kusa dana su mimi ta shiga aleesha ce kwance kan gado tana kallo da mackbook inta sai khadija tana kan sofa tanata chatting tana smiling  sallama tayi a tare suka dago suka kalleta inaayatu kune kukazo yakenan ya kike ya mamii cewar aleesha .
“Mamii tana lafiya tana kasa tareda ummi”
“Su inee university babes inji khadija tana dariya don tasan inaaya batasan a ce mata uni babe
“Kaii ya khady bawata university babe fa ni da secondary school nake ma”
Dariya khadija tayi tace tou ya hutu is it nice
“Wallahi babu dadii ya. Khadijo har na gaji fa” stucking toungue inta tayi ma inaaya tace serves you right tana dariya haka sukayita fira da khadija da aleesha suna dariya suka ji an bude dakin mimi ce ta shigo habaa inee inata jiranki kinzo kin zauna a nan lets go.
Tabe baki su khadija da aleesha sukayi a tare suka sa dariya sai mimi ta kara hade rai ta ja inaaya suka bar dakin suka koma dayan dakin sunata fira na school da rayuwa har aka kira sultana da inteesar suka hada conference call suka yi ta fira har saida janette ta shigo tace ummi na kiransu sannan suka kashe suka nufa kasa, mamii ne da ummi zaune sai ummi tace masu”kun shige ku kun hadu da juna to kuzo muci lunch ko shima kun yafe”
Smiling sukayi su biyu mimi taje tana rungume mamii tana gaisheta suka gaisa suka hau dining table don cin abinci jollof rice ce da shredded beef sai coleslaw da zobo mai sanyi dama kuwa inaaya nasan zobon ummi its the best in town sun fara cin abinci sai ga aleesha da khady sun zo sun zauna suma suka gaishe da mamii suka gaisa sanna suka fara cin abincin shiru kakeji sai karan spoons har suka gama kowa ya koma abunda yake. Haka har dare yayi bayan magrib su inaaya zasu tafi basu ga baffah ba don ya tafi kaduna wani aiki mimi ta sauko stairs da gudu da dan karamin trolley inta tana cewa ummi danAllah ummi ni su inaaya zani bi nagaji da zama shiruu dariya ummi tayi tace to shikenan ai yanzu dakun shirya da su khadijan na ganki kin dawo smiling kawai mimi tayi tana ma su khady da aleesha stucking tongue haka tabi su inaaya suka tafi.
Bayan sun koma gida sun gama sallahn isha da cin abinci har daddy ya dawo lokacin sun gaisa da mimi yake cema inaaya ta shirya idan zataje kano in ranar monday za aje daukan aneesah har da tsallenta da jin dadi nan take mimi itama tace zataje sunata jin dadi haka suka tafi daki amma basuyi bacci ba har wurin 2am sun maida room in mini cinema da popcorn insu da ice cream sunata kallon “money heist” a macbook in inaaya sai past 2 sukayi bacci da kyar suka tashi asuba saboda bacci suna gama sallah suka koma har sai to one suka tashi dama inaaya ta gayama mimi yau zasuje gidansu sultana, haka kowanne su yashiga yayi wanka suka shirya cikin black abaya almost the same sunyi kyau MashaaAllah! Haka suka sauka parlour babu kowa sai kamshin dake tashi kitchen inaaya ta nufa taga mamii tsaye suna abincin lunch ta gaisheta da fara’a amsawa mamii tayi tace ina mimi
“Mimi na parlour mamii”
“Tou kuje kuci breakfast ko”
Eh tace kafin ta bar kitchen in takoma parlour wurin mimi tace suyi breakfast  to mimi tace kafin ta tashi ta nufa kitchen ta gaida mamii sannan ta koma wurin dining table inda taga inaaya zaune har ta fara cin breakfast inta pancakes ne da syrup “yeey pancakes” cewa mimi zama sukayi suka gama ci sannan suka koma daki don gabatar da sallah. Bayan sun gama sallah suka sauka parlour domin gayama mamii zasuje gidansu sultana mamii bata parlour saida suka shiga dakinta suka gaya mata “to banda yawo kuma kar kuyi dare kuje baba hassan zai kaiku”
A tare sukace to mamii suka fita da sauri suka gama shiri suka tafi.
Saurayi ne dan kimanin shekaru 29 dogo ne sosai ba fari bane kuma ba baki ba irin wa inda ake cewa chocolate color hanci gareshi dogo da cute lips in shi ga eye brows inshi very thick and arched, yanada full and thick beard da gashin kanshi black sosai kaman na larabawa yanada idanu farare tas ga kwarjini a tare da su.tafiya yake da sauri har ya isa bakin mota ya bude ya shiga ya tada ya wuce. Wani gate ya tsaya dan madaidaici yayi horn mai gadi ya bude da sauri shiga yayi da motan yayi parking ya fito suka gaisa da mai gadin ya wuce cikin gida bai tsaya ko ina ba sai wani daki babba ne dakin da king sized bed a ciki white color sai study table da dressing mirror a gefe sai kofan closet da bathroom a cikin closet in towel ya daura ya fada toilet ya sakan ma kanshi shower ya kusan 30 minutes a cikin kafin ya dauro alwala ya fito wani dark blue moroccan jallabiya ya saka ya feshe jikinshi da turare sannan yasa abun sallah ya gabatar da sallahn isha ya gama yayi folding mat in ya koma kan gado ya kwanta yana lumshe ido.bayan kamar 20 minutes kaman wanda ta tuna wani abu ya jawo wayanshi kirar iphone 11 pro max midnight green color dialing number yayi ya sa a kunnen shi ringing biyar aka dauka “hello son” akace daga dayan bangaren “ammi” yace in his cool voice that ladies can die for😉 “ammi barka da dare” “yawwa alii ya aiki” lafiya ammi but it’s stressing “sai hakurii son it’ll be worth it InshaaAllah” eh ammi InshaaAllah ya abba? “yana nan lafiya we’re going to Nigeria ma on Friday InshaaAllah” kaii ammi ai da kun gaya mani it’s been long da naje nigeria fa almost 17 years fa “yes son yakamata kaje very soon gaskiya” to ammi InshaaAllah I’ll try and take a leave from work naje hutu ko one month nayi “ok Allah ya taimaka ya tsareka son” Amin ammi Allah ya kara girma my regards to everyone goodnight “ok son night bye”
Kashe wayan yayi yayi murmushi sannan ya gyara kwanciya yayi addu’a sai bacci yayi gaba dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page