UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 11 BY SHATU
UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 11 BY SHATU
Seda akai sadakar bakwai sannan washegari Baba yazo Dan daukata tareda Ammi da Gwoggo da zata Kara musu gaisuwa, Tunda garin ya waye Mama ke kuka, Baffa kamar yadda suke Kiran mahaifin su Yana ta lallashin ta da ni kaina da nake ganin zuciyata ta gaza, Ina ganin kamar rayuwata karewa zatai, ban taba kawowa cewa haka zamu rabu ba, ban taba kawowa zai tafi ya barni a duniya ba so early, Allah ya kaddara hakan ce zata kasance, Amma ban kawo hakan ba. Da kyar aka banbare ni daga jikin ta na nufi mota, inata kuka Wanda har yau idan na tuna dacin da naji lokacin da nake kukan se naji idanuna sun ciko da kwalla, se naji wani Abu more of a lump ya tsaya min a makoshi. Kuka nayi na rashin abinda zuciya take so, I just longed for him, his voice and everything about him, lokuta da dama se naji kamar echo din muryar shi, ko kuma Ina zaune se naji kamar ya shigo na Jima ban daina kukan rasuwar shi ba, ta girgiza ni tazo min a bazata, ta Kara sakawa na Kara Zama
reserved. Seda muka tsaya a asibiti aka duba hannuna sannan doctor ya bawa Baba shawarar ya nema min psychotherapist saboda yadda yake gani I’m already in a state of depression. Gaba daya a kwanakin Baba hankalin shi a tashe yake, karku manta Anty Rumasa’u tana can asylum bawai ta warke bane, dukda jikin da sauki matsalar da ta fara samun sauki se hallucinations su dawo shikenan se ta koma gidan jiya.+
Se yamma muka karasa Gumel, Ammi ta hada min ruwa wanka, Rayha ta taimaka min nayi wanka sannan na dawo na shirya na kwanta kan gado, Ayaan na dauke da Little tana Mata Wasa yarinyar nata bangala bakin da Babu ko hakori daya tana dariya, kawai se na shagala Ina kallonta, har a lokacin na manta da damuwa ta, ganin hakan yasa Ayaan daura min ita akan cinya ta, na rike ta Ina jin soyayya ta cikin zuciyata,ita Kuma tayi tunanin Rayha ce se ta kwantar da kanta a jikina, Amma tana jin sallamar Rayha ta dago ta kalleni sannan ta kalli Maman ta se ta gangara zata tafi, Rayha ta dubeni tana murmushi jin dadin ganin Ina murmushi tace
” Wai ta gane bani ba ce”
Dan shafa kanta nayi na gyada Kai bance komai ba, Zama tayi tana Dan min hirar can Qatar din Amma ko kadan ba gane abinda take fada nake ba. Can na dubeta nace
” Anyi retrieving wayata a gurin kuwa?”
Ta gyada Kai ta dakko min wayar da taci screen Amma Baba ya sake min wani sabo, cikin sauri na shigo scrolling pictures Dina, hotunan shi na samu tsiraru saboda da mukai fada na riga na goge, I felt heartbroken da bamuyi fada ba da may be bazan rasa hotunan sa da conversation dinmu ba. A hankali labari ya bazu aka ta min taaziyya, Yaya Ismail yazo shida Hanifa dake da karamin ciki. Ina zaune a kofar parlon Ammi ta shimfida min sallayya, hannuna rike da wani sabon book da Baba ya kawo min dukda kokarin focussing da nake amma dukda haka wani lokacin se na gagara gane abinda na karanta. Sallamar da naji yasa na dago idanuna, Yaya Ismail ne a gaba se bayan shi Hanifa, nayi mamakin zuwan ta Dan ko Anty jidda Bata je maska ba haka ba ta Kira ba, dukda mutane da dama da banyi expecting ba sun kirani sun duba ni sun Kuma min gaisuwa. Na rufe littafin hannuna Ina Dan sakin fuska ta, suka karaso har zata zauna gefena nace
” A’a mu Shiga ciki”
Mikewa nayi na Shiga ciki Ina jin kaifin idanun Ismail akai na, seda suka zauna sannan na Kira Ammi, Rayha already sun koma Kano, su Kuma su Anisah sunje gidan Gwoggo. Ammi ta fito Suka gaisa tana tambayar su yadda suke, suka Mata gaisuwa sannan na zauna Nima Suka min gaisuwa, Hanifa tace
” Kina cin abinci kuwa? Kin rame da yawa”
Na danyi murmushi na shafa wuyana nace
” I’m fine”
Amma nayi mamakin yadda take min magana a hankali with concern, Ashe ita bani ce target dinta ba, sun Jima sannan suka tafi Bayan sun kawo kayan duniya da yawa, se books da ya siyo min yace na dinga karantawa zai dauke min hankali. Bayan rasuwar shi da wata daya na Dan ware ba kamar ko yaushe ba, Ina Hira na Dan saki jikina, hannuna an cire cast din Kuma cikin aminci Allah ya nufa gyara yayi, a wañnan lokacin Kuma se wata matsala ta kunno Kai wadda daya nayi expecting hakan daya Kuma ban taba kawowa ba.
STORY CONTINUES BELOW
Ina zaune akan kujera da wayata a hannu muna Hira da Widad, lokaci lokaci Ina Kara bibiyar chat dinmu da ya riga ya shude, na duba last seen dinsa a month and days offline, se naji idanuna sun Kara taho min, da sauri na maida su Dan munyi da Ammi na daina kuka, saboda idan Ina kukan tayar Mata da hankali nake, shiyasa yanzun ko abun ya ciyo ni sede naje dakin mu na kwanta nayi me isata. Wayata ce ta fara ringing se ta katse min tunanin da nake, hakan yasa na girgiza kaina Ina duba caller ID din, Anty yusra na fada a hankali sannan na Kara a kunnena.
” Sofyn Ammi”
Haka ta koma fada min, na danyi murmushi na gaisheta ta amsa tana fadin
” Bakida kirki yanzun anyi Miki irin wannan rasuwar sede Hussy ta fada min ko?”
Na Dan girgiza Kai nace
” Anty yusra bazaki gane ba, gaba daya ban Jima da dawowa nutsuwata ba, wallahi Babu Wanda na fadawa kowa a gari yaji. Amma kiyi hakuri”
Se ta sassauta muryarta tace
” Allah ya jikan shi ya Masa rahma, ke Kuma ya zaba Miki mafi alkhairi”
Bana son wannan adduar da ake min, to Amma ya zanyi tunda har ni din ban mutu ba Dole ne ayaimin, mundan taba Hira tace min zata zo har Gumel tayi min gaisuwa, nace ba se tazo ba wayar ma ya Isa. Da haka mukai sallama tana ta insisting, se na kyaleta kawai.
Washegari na manta munyi maganar da ita se nabi Ammi shagon ta, tana bude shagon naji kawai bana son Shiga Dan haka na tafi gidan Gwoggo. Anan na samu Anty jidda tazo itada Anty Ikhilima . Na gaishe su na wuce dakin Gwoggo se naji ta kwala min Kira, na fito tace min
” Sofy ya jikin?”
Na amsa da da sauki kawai na koma ciki, Ina ji suna magana kasakasa Amma banma bi takan su ba. Ban Jima da kwanciya ba se naji sallamar Ammi, na sakko Ina jinta suna gaisawa da Gwoggo tana fada Mata nayi baki ne, fitowa nayi nace Mata
” Su waye?”
Ta dubi su Anty jidda da Suka kasa kunne se Taki amsa ni haka na ma Gwoggo sallama muka tafi. A kofar gida na ganshi a tsaye hankalin shi dukka akan wayar dake hannun shi, tundaga nesa nasan ko tantama Babu shi ne, Muna zuwa daf dashi ya dago Yana kallona, se kuma ya maida wayar aljihu ya leka motar yayi magana Sega Anty yusra ta fito, zuwa lokacin muka karasa inda yake tsaye, ya tsugunna har kasa ya gaida Ammi sannan ta shige ciki itada Anty Yusra ni Kuma na tsaya a gefen shi, tubda na tsaya yake kallona ni Kuma uffan Bayan gaisuwa bakina ya kasa furtawa se takura da naji nayi.
” Kiyi hakuri! Allah ya jikan shi yayi Masa rahama”