UWAR GIDAN BAHAUSHE BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 13 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 13 BY SHATU

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Naji saukar shi daga gadon, naji  Kuma fitar shi daga dakin, Amma gajiyar da Kuma baccin da ke cikin idanuna se Suka hana ni na bude idon, ban Kara kwakwaran motsi ba se wajen karfe goma na safe sannan na tashi, shima Rana ce ta cika dakin ta damu idanuna, Babu yadda zanyi Dole haka na Mike Ina jin jikina duk yayi min tsami kamar nasha duka. Na daga kafafuna cikin dabara na wuce toilet, daga idanuna nayi na kalla toilet heater se Naga ta ma tafasa, I had a hot bath da yasa na danji Dadi sannan na fito na dawo dakin, yadda na barshi haka nan yake, se na fara tunanin Ina Albi yaje da safiyar nan, se na Kuma tuna ko ya leka wajen matar shi. Na zauna gefen gadon bayan na jona hair dryer a socket na busar da kon sannan na shafa Mai na Kama da band. Na goge jikina na

shirya cikin bakin lace me adon orange flowers. Nayi stretching sheets din gadon, daga karshe se na yaye sheet din na dakko sabo na shimfida, sabuwar rayuwa na ayyana a raina, na kalla komai na dakin Wai mallaki nane, nawa ne duka.

Ina fitowa parlor ana kawowa wuta se kawai na kunna incence burners Dan turara gidan. Wayata na Nemo na kunna na fara Kiran Ammi Bata dauka ba se Anisah ce ta dauka, se naji dadi naji Ina missing gida, Ayaan ce muka gaisa karshe sannan na Dan kwanta na lumshe idanuna Ina jin yunwa na kwakular cikina. Can na kasa hakuri har Sha daya ta kusa se kawai na nufi kitchen na hada tea na fito dashi a mug Ina juyawa Dan ya huce, turo kofa naji anyi se Kuma ya bayyana gaba daya, hannun shi dauke da ledoji da waya a kunne alamar waya yake, Yana sanye da Ash top se bakin wando. Tea din na aje na karasa inda ya tsaya na karba kayan hannun shi sannan na zauna na fara shan tea din, gefena ya dawo ya zauna tareda aje wayar hannun shi ya daura kan table din dake gefen mu ya shafa fuskata

” I’m sorry na fita na barki da Yunwa, na fita na samo Miki abinda Zaki ci. Ya Kika tashi? Ya jikin naki?”

Bawai maganar tashi bace tasa na kusan zubar da tea din hannuna a’a yadda yaki tsayar da hannun shi a jikina yasa tea din ya nemi zubewa, dariya ya fara Yi a hankali ganin duk na rikice ga kuma Bata Rai da nayi, yace

” Why are you frowning, ko gaida ni ma bakiyi ba”

Na janye jikina nace

” To ba Kai bane ka tafi ka barni ba”

Ya Mike bayan yace nayi hakuri, da kanshi ya dakko plate ya juye abincin daya kawo cikin disposable packs, sannan na sakko muka fara ci, seda na koshi sannan ya ballo min pain relievers na karba kaina a kasa nasha. Ni na tattara gurin na dawo na samu ya fita, Bai Yi minti goma ba ya dawo ya sameni Ina kwance nayi shiru deep in thought,

” Menene?”

Ya fada Yana dago kaina ya daura saman laps dinsa, kaina na girgiza Ina murmushi nace

” Babu komai”

Yace

” Baki jin dadin zaman ne, kinyi shiru”

Na girgiza Kai Ina murmushi nace

” Kai Albi waye ya Fadi haka? Ai baka nan shiyasa yanzun tunda ka dawo se muyi ta magana”

Ya gyada Kai ya fara min Hira, Ina dariya Ina Kuma sauraran shi,seda aka Kira azahar yace min zaije masallaci me zanci ya taho min dashi, nace

” A’a zanyi girki”

” No! Ko na yau ne kadai Zan kawo idan yaso gobe seki fara”

Haka ce ta faru seda nayi kwana biyu shi yake siyo Mana abinci se a Rana ta uku sannan muka fita da yamma Dan yin cefane, bayan nayi sallar laasar na shirya cikin abaya maroon, na saka golden din turban cap a kaina sannan na yafa veil din abayar, wayata kawai na dauka na fito, na kulle part din sannan na nufi bangaren Maman Afaf, shima shi yace nace Mata Zan fita, da sallama na shiga parlon tana zaune ta daura kafarta akan center table tana kallo, na shiga Bayan ta amsa na zauna na gaishe ta, idonta na kan tv din ta amsa, nace

” Zan fita ne”

Se ta kalleni sannan tace

” A dawo lafiya”

Na amsa da Amin na Mike Zan fita se na juyo nace

” Su Afaf basa nan ne?”

Ba tareda ta kalleni ba tace

” Eh!”

Se na gyada kaina kawai na fita, tabbas Kubra da gaske take da tace Bata iya munafurci ba, ni hakan yayi min, da ta nuna tana Yi Dani ta fitine ni gwara kowa yayi ta kanshi, tashi ta fushe shi. Se wajen maghrib muka dawo Dan seda muka tsaya gidan Adda Nanah dake kusa da inda muka je. Zama nayi na gyara kayan Miyan na saka cikin freezer komai na Masa guri tunda Naga muna samun wuta sosae. Ranar da na cika kwana biyar ranar nayi baki, tun dare Baba ya fada Masa zuwan su, Dan haka Ina tashi da safe na hada stew se wajen eleven na Gama girkin sannan nayi wanka na shirya. Wajen Sha biyu Sega Ummaah, Anty jidda, Anty Safara’u, Anty lubabatu, Maman Yaya Fahad, da wasu aunties Dina su uku. Dukda yawancin su bana shiri dasu Amma hakan Bai Hana naji dadin zuwan su ba, nayi ta murna na bisu na rungume su sannan na kawo musu abin da zasu Sha, mun Dan fara Hira Ummaah tace na raka su wajen Kubra. Haka na dakko hijab Dina na tafi bangaren ta, su Afaf na Wasa sun dawo a makaranta ko uniform Basu cire ba, tana ganina ta taho ta fado jikina, nayi murmushi nace

” Ina mamanku?”

” Tana daki” ta bani amsa nace tace Ina parlon Ina magana, se gata ta fito kanfin ma Afaf din ta Shiga, na gaishe ta tayi kyau cikin shigar shadda ja da tayi, ta amsa nace Mata

” Aunties Dina Suka zo zaku gaisa”

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE