HEEDAYA CHAPTER 8 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 8 BY By Khaleesat Haiydar

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mami ta bude kofar parlonta jin ana knocking, suka yi ido hudu da Shuraim, sauke idonsa yyi da sauri, murya can 

kasa yace “Ina kwana” A takaice tace “Lafiya…. Ya aka yi?” Yace “Karatu xa mu yi?” Mami tace “Da wa?” Ya d’an 

yi shiru sannan yace “Ban san sunanta ba” Mami tace “Toh sai kayi kokarin sanin sunan nata coz gida daya ku ke 

ynxu” daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta da wani irin kallo, Mami ta karasa sa ma Heedayah kayanta don har 

tayi wanka, ta dau hula ta sa mata a kanta sannan tace “You listen and pay attentive kin ji, Kuma kiyi kokari sosai, 

idan kin dawo xaki koya min nima” tace “Toh Mami” Mami ta kama hannunta suka fita xuwa parlor, har sannan 

yana tsaye, dai dai kusa da shi Mami ta tsayar da Heedayah, sannan ta juya ta koma ciki ta kulle kofarta, Heedayah 

ta kai hannu tana laluba wajen ta ji inda yake, hannunsa ta ta6a, bbu bata lkci kamar jira yake ya buge mata hannun 

yace “Are you stupid” Ta janye hannunta da sauri kamar xata yi kuka tace “Ni me na maka??” Ya kalli left sannan ya 

kalli right ya fixgo hannunta ya fara tafiya, bin sa take hawaye cike idonta tace “Ni ka sake ni bana so, baxan yi 

karatun ba kuma, baxan yi ba….” Ko saurarenta bai yi ba har ya isa wani area cikin parlon wanda ya kasance study 

area din Abba, sannan ya saketa yana mata wani kallo yace “Kika ce baxa ki yi karatun ba??” Cikin kuka tace “Ehh 

ni baxan yi ba, ka kai ni wajen Mami” ya ja kujera ya xauna yace “Sai ki kai kanki ai” durkushewa tayi a kasa ta fashe da kuka sosai tace “Ni sai na gaya ka da Abba wllh….” bude kofa aka yi Shuraim ya juya da sauri bai jira ya ga 

wanda ya bude kofar ba ya xamo kasa kusa da ita ya dake cike da karfin hali yace “Okay, sorry mu yi karatun ynxu” 

ta make kafada tace “Ban so” satan kallon cikin parlon yyi duk da bai ga wanda ya fito ba har sannan, ya wani hade 

rai yace “I said sorry” Kamar jira take tace “Ban so nace” sai kuma ta fashe da wani sabon kuka, kamshin turaren 

Abbansa da ya ji yasa yasan Abba ne a parlon, ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta a hankali yace “But nace kiyi 

hakuri, I’m sorry” ta turo baki tace “To me yasa xaka buge min hannu sbda bana ganin ka, kuma shine kake ja na don 

in fadi in ji ciwo” Ya kara satan kallon parlon cikin dakiya yace “To rama” ta kai hannu ta laluba kafarsa sannan ta 

maka mashi duka a nan, kallonta kawai yake da mamaki xuciyarsa na tafarfasa, still controlling himself yace 

“Shkkn?” Ta gyada masa kai a hankali tana goge idonta, ya koma saman kujera yace “To fara karatun” tayi kasa da 

murya ta fara karatun a hankali, har Heedayah ta tsaya a aya na 15 bai ji inda xa ayi mata gyara ba, her recitation 

was perfect and cool for her age, sai dai wayarsa kawai yake dannawa, Ya saci kallonta ganin tayi shiru sai dai bai ce 

komai ba still pressing his phone, ta turo baki tace “To ai a nan mu’allimata ta tsaya min” yace “Toh sai ki tsaya a 

nan din” yana fadin haka ya mike ya tafi kitchen, Sabuwar me aikin da Mumy ta dauka ne a kitchen din tana ta gyare 

gyare da goge goge, yace “Wancan yarinyar xaki dauka ki kai ta wancan part din…” Gaishesa tayi da ladabi tace 

“Wace yarinya yallabai?” Fita yyi kitchen din yace “Ki taho ki ganta” sai da ya tabbatar ta ga Heedayah sannan yayi 

wucewarsa sama, har part din Mami mai aikin ta kai ta, duk da sai faduwa gabanta yake don ba karamin warning 

Mumy tayi mata ba kan cewa ko bangaren Mami kar ta kuskura ta bi balle ta shiga, Mami ta bude kofa ta amsa 

gaisuwan mai aikin sannan ta kama hannun Heedayah suka koma ciki ta kulle kofar, Mami na kallon Heedayah tace 

“Ina me koya maki karatun?” Heedayah tace “Mami bai koya min komai ba” Mami tace “Me yasa?” Heedayah ta 

6ata fuska tace “Mami mugu ne, I don’t like him to teach me anymore….” Mami dai bata ce komai ba ta wuce can 

bedroom da ita, Heedayah tace “Mami he is wicked, ni nafi son wannan din nan ya koya min” Mami tace “Wa?” 

Shiru Heedayah tayi sai kuma tace “Yace min sunansa Fatima shi ma, kilan baya son gaya min sunansa” Mami na 

kallonta tace “A ina yake?” Heedayah tace “Wanda ya xo jiya ya tafi da ni” Mami tace “Sunansa Junaid, but you call 

him Yaya” tace “To, na fi son Yaya ya dinga koya min” Mami bata kuma cewa komai ba ta xaunar da ita saman gado 

tace “Kwanta kiyi baccin ki xan je in hada maki breakfast” daga haka ta fita dakin, Heedayah ta kwanta. Mami na 

tsaye kitchen su Rabi’ah suka shigo ajiye plates da cups da suka yi breakfast duk suka fice bbu wanda yace mata 

komai, ta gama dafa Indomie da kwai da shayi da take yi ma Heedayah ta fito kitchen din, a parlor ta tadda Abba 

alamar he is going out kuma ita yake jira ta fito kitchen, yana kallonta yace “Ina Heedayah, bata gaisheni ba yau” 

Mami tace “Let me bring her” daga haka ta wuce bangarenta, Duk wannan abun Mumy na ta kai komo parlon kai 

kace wani abu take yi, Abba dai bai ce mata komai ba don har ranan bata gaishesa bata masa magana a gidan, Yana 

ta tsaye parlon Shuraim ya fito shi ma xai fita, Abba yace “Yaushe rabon ka je gaida kaka Aliyu?” Ya d’an yi shiru 

kafin yace “Abba bana dawowa da wuri ne ynxu” Abba yace “Ohk yau ka je ko da kuwa tsakar dare ka dawo, and 

you go with Heedayah ita ma ta gaisheta, she is complaining ba a kai ta ba jiya da naje….” Shuraim ya kalli Abba, 

amma bai ce komai ba, Abba yace “Su Khadijah ma nace idan sun dawo islamiyya su wuce can, so idan ka je sai ku 

dawo tare gaba daya” Mami ce ta karaso rike da Heedayah, Abba na kallonta ya dafa kanta yace “How are you 

dear?” Tace “Good morning Abba” yace “Morning Daughter, kun yi karatun yau koh?” Ai ko rufe baki Abba bai yi 

ba Shuraim ya nufi kofa, Heedayah tace “A’a bai min ba” Abba ya kalli Shuraim da har ya isa kofa cikin tsawa yace 

“Aliyu” Mumy ta karaso cikin parlon da sauri tace “Ba gane Aliyu ba?? Shi Aliyun malami ne ko kuma makafi na 

haifosa ya xo ya dinga yi ma karatu, kaga a gaskiya barrister ku tsaya iya Lane din ku kai da Sabuwar matarka da 

makauniyar ka a gidan nan, ku fita harkarta da ta ‘ya yana, Yaushe aka sa Shuraim ya dinga koya mata karatu bani da 

labari? Kanninsa da suka fito ciki daya ma an ga yana koya masu karatu balle makauniya, to wllh ni a kiyayeni a 

gidan nan, ku bar ni kawai yanda ku ka gan ni ayi ta tafiya a haka kar ku kai ni bango….” Abba yana kallon Shuraim 

da kyau yace “Me na ce maka jiya da asuba?” Yyi kasa da kai bai ce komai ba, Abba yace “Good, idan kana son 

ganin the other side of me ka sake tsallake magana ta a gidan nan, wllh sai dai ka tafi wani gidan uban amma ba 

wannan gidan ba, yanda uwarka ta isa ta fada maka kaji, haka nima, idan kuwa watsar da maganata xaka dinga yi a 

kan wani banxa son xuciya na uwarka to you have to change anoda father and anoda home, Kuma ni nayi instructing 

dinka ka dinga koya ma Heedayah karatun qur’ani in har ka isa ka tsallake instruction din in gani” A mugun fusace 

Mumy tace “To sai me don kace ya canja uba ya bar gidan nan?? Kansa farau barrister? Ai ba abun mamaki bane 

don ka fadi haka tunda an gama da kai an shanye ka, nan gaba mu ma duk kora mu xaka yi ka cika gidan nan da 

agololi da ‘ya yan tsintuwa, Kuma in har ni na haifesa baxai koya ma wata makauniya karatu ba tunda ban ce yaje 

xai gani ba” Dariya Mami tayi ta kama hannun Heedayah ta koma bangarenta tana girgixa kai, Shuraim dai bai iya 

yace komai ba, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon, Banda kallon Mumy bbu abinda Abba yake as if thinking of 

how to punish her, cike da neman fitina tace “Ehh ka kalleni da kyau, cewa nayi in dai ni Maryam ina gidan nan 

wllh wllh Shuraim baxai koya ma wata shegiyar makauniya karatu ba, uwar me ya hada da ita xaka ce ya koya mata 

karatu???” Calmly Abba yace “Maryam ki tafi gidanku sai na neme ki, bana son in dawo in tarar da ke gidan nan 

don wllh in har na dawo na same ki a cikin gidana to na sake ki….” Yana fadin haka ya nufi kofa walking just as the barrister he is, Mumy ta bude baki ta bi sa da kallo a sanyaye ta kasa cewa komai…. Kuka bbu irin wanda Mumy 

bata yi ba a dakinta, ta kira duk kawayenta ta sanar masu abinda ake ciki, Hajiya Sadiya ce ta samu karshe a waya, 

Hajiya Sadiya ta dinga salati tana cewa “Ki tafi gida kuma?? Anya kan barrister daya kuwa, yaushe kika dawo daga 

gidan xai ce ki koma? Ehh lallai bbu lafiya, ba dai kin tsaya fi’ili wai ke baxa ki je a nema maki taimako ba, ke da 

kika fi kowa imani, to wllh taki ta sameki, shegiya nake idan haka yar bokon nan ta shigo maki gida, wllh da shirinta 

ta shigo, lafiyayyen shiri kuwa, mance komai xaki yi Maryam mu tafi mu san nayi kafin lkci ya kure maki, ba fa 

karamin case bane wnn wllh, tunda kike da barrister ya ta6a cewa ki tafi gidanku, ki xauna fa kiyi naxari, to wllh ana 

dab da kwace maki gida da mijin ki, wnn makauniya dai ta jaza maki abubuwa iri iri a rayuwa, duk ita ce silar 

faruwar komai” kuka kawai Mumy take kamar ranta xai fita tana cewa “Wlh Sadiya na canxa xuciyata xan iya kashe 

yarinyar nan idan hakan kadai ne mafita gareni, ta tarwatsa min farin ciki, ta tarwatsa min gida, a kanta barrister 

yake min duk abubuwan nan, ga kishiya ta sa an rangada min….” Sadiya tace “Bbu wani lkcn kuka da kumfar baki 

Maryam, ki dau duk abubuwan da kike bukata ki baro gidan nan kafin ya dawo saki ya tabbata a kanki, ki taho nan 

gidana mu san abun yi cikin gaggawa, maxa ki fita daga gidan, Kuma a gaban yar bokon yace ki tafi gida?” Mumy 

ta kara rushewa da kuka tace “Wa ya sani ma ko tana labe duk tana ji, ni dai ga ni nan xuwa ynxu” daga haka ta 

katse wayar ta shiga hada yan kayanta da sauri kar barrister ya dawo, cikin mintunan da basu wuce goma ba ta bar 

gidan xuwa gidan Sadiya. Mami na xaune parlonta misalin karfe biyar na yamma da frnds dinta uku da suka kawo 

mata ziyara, ko marmarin xaman main parlor din gidan bata ta6a yi ba tun xuwanta, hatta bakinta bata bari su xauna 

main parlor, nata parlon take kawo su, bata ma san Mumy bata gidan ba tun safe, aka kwankwasa kofar parlonta, 

mikewa tayi ta isa bakin kofar ta bude, Shuraim ne tsaye sanye da kananun kaya, yyi kasa da kai yace “Ina yini?” 

Tamkar ana tilasta sa ya gaisheta can ciki ciki, Tace “Ya aka yi?” Bbu walwala yace “Abba yace xa mu je can gidan 

kaka da ita” Mami tace “Ita wa?” Yace “Yarinyar” Mami tace “Yarinyar bata da suna?” Shiru yyi mata, can yace 

“The blind girl” Mami tace “Toh ka kirasa ka tambayesa sunanta, kada ka sake xuwa min bakin kofa kana neman 

blind girl I don’t have any” tana fadin haka ta rufe kofarta almost on his face. Da ba don ya san Abbansa is jet angry 

at him ba kuma kar ya sake wani laifin da wucewarsa kawai xai yi ba tare da Heedayah ba, gaba daya ya rasa yanda 

xai yi, bayan kusan minti biyar ya sake kwankwasa kofar, ba Mami bace ta bude kofar wnn karon, Barrister Zuwaira 

ce ta bude, yace “Ina yini?” Tace “Lafiya lau…. A carbon copy of ur father facially but not physically, ba haka 

Barrister Ahmad yake ba gaskiya, be human plss, let me get u the little girl” daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta 

da wani irin kallo, sai ga ta ta dawo da Heedayah da Mami ta sama Hijab har kasa duk da kananun kaya ne sosai 

jikinta tunda gidan Kaka xa a je, Barrister Zuwaira ta mika masa hannun Heedayah da ta bata fuska, ya kama 

hannun nata, ta rikesa gam ya juya ya bar wajen, bin sa kawai Heedayah ke yi kmr xata yi kuka har suka fito balcony, 

a dai dai nan ya kwace hannunsa daga nata ya sauka balcony din fuskarsa daure, a hankali take tahowa bayan ya 

saketa, shi ko har ya fara tafiya ya tuna few stairs dake wajen ya juya da sauri…. Bai yrda ta kai kasa ba ya dauketa 

irin rikon newborn with both hands, ba karamin tsorata tayi ba jin ta tafi xata fadi sae kuma taji an dauketa bata fadi 

ba ta ta6a kirjinsa kamar xata yi kuka tace “Ni dai baxan je ba kuma..Shuraim bai saurareta ba har ya isa motarsa ya bude back seat ya jefata ciki ya kulle sannan ya xaga ya bude 

maxaunin driver ya shiga, tuni Mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan, Har ya isa kofar gidan Baffa bai kalli 

Heedayah dake bayan mota ba, ta rungume hannu kamar xata yi kuka, a compound din gidan yyi parking, sai a 

sannan ya kalleta ta madubi, ya wani hade rai kamar tana ganinsa, d’an tsaki ya ja ya bude motar ya sauka sannan ya 

bude mata side dinta yace “Fito min a mota” Ta make kafada a hankali tace “Ni ka maidani wajen Mami baxan fitoba….” Yace “Kee…. an ta6a xaneee ki???” Bai jira cewarta ba ya jawota ya fiddo ta daga cikin motar ya ajiyeta kasa 

ya rufe motarsa yace “Idan ina magana kina yi sai na fasa maki baki wllh….” Ta fashe da kuka sosai tace “To me 

bakina yyi maka, ni bana sonka you are wicked….” Sudais ya hango ya fito daga cikin gida, hakan yasa ya kai 

fuskarsa dai dai nata yace “Xa ki san I am wicked soon….” Daga haka yyi wucewarsa ya bar ta nan a tsaye, yana kai 

wa inda Sudais yake, Sudais yace “why are you leaving her all alone, how did u expect her to walk alone” Shuraim 

yace “Toh ni d’an jagoranta ne aka ce maka??” Bai jira cewar Sudais ba yyi wucewarsa ciki, Sudais ya karasa inda 

take da sauri ya kamo hannunta ya duka yana kallon manyan idanuwanta da ya cika da hawaye yace “What 

happened cutie…” Cikin rawar murya tace “I hate him….” Sudais ya rungume ta yana goge mata hawayen idonta 

yace “Noo cutie cry no more, mu tafi ciki ki gaida kaka….” Kamar ko jira take ta fashe da kuka sosai, rikicewa 

Sudais yyi ya shiga lallashinta, har sai da ya ga tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, lkci daya ya ji ransa ya baci, ya 

mike ya kama hannunta suka wuce ciki, parlon kaka ya tadda Shuraim, Kaka sai harkar gabanta take tana ‘yan wake 

wakenta na tsofaffi ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma bai kalli inda take ba yana danna wayarsa, Sudais na 

kallonsa fuska daure yace “Shuraim why will you leave the innocent girl all alone….” Shuraim yace “Plss Sudais 

don’t question me, I am not ready to answer you…” kaka ta ajiye tsummar hannunta tace “Me ya faru Sudess?” A 

fusace Sudais yace “Kawai barin yarinyar yyi ita kadai a tsakar gida ya san ba gani take ba, what sort of nonsense is 

that” Kaka ta nemi waje ta xauna tayi tagumi a hankali tace “Ohh naga abinda ya isheni ni patuuu, Kai amma dai 

Amadun ne gantalalle wllh, me yasa xai hada baiwar Allah da bata san komai ba da wannan katon mutumi, wato 

Amadu ya raina mugun halin d’an nan nasa koh? Bai san abun ya wuce misali ba, ya wuce hankali ya dauka ba ko, 

Wllh shuree yake ko wa?? ba shi da xuciya me kyau ina fada kuna ganin kamar wasa nake, Baka ga ko gaisheni bai 

yi ba da ya shigo yana jiran ni in gaishe sa d’an banxa, ni dai ba ruwana don na haifi ubanka ba yana nufin ina da 

wani alaka ko dangantaka da kai bane, kayi ta kanka inyi ta kai na, makauniya kuma sai Allah ya saka mata tunda 

bata cuce ka ba….” Sudais dai sai hararan Shuraim da yyi kamar bai san suna yi ba a parlon yake, wayarsa kawai 

yake dannawa, kaka ta kamo hannun Heedayah ta xaunar da ita saman kujera tace “Sannu da xuwa Deedaya, ai da 

kyau tunda ba a titi ya gantalar da ke ba yyi wucewarsa ya ja ma d’a na fitina, haka nan muke fama da shi da mugun 

halinsa, mu ma ba kyale mu yyi ba, Bai san ba sonsa Allah ya fi yi da ya bar sa da idanuwansa ba ke kuma ya barki 

bbu idanuwa, shi fa Allah ba ruwansa gobe Shuree na iya tashi ya gansa a duniyar makafi to sai yyi yaya??” Tsaki 

Sudais ya ja ya fice daga parlon, Shuraim ya bi sa da wani kallo ta gefen ido, Kaka ta bude fridge ta fiddo malt ta 

bude mata tace “Wnn yaron kirki Junaidu ya xo jiya ya kawo min su da yawa, to bai fiye min wasu ba Allah na tuba, 

bbu abinda fa na hada da shi, kawai dai babarsa na auren d’a na ne, amma ko shekaranjiya sai da ya xo nan gaisheni 

muka yi ta hira gwanin ban sha’awa, to wasu ma idan suka xo sai dai su dinga tunanin ynda xa su cuceka kafin su 

wuce…. To ni dai bbu ruwana” A hannun Heedayah Kaka ta saka malt din, Heedayah ta fara sha a hankali tana 

lumshe ido, Kaka ta xauna tace “Toh madallah, yau dai na gama aikin da wuri, na gode ma Allah” Shuraim ya kashe 

wayarsa calmly yace “Ina yini Kaka?” Tace “Lafiya lau wllh, ai tun safe sae ynxu na gama kimtsa ko ina, baka da 

lafiya ne na ganka duk wani iri yau?” Yace “Lafiya ta lau” tace “Atoh naga duk ranka a bace ne ai, ko kai ma in 

kawo maka mantinan ne?” Ya girgixa kai kawai, tace “Toh in xubo maka abinci, shinkafa ce dai da miya” nan ma ya 

girgixa mata kai, tace “Toh ban da abinka meye na bacin rai kuma Mai gida, da shi Amadun yace ka kawota nan sai 

kace masa gaskiya kai kana da wajen xuwa, ae ba ajiye ka yyi ba, ban da neman magana irin tasa kai xai sa kayi ma 

yar makauniyar direba, shi da ya jajubo ta ba sai ya kawota da kansa ba, ni ba ruwana bana son rashin gaskiya, abu 

dai ba ayi tsakani da Allah, ae baxa ka rasa uxurin gabanka ba kai ma” Mikewa Shuraim yyi ya dau bottle water 

daya a fridge yace “Xan shiga in gaida su Umma” Kaka tace “Toh sai ka dawo, sai dai yau ko yar kazan nan ba a 

kawo min ba Mai gidan, ko da yake ina xaka kawo min kaza an hada ka da yarinya ba dangin iya balle na baba….” 

Fita yyi parlon, kaka ta tabe baki ta mike ta dau tsumman ta ci gaba da goge gogen da tace ta gama, Heedayah na 

gama shan malt din ta jefar da can din nan parlor, kaka ta leko daga d’an kitchen dinta tana kallonta tace “Ehh lallai, 

to sauka ki dauke ki fita da shi bola, ae ni ba baiwar Amadu bace balle ke” Heedayah ta sauka da sauri ta durkusa 

tana laluba Inda xata ji can din, kaka tace “Laluba gefen ki maxa ki dauke ki fitar min da shi ni ba yar bola bace, kaji 

min yarinya in mata inuwa tayi min rana, duk gidan nn bbu wanda na bai wa mantinan nan sae ke, shine xaki 

walakanta min parlor” Heedayah ta samu ta dauke can din ta mike duk a tsorace, a hankali tace “To bana gani” kaka 

tace “Hagun ki xa ki bi ki fita, ni xa kiyi ma karya kice ba kya gani” dai dai nan Sudais ya shigo parlon, kaka tace 

“Kaji wai xata je ta yarda gwangwani ta ja min salalan siya wajen Amadu Sudess….” Tsayawa Heedayah tayi tana 

kalle kallen kamar mara gaskiya, Sudais ya kama hannunta suka fice daga parlon, kaka tace “A’a, yau ga ikon Allah, 

ya xan ce a kawo min yarinya takanas kuma ka xo ka dauketa Sudess” tuni Sudais ya kulle mata kofarta, ya wuce 

xuwa dakinsa yana rike da hannun Heedayah, Heedayah ta ta6a hannunsa tace “Waye kai?” Ya kai bakinsa kunnenta 

yace “Heedayah ne ni” tana jin muryar sa ta washe hakora tace “Baka bani sauran chocolate dina ba” yace “Shi xan 

je in baki yanxu” ta kankame hannunsa tace “Mu tafi gida wajen Mami da kai sai mu bar wnn mugun a nan plss” 

dariya yyi ya wara ido yace “Da gaske” ta gyada masa kai tace “Ehh I don’t like him, shi mugu ne….” Bude kofar 

bedroom dinsa Sudais yyi yace “To gaya min me da me yyi maki” Shuraim dake kwance saman gadonsa ya juya yana kallonsu, tace “Komai ma yana min ai, first ya fara buge min hannu don yaga bana gani, kuma Abba yace ya 

min karatu ya ki yyi min…” ta girgixa kai tace “Noo… I just don’t like him, and I will never like him….” Dariya 

Sudais ke yi yana kallon Shuraim da ya mike xaune fuskarsa a daure yana kallonta, Sudais ya dagata ya xaunar 

gefen gado yace “Toh kin gaya ma Abba abinda yake maki” tace “Yau duk xan gaya masa ae, har da duka na da 

yyi….” Ta wara ido tace “Ae kai ma ka iya suratul jinnnn Koh?” Ya gyada kai yace “Sosai ma” tace “Toh mu tafi 

gida da kai sai mu bar sa wajen matan nan me yi ma mutane fada” Sudais yyi dariya yace “Sunanta kaka” tace “To 

mu bar sa wajen kaka shi, bana son ya bi mu” Gaba daya Shuraim ya kasa cewa komai, Sudais na kallon manyan 

idanuwanta yace “Toh xa mu bar sa a nan mu tafi gidan tare kin ji cutie” ta washe hakoranta tace “Toh ina chocolate 

dina” mikewa yyi yace “Bari in dauko maki” Sai a sannan Shuraim ya fixgota da karfi yace “Uban waye mugu?” 

Sosai ta tsorata jin muryar sa, ta fasa ihu tana son kwace kanta, Sudais ya dawo da sauri yace “Don’t you dare touch 

her, don’t try that” yana fadin haka ya dauke Heedayah da jikinta ke rawa a wajen, ta kankamesa cikin rawar murya 

tace “Take me away plss” ficewa Sudais yyi daga dakin nasa ya kulle kofar trying hard not to laugh. Mumy ce xaune 

parlon Hajiya Sadiya tayi tagumi, Hajiya Sadiya tace “Anya kina ganin baxa a xarge ki ba Maryam, hakan yyi wuri 

ai wllh, ki bari kawai mu lallaba ayi duk abinda xa ayi a samu ki koma dakin ki, kinga idan kina gidan ko ma me ya 

faru bbu wanda xai xarge ki bbu wanda xai kawo ki a rai, amma yanxu fa?? ai daure kanki kawai xa kiyi, barin mijin 

ki barrister, kishiyar ki barrister” Mumy tace “Nima wllh tunanin da nake kenan, gaskiya kika fada, bari a share wnn 

batun ynxu kawai….” Hajiya Sadiya tace “Yauwa, yanxu kina komawa nunawa xa kiyi kin fi kowa sonta ma a gidan, 

kiyi iya bakin kokarinki ki danne komai a kasar xuciya ki, ita kanta kishiyar taki ki d’an fara sake mata kuna gaisawa 

yanda bbu wanda xai samu damar xargan ki nan gaba, karatu kuma kiyi ta tausasa Shuraim yyi mata, yaranki duk ki 

sa su dinga shiga gun kishiyar taki su dinga jan makauniyar a jiki, wllh duk kika bi shawarata komai xai xo mana da 

sauki Maryam….” Mumy tace “Kai da bani da ke da nayi Kuka Sadiya, nagode aminiyar kwarai Allah ya bar 

xumunci, amma ita wnn tsohuwar kuma ya kike ganin xan yi da ita in huce takaicin annamimancin da ta min” 

Dariya Hajiya Sadiya tayi tace “Ke wa ke sa wnn ta6a66iyar a lissafi, ba fa isasshen kwakkwaro gareta ba, ynxu dai 

muyi concentrating a abinda yake gabanmu ki ajiye batun wnn tsohuwar” Mumy tace “Toh shkkn, ynxu dai bari inje 

gida wajen Salima in ji ita kuma ya ake ciki, daxu na kirata tace da yamma xata koma gida, bari in je in dawo” da 

haka suka yi sallama Mumy ta bar gidan Hajiya Sadiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page