UKU BALA'I COMPLETE

UKU BALA’I CHAPTER 5

UKU BALA’I CHAPTER 5

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tun ranar da Dr.Aqeel ya dauki kafarsa ya bar kasa najeriya shikenan natsuwar zuciya da ruhi suka gagari duniyar Mariya sosai ta shiga tashin hankali mara musaltuwa bata taba zaton zata yi k’ewarsa har haka ba bata zaton zuciyarta da gangar jikinta za su kasa sukuni har haka ba tayi kuka, kukan wanda take zaton zai rage mata raɗaɗi zuciya amma hakan bai yuwuwa ba sosai ta raya darurruka masu yawa cikin yanayi na damuwa da takomshin saƙar zuciya.

Sosai takoma shiru-shiru magana ta za me mata wani aiki kato a duniyarta ba ta san ya kayi ta batawa ran mutumin da ya jikanta a rayuwa ba ba ta san mai yasa tayi gangancin  haka ba bata san mai yasa a ranar da za su rabu ta barshi sa tukwuicin bacin rai ta sani da fushin ta ya bar kasan nan ta sani dole ya shiga cikin yanayi na bacin rai duk a dalilin ta ina zata gan shi ta bashi hakuri a ina zata ganshi ko ba a zahiri ta wanke laifin da ta yi masa ta sani sosai yayi mata nisa nisan da ba ta da damar da zata je in da yake har karshen rayuwarta in bashi ne ya dawo ba ya tadda ita tunanin ya ta’allaka ne a yarda za t rayu dashi a zuciyarta wanda ba ta san adadin lokacin da zai dauka kafun ya dawo ba sosai take hango gangancin da tayi na bata damar da ta samu.+

Haka ta cigaba da rayuwa cikin wannan yanayi da tunanin Dr.Karami lokaci mai tsayi cikin duniyarta haka ta cigaba da zuwa makaranta tana karatu da tunanin Dr.Karami a ranta da ruhi dama duniyarta baki daya.

Mutum daya ce take samun damar da take zama tana zantawa da ita har ta rage mata damuwar dake addabar zuciyarta sosai Baseera ta taka muhimmiyar rawa a duniyar Mariya sosai take nuna mata rashin dacewa ga halin da ta je fa kanta duk yarda zatayi don ganin ta rage mata tunanin abin dake  dawainiya da Mariya tana yi sosai take hanata zaman shiru kulli-yau min in dai basu da lesson to tabbas zaka same su zaune waje guda suna bitar karatun su domin Baseera ta hakikance haka ne kawai zai rage abubuwa da yawa a duniyar Mariya da suka addabe ta.

A bangare guda kuma Dr.Aqeel da Huzaif suma sosai suke saka ta cikin halin rashin kwanciyar hankali domin ta hakikance a ta dalilinsu komai ya faru da ita tsakaninta da Dr.Karami sosai take jin tashin hankali a duk lokacin da suka kwaso jiki suka zo gareta bata san abin da suke nufi da ita ba sosai take ganin suna takura mata domin kuwa laifin komai da komai da ya faru akan su ta daura su ne silar faruwar komai.

Ko dai dai in tayi duba ta wani fannin duk wanda ya zo a tsakaninsu tana kula su hakan kuma na kara tuna mata da Dr.Karami tana ba su lokaci sosai da sosai domin Dr.Aqeel ba abin yadawa bane shima ya taka muhimmiyar rawa a duniyar rayuwarta sosai da sosai ba za ta yi masa halin dan’adam ba mai mai da alheri zuwa akasin sa.

Haka shima Huzaif duk da tabon da yayi mata a zuciya hakan bai sa ta watsar dashi tun da ya nuna nadamarsa akan abin da yayi amma kuma ba hakan bane ya sanya ta tsayawa dashi har ta bashi lokacin ta illa soyayya da yake nunawa kaninta Mu’azzam soyayya ce mai girma a tsakaninsu gami da shakuwa sosai da sosai yake bashi kulawa yake tattalin sa kamar dan’uwansa na jini hakan ba karamar rawa ya taka ba har Huzaif ya samu matsayi a filin zuciyarta.

ba ta san wata irin ƙaddara bace take yawo da ita a duniyarta a duk lokacin da ta tuno abubuwa da suke ta faruwa da ita a filin rayuwarta sosai take hango tashin hankali mai girma nan gaba duk ranar da Dr.Karami ya duro kasar nan.

*****

“Nikam ina ganin Bariki ‘ya duk idanuwanta sun gama buɗewa tana kallon mutane ɗai-ɗai kamar tsararrakin ta ni ban san wani tsohon makiri bane da wannan danyen aiki in ban da son sani da kalan-dangi  da neman mai da yariya karamar yar duniya me nene haka kullum yarinya kenan da tsukanken wando da guntun hijabi tana zarya a hanya kowa ni kare da doki suna kare mata kallo”.

Goggo Marka ce take fadin haka  tana tafa hannu a daidai lokacin da Mariya ta dawo daga makaranta jikinta sanye da Uniform riga da wando sai hijabi wanda iyakarsa kirjinta.

STORY CONTINUES BELOW

Tun da Mariya tafara daukar kafarta zuwa makaranta tun daga wannan rana Goggo Marka take debe mata albarka akan cewa iskanci kawai da duniyanci ya sanya  aka saka ta makarantar yahudawa yarinya sai kara girma take yi tana buɗewa kowa ni namiji sai kallon ta yake yana haɗiyar yawu.

Ba karamin tashin hankali Mariya tashiga ba a ranar da taji mugun nufin da Goggo Marka ke jfanta dashi tayi kuka kuka mai amsa sunansa kuka Umma ita kanta tayi bakin ciki mai girma sosai zuciyarta tashiga tashin hankali jin mugun nufin da ake jefar ‘yarta da shi a ranar ta so ta hana Mariya zuwa makarantar amma zuciyarta ta hanata tana mai gargaɗin ta akan sabawa alkawari da kuma rashin baiwa Dr.karami muhimmancin abin da yayi musu na alheri sosai tayi duba akan ilmi tasan ilmi na da matukar muhimmanci a duniyar rayuwar ‘yarta sosai karatun da tayi zai taimaka mata a fannoni masu yawa a wannan zamanin da ake ba wai ita kadai Mariya ba har da su iyayenta da al’umma a duk ranar da ta zama wani abu a filin duniyar nan a dalilin karatu tasan za suyi alfahari da ita sosai da sosai.

Ta sani dole ne ta jajirce  sannan ta kau da kunnuwanta  ga sauraron duk wani mugun furuci da za a fada mata ita da ‘yarta dole ta rarrashi zuciyarta dole ne ta cigaba da yi ma ‘yarta addu’a sannan ta kara mata karfin gwuiwa ta nuna mata amfanin karatu a duniyarta da su iyayenta dama Al’umma gabadaya ita dai fatanta a kullum Mariya ta tsare rayuwarta da martaba gami da darajarta ta dage wajan karatu sosai da sosai duk wuyarsa da wahalarsa zata ga amfaninsa nan gaba sosai da sosai domin a yarda suke yanzu karatunta zai matukar taimaka masu nan gaba sannan ta kara tunatar da ita cewa ta dube su da rayuwar da suke yi ta tabbata in da sunyi karatu a zamaninsu ba a za su fuskanci kalubalin rayuwa har haka ba ko ma za su fuska to ba zai yi tsauri haka sosai da sosai ba.

Huɗubar Umma sosai ya samu waje a filin zuciyar Mariya ta ajje waje na musamman.

Sosai take jin tausayin iyayenta na kara samun fili mai girma a zuciyarta da ruhinta sosai take hango irin rayuwar da suke gudanarwa tana hasashe kafun zuwanta duniyar nan ta sani sun fuskanci KALUBALE sosai da sosai in tayi duba da yarda auren iyayen nata ya kasance a yarda take samun labari sosai suka shiga tashin hankali kafun tabbatar auren iko na Allah ne kawai yayi aiki a tsakanin iyayensu har suka bar su suka auri junansu.

Domin sosai ake fuskarta matsala tsakanin Fulani iyayen Habeeba da manoma iyayen Bello sosai rashin jituwa ke tsakaninsu amma sai Allah ya kulla soyayya mai girma tsakanin ‘ya’yansu wanda haka sam bai yi musu dadi ba su iyayen musamman ta bangaren iyayen Habeeba domin AKAN SO da take yi wa Bello ta zabi kin bin iyayenta domin da rigima tayi rigima abu yaki ci yaki cinyewa sosai suka fara kokarin haɗe kayan su domin canza mazauni nan Habeeba tayi tsalle ta dire ta nuna ita ina ba za ta bi su ba  komai za suyi mata kuwa tana tare da Bello  gani take in aka raba ta dashi to tabbas zata iya rasa rayuwarta sosai iyayenta sukayi fushi da ita har ya kai ba sa yi mata magana ganin da sukayi da gaske take sannan da ban baki da mutane suke ba su hakan ya sanya su barwa Habeeba auranta akan kuma komai yasa me ta kar ta sake ta tako kafa in da suke domin kuwa duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka a ranar da aka daura auren Habeeba da Bello a ranar iyayenta suka bar garin Gwada gabadaya zuciyoyin su cike da abubuwa marasa dadi su yi KUDIRI  a ran su ba za su sake takowa zuwa wannan garin ba har gaban abada.

A lokacin da akayi auren Bello mahaifiyarsa bata raye mahaifinsa ne kawai yake duniya sai matarsa Marka wanda tun lokacin ita ce take rura wutar komai domin sam bata kaunar auren ta tsani Bello da uwarsa domin a tunaninta shi ne ɗa namiji a gidan kuma shi ne magaji ita kuwa ‘yarta daya  Zainabu wanda suke kira da Abulle Abulle macece mai hakuri bata biyo halin mahaifiyarta ba domin sosai take bakin cikin duk abin da taga mahaifiyar ta ta nayi wa su Bello Abulle ta riga Bello Aure domin tun tana shekaru sha biyar aka auren da ita tun da tayi auren bata taba haihuwa ba har akayi bikin Bello lokacin da Bello shima ya tare a nan gidan su sun jima kafun ita ma Habeeba ta samu ciki wannan rashin samun ciki sai ya buɗe wa Goggo Marka katon filin tsula rashin mutunci ga Habeeba tana mai aibata ta wai juya ce bata haihuwa kila  ta gama yawon bin mazan ta acan rugarsu ta gama zubda kwayayen haihuwarta a layi wajan tallar su ta gado shine aka likawa Bello sosai take jin bakin ciki da takaici sosai ta so yin dana sanin auren Bello amma in ta tuna irin HALACCI da yayi mata ya nuna mata so da kauna ya tattale ta ya za me mata MIJIN MARAINIYA sai taji a ranta za ta iya zama dashi da ko wani irin hali ne ko da kuwa Goggo Marka za ta dinga yankar naman jikinta ta miya dashi.

STORY CONTINUES BELOW

Ba karamin tashin hankali Habeeba ta fuskanta ba a tsayin shekaru biyu da tayi a gidan auranta sosai duk hakurin ta da kai zuciya nesa hakan bai hana ta shiga matsananciyar damawu ba duk da bata gayawa Bello abin da ke faruwa tun ba ya ganewa har ya zo ya na fuskanta ya yi bakinciki ya nuna bacin ransa amma mahaifinsa ya dinga ba shi hakuri akan kar ya damu wata rana sai labari.

A na cikin wannn tataburzar ciki ya bayyana jikin Abulle Innalillahi wa inna ilaihir raji’una.

Ina wuta Goggo Marka ta saka Habeeba nan fa ta sake bude sabon shafin  gori da aibatawa  bakaken maganun kuwa ba a magana a lokacin Habeeba ta ga tashin hankalin da bata yi tsammani ba domin kuwa Goggo Marka zuwa tayi da kanta tun cikin na wata bakwai ta danko Abulle ta kawo gida bayan an sha dirama in da Abulle tace ba in da zata je a bar ta gidan mijinta ita kuwa ta dire tace bata san zance ba haihuwar farko ce dole sai taje gida GOYON CIKI ban dan ta so  ba haka ta kwaso jiki ta zo gida bayan mijinta ya amince mata ganin da yayi Goggo Marka na shirin birkita musu rayuwar auren su.

Tun da Abulle ta dawo gida fa nan Aiki ya cewa Habeeba Salamu alaikum domin komai na Abulle ita ke yin sa ba abin da aka dauke mata hakan bai dame ta ba domin Bello ya bata baki akan cewa tayi kwana nawa ne Abulle zata koma gidan mijinta a haka har ta haihuwa inda ta samu ɗa namiji nan wata sabuwar duniyar habaici da cin mutunci ta buɗe akan Habeeba haka zata shiga daki tayi kukanta ta godewa Allah duk abin da ke faruwa Abulle na sa ne wani lokacin haka za ta faki idon Goggo Marka ta fada dakin Habeeba tai ta bata hakuri akan abin da ke faruwa domin har ga Allah tana jin bakin ciki da takaicin abin da ake yiwa Habeeba sai dai bata da damar hanawa in tayi magana haka Goggo Marka zata ta surfa mata zagi wai bata kishin kanta sannan ai Habeeba bata da amfanin komai a gidan tun da ba haihuwa take ba sai dai taci ta kwanta tayi kashi.

Sai da Abulle tayi wata biyu cur! san nan ta koma gidan mijin ta a dan tsakanin Habeeba ta samu sa’idar aiki.

Shekarun Abulle ashirin da Haihuwa ta sake samun ciki a lokacin ita ma Habeeba Allah ya taimake ta  ya amsa du’a’in ta ya bata na ta rabon.

Yaa Allah!

Ku zo ku ga murna wajan Habeeba da Bello da Mahaifin Bello wanda a lokacin girma ya kama shi sosai da sosai.

Ita kuwa Goggo Marka ji tayi kamar ta hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki da takaici haka tana kallo Habeeba tayi rainon cikin ta da taimakon mijinta har ta sauka lafiya ta samu ‘ya mace hakan yayi wa Goggo Marka dadi sosai domin haihuwar mace da akayi ta san ko ba komai dai ai an rage mugun abu in da namiji aka haifa ai da ta shiga uku.

Satin su daya ita ma Abulle ta haihu ita ma dai ‘ya mace ce.

Ranar su aka sanyawa yarinya Mariya ita kuma Abulle aka saka ma ‘yar ta ta Hafsatu.

Tun daga wannan lokacin zama dai ya ki dadi a tsakin Goggo Marka da Habeeba  har zuwa lokacin da su Mariya suka isa Yaye a lokacin Goggo Marka ta dauko Hafsatu da sunan yaye ta tun daga lokacin ta zama ‘yar gidan ta sosai ta sargarta ta da sunan wai gata ba ta jin kunyar uban kowa tun tana karamar ta ta iya zagi da dukan mutane ba yarda Abulle bata yi ba domin ansar ‘yarta ganin irin tarbiyar da ake yi mata Goggo Marka ta hau ta dire akan ba wanda ya isa ya rabata da Hafsatu wannan shi ne silar sangartar Hafsatu sai ta ga dama take zuwa wajan iyayenta ko taje to da rigima suke rabuwa da uwarta ta dawo tana kuka haka Goggo Marka zata zari mayafi ta je har gidan Abulle tayi mata rashin mutunci ta dawo gida.

