SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 5 BY Xayyeesherthul-humaerath
SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 5 BY Xayyeesherthul-humaerath
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wayarta ta mutu,wani irin tsaki tayi domin batama lura da cewa chajin wayar ya kusa karewa ba sai ganin mutuwarta da ta yi adai,dai lokacin da tafi bukatar wayar Amman ba dama,ba ta San lokacin da kwalla ya fara zubo mata ba gashi ba nefa alokacin ji take tamkar An rabata da muradin rantane baki daya,kuka tayi mai isanta har barci ya dauketa batare da ta sani ba.
Da Asuba kuwa Mammah na tashinta kan ta yo alwala sai da saka wayarta chaji, tsabar wayar ta kona mata rai bata kara bi ta kanta ba sai da ta gama shirin tafiya skul,ko kunnata ba tai ba, tasa acikin Jakarta kawai.
Tare da suka fito da Mammah ,Ita tai Skul Mammah kuma asibiti shi ko Sabeer tun karfe bakwai ya tafi skul.
Nafe daya suka shiga sai da aka sauke Nafeesa Kan Mammah ta huce asibiti.