Uncategorized

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 6 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 6 BY Fateeyzah mbs_✍️*

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Murmushi tayi sannan ta fara da cewa “A lokacin da Daddy yazo min da mganar zai k’ara aure,ba k’aramin bori na masa ba, ke har ta kai ya dena kwana a gidan nan saboda ni, saboda rashin mutunci ba wanda ban masa ba, yara kuma abu k’ad’an zasu yi in hantaresu, amma duk abunnan danake yi bai hanasa ci gaba da shirye shiryensa ba, ni kuma kullun da sabon tijarar da zan masa, ranar kawai naji ina marmarin hawa Facebook, don rabon da inyi wani chat tun ran da Daddy ya sanarmin da maganar k’arin aurensa, ina shiga naci karo da post din *Fateema Zahra Muhammad sani(Fateeyzah mbs)* admin ta group din  *A Turakar mijina* da kuma *Sirrin Turakar miji*, wallahi post d’in kamar don ni tayi sa, wanda take magana akan haukan da uwargida take yi in maigida yace zai k’ara aure, sannan da shawarwari da ta bada, wallahi ina

karantawa naji na muzanta, jikina yayi sanyi, hakan yasa nabi ta private, sai dai bata min reply ba, hatta friend request d’in dana tura mata  bata yi accepting ba, nan hankalina ya kuma tashi, na kuma bin ta post d’inta na mata magana, nan ma bata min reply ba, sai dai sauran members da suka min reply da inyi hak’uri zata amsa ni, mutane ne ke mata yawa, sai da nayi sati d’aya da mata magana sannan tayi attending d’ina, inda na mata introducing kaina tare da karanto mata matsalolina, wallahi cikin 20minutes ta bani shawarwarin da har yanxu akansa nake, wato inyi hak’uri, in danne kishina, in kuma mik’a lamurana ga ubangiji, nan ta ce in duba group d’in in bincika duka posts d’inta zanga sauran bayani, da shawarwarinta da lectures d’inta nake amfani, shiyasa kullun nake addu’a Alherin Allah ya kai mata a duk inda take”.nan ta tsagaita tana mai binsu da ido

 Ganin ba wanda yayi magana yasa ta ci gaba da cewa ” a ranar na tura ma Daddy text message na bada hak’uri, sannan da ya dawo ma na bisa d’aki  na zuk’unna har k’asa na kuma basa hak’uri, wannan duk shawarar fateeyzah ne, wallahi a ranar farin cikin gidan nan ya dawo haka muka wuni muka kwana cikin walwala, hidimar bikin gaba d’aya ya dawo da ita hannuna, sannan ganin na kwantar da hankalina yasa ya siyan mata wanu gidan ya fasa ajiyeta a d’ayan part d’in gidannan, haka ya canza mana furnitures mu da yara, sannan ya bani mak’udan kud’i yace inje in had’o ma amaryarsa lefe, nan kishina ya motsa, na tafi da niyyar siyo mata kaya masu arha, marasa quality, sai dai anan na tuna da shawarar fateeyzah da tace in tsayar da gaskiya ta, haka ko na daure na zab’ar mata kaya masu kyau da tsada, sannan akwati na siyan mata set 2,  komai dozen na saka mata, daga Atampa, lace, shadda, materials, abayoyi, takalma, jakunkuna, hatta sark’ok’i, sannan na saka mata gwal set biyu, guda  full set, guda half set, sai kayan shafa, da inners masu tsada, haka nayo uban kaya na dawo dasu gida, ashe duk siyayyar da nake Daddy ya saka wani yana watching d’ina, na dawo  bai fi da awa d’aya ba, sai gashi shima ya dawo da uban kaya , dana bud’e babu abunda ya banbanta da wanda na siyan ma amarya, sai dai banbancin colour, nan yake cemin nawa laifen ne, a lokacin na kumq godiya ga Allah, da na mata mugunta da shikenan nima shi zai kwaso mini, in tak’aita muku a wannan bikin ba k’aramun alheri na samu ba, don a lokacinne ya siyan mini babbar mota, duk mai yajo haka?, saboda na kwantar da kai, ko da aka kawo amarya bai canza min ba,  sai ma dad’a kyautatamin da yake yi, amarya tsakanina da ita kuma sai gaisuwa da ganin girman juna, inkin ga tazo sai in wani abune ya faru kamar rashin lafiya, haka nima, ko kuma mun had’u a sha’anin dangin miji, sanna kuma in ba gidanki miji yake ba, baki isa ki kirasa ba, sai dai inshi ya kiraki, wannan kuma duk dokar Daddy ne, shiya sa wallahi ni wani zubin nake mantawa ma ina da kishiya, don sai inyi watanni ma ban ganta ba, don haka Hajiya Turai shawarata gareki itace kiyi hak’uri, kinga dai shi auren nan ibadane, kuma Allah shi ya umurcesu da su auri har hud’u in suna da hali, kinga niyyar dakatawa kamar isgiline “.

“Hajiya Luba kenan, gaskiya a shawarki babu wacce zan iya d’auka balle har inbi, ke in kin had’u da kishiya ta kwarai to ki sani in ba dole bane in had’u da ita, a irin ‘yan matan zamanin nan da suke kokarin raba mata da mijinta tun kafin su shigo, burinsu kawai u fitar data gidan, sannan kuma ke Allah ya had’aki da miji mai nagarta, to ni ba hakan bane, don Alhajina ina ni d’aya ma ya aka k’are balle ya k’aro wata, kuma ko a cikin ‘ya’ya ya iya nuna banbanci balle matansa,  don haka ku barni kawai in d’auki mataki” cewar hajiya Turai cikin b’acin rai.

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE