ZANEN DUTSE CHAPTER 1 BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 1 BY AISHA-SHAFIEE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk da girma irin na gidan sarautar KIYARI, babu lungu da sak’on da zaka kurd’a sautin wak’ar da ake gudanarwa daga can wajen kamun bikin bai shiga kunnenka ba, sannan ga mutane nan birjik! Tun daga bayi na cikin masarautar har zuwa tarin jama’ar gari da suke d’id’ikowa don gane wa idonsu shahararren bikin da aka fara gudanarwa a yau.+
Biki na gimbiya kuma ‘ya mace ta biyu a gurin mai martaba ‘Ahmad Uba Kamsusi’, Haka nan kuma biki na farko da aka fara gudanarwa a gidan sarautar tun bayan zamanin da mai martaba ya gaji mahaifinsa.
Duk inda zaka duba ko ka kalla ado ne na k’awa anyi shi birjik cikin nau’i kala-kala don burge al’umma da kuma dangin ango wanda suma suka kasance jinin sarauta daga garin Sakkwato. Ba wai barin mutane ake su k’arasa can inda ake gudanar da
Kamun ba, amma duk da haka saboda wadata abubuwa kai ba zaka ce ba ko’ina ake bikin ba, don kalolin abinci yawo kawai suke tsakanin mutane kowa na zab’ar ra’ayinsa yaci ya cika cikinsa harda guzurin na gida ma, sannan kuma kid’an daya karad’e ilahirin masarautar ma ya k’ara zirga-zirga da kuma hada-hadar mutane.
A cikin wannan hayaniyar Maijidda na can tsaye ita da Suraj daga bayan hanyar da zata kai ka shamaki inda babu wulgawar mutane sosai. Hannunta rik’e yake da wani kwando mai cike da wasu k’anana abubuwa masu kyalli sai juya shi take cikin yatsunta.
“Dan Allah ki gaya min mana, me Baddon tace da kika gaya mata?”
Muryarsa ta tambayeta a hankali amma cike da zumud’i. Ta d’an cije lebb’enta kad’an tana kallonsa sannan tace.
“Me kake tunanin zata ce?”
“Wallahi ban sani ba tunda kinga ai ba saninta nayi ai sosai ba, kawai ki yanke dogon zancen ki fad’a min ko zuciyata ta nutsu…”
Girarta biyu ta had’e alamun rashin fahimtarsa.
“To meye duk ka wani tashi hankalinka ka san dai ai ba zaginka zata yi ba ko?”
Maganar tasa shi dariyar da bai shirya ba a lokaci guda.
“Zagi kuma Jidda? Wa yake zancensa anan? Kawai fatana Allah yasa ta amince dani ne.”
Jin haka yasa ta juya ga barin kallonsa sannan ta d’anyi murmushi kad’an tace.
“Ai kaima ka san da tace wani abu da ba zan tsaya anan ina sake maka magana ba.”
“Allah da gaske kike? Bata ce miki komai akaina ba?”
Wannan rashin fahimtar ya sake dawowa kan fuskarta, ta juyo ta kalle shi.
“Me kake tunani zata ce? ni fa kawai tace min ne ta san Babanka ya tab’a aiki a b’angaren Fulani kafin ya koma wajen mai martaba, bayan haka bata ce komai ba.”
“Haka ne…” Ya fad’a yana gyada kai.
“… zata sanshi, Baddo ai ta dad’e a masarautar nan, ina jin tun farkon zamanin Sarki Uba take ko?”
Ta d’aga kanta a hankali.
“Na san dai tun mai martaba na yanzu bai yi aure ba suka zo ita da mamanta.”
Ya sake gyad’a kansa sannan yayi shiru kuma, zuciyar Jidda ta d’an matse kad’an, ta zata a lokacin ko zaiyi mata zancen turo iyayensa ko kuma wata maganar auren da zata kaisu ga mataki na gaba kamar yadda ta dad’e tana sak’awa a zuciyarta amma kuma baice komai ba.
STORY CONTINUES BELOW
Yatsun hannunta na dama na kanannad’e cikin hannun kwandon ta d’an b’ata rai, Allah ya sani zuciyarta tana bashi wata irin yarda tun daga lokacin da ta fara saninsa kafin ma yace yana sonta, amma kwanan nan yanayin mu’amalarsu yana yawan zana mata ayar tambaya a tunaninta… Bata jin kuma zata jure hakan gwara ta fito kiri-kiri ta tambaye shi me yake nufi game da ita, amma zata bashi lokaci dai tukunna.
“Jidda.”
Muryarsa a hankali ta katse tunaninta, ta d’ago da sauri ta kalle shi sannan a lokaci guda tunaninta ya wargaje saboda irin kallon da yake mata, ta san Suraj yana da kyau kuma saboda haka ma take sonsa ko don ace saurayinta na da kyau… Don irin kyan nan ne da baya cikin k’abilar Hausa-Fulani illa irin jinsinsa na Shuwa-arab, amma me yasa kullum take k’ara ganin kyan nasa ne?1
“Kin san me na taho miki dashi?”
Ya tambaya shima yana kallonta, sai ta sake k’ank’ame kwandon hannunta tana murmushi alamun dad’i kafin tace.
“Kace min fura.”
Ya girgiza kansa.
“Tanderi?”
Ya sake girgiza kansa.
“Awara? Dan Allah ya zama Awara?”
Ta fad’a tana langab’ar da kai had’e da k’ank’ance ido, hakan yasa shi dariya mai zurfi yana girgiza kai kafin ya mik’o mata ledar hannunsa.
“Allah ya amsa miki, Awara ce mai zafi ina zuwa gida na tarar Mama tayi.”
Ta karb’a da hannun dama ta bud’e, idanunta suka haska da kyallin murna da godiya sannan ta d’ago ta kalle shi.
“Jidda!”
Muryar Jamila data karyo kwana ta katse abinda shi da ita ke shirin fad’a.
“Yanzu tun dazu kina nan? Hankalin Baddo ya tashi an kusa gama wankan amarya, Jakadiya Babba sai fad’a take ba’a kawo kyallin ba.”
“Kinga kije kawai ba matsala, Gobe zan shigo ai insha Allah.”
Cewar Suraj sanda Jamilan ta k’araso inda suke tsaye.
“To shikenan, Nagode, Nagoode!”
Ta fad’a da k’aton murmushi tana sake damk’e ledarta.
Shima ya mata murmushin, sannan ya gaida Jamila da ka, kafin ya juya ya tafi.
“Allah zaki ci fad’an Baddo, da kika san wajensa zaki tsaya ba sai ki kawo mata aiken ba tukunna.”
Jin haka yasa ta d’an b’ata rai tace.
“Ni ai bata ce min yanzu za’ayi amfani dashi ba shi yasa da na ganshi na tsaya…”
Sai kuma tayi murmushi, ta nuno mata ledar hannunta game da d’aga gira.
“Kin san me? Awara ya kawo min.”
Jamila ta ja tsakin ta bata shirya masa ba kafin ta fizge kwandon hannunta tayi gaba.
“Wallahi abinda kike baya kyautuwa Jidda, nasha gaya miki da ace a wajen wata kike ba Baddo ba da tuni kinsa an dad’e da korar mu daga gidan nan, yanzu in banda sh*g*n kwad’ayi duk abinci da yake yawo a gidan nan me zaki yi da wata awara…”
Tana magana Jiddan na biye da ita, jinta kawai take yi don daga fad’anta har na Baddon ba wanda zai dameta, suna gamawa zata sami waje taci awararta, bata san kuma me ta manta ba bayan hakan.
“… Na rasa waye ya shiga kwakwalwarki ya goge miki sanin cewa a duniyar nan ba kowa ake yarda dashi ba, don wallahi bani ba na san ko ita Baddon ba son wannan Suraj d’in take ba.”
“Wai yaushe za’a daina zancen nan ne? tunda nace ni ina sonshi ba shikenan ba.”
Ta fad’a cikin kunkuni sanda dogarawan dake tsaye suka basu damar shiga babban soron da zai sada ka da kwaryar gidan sarautar inda ake gudanar da bikin. Jamila ta harare ta da gefen ido sannan ta girgiza kanta kawai.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan tarin adon dake wajen idonka zai gano maka taron mutane birjik! Wand’anda ke zazzaune akan wasu tausasan dardumai kashi-kashi da aka tsara maimakon tebura, kowa cikin kwalliya sannan mafi yawansu rik’e da waya suna d’aukar wankan amaryar da ake gudanarwa daga tsakiyarsu, kan wani d’an dandamali da aka fitar masa da rariya musamman saboda bikin.
Amaryar, Gimbiya Aisha Ahmad Kamsusi, na zaune kan wani sabon turmi cikin shigar wata farar doguwar riga da lullubin farin mayafi yayin da tsofaffi dangin iyayenta ke ta kwara mata ruwan farar Humra suna zubo tarin addu’o’insu wanda ya had’e da yanayin wak’ar wajen ta yaren al’adarsu da aka kunna.
Jidda na iya hango fuskar Amaryar ta tsakanin matan dake kanta, ta sunkuyar da kai sai sheshek’ar kuka take, wani zaice ba itace mai d’agawar kan nan da zuba tarin rashin mutunci ga bayin masarautar ba kamar mahaifiyarta, Fulani Hafsatu, hamshakiyar uwargidan Sarki mai cika da izza.!
Allah ya sani tun zuwanta masarautar ranta baya son matar nan, saboda bak’in halinta da kuma bautar da kakarta keyi a k’ark’ashinta, bautar da tun kafin rasuwar mahaifiyarta ba irin k’ok’arin da ba’a yi akan ta bar gidan sarautar ba amma fafur Baddon tak’i, a cewarta yadda mahaifiyarta ta mutu k’ark’ashin kulawar masarautar haka itama zata koma ga Allah anan.
“Jidda tun d’azu muke nemanki, ina kika shiga?”
Muryar Sadiya ta fad’a sanda ta dafo ta daga baya.
“Wallahi Baddo ce ta aike ni can wajen Magajiya na karbo mata sak’o.” Ta bata amsa sanda Sadiyan ta tsaya kusa da ita.
“Taho muje ki zauna tare damu mana, ga inda muke zaune can ana ta hoto a wayoyin su Amina.”
Jidda ta juya ta kalli can inda ta nuno mata, darduma ce guda ta ‘yanmata irinsu ‘ya’ya ko jikokin bayin masarautar har da wadanda bata fiye ganinsu ba, dukkaninsu sun sha ado babu mai babanta su da sauran ‘yan bikin, don haka ne ma duk irin abincin da aka ajiye a kowacce darduma suma akwai a tasu, sai hayaniya suke yi suna d’aukan hotunan kamar yadda Sadiyan ta fad’a. Zuciyarta ta d’an had’e kad’an, taji zata so ace itama tana cikinsu ana hirar, amma sanin abinda zai biyo baya yasa ta girgiza kanta.
“Kin san bana son rashin mutuncin k’awayen nan naki Sadiya, don haka kije kawai.”
“Haba Jidda, wai ta yaya ba zaki manta komai bane ba, wallahi yanzu babu me miki ko kallon banza tunda kun riga kun fitar da raini.”
Ta sake girgiza kanta.
“Allah kije kawai, tare da Jamila ma fa nake, ta tafi kaiwa Baddo sak’on yanzu zaki ga ta dawo.”
Daga yanayin Sadiyan bata so haka ba, amma sanin Jiddan ba canja ra’ayi zata yi ba yasa ta gyad’a kai tace.
“Toh shikenan sai mun had’u a cikin gida.”
Bayan ta juya, Jidda ta sake hangar wajen ‘yanmatan a karo na biyu kafin kuma ta
shiga neman Jamila ta cikin tarin hayaniya da kid’an dake tashi a wajen, sai dai duk irin hangen da take yi ba Jamila ba alamarta balle kuma uwa-uba Baddon da sune masu gudanar da tafiyar bikin.
Saboda haka ta juya don neman waje taci awararta, ganin kusan ko’ina da wulgawar mutane yasa ta nufi hanyar fita ta k’ofar yamma inda zata kaika ‘Cikin Gida’ ma’ana b’angaren iyalan Sarki da kuma Turaka da fadarsa ta zaman hutawa, sai dai kafin ta kai ga fita wani daga cikin masu rabon abincin yazo wucewa da katan-katan d’in ruwa don haka ta tsaya rok’arsa ya bata d’aya.
Kafin ya farka katan d’in idonta ya hangi sanda ake zubawa Amaryar wannan kyallin da ta karbo yayin da wani tartsasin wuta daga cikin wasu abubuwa da wasu inyamurai suka zo suka kafa tun safe ya shiga baibaye ilahirin wajen. Gud’a da tarin hayaniya ta sake rud’ewa, wajen yayi kyau sosai taji ya burge ta kuma ta san zata iya ganin Baddon yanzu don a matsayinta na Babbar Jakadiya dole tana wajen amma sai ta yanke shawara fara cin awararta tukunna don haka ta karb’i ruwan ta fita.
STORY CONTINUES BELOW
A bayan wani gini cikin tamfatsesen tsakar gidan ta samu waje ta zauna, anan d’in ma mutane ne ke ta zirga-zirga daga wajen bikin zuwa cikin b’angaren Fulani (mahaifiyar Amaryar) amma inda ta zauna saman tudun wani tanki ya shiga daga d’an lungu saboda haka ba kowa ne zai ganta ba sai hankali yaje wajen.
Ta bud’e awarar ta fara ci hankalinta a kwance, hannunta d’aya na wasa da ‘Fullo’ dake rataye a wuyanta kamar sark’a. A hankali kamar koyaushe idan ta kad’aita ita kad’ai kalaman mahaifiyarta na k’arshe suka shiga yawo a kwakwalwarta.
‘Bana son ki koma wajen dangin mahaifinki Jidda, nafi son kije ki zauna tare da Baddo, ba wai don ina son zaman inda take ba sai don ko ba komai in kina gabanta na san zaki tashi da irin tarbiyar data bani, watak’il ma wannan halin naki ya gyaru saboda wata k’addarar…’
Ta rufe idonta a hankali tana tauna wadda ke bakinta, amon muryar rad’au yake amsawa a kunnenta kamar yanzu aka yi ta, don tana d’aya daga cikin doguwar magana ta k’arshe da mahaifiyar tata tayi mata kafin ciwo yaci k’arfinta ya zamo harshenta ya nad’e har ta daina iya magana kwata-kwata.
A wannan ranar ne kuma ta bata ‘Fullo’ d’an zagayayyen dunk’ulen zinaren data mallaka daga wajen mahaifinta, tace mata mahaifina ya bata shi ne a ranar da aka saka ranar aurensu, don haka ta sanya masa sunan ‘Fullo’ wanda ma’anarsa shine ‘Baiko’ da fulatanci.
Bata san wace irin k’addara mahaifiyarta take nufi ba, amma Allah ya sani ita kanta ta matsu k’addarar ta k’araso ta canja akalar rayuwarta don ko kad’an ba jin dad’in zaman masarautar take ba, daga Baddo har Jamila hankalinsu yafi karkata ga aikinsu fiye da ita, shi yasa babu wayewar garin Allahn da bata kewar mahaifiyarta da kuma rayuwarta ta baya…
“Kin tabbata nan kuwa tace?”
Muryar wata mata data fito daga d’an nesa da bayan tankin yasa tayi saurin bud’e ido, tunaninta ya katse.
“Wallahi nan gurin tace Ladi, bakina da nata fa tayi min bayani, tace daidai bayan ginin nan malamin daya bada aikin yayi kwatance kuma in ya wuce gobe ba’a binne ba aikin ya lalace, to kema ai kin san kuwa ba zan kuskure ba, duba dai kiga ba kowa ko?”
Ba tare da ta san dalili ba, Jidda ta nad’e k’afafunta zuwa kan tudun sanda k’arar takun matar ya shiga kunnenta, taji alamun tayi ‘yan dube-dube kafin tace.
“Babu kowa, kinga dan Allah muyi sauri mu hak’a mu bar wajen nan, bana son wani ya gan mu.”
“Ki kwantar da hankalinki Ladi, nace miki babu abinda zai faru ba mai ganinmu, kudinki kuma cas! Zaki kwana dasu a hannu don Jakadiya bata da sab’a alk’awari.”
K’arar hak’a ta shiga kunnen Jidda kafin wadda aka kira da Ladin ta sake magana.
“Hankalina ne bai kwanta ba jin yawan kud’in nan da za’a bamu, tunani nake in babu hatsari a cikin aikin nan Fulani ba zata fitar da kudi haka ba.”
D’aya muryar ta ja tsaki.
“Ke fa matsalarki gidadanci, to wallahi Jakadiya ta tabbatar mun in muka bada had’in kai fin haka ma zamu iya samu, don Fulani babu abinda take so illa ganin k’arshen MADAKI, kuma ni kaina shaidace zata iya komai akan hakan don wannan had’in da kike gani tace tun daga can k’asar Gabon aka karb’o mata shi.”
Jidda ta had’iye yawu, jin cewa asiri suke binnewa a wannan lokacin kuma cikin umarnin Fulani da Jakadiya, tukunna ma wacce daga cikin Jakadiyar? Ba dai Baddonta ba? Ta sake had’iye wani yawun tare da ragowar awararta sanda muryarsu ta cigaba da magana k’asa-kasa.
“Kin san jikina na bani Fulani zata sami abinda take so wannan karon, saboda kinga na san tasa anyi masa na kiranye mai k’arfi, don Jakadiya tace dole ne zai dawo gida wannan karon sai dai ba’a san yaushe ba. Sannan wannan kuma tace daya sako k’afarsa cikin gidan nan ba zai sake mararin komawa ba, wanda za’a binne wani satin kuma a cikin lambun bayan turakar mai martaba shi kuma na k’ulle bakinsa ne, tace in har aka same shi, to bai fa isa ya sake mararin komai ba bayan umarnin Fulanin.”
“Cabd’ijam!” Cewar Ladin.
“Wai yanzu duk taurin kai irin na Madaki shine zai sauko har ya dinga biyewa Fulani? Anya kuwa Hadiza? Abinda ba’a same shi tun da ba kina ganin zai yiwu yanzu?”
Hadizan ta sake jan tsaki.
“Me ko zai hana shi yiwuwa? Aikin baya da aka kwantar dashi jinya har ta sami wad’annan kud’ad’en ke kika hana shi yiwuwa? Balle yanzu da aka sami wannan garantin malamin… Ance shekararsa saba’in kenan yana wannan aikin kuma ko sau d’aya bai tab’a bada maganin da bai ci ba.”