Shekarun Mariya Hudu Allah yayiwa  kakanta Mahaifin Bello rasuwa sakamakon gobara da ta kama gidan duk kan su ba sa nan shi kuma jikinsa yayi nauyi sosai da sosai ko tashi bai ya iyayi haka yana kallo wuta ta kama shi ba shi da halin taimakon kan sa.

A ranar sun ga tashin hankali a gidan domin komai ya kone ba abin mamora gabadaya  wannan shine silar fadawarsu kangin rayuwa su ka fuskanci kunci sosai ya kasance abin da za su samu su ci ma sai Bello ya fita yayi buga-buga domin dama sana’ar tambobi yake yi to duk gobara ta lamushe jarin d kuma sauran dambobin da yake kiwo cikin gida.

STORY CONTINUES BELOW

Wannan kenan!

********

Sanye take da bakar jallabiya mai dogon hannu wanda ta dan kamata jikinta kadan sai hijabi mai kalar pink sai  fulawowi masu kaloli da suka karawa hijabin kyau sosai tayi wa kayan kyau ba wai su sukayi mata kyau ba ba wata kwalliya tayi ba a fuska ba  domin Mariya sam ba irin matan nan ba ne masu son kwalliya in kuwa ka ganta da kwalliya to tabbata Baseera ta zo gidan ko kuma ita taje gidan su.

Bayan ta gama shirin ta dubi Umma dake sauyawa Mu’azzam wando.

“Umma ni na tafi sai na dawo”.

Ta fadi tana mai daukar jakar Islamiyyarta dake rataye.

“Allah ya kiyaye hanya a kula sosai Mariya Allah ya bada ilmi mai amfani a dahe da karatu kin ji karatu yana bukatar jajircewa da mai da hankali akan abin da ake koya wa”.

Murmushi Mariya tayi tana mai gyaɗa kai a kullu-yau min in zata tafi makaranta maganar Umma kenan na nuna son ta kula da kanta kuma ta mai da hankali akan abin da taje koya har ta hadda ce maganar ta ta wanda ta samu fili a zuciyarta ta ajje ta kuma tayi Alkawari in Allah ya yarda za ta yi abin da Umma ke so ta ga ta yi.

Da wannan tunanin ta fice daga dakin bayan ta jawa Mu’azzam hanci da yake ta faman kallon ta dariya ya saki ita ma mai da masa tayi sannan ta fito daga cikin dakin.

Ta na cikin saka takalmin ta ta tsinkayi muryar Goggo Marka.

“ina ganin lalata nikam wai sai a zage ai ta nuna wa mutane Allah a baki zuciya kuwa ta fir’auna ce yanzu in ban da kuturun kinibibi Hafsi ji be ta don Allah ta zabga doguwar riga har da zabgegen hijabi an rakito jaka wai za a karatun addini bayan an gama tambaɗewa a waccan boko jahanna ma din wai mu za ayi wa BIRI BOKO”.

Tsaki Hafsi tayi daga in da take zaune ta mimmike kaf kamar sabuwar ‘yar kaciya sai faman kai noma bakin ta take yi.

“Uhmm yo Goggo wani dare jemage bai gani ba ai sai na mutuwarsa ai mu tuni muka gane barno ba gabas take ba balle a juyar mana da alkibla kawai kallon mutum muke”.

Ta karashe tana sake yanko katuwar lomar taliya da taji yaji da mai har canza kala take yi kallo daya zakayi wa taliyar kasan an kashe mata kuzarin ta da barkono.

In da sabo Mariya ta saba da irin wadannan habaice-habaicen don haka ko ta kan su ba ta bi ba ta na saka takalminta ta kama hanyar ficewa daga cikin gidan.

“Hehehehe wai mu za a nuna wa bariki”.

Fadin Hafsi tana daukar kofin ruwa tana kai wa bakin ta gabadaya ta gama hada gumi kamar mai jego a lokacin zafi ta sha kunun kanwa.

Zuciyarta sosai ta kuntata jin abin da Hafsi ta fadi akan ta a duniyar nan ba abin da ta tsana irin ace da ita ‘YAR DUNIYA ko ‘YAR BARIKI sosai take jin zuciyarta na kuna da zafi…

“Mariya!”.

Kamar daga sama taji amon muryar ko ba a fadi mata ba ta gane ko waye in hadda ma ake akan muryar mutum ita kam! ta hadda ce.

Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba tana jin takusan har ya iso in da take tsaye ya zo ta gabanta ya tsaya hannayensa harɗe a kirjinsa sosai yake kallon ta da duk idanuwansa sosai ya karanci akwai abin da yake faruwa da ita mara dadi daga cikin gidan kafun fitowarta ga idanuwanta   sun kaɗa sun yi jajir numfashi ya ja mai girma kafun ya kau da idanunsa yana jin wani iri game da ita a zuciyarsa wanda har zuwa wannan lokacin ya kasa yarda da hakan sai fafatawa da zuciyar tasa yake yi akan kalubalantar ta akan abin da take sanar dashi.

STORY CONTINUES BELOW

“Me ya same ki Mariya?”.

Ya fadi idanuwansa sosai a fuskarta da kallon tuhuma.

Kasa ta karayi da kai tana mai girgizawa alamun babu komai a zuciyarta kuwa ba abin da ke kona mata ita sai kalaman Hafsi sosai ta tsani taji an jona mata rayuwar duniyarta da bariki ta tsani haka amma ita kuwa Hafsi ta mai da mata rayuwa kamar wacce take zaman kanta ko wacce aka ce je ki kya gani in dai duniya ce.

“haba mana Mariya dake fa nake”.

Ba ta son tsayawa bata son bata lokacin ta  tana bukatar ta isa makaranta da wuri.

“Ba komai kawai dai yau na tashi ne bana jin dadin jiki na”.

Ware idanu yayi yana dubanta cikin yanayi na tausayawa kafun ya ja numfashi.

“Amma kuma a haka zaki tafi makaranta kin san bakya jin dadi ya kamata ace kin sha magani kin kwanta”.

maganar ta fara gundurarta don haka ta dago idanuwanta ta dube shi sosai kafun ta kau da idanunta ba ta so suna hada idanu da Huzaif sosai take jin wani iri a zuciyarta da duk kan gangar jikinta sosai take hango wasu abubuwa masu girma cikin ƙwayar idanuwansa wanda ta rasa da me zata danganta su.

“ba wai bani da lafiya bane, kawai dai yanayin garin ne yau gabadaya naji shi ba dadi”.

Ta karashe tana mai daga kafafuwan tana wuce wa.

“Sai anjima”.

Ta sake fadi bayan ta gota shi tana cikin tafiyar cikin yanayi na rashin armashi ta tsinkayo muryar Hafsi na daka mata kira kiran da taji shi har tsakar kanta gabanta taji yayi wani irin bugawa kamar zuciyarta zata faso kirji ta fito.

Da sassarafa ta iso gareta fuskarta ba yabo ba fallasa ta mika mata hannu.

“Bani abin da kika dauka inji Umma”.

Duban rashin fahimta Mariya ta shiga yi mata mamaki ya cika mata zuciya akan abin da taji tace da ita to mai ta dauka mai Umma zata aiko Hafsi ta amsa a wajanta mai yasa tun kafun ta fito ba tayi mata magana ba sai bayan ta fito ta ya ya tasan tana tsaye kofar gida bata wuce ba har zuwa wannan lokacin?.

Ware idanunta tayi sosai akan Hafsi da ta mata kerere akai sai faman yatsine baki take yi kamar ta ga wani abin kyankyami a hankali ta shiga motsa bakin ta cikin rashin abin cewa.

“Ban gane ba”.

Ta fadi bakin ta na rawa sannan tana juyar da kallonta zuwa Huzaif da ya harɗe hannunsa yana kallon su gabanta taji ya sake faduwa domin ta gama yanke hukuncin akwai kullin da Hafsi ke kokarin yi mata domin tsinka ta a gaban Huzaif ba yau bane ranar farko da ta fara zuwa in da take tare da Huzaif in ya zo wajanta tana neman shafa mata bakin fatti ta tabbata yau nasara take hangowa a idanun Hafsi…

“Kudin da kika dauka ta ce ki bani”.

‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un

Yaa hayyu ya kayyum’.

Ware idanu tayi sosai tana duban Hafsi da take jin kalaman ta kamar saukar aradu akan ta sosai ta hango tsabar kullin zarge a idanunwanta yarda take yawo da idanuwanta da motsa baki sai ka rantse da Allah gaskiya ne ga hannu data turo mata alamun ta ba ta kudin ji tayi kamar kasa ta tsage ta fada ciki don takaici da bakin ciki sosai taji a jikinta Huzaif na kallonta kallon da ba ta san wani yanayi ya ajje shi ba ta sani kallon wata iri yake yi mata ta sani yanzu haka a zuciyarsa ya yarda da maganar Hafsi da ta zo dashi kuma ta sani yanzu haka kallon tuhuma yake yi mata kuma wacce bata da GASKIYAR RAYUWA cikin duniyarta.

STORY CONTINUES BELOW

“Hafsi kudi fa ki kace ita Umma din ta ce ki biyo ni ki amshi kudi?”.

Mariya ta fadi muryarta na karyewa da wani irin yanayi mai girma da tashi a hankali acikinsa wata irin sarawa taji kanta nayi kamar zai rabe gida biyu a hankali ta kai hannunta ta dafe kan.

‘Yaa Allah’.

“Malama ni fa ‘yar aike ce ba wai ni nayi gaban kaina ba don haka ko ki bani ko kuma ki fada min abin da zan fada mata don cewa tayi in amso mata kudin ta in ba haka ba kar in sake in dawo domin sai ta bata min rai”.

‘A’uzubillahi minal shaiɗanin rajim’.

Mariya ta fadi can kasar zuciyarta da ruhi wata irin juw ta ji ta na daukarta tana kokarin dire ta da kasa da sauri ta dubi Hafsi izuwa lokacin idanunta sun tara kwalla sosai take kallon ta da yanayi na baki yi min adalci ba ba ki kyauta min ba.

Amma ita sai faman kau da fuska take yi tana kara tafke ta alamun ba wasa.

“Wai shin me ke faruwa ne?”.

Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Huzaif ya na fadin haka.

‘Yaa Allah’ .

Mariya ta sake fadi ita kadai take jin abin da take ji a zuciyarta sosai take cikin tashin hankali wanda bata taba zaton ƙaddara za ta dauko mata ta kawo mata ba kuma da ta tashi dauko mata sai ta jeho mata  Hafsi dauke da makirci ta zo ta dire mata a gaban Huzaif da yake mata kallon mutunci da mutuntawa.

“Kudi ta dauka shi ne aka ce in biyo ta in ansa shi ne fa ta tsaya tana min yawo da hankali bayan kuma ta san ita ce ta dauki kudin”.

Muryar Hafsi ta karaɗe kwanyar Mariya da kunnuwanta da karin bayanin da take yi wa Huzaif wanda ta tabbata hakan zai kara mata wani bakin fatti a zuciyarsa.

“Hafsi!!”.

Mariya ta fadi da sauti kafun ta dago jajjayan idanuwanta tana mata wani irin kallo na ban kiyi mani adalci ba.

“Mariya”.

Taji Muryar Huzaif wani irin yankewa taji gabanta yayi a hankali ta juyo da kallonta zuwa gareshi sosai ta hango kallo wanda ba tayi tsammanin shi za ta gani ba kallo ne na rauni da tausayawa ta hango cikin idanuwamsa sai faman gyaɗa kai yake yi alamun tausayawa.

“wuce ki tafi makarantar ki karki bata lokacin ki”.

Abin da taji ya fadi kenan da sauri ta ja jiki ta tafi zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi sosai taji abin da Hafsi tayi mata ya taba mata zuciya ba kadan ba amma abu daya ya sanyata tafiya shine ganin irin kallon da Huzaif yayi mata wanda ba tuhuma ko zarge a cikinsa amma duk da hakan zuciyarta ta yi matukar kaɗuwa da faruwar wannan lamarin a gaban sa da wannan tunanin ta bar layin nasu.

Huzaif da yake kallonta ganin ta kule ya juyo ya dubi Hafsi da tayi masa ƙyar da idanu tana kallonsa kamar wanda ta ga sabuwar halinta a duniyarta.

“anshi ki kai wa Umma din sannan ki ce mata ba Mariya ba ce ta dauki kudin domin an duba ba a gani ba a dai sake duba cikin gidan a in da aka ajje su”.

gudar duba ce ya zaro ya mikawa Hafsi a dan kuntace ta ansa ba haka ta so ba ta so ace Huzaif ya ci mutuncin Mariya sosai a gabanta hakan zai fi mata komai farin ciki kwaɓa tayi tana mai juya duba dayar a zuciyar ta ce

“raba mugu da makami ibada ne”.

Wani kallo ta jefawa Huzaif da wani irin yanayi kafun ta ja kafafuwanta ta koma cikin gida ranta fes ta sani dole zargi ya dalsu ko ya ya ne a zuciyarsa musamman irin kallon da ta ga yana yiwa Mariya da kuma irin muryar da yayi amfani da ita wajan yi mata magana.

A hankali ya isa motarsa ya buɗe ya shiga yana jin wani irin sarawa da kan sa ke yi kamar zai rabe guda biyu don tsananin kaɗuwa da yayi da abin da ya faru yanzu duk da dai zuciyarsa ba wai ta amshi lamarin bane da gaskiya amma ya ji rashin jin dadi a zuciyarsa.

Da wannan tunanin ya ja motarsa ya bar unguwar zuciyarsa fal da tunanin Mariya gami da damuwa da yanayin da ya ga ta shiga lokaci guda…Sosai da sosai zuciyar Mariya ta taɓu akan abin da Hafsi tayi mata na kulla sharri ba abin da ke kara sanya ta cikin bakin ciki in ta tuna kamar yarda ta tsinka ta a gaban Huzaif wanda sam ba ta so haka ba inda ta san abin da Hafsi za tayi mata kenan da bata tsaya ta saurare ta ba balle ta saka mata CIWON RAI.+

Haka ta je makaranta har ta gama zaman ta ba tare da ta fahimci abin da aka koyar da su ba da wannan yanayi aka ta so su ta yo gida gabanta na tsananta bugu ba ta san ya Umma zata karbe ta ba, ba ta san da wata irin fuska zata kalle ta ba in abin da Hafsi tayi mata ya tabbata tabbas zata shiga yanayi mai taba zuciya sosai da sosai tana tsoron fushin Umma gareta sosai take tsoron abin da zai je ya dawo ta sani wannan halin da Hafsi ta jona mata yana cikin abubuwan da Umma ta tsana tsana kuwa mai tsanani domin a kullu yau min in tana yi mata magana akan abin da ta tsana dauke-dauke na sahun farko musamman akan abin da ba naka ba kuma ba tare da sanin mai shi ka dauka ba.

Sosai zuciyarta tayi rauni wasu hawaye masu zafi da taba zuciya da ruhi ta ji suna sauka saman fuskarta sosai take jin zafin su a fatar fuskarta tana jin wani raɗaɗi mai ciwo na bin ko wani sashi na jikinta.

Hannayenta ta saka duk biyun ta na shafe fuskarta ba abin da take ai yana wa a zuciyarta sai.

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE