MAI TAFIYA

MAI TAFIYA CHAPTER 5

MAI TAFIYA CHAPTER 5

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Son kasancewarmu tare daga zuciya ne!+

Kano, Nigeria

“A’ataqidhu inni waqa’at fil hub!”

( ina tunanin na fada soyayya)2

Luba ce ke zuba wannan zance a gaban Hindu , Rukky da ‘yar modu. Zaune suke a falon Hajiya Kububuwa ana taya Hindu kwashe kayanta za ta koma sabon gida. To amma aikin na su bai je ko’ina ba saboda abun almarar da Luba ta shigo masu da shi. Bin ta kawai suke da kallo saboda tsananin mamaki. Ta ce

” Sai ina ganin kamar ba ni ba ce. Kun ga Almustapha kuwa Wow..mashallah..mashallah. Ban taba haduwa da mutumin da na ji ina son shi farat daya kamar shi ba! Ai kwana biyun nan da ba ku ganni ba ina gidansa. Kun ga gidan? Aljannar duniya!Dole ne yau na wuce wajen Iyannan na gaya mata yau fa na samu mijin aure! Don bazan juri na ga Almustapha da wata ba! Almustapha…ya rouhi..ya habibii qalbee!”8

Rukky ta taso ta zunguri Luba ta ce

” Wai mafarki ki ke ko idonki biyu? Ko dai wani abu kika sha ya gaya miki karya? Na ji har kina batun aure”

Luba ta ce

” Garau nake ras! Ai daga nan wajen Iyannan zan je kawai ta fara shiri”

Rukky buga tsaki tayi ta koma ta zauna ta ce

” A duniyar nan dai luba, a yanzu ban ga son da za a yi masa marmarin aure ba!

Ta koma ta zauna.

Luba ta yi mata kallon sakaka. Sannan ta taso ta zungureta ta ce

” Sukari kin san wanene wannan mutumin kuwa!Uban gidan Idi maina ne fa. Ai irin wannan ba ka dangwali arziki ka bar shi ba! Ka bar shi ka je ina? Ai gwara ka samu gurbi ka dawwama anan daga ‘ya’yanka har jikoki sun huta da jaje! Me aka yi da maza in ji karya!Idi Maina ma mene ba a samu a jikinsa ba ballantana ubangidansa.”1

Rukky ta ja dan karamin tsaki ta ce

” Ai ko wanene tsakanina da shi mu rabu a hanyar da mu ka hadu. Kurunkus!Wai tukunna ma dan gidan wanene?”

Luba ta yi ma ta kallon uku saura kwata ta ce

” ji fa! Ji fa sukari da wata irin tambaya. Yo…idan kin ji ana waye ubanka ai kai ba wani ba ne! Shi fa ogan Idi Maina shi ne shugaba kankat. Shi ke da kamfani shi kuma ke juya kowa da komai. To ina ruwana da ubansa? Tunda ba shi ba ne mai kudin. Watakila ma wani tsohon matsiyaci ne can a kauye, dan ya tura masa a bunda ya sauwaka. Ni ko aurensa nayi ko inda danginsa suke bazan dosa ba!”1

Sai a lokacin Hindu ta saka baki ta ce

” This is surprising yau da bakinki Luba kike ambatar aure? Gaskiya zan so in ga wannan mutumin dan na san ya isa! Isar tasa ma ta isa!”2

Luba ta miko mata hannu suka kashe.

Sai a lokacin ‘ yar modu ya tashi yana rawa yana rera wata waka

” Ayyaraye daure jure

Zaman gidan wani tilas ne

Zaman gidan wani sai hakuri

Ai ba da kan ki aka fara ba

Ai da da kan ki aka fara ne

Da kin yi kuka kin koshi

Hindu ce ta taso ta biye masa suke taka rawa. Wai su a dole aure ya zo har ya tabbata.’Yar modu ya karkace baki ya rangwada guda suka tafa da Hindatu ya ce

” Wannan abu yana min siga! Muna jin aure a makwabta yau bana dai tamu za mu kai. Kuma dama ai abun na Allah ne budurwa da jika. Da haka da haka mu ma za a zo kan mu , ba mu fidda rai ba Alquran! Eh ai muna gayawa Azza wa jallah. Kawata lubancy ni zan miki babbar kawa. Billahillazi rabon cingan daga nan har kawayenki na kwatano. Abu namu maganin a kwabe mu! Ahayye Allah na dawo!”3

STORY CONTINUES BELOW

Hindu ce ta tunkude shi ta ce

” Babbar kawa ki ke ko ni? Ji shisshigi da kwala kai a faranti”

Yar modu ya kama baki ya ce

” Yau naga abun da ya isheni ni jikar A’i. Wannan da da ke aka shimfida duniyar da ba kya bari mu karaso ba! Yo kin zama mahandamiya. Ki ci nan ki ci can dangin makwadaita! Don kawai kin ji nace ni ce babbar kawa shi ne kike tada jijiyar wuya? Kai Hindu amma kin yi faduwar bakar tasa! Kyangarann!”3

Suka kwashe da dariya suka kara tafawa.

Luba ta ce tana fari da ido

” shirun ka nawan..ai ni kadai na san matsayin da zan baka. Ka manta kai ka fara kaimu la mirage. Ai da bazarka nake rawa!”2

“Idan kima kara sa ni a cikin jinsin da ba nawa ba..babu abunda zai yana in yi tsallen alkafira nayi kuli kulin kubra da ke!” Cewar ‘yar modu5

“Laaaa..yar modu wulakaci” luba ta fada tana masa kallon kasa kasa

Hindu ce ta ce

” Look guys..ku fa kun cika yarinta dayawa. Ke Luba wai ya ma aka yi kika san aure yake so. Kin san fa halin mutanen mu”

Ta harari Hindu da wasa ta ce

” Ai yanzu ba sai namiji na son aure ba ake aurensa. Yanzu ke ce zaki so auren sai ki bi dare ki bi rana kuma dole aure ya dauru! Zauna nan Hindu idan a tsaye kika kwana ni a tafiye na kwan! Wai kin ga gidan mutumin? Gari guda kamar wata masarauta. Da sannu zan zama sarauniya a masarautarka ya Nouri Mustapha! Kin san kuma shi ma fa na ga yana ra’ayina! Wallahil azeem faduwa ce ta zo daidai da zama!”4

“Da kyau mutuniyar” ‘yar modu ya bata hannu suka kashe.

Duk abinda suke yi Rukky ta zuba musu ido bata ce komai ba.

Luba ta fara tattara wata jakarta ta hannu tana mikewa ta ce

” Bari ku ga. Ba a bori da sanyin jiki. Bari na je wajen Iyannan. Ina ga nayi wata 3 rabo na da gidan sai aike”2

Hindu ta yi sauri ta ce

” Au ba zaki raka mu wankan sabon gida ba?”

Gaba tayi ta ce

” Hindu kiyi ta kan ki in yi ta kai na”4

Wata motar ta kirar corolla ta shiga tana tukawa tana tuno abubuwan da suka faru kwana biyu da suka wuce.

Duk yadda take tunanin masoyin na ta da arzikinsa ya wuce nan. Ta tuno irin baja bajan da ta samu a gidansa da makudan dalolin amurkan da ya cika ta da su kafin ta baro gidan.3

To yanzu da take a matar waje kenen ballantana ta shiga daga ciki! irin shagalin da za a yi a wajen bikinta abun sai wanda ya gani. Dole ne ta rarrabawa malamanta kudi su sa shi a gaba! Ina ba zai yiwu ba alewa ta zo hannun yaro sannan ya bar ta ta fadi kasa! Inaa…6

Gidansu na nan a yadda yake sai dakin Iya Tamadi da ya banbanta da na kowa. An sake masa ginin bulo an yi fenti an sa mata sabbin kaya. Shi kuwa baban yara da aka ce za a mishi gyara cewa yayi ba ya so a bashi kudinsa a hannu.

Ba ta yi sallama ba don yanzu ita ta fi karfin sallama idan za ta shiga gidan. Sannan uwar gulma Iya Asabe za ta kafa ta da habaici. An ya kuwa ba zata sa a batar da matar nan ba? Tunaninta kenen.3

Rashin sallamar tata bai sa ta kasa yin ido biyu da Iya Asabe ba daga shigowarta. Ta watsa mata harara ta ‘ba ki isa ba’ ta wuce dakin uwarta. Tana jiyo Iya Asabe na cewa

” Ah fulanin tashi yau an bayyana kenen”1

Iya tamadi na zaune tana tsintar wake tana kallon wani shiri a talabijin Luba ta shigo.

STORY CONTINUES BELOW

“Lale lale maraba da auta”

Cewar iyannan fuskarta fal faraa . Ko banza ta san yau ranar samu ce. Luba zata zauna ta ce2

” Auta kar ki zauna anan. Ga wata dadduma can dauko ki shimfida ai ta fi laushi”3

Maimakon ma ta ji tayin da ake ma ta sai ta fasa zaman kasan ta fada kan kujera. Ta buga wani uban tsaki ta ce

” Gaskiya ina da mahassada. Amma …k’ ”

Iyan ta kalle ta ta ce

” Au na san ba zai wuce Asabe ba. Ai ita Asabe wannan shigar da take ganin kina shigowa da ita ta alfarma da wannan dankareriyar motar su ke ruda ta. Bar ta! ‘Yar matsiyata har ubanta ya mutu da tsohon bashi akansa! Baruma ce fa ai anan tsiya ta kare!2

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE