ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya 

Granny yanzu komai ya na hannunki, dole ne mu san abin yi kafin ya dawo. Don nasan matukKar ya gane Zuri’a daya muke, ba zai yarda na cigaba da zama ba yadda ya tsani Mahaifina, nasan kuma dole tsanarsa nima ta shafeni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Don a cikin ma su yi masa laifi daga Daddy sai Abbana, saboda a cikin labarin da ya bani a taKaice yayi min bayanin irin juya masa baya da suka yi. Kuma na ga tarin tsana da Kiyayyarsu a cikin idanunsa. . °
Granny ki daure ki bani dama na gyra zumuncin mu, ina son mu dawo ZURI?A DAYA kamar yadda muke tun tasowar mu”
Cikin Kwalla Granny ta riko hannun Sameer – sannan ta ce, “Maigidana Allah ya na tare da mu, tunda ya san Kudirinmu na Alkhairi ne. ina son ka saki ranka ka dawo cikin mu, ka bar komai a hannuna. don mu ma nan burinmu kenan ni da

Kanwarka da kuma dan uwanka Mustapha Karami, shi muke jira ya dawo sai mu tunkari Zuri’armu.
Dole ne iyayenku su russuna, don ba za mu barsu su dinga yi mana abin da suka ga dama ba. Insha Allah wannan bakar gabar sai ta zo Karshe, ba za mu bari ‘ya’yan cikinmu su dinga juya mu ba yadda ransu ke so. Ko ban auri Alh Nasiru ba ai Kanwa nake a gare shi, ba zan zuba idanu ina ganin ‘ya’yansa suna gaba da juna ba kuma na barsu. Idan da zuciyoyi sun fusata, to dole ne kuma yanzu su sauko. Da ace ana mutuwa a dawo, idan Alh ya dawo ya ga yadda Zuri’arsa ta raba gida biyu sai ya yi kuka da ni ya ce ban tsaya na tsawatar musu ba”.Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan hawaye suka wanke mata fuska. Daga Sameer har Haana sai da suma suka ji zuciyarsu ta _ karaya.


Nan Haana ta sanya hannuta tana goge mata hawayen da suka cika kumatunta sannan ta ce.
“Granny ki daina kuka, Allah ya kawo Karshen komai tunda ki-ka fadi haka, mutuKar kuma ki ka nuna damuwarki sosai akan Abba nasan zai yi miki abin da ki ke so, dama dai kin barshi ne shi yasa’, ‘
Nan Granny ta saka hannu ta riKo nata sannan ta ce. “Haka ne Rahinatu, ni na barsu har suke yin
‘ abin da suka ga dama. Amma daga yau komai ya Kare, ba zan sake barinsu su yi mana abin da ransu ke so ba, tunda dai mu ne muka haifesu ba su suka haifemu ba. Maigidana Sameer ka kwantar da hankalinka, ka kuma saki ranka da walwalarka a cikinmu. Nan gidan ku ne, saboda haka yanzu ka mike mu je ka shiga ciki ka ga iyayenka da kuma Kannanka wanda ba ka san su ba, suma kuma ba su sanka ba”.
Tsananin murna da doki a zuciyar Haana kamar ta zuba ruwa a Kasa ta sha, don burinta ya na daf da cika. Haka suka taho har zuwa cikin gidansu tare da Sameer.
Ammi da Mama ma sun yi matuKar farin ciki da murnar ganin dansu. Har cikin ransu sunji dadin ganinsa,.don Mama ma har sai da ta zubar da hawaye.
Nan Granny ta sanar da su duk yadda suka yi da Sameer, da kuma yadda suka shirya yadda za su bullowa Abba Mustapha da kuma Abba Mukhtar. Sannan ta Kara da cewa . Dole ne Mustapha da Mukhtar su bi umarni na, don so nake komai ya dawo dai-dai kamar yadda yake a baya’”’. – Www.bankinhausanovels.com.ng
Hakika duk sun ‘yi farin ciki Kwarai da jin maganar Granny, a take su ma suka goya mata baya. Babu kamar ma Sameer saboda ganin irin Kaunar da Zuri’arsa suka nuna masa. Haka ya dinga jin so da Kaunarsu ya na shigarsa ta ko ina, saiya dinga jin dama tuntuni da su yake rayuwa, nan ya Kara jin wata Kaunarsu ta musamman ya kuma hakikancce da cewa lallai su aka zalunta kuma aka guje su don son zuciya duk irin wannan
KARAMCI da suke dashi, amma sai da aka Bata musu.
Nan cikin ransa ya godeewa Allah da ya taimakeshi akan shi zai yi sanadin shirin Zuri’arsu, ta hakan ne zai wanke wawakeken gibin da mahaifinsa ya taimaka na wargajewar ZURI’A DAYA.
Tabbas yasan Mahiafinsa zai yi matukKar farin ciki idan ya ji cewa dansa ne ya yi sanadi da kuma Kokarin haduwar kan Zuri’ar, don dama_ babu wanda ya san abin da ya shirya idan ka dauke Alh_. Ammar.
Haana da Rauda da kuma sauran Kannensa haka suka wanzu cikin farin cikin murna na sun sake’ samun Yaya. Sameer bai bar gidan ba sai wajen tara na dare saboda hira suke ta yi na yaushe gamo.
Mama ma gidanta ta baro suka zo aka hadu ana ta hira tana ta basu tarihin Zuri’arsu, da kuma irin yarintar su Sameer da su Yaya Abba. Haka dai suka yi ta cin dariya da jin dadin yadda suke jin labarin abubuwan da ba su sani ba.
A haka suka dinga haskowa kansu rayuwar a idanuwansu kamar a film suke gani. Rauda kuwa da Haana har wajen bakin get din gidan da yake ciki suka raka shi, sannan suka dawo gida kowa . zuciyarsa cike da farin ciki.
Yau dakyar Haana ta iya samun runtsawa, domin gaba daya tunanin Malam M.J yha Hanata saket. Duk wani juyi da za ta yi sai taga
kyakkyawar fuskarsa ya na yi mata murmushi Haka ta zamo kamar wata zautacciya har da ‘yan surutai Malam M.J na mai yasa ka yi min haka?, ka tafi ka barni da kewarka, bayan kuma yanzu ne lokacin da na fi buKatar ka a kusa da ni.
M.J na yanzu ne na san cewa zuciyata da kuma RUHINA sun gama kamuwa da so da Kaunarka. Please ina rokonka ka dawo cikin rayuwata, kada ka yi nisa da duniyata.
Yadda nake ji a raina idan ka barni ba ni da wani buri ko farin ciki da zan yi a rayuwata, ban tanadarwa kaina komai na farin ciki ba da ya wuce kai, domin kaine komai nawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariyata, kuka na, farin cikina. Kai da duk wan shauki na rayuwata kai ne shi. Don haka nake fata da rokon ka dawo cikin rayuwata, mu rayu tare da kai”.
A haka ta wanzu cikin wannan surutan nata har lokacin da barawo barci ya yi awon gaba da ita.
A bangaren Sameer kuwa shima kasa runtsawa ya yi, duk juyin da zai yi sai yaga kyakkyawar fuskar Haana dauke da murmushi tana gilma masa. Tabbas yau ya ga kalar matar da yake so a rayuwarsa.
Ashe dama haka Allah ya ke da ikonsa?. Duk abin da ya sa ya kasa tsayar da matar aure kenan, wato ‘ashe zai zo ya tarar da Haana, ita ce kuma yake jiran ta shigo rayuwarsa duk faman da ake ta yi da shi na ya fitar da mata amma ya Ki.
To yanzu dai komai ya zo Karshe, yau ga shi ta hanyar gyara zumunci ya hango wacce ya ke so. Lokaci guda ya ganta, kuma a lokacin ya kamu da sonta. Tabbas ya yi nasara.
Nan ya shiga juyi a gado ya -na_ tunaninta. Allah-Allah ya ke gari ya waye ko ya samu ya je ya yi tozali da abar Kaunarsa. Da wannan tunanin shima bacci ya yi awon gaba da shi. Amma fa kafin nan sai da ya jima ya na kai kawo a cikin dakin nasa.
Wannan ma kuma haka yake a wajen Rauda, domin ita neman baccin ma ta yi ta rasa, domin tuni zuciyarta ta yi gaba kan tunanin kyakkyawar – fuskar Sameer. Tun da take a rayuwarta ba ta taba ganin da namiin da zuciyarta ta kamu da son shi lokaci guda ba sai a kanshi.
Wani irin son shi ne ya kamata farat daya, wanda ta ji matuKar in ba ta same shi ba to kuwa ba ta jin za ta iya rayuwa cikin farin ciki. Duk wani buri da kuma irin tsarin da take son saurayi ya kasance yau ga shi Allah ya bata shi a zaune, kuma bai tashi fitowa ba sai ya fito mata a cikin Zuri’arta.
