MAFARIN SO CHAPTER 8 KARSHE
MAFARIN SO CHAPTER 8 KARSHE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Washe garin ranar su Aunty Deejah suka dawo, su Rabi’ah na zaune falo, faɗa suke akan ita sai ya barta taje gidansu Amrah da Zahra, shi kuma yace sai dai ta bari ya kaita da Yamma, tun yana lallaɓata har ya koma musu faɗa, da yake mai hali bai fasawa🤣. Tana niyyar jifanshi da filon kujeta, ya kamota ya kwantar a jikinsa duk sai tayi lak’was.
Sallamar su Hayrah ne ta katsesu, da sauri ta zame jikinta daga nashi, duk suka tsaya suna kallon Rabi’ah kaman sabon abu, don basuyi zaton tazo gidan ba,
Hannu ta ware musu alaman su taho,
“what are uh waiting for? Come here”
Ai da gudu suka taho rungumeta, duk suka mak’aleta suna murna, Ahmad ya rungume hannuwansa yana kallonsu,
“Aunty kaɗai kuka sani ko?”
Suka saketa, shima suka rungumeshi suna musu sannu da zuwa, sai ga su Aunty Deejah sun shigo, itama tasha mamakin ganinsu Rabi’ah, duk ta taga gidan a buɗe.+
Yayanta ya shigo, shima tsayawa yayi yana kallonta, daga fuskarshi zaka iya gane tsantsar farin cikin daya shiga na ganinta, yana son mata magana anma ya kasa, ya wuce su kawai,
“Sannu da dawowa Yayana”
“Yauwah” ya faɗa ba yabo ba fallasa, ba tare daya tsaya ba.
Su Aunty Deejah daman haka akeso, da mamakin Rabi’ah sai taga ta sakar mata fuska.
“Amaren Yola saukar yaushe?”
Itama ta ɗan saki fuskarta,
“kusan sati ɗaya kenan, munzo bamu iske ku ba”
“bak’i sunma zama en gida ashe”
“eeh fa, bamusan da dawowarku yau ba, ku huta Aunty bara na shiga kitchen don yanzu kune bak’in”
Ta sakar mata murmushi, sannan itama tabi bayan Yayan Rabi’ah, su Hairah kam na mak’ale da Ahmad sunata zuba mishi fira.
Sai da yaga Rabi’ah ta nufi kitchen sannan ya bita don ya taimaka mata.
Tare sukayi girkin da Ahmad cikin annashuwa kaman basu ba, da yake duk a gajiye suke saita kaima kowa ɗakinshi, daman ta saba sanda take gidan ita take kaima Yayanta, tare suka tafi da Ahmad ya tayata ɗaukan wasu kayan.
Yana kwance kanshi na kallon silin, faran-faran ya amsa gaisuwar Ahmad da sannu da zuwan da yake mishi, har suka ɗan taɓa fira, anma ita sannu da zuwan data mishi dak’yar ma ya ansa.
Tun tana daurewa, batasan sanda kuka ya k’wace mata ba, da duk’e anan wurin ta fasa mishi kuka, ganin hakan Ahmad ya fita ya basu wuri.
“don Allah Yayana kayi hak’uri, ka yafemun zan iya jurar komai anma banda fushinka, kai kaɗaine gatana, don Allah ka yafemun, na anshi duk wani hukunci da kamun, a shirye nake dana k’ara ɗaukar wani indai zaka yafemun”