SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Two years Later!+

Acikin shekaru biyunnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda haihuwan Husnah, da kuma ƙarin girman da akayiwa Doctor Sadeeq a wajen aiki, Zahrah kuwa tazama lecturer acikin jami’ar da tayi karatu. Abubuwa dayawa sun faru acikin waƴannan shekarun.

Tsaye take agaban wani babban table tana haɗa wasu takardu dake gabanta, ajikinta sanye take da Abaya gown, maroon colour, wanda jikinsa yaji adon duwatsu da kuma flowers masu kyau,  yayinda  Abaya Vail ɗin dake yafe saman kanta, ya sauƙo har zuwa ƙirjinta,   babu wani kwalliya akan fuskarta, lipstick ne kawai sai kuma kwallin data sanya acikin ɗara ɗaran idanunta,   sosai taƙara kyau, cika da kuma wayewa, duk da cewa a ƴan shekaru biyun da suka wuce itaɗin ba baya bace wajen kyau, amma ayanzu komai nata yaƙara ninkuwa akan nada, yanzu tana amsa sunanta na cikakkiyar mace.  Kallonta ta maida kan agogon dake ɗaure akan tsintsiyar hanunta.   “4:30 pm” ta faɗa tana ɗan waro idanunta, da sauri tacigaba da tattare takardun, wasu tasa acikin jakarta, wasu kuwa ta sanyasu acikin wata drawer dake cikin office ɗin. Wayarta da jakarta ta ɗauka, kana ta nufi hanyar fita daga office ɗin.

STORY CONTINUES BELOW

Motarta ƙiran  Corolla LE  tashiga haɗe da bata wuta, ta fice acikin jami’an..    Bata wani jima sosaiba ta isa sabon gidansu wanda suka koma babu jimawa.

Da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, babu kowa afalon, sai TV Plasma ɗinsu dake ta aiki shikaɗai.  Direct wani ɗaki dake cikin falon ta nufa,  tsayawa tayi ajikin ƙofar ɗakin tana sakin murmushi, idanunta nakan wani yaro da shekarunsa na duniya bazasu wuce uku ba, ya nata  ƙiriniyansa  shi kaɗai, yaron kyakkyawane sosai, gashin kansa kuwa kamar na larabawa.  Cikin sanɗa tashiga takawa harta ƙarasa wajen dayake zaune, murya a hankali tace.

“Babyy!”    Jin muryar mahaifiyarsa acikin kunnuwansa yasashi juyowa da sauri, yana ganinta, ya tafi ya faɗa jikinta, yana dariya, itama dariyan tayi haɗe da manna masa kiss akan bakinsa, cike da kulawa haɗi da ƙaunarsa.  

“Aunty Sannu da dawowa” cewar Haulat me yi mata rainon yaron, idan zata aiki.

“Yauwa Haulat sannu da gida” Zahrah ta amsa mata fuska a sake.

Ɗaukan yaronnata tayi suka fice daga ɗakin, direct sama ta haura inda anan bedroom ɗinta yake.

Aje yaron nata tayi akan gado haɗe da durƙusawa agabansa, chocolate irin marar zaƙi sosai ɗinnan ta ciro ajakarta, kana ta ɓare ta basa a hanunsa, da murna Asad ya karɓi Chocolate ɗin,  matso da fuskarsa yayi daf da tata, kiss yayi mata akan kumatunta haɗe da cewa “Thank you Mummy!” yayi maganar ne cikin muryarsa dake ɗauke da tsananin yarinta.

Murmushi tayi kana taɗanja kumatunsa, miƙewa tayi ta wuce cikin bathroom acan ta cire kayan jikinta haɗe da sakarwa kanta shower. 

Koda ta fito sama sama ta shafa mai domin yanayin garin ana ɗan busa zafi,    wani dogon skin tight  baƙi ta sanya, wanda yayi matuƙar bayyana surar jikinta, bama kamar hips ɗinta da suka sake cika,  wata riga mai  net tasanya, irin fitted ɗinnan, sosai rigan tayi mata kyau,  ƙirjinta ne kawai yazamana a rufe, amma gaba ɗaya jikinta daga cikinta zuwa bayanta a bayyane suke, haka tsarin rigar yake.

Da Body Spray ɗinta me daɗin ƙamshi ta feshi jikinta,   dogon gashinta dayasha kitson kalaba, ta kama ta ɗaureshi da  ribbon,  direct gaban ɗan madaidaicin fridge ɗin dake ɗakin ta nufa,  buɗewa tayi ta ɗauko goran Yoghurt, buɗe murfin goran  tayi tasoma sha ahankali.

Shigowarsa ɗakin kenan, amma kuma kokaɗan bataji motsin buɗe ƙofarsa ba,   yana sanye da riga da wando na Suit navy blue colour masu kyaun gaske,  tabbas ya sauya daga kamanninsa nada, yaƙara haske da kyau, ga lallausan sajensa da ya kwanta luf akan fuskarsa,  yazama wani na musamman dashi, me tafiya da hankalin ƴan mata, yaƙara zama Handsome, dagani kai kasan kuɗi sun zauna masa..

Dariyan Asad da taji ne yasata waigowa ta kalli yaron, atunaninta ko ɓarna yakeyi mata, gani tayi idanunsa nakan ƙofar shigowa ɗakin, saboda haka itama ta maida idanunta wajen, da taga Asad ɗin na kallo.

Idanunsu ne suka sarƙe a cikin na juna, wani irin murmushine ya ƙwace mata, haɗe da lumshe idanunta, ta kuma buɗesu alokaci guda, shima murmushin yayi mata, kana ya buɗe duka hannayensa, alaman ta taho garesa,    babu musu ta ƙarasa garesa, haɗe da faɗawa cikin jikinsa, atare suka rungume juna, tare da sauƙe ajiyar zuciya.

Hanunsa yasanya yashiga shafa bayanta, haɗe da soma hura mata iskan bakinsa, cikin kunnenta.  Luf tayi acikin ƙirjinsa, tana mai jin daɗin abun da yakeyi mata, idan har tanajin iskan bakinsa acikin kunnenta, sosai take samun nutsuwa acikin ruhinta.

Sun kusan mintuna 10 a haka kafun tace dashi cikin sanyin murya.    “Sannu da dawowa!”

Bai amsa mata ba, saima hannayensa daya ɗaura a gefe da gefen cikinta, yashiga shafawa a hankali,  shiru tayi aƙirjinsa tana sauƙe numfashi.  Ɗayan hanunsa yasanya ya ɗago haɓarta, suka jefa idanunsu acikin na juna, wani irin kasalane ya dirar mata alokaci guda, sakamakon tozali da kyawawan idanunsa da tayi.  lumshe nata idanun tayi, tana sauƙe numfashi a hankali, matso da tasa fuskar yayi gaf da tata, harsuna iya jiyo hucin numfashin juna,  bakinsa ya buɗe haɗe da kamo lip ɗinta na ƙasa, yasoma sucking a hankali,  tsikar jikinta ne, ya shiga tashi, take wani shauƙi yasoma ratsa ta,  kusan mintuna 6 yana sucking lip ɗinta, kafun ya tsagaita yashiga maida numfashi.  Ganin haka yasanya ta sanya hanunta akan wuyansa, haɗe da sanya bakinta acikin nasa, ta laluɓo harshensa, tasoma masa shan sweet,   yanda take sucking ɗinsa tausassun laɓɓanta na kai komo cikin bakinsa shine abun da ya ƙara hautsina tunaninsa,  tsananin sha’awarta ne yasake ninkuwa acikin zuciya da jikinsa.  Hannayensa yasanya yana ƙoƙarin buɗe gaban rigarta. Kukan Asad ne ya katsesu daga duniyar da suke ƙoƙarin faɗawa, gaba ɗaya su sunma manta da cewa yana ɗakin. shikuwa Asad chocolate ɗinsane yafaɗi ƙasa, shiyasa sa fashewa da kuka.

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri Zahrah ta ƙarasa garesa haɗe da ɗaukan chocolate ɗin  ta danƙamasa a hanunsa, dawo da kallonta tayi ga Doctor dake tsaye idanunsa sunyi ja. Murmushi tasakar masa, tare da takawa ta ƙarasa garesa, hanunsa ta kama ta zaunar dashi akan gado, kayan jikinsa tashiga rage mai, saida ya rage dagashi dai dogon wandon suit ɗin dake jikinsa.    Bathroom tashiga ta haɗa masa ruwan wanka.  saida taga shigansa wankan kafun ta ɗauki Asad suka fice daga cikin ɗakin, wajen Haulat tamaida Asad, itakuma ta wuce kitchine. Milk Shake tahaɗa masa, haɗe da ɗaukan wani tray na tangaran me kyau ta yayyanka kayan marmarin aciki.   ɗaukan ɗan madaidaicin tray ɗin tayi, tare da cup ɗin da  milk shake ɗin ke ciki, ta nufi ɗakinta.

Harya fito a wankan yana zaune akan gado, dagashi sai long jeans ajikinsa,  tanashigowa cikin ɗakin, ya kafeta da  tsumammun idanunsa,  ɗan madaidaicin stool ta jawo ta ɗaura kayan hanunta akai, zama tayi akusa dashi. Da kanta tasoma bashi fruit ɗin abaki.  Yanacin fruit ɗin amma gaba ɗaya hankalinsa na ga breast ɗinta da suka bayyana kansu ta saman rigar dake jikinta.  Sarai ta kula da cewa hankalinsa naga breast ɗinta, hakan yasa da gangan ta kuma saɓule wuyar rigan don yagani da kyau.  Tana kammala bashi fruit ɗin, aka soma ƙiran sallan Magriba,  alwala yayi haɗe da ɗaura brown ɗin jallabiya akan wandon dake jikinsa yafita zuwa masallaci, itama alwalan tayi, ta gabatar da sallah, bata tashi akan sallayan ba har saida tayi sallan isha.   Wanka takuma yi, yanzu kam wata fitinanniyar sleeping gown ta sanya wacce iyakarta guiwa,  turarenta da tasan yana tafiya da imaninsa tashafa, haɗe da ɗaukan wani wanda ƙamshinsa ke haifar da kasala, tashafa aƙasan breast ɗinta dama duk wani lungu da saƙo na jikinta. 

Tana tsaye agaban dressing mirror ɗin yashigo cikin ɗakin, dawowarsa daga masallaci kenan.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗewa,  idan yabiyewa Zahrah zata zautar dashi ne kawai, gaba ɗaya yawani zama soko akanta, kullum ƙara kyau da cika take, sannan kuma duk kwanan duniya ƙara fito da wani sabon salo take, wanda take rikitasa da su,  ga tarin soyayyarta dake ƙara wanzuwa acikin jini da jikinsa, shikansa baisan wani irin so yakeyi mata ba, amma yayi amanna da cewa, bayan Zahrah babu wata,  ita kaɗaice bata da tamka, ita ta musammance acikin matan duniya. baisan wata mace ba aduniyarsa bayan ita, amma kuma yanaji ajikinsa cewa, yayi dace, yakuma samu gamdakatar wanda bayajin akwai wata wacce zata kama ƙafarta.

Ƙarasowa yayi gaban mirror ɗin ya rungumeta ta baya haɗe da kwantar da kansa abayanta, yana sauƙe ajiyar zuciya, iya ƙamshin dake fita ajikinta ma kaɗai, ya isa yasanya masa feeling, ina kuma ga ya taɓa lallausan fatar jikinta.

Hanu tasanya ta shafi gefen fuskarsa, haɗe da ɗan zame jikinta daga nasa.  Hijab ɗin dake aje kan gado ta ɗauka, haɗe da zurawa ajikinta.

“Hubby Nasan Babyna yayi bacci, banaje na dubasa” tafaɗi haka tana me nufar hanyar fita daga ɗakin.

Bai iya ce mata komaiba harta fice.

Tanazuwa ɗakin Asad ɗinkuwa tasamu yayi bacci akan lallausan gadonsa,  yayinda Haulat mai kula dashi itama tuni tayi bacci, zama tayi ta tofeshi da addu’a, haɗe da gyara masa kwanciyansa. Rage musu hasken wutan ɗakin tayi kana ta yi ficewarta.

Tana shiga tasamesa tsaye dagashi sai towel ɗaure a ƙugunsa, yayinda jikinsa ke ɗauke da danshin ruwa, da’alama ruwa ya watsa wa jikinsa.    Cire hijab ɗin jikin nata tayi, ta nufo inda yake,   atare suka sakarwa juna murmushi,    jawota yayi haɗe da mannata da ƙirjinsa,  hanunsa yasanya acikin gashin kanta, murya asanyaye yace.

“Nayi kewarki dear, muna gida ɗaya amma yau two days kenan banji ɗumin jikin ki ba!”  yaƙare maganar yana me cusa kansa acikin wuyanta.    Lokacin da sajensa ya taɓa fatar wuyanta,  saida taji wani yarrrrrr ajikinta,   hanunsa yakai kan cikinta, ya warware igiyan da tazamo mahaɗin rigar dake jikinta, aikuwa take rigar ta buɗe ta gaba, hannayensa duka yasa ya juyo da ita suka zamana suna fuskantar juna.    kallon juna suka shigayi cike da shauƙi, hanunta ta ɗaura akan chest ɗinsa tana shafawa a hankali, lumshe idanunsa yayi haɗe da laluɓar fuskarta ya haɗe bakinsu waje ɗaya.   A hankali suke sucking lips ɗin junansu, suna fidda wani irin numfashi mai sauti,   cike da nutsuwa ya zame gaba ɗaya rigar jikinta, tayi ƙasa,   hannayensa yaɗaura abayanta yashiga shafawa yana yawo dasu ahankali har ya gangaro zuwa kan ƙirjinta, still bakinsu na haɗe dana juna suna bawa kansu hot kiss.   Saida sautin numfashinsu dukansu ya sauya, alokacin da hanunsa suka shiga yawo akan breast ɗinta, cire bakinsa yayi acikin nata kana ya gangaro da bakinnasa zuwa wuyanta,  tsotseta yake son ransa, yana fidda wani irin numfashi dake nuna yana cikin tsananin mayen sha’awa dakuma sonta.   ƙafafunsu ne suka soma gazawa wajen ɗaukarsu,  tana acikin ƙirjinsa suka nufi kan bed.  Maƙalewa tayi ajikinsa, ahankali take goga masa breast ɗinta akan chest ɗinsa, hakan kuwa sosai ya ruɗasa,   tana kwance aƙasansa yayinda shikuma ya yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, sukansu basusan awacce duniya suke ba,  gaba ɗaya sun zauce,  alokacin daya gama ratsa cikin jikinta, sai da wasu hawaye masu ɗumin gaske suka gangaro daga cikin idanunta, sam hawayen  bana baƙinciki ko damuwa bane, wannan hawayen sukan fitane alokacin daya dace, lokacin da mutum yakasance baya acikin duniyarsa, irin wannan hawayen sukan fitane, alokacin da mutum wanda ke acikin tsananin magagin sha’awa da kuma so yasamu abun dayakeso a lokacin daya kusa zautuwa,  wannan hawayen na musamman ne, wannan hawayen sukan fitane alokacin da mutum yasamu cikar muradinsa.

Yanayin da suka samu kansu aciki, yakasance me daɗi agaresu,  gaba ɗaya daren sun ƙare shi ne cikin soyayya, yayinda Zahrah keta zuba masa shagwaɓa shikuma ya dage sai lallaɓata yake, koda sau ɗayane bayason abun dazai ɓata ranta.  Gaba ɗaya yagama shagwaɓata, yamai da ita saikace wata ƴar 7 year.    Yanzuma shagwaɓan tagama zuba masa,  tana kwance luf acikin ƙirjinsa, yayinda shikuma ya kafeta da idanunsa, dake ɗauke da mayen sonta.   Kissing ɗinta yayi akan goshinta, haɗe da maida duka hannayensa cikin ƙirjinta, har yau jinta yake kamar sabuwar budurwa, koda yaushe ƙara shiga zuciyarsa take, sannan babu wani abu na jikinta daya sauya daga mai kyau zuwa marar kyau, breast ɗinta har yau sunanan a yanda suke babu wani abu daya samesu,  hakan nema yasa ako da yaushe yake nanuƙe mata, ya murzata son ransa, atunaninsa bacci  take saboda haka yayi ƙasa da kansa zuwa ƙirjinta, wani numfashi ta sauƙe alokacin da taji hucin numfashinsa, na sauƙa akan ƙirjinta ahankali,   dama baccinta baiyi nisa ba,  duka hannayenta ta cusa acikin gashin kansa, tana yamutsawa slowly,  ahaka har bacci ya ɗaukesu  dukansu..

(Nima bacci nakeji, kuyi haƙuri typing ɗin dare nayi,  yanzu nagama kuma dare yayi sosai, saboda haka da safe idan Allah Yakaimu zan sake muku shi. Please kubani Vote sosai a wannan page ɗin, Inason wannan page ɗin, da wanda zanyi gaba sufi kowanni page na baya yawan vote, next page na Zaidun mune.)

Rayuwa tana tafiya ne da gudu gudu batare da wani mai rai ya ankara da hakan ba, akullum kwanan dunia shekarunmu ƙara ƙarewa suke, sannan ƙara girma muke, sake kusantar mutuwa muke.   Daga kwana ɗaya anzarce kwanaki daga kwanaki anwuce satuttuka daga satuttuka anwuce watanni daga watanni anɗarawa shekaru. Haka yake ako da yaushe, acikin waƴannan kwanaki da shekarun kuma abubuwa ne masu yawa suke faruwa  suke kuma shuɗewa, wani yasamu cigaba wani kuwa yasamu naƙasu, wani ransa yayi baƙi wani kuwa ransa yayi fari ƙal.  To hakance takasance acikin labarin ZAID da ZAHRAH,  shekaru sunja rayuwa ta haɓaka,  shekaru sama da biyar kenan yanzu,  har lau kuma rayuwa suke cike da farinciki….+

“MY SOUL!  MY SOUL!!  MY SOUL!!!”    muryarsa daketa kwaɗa ƙiran sunan MY SOUL ta ƙaraɗe ilahirin farfajiyan gidan, tundaga cikin katafaren falonsa, keta kwaɗa ƙiran har ya kawo compound ɗin gidan.

Sanye yake da wando track suit sai kuma wata farar t-shirt ƙafarsa sanye suke cikin wani takalmi mai igiyoyi.     Tsayawa yayi haɗe da sanya hannayensa akan ƙugunsa yana fesar da numfashi, yayinda yaketa baza idanunsa, ko zai hango wacce yake nema.   Babu wani abu daya sauya ajikinsa, sai ma kyau da hasken fata daya ƙara, ga wani haɗaɗɗen ƙasumba daya daɗa ƙawata kyakkyawar fuskarsa, lallai shiɗin namiji ne cikekke, wanda zai ɗauki hankalin duk wata mace data gansa, ya haɗu sosai da sosai, duk da cewa shekarunsa sun ƙaru akan nada, amma duk da haka yana nan ayanda yake, kyawunsa da kwarjininsa suna nan,  haryanzu shiɗin mutum ne mai tsananin son gayu, sam bayason ƙazanta,  komai nasa me ajine.  ZAID kenan namijin dayazamo abun kwatance acikin sauran mazaje, namijin daya iya jure dakon soyayya me tsananin zafi, namijin daya zamanto sadauki, akan soyayya.

Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da ƙara furta ƙiran sunan

“MY SOUL”

Da gudun gaske wata kyakkyar yarinya wacce bazata wuce 6 year ba ta ƙaraso tsalle ɗaya tayi ta haye bayanshi,   lumshe idanunsa yayi, alokacin dayaji an ɗale kan bayansa, yasan babu wani ko wata da zaiyi masa wannan aikin idan ba MY SOUL ɗinsa ba.    Hanunsa yasanya ya jawota daga bayansa, zamewa yayi akan guiwowinsa haɗe da ɗaura duka hannayensa akan kafaɗunta. 

“Maƙoshina saura kaɗan yafashe My Soul duk kuma akanki ne, kinaji inata ƙiranki shine kikaƙi ki amsa ko?”  tamkar wani ƙaramin yaro shagwaɓaɓɓe haka ya faɗi maganar.

Dariya  fara kyakkyawan yarinyar da yanayin fuskarsu ke shige da tata tayi, haɗe da sanya hanunta akan dogon hancinsa. 

“I’am Sorry My Papa luv, ina cikin garden ne, kuma na amsa amma bakaji ba” yarinyar tafaɗa tana ɗan juya idanunta.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushinsa mai kyau yayi mata haɗe da jawota jikinsa ya rungume.

“Bazaki daina juya idanunki idan kina magana ba ko?” yatambayeta yana me shafa bayanta ahankali.

“Papa luv banice fa nakeyin hakan da gangan ba, nima banasanin najuya idanuna idan ina magana!” tafaɗi haka a shagwaɓe hartana ɗan buga ƙafafunta a ƙasa.  

Lumshe idanunsa kawai yayi yana maijin ƙarin ƙaunar ƴartasa na ratsa jini da tsokan sa,   sosai yanayinta ke kama dana Zahrah babba, haka kuma ɗabi’ar Zahrah ne wani lokaci idan tana magana takan juya idanunta, to itama wannan haka ta keyi,  sau da dama idan tana abu, kallon  real Zahrah kawai yakeyi mata,  domin kuwa yanzu da ta ƙara girma kamanninta da Zahrah sai ya sa ke fitowa,   baisan wani irin soyayya yakeyiwa  ZAHRAH ƴarsa ba, gaba ɗaya soyayyan da yayiwa Zahrah itace ta dawo kan yarinyar, wani irin so yake yi mata da baida misali, jinsonta yake ako ina na jikinsa,  Zahrah ƴarsa itace rayuwarsa, itace Hasken sa, itace madubinsa, wacce idan ya duba ransa keyin sanyi, samunta yafiye masa komai aduniya, samunta wani alkhairi da ginshiƙi ne acikin rayuwarsa, domin kuwa tunda yasameta, arzikinsa suka yalwata akan nada, shikansa ayanzu baisan iya adadin dukiyarsa ba,  itakanta yarinyar kamfanoni masu tarin yawa ya buɗe mata, sosai yake samun alkhairi adalilinta.

“Papa Luv!”  yarinyar ta ƙirasa murya a sanyaye.

Buɗe idanunsa yayi ahankali haɗe da sauƙesu akan babyn ta sa “Na’am My Soul” ya amsa mata.

Ya mutse fuska tayi haɗe da cewa “Yunwa nakeji Papa Luv banyi breakfast ba”

Waro kyawawan idanunsa yayi haɗe da  miƙewa tsaye ya sungumeta suka nufi inda zai sadasu da babban falon gidan. 

Tana tsaye agaban dining area tana nunawa hause girl yanda zata shirya musu dining ɗin,  tasha adonta cikin wani jan lace me kyau da burgewa, taƙara cika ta zama babbar mace, dagani kai kasan tana murza naira son ranta, domin wani haske ta ƙara tayi fat da ita.     Shigowarsu cikin falon suna dariya yasanya ta maida hankalinsu gareta, batasan wannan wace irin soyayya bace ke tsakanin Zahrah da Babanta Zaid, soyyace irin ta bugawa a jarida.

Tana tsaye tana kallonsu suka ƙaraso dining area’n kujera yaja ya zauna akai kana ya ɗaura Zahrah akan kujeran dake gefensa na dama, dama kuma haka suke zama koda yaushe.

Murmushi Afrah tayi haɗe da cewa “Nashiga ɗakinka banganka ba ae, sainayi tunanin kana wajen yin gym, ashe ma kuna tare da Zahrah”

Murmushi kawai yayi haɗe da sanya hanu ya shafi kan Zahrah, baitankawa Afrah ba saima duban Zahrah da yayi cike da so yace “Me zan zuba miki?”

“Duk abunda zakaci Babana nima shi zanci!” Zahrah tafaɗi haka tana kashe masa idanunta ɗaya.

Dariya suka sanya atare haɗe da bata hanunsa suka tafa,  abinci yasoma zuba musu da kansa, acikin plate ɗaya, dama kuma a yanzu baya taɓa cin abinci saida Zahrah, zaiƙi ci da kowa amma zaici da ita, kujera Afrah taja ta zauna itama, haɗe da soma yin serving ɗin kanta, don ta lura babu wani wanda yake ta ita, daga Zaid ɗin har Zahrah, su dama kansu kawai suka sani. 

Shida kansa yaciyar da ƴartasa, itama haka ta dinga basa abincin abaki har ya ƙoshi,   sama sama suke hira da Afrah, nan ma itace take jansu da hira, amma daba haka ba bazasu kulata ba, ita har mamakinsu ma take, Zahrah sam bata damu da ita ba, kamar ba itace ta haifeta ba, zancenta baya wuce mahaifinta dakuma Momyn Friend ɗinta, wanda suke makaranta ɗaya dashi.

Tana gama goge bakinta da tissue ta kalli Papa Luv ɗinnata ashagwaɓe tace.    “Please Papa luv yau muje shan ice cream mana!”

“My Soul yau inada aiki, mubari sai gobe mana, kinga fa next week zamu koma U.S.A, akwai abubuwan danakeso nayi kuma kafun mu koma” yafaɗi haka bayan ya aje kofin tea ɗin dake riƙe ahanunsa.

STORY CONTINUES BELOW

Sake shagwaɓewa tare da narke fuskarta tayi, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa

“Ae Dan Allah Nace Papa Luv, inaso naje ne!”

“Shikenan zo muje na shiryaki” yafaɗi haka yana mai miƙo mata hanunsa.

Tsalle ta doka haɗe da faɗawa jikinsa ta rungumesa, cike da farinciki ta kai masa sunbata akan ƙuncinsa. 

“Thank You Papa Luv”

Ɗagata yayi caɗak akan kafaɗunsa haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan table, direct suka wuce ɓangarensa. 

Kai kawai Afrah ta girgiza haɗe da cigaba da cin abincinta, sam abunsu baya damunta, tasaba da hakan, koda yaushe haka suke, kamar tip da taya basa rabuwa.

Shida kansa yayi mata wanka yashiryata cikin wasu riga da wando na jeans masu matuƙar kyaun gaske, naɗe mata dogon gashinta yayi a tsakiyar kanta, da wani babban ribbon,  lokaci ɗaya kyawunta da tsananin kamaninta da Zahrah suka sake bayyana, shima wanka yayi kana ya shirya kansa, cikin wasu riga da wando masu kyaun gaske,  sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake,  Little Zahrah dakanta saida tayaba kyawun da Papa Luv ɗinta yayi.  

Yana riƙe da hanunta suka fito harzuwa falo, kallonsa ya maida ga Afrah wacce ta mato akan kallonsa.

“My Wife bazaki zo kirakamu bane?”  ya tambaya.

Murmushi kawai tayi haɗe da lumshe idanunta, akasalance tace “Kuje kawai Dear nikam inanan, amma ku tahomin da nawa ice cream ɗin”

Hanu Zahrah ta ɗaga mata alaman bye bye kana suka fice daga cikin falon.  

Barinta yayi awajen sayan kayan maƙulashe irinsu chocolate da sauransu shikuma ya nufi wajen turaruka.    Tana tsaye ta ƙurawa wani babban ledan chocolate dake can sama idanu, so take ta ɗaukoshi ta sanya acikin kayanta amma kuma wane ita, ya ɗarawa tsayinta,  jitayi anrufe mata idanu a hankali,   a iya saninta mutum ɗayane keyi mata hakan,  saboda haka yanzuma tasan cewa shiɗinne, dariyan farinciki tasaka haɗe da cewa “ASAD!” 

Dariya yayi haɗe da sake mata fuska ta juyo zuwa garesa, kyakkyawan yarone wanda bazai wuce 7to8 year ba, yarone fari tas dashi tamkar ajinsin larabawa yafito,     tsallen murna Zahrah tasanya haɗe da rungumesa, shima rungumeta yayi cike da jin daɗin ganin ƙawartasa wacce rabonsa da ita yau tsawon sati uku kenan, tun da aka basu hutun makaranta rabonsa da ita..

Cike da ɗokin ganinsa Zahrah tace.    “Laaa Asad dama zanganka anan? kaida waye kukazo? nidai nida Papa Luv ɗina mukazo, aibansan zamu sameka anan ba da munzo tunda wuri”

Hanu yasanya ya ɗan murɗe bakinta cikin halayyarsu ta yara yace “Baki gajiyawa da Surutu Soul ina Papan naki?”  yaƙare maganar yana me baza idanunsa.

“Asad me kakeyi anan, bacemin kayi chocolate zaka ɗauka kazo ba?”  

Daga Asad har Zahrah atare suka juya suna kallon mai maganar.     Kyakkyawar mace wacce ta amsa sunanta mace mai aji da kamala, sanye take da abaya gown black colour ta yane jikinta da mayafin abayar, komai nata na burgewa ne, kallo ɗaya zaka mata, kakuma son sakewa domin ba irin ƙananan matannan bane, duk da cewa bata da wani jiki, haka kuma bata wani sanja ba, har yanzu  tana nan da kyawunta mai fusgar hankali.

“Itace Mamanka?” little Zahrah tafaɗi haka ƙasa ƙasa tana kallon Asad.

Kai Asad ya kaɗa mata alamar “Eh” 

Da gudunta ta ƙarasa wajen Momyn Asad ta rungumeta,  cikin surutunta daya zame mata sabo tace.

“Oyoyo Mom Asad, dama inataso mu haɗu dake, amma bakya zuwa school ɗinmu, Dad ɗin Asad ne kawai yake zuwa,  ni da Asad abokaine sosai, kuma dan Allah kudawo U.S.A kunji, muma kunga can zamu koma” tunda little Zahrah tafara zuba bata tsagaitaba sai yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

Hakanan Zahrah taji yarinyar ta burgeta, durƙusawa tayi agaban yarinyar haɗe da sanya hanu ta shafa fuskarta, hakanan taji bugun zuciyarta ya ƙaru, “Idanunta ne ke mata gizo kokuwa dagaske kamanninta take hangowa akan fuskar yarinyar?” tambayar da tayiwa kanta kenan, cike da son sanin amsa.

Murmushin da Little Zahrah tayiwa Mom Asad ne yayi sanadiyar kusan rugujewar zuciyarta.    “ZAID” tafurta sunan acikin maƙoshinta da kuma kan laɓɓanta, sai dai kuma amon sauti baifito ba.

“My Soul”

Taji wata murya dabazata taɓa mantawa da ita ba tafaɗa.

Dagudu Little Zahrah takamo hanun Papa Luv ɗinta dake tsaye.

“Yauwa Papa zokaga Momyn Friend ɗina Asad, wacce nafaɗamaka tana da kirki, tana bawa Asad abun daɗi, shikuma yana bani.” 

Idanunsa ya sauƙe akan bayan wata mace dake durƙushe a ƙasa tabasa baya,   cigaba da jansa little Zahrah tayi harzuwa inda Mom Asad ke durƙushe amma bata ɗago fuskarta ba.

“Momyn Asad, ga Papa Luv ɗina nima, tare dashi mukazo” little Zahrah tafaɗa cike da kauɗi.

Ahankali ta ɗago manya manyan idanunta ta ta kalli mutumin da Zahrah ke cewa shine Papa Luv ɗinta.

Atare bugun zuciyarsu suka tsananta, take wani irin abu ya tsarga jiki da jijiyoyinsu.

Da ƙyar ta’iya daure zuciyarta ta ƙaƙalo murmushi.

Shima murmushin yayi haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa.

Hanun Asad ta kama jiki asaɓule ta juya daniyar barin wajen.

“Asad” taji muryar Zaid yaƙira sunan yaron.

Tsayawa sukayi cak amma ita bata juyo garesa ba,  takowa yayi har inda suke ya durƙusa haɗe da kamo hanun Asad. 

“My dear ya hutu?”  yatambayi Asad.

“Lapiya”  Asad yabashi amsa yana murmushi.

Kallonta yayi haɗe da cewa “Dama Asad ɗanki ne?” 

Kanta kawai ta jinjina masa alamar “Eh” gaba ɗaya ta ƙosa subar wajen shikuma yakama Asad ya riƙe ƙam.

Murmushin dake ƙarawa  fuskarsa kyau yayi haɗe da cewa “Fine boy, natayaki murnan samun wannan kyakkyawan yaron,  amma kuma saidai inajin tsoron abunda zai faru anan gaba,  Asad abokin Zahrah na ne, idan nan gaba yasan nayiwa mahaifiyarsa laifi mai girma yakike tunanin zai ɗauki abun?” 

Kanta ta girgiza masa haɗe da ɗanyin murmushi.  “Kada kace haka Zaid, abu idan ya wuce yana da kyau amantasa, afuskanci gaba, banafatan Asad yasan abun da ka aikata agareni” ɗan numfasawa tayi tare da kama hanun Asad.     “Sauri nake zanwuce gida”  kallonta ta mayar ga Little Zahrah da ta ƙura mata idanu tun ɗazu, murmushi Zahrah tayi mata, haɗe da shafa kanta, sosai taji son yarinyar acikin ranta.

“Allah ya albarkaci rayuwarki Rabin raina”    Tana faɗan haka taja hanun Asad suka bar wajen.

Saida ta ɓacewa ganinsa kafun yasaki wani murmushi haɗe da cusa duka hannayensa acikin aljihun wandon jeans ɗin dake jikinsa.   Little Zahrah ce tataho zuwa garesa haɗe da maƙalewa acikin jikinsa, murya asanyaye tace “Papa dama kasan Mommyn Friend ne?”

Murmushi yakumayi akaro na sau babu adadi,  hanunta yakama suma suka bar wajen, batare daya bata amsar tambayar da tayi masa ba.

Tunda suka shiga mota batace da yaronnata ƙalaba,  shima baitanka mata ba, domin dama shi hakanan yake ba mutum ne mai son yawan magana ba, yana da miskilanci wani lokaci.  Ganin da yayi cewa kamar Momyn nasa na cikin damuwa ne yasanyashi gyara zama haɗe da cewa.

“Momy wani laifi ne Papan Friend yayi miki?  naji kamar yace wai bayaso muji ko mu sanine oho”

STORY CONTINUES BELOW

Harara ta watsa masa, hakan yasashi yin gum da bakinsa, shidama gulmace ke cinsa, da yasani ma da baitambaya ba.

Tana isa gida tasamu Husnah da Areefa matar Asad, sunzo suna jiranta, sam basu sanar da ita zuwansu ba,  batayi mamakin ganinsuba kamar yanda tayi mamakin  ganin yanda aka sauya mata tsarin falonta, aka mamaye gaba ɗaya falon da decorations masu kyaun gaske,  tsayawa tayi tana ƙarewa falon nata kallo.

“Happy Birth Day to you my dear Wife!!!” 

muryar Dr.Sadeeq ta karaɗe ilahirin kunnuwanta, kallonta ta maida inda taji muryartasa na fitowa.

Fitowarsa daga ɗaki kenan yasha ado cikin riga da wando na jeans masu matuƙar kyau.  Murmushi tasakar masa,  gaba ɗaya ita tamanta da cewa yaune birth day ɗinta.

Hanunta yakama suka nufi wani ɗan keɓeɓɓen waje dake cikin falon, sosai aka ƙawata wajen da decoration’s  mai kyau,  kusan suman tsaye tayi alokacin dataga irin hidiman da mijinnata ya shirya mata, manya manyan cake masu kyau da tsada yasa akayi mata har guda uku, ga kayan ciye ciye dana shaye shaye, tsananin farinciki da ƙaunarsa ne suka mamaye zuciyarta, juyawa garesa tayi ta rungumesa, haɗe da cusa kanta acikin ƙirjinsa tana shaƙan daddaɗan ƙamshin jikinsa.  

“Thank you so much my lovely husband!!!” tafaɗa cikin sanyi yayinda ƙaunarsa ke ƙara ratsa zuciyarta.

“Babu godiya atsakaninmu My Wife kina da babban matsayi a wajena, keta musamnan ce, inasonki da duka zuciyata!” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana ƙara matseta acikin ƙirjinsa.

Kwantar dakanta tasakeyi ajikinsa cike da ƙaunarsa, haƙiƙa tasamu duk wani abu da takeso, farinciki, soyayya, da kuma zaman lafiya, sosai Doctor ke bata kulawa, bayason ɓacin ranta ko kaɗan,  yana ƙaunarta har acikin jininsa, itama kuma tana ƙaunar mijinnata sosai, ayanzu yafiye mata kowa da komai,  yabata farinciki haka kuma yabawa iyayenta, yamantar dasu komai na ɓacin rai da talauci, ya wadatasu da komai na rayuwa, bata da wani  TAURARO sama da shi, shiɗin na musamman ne arayuwarta, koda sau ɗayane bata taɓa yin danasanin kasantuwarsa amatsayin mijinta ba, ko da kowa aduniya zai juya mata baya, tasan banda Mijinta Haskenta Abun Alfaharinta.    Rayuwarta tayi mata daɗi akoda yaushe saidai tace ALHAMDULILLAH..

***

Yana tsaye agaban dressing mirror  yayinda little Zahrah ke tsaye agefensa, tana shan chocolate, Afrah ce tashigo cikin ɗakin hanunta ɗauke da kofin coffee wanda take haɗamasa kullum daren duniya.

Miƙo masa kofin coffee ɗin tayi, ya amsa yana murmushi, aje kofin yayi haɗe dasanya hanu ya jawota jikinsa ya rungumeta, bakinsa ya kai dai dai saitin kunnenta, ahankali yace “Inasonki ƴar lukutar matata!”  

Dariya Afrah tasanya haɗe da cewa “Nima inasonka ɗan lukutin mijina” 

Murmushi kawai yayi haɗe da sanya hanu yashafi kumatunta.

“Nima inasonka Papa na!!”  little Zahrah dake tsaye a gefensu tafaɗi haka da ƙarfi.

“SON SO nake miki farincikina, idan babuke acikin rayuwata, to babu wani haske dazan sake gani, Allah yarayamin ke na aurar dake ga miji na gari!!” yafaɗi haka yana dariya, acikin zuciyarsa kuwa, har yau tsananin danasanin yanda halayansa suka kasance a baya yake,  yayi danasani sosai, har gobe kuma akan danasani yake, bazai kuma taɓa daina Istigfari ba har ƙarshen rayuwarsa.

Duk da Little Zahrah  bata fahimci me maganganunsa ke nufi ba, amma tasan cewa mace da namiji suna aure, domin wancan satin daya wuce ma sunje auren ƙanwar momynta.

Dagudu taƙaraso ta rungumeshi,  ƙasa ƙasa tace  “Nidai ko zanyi aure bakowa zan auraba sai Friend, aishima yanasona ko Papa?”

Durƙusawa yayi agabanta cike da soyayyarta yace “Yanasonki mana, ai aduniya babu wani wanda zaiƙi me wannan kyakkyawar fuskar, ke ɗin ta musammance My Soul!”

Daɗine yakama Zahrah, sake rungume mahaifinnata tayi, aranta tana ƙara ƙaunar papan nata, domin adunia tasan bayan shi babu wani wanda zaiyi mata irin wannan soyayyar dayakeyi mata a yanzu……

*** *** ***

Duka ahali biyun rayuwarsu ta miƙa komai suna yinshine cikin farinciki da jin daɗi, akowacce rana ta duniya ƙara ƙaunar junansu suke, saidai muce  MASHA ALLAH.

*Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen labarin SHU’UMIN NAMIJI ina fatan zakuyi aiki da abun dayake dai dai aciki, inda nayi kuskure kuma Allah Ubangiji yayafemin, nagode sosai da sosai masoyana, haƙiƙa kunbani haɗin kai nakuma ji daɗin haka Allah Yabar Ƙauna,   waƴanda na ɓatawa rai don Allah kuyi haƙuri, balaifina bane, haka labarin yake, haka kuma ƙaddaran  ZAID  da ZAHRAH yake, babu wanda ya isa sauya ƙaddaransa.

*Ku ci gaba da bibiyana Insha ALLAH Zakujini da labarai kala kala wanda ina da tabbacin zasuyi muku daɗi, Ina muku SON ƘAUNA!!!  Insha ALLAH Ina zuwa muku da wani sabon labarin wanda zai ɗare ma Shu’umin Namiji, ina kuma da tabbacin cewa zaku ji daɗinsa sosai, na katse muku labarinne saboda wani babban uzuri.* 

      

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page