Hausa Novels

SIYASA TAAH CHAPTER 4 BY MAMAN TEDDY🧸

SIYASA TAAH CHAPTER 4 BY MAMAN TEDDY🧸

Nan take ya hau gudu,gudu kam irin na kwatan kai,wanda a haka dai Allah ya taimaki Meemah ta tsere mawa wannan sojojin ta hanyar shigewa wata adaidaita dake tafya a tsakiyar kwalta,amma a haka ta shige,nan ko me Adaidaitan da yake ta hadu da dan arxiki ba tare da yaji inda zai kaita ba,da kuma inda take yajah hadi da figarta da karfi kaman zai kifah…ita dai Meemah Salati take,wanda sam Hankalinta bai natsu ba sai da taga tayi nesa da inda Sojojin suke,sannan tafara maida numfashi.

Sukan Wannan sojojin babu wanda basuyi nasarar kamawa ba sai Meemah,Wanda a haka suka tarkatasu suka nufi dasu gidan gonan da Major yabasu umarni,tun kan su isa suke azabtar dasu,suka fara shan duka,niko nace wannan inaga kuma Ankai su wannan wuri?….

Bayan ankaisu ne M Abdurrahman ya tambaya ciki kam da akwai wannan yarinyar? Wato meemah,anan ne suke shaida masa da cewa”Ai ta boye masu,sam basu ganta ba. Shiru Major yy na sakanni kamin yace”Ohk tom zanyi tunani akan wannan yarinyar,yanxu ko horamun wanda kk kamesu……Yana fadin haka baijira jin mai sojan zai fadi ba ya datse kirar tasa.

Ako can bangaren Honorable dasa’a,kaman yanda yasaba,koda.aka kawo masa yaran gidan marayun  nan sun kai mutum 12,bai saka an basu komai ba,a haka sai da suka kwana biyu,kamin nan tuni suka galabaita…babu yaron dake iya sarrafa kanshi saboda yunwa.

Sawa yayi aka fara fito maasa da yaran,kamin ya umarci wani babban sargent ya fara aikin shi,da ido yaran ke bin shi da kallo,nan take ganin wannan katon mutumi mai kama da super D yana tunkarosu hannun sa rike da wata irin makami,wanda fasalta irin shi zai wuya,babu tausayi bb imani,yafara cafko Yarannan yana daga su da hannu daya,kawai sai ya jefah a wani daki,wanda daga wajen shi wani irin duhu xaka gani,sai wurin da zaka hanga kaman rijiya….ihu yarannan suke,wanda a haka yake daukar daya bayan daya yana antayawa,shikam Honorble sai mirmushi yake yana fadin lallai siyasata zai kyau…Sukam makafi da basa gani sai dai suji kawai anyi sama dasu an wurgasu wannan daki,wanda shikenan sai kuma a Lahira. A haka ne y zamana saura mutane uku ciki kam harda Ahyan,hannu wannan mutumin yasaka yana kokarin dago Ahyan,amma sai yaji tayi masa nauyi kaman dutse,sam ya kasa Daukarta,wanda sao a sannan ya bude yan ficificin idon sa,wanda daka gani kasan babu imani a cikin su…. Firgigit yy ganin yanda kamannin ta ya sauya,kwarmin idon ta na fidda ruwa,amma bana hawaye ba,a wannan karon farin ruwa yake xuba daga idon ta kaman Nono ko madara. Kamin yy mata mgna ne cikin wata murya mai fitar da sautin Amo take cewa”karda ku taba ni,kada kuyi yunkurin cutar dani,mun dade muna rangwama maka ,tayi mgnar tana kallon Alh Dasa’a da shima abun ya dan firgita shi,duk kyaun yarinyar lokaci daya ta koma kaman Aljana. Kai yanka mun ita gunduwa gunduwa kamin ka jefah fah ta cikin dakin dodon. Cike da himma Wannan mutumin ya nufi Ahyan,wanda da isan sa ne suka yajah ya tsaya da wuka a gaban ta,sai kuma suka ga yafara kasa,kan sa yafara faduwa sai gangan jiki da kafafuwa duka suka xube sukayi gunduwa gunduwa……jah baya sukayi wanda kamin suyi Aune kawai sai sukaji zafin wuta ta koina na tashi,waigawar da zasuyi ne nan sukaga Wuta ya kama gidan baki daya,wanda allah ne kadai zai tsiratar da mutum…ai ba shiri harta Honorable guduwa yy,kowa na son ceto rayuwarsa…Gigif tayi kaman wanda ta farka daga barci,kamin ta hau ware² tana duba inda mutanen sukayi tana Mamaki ganin bb kowa. Ahyan…!! Tajiyo an kirata da muryar da tafi kama dana Wani mugun halittan…juyowa tayi nan taga Matan tsaye tana sakar mata murmushi,kamin tace kina so na koma dake gidan Marayu n ki,ko na tafi dake inda muke rayuwa? Hannun matan Ahyan ta rike,wanda yanda ta saki jikin ta zai nuna maka alaman da tasan matan ne… A’a ki maidani gida,tayi maganar cikin zazzkar muryar ta mai dadin sauraro…murmushi matan tayi kamin takai hannu tana rufe idon Ahyan,sai kuma taji ta bude mata,a cikin gidan Marayun ta tsinci kanta,wanda ware² tayi a wannan karon babu wannan matan,cike da ko inkula tafara tafiyarta tana nufar sasan su,wanda a filin gidanne ta tadda Mama Batula….

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE