RAINON Y’AN HUD’U CHAPTER 1 BY Khadijat M Abdullahi
RAINON Y’AN HUD’U CHAPTER 1 BY Khadijat M Abdullahi
Wayyo ! Wayyo !! Habibi Dan Allah nace ka dauko min Kofi nasha ruwa,wallahi cikina yayi nauyi sosai,…
Haba Sahibata wallahi ni har na gaji da yi maki aiki, ke wai sauran Mata haka kika ga suna yi ma mazansu,ciki ai ba hauka ba ne.
Habibi wallahi ba da gangan nake maka ba, cikina yayi nauyi kamar ro di, “A gaskiya ni na gaji gwara kizo ki haiho wannan cikin hakanan, Habibi cikina wayyo ! Kuguna ka kama ni Na koma d’a’ki please, Farida wallahi bari kiji maganar gaskiya ni na gaji, Babu yacce za ayi naje gurin aiki waje Na dawo gida kuma Na d’ora wani ,….
Kuka Na fashe dashi ina kiran sunan Umma,ta’shi yayi yana kunkuni ya talallabani da kyar Na mi’ke , Wàta muguwar k’ara Na Saki ina kiran sunan Allah gami da kiran sunan Umma, …..
Habibi ya ce” Farida mi kuma ke damunki ?
Wayyo ! Wallahi marata kamar zata fashe nake ji, wallahi habibi daga wannan cikin bazan k’ara kwasar wani ba, Na daina wallahi Na daina indai cikine, ..