DR MUHSEEN CHAPTER 15 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 15 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

            Www.bankinhausanovels.com.ng 

       📝………………….Haka rayuwa tayi ta tafiya har wannan satin ya shude inda satin bikin su Dr muhseen ya kama,dukda ba wata hidima ta karya aka dauka ba domin su Uncle Yusuf sunce walima kadai za’a gudanar a holl din,sai Kamu da za’ayi daga su babu sauran wata bidi’a.

A bangaren Hindatu, Rukayya da Ameerah shirye-shiryensu kawai suke yi duk sun raba IV ga kawayensu da abokan arziki,an gayyaci Yan kauyen Kanto.

Haka su Dady Muhammed da Hajiya Mariya shiri suke yi sosai .inda Hajiya Mariya ta dage dan ganin ta gyara diyarta ta ciki da waje.shiko Dr muhseen tunda ya tafi aka turashi maiduguri inda zasu gudanar da wani aiki na tsawon wata ukku,Dan haka yaji dadin tafiyar domin bayanan za’ayi mai wannan kaddararran auren.tunda ya tafi hankalin shi konce Amma kusan kullun sai sunyi waya da Aunty Hajara duk wani abu da yake gudana Yana samun labari.

      A bangaren Seeyerma kuwa ba ruwanta da hidimar kowa ankon bikima da aka anso daga wajen dinki cewa tayi bata so,sai Faruk yaba Khadijah ta ajemasu kafin ranar yinin bikin kusan kala biyar-biyar yayimasu .tunda satin bikin ya kama su Aunty Aliya suka iso estate din harsai an kammala hidimar bikin kafin su koma.kallo daya tayima Seeyerma zuciyarta ta cika da dinbin mamakin ganin yadda yarinyar ta koma,dukda daman tana da garin jiki Amma ta Kara murjewa fatarta tayi gwanin kyau.da dare haka suna hira da Aunty Hajara take tambayata “Wai meya samu Seeyerma haka taga tayi wani irin kyau kamar wadda take shan wani abu”?sosai gaban Aunty Hajara ya fadi jin wannan tambayar Amma haka ta dake tana bata amsa da “kawai Yana yin hutu ne,kinsan yanzu babu hidimar school shiyasa jikinta ya murje,last week sakamakon Jarabawar su ya fito to saboda yayansu bayanan nadai sanar da shi a waya,Amma ya ce a bari ya dawo saboda alhakin hidimar karatunta Yana hannunshi”.

    Ita dai Aunty Aliya bata Kara cewa komai ba sai uuuhmmm data bita da shi.amma zuciyarta ta kasa yadda da abinda matar yayanta ta fada.koda ta je part din Hajiya Kaka haka tayi ta kallon Seeyerma duk inda tayi idonta Yana kanta.gano haka da Seeyerma tayi yasa ta sadade part din Mama bata Kara dawowa ba,sauran kayanta ma na hidimar bikin sai Khadijah ce ta kaimata.

    Aunty Aliya tanaso tayima Hajiya Kaka maganar,Amma ganin ana ta hidima yasa ta kyale sai idan bayan an gama sun tattauna akan lamarin.

A Sudan kuwa sosai Ummeey ta shiga damuwa da tashin hankali jin Wai Ameerah za’a aurama Son dinta,tabbas tasan a cikin wannan abun akwai chakwakiya mai rikitarwa,tasan da gayya akayi wannan hadin,Amma a kullun tana yima danta addu’ar Allah zabawa son dinta mace ta gari wacce zata zamo nutsuwa a gareshi .

Data sanar da Mahaifiyar su itama ta girgiza da jin wannan hadin,Amma haka tayi addu’ar fatan alkhairi.

     Lailah kuka ta sakamasu ita sai an kaita Nageria wurin su Hajiya Kaka Dan ayi hidimar bikin da ita.rarraahinta Ummeey ta dinga yi har ta kontar Mata da hankali akan cewar Ya Muhseen zaizo su tafi tare.jin haka yasa ta saki ranta tana murnar zata je Nageria.

     Ameerah tunda Hajiya Mariya ta fara gyarata ta daina zuwa koina acewarta gwamma ta natsu yadda Muhseen zai sota.(Niko na ce daga baya kenan😂).

    Sosai Hajiya Mariya hankalinta yadan konta ganin komai ya daidaita,yanzu ta fara ji a jikinta burinsu Yana gaf da cika,Dan idan har wannan aure ya tabbata to sun Kara samun wasu damar a hannunsu na su ci karensu babu babbaka.

 Dr muhseen ayyuka sunyimai yawa a maiduguri,Amma hankalin shi Yana Kan Seeyermar shi sosai tunanin yarinyar yake addabar zuciyar shi,daurewa kawai yake yi Haka yake ta addu’ar Allah yasa wata rana ya mallaki Seeyerma a matsayin matar shi,dukda Aunty Hajara ta sanarmai cewa Jarabawar su ta fito Kuma taci sosai.yayi alkawarin zai kashemata kudi dan ganin tayi karatu.

Maganar da sukayi da Aunty Hajara na Uncle Yusuf yaki amincewa da maganar hada aurensu da Seeyerma haka tasa dole ya hakura.saidai wani lokaci yakan ji a ranshi cewa komai daren dadewa Seeyerma zata zama matarshi .duk lokacin da yayi wannan tunanin sai ya ji hankalin shi ya dan konta,harya manta da wani auren Ameerah da za’a kwakuba mai.

   Koda safiyar ranar Alhamis tayi tunda asuba ake ta shirye shirye,wasu sunje saloon wankin Kai da kunshi wasu ko sun tafi wurin gyaran jiki.Amma Seeyerma tana dakin Mama a konce sai baccinta take yi hankali konce tamkar Bata da wata damu,dukda idan ta tuna yau sauran kwana biyu a daura auren ya Muhseen sai taji duk takaicin duniya ya lullubeta,Dan a fannnin ya Faruk bata jin komai saboda yadda Aunty Hindatu take nunamata kauna,hakama Aunty Rukayya da ya Jabeer suna ta kontar Mata da hankali ganin kamar hankalinta ya tashi.musamman Aunty Rukayya data gama gano cewa Seeyerma ta kamu da kaunar ya Muhseen.hakan yasa take ta rarrashinta saboda ta san akwai yarinyarta a tare da ita,dazarar sunyi kuskuren wannan sirrin ya fita to su Hajiya Mariya zasu iya tayar da hankalin su har su dauki amataki akai,tanaso Koda maganar zata fasu sai bayan ya Muhseen ya dawo yadda koma maizai faru saidai ya faru.ko jiya data Kira shi maganar da sukayi kenan,Dan Rukayya ita ke daukar Seeyerma hotuna tana turamai wani lokacin har Vedio take yimata ba tare data sani ba.akwai wani Vedio da tayimata ta fito daga toilet kenan tana taje gashin kanta daya jike da ruwa tsalle take yi sosai saboda yadda take jin zafin taje Kan da take yi.cike da shagwaba ta fadi kasa tana kuka,haka su Rukayya da khadijah suke yimata dariya,cike da zolaya Hindatu ta ce “kawai ki zo na aske maki gashin ki huta da ciwon Kai yarinya”

   Jin haka yada Seeyerma ta Kara saka kukan shagwaba.

   Tunda Rukayya ta turamai Vedion ya gani yake faman dariya.sosai ya shiga shauki da annashuwa ji yake kamar Yana kusa da yarinyar,shidai sakarcin yarinyar da shagwabarta suna birgeshi.

     Lura da Rukayya tayi bataga gittawar  Seeyerma ba yasa ta nufi part din Mama .cike falon yake da Baki Yan Kanto da sauran familyn su.haka ta kutsa kanta wasu suna ta faman janta Yan uwan Hajiya kaka ne.

      Can kuryar gadon ta hangota ta kudundine cikin blanket tana ta aikin sharar bacci.saidata haura saman gadon kafin ta yaye blanket din tana bububbuga gefen filon da take konce.

     A hankali ta fara mirginawa har saida ta kusan fadowa kasa kafin Rukayya tayi saurin tareta tana cewa “ke ki tashi kada ki fado fa”.

Kokarin bude idonta ta fara yi wani dishi-dishi take gani tsabar baccin da yake cin idonta.

Daidai nan wayar Rukayya tayi kara,da sauri tayi picking ganin sunan ya Muhseen akan wayar.

Cikin natsuwa ta gaishe shi,itako Seeyerma ganin haka yasa ta mayar da idonta ta lumshe tana Jin wani sabon bacci da kasala suna Kara saukomata.

    Wayar ta dora akan kunnen Seeyerma tana cewa “ka ganta nan inata fama da ita ta tashi ayimata kunshi da dilka Amma ta ki tashi”.

    Cike da kasala ya ce “Dear wake up mana,idan bakiyi kolliya ba zanyi fishi da ke,but idan kunyi Kuma kada ki bari kowa yayi ta kallonki”.

  Da sauri ta zabura tana mirje idonta jin yadda muryar shi ta daki dodon kunnenta.tayi tunanin duk dadin baccin ne yasa take mafarkin shi,saida ta ji ya Kara cewa “Dear kina jina kika yiman shiru ko”?

  “Uhmmm”kawai ta ce tana hamma Dan haryanzu baccin bai karasa sakinta ba.

Fita Aunty Rukayya tayi jin Hindatu na nemanta.kicibis sukayi a bakin kofar sai Suka dawo cikin dakin a tare

Hindatu ce ta kalli Rukayya tana cewa “Wai Ina Seeyerma ne tasaka ya Muhseen sai faman kirana yake yi Wai na saka ayimata kolliya,Niko harna gaji da cigiyarta Dan Allah ki dubota sai ki kawota part din Aunty Hajara Zan Kira Yaya Faruk ya fara kaita wujen wankin Kai kafin su dawo ankarasa Mana kunshin sai ayimata nata”.

     “Ai Aunty Hindatu na gantafa baccinta kawai take yi,Nima shiya taso ni Ashe tana nan dakin Mama”

Da sauri Aunty Hindatu ta kalli saman bed din hango Seeyerma konce da waya makale a kunnenta tana magana kasa-kasa yasa ta juya tana mamakin wannan boyayyar soyayya.itama Aunty Rukayya bin bayanta tayi suka koma part din Aunty Hajara inda acan ne suke gudanar da hidimomin su,Amma banda Ameerah ita tana part din Hajiya Mariya da sauran Yan Uwanta.

    Duk surutun da yake yi ta kasa cewa komai saidai ta ce “Uhmm”lura da yayi kamar bata son yin maganar yasa ya ce “ki tashi ki shirya yanzu zan Kara Kira”Yana gama fadin haka ya katse Kiran Yana bin wayar da kallo,gani yake yi kamar zai ganta.

     Tunda ya katse call din ta dade a zaune tana jin haushin kanta na shiru da tayi har yayi zuciya ya katse Kiran.

Dakyar ta mike tana jan kafa ta nufi toilet din da yake cikin bedroom din.

Sosai take jin jikinta yayi Mata wani nauyi,ta rasa wa zata sanarwa some time takanji kamar Bata da lafiya.ko jiya kafin ta konta saida tayi danwake  taci kafin ta iya yin bacci,saboda wani mugun kwadayin shi da ta ji ya kamata.

    Ta jima a toilet din saida ta gurje jikinta tas kafin ta dauro dan karamin towel ta fito.

Kallon kanta take yi a jikin madubi,ita kanta sai yanzu ta lura da wani mugun Kyau data Kara yi,Koda su Khadijah suna janta ita gani take yi kawai ba’a ce suke yimata.

Kafadarta ta dage alamar ko a jikinta taci gaba da shafa lotion a jikin tattausar fatarta mai kamar data sabbin jarirai saboda tsabar taushinta.

Tana idarwa ta saka wani riga da siket na green din atamfa.sosai dinkin ya amshi jikinta,tsam ya kameta tamkar a jikinta aka dinka su.ko powder bata shafa ba sai kwalli kawai data zizara a idonta.dankwalin tayima daurin zara cap dan siririn mayafinta ta dora bisa kafadarta .harta je bakin kofar fita ta tuna tabar wayar Aunty Rukayya dawowa tayi ta dauka kafin ta fice daga dakin bayan ta Kara fesa turaren Arabian uhd mai kwantaccen kanshi.

    Tunda ta doso falon kowa yake kallonta ganin yadda yarinya karama Allah yayimata baiwar kyau irin wannan.

Tunda ta taho idanun Aunty Hajara a kanta,ji tayi gabanta ya bada wani sautin  rassssssssss jin Yayarta Rabi’atu  tana cewa “Hajara wannan wane irin sakaci ne? me kuke kallo ace  kuna zaune da yarinya dauke da ciki Amma baku sani ba?”.

   Firgici tsoro da tsabar kaduwa sune Suka bayyana akan fuskar Aunty Hajara,daidai Seeyerma zata wuce ta kusa da su,cikin kakkarwa ta bude Baki tana cewa……………

.Cikin kakkarwa ta bude bakinta ta ce “Innalillahi Yaya Rabi’atu shin abinda kike fada da gaske ne! ko kuwa mafarki ne nake yi?”

   “Kin jiki da wani abu yo ya za’ayi nayimaki wasa da wannan maganar,ku saka a aunata anan zaku gane maganata gaskiya ce”cewar Aunty Rabi’atu tana kallon yadda kanwarta ta rude da jin maganar.

Cikin tashin hankali Aunty Hajara ta nufi bedroom din Mama ,itako Seeyerma tuni ta fice daga falon dan duk maganar da suka yi ba Wanda ya ji kasancewar suna gefe daya.da sauri itama Aunty Rabi’atu tabi bayan yar’uwata ta da tana hango tashin hankalin dake tunkaro su,domin duk irin cakwakiyar dake wakana a wannan family tana da labari,shiyasa ta fasa wannan maganar domin tana ganin ta wannan hanyar za’a iya fasa auren Ameerah da Muhseen a bashi Seeyerma.

Tana shiga taga Mama bata a cikin dakin dan haka ta juya zuwa part dinta.yanmatan duk sun cika falon sunata hidimar su,duk ba Wanda ta kula direct ta wuce dakinta.

   Jin an bude dakin yasa Aunty Hajara dago kanta tana duban bakin kofar,ganin Aunty Rabi’atu yasa ta mayar da kanta tana jin daci a zuciyarta.

   Hangota tayi zaune a gefen gado tayi tagumi tare da lulawa duniyar tunani.

A hankali ta zauna kusa da ita,saida ta dafa kafadarta kafin ta fara magana kamar haka “A matsayinki na mace kinsan yadda zaki sanar da mai gidanki wannan maganar,ki Kuma bashi shawarar yadda ya kamata yayi dan ganin wannan sirri bai fita ba”

    Saida ta mike tsaye ta nufi hanyar fita daga dakin kafin ta Kara da cewa “Ki sani Seeyerma marainiya ce tana bukatar taimakon ku,sannan mu kanmu bamu San me hakan yake nifi ba sai Allah shikadai ne masanin komai,idan har rayuwar Seeyerma ta samu matsala to tabbas ku za’a zarga sannan duniya ta zage ku akan kun kasa tarbiyantar da ita,Dan haka ku hanzarta samo mafita tun kafin mutanen da muka tara su fahimci abinda yake faruwa”tana Kai karshen zancenta ta fita daga dakin.

   Itama Aunty Hajara tashi tayi tabi bayanta.a tare suka Kara komawa part din Mama.

A kitchen suka hangota tana aiki ita da kawayenta.

Ganin sun shigo kamar ransu a bace yake yasa ta kallesu tana cewa “ya akayi?ko akwai matsala ne?”.

Ba Wanda ya samu damar bata amsa a cikinsu.sai juyawa Suka yi suka fita,da sauri ta aje ludayin hannunta tabi bayansu.bedroom dinta Suka nufa tana biye da su.suna shiga ta sakama kofar key tana kallonsu.

       “Kunshigo ranku a bace Ina ta magana kunyiman shiru a a Wai ya kuke so ayi ne?”cike da bacin rai tayi maganar.

   Aunty Hajara ta fara zama bakin gadon kafin suma suka zauna.

     Shiru ta ratsa wurin na wasu dakika kafin dakyar Aunty Hajara ta bude bakinta Wanda take ji yayimata nauyi ta ce “Maman maman Faruk Seeyerma ce…….”sai Kuma tayi shiru.

     Jin tayi shiru yasa Mama ta sake cewa “Dan Allah ku sanar da ni abinda yake faruwa?kun saka ni a rudani”?.

    Aunty Rabi’atu ce tayi karfin halin cewa “Seeyerma ce aka gano tana dauke da ciki”.

 Cike da tsoro mama ta mike tsaye tana binsu da wani kallo mai kunshe da wani abu.

“Garin ya haka ta faru?”

     Cike da jimami Aunty Hajara ta ce ” *kaddarar rayuwa ce* (book din Ummu maher),tabbas shi Allah ba’a yimasa wayo mun rufe wani sirri ne baya da wata biyu,sai dai kash yanzu sirrin ya bude a tsakiyar makiyanmu,a daidai lokacin da kunya zata rufemu”.dukansu shiru sukayi kowa da tunanin da yake yi.

Can andau tsawon lokaci Mama ta sake tambayar su da cewa “kun tambayeta Wanda tayi Mata cikin?”

   “Ita Yarinyar bata da masaniyar cikin dake jikinta,Amma kin ji abinda ya faru……….”Anan Aunty  ta sanar da ita cewa Muhseen ne .

Ita kanta Mama ta girgiza da jin wannan sirin.inda ta Kara jinjina girman mahaaliccinmu domin shi kadaine masanin gobe.

   Da sauri Mama ta danna Kiran wayar Faruk,ba tare da bata lokaci ba yayi picking.

Jin alamun muryarta cikin wani yanayi yayi saurin cewa “Mama lafiya?ko wani ya bata ranki?

A gajarce ta ce “ka same ni a bedroom dina yanzu”ta katse Kiran tana faman yawo a tsakiyar dakin.

Shiko Faruk sororo yayi Yana bin wayar da kallo.kallon su Jabeer yayi Wanda suke zaune suna kallon masu jera Kaya a part din da za’a kawo amaren.

Baice uffan ba ya mike ta fice Yana ta sauri tamkar Wanda zai kifa.ba Wanda yayi yunkurin binshi sai mayar da hankalinsu suka yi ga masu aikin.

    Dukda kasancewar part din cike yake,Amma haka yayita ratsa mutanen har yakai kofar dakin.

A hankali ya tura bakinshi dauke da sallama.

Ba Wanda ya samu damar amsawa sai Aunty Rabi’atu ce tayi karfin halin amsawa itama murya can kasa.

   Ganin sunyi jugum-jugum yasa ya ji gabanshi ya fadi,Dan tabbas yasan akwai abinda ke faruwa.

Cikin sanyin murya Mama ta kalli Faruk tana cewa “Faruk ka ji wata kaddarar da take tunkaromu, Seeyerma ce ke dauke da ciki”.

  Cikin dimaucewa Faruk ya zabura Yana cewa “ciki Kuma mama? Seeyerma dai wacce na sani take dauke da ciki? Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un Allah ya Allah mun tuba,ya Allah ka fitar da mu kunyar maraicin wannan yarinya”.sosai muryar shi tayi rauni tamkar Wanda yake Shirin fasa kuka.

     

    Seeyerma kuwa tunda ta fita ta nufi part din Unlce Yusuf Dan tasan su Khadija suna can.

Daidai ta kusan shiga wayar Aunty Rukayya dake hannunta ta sake yin kara,alamun Kira ya shigo.cike da farinciki ta daga Kiran ganin sunan Ya Muhseen ne.

   Bayan gidan ta nufa,hango wani bishiya tayi direct ta nufi can tana faman murmushi.

Cikin muryarta mai dadin sauraro tayi sallama.

   Gyara konciyar shi yayi jin ita ce ta daga.

   Cike da kasala yace “Dear bara na Kira ki Vedio call”

Harzai katse jin tayi shiru bata ce komai ba ya sake cewa “kin ji Dear inaso na ganki ne,nasan kin Kara kyau”.

“Uhmmm kadai ta iya cewa”ya katse Kiran.

Vedio call din ya kirata.saida ya zauna akan wata Yar kujera data gani kafin ta daga Kiran.

Tana dagawa ya fara cin karo da kyakykyawar fuskarta da sauri ya zaro manyan idanuwan shi waje Yana Kara kallanta.

   Itako dariya ya bata ganin yadda yayi,darawa tayi har saida dumple dinta ya lotsa.

    Murya cike da tsoro ya ce “Dear yausha rabonki da kiyi period?”.

   Rufe idonta tayi da dayan hannunta tana jin kunyar tambayar da yayimata.a ranta ta ce Ashe shiyasa ake cewa wasu mazan Basu da kunya.

Ganin ta rufe fuskarta alamun ta ji kunya yasaka shi cewa “please tell me mana”jin yayi maganar cikin serious voice yasa ta ce “Nafi two months rabon da nayi”Dan ita harga Allah ta manta da batun wani period Dan irin bakar wahalar da take sha idan zata yi,shiyasa da taga Bata yi ba sai bata wani damuwa,Dan ita a ganinta ta huta da shan wahala.

    “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un”shi ne kalmar da taji ya furta, Sai ta katse Kiran.

   Wayar tabi da kallo tana tambayar kanta ko laifi tayi mai ne shiyasa ya kashe,a maimakon ya bari ta bashi hakuri.

    Itama sharewa tayi ta karasa part din inda anan ne za’ayimata kunshi da dilka.

  Tana shigowa falon gaba data Suka saka ihu suna Koda irin kyawun da tayi.ita dai bata cewa komai sai dai tayi Murmushi.

  Shiko Muhseen Yana katse Kiran ya fara kokarin Kiran nomber Aunty Hajara.su Kuma a daidai wannan lokacin sunyi shiru bamai cewa komai a cikin su sai faruk da yake sanar da su cewar “ya zama dole fa a wannan karon Hajiya Kaka tasan abinda ke faruwa,domin ni a ganina boyemata da muke yi baya da wani amfani,itace kadai idan ta yanke hukunci babu Wanda zai misalta shi,sannan ni a ganina wannan itace hanyar da zamu tarwatsa manufar su Hajiya Mariya da makarrabanta ta hanyar bawa Kaka shawarar ta hada Seeyerma da Muhseen aure”.

  Dukansu shiru sukayi suna Kara nazarin maganar Faruk.

     A karshe dai  shawarar shi suka dauka.

  Kowa ya koma wurin hidimar shi,Amma daka kalli fuskokinsu kasan akwai abinda yake faruwa.

Sai gaf da la’asar kafin aka kammalawa Seeyerma kunshi da dilka,sai kanta da Aunty Hindatu ta Kara gyaramata yayi gwanin kyau.kowa sai santin gashinta yake yi saboda kyanshi da santsinshi.

    Bayan la’asar kowa ya shirya cikin ankon doguwar rigar leshin,dinkin buba ne kalar leshin din ya dace da kalar fatar su.wacce suka dauko mai makeup haka duk ta tsaba masu kwalliya mai kyau da daukar ido.

Ras yan’matan suka fito kamar ka sace su ka gudu..

 A bangaren su Jabeer kuwa tun azahar suka kawo masu yin decretion Suka kawata holl din gwanin sha’awa.kama daga kujeru da kayan kwalliyar wurin komai kalar blue ne da pink.

     Ameerah ana bangaren Hajiya Mariya sai wannan iyayi take ki da kwatale Wai ita Amarya.kunshimai ita ta bayar da sitel din da za’ayimata.

 Ba laifi itama tayi kyau dukda su Seeyerma sun fita haske da doguwar fuska.

Karfe buyar aka fara fita wurin kamu,kama daga manya yan’mata da samarin estate din da baki,manyan ne kawai Basu je ba,sai Yan part din Kaka da wasunsu duk tsaffi ne.

Haka aka fara gudanar da kamu babu ango muhseen.wanda tun Bayan katse Kiran da yayi da Seeyerma take ta kokarin Kiran wayar Aunty Hajara Amma ya kasa samunta.haka ya hakura ya rungumi kaddarar shi,Amma ya tabbatar ciki ne a jikin Seeyermar shi,nan take ya ji Yana kaunar cikin dukda yaso ace suna da aure aka same shi,Amma Basu da yadda zasu yi da rubutacciyar kaddarar su.sai zuwa dare ya samu nutsuwa WhatsApp ya hau ganin Hindatu ta turomai Vedion da akayi na kamu.

Tunda ya fara kallon hankalin shi Yana Kan Seeyerma da take faman tikar rawa kamar wacce taje gidan gala.sosai abin ya bashi haushi ganin yadda samari suke ta yimata liki,rabinsu duk abokan su Faruk ne da Jabeer.baisan sadda yaja wani mugun tsaki ba Yana kife wayar a ranshi ya ce “lallai yarinyar nan ta raina ni da cikin nawa a jikinta take wannan rawar,sanadin ta zubarman da shi” .lebenshi na kasa ta kamo Yana cizawa tunawa da yayi irin wahalar da suka Sha daga shi har ita a wannan ranar musamman ma ita da harsaida aka yimata dinki.

   Hindatu ya Kira Yana cewa ta hadashi da Seeyerma.haka tayi ta dubawa bata ganta ba,Dan lokacin kusan karfe tara ne na dare.

  Seeyerma ko tana kitchen din Aunty Hajara tana dafa danwake,Dan harta konta ta tashi Jin wani mugun kwadayi Yana tasomata.

   Jin motsi a bayanta yasa tayi saurin juyawa.Aunty Aliya ce a tsaye jikin kofar tana karemata kallo.

   Da sauri ta mayar da hankalinta Kan tsame danwaken da take yi,saboda ita bata son irin wannan kallon da take yimata.

  A hankali Aunty Aliya ta karasa shigowa kitchen din tana tambayar ta meye take dafawa.

Cike da yarinta Seeyerma ta ce “Wallahi Aunty harna konta naji bazan iya bacci ba idan banci wannan danwaken ba,jiyama saida na ci,yanzu ganda nake so Kuma gashi na rasa inda ya Faruk yake nasan shi kadai zai iya sayoman”ta karasa fadar maganar daidai lokacin da take zuba yaji a ciki.sosai ta zanbada uban yaji Wanda yake ta faman kanshin tafannuwa.

  Ita dai Aunty Aliya bata ce komai ba ta fice daga kitchen din,tana rayawa a ranta wato Faruk shi ne ya dirkama yarinyar nan ciki,tunda gashi tace shi kadai ne zai iya sayomata ganda.lallai Faruk yaci amanarta wato haka zasu yimata,duk yadda taso su rike yarinyar nan da mutunci kasawa sukayi.

Wani murmushi naga tayi Wanda yake kunshe da manufofi da dama.kafin Naga ta shige wani daki a cikin part din.

   Around 10 pm su Uncle Yusuf ne da Aunty Hajara, Mama,sai Aunty Aliya a falon  Hajiya Kaka.dukansu sunyi cit suna sauraren bayanin da take korowa.

“Ni nasan idan kun boyeman to bazaku iya boyewa mahaaliccinmu ba,domin shi ne mafi sanin dukkan rayuwarmu, kunyi tunanin boyeman shi zai saka asirinku ya rufu ko?to ni bana zarginku da yin sakaci da tarbiyarta,domin kowanne bawa da irin tasa kaddarar,Dan Allah ku dauka wannan kaddara ce daga Allah mahaliccinmu”.

Saida tayi shiru bayan ta saka ballin goro a bakinta kafin ta ci gaba da cewa “Amma ku sani aure a tsakanin Maigida da Seeyerma b…………..?³¹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page