KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 11 KARSHE BY ayshay bee

KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 11 KARSHE BY ayshay bee

 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kallo ta bi dashi cike da mamakin abinda ya Zo ma ta dashi, shawaranta fa ya ke nema gsky she can’t believe it.  “Ke fa na ke saurare ya tunasar da ita”

“Why not ka raba kudin Kashi uku” ta fada tana Kallon reaction in shi.

“Wai miye kike ta kallo na”

“Allah hubbie ba zan boye maka ba ko am suprise ne”

“Why are you suprise”

  “Wasu mazan fa ko da wasa ba sa Bari Matan su su San karuwan su fa ballan tana Kuma neman shawarar su”

Murmushi ya saki sannan ya ce “kin San me?” Girgiza mishi Kai tayi.

“We are building a family so Dole na yi shawara da ke domin duk abinda ya same ni ya same ki ne ke da Ya’ya’n da Zaki haifa min” ajiyan zuciya ya yi ita ko ta yi jim tana Kallon shi “so Dole ke ce abokiyar shawara ta” ya cigaba “Its our benefit ko ha Haka ba”

“Hakane” ta amsa

“So stop wondering Ina jinki”

  “Ehmm as i was saying ka raba Kashi uku, Daya business za a nema a fara komai a rayuwa ya na bukatar plan sbd gaba are hangowa ba yanzu ba, profit a bude separate account a dinga tarawa believe me tym in da nauyin yara zai hau kanmu za suyi amfani wurin bukatun yaran”. Gyade Kai yayi sannan yace “shawarar na yayi Fateema Kuma hakan zai sa mu ga riban kudin da muke tarawan Nan gaba”

“Yauwa toh na biyun Kuma gidan marayu, asibitoci da prisons ya kamata akai taimako, ka San ance abinda ka ba ma wani shine na ka ranar lahira mu tunda Allah ya hore Mana sai mu taimaka musu, you have no idea wani irin ceton rai za kayi hubbie hakan zai Kara maka cigaban rayuwa ma gabadaya”

“Gsky kina da tunani me kyau shi fa ya sa aka ce shawarar Mata abun dubawa ne, wannan Abu ne Mai kyau da yakama ta na fara tun tuni but Kinga kwata kwata na shagala, don in kin banni kadara Zan siya da kudaden Nan wlh Ashe alkhairi ya sa nazo neman shawara gunki”. Murmushin alfarma ta saki “hakane hubbie Daman Dan Adam Yana bukatar tunatarwa a koda yaushe shi ma ya sa shawaran ke da kyau ai”

  “Na ukun fa hajiyata?” Hararan shi tayi sannan ta hade Rai “na tsufa ne da za ka ce min Hajiya”

“Au sai ka tsufa ake ce ma hakan?”

“To ba Babban Mata ake cewa haka ba” ta fada cike da shagwaba.

“To sorry my baby”

Tabe baki tayi “sai dai kace wata Yar tsana”

Girgiza Kai yayi Yana fadin “Diva ba ki dai da dama”

“Toh ka baza ka bani hakuri ba?” Ta fadi hade da turo bakin na ta da ya riga ya zame ma ta jiki.

“Ke dai wlh Yar rigima ce Kuma ki maida bakin Nan naki kafin in yi maganin shi” ba shiri ta koma ta saki fuska don ta San hali yanzu ya saka ta a wani hali na tunani…

“Yauwa ka na ji ba su Ammi da Abbah za ka yiwa amfani dashi, they will proud and za su sa ma ka albarka ka San addu’an iyaye Kan ya’yan’su”

“Diva me su Abbah su ke bukata, Alhmdlh Allah ya hore musu komai” ya fada cike da mamaki.

Girgiza Kai tayi sannan ta fahimce shi sosai “Aa Hubbie hakin su ne ko suna dashi ya kamata ka sauke, Abu ne ma da ya kamata ko da ko Allah ya hore mu su ba ma su kadai ba har ma sauran family members in akwai kyautatawa ko Dan a karfafa zumunci”

Ajiyan zuciya yayi “Shawaran ki yayi Diva sosai na ji dadin shi, Allah ya Kara kaifin basira, ya bar Miki ni, ya bamu ya’ya’ masu albarka”

“Ameen” ta fadi tana dariya hade da rufe idanuwan ta.

“Wai ke fa da gaske kunya ta kike ji ko?” Gyade mishi Kai tayi still idonta a rufe tana sunne Kai kasa.

Shaking head in shi yayi sannan ya ce “You are not serious Allah, Allah ya shirya min ke, haka yaran za su Zo ana Jin kunyan babansu?”

Tsuke baki tayi sannan tace “yanda fa kake maganan yaran Nan sai kace gobe xa su xo gabadaya”

“Indai da rai da lfy ai abin kaman gobe ne ke dai kawai ki rokon Mana Allah masu albarka, ko baki son su ne?” Da sauri ta dago Kai ta kalle shi cike da mamaki.

“Ai naga kaman ba ki damu ba ne saboda reactions inki in nayi maganan su”

“With time” ta fada tana lumshe ido sannan ta kwantar da kanta Kan cinyan shi.

Gashin kanta da ya Sha kitso ya fara shafawa zuwa fuskan ta. Firgigit, kaman ya tuno abu ya tsaya “keh kinsan me?”

  “No no no” ta amsa kasa kasa

“Ba ki taba ce min kina Sona ba”

  “Kai hubbie mana”

“Bawani yarinya na ki wayan sai kin fada min”

“Allah hubbie fa ranar fa na fada maka a Zaria” ta fadi cike da shagwaba.

“Ba da bakin ki ka fada ba ni Kuma so nake na ji kin furta so can you please save us and say it?”

“Hubieeeee” ta fada tana Jan sunan.

“Kinga dagani ni tunda ba Zaki fada ba inda abin yi” mikewa yayi ya daure fuska ya fada feigning hurt.

“Ni fa bance ma ka Bazan fada ba”

Tabe baki yayi hade da shrugging shoulders in shi “as you wish”

“To ka zauna Mana hubbie sai in fada”

“Ni Zaki Bata min lokaci” tafiya ya fara yi.

Taku Daya biyu yayi na uku sai Jin mutum yayi a baya shi, rungume shi kankam ta yi, a hankali ta fada “I love you very much hubbie, Ina son ka sosai” da sauri ya juyo da ita ta gaba suna fuskan tan juna. For the first time ta yi juriyan hada ido dashi, a idon nashi ta gama karantar komai game da ita ba ta da haufi akan son da hubbien nata ya ke Mata, “are you sure?”

Ya fada Yana Kallon cikin idon ta still yayin da su ke kokarin aikawa junan su sakonni. Kai ta gyade mishi, at that moment zuciyoyin su sun gama aminta da kaunar junansu da ya riga ya fito baro baro, jinta su ke a kowani Bari na jikin su yana yawo, there is no doubt ba za su iya rayuwa ba tare da juna ba, Daman can they are created for each other kawai akasin fahimta ne.

“Ina sonki fiye da tunaninki Fateema” ya fada kafin ya rungume ta Kam Kam “You are such a blessing in my life Diva”

“I love you more than you love me hubbie, in ba Kai ba sai rijiya, I can’t do without you”

“Ehm ehm haka matar tawa ta iya kalamai? Kar ki damu ba Zaki fada rijiyan ba ma am already yours remember?”

Gyade Kai tayi ta boye fuskan ta a kirjin shi cike da kunya dan ba ta ma San ta fadi maganan ba sai da ya fito ta iya releasing.

“Haba Yar soyayya ta wani Kuma kunya bayan an gama kashe ni da kalamai, come on be free am ur husband”

Dago fuskan ta ya fara kokarin yi tana noke wa da kyar ya rabo fuskan da kirjin shi Yana Kallon ta Amma ta rufe ido kyam kyam, lips in Shi ya Kai Kan idon nata yayi pecking insu a hankali har ya gangaro Kan lips inta.

             Light fades

8:30 pm dai dai ya dauko ta daga gidan Maman khalipha, yau a can su ka wunin ma ta ita da Nanah, coincidence har fareeda ma ta je ranar ai sun Sha hira.

Tare su ka je daukan su shi da Umar Amma kowa a motan su, wani aiki su kayi tun safe sai Daren su ka samu suka gama, ko da su ka Isa fareeda har ta tafi while Zahrau ko har ta yi bacci.

Still sai da su ka taba hira da Salim kaman ba tare su ka wuni ba sannan su ka Mike. Da kyar Maman khalipha ta taso ta tsabagen baccin da ke idon ta.

Gyangyadi kawai ta ke har su na karasa motan da kyar “Diva Wai lafiyan ki? Wannan wani irin bacci ne”

Hamma tayi sannan ta kalle shi “ni fa kaina har ciwo ya ke ka tashe ni in mun isa Gida” wani hamman ta Kara yi ko kafin ya Kara magana har ta koma baccin ta, da suka isa Gida ma da kyar ya samu ta tashi sai da ya rungume ta a jikin shi tukun su ka shiga gida.

“Ni Kam Allah wani baccin na ke ji hubbie bara in shiga sai kazo” carab ya riko hannun ta “ba ki Isa ba Allah hira za muyi” make kafada tayi.

“See what i buy for yo..” ko kafin ya karasa maganan ta yi wuf ta kwace roban ice cream in da ke hannun shi.

“Hey ba kwace wa zanyi ba so calm down ki Sha a hankali Amma fa ki tsaya muyi hira”

Gyade Kai tayi ta dinga Shan ice cream in kaman an Aiko ta lbr ma ya ke Bata Amma hankalin ta Bai wurin.

Sai ta shanye tas sannan ta dago ta kalle shi “Hubbie ba wani” girgiza ma ta Kai yayi “Bbu Kuma ma dai kinsan Bazan barki ki Sha dayawa ba ko?” Turo baki tayi shi ko ya daure fuske gudun ta samu wurin yi mishi rigima, ya ma dauke Kai gabadaya.

Yayi mamaki da ya ji ba ta Kara complain ba ko kunkunai bai ji tayi ba, sai dai ko da ya juya mutuniyar ta shi ta dade da yin nisa. Murmushi kawai yayi ya kashe wutan Falon da TV gabadya, daukan jarirai ya Mata har daki Amma ko motsin kirki ma Bata yi ba.Yau ta riga shi dawowa gida da wuri, driver ya sa ma ya je ya dauko ta.+

Gabadaya ba ta Jin dadin jikin ta, tafiya ma da kyar ta ke saboda ko motsa jiki Mai kyau ba ta son you. A daddafe ma ta samu ta yi Sallah, tana idar wa ko hijab ka sa cirewa tayi ta kwanta a wurin, ba wani dadewa tayi a asibitin ba Amma Kuma ta Sha wahala saboda ranar supervisor inta ya Zo ganin ta. Wani azzababben ciwon Kai ke damun ta duk a zaton ta na gajiya ne shiyasa ma ta ke so ta samu bacci ga uban yunwa da ke kwakulan cikin ta Amma ba za ma ta iya tashi ta yi girki ba.

Da kyar ta samu wani bacci Mai nauyi ya dauke ta ba ita ta farka sai da aka Kira La’asar, sai dai Kuma ciwon kan Nan ya na Nan ba inda ya je sai ma Kuma rawar dari da ta fara, Baiwar Allah tunanin ta Daya Aliyu in ya dawo ba ta tanadar mishi komai ba ba zai ji Dadi ba, wayanta ta lalubo ta Kira shi dab da za su shiga wani meeting akan wani tarzoma da su ke so su kwantar a wani jaha cikin south Africa, ana son  za a tura su wurin na one week, har yayi tunanin ya bari in sun fito ya Kira ta saboda ana jiran su sai Kuma zuciyan shi ta yi preferring akasin hakan, saurin daukan wayan yayi

“hello hubbie” ta fadi kasa kasa.

“Diva ya akayi?”

“Nace ba please in za ka dawo ko za ka saman Mana abinci a wani wuri, banji Dadi ba Zan iya ba” ba ma sai ta fada ba muryar ta kadai ya tabbatar mishi da bata Jin Dadi.

“Subhanallah sannu kinji, me ke damun ki?” A rude yayi maganan

“Ciwon Kai ne” ta amsa a sanyaye

“Sorry gashi Kuma ba yanzu Zan dawo ba Kar ki zauna da yunwa ba ra in Kira driver ya samo Miki yanzu ko”

Shiru tayi saboda maganan ma da kyar ta ke yi, ita ba ta yunwa ta ke ba Daman shi ta ke ji.

“Diva ko in ce ma Umar ya turo Miki Nanah ne”

“A a ka barta kawai” ta amsa sannan ta katse wayan.

Kokarin Kiran ta yake yi yaji ana mishi magana ya shigo. Ba musu ya shiga Amma kusa da Umar ya nema a hankali ya fada mishi abinda ya ke so ta yanda su biyu kawai za su ji.

SMS Umar ya tura wa Nanahn kawai.

  Haka ta daure da kyar ta Mike ta yiyo alwala Sallan ma dole a zaune ta yi shi saboda jirin da ta ke ji yana diban ta inta tsaya, kafin kace kabo gabadaya jikin ta ya rufe da zazzafan zazzabi sai karkarwa ta ke yi, hakuren ta har hadewa ya ke sai Kuma numfashin ta ya fara kokarin daukewa ganin abun bana kare bane ya sa ta fara kokarin Jan jiki ta lalubo wayanta. Kusan 3 missed call ta Mai Amma shiru kake ji.

Ta Kai mintu goma a hakan da kyar ta dinga struggling da numfashin ta a hakan ta tsinkayi Sallama a kofan first parlor insu an ya Kai sau uku ba ta da karfi da za ta iya amsa.

Karasowa ciki Nana tayi Jin shiru ya sa direct ta nufi dakin Zahraun, da gudu ta karasa gunta ganin yanda ta ke, gam Nanahn ta ririketa tana Jan numfashi, tsorta Nanahn tayi Jin jikin ta ma yayi zafi kaman wuta gashi jikin ta sai rawa ya ke.

Rasa ma abin yi tayi kawai ta dauko wayan ta ta dinga Kiran Umar shiru Bai dauka ba ta dauki wayan Zahrau ma ta dinga Kiran Aliyu still dai ba response gashi Zahrau sai Kara jigata ta ke wani tunani ya fado Mata da sauri ta yi dialling numban Maman khalipha “hello Anty Amina please in kina gida ki Zo Zahrau ba lafiya sosai” a gaggauce ta fadi maganan.

Ba ta iya Jin abinda ta ke fada daga dayan bangaren ba illa kawai “gani Nan zuwa” da ta jiyo ta yi ending call in.

Mintuna goma cikaku basu yi ba Maman khalipha ta shigo gidan a rude “Subhanallah Nanah ya Kika barta haka oya maza kiga” rikota tayi ta dayan side in Nanah ta talloba ta ita ma, Allah ya so da hijabi a jikin ta takalmi kawai su ka sa Mata su ka karasa da ita mota.

Da sauri Anty Aminan ke driving har su ka Isa asibitin su ma suna hanin condition inta su ka wuce da ita Emergency.

Sun samu sun daidaita numfashin na ta har ta samu bacci, two hours tayi ta na bacci an sa Mata drip Dr yayi suggesting a sa ma Mata abu Mai ruwa ruwa ta ci ko da su ka tmby ta kunu kawai tace za ta iya Sha, gabadaya Bata da appetite, Anty Amina ta sa aka kawo da ga gidan ta, ta dan Sha da dama sannan ta Sha magani zazzabi da ke jikin ta ya dan sassauta sai dai ciwon Kai. Tana gama Shan magani ta nemi ruwa ba musu Nanah ta Mika Mata ai ko tana gama Shan ruwa ta amayo komai da ke cikin ta, Nan take gabadaya ta galabaita.

Dai dai lokacin Aliyu, Umar da Salim su ka shiga sun lokacin an idar da  Sallan Asuba.

Sannu su ka dinga Mata da Kai ta iya amsa musu ba karamin Jin jiki ta ke ba, kasa jurewa Aliyu yayi ya karasa wurin nata har Kan gadon ya hau ya riko hannun ta “Diva me ya faru?” Kanta nuna mishi, fahimtan da yayi ba za ta iya magana ba yasa ya juyar da tambayan shi wurin su Nanah. Nanar ce ta mishi bayanin komai ta fada mishi tana ta Kiran su basu dauka ba “mun shiga meeting ne, Ina doctor in?”

“Ya fita, sun dauki jinin ta Wai za su Mata test”

“Okay bara na ganshi” ya ce sannan  ya fita dakin.

Nurse ya haduwa da za ta shigo dakin da magunguna, dakatar da ita yayi ya tambayeta Dr ta mishi kwatancen office in shi.

  Knocking office in yayi aka bashi izinin shiga, Murmushi doctor in yayi sannan ya nuna mishi wurin Zama “Bismillah” ya ce sannan ya Mika mishi hannu su ka gaisa.

“How may i help?”

  “Am here about the case of ur patient, Fateema maitama”

“Are you her husband?” Nodding Kai yayi

“Ma Sha Allah, perfect couples”

“Thank you”

“My pleasure, you know am just working on her case and planning on coming to the room after am done but its good that you are here”

Shiru Aliyu yayi Yana sauraran shi “Your wife is pregnant Mr Aliyu right?” Bude baki Aliyu yayi Yana Kallon shi cike da mamaki, happiness is written all over his face.

“So congratulations” Doctor in ya Kara fadi, murmushi kawai Aliyu ya ke yi ya ma kasa rufe baki balle yayi ma doctor in magana.

“Normally kasan Mata kala kala ne kowacce da irin laulayinta so ita nata naturally haka yake za ta dinga Sha wahala. Frankly speaking we can’t do anything to avoid it totally but we will try, akwai magungunan da za mu Mata prescribing more expecially na Hana amai da Kuma na zazzabi da sauransu, sai Kuma matsalan daukewan numfashi inaga wannan due to ciwon ta ne na asali coz a tests In da muka mata mun gano tana dauke da matsalan heart, sai Kuma treatment in BP da muke ganin ya kamata a daura ta a Kai kasan normally masu ciki suna fama da matsalan so sai ana hadawa da medical checkup before ta Kai time in da zata fara antenatal. Kuma za mu dan riketa zuwa gobe ko jibi haka saboda ta dan samu karfi, ehmmm ta dinga cin abinci masu gina jiki Kuma”

“To Likita mun gode sosai Kuma in Sha Allah za mu kiyaye” Aliyu ya amsa.

Ko da ya shiga dakin samun ta yayi ta na amai gabadaya ta galabaita, duk wani iri yaji da sauri ya karasa gurinta yana Mata sannu tana gama Aman ta samu bacci.

“Oh wannan ciwo lafiya ko Mai ta Sha sai ta amayo” Anty Amina tayi maganan duk da dai tana zargi.

“Gsky kam ba na lafiya ba, me doctor ya ce maka yana damun ta?” Salim yayi tambayar yana Kallon Aliyu.

“She is pregnant” ya amsa mishi.

“Ma Sha Allah” kusan a tare su ka fada.

Poor ZahraKwanan ta biyu a asibitin aka sallameta a asibitin kaman yanda likitan ya fada, Nanah ce kwana da ita Anty Amina Kuma ta wuni, Aliyu ya so su barshi yayi jinyan ta da kanshi fir abokan su kaki, acewar su sai dai kace ba a tare dole ya sa ya hakura Kar su ji wani iri ganin Kara su ke son mishi.+

Ba laifi ta warware sai dai Kuma cikin na matukar wahalar da ita, tuni ya Kira ya fada a gida gudun samun matsala, Ammah da Mami dai tunanin su daya Allah ya sa ba irin laulayin Mahaifiyar ta za tayi ba. Abbah da Baffah ko musamman su kazo har asibitin su ka duba ta tare da Hamza, Deedat, Shaheeda da Yusrah.

Aliyu ya nemi su bar mishi Shaheeda da Yusrah su zauna dasu saboda condition in Zahraun, akwai abun ya zo dai dai, Shahida ta gama secondary school ta na jiran admission, Yusrah Kuma ta gama junior secondary sai dai ita Nan da 3 weeks za ta koma SS1, ba musu Abban ya amince kasancewar shi ma ya na matukar tausaya Mata, Deedat aka yi Akan zai kawo musu kayan nasu da ke Yana yawan shigowa Abujan.

Tarairayan da Aliyu yake was Zahrau ya linka na baya sosai, wani irin tausayin ta ya ke ji ganin irin wahalan da ta ke Sha komai ta ja tana bukata Nan da nan zai yi kokarin yi Mata wani abun ma ba sai ta fada ba sai aukin bacci kace kassa.

Yau ma hakan ce ta kasance da kyar ya tashe ta tayi Sallan Asuba ta koma, sun yi da ita ranar za ta cigaba da zuwa asibiti amma shiru kake ji ba alamun za ta tashi, da ke ma bai fi 2 months ya rage musu su gama IT in ba gabadaya ma.

Hura Mata iska yayi a kunnen ta ko za ta tashi, dabarun da ya dinga yi sun fi a kirga Amma duk a banza coz ba Wanda yayi aiki Amma wannan in da alamun zai yi tunda har ta fara motsi da idanuwan ta. Yana bin ta a hankali sbd Bai so ta tashi a firgice ga situation in da ta ke ciki, gabadaya gani ya ke shi ya ja Mata komai na wahala da ta ke Sha tunda ajiyan shi ne a cikin na ta. Iskan ya Kara hura mata, a hankali ta fara motsi da idanuwan ta har sai da suka bude gabadaya, Murmushi ta sakan mishi immediately her gaze fall on him “Morning Hubbie” ta fada da muryar baccin da bai gama sakin ta ba.

“Morning Diva ba Zaki Hospital in bane?”

Kwalalo ido tayi “am i late?”

Girgiza ma ta Kai yayi “you can make it, kawai ki tashi”

Da sauri ko ta Mike tayi azaman shiga wanka, tun Yana jiranta har ya fara tunanin lfy? Ko da ya bude toilet in samun ta yayi tana ta bacci a cikin bath tub in, sakin baki yayi Yana Kallon ikon Allah dai dai Nan ko ta tashi tana mitsika ido “kinsan me? Kawai ki hakura Zan yi reporting case inki” ki tayi a dole ya taimaka Mata ta shirya ya sauke ta.

Kullum ko sai ta je Amma ba amfani, is either tana bacci ko Kuma ba ta Jin dadin jikin ta ta kasa yin komai gashi har yanzu ba wai ta daina Aman gabadaya bane, Daga karshe dole ya sa ya Mata Jan ido ta hakura da maganan asibitin kwata kwata.

Satin su Shaheeda Uku ya ce zai maida Yusrah saboda makaranta taso ta ce zata bishi Amma rashin ganin fuska ya sa ta kasa yin hakan, kwana biyu yayi daga ita sai Shahida a gidan Dan ma suna dasawa har labarin saurayin ta take Bata Wanda ya ke residing a Abuja daga karshe ma har gidan ya Zo gaida Zahrau Amma fa Aliyu na Zaria lokacin.

“Shahida babba ne fa, he looks responsible aure za kiyi ne soon?” Ba kunya ta gyade kanta “Anty Ina son shi fa sosai Kuma ya ce min Yana so yayi settling soon, Maman shi ta dame shi da maganar aure Kuma ni Kinga ban son na rasa shi”.

“Abin na ki da gaske ne, Wai ma Ina kuka hadu dashi?” Zahrau ta tambaya.

“A kano da na je wurin Anty Zee, Neighbors insu ne”

“Abbah zai barki Shaheeda? Ki Bari ki fara schl Mana to sai ku taso da maganar”

“Haka na fada Mai Nima”

“Ma Sha Allah Allah ya tabbatar Mana da alkhairi”

“Ameen” Shahida ta amsa sannan su ka cigaba da kitson da suke yi bayan sun dasa sabuwan hira.

     Cikin jikin Zahrau na wata Uku ta warware gabadaya, ba ta da wani matsala in ba kwadayi ba mijin ta ko ya tsare ma ta wannan sai Kara shagwaba ta ya ke yi, tayi fari tayi kiba tayi kyau abinta Ma Sha Allah.

Wata ta Kama December, A lokacin su ka tafi Zaria bikin Ya Deedat. Lokacin kuma yayi dai dai da fara registration in su na shiga Level Four, waya ga su Zahrau a final year.

Shi dai gogan na ta ba wai Yana son komawa school in da za tayi bane saboda shi zaman shi ba zai yiwu a Abuja kaman yanda dole ta zauna a Zaria gashi final year balle ya fara maganan transfer, Dan ba yanda xai yi ne Amma da makarantar ma barin shi za tayi tunda dai Allah ya hore mishi Kuma ya tsare Mata komai. Hmmmm ni dai nace ko waya fada wa maza amfanin karatun mace Dan Wanda za ta aura Bai dashi ne? Allah dai ya kyauta Mana kawai.

Hamza ya sa ya mata registration in, anyi biki angama har ma da na Sumayya Amma Kuma ba su koma ba Saboda shi ma Yana hutun karshen shekara, Kiri Kiri ya Hana ta komawa sai bayan New year.

Budewan school insu yayi dai dai da komawan aikin shi, Lokacin cikin ta ya fara fitowa Dan ma ba Mai tsinin ciki bace.

Tana hada kayan da zata koma samarun da su ya shigo daki ya same ta, Zama yayi a hankali kusa da ita jikin shi duk yayi sanyi “Diva yanzu ba za ki Zo mu koma Abujan ba?”

Juyowa tayi dan ta ga gskyn abinda ya ke fadi aiko ba ta ga alamun karya ba a fuskan shi “So kake in bar makarantan ne?” Ta fada with a shaky voice, kafin ya Kara wani har ta fara hawaye “shknn tunda ba kason cigaba na na hakura ba Zan koma ba” wullar da kayan hannun ta tayi ta fita ta bar mishi dakin.

  Bin ta yayi da kallo a fili ya ambata “Daga magana” girgiza Kai kawai yayi shi ma ya fita masallaci domin Sallan Azahar.

Ba shi ya koma gidan ba har sai bayan la’asar, a falo ya iske ta tana Kallon Korean series. Yana sallama ta taho da gudu ta rungume shi tana Mai sannu da zuwa, saurin ture ta yayi ta dago tana Kallon shi cike da mamaki, kunnen ta ya Kama a hankali ya ciza ta saki Kara “ba na hana ki gudu ba wai”

“Sorry sir” ta fadi tana murmushi.

Mamakin saurin saukowan ta ya ke ita ko dama ba tayi da wani manufacturer bane sai dan Kar ya Kara Mata maganan komawa Abujan don tsaf ta San zai iya dagewa Kuma shikenan karatun da ta Dade tana yi ya tashi a banza, shiyasa Nan da nan ta nuna mishi baccin ranta.

“Kin daina fushin kenan” ya tmby.

Girgiza Kai tayi “Ba a fushi da hubbie, shine kaki dawo wa tun dazu ko?”

“Na dauka ba ki son ganina ne ai yanzu ma shahada nayi na taho”

“Wa ya gaya maka akwai San da ban son ganin ka, mu je kaci abinci” ta karasa tana Jan hannun shi.

Washegari da Yamma ya maida makarantan bayan ta je ta yi ma su Ammah sallama duk sun Mata fatan alkhairi. Sun fi 30 minutes a mota su na jimamin rabuwa fa juna, wani irin sabo su kayi na ban mamaki kowa ya San zai ji jiki in har ya rabu da Dan uwana shi.

Sai da Fateema ta Kira ta tana tambayan lfy ta jita shiru da ke ita since ta iso daga Kano. “Hubbie ya kamata ka tafi Kar dare ya maka a hanya”

“Au Kora na ma kike yi kenan Koh”

“Lah Wlh ba haka bane Naga yamma nayi kenan”

“Shknn bara na wuce inda ake nema na”

“Ni dai bance komai ba”

“Nima ai bance kin fada ba”

A tare su ka fita daga motan ya bude Mata boot “wa zai shigan Miki da kayan”

“Ina zuwa” ciki ta shiga ba dadewa su ka fito da Fateema da wasu yara.

Yaran su ka shigan Mata da kayan, Fateema ko su ka tsaya gaisawa da Aliyu.

Gaishe shi tayi cikin sakewan fuska ya amsa “lafiya kalau Amarya, an iso lfy”.

Mamakin da Fateema ta shiga kasa boyuwa yayi a fuskan ta, she can’t believe Aliyu ke Mata magana cikin raha har da wasa.

“Lfy kalau, mun same ku lfy?”

“Kalau, ya kanon na KU ne” hira ya ta janta dashi sosai ta ke mamakin abun, ni Kam nace mamaki ma tukunna fati.

“Bara in wuce ina Kan hanya” ya fadi ya na duba agogon hannun shi.

“To Allah ya kiyaye hanya”

“Ameen nagode Amarya ga Kuma amanar tawa Amaryar Kar wani Abu ya taba min ita” murmushi kawai tayi.

“In ba Hakan ba Kuma” ya cigaba “Angon Nan na ki barrister Zan sa a kama”

“Lallai muna da zaman kotu Ashe”

“Ahhhh rufa min asiri” ciki ta shiga ta Basu wuri suyi sallama

“To Diva ba ra na je ko” daga Mata gira yayi Yana Kallon cikin idon ta itama in shi ta ke kallo cike da so da kauna kaman su tsaya a haka su yita Kallon juna.

“Ka tafi hubbie” ta fadi tana kokarin janye hannuwan ta daga cikin nashi.

“Ehmm” ya amsa, sunkuyo da kanshi yayi yayi perking inta a cheeks “Take care of yourself for me” hannu ya Kai Kan cikin ta ya shafa “and our baby” daga mishi Kai kawai tayi ya shiga mota sai da yayi reverse sannan ya dago Mata hannu ita ma hannun ta dago mishi tana Kallon motar shi har sai da ya bar layin, kaman ta daura hannu a Kai ta kurma ihu haka ta ke ji, jiki a salube ta lallaba ta shiga gida.

Sai da ta shiga jiki sannan Fateema ta lura da cikin da ke jikin ta Nan fa ta hau Mata tsiya tana kumbure kumbure kafin kace kwabo ta fashe da kuka, sakin baki tayi tana Kallon ta, ko Zahrau ta mance da yanzu ba tare da hubbie ta ke ba? Fahimtar hakan da tayi ne ya da tayi saurin share hawayen ta, Sai a sannan suka fara Hira Fateeman na fada Mata irin mamakin canzawan Aliyu da tayi, ba ta ga mamakin ba kuwa sai da taga wayan da suka yi yafi uku kafin ya Isa Abuja, bini bini zai Kira ta Yana tambayan ta ya take ita ma da taji shiru za ta Kira shi.

            3 weeks later.

Zuwa yanzu Fateema ta Saba da ganin kallan soyayyan Zahrau da Aliyu, Abu kadan ta ce Miki hubbie kaza, hubbie ya ce kaza komai dai hubbie har tsiya ta ke Mata tayi tayi auren ta yayi ta ji abinda ake ji in anyi aure, rasa baki magana Fateema ke yi ganin yanda Aliyu gabadaya ya canja Mata kawa kamar ba Zahrau da ta sani ba tun suna JSS1.

A Rana za suyi waya yafi sau uku a haka kullum Yana cikin bata hakurin aiki ya mishi yawa, video call ko in su ka fara har mantawa Fateema ke yi da suna wayan. Rayuwa juyi juyi kenan a sati ukun sau biyu yazo ganin Zahrau a cewan shi sai bikin fateeman zai Zo su tafi. Ai ko haka aka yi suna samun hutun mid semester ya Zo ya tafi da su Kano tare da Amaryan gabadaya. A hanya ya ke sanar Mata ranar a ka sa auren Shahida, ta Mata murna ganin cewa burin Yar uwar na ta ya cika, Amarya dai ta ga soyyaya kala kala kafin aka karasa Kano.

Ta so sauka gidan su Fateeman kawai Sam ya ki yarda a cewar shi gidan sha’ani cike ya ke da jama’a ita ko tana cikin situation in da bata son takura don haka suna sauke Fateema ya wuce da ita gidan Anty zee.

Ummiy ta so ta sauka gidan ta Amma fir ya ki “yaushe Ummiy tayi hankalin Kula kin da ke Diva ba zai yiwu ba ki dai je ki wuni Mata” ita Kam Kallon mamaki ta bishi dashi coz Ummiyn ma ta haihu already.

Dole su ka hakura sai dai ta je mata wuni, a gidan Anty zee ta zauna har aka kare bikin fateeman Nan Kano aka Kai ta Sokoto road, daurin aure kawai ya jira sannan ya koma Abuja straight.

Satin ta Daya da kwana uku a kano ya Aiko Hamza ya maida ta Zaria, hutun su saura kwana biyu a koma Amma ya matsa Mata sai tazo Abuja fir ta ki, a ganin ta final year ta ke so she have to focus, ga project Kuma da ya taso ta a gaba Dan ma Yaya Deedat na taimaka Mata sosai.

Sai dai me? tun ranar da ya Mata maganan zuwa Abuja ta ki yayi fushi Bai Kara Kiran ta ba sai dai in ita ta Kira shi, shima iyaka ya tambayeta ya take ba sa wani hiran kirki zai kashe a cewar shi akwai aikin da zai yi. Tun abun Bai damun ta har ya fara a haka su ka koma schl ya Deedat ke kaita ya dauko ta wata Rana Hamza da ke Fateema ba ta dawo ba tukun.

Gida duk ya Mata kunci ta rasa Ina za ta sa kanta a haka Fateema ta dawo schl, tuni ta hada kayan ta tawa samaru diran mikiya, karatu su ke sosai hakan ya sa ta rage damuwan abinda Aliyu ke mata.

Abu kaman wasa daga kwananki ya koma satuka daga Nan Kuma ya koma watanni kusa wata na uku kenan, gashi tayi nauyi sosai, still dai ba ta hakura ba tana Kiran shi shi ko a sati Bai fi sau biyu zuwa uku ba.

Ranar kaman ance Mata kunna data ta ganshi online a WhatsApp Daman kullum ce Mata ya ke aiki ya sa shi gaba in ta Kira shi, magana ta mishi yayi banza da ita karshe ma da ta ishe shi yayi blocking inta.

Bin wayan ta ke da kallo unbelievable, Nan da nan ta fara zufa ta Kira shi a waya “hubbie blocking Ina kayi?”

Kai tsaye ya amsa ma ta da eh, sakin wayan ta ya fadi kasa yayi dai Daya, kafin kace Mai numfashin ta ya fara kokarin daukewa da gudu Fateema ta yi kanta ta na neman agaji. Ina tuni ta Suma, neighbor insu da ke da mota ta taimaka aka Kai ta ABUTH emergency su ka wuce da ita direct. Da kyar Fateema ta lalubo wayan ta ta Kira Aliyun ta fada mishi halin da ake ciki…

Hmmmmmmmmmmm…A rude ya ke bin wayan da kallo, kasa aiwata komai yayi saboda jikin gabadaya rawa ya ke yi.

Da kyar ya Kai Kan shi tsakar gidan shi, da hannu ya yafito driver in shi ya karaso, key mota kawai ya Mika mishi sannan ya bude motan ya shiga.

Driver in Bai tsaya Kara wani tambaya ba domin ya gane abinda ogan shi ke nufi sai da ya fita titin layin sannan ya tmby shi inda za su je.

“Zaria” kawai ya amsa Mai sannan ya runtse ido, cike da mamaki driver in ya bishi da kallo, Anya kuwa ya ji da kyau? As in Zaria hakanan kawai.

“If you won’t drive hand the key over!!” hannu ya mikawa driver in da ya daburce saboda tsawan da ogan shi ya mishi.

Nan da nan ya fara driving ya Kama hanyan fita Abuja, gudu ya ke sosai Amma Aliyu bai ganin hakan.

Sai da su ka iso zuba tunanin Kiran Deedat ya Zo mishi, Allah ma ya sa Yana gari. Numban Deedat in yayi dialling, Yana fara ringing ya dauko “hello Ya Aliyu”

“Kana Ina ne” ya tambaya direct.

“Ina Nan Asibitin, Doctors in suna kanta”

“Okay sai na zo” ya fadi sannan yayi ending call in.

 

In 3 hours su ka Isa Zaria, Kai tsaye samaru su ka nufa zuwa asibitin shika sannan ya Kira Deedat domin ya mishi kwatancen inda su ke.

Ko da ya Isa a kofan daki ya iske Hamza da Deedat in suna zaune, Daurewa yayi su ka gaisa sannan ya bukaci sanin halin da matar shi ta ke ciki.

“Alhmdlh komai yayi dai dai Ina ga ma bacci ta ke, ga dakin da suka ba mu Nan” Deedat ya fada Yana pointing dakin.

Handle in daki ya murda yayi sallama. Shahida, Yusrah, Fateema da Ammah ya tar a dakin, Amman ya fara gaidawa sauran su ka gaishe su ya amsa game da tambayan Mai jiki.

Ya na shigowa dakin ta farka sai dai jin muryar shi ya sa tayi lamo kaman da gaske baccin ta ke. Jefi jefi ake Hira a dakin shi dai ita kawai ya ke kallo ya na rokon Allah  ya sa ta farka ko sa yi magana, Kiran Sallan la’asar ya sa dole ya bar dakin su ka nufi masallaci. Ana idarwa ya yanke Shawaran wuce wa cikin Zaria ya gaida Mami.

A Falon ta ya iske ta tana cin kallo, bayan su gaisa ne ta ke tambayan shi Mai jikin. “Aliyu ni ko sai Inga kaman abu aka ma yarinyar Nan ya sa ciwon ta ke neman tasowa, Anya Aliyu?”

“Mami me Kika gani? Kinsan sha’anin masu ciki balle ma ita nata da ya ke bata wahala tun farko”

“To Allah ya sa, ni dai ban yarda da Kai ba, ka dai ji tsoron Allah, Allah ya kyauta” sosa Kai ya fara yi ganin Mami na neman turke shi, a hankali ya silale ya bar dakin kafin asirin shi ya Kai ga tonuwa gabadaya. Wurin Baffah ya nufa su ka tattauna wani business in da ya ke Shirin farawa, Abbah Kam Bai ma gari.

Sai da akayi Sallan Magrib sannan ya koma ko da ya Isa Isha’i tayi ya sa ya tsaya yayi Sallah sannan ya karasa dakin da aka yi admitting in nata.

Ko da ya Isa Ammah da Yusrah na Shirin komawa gida, Hamza zai Mai da su. Shahida da Fatima ne za su kwana wurin ta.

Su na tafiya Shahida ta fita haraban asibitin Wai za ta yo kallo, ni ko nace Anya kuwa?

Zaune ta ke Kan sallaya ta idar da Sallah tana tasbihi yayi Sallama ya shiga Fateema na gefen ta zaune akan plastic chair.

Bakaken ledan da ya shigo da su ya ajiye kan fridge in dakin, Fateema na ganin Shi ta Mike ta koma Kan gado ta bashi kujeran. “Thank you Amarya, ya jinya” amsa mishi tayi sannan ya dan fara Jan ta da hira ya na tambayan mijin nata kafin Zahrau ta gama tasbihi.

Kiran mijin na ta ya shigo wayanta, da ma ta fuskanci Aliyu na bukatar magana da Zahrau n hakan ya sa ta fita waje kafin ta yi picking in call in.

“Sannu Diva ya jikin?”

Kallo ta bishi dashi galala sannan ta tabe baki “Am alive” ta bashi amsa.

Wani murmushi ya saki da ya Kara fiddo ma ta da kyaun mijin na ta sosai “am sorry please, tuba na ke” ya fada Yana hadda hanayen shi alamun neman afuwa.

“Hmmmm” kawai ta ce.

“Kinsan me? Ke fa Kika ja ni Kuma I never thought abin zai Kai da haka, infact na zata ki daina damuwa da nine”

“To ni me nace?” Ta fadi tana kokarin fiddo wayan ta.

Taso yayi ya karaso inda ta ke hade da karban wayan na ta ba musu ta sakan Mai. Sai ranar ta yadda tayi missing in shi, hannayen su kawai da su ka gogi juna ya tabbatar ma ta da hakan.

“I miss you” ya fadi Yana kokarin jawo ta jikin shi. Kasa mishi musu tayi saboda wani irin kewan kwanciya a jikin shi da taji tana yi.

“Sorry my Diva kinji?” Ya fada Yana shafa Kan fuskan ta kafin ya koma Kan cikin ta Yana shafawa, “ya babynmu, ya fara motsi”

Turo baki tayi tace “you don’t even care to know ai, hadda blocking Ina kayi a WhatsApp da Kar inga hotunan Yan matan da za ka daura right?”

Tsaro idanuwa yayi “waya fada Miki? Kishi ko? Haushi Kika bani, sai nayi tunanin in na horar da ke ta hakan za ki yadda ko 2 days ki Zo ki min a Abuja”

“Hubbie ba fa kin zuwa nayi ba, Karatu ne ya min yawa Kuma na sanar da Kai mun kusa fara exams”

“Da karatu da aure wanne ya fi mahimmanci, haba Fatima ni fa ba dutse bane, I’ve feelings. To Bari ma in fada Miki gsky, I almost fall on a lady trap Allah ne ya kare ni” Saurin janye jikin ta tayi da gare shi ta ja baya.

“Me kake nufi, Zina?”

  Hade Rai yayi ya Sha mur “nace Miki nayi? Kuma ma da ya afkuwa ai woh hadda laifin ki”

“To Kai me ya hana ka zuwa” ta bukata.

“I’ve no chance, yanzu ma taking risk nayi, tun dazu Ma Umar ke Kira na sai da na fada musu halin da ake ciki sannan su kace za su San abin yi”

“Ni dai to Kar ka Kara min haka”

  “Sorry my lady ba zai Kara faruwa” sun Dade suna hira game da kokarin nuna wa juna yanda su kayi kewan kasancew tare, sai da Shahida ta shigo dakin tukunna ya musu sallama ya wuce gida.

Washegari da sassafe yayi samakkon zuwa asibitin, dole ranar zai koma saboda uzurin sa, sun dan Jima suna tattaunawa kaman Kar ya wuce haka ya daure ya koma.

Zahrau ko abinda ya fada Mata gabadaya ya tadar Mata da hankali, tsoron ta Daya Kar Matan Nan na bariki ma rasa kunya da tsoron Allah su yi nasaran kwace Mata miji, shikenan fa ta shiga uku ta lallace.

A ranar aka sallameta su ka koma gida, Allah Allah ta ke su gama Exams ta koma gida saboda gudun samun matsala, duk bayan awanni sai ta Kira shi duk Wai dan gudun samun matsala, abin ba daganan ya ke ba Hajiya Zahrau.

                           “

  A daddafe ta gama Exams in, kwana biyu ba ta Kara ba tayi wa Abuja tsinke, sai da ta tabbatar da mijin ta ba da wani alaka da wata tukunna hankalin ta ya kwanta coz ya tabbatar da kewan ta da yayi.

Cikin ta ko ya tsufa sosai, tafiya ma da kyar ta ke, 1 week to EDD inta Nanah ta haihu su ka je Kaduna suna daganan ya karasa da ita Zaria coz can su ka shirya za ta haihu da ma.Aikin shi Bai bari ya zauna ba Dan dole ya koma Abujan don can ma ba Zama ya ke ba. Yau Yana wannan garin gobe Yana wata har ma kasar akan fidda su.

Har ta kwanta bacci ta ji abu kaman Yana tsungulin ta, daurewa ta yi saboda wani irin azzababben baccin da ke idon ta, sai dai me? Wani irin ciwo ta ji ya taso daga maranta, bayanta, kafanta Kai ko Ina ma ta ke ji, ba shiri ta ji baccin ya washe gabadaya, tun tana dauriya ta ji ba zata iya ba.

Ammah ta fara kokarin kwalla wa Kira Daman tun farko part inta ta sauka, a cewarta ya za ayi ta je haihu gun Mami bayan a matsayin surukar ta take, Sarai mamin ta fahimce abinda ta ke nufi ta share ta.

Da sauri Ammahn ta karaso tana tambayan ta lfy? Mara ta ta fadi tana kokarin amabatan duk addu’an da ya Zo Mata, za ta iya rantse tun da tazo duniya ba ta taba Jin zafin ciwo ya irin wannan ba, Nan da nan Ammah ta gane nakuda ce ya Zo was Zahrau, saurin Kiran Hamza tayi a waya ya fito da mota.

A Daren su ka nufi asibiti, Nurses da Likita na ganin ta su ka tabbatar da haihu ce sai dai shiru kake ji har safiya gabadaya ta gama wahala ta galabaita, Mami ne ta Kira Aliyu ta sanar dashi shi din ma gabadaya a rude ya ke ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi a Zaria gashi ba dama, A haka ogan su ya sanar da ya na neman su kowa yazo Daman sun je ibadan ne, kaman yayi hauka haka ya tafi amsa Kiran Nan ba wai dan ya na so ba.

Bangaren Zahrau ko gabadaya ta fita hayyacin ta har an fara batun yi Mata tiyata sai ga nakuda gadan gadan, kafin kace kwabo har Kan jariri ya fara fitowa, Nurses in su ka taimaka Mata har babyn ta fito gabadaya, Nan take ta samu saboda wahalan da tasha sai da su ka yayyafa Mata ruwa ta farfado, Ita da babyn gabadaya a ka gyara kafin likitan ya duba ta saboda jinin ta ya hau, drip ya sa Mata sannan ya mata alluran bacci ta dan huta.

Ana gama gyara baby aka Mika wa su Ammah ita, sak babanta haka kowa ke fada sai dai haske nata ya fi kama da na mamanta.

Ta Kai 3 hours tana bacci sannan ta farka sai sannu ake Mata, kafin aka hada Mata Shayi ta Sha, Gabadaya jikin ta ciwo ya ke Mata. Aliyu dai dole sai ta waya su ka yi magana ya Mata ban gajiya, baby kuwa pictures inta ya sa aka daukan mishi.

Kwanan ta biyu a asibitin ta warware a ka sallamo su, Nan fa gida ya cika da Yan barka har da su Nanah Sabon jego. Ango karnin Kam bashi ya samu zuwa ba sai ana gobe suna a hakan ma da kyar.

Su na hada ido ya rungumeta ya na ma ta sannu hade da shi ma ta albarka sannan ya dauki baby ya hade su ya rungume.

“Diva na Miki wayau babyn Nan da ni ta ke Kama Allah” murmushi kawai ta yi kowa ma haka ya ke fada. Aliyu dai ranar baki kaman gonar auduga ya rike Yar shi ta kanshi Allah abin godiya.

Ranar Suna, yarinya ta ci sunan Ammah domin kuwa tun can Aliyu ita yayi niyyan yi wa Mai suna, Mami ma ta San da hakan, ai ko sosai ta ji dadi domin a cewarta Kara su ka Mata.

A gurguje, An koma second semester schl, haka Zahrau ta yi ta fama ga baby ga lectures sai dai hakan bai San ta yi wasa ba ta samu ta cinye jarabawan ta gabadaya. Alhamdulillah! Sunyi nasarar gama ABU a wannan shekaran ita da Fateema gabadaya ba tare da wani spilling ba Kuma results insu is good.

             Bayan shekara biyar

Dai dai gate in wani School da na ga an rubuta Esteem su ka yi parking sannan ta bude kofa ta shiga schl ba dadewa ta fito hannun ta rike da yarinyar da ba za ta gaza shekara hudu ba, suna fitowa gate ta hango Baban ta jikin mota ya harde hannu akan kirjin shi ya na jiran fitowan su, tana ganin shi ta kwace hannun ta da ga gun Maman nata tayi gun shi tana fadin “Daddy oyoyo” durkusawa yayi ya rungumota sannan ya daga ta sama “oyoyo ummin Daddy, ya schl yayi dadi?”

Turo baki tayi “Ni dai ban Kara zuwa ai ba Ka Nan ne Mommy ta min wayau ta Kai ni”

“Kai Ummi na makarantar za ki saba da Dadi” ba ta tsaya Jin me ya ke fada ba ta shigo mota gun kanin ta da ta hango Yana wasa da abun wasan shi, wasa ta hau mishi ya na Mata dariya. Girgiza Kai kawai Aliyu yayi ya shiga motan ita ma Zahrau ta shiga sai da ya fara driving ya juyo ya kalle ta “za ki sa yarinya ta ta biyo ki ko?”

“Da ta yi me?”

“Gashi ba ta son makarantan sai dai son wasan tsiya ji yanda hankalin ta gabadaya ya dauke”

Tabe baki tayi “to sai Kuma aka ce Nina sa, Kai Dai kawai haka yarka ta ke”

Murmushi yayi sannan yace “oho dai Nono alkalin da”

Kaman an zungure ta ta taso “mommy Wai kinsan me aka ce? Sunana Aisha Aliyu” ta karasa tana dariya.

Dariya ma ta Basu ai ko ranar gabadaya duk Wanda ta gani sai ta fada mishi sunan ta Aisha Aliyu.

A gurguje, Aliyu ba karamin farin cikin auren Zahrau yayi ba don ko ta zame mishi haske a rayuwar shi, yana matukar yabawa da ita Nan ya ga mahimmanci bin zabin iyaye, sau dayawa Yana yawan shiwa Umar albarka domin shi ya ceto rayuwar shi daga fadawa halaka, lallai Umar aboki ne na gari ba karya ya shaida hakan. Su Kan su dangi suna matukar yabawa zahrau domin kuwa alkhairin da ya ke musu abin har ba a magana, ga yawan sada zumunci sai ka rantse da Allah ba Aliyun Nan ba ne miskili, miskilancin shi gabadaya ya Zama tarihi, za kayi mamakin yanda ya ke sakewa faran faran ayi Hira dashi, gashi da wasa, tsokana da raha. Kowa mamaki chanjawan shi ya ke, tsakanin shi da su Ummiy kuwa kaman wani Abu Bai taba shiga tsakanin su ba sai kaga yanda su ke haba haba da junan su, sosai ya tsaya musu a ko wani fanni na rayuwa duk da ba Wanda mijin ta ya gaza a cikinsu, A yan’uwan su kusan mutum 20 ya Kai hajji duk a sanadin saving da taimako da Zahrau ta daura shi akai, ai ko Yana ganin alkhairin abin, the more Yana badawa the more wasu na shigowa, ko ta Ina arziki ya Buda mishi sosai, an Kara mishi matsayi gun aiki, zaman su da Zahrau ko sai Sam barka bayan Ummi ta haifi namiji da aka sa wa Abbah Mai suna yanzu haka wani cikin gare ta ko mace ne ko namiji ne sai dai ya fito za a gani…

Zaune ya iske ta a falo tana kallo a Arewa 24, program in Dadin kowa da tayi missing ta ke kallo.

“Dadin kowa dadin kowa dai Diva baki gajiya?”

Murmushi ta sakan Mai “Allah hubbie da dadi gashi akwai lessons na zaman rayuwa”

“Ehmm ki ce a Nan Kika koyo?”

“No, Ina dai Kara sani?”

“To Ina kika koyo, in kina bani shawara yanda Kika San wacce ta San komai na zaman duniya”

Murmushi ta Kara yi “Tun Ina karama Ina yawan karance karance Novels, mafi akasarin Yan Mata a lokacin su Kan karanta ne saboda dadin labarin da Kuma soyayyan da ake cikin littafin sai dai ni ko wani abu na zamantakewa da ake rubutawa su ne abun dubawa na, musamman iya Zama da mutane da Kuma Kula da miji da gidan aure”

“Nagode wa Allah da ya bani mace irinki Mai kaifin basira Fateema, Ina matukar alfahari da ke, hakika kin gama min komai a rayuwa”

“A ko yaushe ka yabawa kokari ne wani irin farin ciki da annashuwa ke ziyarta ta samun Miji irin ka mai matukar yabawa da kokarin matar shi yayi karanci a yanzu, na kasance kullum cikin godewa Allah da ya hada ni Zama na din din da Kai, ba abinda na nema na rasa kullum burinka ka kyautata min”

Kallon ta ya ke har ta Kai aya, a hankali ya karaso gare ta ya jawo ta jikin shi “Ina sonki Zahrau, Ina sonki sosai”

“Its sounds weird you know”

“Why?”

“You hardly call me Zahrau”

“Its your fault ai Nima ban San na fada ba duk kin ruda ni”

“Ka tabbatar da hakan?”

“Sure” ya Bata amsa

“I love you too sweetheart, my love my hubby” Kara shigewa jikin shi ta yi Kan kirjin shi tasa kanta tana jin wani natsuwa Yana saukan Mata, she always feels comfortable there “my uncle Aliy” ta fada cike da tsokana, hararan ta yayi ba wai Dan ta na ganin Shi ba, da sauri Kuma ya cire ta daga jikin shi game da daka Mata tsawa “dalla matsa min!!” A firgice ta dago tana Kallon shi duk Wanda ya ganta ya sa ta tsorata. Dariya ya kwashe Mata dashi “matsoraciya kawai you will never change”

Ita ma dariyan tayi “ai Kai ka koya min kasan Ina Jin tsoron ka Amma ka yita cin zali na”

“Amma tsoran nawa Bai taba Hana ki rashin ji ba ko?”

Nan su ka koma suna tuno old memories insu suna dariya, Wai kaman ba ayi ba, duniya kenan Daman komai canja wa yake, Allah ya sa mu Dace, Ameen ya rabbi.

Tammat bihamdillah

Aka ce wai laifin dadi Yayi karewa…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page