KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 7 BY ayshay bee
KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 7 BY ayshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
Washegari, karfe 10 na safe ringing in wayan ta ya tashe ta daga bacci, Ummiy ce. Ba wai Dan tana so ta ke baccin safen ba illa don ragewa kanta kewa sai da tayi wanka sannan ta Kira Ummiyn “Amarya dadin Amarcin ne ya sa a ka ki daukan wayana?” Ta fada cike da zolaya “Ummiy ya kuke?” Ta fada cike da takaici “Zahra ya miki wani Abu ne, wlh duk abinda ya miki ki rama in ba haka raina ki zai yii Allah ki ajiye wannan tsoron na ki in ba haka ba sai ya kashe ki” “lallai kin iya ba da shawara coz na ki daban ya ke da na kowa” ta fada tana dariya sanin zafin Ummiyn “Zaki Sani an sa ranar biki fa ending December”. ” Dan Allah da gaske?” Ihun murna ta fara yi sannan su kayi sallama.+
Yau ma a dinning ta iske abinci ganin bai falon ya sa ta lallaba ta zuba ta ci a nan, kwana biyu kawai dakin ta ya fara gundurar ta, wani ta ga ya fito daga kitchen din da tsintsiya a hannun shi “morning madam” ya fada yana rusuna wa, ita abin mamaki ma ya bata kar dai ace wannan ne mai aikin gida “madam oga don know how to choose very well oh, you don pretty well well” ya fada yana yashe hakora yanda yayin ne ya sa ya bata dariya. “So you laugh oh, oga don’t laugh oh you are nice, is the food nice? We cook together with MUSA but oga send him away because you are coming so now am to do all the chores, I don suffer gsky”
“Sorry” ta fada tana dariya da alamun akwai surutu ganin informations in da ya jero ma ta ba tare da ta tmby ba. “Thank you so much madam, you must be nice atleast you are here now things will get easy” ita dai kawai murmushi ta mishi sannan ta ce “You are welcome” “seriously madam you don resemble all this fan oyinbo ladies we go see on TV, is just that them are stupid to be walking half naked showing their body they are all ashawo…” Fitowan Aliyu daga daki ne ya katse mishi maganan da ya ke yi. “Morning oga” ya fada yana sada kai kasa “What are you doing here David?” “Sorry oga, I want to sweep the first parlour, am leaving ya fada jikin shi na rawa yayi saurin barin wurin ya nufi falon.
A hankali ya karaso dinning ya ja kujera sannan ya zauna ko kallon gefen da ta ke bai yi ba ” INA kwana uncle” ta fada cikin rawar murya, daga ma ta hannu yayi alamun ya ji sannan ya cigaba da cin abincin shi. Ta Riga ta gama cin abincin gashi jikin ta sai rawa ya ke hakan ya sa tayi saurin tashi domin komawa prison in ta wato dakin ta. “Dawo ki zauna” ya fada in a commanding voice. Jiki na rawa ta koma inda ta ke ta zauna, a hankali ya fara magana “ban ga amfanin zaman ki a gidan nan ba so gwara ki dinga ayyukan gidan nan domin ni ba a zaman min gida a banza, Shara, mopping, goge da sauran su na can dakunan” ya nuna dakunan da ke side inta “sannan parlour duka biyu da kuma kitchen ban bukatar ki taba min komai a nan dakunan” ya nuna side in shi “sai kuma kitchen akwai kayan abinci duk abin da bbu ki rubuta ki ba David house boy INA ne zai hada da sauran abubuwa, kuma kar ki sake ki ce zaki dinga girki da ni sanin kanki ne ba zan iya cin jagwalgwalan ki ba sannan yau ya za mo na karshe da zan kara fito wa in same ki a falo, dakin can kadai na baki daman zama kina iya komai a cikin shi ciki ko hadda cin abinci, hakan ma Dan ba yanda na iya so ki kiyaye mu rabu lfy zuwa lokacin da zan samo dalilin da zai sa A warware wannan hadin ko kadan ni ba ajin ki bane so kar ki taba sa wa ranki akwai ranar da zai zo mu yi irin zaman da ake miki nasiha akai, No way ma so ke ma in kin gaji its free you can also find your way, daga yau kar ki bari in sake ganin ki domin hakan kadai ba ta min rai ya ke kaf mata a rasa wacce za a bani sai ke, Kinsan time in ayyukan ki daga yau ko motsi na kika ji ki koma daki Allah ya gani ban bukatar ganin ki” shiru ta yi har ya gama maganganun shi sai dai ko me yace yana isa cikin jikin ta, ko kadan ba ta yi mamakin abubuwan da ya fada ba asali ma ta yi tunanin fiye da haka, sai dai ita ma ba abinda za ta yi dashi Dan ko kadan bbu burbudin son shi a zuciyar ta kai ita ko a matsayin Dan uwa ma ba ta tunanin akwai.
Tun daga ranar ta fara duk abinda ya lissafa ko a jikin ta da ke daman ba kiwuya gare ta ba hira ko daga ita sai wayan ta, Anty Amina ma ta kara dawo wa sau daya sai Umar ya kan leko ta akai akai ba ta yi tsammanin yana da kirki ba kila tausayin ta ya ke ji ko da ta fadawa su Maijidderh yanda ya ke mata su kayi ta mamaki ita dai Nanah CE wa ta yi daman mai kirkin ne.
Mopping falon ta ke ya shigo, bai yi sallama ba kuma itan ma hankalin ta gabadaya bai jikin ta ta tsunduma cikin duniyar tunani hakan ya sa bata ji motsin shi ba. Wani irin wawan rankwashi ta ji a kan ta tsabagen a zaba da firgita ya sa ta yi kanshi ta ririke shi hankadar da ita yayi ta fada kasa ta buge kai da kujera, wani kara ta saki tana haki. Sai ranar ta kara tabbatar da Uncle Aliy bai da imani kallon ta kawai yayi ya ce “Wannan shi ne punishment inki gobe ki bari mu kara haduwa” sai da ta sha kukan ta sannan ta lallaba ta tashi ranar ko abinci ba ta ci ba amma da ke ba Wanda ya damu da ita ba a ma Sani ba.
Three weeks ta yi a gidan aka koma school, Mami ta yanke shawaran kira amma ko da ta kirata har su ka gama waya ta kasa fada mata nauyin ta tmby ta me ya sa ba ta fada mishi ba ta ke ji domin kullum mamin sai ta kira ta ji ya zaman su ya ke. Ammah ta kira bayan sun gaisa ta sanar ma ta “Ammah mun yi resuming school”
“To kin fada wa Aliyu a ji yanda za a yi?”
“Aa Ammah Ku fada mai mana”
“Saboda wani dalilin ma za ki je ki fada mai kina ji na” ba yanda ba ta yi amma Ammahn ta ki haka ta hakura ta yanke shawaran tunkarar shi, a hankali ta dinga dakon fitowan shi falo kusan awa daya sannan ta fito, links ya ke daura wa a hannun shi da alamun he is in hurry amma this her only chance she won’t miss it, jiki na rawa ta karasa gaban shi wani irin kallan baki da hankali ya mata ganin ta na kara nufo shi ya sa yayi saurin dakar da ita “tsaya daga nan malama, lafiya za ki zo ki sa ni gaba”. “Mun koma school” ta amsa cikin In ina” tsakai ya buga sannan yace “hakan ne ya sa zaki karya min doka ko? Ina ruwana da karatun ki? Ni na sa ki ko ni na nasa a kawo ki garin nan” ba ta San lokacin da ta amsa mai ba “Aa amma pls ka maida ni wurin wadan da su ka kawo nin za suyi farin cikin mai da ni schl …” Saukan Marin da ta ji a fuskan ta ne ya sa ta kasa fadan abinda ta ke bakin ta, dafe wurin da ya mare ta tayi sannan ta sadda kai kasa za ta iya rantse wa shatin hannun shi ya fito akan fuskan ta wani zafaffen kwalla ta ji ya sako kan kumatun ta ba za ta iya tuna ranar da aka daga hannu a ka mare ta ba “har kin yi girman da zaki fara gaya min magana ko? To ko Deedat ba zai taba maida min magana ba balle ke kanwata ta nawa in kuma aure da kike ganin an daura ne ya sa kike ganin mun zama sa’anni to kiyi maza ki farka daga mafarkin da kike yi, this should be the last” ba ta tsaya jin karshen zancen shi ba ta ruga daki, kuka ta yi tsakanin ta Da Allah ta na mamakin wannan bakin halin Aliyu. Babban Yaya ne ya fado mata a rai tabbas uncle Aliy ba zai ki jin maganan shi ba she can’t bear loosing her studies sai dai kome zai faru ya faru.
A lokacin ta kira shi tana kuka, a rude ya ke tmbyn me ke faruwa, kasa fada mishi komai ta yi illa Aliyu ya hana ta koma wa schl lallashin ta yayi da kyar sannan ya tabbatar ma ta za su yi magana.Abinda Aliyu bai Sani ta fi shi rashin son zaman gidan da ya kira nashi Dan dai a wurin ta kufai ma ya fishi, kwana uku kenan da maganan ta da babban yaya amma shiru kake ji ba ta so kuma ta kira shi ya ga kaman tayi gajen hakuri, karatun ne kawai a ranta dan ba wai farkon komawa bane balle ace ba a komai hutun mid semester, New year da Christmas break ne so tana da tabbacin karatu ake sosai gashi 200 level ne lokacin su ke fara departmental courses insu.+
Novels in ta da su ka zame ma ta abokan hira ta zauna tana karanta wa a wattpad, English novel ne ya mata dadi sosai, ba ta Ankara ba sai ganin mutum ta yi akan ta yana huci Sam ba ta ji takun tafiyan shi ba balle kuma lokacin da ya shigo “wani sabon iskanci kika koyo ko? Ki naji ina ta kiran ki ba zaki amsa ba, well ba laifin ki bane cuta na da aka yi aka hada ni da ke ne ya jawo hakan” kan sofan ya nemi wuri ya zauna hakan ya sa ta yi saurin tashi ta zauna tana kallon kasa “Sanin kanki ne ba ki kai matsayin da zan zauna in yi maganar hankali da ke ba saboda hankalin ma ba wai kuna dashi bane, anyhow I have no choice” ya fada yana daga kafada, folding lips in shi yayi sannan ya kare ma ta kallo daga sama zuwa kasanta, tsarguwa ta yi da kanta ita ma ta fara kallon jikin na ta dogon riga baka ke jikin ta kuma ko kadan bai kama ta ba balle ace jikin ta ya fito, wani siririn tsaki ya ja sannan yace “hey calm down ba ki da abinda zan iya kallo a jikin ki INA kallon irin cuta na da aka yi” ita dai kala ba ta ce mai ba coz da zai gane ita ganin shi a gaban ta ma ba so ta ke ba talk less of maganganun da yake ma ta “Zaki koma schl kaman yanda kike bukata amma fa da sharadi” kallon ta yayi yaga expression inta ga mamakin shi attention in ta ma bai kanshi gabadaya sai dai da ka kalle ta kasan a tsorace ta ke “Kehhhhhh” wani irin tsawa ya daka mata da ya sa ta saurin dagowa tana kallon shi jikin ta ko sai bari ya ke “Ina miki magana kina wani abun? Ni tsaran ki ne?” Saurin girgiza kai tayi “Aa” ta furta muryan ta na shaking ta San karamin aikin shi ne ya ce zai taba lafiyan ta yanzu su biyu kadai a gida ba mai ceton ta “Gobe zan sa a maida ki Zaria amma fa sai kin amince you will do everything possible ki ga ba ki dawo gidan nan ba” Ganin yana kallon ta alamun yana jiran amsan ta ya sa ta tmby “How”. ” I don’t know kawai ni dai na San ban bukatar ki a rayuwa ta so find a way in ba haka to Wlh duk ranar da kika kara dawowa gidan nan ke da makaranta sai dai ki ga wasu nayi” “Na amince” ta yi saurin fadi. “Kin taimaki kanki ki hada kayan ki” mikewa yayi ya bar daki, kaman an mata albishir da aljanna haka ta dinga ji ranar kafin kace kwabo ta hada kayanta akwati biyu ciki ko ba kayan ta da aka kawo da sunan lefen ta ko daya bata taba ba.
Ta yi murnar ganin yan gidansu sosai sai dai yan uwan na ta sun koma schl dai hamza da deedat da su ka tasa ta gaba da tsokana wai ta dinga bi musu hankali da yaron su ko INA su ka ga cikin oho!. A wurin Mami ta ke jin Uncle Aliy wani course ya tafi na nine months a Florida sannan an kara mishi matsayi daga captain zuwa major, ta dai nuna ma ta ta Sani coz shi ma abinda ya nuna mata kenan apparently, Baffah ce ma ta yayi ta koma gidan Aliyun da ke nan kuda da gidan su ta zauna amma fir mami ta ki tace ba za ta zauna ita kadai ba ta zauna a gida har a ga dawo wan shi.
Aliyu namijin duniya ne na karshe har wani driver ya kawo musamman da zai dinga kai ta schl ya jira sai ta gama lectures ya maido ta duk Dan kar a zargi wani abun, duk end of month kuma sai ya aiko wa deedat makudan kudi a bata ita dai amsa kawai ta ke ta ajiye saboda dga Abbah har Baffa sun wadata ta da komai.
Duk yanda Aliyu ya so boye abun shi sai da Mami da Ammah su ka dago shi ita dai Ammah shiru ta yi kawai ta zuba wa sarautar Allah ido Mami ko sai da ta tsare Zahrau ta fada ma ta yanda su ke da Aliyu amma mai? Ita kan ta Zahrau sai ta zabi boyewan saboda su rabu lfy kar ya hana ta karatun ta.
9 months later
Zahrau karatun ta take sosai ba ta da wani damuwa ko kadan karshe ma wurin Fatima ta koma a off campus da farko kin yadda aka yi sai da ta kira Umar da ke daman ya kan kira ta akai akai ya ji yanda ta ke, shi ya tura ma ta numban Aliyun, text ta tura mishi domin ko ta kira ba ta San mai za ta ce mishi ba, reply ya mata akan ta yi duk abinda ta ga dama she is free, amma kuma wani abun mamakin da kan shi ya kira Baffah akan a barta ta je Dan Allah zai fi ma ta saukin karatu.