KALLON KITSE CHAPTER 12
KALLON KITSE CHAPTER 12
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yayi tambayar cike da sha’awarta, dan yadda ya lura duk ta fita hayyacinta, daga can bayansu yaji inna na cewa, “me kuma ya kawoka kicin?”
da sauri ya juya inna ina wuni? Ya gaisheta, tare da barin wurin, “inna kin fita ne tun dazu na shigo ina sallama ashe tana kicin taki amsawa”
toh aini banji ba.” uwani ta fada.
Inna taji da gangan taki amsawa.”
toh ai kaji tace bataji ba, tunda ba kunne daya kuke dashi ba, ina zaka sani? Yayi murmushi, “toh ki kawo min abincina, bai jira amsarta ba ya wuce dakinsa.
Mirsisi tayi, saida inna tace, “ki dauka ki kai masa mana ‘yar inna.” ta dauka acikin sanda ta isa dakinsa, tana isa ta ajiye a bakin kofar, ta ruga cikin gidan. Ya kalleta, murmushi yayi, ya karasa dashi cikin dakin.
Washe gari ya shigo gaida inna, take ce masa, “tunda kasa aka daura ma aure da uwani, nima inada nawa sharrudan, na farko inaso saina shirya bana so kayi maganar tare warta har saini karan kaina nayi tunanin hakan, sannan zata ci gaba da zuwa makarantarta.
Yace, “na amince inna, a lokacin uwani ta shigo idonsa akan kugunta, ‘yan kayan data sane ya fito mata da surarta, yayi ajiyar zuciya, amma idonsa na kanta, gun inna ta nufa ta zauna. “ina kwana uncle? Ya amsa aciki, tayi kamar bata lura da yadda yanayinsa ba a ranta tace kai ka sani, kar ma ka amsa mana.”
taci gaba, “inna inaso inje gidan amarya balaraba, nida lawisa.”