AMANAR MU CHAPTER 5
AMANAR MU CHAPTER 5
K’arfe 6 daidai Zee ta isa garin abj already driver na jiranta a tasha hakan yasa tana zuwa ta zarce mota!+
Gidan koda tashugo babu kowa da alamu dukkanin baqi sun koma, fitowa tayi daga cikin motan sannan driver ya jaa mata trolley d’inta zuwa cikin gida.
Harta gifta zata shiga cikin gida sai ta tuno da zancen Humy data sameta in private (cikin sirri) ana gobe d’aurin auranta!
_Zee dan Allah inaso kimin wani alqawari_
Kallonta Zee tayi sannan tace “ok inaji ”
_Zee dan Allah ina rok’anki bayan tafiyana kiruqa shiga kina duba su baba koda sau d’ayane a rana kimin alk’awari zaki ruk’a kula dasu saboda sunada tsananin Buk’atan wani a kusa dasu,kinga yanzun zan tafi zuwana abuja zai ruqa d’aukan lokaci!_
_Kinga babu kowa yanzun a cikin gidan sai ke da momy da masu aiki su kuma kinsan ba kwana sukeyi ba momy kuma sai yamma take dawowa aiki,Na rok’eki Zee kiruqa shiga kina d’ebema su mama kad’aici daga ita sai baba kawai suke wuni acikin gidan nan fa! Mama ita kad’ai kema Baba duk wani hidima nasa tayi na baba tazo tayi nata baki ganin k’arfinta yafara k’asa masu aikin nan ko ance suyi ba yi suke sosai ba! Zee awannan lokacin iyayenki nada matuk’ar buk’atanki wlh Zee kinada Zuciya mai kyau wanda bai maki farin sani bane kawai zai d’auka zuciyanki ba fari bane amman ni Humy nice nasan Wacece Zee kuma nasan zaki kula da mama da Baba a wannan lokacin dan kece kawai zaki zama mafi kusa dasu a yanzun! _
Dogon lumfshi Humy tasake dan taga alama tamkar Maganganunta sun fara ratsa Zee d’in dan haka ta kuma sassauta kalamanta had’ida dafa Zee d’in sannan ta cigaba da cewa;