Don haka babu abin da za ta cewa Allah sai dai godiya kawai da ya kawo mata jan gwarzon saurayinta cikin rayuwarta. A yanzu ne ta samu damar da za ta sallami Abduljabbar ta huta da bakin nacinsa don ta samu ta sarara.
Yau da wuri Haana ta shirya don zuwa zana jarabawarta ta Karshe daga wacce daga ita ba za ta Kara zuwa ba har sai sun dawo daga hutu. Ta kuma Www.bankinhausanovels.com.ng
shigo da wuri ne makarantar don kawai ta nemo lambarsa (Numbcr) a wajen Malaman da take da yakinin samunta a wajcnsu,
Ta rasa yadda za ta yaki zuciyarta da tunanin Malam M.J, amma abin ya faskara. Kai tsaye ofis (Office) din Malam Usman ta nufa, ta kuwa ci sa a ta same shi bai jima da shiga ba.
Nan suka gaisa, sannan ya Kara kallonta ya ce “Ya ya Jarabawa, yau ai za ku gama ko?”. Ta amsa masa cikin sakin fuska ta ce“Eh Sir, insha Allah”. .
“Ok, to shikenan Allah ya taimaka”. Amcen”’. Ita ma ta amsa. Ya sake dubanta, sannan ya ce
“Raihanatu kina bukatar wani taimako ne, ko kina da wata matsalar ne?”.
Cikin sassauta murmushin da ke kan fuskarta ta ce.
“Eh, a’ah. Dama dai na zo ne na tambayeka ko zan samu lambar Malam Muhammad ne, saboda tunda ya tafi ba mu yi waya ba, ina son jin lafiyar Mahaifiyarsa ni da sauran dalibai don har yanzu mun ji shiru. Ga shi kuma yau kos (Course) din sa ne za mu yi (Final Exam) har yanzu kuma babu shi ba labarinsa”Murmushi ya yi, sannan ya amsa mata da
“Allah sarki, kun yi hankali. Sai dai kash! Bana Jin. akwai yiwuwar dawowar Malam M.J Makarantar nan, saboda dama ba wai (Permanent lacturer) bane. Zuwan da ya yi mana dama wani (Contract) ne.
Ya na kuma daf da gamawa ne sai kuma matsalar ciwon Mahatfiyarsa ya sa ya ajiye koma ya tafi, bai kuma sanar da mu cewa zai dawo ba gaskiya. Ban da wannan kuma ba mu yi waya da shi ba gaskiya.
Na dai ji Dr.David ya ce sun yi waya da shi bayan ya je can. Da kuma na yi masa maganar ya bani lambarsa (Numbcr) da suka yi wayar sai kuma yace min a ranar da suka yi wayar kuma bayan ya fita wayar tasa ta fadi.
Ya kuma fada min cewa Malam M.J ya ce masa ba zai dawo ba, zai dai je ya yi jinyar Mahaifiyarsa, domin tana cikin (Critical Condition). Har ga Allah ni ma na yi matukar jin zafin rashin samun lambarsa (Numbcr). Amma nasan wata rana zai kira ni, idan ya kira kuma insha Allah zan baki lambar tasa.
Sai dai yanzu mu _ shigar da addu’a ga Mahaifiyar tasa na Allah ya bata lafiya, don ya sha fada min cewa, ya na matuKar ji da Mahaifiyarshi, don kawai farin cikinta ya dawo Kasar nan akan wani buri da bai fada mana ko mene ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin sanyin jiki ta baro (Office) din, domin ba haka ta so ba. Haka kawai ta dinga ji farin cikinta ya na gushewa. Dole ne ta yi KoKarin kawar da damuwarta a wannan lokacin don kar ta samu matsalar jarabawarta da za ta yi, ga shi kuma a (Course) dinsa.
Ba za ta taba farin ciki ba hakan idan ta faru, dole ta yi KoKarin kawar da wannan damuwar, sannan kuma ta dora damba a ranta cewa, kamar ya na nan. Domin zai yi matuKar farin ciki idan ya samu labarin ta cinye (Course) din sa gaba daya.
A zaune ta ke kan Resting chair ta cikin Makarantar. Ta jima da fitowa daga dakin Jarabawar, tana jiran su Zahra ne don su yi sallama. Gaba daya ta tafi duniyar tunani, cikin ranta tana ayya nawa cewa
“Shin yanzu idan Malam M.J ya tafi gaba daya, ma’ana ba zai sake dawowa ba, ya ya za ta yi da rayuwarta da kuma so da Kaunar da take yi masa wanda ya hanata duk wani farin ciki da walwala?.
Yanzu wane matsayi za ta baiwa Malam M.J a wajenta, macuci, ko kuma mayaudari?”. Sai lokacin da ta gama ajiyewa rayuwarta cewa shi ne wanda ta tsayar a matsayin ABOKIN RAYUWARTA, yanzu kuma ya zo ya yi mata nisa a rayuwarta. Yanzu kuma a ina za ta ajiye tunaninsa da Kaunarsa da suka cika mata ko ina na cikin zuciyarta. Anya ma kuwa za ta iya wata rayuwar farin ciki matukar Malam M.J bai dawo rayuwarta ba?.
Nan take zuciyarta ta hore ta da cewa. “Ka da ki sake ki kira Malam M.J da duk wadannan sunayen da ki ke son ki JikKa masa. Sam ko kadan bai dace da su ba. Tunda bai furta miki cewa ya na sonki ba, haka kuma kema ba ki furta masa kina son shi ba.
Babu abin da ya rage miki yanzu illa ki dage da addu,ar Allah ya dawo miki da shi cikin rayuwarki”, Tana cikin wannan tunanin ta ji an bugeta a kafada. Da sauri ta dago kai, Zahra ce isaye a gabanta.. Kallon tuhuma ta ke mata tare da cewa.
“Haana ba dai tunani ki ke yi ba?. Na yi miki sallama har sau biyu, amma ba ki amsa min ba sai da na taba ki. Da fatan dai ba tunanin ki ka je ki ka rubuta ba sannan ki ka yi (Submit)?
Haana anya ba wata matsala ki ke so ki janyowa kanki ba?. Na fuskanci cewa Malam M.J ne da tunaninsa suke son hanaki farin ciki da walwala. Na roKe ki da ki cire tunanin nan ki fuskanci karatunki da rayuwa ta cigaba. Mutumin nan ya tafi, kuma bai neme ki ba, kuma bai kira wayarki ba. To mai zai hana kema ki nemawa kanki mafita tun yanzu?”Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce Zahra ko kadan ba tunani na rubuta ba, ina kuma mai tabbatar miki da cewa duk abin da ake tambayeni to na bada amsa dai-dai, kuma insha Allah bana jin zan samu matsala akan wannan jarabawar. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai dai kuma ba zan boye miki ba, Malam M.J duk wata dakika da zuciyata za ta buga, to suna bugawa ne da tunaninsa a raina. Zahra ina son M.J fiye da tunaninki, zan kuma iya jiransa har ya dawo cikin rayuwata saboda ba zan iya rayuwar  babu shi ba.
Ban kuma Kara jin ina son Malam M.J ba sai yanzu da bana ganinsa, kuma insha Allah ba ni da wani miji a gidan duniyar nan idan ba shi ba. Zuciyata da gangar jikina da shi kadai suka aminta’. Murmushi kawai Zahra ta yi sannan itama ta dora da cewa
‘“Haana zan fi kowa son ganin kin dace da duk abin da ki ke son ki mallaka cikin rayuwarki, don haka ne ma a matsayina na Kawarki na ke son na ankarar da ke wani abu da ki ke son ki kasa ganewa.
Bana so ki bari so da Kaunar Malam M.J su rudeki ki manta da kanki. Shin kina tunanin yadda Malam M.J ya ke a haka bai bai yiwa wata tanadin kansa ba?. Ba ki san komai nasa ba, ina nufin tarihin rayuwarsa, haka kuma bai fada miki da bakinsa ya na sonki ba har ya kama gabansa. Sai dai kuma idan so ki ke ki jefa rayuwarki cikin damuwa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ina son ki cire son shi tun da wuri, kar abu ya zo bai samun yadda ki ke so ba ki shiga cikin wata damuwar, tun da dai babu wanda ya san ranar
dawowarsa. Don ni kaina da ki ka ganni nan, babu irin binciken da ban yi miki ba a kansa, don dai kawai na nemo abin da zan fada miki ki samu farin ciki.
Amma kowa na tambaya sai ya ce min gaskiya ba shi da tabbacin dawowarsa. Don haka mu cigaba

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE