MAFARIN SO CHAPTER 3

MAFARIN SO CHAPTER 3

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da fatan kajini da kyau” Rabi’ah ta faɗa, bai iya cewa komai ba dan kar ya buɗe ido barkono ya shiga ya kama idon ya rufe ruf,

    Amrah tace, “haba bestie miye haka wannan ai wulakanci ne,”

   Abba ne yace da sauran jama’ar wajen “ku ƙyale su wannan faɗan da kuke gani na masoya ne,”

   wata kawar amarya ce tace da Abba “Kace faɗan na manya ne, fadan masoya wanda ya shiga shi keda kunya, anjima zakaga sun dawo dai-dai”+

   Abba yace da Rabi’ah    

     “a taimaka mishi ya wanke mana, ko sai ya makance?”

   taja ƙwafa tace “Ai ko damun huta”,   

   “wanne hutu kuma keda zaki koma jagora?”

     “Tabɗijan” ta faɗa, , Abba da yaga da gaske take yace, “bari dai nakai miki shi, anma ke zaki zuba mishi ruwa ya wanke”

      “Wa? Badai ni ba”

   Amrah tace “Kinga Malama, kefa kika zuba mishi miyarnan, tashi zaki ki wanke mishi”

   Ta ansa sabulu tabi bayansu tana kumburi,

Abba ne ya kaishi har toilet yana riƙe da hannunshi sai lalube yake kaman sabon makaho, famfo ya kunna mishi yanda zai wanke,  ya wanke da ruwa sannan ya ce wa Abba

      “ina sabulu?” Abba yace “yana hannun kawar ka,” sannan yayi tafiyanshi, ya barsu Sabulun yace ta bashi,  

    “Tab ni zan ma baka sabulo ko? to gashinan a ƙasa idan kaji zaka iya ɗauka ka dauka idan kuma baza ka iyaba ruwanka dan ni kaga tafiya ta,”

    “Au tafiya zakiyi ma ko” ya faɗa,

   tace “A’a wanka zan tsaya inyi maka,”

    “Saurin me kike?” ya faɗa, “ai akwai lokacin da zakiyi mun wankanma, ko yanzu kikeso ki fara?” duk da idanunshi a rufe saida ya kashe mata ɗaya,

      tsaki taja,  tayi hanyar fita da sauri, lallai ta tabbata mutuminnan ɗan iskane, jin alaman tafiyanta yasa yace, “bikiji ba”

    Ta tsaya kawai, 

    “in kinje ki cewa Abba ya dauki key ɗin mota na yaje ciki akwai fararen kayana ya ɗaukomun”  

    “To Oga” ta faɗa “ga yar aikin ka ko? Zan faɗa mishi”

      “Yauwah, kiyi sauri jiranki nake” tayi er dariya kawai ta wuce, don ita kaɗai tasan meta shirya mishi,1

Tana zuwa wuri ta nema tayi zamanta, Abba yace “ina kika baro mutumin naki?”

     “Ohon mishi, yace inzo ne yana zuwa” ba wanda ya ƙara tambayarta kawai sukaci gaba da firarsu, har kusan Awa ɗaya,

    Wayanta ce tayi ringing, ta fito da ita kiran yayanta ne harya katse, sannan taga shine misscall na 22, gabanta saida ya faɗi da sauri ta duba lokaci, saiga kiranshi ya sake shigowa da sauri ta ɗauka, ya sauke sanyayyar ajiyar zuwa,

     “Hello! Ƙanwana?”

   “Naam yayanah”

   “Haba Rabi’ah! Kin manta da yayanki bazaki kira ki faɗamun yanda kuka isa ba?”

    “lafiya lau Yayana, wallahi hayaniya, kayi haƙuri plz”

      “Yanzu kam hankalina ya kwanta, ina fatan dai kina hanya kin kusa isowa?”

     “Eeh Yayah insha Allahu yanzu zamu taho”

     “Zaku taho fa kikace? Kinsan kuwa ko ƙarfe nawa?”

    “eeh Yaya zamu iso yanzu insha Allah”

    “Yauwah ƙanwana, ki tashi yanzu maza ki taho, bazanyi barci ba har sai kin dawo”

    “Tohh Yaya” harma ya kashe wayan,

  

Ta kallesu,

    “Wai yaushene za’a fara maida waɗanda bazasu kwana ba?”

     Khaleed yace “wanne wanda basu kwanan? Ai an gama maida kowa, duk wanda kika gani anan kwana zasuyi, muma daganan hotel mukayi”

     “Na Shiga Uku! Ya akai ba’a faɗamun ba?”

    “ai tun zuwanku anan suka juya”

   Zahra tace “Sis ai yanzu darema yayi, ki kwana anan kawai”

    Kaman zatayi kuka, “Haba sis, kaman bakisan Yayana bane? Bance mishi zan kwana ba, kuma dai kinsan bai taɓa barina na kwana a wani wuri ba”

     “ki buga ki tambayeshi mana”

    “A’ah nifa gida zan koma, duk dare a katsina zan kwana”

    Kaman zatayi kuka duk ta damu,

     “duk ku kuka hanani tahowa da motana, dana tafiyana kawai”

    “cikin darennan zaki koma ke kaɗai?”

     “eeh mana” tana magana kaman ta fasa kuka, duk sun tausaya mata, kawai gani sukai Abba ya fara dariya, duk suka tsira mishi ido suna tambayarshi lafiya? Dariya ma ya hanashi faɗi,

    “Haba Abba, bafa abun dariya bane” ta faɗa cikin jin haushin dariyar,

     “tohh ai bakusan abun dariyar ba”

   Har suna haɗa baki, “Menene? Faɗa mana”

      Daƙyar ya iya faɗin, “Ahmad ne kawai zai koma katsina yanzu, don shima ya faɗamun bazai iya kwana kano ba” aikam gaba ɗaya suka kama dariya,

     Ta zaro ido cikin tashin hankali, sai yanzu ta tuna data baroshi toilet da jiƙaƙƙun kaya, Anya kuwa zai kaita? Itama tunanin ta yanda zata fara binshi take cikin darennan.Jiki a sanyaye Rabi’ah tace ma Abba “namanta Ahmad yace ka ɗauko mishi kayanshi a mota,”

    Abba yace ” Badai yana bayi  ba  tun ɗazu?” Kai kawai ta iya ɗaga mashi, dan tama rasa abinyi tana tunanin yayanta kuma tana tunanin wannan Ahmad ɗin ƙwaƙwalwarta duk ta ɗau caji,+

   Abba kuwa yaje ya daukoma Ahmed kayanshi, ya kaimashi toilet ɗin Abba ya ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin Ahmad yace “waye ne?” 

   Abba yace “Nine Aboki ga kayanka,” Wata nauyanyar ajiyar zuciya Ahmad yasaki kafin ya ce ” To”

Ya bude  ƙofar da jiƙaƙƙun kayanshi harsun fara bushewa, sannan yace “kaga yadace abunda kamun tsawan lokacin da nace ka  ɗaukomin kayana  shine  kashareni anan ko?  Ya maka kyau ba  damuwa nagode,” Cikin bacin rai yake magana,

Abbah yace “haba Aboki  miye na daukar zafi haka bayan baka da tabbacin saƙonka yazo gareni ko baizo ba, ka fara zubamin ruwan masifa,”

   Sai a lokacin ya tuna da wacce  yabawa sakon ta fadawa Abokin nashi,

“Hmm bakomi ya fada ni zataiwa ɗanyen rashin mutunci ko”

   Abba yace “bakamasan wani abu ba Aboki kasan fa yanzu zata koma katsina,”

   “Ah haba dan Allah” Ahmad ya faɗa,

Abba yace “da gaske makuwa,”

      “ita dawa zata tafi? Kuma naga kaman bada mota tazo ba”

     “waye zai koma bayan kai?”

   Wani guntun murmushin mugunta Ahmad ya saki, sannan Abba ya bashi wuri ya canja kaya, kayan  sun karɓe shi sosai, har sunfi wanda ya cire yi mishi kyau, tare suka koma cikin palo inda su Rabi’ah suke.

   Sallama sukayi sannan suka shiga.

   A tsaye suka tarar da Rabi’ah ta matsawa Amrah akan lallai sai sun rakata tasha tahau  motar haya,

Amrah ko magiya take mata akan takira yayanta tace dashi zata kwana a Kano in yaso washe gari sai suyi asubanci suje katsinan idan Allah ya yarda,

   Rabi’ah tace “kibar ni kawai besty idan bazaki rakani ba ni kinga tafiya ta dan haka saduwar Alkairi,”

    Ahmad ne yace “to ainima yanzu zan wuce katsinan,”

    Abba yace “yawwa Aboki to dan Allah kabiya da ita mana kaga yanda mukazo dasu amana ne awajen mu dan haka ga amana nan mun damƙa a hannunka ka kula da ita sosai kaji,”

   Rabi’ah tace, “Allah ya tsare da nabi wannan dan rainin hankalin”

   Ahmad yace “waye zai tafi da wannan shugabar en ji da kan?”

  Abbah yace “kunga ku taimaka ku aje wannan Alayin soyayyar taku, dare yakeyi kuma kunga hanya zaku dauka,”

  Amrah tace  “Dan Allah Besty kije mana ku tafi kinsan fa Yaya yana jiranki,” Hankalin Rabi’ah yakara tashi gashi ita bata hau motar hayar ba  kuma ga wannan ɗan dandalin yana ɓata mata lokaci,

   Ahmad yace “to nidai natafi kumin fatan Alkairi,

   Abba yace da Rabi’ah “kitafi kuje mana,” a sanyaye tace “to,”

  Ahmad yace “waye zai biya kudin motar dan ban tsara da zan dauki kowa a motata ba?”

   Abba yace “naji zan biya ko nawane”, Rabi’ah kuwa a zuciyar ta cewa tayi  kowace balagazar mota ce dashi har yake ma mutane iya yi, bayanshi tabi suka fita Abba da Amrah ne suka rakasu har bakin get sannan suka masu fatan sauka lafiya,             

    Dai-dai saitin Ahmad, Abba ya duƙa a hankali yace mishi “wlh Aboki kowa zai dauka matarka ce dan kunyi masifar da cewa, ya kamata tazama takafa,”

Daria Ahmad yayi tare da fadin “wannam ai gulmane da sa ido”

    “ba wannan maganar Aboki”

Sannan sukayi bankwana dasu.

   Motar shi fara kirar (Audi) irin motocin nan da ake kira masu numfashi, Da bisminllah ta chiga sannan ta fara karanto addu’ar hawa abin hawa

(Subhanan lazi sakara lana haza wama kunnan lahu mu’ouridun wa’in,na illah Rabina lamun’kalibun) Sannan ta hada da Lakad ja’akum rasulun……

Ta tofa ta shafe jikinta duka, shima addu’a yayi sannan ya dauki hanyar zuwa katsina sunfi kusan muntina sha biyar ba Wanda yace da wani ƙalah,

  Ahmad ne ya gaji da rashin maganar tata, kuma yana gudun shi ya mata maganar taji dadin kara jan aji,

Hakanan ya daure “yace wai ke kurma ce?

   Bata ko kalli inda yake ba tayi banza dashi kamar ma ba da ita yake ba

   Ya sake cewa ” Ja aji kitsufa gidan ku An mata”

    Da tayi kamar bazata mishi magana ba, kuma sai tace tana taɓe baki, ba tare data ko kalleshi ba.     

    “daɗinta dai a gidan namu zan tsufah ba gidan wasu balle aji dadin yimin gori kuma aji ai sai cikakkiyar mace,” taja karamin tsaki

   “Waye cikkakiyar macen anan?”

    “gata a gabanka”

   “da wuri haka har kin faramin tallar kanki”

   Tsaki taja sannan tace “da ma wani cikakken namiji kace”

   “Tabdijan ni zaki fadawa wannan maganan”

   “Eh an faɗa maka idan kana da abinda zakayi ai sai kayi ko”

    “Eh niko nake da abinyi bari ki…” Kasa ƙarasawa yayi sanadiyar karo da motar ta kusayi da wata bishiya

   Rabi’ah kuwa Inna lillahi… Kawai take ta nanatawa abakinta dan tasare da rayuwa.Rabi’ah ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba har saida en cikinta suka kaɗa, duk ta dunƙule wuri ɗaya tana kalmatus shahada,

    Shikam daya samu ya tsaida motan cikin ikon Allah basu kaima iccen karo ba, yana kallonta me zaiyi ba dariya ba harda riƙe ciki. Can ta fara jiyo dariyarshi, ta ɓata rai ta ɗago da fuskanta, sannan ta fahimci meke faruwa.

    “me abun dariya anan?”

    Ya ƙara kyalƙyacewa da dariyan yana kallonta, “ki barshi kawai ke bazaki gane ba”

   Ta ƙara tunzura, “jakkar Ajinmu nake, ƙarewar rashin ganewa, tashin hankalin daka sakani harka samu abun dariya?”

     “kika sakamu dai, duk waye ya kusa ja mana idan bake ba?”

    “watau laifina ma kake gani kenan?”

    “toh dafa? Kinga kuwa yanda kika maƙure ashe dai kina tsoran mutuwa?”

     hararanshi tayi, “so kayi ka ƙarasani kenan?”

    Anan wani faɗan yaci gaba, gashi su biyu babu mai rabawa, sun ɓata lokaci sosai a haka, kafin yace mata,

    “Yanzu masifar zakici gaba ko zaki barni mu fita daga dajinnan? Don ni ina da abunyi a katsina in ke baki da”

     “Waye masifaffiyar? Nayi maka kama da marar abunyi ne?”

   “toh malama mai abunyi muje” ya tada mota suka tafi,+

Wannan karon a hankali yake tafiya sosae, ko mai tafiya a ƙasa zai iya rigansu ƙarasawa inda zaije, tasan duk son ta kulashi ne, tayi mishi banza kawai, yana en waƙe-waƙenshi na india, (waƙan cikin Tevar, Hey listen baby, baby i will do anything for uh, Nah M just jocking……).

    Ta shareshi kawai ta kwantar da kujerar zata jingina, da sauri ya tareta.

     “ɗan tsaya man,” ta ɗaga ido tana kallonshi baki buɗe,

    “kuɗin motar da aka biya miki, na zamane kawai banda kwancia”

    Dogon numfashi taja, sannan tayi sama da idonta ta sauke, “idan duka kuɗin motar kake buƙata, ka faɗamun zan siya, saboda wannan ƙarfen da yayi kaɗan a kirashi mota sai wani ɗaga kai kake”

     “yaushene nace miki zan siyar da motana? Kawai dai kwanciya ne na hana”

    “sai inga ta yanda zaka hana ɗin” ta gyara wuri ta kwanta tana murguɗa baki, murmushi kawai yayi yana riƙe baki cikin tunani,

     “Yauwah, nikam ɗazu naji kina magana akan kina na qarshe a aji, ya baki taɓa faɗamun ba?” ya ƙarasa magana yana ƙoƙarin riƙe dariyarsa,

   Wannan karon yafi ƙarfin ta maida da baki, kusa da ita ta duba, babu abun duka, cire gyalenta tayi ta ƙudundune ta fara dukanshi, sai karewa yake yana dariya.

     “kinga karki ƙara sakawa muyi na ɗazu”

     Ko saurarshi batayi ba da yake taga a hankali yake tafiyan, saida taga yana ƙoƙarin riƙota ne, gashi motar ta fara tangal-tangal sannan ta haƙura ta koma ta kwanta tana maida numfashi.

Motance ta tsaya, a dai dai sun kusa isa garin Ingawa, ta tashi zaune,

    “me kuma ka tsayayi?”

  Buɗewa kawai yayi ya fita ba tare da yace da ita komi ba, ta buɗe itama ta bishi,

     “ina zakaje ka barni cikin tsohon darennan kuma ko faɗamun bazakayi ba?”

     Gaban Motar ya buɗe, ya ɗanyi taɓe-taɓenshi ya rufe ya koma ciki, ta bishi da sauri.

     “Dakai fa nake magana”

  Ya sake tadawa duk batayi ba, ya dafe kanshi, duk ya haɗa zufa, ya sake fita yana ɗan tafiya, tasha gabanshi.

     “malam magana nake maka fa, ka kama ka kashe mota, kaje mu tafi”

     “mu tafi ina? Nasan kinajin yunwane na fita in duba ko akwai restaurant anan, kici abincin”

   Duk bata gane baƙar magana ne ya mata ba, “an faɗa maka a gidanmu babu abincinne? Idan bazaka tafi ba nizan iya tafiya” tun kafin ta ƙarasa magana ya miƙa mata mukullin, ta saki baki tana mamaki, ta anshe ta shiga motar, tadawa ta shigayi anma mota taƙi tashi, duk da haka taƙi haƙura don kar yaga gazawarta, sai data gaji don kanta ta daina, ya duƙo da kanshi ta glass ɗin motar.

      “Yadai? Taƙi tashi ba? Kin ɗauka da gangan na kashe motan don kawai inason sauraren masifarki?”

    “Na shiga Uku, mota ta lalace mana a dajinnan?”

     “kin gane kenan”

   Ɗaura hannu tayi akai zata fara rusar kuka.Ahmad ya riƙe baki,

   ‘kajimin er rainin hankali wato kukama zakiyi bazaki tsaya mu nemi mafita ba, bayan kuma kece silar komai,”

   A harzuƙe ta taso masa “wato nima zakace, da gani daman ka saba wahala da wannan tsohuwar motar taka, zakawani laƙamin sharri, 

Tun wuri ma gyara kasan abinyi dan Allah bazaka barni a dokar da jin nan ba”

  Har tayi shiru ta ƙara kallonshi, “Kuma dole mu isa katsina a yau saboda wlh bazan ɓatawa yayana rai ba saboda da kai”

   Ahmad yace “dole mu kwana a katsina yau? saboda ke keda iko da komai ko, bazaki ce insha Allah ba”

    “To ai dama komai sai da yardar Allah muke yinshi” Rabi’ah ta faɗa,

  “Da wannan masifar da kike da ma tunanin mafita kika mana da yafi miki,” Rabi’ah tace “aikai kataho dani sai kasan yanda zakayi dani dan Wlh bazan kwana a jejin nan ba, koka manta kuɗin mota aka biyamun?, ka kira makanike yazo ya duba mana motar ko masan inda dare ya mana”

   “Wato saboda bashi da aikin yi shi makanikan sai hidimar mota ko? to ki duba Lokaci karfe nawa yanzu, idan mijinki ne kinji daɗi ya fito yabarki cikin tsohon daren nan don ya gyarawa wani mota ba hatsari ba, ba komaiba balle ace ceton rai ya fito,

Mota kuma tanshin kinkine yasa battery yayi sanyi dan haka dole saida safe idan Allah ya kaimu an chager shi saimu wuce gida , kingane?” ya faɗa tare da kashe mata ido ɗaya.

Rabi’ah kuwa ta cika tayi fam tunanin Yayan ta ya faɗo mata, motar ta buɗa zata ɗauka wayanta a jakarta, don ta sanar dashi halin da ake ciki. Kawai ta duba ko sama ko ƙasa babu ita,  sai lokacin ta tuna taa barota a gidan Amarya, haƙura tayi kawai da neman ganin babu yanda zatayi.

   Ahmad kuwa jira yake yaji kuma da wane bala’in zata fara zazaga mashi,

Anma abin mamaki sai yaga ta juyo ta kalleshi jiki a sanyaye da Alamun nadama a fuskarta,

Azuciyarshi kuma cewa yayi ‘nasan wani munafuncin takeson ƙullawa chine tayi kalar tausayi…

  Maganarta ce ta katse shi da cewa “Dan Allah ka bani Aron wayarka zanyi kira”

  “Awwh! babu credit a naki wayan?” ya faɗa,

   “A’a na bar jakar ne a gidan Amarya, nasan su Zahra zasu tafomun da ita”

   “saurayinki zaki kira yazo ya ɗaukeki ko?”

A zuciyarta tace ‘dan na tambayeka ne zakamin rainin hankali ko ni badan yayana ba ka isa na karɓi wayanka’

   A zahiri kuwa cewa tayi “A’ah Yayana zan kira na faɗa mishi dan kada hankalinshi ya tashi”

   Ahmad yace “dan mi bazaki kira ummanki ki faɗa mata ba? Ai hankalinta zaifi na yayan naki tashi”

  Maganarshi tasa jikinta yayi sanyi sosai wasu siraran hawaye ne suka fara bin kuncinta kawai tunanin iyayanta ya faɗo mata a rai ashe marainiyace ita, ko soyayyar yayanta gareta yasa tamanta da mairaicin da take ciki ƙafafuwanta sun kasa riƙeta dole ta jasu hakanan takoma cikin mota ta zauna hawaye kawai take wasu nabin wasu,

   Ganin halin data shiga ne yasa Ahmad cikin damuwa shima binta yayi motar yace “dan Allah kiyi hakuri bansan zan ɓata miki raiba, kinji pls m so sorry wlh banason ɓatawa wani rai wannan ma bansan ranki zai ɓace ba dan Allah ki yafeni”

   “Bakomai” ta faɗa, “kawai ka tunamin ne da maraici na, Yayana shine Uwa da Uba a waje na ya maye min gurbinsu domin mun rasasu gaba ɗaya”

   Jikin Ahmad ya mutu sosai Wani tausayinta ne ya shiga ƙoƙon zuciyarshi, jiyake ina ma ace zai iya rungumeta ya rarrasheta sai dai ba hali anma ya ƙudurta azuciyarchi, bazai iya barinta ba koda kuwa zaya shiga matsalane, ya rasa mema yakeji a jikinsa tausayinta ne duk yabi ya mamayeshi

“Allah sarki kiyi hkr dama duk mai rai mamaci ne, sannu kinji ba kukanki suke bukata ba addu’arki ce mafi soyuwa a wajensu” hkr yabata sosai cikin Wata sassanyar muryar da batasan daga ina ya samota ba  sai da yaga ta nustu sosai sannan ya bata wayarshi ta karɓa sannan tasaka number Yayanta anma takasa samu Busy kawai ake ce mata, gashi wayan Ahmad ɗinma Charge ya kusa ya ƙare, tayi kira yafi a ƙirga anma Busy kakeji  yaƙi shiga, tasan ita yake nema, A dole ta haƙura akan idan ya daina kira zata kirashi, gashi wayanta silent ballantana Amrah taji ƙararta ta ɗaga kiran.

  A ɓangaren Yayanta kuwa ya kasa sukuni domun kwata-kwata hankalinshi a tashe yake ya kira Rabi’ah yafi a ƙirga anma taƙi ta ɗaga, tunaninshi ba lafiya ba Aunty deeja kuwa cewa tayi “kabi duk kadamu da ita bayan ita ɗin bata damu da kai ba tanacen tana sheƙe ayarta ita da abokan shashancinta, dama ya lafiyar kura bare tayi hauka, tana garin nan ma a tare da mu tayi balle garin da ba idanunmu aiko sai abinda Allah yayi, idan ina faɗa maka ai ƙin yarda kakeyi, gashi nan ka gani da kanka, tun ɗazu kayi waya ance maka ta taho, shin ko wani abu ya faru ai dole za’a samu wanda zai ɗaga kiran, ka daina damun kanka ma, kananan zakaga ta dawo sanda taga dama”Dan Allah muje ka kwanta ka huta in yaso sanda ta dawo ai sai kaji inda ta shige ko,”

   Baiko kalleta ba, yanata zarya tsakar falon yace “kije ki kwanta kawai  in zaki iya,”

   tace “to mezai hanani iya bacci ni kuwa? kai ma ai dan ka saka kankane shiyasa tana can tana sheƙe ayarta dan haka ni saida safe, bacci ya kama ido na sosai kabiya ta dakin su Hayrah Kai masu addu’a sai kashigo daga ciki kaji”

     “OK” kawai ya iya faɗa ita kuwa Anty deejah dakinta ta nufa sam babu abinda ke damunta game da rashin dawowar Rabi’ah gida.

    Ta ɓangaransu Rabi’ah kuwa sunga dare yaja sosai Ahmad ne yace da ita “wai ke a ina zamu kwana kinsan baza muyi bacci Annan mukadai ba KO kuma ni banga Alamun hotel anan ba” 

    Rabi’ah tace “ai dama duk mazan takar da kake nunawa ta banzace bazaka iya kwana a dokar daji ba, hmm to ai kai zaka nemi mafita dan ni hannun direba aka bayar da amanata dan haka haƙƙin driver ne ya nemamin gurin kwana”

   Agogon hannunshi ya duba yaga dare yayi sosai  shiyasa bai kulata ba dan yasan idan ya biye mata Wata sabuwar rigimar zasu shiga kawai shiya fito daga motar ya nufi wani dan guri daya ke ganin haske haske kamar alamar gidane awajen.

Rabi’ah ko ganin ya mike hanya yana tafiya yasata fitowa da sauri daga motar tare dabin bayanshi cikin sassarfa har ta isa gurinshi.

   Jin kamar tafiya bayanshi ya sashi waigowa ganinta dayayi bayanshi ya bashi mamaki, yaushe tabiyoshi,

Yace “wato biyoni ma kikayi ko”

   “Au nufinka in tsaya acen ko wato ka gama cinikin kaina Wanda ka saidawa suzo sutafi dani shine ka faki idona kataho ko? to naganka shiyasa na biyoka inyaso sai su ɗauki motar taka badai kaina ba”

   Daria sosai tabashi wato tsoro ya hanata zama ita kadai kenan shiyasa ta biyoshi

Bari kiji na faɗa maki wannan guntun Kan  naki ba zaki bada abinda akeso ba koda sai dashi akai, sai na bari lokacin da mukayi aure na ciyar dake sosai kan yayi girma lokacin sai in sai dashi matsoraciya kawai, anma dazu harda cemin ba namiji ba miyasa yanzu ke kikaki komawa namijin?”

   “Hmm, Kenan ma kaji ƙyaleni ne kayi”

   “Idan ban ƙyaleki ba biyeki Zani Kenan, kina zuba mani hauka ina ɗauka”

    “Wato ma A layin mahaukata ka sakani Kenan to aide Nafi..”

     “Wlh kimin shuru anan idan zakije ki wuce mu tafi idan kuma bazaki ba ki koma mota”, yayi gaba ya ƙyaleta, bayanshi tabi sunata tafiya sunyi tafiya mai nisa sannan suka isa wajen da yaga hasken ga mamakinshi mutun biyu ya iske a ƙofar gidan da alama magidan ci ne da matarshi.

Sallama ya masu cike da tsoro suka amsa mutumin yace “Mutun ko Aljan”, gashi dai su duka kyawunsu bai kasa bayyana a cikin hasken ba, abunda ya ƙara tsorata masu gidan kenan,

   Ahmad yace “baba mutane ne, ina wuni”, ya gaishe su, Rabi’ah ma sunkuyawa tayi ta gaishe su, sannan Ahmad yace “kan hanya ne muke zamuje katsina shine motar mu ta tsaya, Alfarma muke nema ko mun samu wurin kwanciya kafin gari ya waye musami makanike”

  Maigidan ne yace “ba laifi ɗaki biyu ne dama gidan namu sai ku shiga ɗayan ku kwanta” ya umarci matarshi data tashi ta masu iso zuwa ɗakin

   Tashi tayi ta rakasu har cikin dakin ɗakin a tsabtace ta kunnamasu wuta tace “asuba ta gari”

    Ahmad ne ya tsaida ita yace “dan Allah zan samu ruwa a buta?” tace “ba matsalah bari na kawo maka” ta fita, ta kawo mishi ruwa sannan ya karɓa yayi alwalah,

   Rabi’ah na zaune daga bakin gado tana mamakin karamcin waɗannan mutane, sun basu masauki cikin darennan ba tare da ko sunayensu sun sani ba, tohm anma a ɗaki ɗaya zasu kwana?

   Yana gama alwalan, ya faɗa kan ɗan ƙaramin gadon ƙarfen dake ɗakin inda Rabi’ah take zaune,

    Ta saki baki tana kallonshi, irin kallon kama rainamun hankalinnan, tace, “me kake nufi ne da zaka kwanta kan gado bayan ga tabarma nan a ƙasa?”

     “Taɓdijan, na miki kama da wanda ya saba kwana a tabarma da zakice wai ga tabarma, ai ke ya kamata ki kwanta kan tabarmar ko”

    “Ni zaka kalla kace na kwana a tabarma, anma wlh ka rainawa kanka hankalima, ka dubeni da kyau Malan dan haka tun wurima ka sauka daga gadon nan tun kafin raina ma ya ɓace” Rabi’ah ta faɗa.

    “Wato dukana zakiyi idan ban sauko ba ko, to bismillah ran naki idan yayi dubu ya daɗe bai ɓaci ba,  kisamo bulalah dan kiji dadin dukana da kyau”1

   Kallanshi take sosai anma hankalinta ba wajen shi yake bâ, tunani take ita dai bazata iya bacci bisa tabarma ba kuma gadon gashi kwancin mutun biyu ne, biyun ma sai mata da miji domin jikin su ma yana goga juna to ita ya zatayi?

   Ahmad ɗago yana kallonta, “kinmun zaune a gado malama, ko so kike ince kizo mu kwanta tare? Ba haka nake ba, ki sauka a ƙasa kiyi tunaninki”

    Murmushi tayi, saboda muguntar data tuna, ta kalleshi, “ai tunaninma ya ƙare, kaa kawo shawara, bazaka sauka ba ko?”

     Yace “eeh ɗin, bazan kwanta a ƙas ba”

    Ta ware hannu, “nima haka, mafita ɗaya kawai ta rage mana kenan”

    “me kenan?”

Gyarawa tayi ta kwanta saman gadon, anma ba tare data taɓoshi ba, da sauri ya tashi zaune, “ke me kikeyi haka? Nifa ustazu ne”

    “kai kasan wannan, nidai nayi wurin kwanciya” harararta yayi, yasan don ya sauka tayi hakan, a ranshi yace ‘aikam bazan bari yarinyarnan tayi nasara kaina ba, idan taga na kwanta naƙi sauka, ita zata sauka ne’ ya koma ya kwanta can gefe ya maƙure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page