BABBAR YARINYA CHAPTER 6 Oum Aphnan
BABBAR YARINYA CHAPTER 6 Oum Aphnan
Razana yayi da yanke Hukunci Alhaji Buba ,take ya soma bashi haƙury don yasan idan har aka haɗa auren shi da Islam ba abunda zai gadar sai rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali,ƙarshenta a rabu kuma zumunci ya lalace.
“Abba ai ma Islam Haƙuri a bata lokaci ta fudda wanda takeso!” tsaki yaja gamida gyara zaman sa sosai
“Ai ba na faɗi magana don Ace mun sorry bane in haƙura ,dakai da islam ɗin duk avun hukunci na ne ,kuma na zartar da hukunci saidai in baka son jinina ne to sai ka faɗa mun inji”
Sunkuyar dakai yayi yina bashi haƙuri amma haka yayi ɓarin iska dashi,ba arziƙi ya ɗauki waya ya fara kiran Inna Lami
Saida suka gaisa kana ya miƙa masa wayar ,Gaisuwar mutumci sukayi kafin ya faɗa mata gundarin dalilin kiran nasa
Ɗauke wuta tayi na ƴan sakonni ,saboda tasan akwai tiƙeƙen aiki in akayi gigin haɗa auren Islam da Akram,Inama zai yiwu ,matar da ta tsanesu take allah wadai da talaka ,har take iƙirarin wanda ya talauce baƙin halinshi Allah ya duba ya barshi a talaka!