SHU'UMIN NAMIJI COMPLETE BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 12 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 12 BY FATYMA SARDAUNA

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tana ganin yagama zare belt ɗin jikinshi, tasoma ƙyaf ƙyaf ta idanu, kamar wacce aka kamata tana sata,  tsoronsa ne ƙarara, ya bayyana akan fuskarta,   ganin sa a haka tun farko, ya isa ruɗata, amma kuma dayake  bariki ne a gabanta, ya sanya bata fuskanci hakan ba, sai yanzune taga, gaba ɗaya yacika mata idanu.+

Cike da tsantsar rashin mutumci irin nasa, yasanya hanunsa ya jawo ƙafarta, zama yayi akan gadon, haɗe da sanya hanunsa akan fuskarta, ya matse mata baki,   idanunsa yaɗaura akan ƙirjinta,  wani irin murmushi yasake, haɗe da cije laɓɓansa,  wai wannan tatsitsiyar yarinyarne, takeson ɗaukar hankalinsa,      yaga waƴanda suka fita komai, bai kuma ji wani abu akan su ba, balle kuma ita ƙaramar alhaki,  yanaji ajikinsa cewa.   “A yanzu ba ayi wata mace wacce zata ɗau hankalinsa sama da Zahrah ba”   

Hanunsa yakai kan wuyanta, yashiga shafawa a hankali,    tsuru Afrah tayi tana kalllonsa, karo na farko a rayuwarta, da taji wani irin mugun fargaba ya daki zuciyarta, akan abun da ta aikata,    “Me zata ce masa yanzu idan har yanemi haƙƙinsa awajenta?”    take idanunta suka kawo ruwa taɗago ta kallesa.1

Ko kallonta baiyi ba, ya ci gaba da shafa wuyanta,  lumshe idanunta tayi, a zahirin gaskiya tana amsar saƙonsa, amma kuma acikin zuciyarta, tsoro ne yayi tasiri.1

Ɗayan hanunsa yasanya ya yakice duk wani abu na sutura dayayi saura ajikinta.

Kamar wata mutum mutumi haka Afrah ta tsaya tana kallonsa.    

“Tashiga ukunta idan wannan ingarman namijin ya haiƙe mata, batare da ya tsaya yayi romancing ɗinta ba”

ta faɗi haka acikin zuciyarta, bata ida tunanin nata ba, taga yayi off na wutan ɗakin..

Kwanciya yayi akanta, haɗe da sake mata gaba ɗaya nauyinsa,  da ƙyar take iya fidda numfashi, sosai yayi mata nauyi,  idan ba mugunta bama, taya zai kwanta akanta haka, aiko katifa ce saita lotse balle kuma ita.1

Cikin zafi zafi yashiga kissing lips ɗinta.   Yi yake kamar zai cijeta, dagani kai kasan muguntane ke cinsa,  baƙaramin zafi kuwa hakan keyi mata ba, gaba ɗaya ya taune mata baki,   lokacin daya ɗaura hanunsa akan breast ɗinta kuwa, saida tasaki kukan wahala,  komai bayayi mata shi cikin nutsuwa, duk wani abu da ƙarfi yake yi mata,  abu yake kamar me huce haushi.1

Ganin da yayi zata cika masa kunne da kuka ne,  yasanyasa sanya hanunsa ya matse mata baki.   Yunƙurin ƙwace kanta takeyi amma ina bazata iya ba riƙon Zaid ba wasa ba. 1

*****

Wani juyawa kansa keyi masa lokaci ɗaya ya firgice,  idanunsa ne suka kaɗa sukayi jajur dasu, yayinda jikinsa ke ɓari kamar wani mazari, iya ƙololuwar ɓacin rai a yau Zaid yashigesa,  da ƙyar ya iya laluɓawa, ya sauƙa akan gadon,  jefa ƙafafunsa kawai yake batare daya koda kalli gabansa bane, yana shiga cikin bathroom ya banko ƙofar da ƙarfin gaske.1

Jikin Afrah ne ya ɗauki tsuma, take ta fashe da wani irin kuka me taɓa zuciya. 

“Wayyo Allah na, nashiga uku, me zancewa Zaid? kaicona, nakasa haƙuri, gashi yanzu na jawa kaina”    abun da Afrah ke faɗa kenan acikin zuciyarta,  gaba ɗaya tsoron ma tashi daga kan gadon take, da ƙyar ta iya jan bargo ta rufe jikinta dashi.1

STORY CONTINUES BELOW

Ruwa ne ke dukan kansa,  yana tsaye agaban shower kamar wani statue,  iyaka ƙololuwar ɓacin rai, yau ya shigesa,   baitaɓa tunanin zaiji ciwo acikin zuciyarsa, wai dan yasamu Afrah ba a cikakkiyar virgin ba, sai gashi abun ya juye tunaninsa.

“Ashe dama haka maza sukeji, idan basu samu  matarsu a cikakkiyar budurwa ba?” yatambayi kansa.1

“ZAHRAH”

itace wacce  tafara faɗo masa acikin ransa,  take fyaɗen da yayi mata yashiga dawowa cikin kansa filla filla, tamkar alokacin komai ke wakana haka yaji acikin jikinsa,    da sauri yasanya hanu ya kama kansa, haɗe da kurma wani uban ihu,   yama manta da cewa acikin toilet yake.    

Wani irin nadama ne me girma  ya ruskesa  acikin  zuciyarsa,   sai yanzu ya tabbatar da cewa bai kyautawa Zahrah ba, yaku ma cutar da ita cutarwa me girma, ya ruguza mata alfaharinta.

“Meyasa yayiwa Zahrah haka?  me yasa yarabata da budurcinta? wani irin cutarwa ne yayiwa Zahrah haka?” yatambayi kansa cikin tsananin tsana da ƙyamar kansa.

“I hurt you Zahrah, why do i did this to you?  I’am stupid, i dont have sense, meyasa zan aikata haka?  kaicona dana cutar da rayuwarki,  na gusar miki da farincikin ki, na hanaki mallakawa mijinki budurcinki, na ƙwace budurcinki taƙarfin tsiya, forgive me, i hate my self, because of what i did to you,  natsani duk wata rayuwar duniyar nan, rayuwa batamin daɗi Zahrah!!”   cikin wani irin murya me haɗe da sautin kuka Zaid ke faɗan haka.   

Haƙiƙa yau baida abun da zaice, yasan Allah  ba azzalumin kowa bane, sai wanda ya zalunci kansa, gashinan shi ya zalunci kansa, kuma yagani,  gashi yanzu Allah ya haɗashi da wata ballagazar mace, wacce ta raba budurcinta ga mutanen titi,  yanzu ga abun da Zina ta haifar masa, bayajin son Afrah ko ɗigo acikin zuciyarsa, amma kuma yaji matsanancin ciwon samunta a haka da yayi, to idan dai shi yaji ciwon samunta ahaka, me mijin Zahrah kuma zaice? shida yake so da kuma ƙaunarta.1

Jingina kansa yayi da jikin bangon toilet ɗin,  yayinda ruwan dake fitowa acikin shower ke dukan bayansa.  Rumtse jajayen idanunsa yayi, haɗe da sanya haƙoransa ya danne laɓɓansa, jiyake kamar yata gwara kansa ajikin bango, har sai kan ya rabe gida biyu, koda zaiji salama, acikin zuciyarsa,      hanunsa na dafe da saitin zuciyarsa, dake yi masa zafi,   yajima a tsaye ruwa na dukansa, har sai da jikinsa yasoma karkarwa kafun ya kashe shower’n….1

Buɗe ƙofarsa, yayi dai dai da bugawan zuciyar Afrah, take jikinta yacigaba da karkarwa kamar anjona shocking.

Ko kallon inda take baiyi ba,  direct gaban drawer ɗinsa ya nufa, wata farar T-shirt ya ɗauka ya sanya ajikinsa.

Ganin baice da ita komai ba, yasanya ta daɗa firgicewa, batasan me ze mataba nan gaba, cikin muryarta me ɗauke da tarin tsoro, haɗi da fargaba tace.  

“Dan Allah kayi haƙur……”

“Get out!!”

yafaɗi haka batare daya bari ta ƙarasa maganar dake cikin bakinta ba.

Cikin kuka takuma cewa

“Dan Allah kayi….”

“I say get out!!!”

yafaɗi haka atsananin tsawace, har sai da Afrah taji ƴaƴan cikinta sun kaɗa.

Gaba ɗaya ta ruɗe ta firgice, yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur dasu, shine abun da yafi komai ɗaga mata hankali,   da gudu ta fice daga cikin ɗakin, ko kayanta bata tsaya ɗauka ba, sai blanket ɗin da tayi amfani dashi wajen rufe jikinta.

Kwalbar turaren dake riƙe a hanunsa ya yi wurgi dashi,  zuwa wajen wani ƙaton mirror wanda ke kafe ajikin bango, take mirror’n ya fashe, haɗe da tarwatsewa a ƙasan tiles.1

STORY CONTINUES BELOW

Wani irin huci yake fitarwa ta bakinsa, yayinda yasanya duka hannayensa ya kama ƙugunsa,  jiyake gaba ɗaya duniyar na juya masa.

“Me ake da irin wannan  rayuwa, me ɗauke da takaicin?” yatambayi kansa.

Idanunsa ya sauƙe akan fridge ɗin dake ɗakin, wanda yake a cike da kwalbar wine ɗinsa,   a irin wannan halin dayake ciki, wine ce kaɗai zata iya bashi nutsuwa, duk da yasan ba lallaine ta iya ciresa acikin ƙuncin dayake ciki ba, amma tabbas zata iya rage masa damuwa, sai dai kuma bayajin aduniya zai iya ƙara aikata wani abu na saɓon Ubangijinsa,  ko a iya nan Allah yaɗauki rayuwarsa, haƙiƙa ya jarabtu, soyayyar Zahrah kaɗai da Allah, yasanya masa, yazamemasa babban jarabawa acikin rayuwarsa.1

Zama yayi a bakin gado, haɗe da bin blanket ɗin dake shimfuɗe akan gadon, da kallon takaici,   bakomai ne yafaɗo masa arai ba, kamar randa yayiwa Zahrah fyaɗe, haka gaba ɗaya tsakiyar gadon ya ɓaci da jininta,  yasamu Zahrah a cikakkiyar budurwa. 

“Yayi gaggawa? me yasa bai bari ya amshi budurcinta ta hanyar aure ba?”  wasu siraran hawayene suka fito daga cikin idanunsa, suka sauƙa akan ƙuncinsa, sakamakon tunowa da yanda ya farke Zahrah da yayi.1

Ahankali ya taka ƙafarsa ya ƙarasa gaban wani tangamemen hotonta, dake liƙe ajikin bangon ɗakin.

Zama yayi agaban hoton haɗe da cewa.

“Kiyafemin Zahrah, a yanzu nayi nadama marar amfani,  ni dakaina namiki fyaɗe, nidakaina nasa aka je har ƙofar gidanku aka ya da ke,  meye amfanina Zahrah?  me yasa nazamo mugu maƙuntaci agareki?  nagodewa Allah dayasa baki aureni ba, domin ban cancanci zama miji a gareki ba,  ni ban dace dake ba Zahrah, to tayama zan dace dake? ninefa wanda yayi miki fyaɗe, nine azzalumin dana rufe idanuna, na aikata ba dai dai ba akan ki,  to taya zaki yarda ki aureni, a’a ko kin yardama ni bazan yarda ba, domin ni dake bamu dace ba, bazan yarda nasake cutar dake akaro na biyu ba,  inasonki Zahrah so ba irin wanda kika sani ba, inamiki son da aduniya banayiwa kowa irinsa, sonki ajinina yake,  har abada bazan taɓa daina sonki ba,   ki hukuntani Zahrah, kimin duk irin hukuncin da kikeso,  nacancanci ki hukuntani Zahrah, ko kasheni kikayi bazanga laifinki ba, saboda nasan koda kasheni ɗin kikayi bazaki huce daga abun dana aikata a gareki ba,  ki ɗaga hanu ki dakeni Zahrah, kice Zaid natsaneka, banasonka, ki faɗi haka agareni Zahrah dan Allah, ki faɗa ko zanji salama acikin zuciyata!!!”

  

kuka sosai Zaid keyi kamar wani yaro ƙarami yana me rungume da hoton Zahrah acikin ƙirjinsa.

Yayi kuka irin wanda bai taɓayin irin saba, yayi kuka wanda har sai da ya haifar masa da ciwon kai,    kusan sama da awa ɗaya ya ɗauka yana zaune, agaban hoton Zahrah, da ƙyar ya’iya jaye jikinsa a wajen, ya faɗa bathroom,  alwala yayi haɗe da buɗe kofar yafito, idanunsa sunyi luhu luhu dasu, kallo ɗaya zakayi masa kasan ya sha kuka ya ƙoshi.

Blue ɗin jallabiya yasanya, direct ya wuce masallaci, duk da cewa kowa yagansa zai gane cewa yana a cikin damuwa, amma sam baidamu da hakan ba, uban kowa ma yasan yana cikin damuwa, shiba damuwarsa bane,  matsalansa ma kaɗai ta ishe sa.

Tunda tashiga cikin ɗakinta take kuka,  yau ne  karo na farko a rayuwarta, da tayi babban nadamar bada kanta da tayi a waje, yau tayi nadama ƙwarai,  yau ta ga sakarci dakuma wautanta, da ta ɗauki kyautar budurcinta sukutum, ta dan ƙawa wani banza, wanda yayi mata ƙaryan zai aureta,  me ake da irin wannan rayuwar, wayewar banza, wayewar wofi,  taɗauki zugan ƙawayenta, da suke ce mata wai inmace batasan daɗin sex ba bata waye ba, ta biyewa son zuciyarta taje ta bawa wani banza kanta, batare da sadaki ba ya haye kanta, ya karɓi budurcinta, batare da ko da sannu ba,  wace irin banzar hallakakkiyar waye wace wannan? wayewar da zata saka kaji kunyar Allah da ta mutanen duniya, kaicon irin wannan wayewar, tir da irinta,    bata taɓa manta yanda su Asma ke zugata akan cewa wai yakamata ta bada kanta ga saurayinta Ameer, ta kuma san duniya,  duniya ma ta santa, har cewa suke wai ita baƙauyiya ce, saboda kawai bata yarda wani namiji ya taɓa jikinta,  haka suke wareta acikinsu, haka suke nuna mata kyara, wai don kawai bata bari maza suna taɓata,  tabiye sharrin zuciya data ƙawaye, ta kuma  ɗauƙi shawararsu, ta yi watsi da mutuncin kanta,  gashi yanzu tun aduniya, ta shiga kunyar mijinta, takuma shiga halin nadama da danasi, ga kuma tozarcin da zata fuskanta daga wajen mijinta.

STORY CONTINUES BELOW

Zama tayi daɓas aƙasa tashiga rera kukanta, haɗe da tsinewa Asma da ma duk wasu ƙawayenta, da sukayi ruwa da tsaki, wajen tsundumata, cikin halakan data faɗa, shikuwa saurayinta Ameer, wanda shiya fara saninta ƴa mace, ta zuba masa tsinuwa yafi guda ɗari biyu,   da ƙyar ta iya lallaɓan kanta tashiga toilet donyin wanka..

Yajima acikin masallacin kafun ya dawo gida, abun dayajima baiyiba kenan, wai yaje masallaci yajima har haka,  karatun Al’Qur’ani yayi, kuma da yardan Allah yaɗan samu salama acikin zuciyarsa..

Afrah najin shigowarsa cikin gidan,  ƙafafunta yasoma rawa, take taji wani irin ciwon ciki ya kamata,  mugun tsoronsa takeji, tun ada ma, balle yanzu kuma da wannan abun yashiga tsakaninsu, ta tabbatar sai yakasheta acikin gidannan, kuma ya kashe banza.

Yana shiga cikin ɗakinsa, ya ɗauki magungunansa yasha,  tashi yayi yafice daga cikin ɗakin nasa, direct ɗakinta ya nufa.

Tanajin motsin ana buɗe ƙofarta ta miƙe zunbur, take wani irin fitsari ya zubo mata, tsabar tsoro, aikuwa tana jefa idanunta, cikin nasa, taji numfashinta, na shirin ɗaukewa.

Da rinannun idanunsa yake kallonta,  ganinta da yayi yasake tuna masa ɓacin ransa,  jiyake ya tsaneta, amma kuma yazama dole yayi mata tambayoyin dake cikin ransa..

“Zauna” yafaɗi haka cikin dakiya.

Jikin Afrah na rawa ta zauna aƙasan tiles.

Ƙafansa ɗaya yasanya, yataka kan gado, haɗe da ɗan ranƙwafowa.

“Dama ke karuwa ce?”  first tambayar daya fito daga cikin bakinsa kenan.

Ƙirjin Afrah ne ya buga, take hawaye suka ɓalle akan fuskarta, kanta tashiga girgizawa alamar

“A’a”

Laɓɓansa ya cije cike da takaici yace.

“Da bakinki nakeso, ki bani amsa bada kai ba.”

“A….a wallahi ni…..ba..ba..ka..ruwa..bace!” murya a sassarƙe tabashi amsa.

“Kinsan me ake ƙira da karuwa?”

Yatambayeta.

Dasauri ta kaɗa kanta, saikuma tatuna da abun dayace mata, baki na rawa tace “Karuwa itace mebin maza, wacce take zaman kanta”

“Good, ashe kinsan mene ake ƙira da karuwa, kenan ke ɗin karuwa ce?”

Da sauri tace “Wallahi niba karuwa bace”

“Idan ke ba karuwa bace, dan ubanki ina kikai budurciki!!!” amatuƙar tsawace yayi maganar, saboda ya matuƙar harzuƙa.

Guntun fitsarin da take ta riƙewane ya silalo, tsabar ta tsorata,    ƙyarma tafara tamkar wata mejin sanyi, tsabar tsorata da yanayinsa da tayi, ta makasa ce dashi komai.

“Shirun da kikayi ya nuna alamar cewa eh ke cikakkiyar karuwace, mazinaciya, me kike nema arayuwarki, kina ƴar ƙaramar yarinya dake?” yatambayeta yana me ƙare mata kallo.1

Kanta tashiga girgizawa, akaro na barkatai.

“Kayarda dani, wallahi niba karuwa bace, bantaɓa karuwanci ba!” tafaɗi haka tana kuka.

“Okay to tunda dai kince ke ba karuwa bace, ba naci ubanki, wataƙila zaki faɗamin inda kika kai virginity ɗinki” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin zare belt ɗin wandon jeans ɗin dake sanye a jikinshi.

Da gudu ta rarrafo ta ƙaraso garesa, zubewa tayi akan ƙafafunsa tana kuka.

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE