UWAR GIDAN BAHAUSHE BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 15 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 15 BY SHATU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Anty jidda ta fito hannunta rike da mayafi da makullin mota. Parlonta bayan Hanifa dake zaune ta Dan fada se Kuma hannunta dauke da jaririyar ta nannade cikin layette, gaban ta abinci cikin plate an rufa wani plate din Dan Kar ya huce, dayan hannunta na rike da katon mug cike da kakkauran tea. Mutanen dake parlon akwai Amira, yayar su se Kuma kawayen Anty jidda guda biyu da cousins din su Hanifa guda biyu. Hajiya hanne ta fara duban Anty jidda tace+

” Ya na ganki da key din motar, se Ina kenan?”

Ta tsaya ba tareda ta zauna ba tace

“Zanje gidan surukan Hanifa ne, bazan iya jira ba Kuma yarinyar yaushe ya aureta zaa saka ya Kara aure?..”

Hanifa tayi saurin aje mug din hannunta tareda fadin

” Dan Allah Mom karki je, ki bar maganar nan kawai.

Ismail threatened me Akan abinda nama Ummaah, karki je ki Kara ballo wani abun”

Wani harara ta Mata tace

” Ke ai na lura Baki San kanki ba, bansani ba ko har yanzun zafin haihuwar ne Bai sake ki ba, tunda ba Zaki iya komai ba ni zanje na kwato Miki yancin ki”

Hajiya hanne da hajja kalsi Suka Mike tareda bin bayan Anty jidda da Bata saurari kowa ba ta fita, duka parlon kowa shiru yayi se Hanifa dake kuka kasakasa. Sister su ta taso tace Mata

” Ki daina kuka Kinga jinin ki already ya hau in Baso kike ya Kara Hawa ba Kuma”

Ta share hawayen da ya Mata kacakaca a fuska tace

” Adda kina gani dai nace Mata Kar taje, shi bashi yace zaiyi aurennan ba, ita komai mum ba zata bi a hankali ba”

Haka Suka lallashe ta har ta Dan kwanta bacci ya dauketa Amma tana hango irin tijarar da zata yiwa Anty jidda matsawar ta ballo Mata ruwa. A bangaren Ismail gaba daya kanshi ya dauki caji ya rasa abinda yake Masa Dadi, yasan Allah ne ya tsara Masa rayuwa haka he doesn’t have Whatsoever Right yayi questioning Allah, Amma tunda Hanifa ta haihu komai Kara lalacewa yake, abin ya masa nauyi ji take shi yasan baa raba bawa da kananan kurakurai, Amma a wañnan extent din Yana jin abin ya masa nauyi, Yana jin kanshi tamkar zai fashe ne, he’s ok living with Hanifa, tun ranar da ya amince auren ta ya riga ya shirya karban ta, ya Kuma bude zuciyar shi Dan ya Bata dama, dukda tsakanin ta da mahaifiyar shi Basu jituwa Amma shi yasan bama lallai Sofy tayi Masa abinda Hanifa ta Masa ba. Se Kuma yanzun ya riga yayi settling Sofy ta riga tayi aure Bayan ya rasata gaba daya sannan Ummaah zata kawo maganar aure, she’s trying to use him ta kuntatawa Anty jidda da Hanifa, shi Baida wani niyyar aje Mata biyu, not when gaba daya Babu zabin shi a ciki, shi kullum mother’s son ne sede ace mahaifiyar shi ta zabar Masa Mata? Shi fa idan zai iya tunawa San Sofy kadai yayi willingly, bawai Ummaah tace Masa yayi ba Amma komai ita take fada Masa yayi, Bata taba barin shi ya zaba ko yayi deciding Abu, she’s the chief decision maker of his life! Wayar shi ta katse Masa tunanin da yayi zurfi a ciki, cikin rashin kuzari ya janyo wayar se yaga mahaifin shi ke Kira,dauka yayi Yana sassauta murya ya gaida shi cikin girmamawa, sannan yayi shiru yana sauraron abinda Wambai zai fada Masa

” Baa kawo min kawata na gani ba, ance min Kuma matar taka tazo har nan, shi ne nace Nanda mintina talatin zanje na ga kawata”

Sosae yaji kunya ta Kama shi Amma ya zaiyi itama Hanifa data je ba zuwan Dadi ya kaita ba. Mikewa yayi yace

” Zanzo na kaika ayimin hakuri”

Wambai yayi murmushi yace

” Ina jiranka”

Daga haka ya katse wayar, Ismail ya fara neman layin Hanifa wadda ke bacci har lokacin, dukda bama jimawa baccin yayi ba, idanunta ta bude ta dauki wayar tana mitar an katse Mata bacci Amma ganin me Kiran se tayi shiru ta Kara a kunnenta, Bai amsa gaisuwar ta ba yace

STORY CONTINUES BELOW

” In less than thirty minutes zamu zo da Wambai, ki fadawa Mom”

Ya katse wayar ya dauki mukullin motar shi me hade Dana parlon ya fice, tashi tayi ta kwallawa Yaya Kira, se gata ta fito dauke da sucker baby da alama sterilizing dinsu take, kallon Hanifa tayi da ta mike tace

” Ki Kira Mom kice ta dawo Baba Wambai zai zo ganin jikar shi”

Cikin hanzari suka Kira Anty jidda wadda saura kiris ta karasa jin bakon da zaizo Dole ta juya kan motar ta koma gida, komai kafin ta karasa ya kammalla se abinda baa rasa ba, kamar yadda yace minti talatin Yan mintina kadan suka Kara akai se gashi ya iso, mahaifin Hanifa ya shigo dashi parlon da yake saukar manyan bakin shi, sunata Hira da dariya har suka karasa parlon seda ya zauna sannan Dad dinsu Hanifa ya zauna Yana gaisawa da Ismail.

” Ka buya yanzun bama haduwa, coming in contact with you is really getting hard these days”

Daddy ya fadawa Wambai dake kurbar ruwan da aka serving Masa, ya girgiza Kai yace

” A’a fa Kaine baka nema na, rabona da Kai tun ranar auren yarannan, you’re really busy into politics”

Daddy ya watsa hannun shi yace

” Gaskiya kam! Kusan shekara da wani Abu. Politics Babu dadi muna tabawa ne saboda shi ne abinda muka iya”

Daga haka hirar tasu me cikeda ilimi ta koma kan matsalolin da Nigeria ke facing da yadda ya kamata ayi fixing abun, shigowar jidda da Hanifa yasa hirar ta tsaya, Anty jidda fuskarta a sake ta karaso ta gaida Wambai, Hanifa dake rike da baby ta karaso ta tsugunna har kasa ta gaishe shi cikeda girmamawa, shima fuskar shi a sake ya amsa sannan ya karba yarinyar dake bacci Babu ruwanta da matsalolin duniya dake. Ya Jima Yana kallonta sannan ya Mata addua ya dubi Ismail yace

” Na Mata huduba da Safiyya, sunan Gwoggo ta Gumel dukda Hanifa kema haka sunan ki yake’

Jikin Ismail yayi sanyi Dan ya riga ya Mata huduba da Furaira, Hanifa taji wani sanyi a ranta yayinda Anty jidda ta Masa godiyar karar da yayi musu. Bai Kara jimawa ba ya musu sallama suka fito Hanifa ta biyo Ismail fuskata da damuwa ganin ko kulata baiyi ba, seda suka ga tafiyr su sannan ta fara murnar canja suna da akai.

Cikin mota ya kalli Ismail dake zaune gefen shi  yace

” Kira min giwa a waya”

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE