Uncategorized

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 4 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 4 BY Fateeyzah mbs_✍️*

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kuma Gyara zama Alhaji salisu yayi, sannan yace ” wallahi matsalarsu tafi ta manya, matsala ta farko, ba don Allah zasu aureka ba, haka kuma badon suna sonka ba,  face don dukiyarka, haka suma iyayensu don kwad’ayin dukiyarka zasu baka, saboda idan ka lura gaba d’aya auren babu match, kai kana da 54 ka auri ‘yar 16 kaga akwai matsala, na biyu kuma basu da kunya, basu da ladabi, daga ranar da ka had’a gado da kai, ta ganka tsirara, to maganar gaskiya ta gama ganin girmanka sai dai kayi ta hak’uri, kai k’arshe ma zaka fad’a mata magana sai kaji ta k’aryataka( zaro ido director yayi cike da mamaki), gyad’a kai  yayi ya ci gaba da yes zata k’aryata ka, ka fad’a mata magana sai kaji tace “Allah!, da gaske!, rantse!” (Kwashewa da dariya

suka yi gaba d’aya) kaga kuwa ta k’aryataka, bata yadda da abunda ka fad’a mata ba, matsala ta uku, bata waye ba, domin tayi rayuwarta daga gida, sai makaranta tare da k’awaye irinta, kai dressing wannan basu iya ba irin na iyayenta zata dinga yi, tunda shi taga ana yi a gidansu, kullun cikin riga da zani, balle kuma aje ga girkin zamani nan zaka sha takaici, kullun daga shinkafa, taliya, dambu, fate  da tuwo zaka ringa ci, ba a san a had’a maka drinks ba balle snack, kuma ga kayan had’in ka siya ka ajiye, kai tawa fa dana aureta bata san banbancin da kuma abunda ya kamata a ci for breakfast, lunch, and dinner ba, don wallahi har d’umaman taliya take min da safe in ta ragu,(dariya director yayi) ga shegen bani², yanxi fa k’ud’in kayan miya kullin 1k nake bata, kaga a week 7k kenan, amma abun naira biyar ta siya sai ta tambayeni kud’insa, wanda ni a tunanina in tayi amfani da kayan miya sosai, ta yi amfani dana 2k, 5k ya zama taci riba dani, amma ita kullun baza da kud’i, ga son nuna suna dashi ga ‘yanuwansu da k’awaye, hade’e da iyayin su matan wane ne, wallahi in na tsaya lissafo maka matsalolinsu sai mu kwana a nan, don dai ni nayi degree, don haka kada ka maimaita mistake d’in da nayi, don ni wallahi a yanxu har gwararmun hajiya Luba, don ita tana d’an tarairaya ta”

 Gyad’a kai yake fuskarsa d’auke da mamaki yana mai cewa “chab di!, nifa wallahi ganinsu nake na kirki, wad’anda zaka iya juyawa, a kula da kai, a kuma baka soyayyayya wal….”, katseshi yayi ta hanyar fadin ” so me?, ba wata soyayya malam sai dai hak’uri, amma wallahi basu iya soyayya ba balle aje da kula da sauransu”.

“To kai yanxu AG wace irin mace kake ganin zan aura?, wacce zan samu duk soyayya da tarairaya, wacce zata zame mini wife material” cewar director yana tambayar Alhaji salisu.

Mik’ewa yayi tsaye yana mai fadin ” zan fad’a maka later, don yanxu lokaci ya tafi, kuma ina so inje wurin staff officer muyi  relocating d’in _*SIWES STUDENT*_ “‘

“Yawwa! dama ina son maka zancen, please kada kh kawo min su office, don na last year banji dad’insu fa, they make me suffered” ya fad’i fuskarsa d’auke da damuwa.

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE