DR MUHSEEN COMPLETE BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 19 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 19 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

             📝…………….. Muhseen saida yayi kwana biyu da tafi ba tare da kowa ya sani ba,Kaka da taga ya daina shigowa tasaka Khadijah a gaba akan ta Kira shi a waya ta ji ko lafiya,domin tana gudun kada ya kulle kanshi a daki tasan halin shi sarai idan yayi zuciya abin ba kyau.

   Haka Khadijah tayi ta faman Kiran wayar shi,Amma is not reachable kasancewar cikin asibitin su wasu wuraren babu network.

   Karshe dakyar suka samu ta shiga,lokacin Yana office din C O dinsu suna tattaunawa akan wasu takaddu da za’a tura Bauchi,Karan wayar da ya ji yasa yayi saurin dubawa ganin nomber Hajiya Kaka yasa ya ceman ogan nasu 

“Parmition sir”.

 

  “Ok”

Cewar C O Nursing.

    

    Yana dagawa yayi sallama.

  Saida ta amsa kafin ta ce “Yanzu mai gida shi ne ka tafi baka sanar da mu ba ko? Saboda mun hanaka wannan yarinyar mai kama da cokali”.

 

   Dariya ta kusan kufcemai Wai mai kama da chakali,Kai wannan tsohuwa da Jan rigima take.

   “Kiyi hakuri matar Zan Kira ki,yanzu Ina office din ogana idan na koma gida zan Kira sai mu yi magana ko?”

  Amsawa tayi da “to ba damuwa Allah ya taimaka ka gaishe da shi”.

   Saida ya amsa kafin ya katse Kiran Yana duban ogan nasu.

Shima duban shi yayi Yan cewa “Daga ji wannan ita ce Hajiya kaka,Dan na gane hakan yadda na ji tana janka”cewar C O Nursing fuskarshi dauke da murmushi dan duk cikin ma’aikatan su Yana jin dadin mu’amulla da Dr muhseen,kasancewar Yana da dunbin ilimi ga natsuwa da girmama manyan shi.

  Sosai Muhseen ya fadada fara’ar shi Yana sanar da shi ta ce tana gaishe shi.

    Cewa yayi “Ina amsawa insha Allah idan munje biki zan shiga na gaishe da ita”.

   Sosai ya ji ogan nasu Yana Kara shiga ranshi ganin yadda yake nuna kulawa ga familyn Shi.

   Haka suka ci gaba da tattaunawa kafin ya koma office din shi .

  A bangarin Hajiya Kaka sai a lokacin ta ji sanyin a ranta,jin muryar babban jikan nata.

   Da dare misalin karfe tara da Yan mintuna Yana bedroom din shi.system ce a gaban shi Yana dubawa.wayar shi ya ciro daga jikin charge kafin ya saka kati daga account din shi.

    Nomber Hajiya Kaka ya fara Kira.

   Ita ko lokacin tana zaune a falo ita da Jabeer kular dafaffiyar kaza ce ya kawo mata,Rukayya ce ta dafo mata,sosai ta ji dadin Naman kazar ganin yadda daguwar tayi romo ga taushi,tana ci suna hira da Jabeer akan al’amuran familyn nasu,da irin yadda kasuwancin yake tafiya.

      Jin wayar ta dauki Kara ya lalubota Yana duba mai Kiran,Maigida yaga an rubuta yasan Muhseen ne.

   Saida ya danna picking call kafin ya mikamata wayar.

   Karawa tayi a kunne tana cewa “yanzu mai gida sai yanzu ka shirya Kira na,tun dazu nake ta jiran ganin Kiran ka,to Daman dan nayima albishir ne na kazo ka tafi da matarka,Amma tunda baka so muma mun fasa baka”

   Ai Muhseen Yana jin haka da a konce yake yayi saurin tashi zaune ya fara zuba mata kirari “Haba kakata ta kaina,tsohuwa mai ran karfe,makiyanki sun buga da ke sun barki,kowa ya ja da ke to wallahi saiya fadi kasa,uwar gida daya tilo a gidan Alhaji Abubakar tubalin GIDAN FULANI,kece hasken ahalin fulani,Allah yaja da ran bafulatanar usili masu asalin kyawu da dukiyar shanu,asalin mutanen kanto.”.

   Jin tsohuwar ta saka dariya yasaka shi sakatawa shima Yana dariyar.

  Jabeer ma dariyar ya saka saboda Yana jin su kasancewar wayar a hansfree take.

  “Kai amma mai gidan ka iya godalo da neman a baka mata,irin wannan kirari haka sai ka saka na ji kamar zan Kara shekaru talatin a duniyar nan,sai dai kash nasan dole wata rana mutuwa zata dauke ni daga cikin ku”nan take Hajiya Kaka ta saka kuka tunowa da tayi babu mai gidanta sannan babu yaranta guda biyu wato Fatima da Jalaludden.

Sosai take kuka harda sharbe majina.

  Cikin yaren fulatanci Muhseen ya fara kokarin ganin ya kontarmata da hankali,sosai ta dan samu nutsuwa kafin suka dan taba hira.

Bayan sunyi sallama akan gobe da safe gashi nan zuwa katsinar kafin ta mikama Jabeer wayar tana goge gunyun hawayen daya rage a fuskarta.

   “Kai wallahi Ya Muhseen Kai dai Allah ya shirya ka”cewar Jabeer bayan ya Kara wayar a kunnen shi.

    “Ka sakamana Yar tsohuwa kuka ko?to Zan wallahi zan hana su Unlce su baka matar inga ta tsiya”.

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE