KALLON KITSE CHAPTER 9

KALLON KITSE CHAPTER 9

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

ga baki dayansu suka kasa amsa sallamar, sai da indo ta amsa ita dake cikin kicin, da sauri ta fito dan babu tantama tasan mai muryar, inna baki ta sake tana kallon kofar falonta, jafar ne ya shigo, yayi saurin isa gun datake zaune ya tsugunna ita kam uwani gefe ta koma, miyau ma ta kasa hadiyewa, sai kallon jafar ta keyi, yayi kiba, yayi kyau. Ita kuwa inna kasa magana tayi, shiya riko hannunta biyu, yasa a nashi shima kasa magana yayi, amma hawayene cike da idonsa, a idonsa yaga inna tadan kara tsufa, farin ciki tareda alhinin abunda ya faru yakeyi, bashir ne ya soma cewa dan Allah inna ayi mana afuwa, munyi laifin da bazamu iya tantacen irin yanayin da muka cusa maku bakin cikiba, amma gamu yau mun dawo muna baku hakuri, ba dan halin muba, a yafe mana.” kukan da uwani ta saki shiyasa suka gane akwai wani kusa dasu. Inna ta kwace hannunta ta rumgume uwani, itama kwallan ne suka cika mata ido, amma tayi na maza ta maidasu ciki, ta mike tsaye tareda riko hannun uwani ta kalli bashir tace, na yafe maku, amma inaso ku tashi, ku koma gun wadda tafimu mahimmanci a rayuwarku.”

zata wuce jafar ya rike kafarta gwiwarsa akasa, inka gani abun tausayi, idon nan nasa jajir kamar jan gauta yace, inna don girman Allah ki sassautamin, wallahi bada son raina haka ta faruba, nima bansan yadda akaiba, kinawa Allah ki yafemin ki daina fushi dani, hakane jafar naji nakuma yafe maka kamar yadda tun farko, saidai na hakura da kai na barwa matarka ai, bakomai, nan ta barshi suka shige daki da uwani, babu magiyar da jafar baiyiba amma taki saurarenshi, saida bashir ya riko shi zuwa kujera suka zauna yana bashi magana,+

wannan shafin yadan yage kuyi hakuri

“haba bashir fadi shawararka, ai ita nake jira, don gaskiya banajin dadin yadda inna kemin, sai kace ba danta ba? Hakane sai dole kayi hakuri, sai shawarar da zan baka, why not ka auri uwani!!!.  Da sauri jafar ya dubi bashir, ya fito da idanuwansa waje, haba bashir wace irin shawarace wannan? Me zanyi da kankanuwar yarinya irin wannan kazamar? Da sauri bashir yace; ada ba take kazamar, amma kasan yarinyar nan  matan manya ce, don babu abunda bata dashi, tun jiya dana ganta nagano inna na matukae son yarinyar, sannan duk wanda zai aureta inna zata soshi, dan haka nake baka shawarar aurenta, sanadin haka zata manta da komai, ko baka ganeba?

Jafar shiru yayi yana girgiza kansa a hankali, anya haka zata yiwu bashir? Yarinyar nanfa bata fi shekara sha shidda, dama gata ta rainani, saboda inna ta faure mata, shiyasa ta shagwaba….

“kai aboki barin fada maka wani abu, wannan yarinyar tafi maka matan bariki dan inaga kai har yanzu baka kawo abunda suka koya maka ba, na wulakantaka, na yaudararka, na wulakanta ‘yan uwanka, in baka saniba, jiya baba yunusa ya bani labarin irin wahalan da suka sha kafin Allah ya dawo dakai gida.

Saboda mace kabar mahaifarka, cikin bakin ciki harna shekaru hudu, amma duk wannan bai isheka tunaniba.

Kai inba son ganin KITSE GA ROGO babu abunda kakeso, macen bariki bala’in ne duk da ba duka aka taru aka zama daya ba, amma am warning you, kayi a hankali saboda ba duniyace mataba, kaje kayi tunani.” ya mike ransa a bace.

Da sauri jafar ya jawo hannunsa, shima ya mike haba aboki yi hakuri mana, kasan Allah na amince dakai, duk abunda kafada gaskiya ne, na kuma amince da shawararka, amma inaso zan kara tunani akai. Bahir ya saki fuskarsa yakai masa duka, “haba ko kaifa yarinyar nan tanada tarbiyar inna, da wani can ya dauketa, gara kai ka aureta, nasan nan gaba kadan zaka gane abunda nake nufi, waikai me matan bariki suke dashine, wai daka manne musu?

Wallahi indai yariyar nan ka aura, toh zaka ga bambanci kaida kanka, saika bani labari.Jafar a daren ranar kasa bacci yay, dan gani yake bazi iya auren uwani ba, she is too toung.” ya fada afili, shikam ai ko ‘yar shekara sha takwas bai iya aurenta,, balle ‘yar mitsitsiyar yarinya kamar wannan.

Shi yafi son matan da suka waye, wadanda suka iya soyayya, ba irin wadanan yaran kauyenba, da basu uya ko gyaran jiki ba, saika ga mace, har mace, amma common kula da jikinta bazata yiba.

Yayi ajiyar zuciya, tareda juya kansa, “it cannoy be possible, bazan iyaba! Duk a fili yake zancensa.

Tsaki yaja ya tashi ya shiga toilet yayo alwalah, ya soma nafilfili kamar yadda ya saba.+

***** ***** ****

uwani wanda a makaranta anfi saninta da Aisha Dalhatu duk da ba wani shekaru gareta ba, amma Allah yayi ta da wayo, tana tsaka tsakiya wurin ilimi, wato average a turance kenan.

Uwani irin yaran nanne da suke da surutu kamar yadda kuka sani tun farko, tanada fada sosai, in kayi da ita, dan hakane bata shiga lamarinka, dan ma kada ku bata.

Lawisa ita ta kasance mai hakuri shiyasa suke zaune lafiya da uwani, sannan sunfi shiri da hafsat, saboda hali ya zama daya da uwani, itama bata da hakuri, duk da bata kai uwani fada ba, sai dai fa’iza itama ba kyaleba, shiyasa basa shiri da uwani sosai, sannan fa’iza ta zama irin ‘yan matan nan da suke nuna komai su suka iya, wani bai iyaba.

Shiyasa a kullum suke fada da uwani, ko dan ita fa’iza tana zama a Abuja ne?oho!

Kamar kowane hutu yanzu ma ansamu hutun mid-term break dan haka fa’iza ta shigo gari itada hafsat.

Uwani ce zatayi sauka tun watan daya shige, sai akayi shawar a bari sai su hafsat sun sauka, sai a shirya walima, dan haka shine aka sa shi dai-dai da mid-term break dinsu,

haka kuwa akayi, dama ana shirin haka jafar ya fado

suna zaune baki dayansu a falo, suna ta hira, inna ma tana zaune tana ‘yan karance-karancenta, daga sama sukaji sallamar jafau, hafsat da fa’iza da sauri suka mike suna fadin, “Oyo-oyo uncle.”

suka rungumeshi, shikuwa cike da fara’a ya rugumesu yace, “a’a daughters yaushe agari?,” suka fada masa, suka sami wuri suka zauna, suna kara gaisawa.

Uwani kam tana gefe ko kallo basu isheta ba, ta maida hankalinta kan t.v tana kallo. Ya dubi inda take, “ke baki gaisuwa ne?

Ta dan wayance tace, “dama inaso in gaidakai uncle, so nake su hafsat su gama nasu.” sai a lokacin ya gaida inna, yace, “ke tashi ki dauka min abinci na.”

ta mike ta fita binta da kallo yayoi, gaskiyane uwani ta girma, dan ba abunda yafi daga masa hankali irin kirjinta, nan gaba inta kara zama mace ba karama  za ayiba.

Kodai ya yadda da shawarar bashir ne? Kai no tayi karama dayawa, zai hakura har sai ta kai munzalin sanin ciwon kanta…..

Ita ta katse masa tunani da ajiye abinci a gabansa, idonsa sai akan kirjinta.

Da sauri ya dauke idonsa, kai su jafar ba dama, dole yasa yaci abincin amma tunaninta na tare dashi, yana satan kallonta, a daburce, namiji kenan!

Hafsat ta matso kusa dashi tace, uncle gift din me zaka bamu? Gobe fa walimar saukar alkur’ani mai girma zamuyi.”

“kai don Allah, inna ba a fadamin za ayi sauka a gidan nan ba?

“toh kaida yaushe ka shigo gidan, da har zaka san abunda ake ciki?

Ya sosa keya, “kai inna kidaina tuna baya mana, am back for ever, tace Allah yasa.”

ya dubesu “toh me kuke so?

“kome ma kasai mana mungode uncle.”

“hakane badamuwa am going to suprise you, insha Allah.”

haka dai sukai ta hirarsu, har karfe goma na dare, sannan ya fice daga daga gunsu, sun shige daki, suka ci gaba da hira, irin tasu ta ‘yan mata. Fa’iza tace, “bara nayi gulmar uncle. Kunga yadda uncle

ya canza kuwa, sai kace irin halfcase din nan, yayi kyau wallahi.” hafsat tace, kinsan nima abunda na gani kenan, gashi dan gaye, gaskiya duk macen data sameshi tayi sa’a, dan ba karamin haduwa yayi ba, uhm kinga kafarsa kuwa, fari tas kamar wanda baya taka kasa, ance shi soja ne, toh amma kamar baya wahala….ke kinga yanda ya goge kuwa? Kinsan ance doctors a sojoji sunfi jin dadi, dan su an daukesu musamman ne agun aikinsu.”

ita dai uwani saurare takeyi, dan tun shigowarsa tasan ya samu lafiya, dan ta shaida kyawun nasa.

Babu abunda ke damun jafar irin yadda inna bata saki jiki dashi ba, sam bata shiga harkarsa kamar da, lallai yayarda da abunda bashir yace masa, dole ne ya fuskanci irin haka, gashi kuwa yana gani.

Yayi tsaki, zaije ya nemi shawarar baba yunusa, dan abun ya isheshi, dakyar bacci ya daukeshi.

Washe gari tunda safe su uwani suka tashi, suka gyara gida kamar yadda suka saba, masu kujeru suka shigo da kujeru a tsakar gida, an fara jerawa, a lokacin jafar ya shigo cikin gida, ya sami inna zaune a kujera, tana karin kumallo, ya nemi wuri dab da ita ya zauna.

“inna ina kwana?.” ta amsa cike da fara’a, saidai abun da ya lura dashi, kamar fara’ar bata kai cikiba.

Ya matso ya laika kwanon abincin data keci, waina ce miyar allaiyahu, tasha man shanu, zaisa hannunsa, saiya lura da tabata fuskarta, ya tuna da inna ba abunda tafi so kamar su zauna suci abinci tare, amma gashi kyamarsa ma Amma gashi kyamarsa ma takeyi, ita ta tsinka masa tunani,

“bari akawo maka naka, wannan nida uwani ne.”

ya saki baki eh lallai ya yarda inna bata sonsa, dole kuwa ya nemi son nan, ya dawo dashi kamar yadda suke da.

In banda sha’anin uwani ba ruwanta dana kowa, su duka ‘yan matan suka shigo falon, ko wacce ta gaidashi, ya amsa cike da kulawa. Uwani ta zauna zata fara cin abinci.

Ya dubeta ke tashi ki debomin abinci.”

inna ta dubeshi tare da bata fuska, “kai dai kazo ka damemu, keyi zamanki har ki gama.”

ya lura uwani taji dadin hakan, shiru yayi yana kallon uwani batada dan kwali akanta, sannan batayi kitso ba, tayi parking din gashinta, gashinta irin wannan mai taushin ne, duk da batasa relazer ba, yayi kwance lub akanta

dan tsantsine dashi.

Gashin yayi masa kyau, da sauri ya kauda idonsa, shi wai meyake damunsa ne, ya ya za ayi yarinya ‘yar kama tana nema ta maidashi wani wawa? Duk inda yake inbanda tunaninta ba abunda yakeyi.

Hafsat ta tsinka masa tunaninsa da ajiye masa abinci a gabansa, “ga abincin nan uncle rabu da inna.” harara uwani ta sakar mata

“toh ‘yar iyayi a rabu da ita din meye ruwanki?

“eh da ruwana, ‘yar shiga sharo ba shanu.” magana uwani zatayi sai suka hada ido da jafar, dauke kansa kenan an dauke wuta, tayi shiru ta maida hankalinta kan abincinta. Lokacin hafsat ta samu damar zakalkaleta. Inna tace, “rabu da ita ke dai ba a magana idan anacin abinci.”

haka suka kare cin abincin, jafar dai a hankali yanata nazarin uwani.

Sai karfe tara da rabi zainab ta iso, gida ya cika da murna, gaskiya mumy (haka suke kiran zainab) kinyi sammako?

“eh toh gara mu shigo kar muyi latti. An shigo da kwanoni dauke da kayan fulawa, irin su, bonus, donut, cake, dabulan, da kuma gurasa da miyarta, sukaita jin dadi, dan suna son gurasa, tunba uwani ba, da yake akwai wata ‘yar kano anan gusau tanayi, fashi kuma ta iya sosai.

Salaha ma ta iso da tata gudumawar, nasu sweet da cewing-gam duk dai komai anshirya, harda na kyauta, ‘yar jakace aka hada hotunansu su duka sai akasa Alqur’ani mai girma dasu hadisai, gaskiya abun yayi sha’awa.

Ancika sosai, a wurin walimar jafar abaya ya soyo musu, shine gudumawarsa, yata jini-ni dasu, salaha wai anki a fadamasa balle yayi wani abun, inna tace, ni nace kada a fada maka, saboda dai an riga da angama shirya komai, yaushe ka shigo? Yau kwananka shida agari, donme za ayi maka maganar walima? Muka san da irin shirinka jafaru?

Kansa a kasa, idonsa jajur, lallai yayiwa inna laifi, tausayinta ya kamashi, ya kirkiro murmushin dole, “o.k hakane inna, amma da andan fadamin koda bazanyi komaiba am part of the family.” inna tai ajiyar zuciya kawai batace komaiba.

Haka akayi taro yayi kyau ko wacce tayi karatu, kuma anyaka raguna har uku, can sai akaga anata shigowa da nama, abun ya basu mamaki, inna ta kira mal. Mamman ta tambaye shi inda aka samo nama yace, “ai inna tun safe jafaru ya aikeni na siyo, ashe bai fada muku ba? Allah yayi albarka,

Allah ya kara budi.” inji mal. mamman, “ai haka ake so.” ga baki daya aka amsa amin.

Anyi walima yayi armashi sosai, saida mangariba aka watse, shikam jafar daya bar gidan, wurin baba yunusa ya wuce, saida

suka zauna sosai sannan yace, “baba nazo da wata bukata ne, don Allah a taimaka min.”

inajinka jafaru Allah yasa zan iya.”

“baba inaso ne ka nema min auren uwani gun inna! Baba yunusa ya wangale baki dan murna, “dama nayi maka sha’awar haka jafaru, da yake ban san ra’ayinka ba, shiyasa banyi maka magana ba, tunda abun ya zama haka ba damuwa, zanyi duk abunda zanyi dan inga haka ya kasance.

“nagode baba Allah kara girma.” hira suka shiga sosai, saboda abun ba karamin dadi yayiwa Alh. Yunusa ba, ya kara nuna masa muhimmanci da kwarin gwiwa.

Tunda safe asabar Alh, yunusa ya shiga gidan, aka tarbeshi da abincin kari, bayan ya gama yace yanaso yayi magana da inna, harda zainab dan saboda a falo suka zauna. Adai-dai lokacin jafaru ya shigo, gabansa sai faduwa yakeyi, ya sami wuri ya zauna, shima baba yunusa, ya fara, “Haj. Fatima gunki nazo, dan jafaru ya sameni da wani sako mai muhimmanci, nasan yayi tunani kwarai da gaske da yayi hakan.

Fatima nazo nemawa jafaru auren uwani, dan kece uwarta, kece ubanta, kinga sai ayi tuwona-maina, Allah ya kawo abunda sauki, ni banyi tsammanin zai sakko hakaba, kinsan shi Al’amari dama na Allah ne, dan hakane nace bara nazo da kaina, ba sakoba in fada maku wannan abun farin cikin.”

ga mamakinsu saiji sukayi inna tace, “gaskiya niban yardaba.” Alh. Yunusa ya dubeta cike da mamaki, baki yarda bafa kikace? Me yayi zafi haka? Bashi ba harda jafar yayi matukar mamakin hakan, lallai inna ta tsaneshi, abun ya daure masa kai, inna ta katse masa tunani, “gaskiya ni ban yarda ba baban yusrah.”

ta kara maimaita maganarta, kuma fuska babu alamun wasa acikinta.

Ta gyara zama, bazan iya ba jafar auren uwaniba, saboda ban yarda dashi ba, bazan iya baiwa uwani mijin da hankalina bai kwanta akan shiba, dan dai yarinyar nan amanace guna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page