SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 5 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 5 BY FATYMA SARDAUNA

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dai dai ta ɗaura hanunta kan handle ɗin ƙofar kenan, aka turo ƙofar daga waje, cikin rashin sa’a ƙofar ya bugeta a goshi, saurin ja da baya tayi haɗe da rumtse idanunta gam, ji takeyi tamkar ta shaƙesa ya mutu, ta tsani ganin kowani irin namiji ne a rayuwarta, musamman ma shi,domin kuwa yanayinsu yana ma ta shige da Zaid, kuma gani take tamkar kowani namiji irin halin Zaid garesa,,

“Ganinki tsaye anan yatabbatarmin cewa guduwa zakiyi, Miye ribarki a rayuwa idan kika gudu daga gaban i yayenki ? nasan duk inda zaki bazakiyi rayuwa mai kyauba, idan kika zaɓi tafiya can wata uwa duniya mai zaki tsinta? ina mai tabbatarmiki cewa babu wani abun da zaki tsinta sai, zallan takaici, dakuma ƙuncin rayuwa, zaman bariki kikeso kiyi? kokuwa zaman kanki kike so kiyi? ” da sauri taɗago manya manyan idanunta dasuke cike tab da ƙwalla ta watsa masa wani irin mugun kallo…

“Babu abun daya shafeka da rayuwata, idan naga dama nayi kowacce irin rayuwa ma baishafeka ba, duk ba kune kuka jefa rayuwata acikin matsanancin duhu ba, wallahi na tsani naji koda kalmar farkon sunan kune a cikin kunnuwana, ballan tana aƙira sunan Namiji akusa dani, natsaneku! natsaneku!! ” wani irin kukane ya ƙwace mata maicin rai,

“Kacuceni Zaid! Kacuceni! natsaneka tsana mafi muni! mai nayi maka dana cancanci wannan sakamakon a wajenka? mai na aikata maka wanda yasanya ka cutar da rayuwata? bazan yafe maka ba Zaid! kacutar dani, karuguzamin duk wani buri nawa, ka tarwatsamin rayuwata, mai yasa saini kazaɓa maiyasa!!!” taƙare maganar cikin ƙaraji da matsanancin kuka, tamkar wanda takama Zaid ɗin a gabanta..

Wani irin mugun tausayin tane yaji ya daki zuciyarsa, haƙiƙa Zahrah abar tausayice, domin kuwa tanacikin wani hali wanda take buƙatar abokin rarrashi da kuma mai kwantar mata da hankali,,, juyawa kawai yayi yafice daga ɗakin, domin kuwa jin kukanta yake har tsakar kansa.

Nurse yaturo tazo tayi mawa Zahrah alluran bacci, domin idan ba alluran bacci akayi mata ba yana da yaƙinin cewa kwana zatayi tana ruskar kuka..

Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa, hakan ya gagara domin kuwa duk juyin da zaiyi wani irin matsanancin tausayin Zahrah ne ke cika masa zuciya, baisan wani irin tausayawa yake mawa Zahrah ba, amma tabbas yasan tausayinta da yakeyi, yayi ƙarfi a cikin zuciyarsa, da ƙƴar dai yasamu ya yakice tunanin Zahrah, a cikin zuciyarsa ya samu yayi bacci, wanda rabin mafarkansa ya kasance na Zahrah ne…

Wanene Dr S.S. ?

Dr Sadeeq yakasance ɗa na biyu a cikin gidansu, Alhaji KHABEER SARDAUNA shine mahaifinsa, Alhj Khabeer wanda ake ƙira da Alhj Sardauna, mutum ne mai matuƙar karamci da kuma kyautatawa na ƙasa dashi, hakan yasa talakawa suke matuƙar sonsa, kasancewarsa ɗan siyasa, Hajiya Habiba itace mahaifiyar Dr Sadeeq, mace ce itama mai tsananin karamci dakuma kyauta, tana da kyakkyawan hali wanda kowa yashaida hakan, Dr Sadeeq shine ɗa na biyu a cikin gidansu, yanada yaya wacce ake ƙira da Aunty Raliya, Aunty Raliya dai, tana aure ne a cikin garin Abuja, tana kuma zaune a unguwar Wuse Zone 2, bayan Dr Sadeeq a kwai ƙaninsa Samad, Samad dai baya zaune a Nigeria yana zamane a Australia, a can yake da karatunsa, tun Dr Sadeeq yanada shekaru 20, Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, mutuwar da ta matuƙar girgizasu, amma babu yanda suka iya dole su ɗauki dangana domin kowani bawa da kalan tasa ƙaddaran.. yanzu tsawon shekaru biyu kenan Hajiya Habiba tana matsawa Dr Sadeeq, a kan cewa yafito da matar aure, amma abun yagagara, da anfara maganar aure sai abun yalalace, ko daga baya yace baison yarinyar, ko yace bata da nutsuwa, da haka dai magana zata ɓalakuce,, yanzu ne Hajiyarsa ta hura masa wuta akan cewa lallai tabasa nanda kwana kaɗan yafito da matar aure dan bazata ci gaba da zuba masa idanu babba dashi ace bai aje iyali ba….

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari..

Ƙarfe 3 da rabi na yamma Dr Sadeeq da kansa ya rubutawa su Zahrah sallama, domin ya fahimci cewa matuƙar bai sallamesu ba, za a iya nemanta a rasa, bakuma zai so hakan ba.

Koda suka fito daga cikin asibitin, duk yanda yaso Zahrah tashiga cikin motarsa ya kaisu gida ƙiyawa tayi, dole haka yanaji yana gani suka tari mai taxi, baiyi ƙasa a guiwaba wajen shiga motar tasa ya rufamusu baya…

Suna isa bakin ƙofar gida, idanun Zahrah ya sauƙa a dai dai wajen da Zaid yake faka motarsa kullum idan yazo, wani irin muguwar faɗuwar gaba taji, take kuma zuciyarta tayi rauni, kuka ne ya kuma ƙwace mata, da sauri tafice a cikin motar dagudu tanufi cikin gida,, saida Inna suka sallami mai taxi kafun suka lura da Dr Sadeeq dake tsaye a bayansu yana ƙarewa yanayin unguwar tasu kallo, “A’a Likita dama kana biye damune ?” Baffa ya tambaya washe da baki,,

“Eh Baffa ina biye daku, dama gani nayi yakamata ace nasan gidan saboda magungunan ta basu ƙareba, nakuma san basha zatanayiba matuƙar ba’a tilasta mata ba”

“Ƙwarai kuwa likita ai taurin kai gareta, dole saida takurawa, to mushiga daga ciki mana ” Baffa yaƙare maganar yanamai yi mawa Dr S.S nuni da ƙofar shiga gidan.. Baiyi musu ba haka yabi bayan Baffa suka shiga cikin gidan,

Inna ce ta baje masa wani ƙaton tabarma ya zauna akai, yayinda ta ɗebomasa ruwa a kofi ta aje mai.

Gyara zama Dr S.S yayi haɗe da cewa “Baffa inaso muyi wata magana ne idan har bazaka damuba “

“Faɗi maganarka kai tsaye likita, kada kaji wani shakku” Baffa yafaɗa yana mai dawo da hankalinsa ga Dr Sadeeq.

“Maiyasa bazaku kai case ɗin Zahrah kotu ba? yakamata ace amatsayinta na marainiya a bimata haƙƙinta, bai kamata ace wani ƙaton banza ya keta mata haddi ba, sannan kuma abarshi yaci gaba da walwala, inaga yakamata ayi wani abu akai” Dr Sadeeq yafaɗa cike da damuwa.

Nannauyar ajiyar zuciya Baffa ya sauƙe haɗe da jinjina kansa, cike da rauni yace “Bazanƙi shawaranka ba likita, sai dai a gaskia bazan ɓoye maka ba, hakan da kake so bazai samuba, domin yanda ka ganmu nan haka muke rayuwarmu, mu talakawa ne, cin yau da ƙyar na gobe da ƙyar, kuma maganan nan ma da nake maka, bansan wanene yayi mawa Zahrah fyaɗe ba, to ka ga kenan babu batun ma ɗaukar fansa”

“Wanene ZAID ?” Dr S.S ya tambayi Baffa.

Washe da baki Baffa yace ” shine yaron da Zahrah ta amince dashi, yake zuwa zance wajenta, idan kuma bazaka mantaba ai nafaɗa maka shiɗin yaron kirkine, na tabbatar da cewa baisan haka yafaru da ita ba, da nasan dole zaizo” Baffa yaƙare maganar yana mai jinjina kai..

“Shine yayi mawa Zahrah fyaɗe !” Dr S.S yafaɗa murya a kausashe,

Gaba ɗaya idanunsa Baffa ya zaro, alamar maganar ta dake shi, “Zaid fa kace likita !” Baffa yafaɗa cikin kaɗuwa,

“Ƙwarai kuwa domin kuwa jiya ta ambaci sunansa, nakuma ji da kunne na, amma tunda kace ba zaku kai case ɗin kotu ba, bakomai ni zan wuce” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai miƙewa tsaye, bayan yaciro damin kuɗi ya a jewa Baffa kan tabarma,,

“A’a hadda ɗawainiya haka likita? to to munagodiya!” Baffa yafaɗa cike da farinciki,

(hmm mai hali dai baya fasa halinsa)

“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Malam hayaƙi, hayaƙi Malam a ɗakin Zahrah !!” Inna tafaɗa cike da tashin hankali, ai da sauri Dr Sadeeq da baffa, suka nufi ɗakin Zahrah’n wanda hayakin haryasoma cika tsakar gidan, dayake ƙofar bata da wani ƙarfi duka ɗaya Dr S.S yayi mawa ƙofar ɗakin tabuɗe, gaba ɗaya ɗakin yaturnuƙe da hayaƙi yayinda wuta kecin wasu kaya dake aje tsakiyar ɗakin, gefe da kayan kuma Zahrah ce durƙushe tana kuka, har wutan yakusa ƙarasowa gareta,

STORY CONTINUES BELOW

Cikin zafin nama, Dr Sadeeq yasanya hanunsa, ya janyeta daga tsugunnen da take, kai tsaye waje yafito da’ita, domin kuwa hayaƙin yasoma shiga cikin maƙoshinsu, Baffa da Inna kuwa ruwa suka ɗebo suka kashe wutan,

Riƙeta yayi gam yayinda ya kafeta da idanunsa da suka rune tsabar ɓacin rai,

Baisan meyake damuntaba, rashin hankaline ko kuma sangartane baisaniba, yasan cewa tanajin ciwo a cikin zuciyarta, amma abun da take ƙoƙarin aikata mawa kanta, kama yake da taɓin hankali, ƙoƙari yayi wajen danne zuciyarsa, haɗe da saisaita muryarsa, “Maiyasa Zahrah ? bazaki ɗau ƙaddaranki ba ?” yayi mata tambayar cikin tausasa murya, hawayene suke gudu haɗi da ambaliya akan fuskarta, gaba ɗaya jitakeyi duniyar najuya ma ta, dawowanta gida yasake tada mata da mikin dake maƙare cikin zuciyarta, duk da kuwa dama cewa mikin bai wau ya kwanta ba ne,,

Saurin saketa yayi sakamakon ƙarasowar Baffa da Inna wajen, zamewa tayi aƙasa dabas tana mai sakin kuka,

Kallon Baffa Dr Sadeeq yayi, kafun Baffa yace komai Dr Sadeeq yace, “Baffa ni nawuce sai nasake zuwa “

“To Likita mun gode ka gai da gida ” Inna da Baffa suka haɗa baki wajen faɗa, da “To” kawai Dr Sadeeq ya amsa musu haɗe da sa kai yafice daga cikin gidan,

Kama hanun Zahrah Inna tayi suka zauna akan tabarma, cike da damuwa Inna tasoma cewa “Maiyake damunkine Zahrah ? sai kace akanki aka fa ra yin fyaɗe? gaba ɗaya duk kinbi kinɗaga hankalinki, muma kin ɗaga mana namu hankalin, a gaskia nida Baffanki munsoma gajiyawa da wannan halin naki, bayan kinso caka mawa kanki almakashi, likita ya hana, yanzu kuma ƙona kanki kikesonyi, wai kina cikin hankalinki kuwa Zahrah?”

“Gaya mata dai Salame, domin nima nan nasoma gajiya da rarrashi, yanzu dakika ƙona kayayyakin daya baki, shiɗin kika ƙona ne? tambayanki nake shiɗin kika ƙona ?” Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa, domin ya lura idan suka biyewa Zahrah tofa bazata taɓa daina yunƙurin kashe kanta ba..

Zuciyar Zahrah ne tasakeyin rauni, ” Allah sarki ni, komai nayi, ganin laifina suke, shin bancancanci rarrashi da kulawaba? fyaɗe akayimini amma hakan baiwani shiga jikin kowa ba, natabbata idan da iyayena suna da rai, to tabbas da bazasu taɓa kwantar da hankalinsu ba, kuma nasan dolene sai sun ɗaukarmin fansa, bakuma zasu taɓa gajiyawa daniba, wayyo Allah na mutuwa tayi mini yankan ƙauna daku iyayena !!” maganar da Zahrah take faɗa kenan a cikin zuciƴarta, hawayenta ne suka sake tsananta zuba, sai yau ta tabbatar cewa Maraici bashi da daɗi, sai yau tasake tabbatar da cewa Allah ne kaɗai gatan ta, Zaid ya cuceta, yayi mata babban tabo wanda hargaban abada ba zata taɓa mantawa dashi ba, “maiyasa Zaid ?” tasake tambayar kanta bayan kuma tasan bata da amsa,,

Haka Inna da Baffa suka wuce ɗaki suka barta zaune a tsakar gida tana tsiyayar hawaye, babu mai rarrashi.

Tuƙin mota yake amma gaba ɗaya hankalinsa yanaga yanda yabaro Zahrah, tsantsar tausayinta yakeji, yanason taimaka ma ta amma to tayaya? ta wacce hanya? duk alokaci ɗaya ya tambayi kansa, wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, Zabba’u shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da ɗaukan wayar yakara a kan kunnensa,

“Cike da sangarta Zabba’u tayi masa sallama, amsa sallaman yayi a daƙile haɗe da cewa “Ganinan zuwa” ƙit yakashe wayar haɗe da cillata kan kujeran mai zaman banza, shi sam baisan yanda zaiyi da Zabba’u ba, amma a zahirin gaskia ɗabi’u da tarbiyanta basu masa ba,duk da kuwa cewa ƴar uwa take a garesa.

New York City

Tsaye yake agaban wani tangamemen cupboard paper, wanda yake liƙe ajikin wani abu kamar allo, sanye yake da 3 guater jeans, yayinda yabar gaba ɗaya surar jikinsa a waje, kasancewar baisanya rigaba, babban abun ɗaukar hankali ajikinsa shine lafiyayyun, 6 packs ɗinsa, dake kwance raɗa raɗa akan cikinsa, riƙe yake da wani dogon pen a hanunsa da’alama dai wani abu yake zanawa mai mahimmancin gaske,, ƙayataccen murmushinsa yasake, haɗe da ɗaukan glass cup ɗin da wine ɗinsa ke ciki, yakai bakinsa, saida ya shanye duka wine ɗin dake cikin kufin, kafun ya aje kofin kan wani ɗan ƙaramin table dake kusa dashi,

STORY CONTINUES BELOW

Hanunsa yasanya akan kyakkyawar fuskar daya zana a jikin cupboard paper ɗin, a hankali yashiga shafa zanen , hanunsa yakai dai dai saitin bakinta, haɗe da shafawa, idonsa ɗaya yakashe haɗe da lasan laɓɓansa,

“Kinkasa barina My Sugar Baby, maiyasa ? ” yayi tambayar yana mai tsare zanen dake jikin cupboard papern da ido,

“Bazaki amsaminba ko? fushi kike dani ko sugar baby na?”

Yasake tambayar wannan zanen dake jikin cupboard paper’n.

Murmushi yakumayi haɗe da matsawa daf da cupboard paper’n bakinsa yaɗaura adai dai kumatun ta yamanna mata kyakkyawan kiss, “Kikulamin da kanki kinji My Zahrah!!” yafaɗi maganar cikin shauƙi,, sai alokacin nalura ashe zanen fuskar Zahrah ne raɗau ajikin cupboard paper’n, bakaɗan ba kuma zanen yayi kyau,, kyakkyawan ƙyalle yasanya yarufe zanen, haɗe da ɗaukar wayarsa yafice daga cikin ɗakin…

Yana fita falo Abid dake tsaye tun ɗazu yana zaman jiransa, ya saki tsuka, haɗe da cewa ” Wai don Allah maika tsaya yi ? tun ɗazu fa kasan nakejiranka, amma ka shanyani “

Zama Zaid yayi akan kujera haɗe da jawo kwalbar wine ɗinsa, yashiga shan abunsa, ganin haka yasa Abid sauƙe ajiyar zuciya haɗe da girgiza kai, wato dai yau ƴan halinne suka motsa, gaskia Zaid yanada wuyan sha’ani, bakoda yaushe kake gane gabansa da bayansa ba, duk da kuwa tsananin sabon dake tsakaninsu, amma shi kansa wataran idan Zaid ya juye tofa baya iya gane masa.

“Kana yawan shan wine Zaid, baka tunanin zata iya janyomaka matsala nan gaba ?” Abid ya tambaya cike da kulawa, domin kuwa, shi ko za’a kasheshi bazai iya shan rabin wine ɗin da Zaid yakesha a rana ba,

“Maiyashafeka da shan wine ɗina ?sanin kankane natsani sa’ido ” Zaid yayi maganar cikin haɗe fuska,

Dariya Abid yayi, domin kuwa yanzu yatabbatar cewa Shu’umin cin nasa ne ya motsa, “Okay i’m sorry bazanƙara ba, amma yakamata ace musauƙa ƙasa, babes ɗin nan fa suna jiranmu ” Abid yafaɗa yana mai duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa,

“Kaje kawai ka sallamesu, nikam bana ma buƙatar ganinsu, mata duk a bubbushe, ba wani diri mai burgewa, sai kace 1, kaje can kata fama idan zaka iya” Zaid yafaɗa cike da ƙuncin rai,

Dariya sosai Abid yayi, haɗe da tashi kawai yafita daga falon, gaba ɗaya kwana biyun nan yarasa maiyake damun Zaid..

Abid na fita Zaid yagyara zamansa, haɗe da lumshe idanunsa, gaba ɗaya fuskar Sugar Babynsa ne yake yimasa gizo a cikin idanun nasa.

Abuja Nigeria

Zahrah ce zaune akan ƴar yaloluwar katifarta, ta tanƙwashe ƙafafunta, yayinda kanta ke kallon sama, ruwan hawayene kawai ke gangarowa daga cikin idanunta, kallo ɗaya zakai mata wata irin muguwar tausayinta yadaki zuciyarka, domin kuwa wani irin muguwar rama ce ta bayyana a jikinta,1

Da sallama Khausar tashigo cikin ɗakin, kamar daga sama haka Zahrah taji muryar aminiyarta ta wato Khausar, tana kai kallonta bakin ƙofa taga Khausar ɗin tsaye tayi turus,,

Ai dagudu Zahrah taje tafaɗa jikin Khausar, haɗe da sakin wani sabon kuka mai sauti, duk da cewa Khausar batasan abun dayake faruwa ba, amma tasan cewa ba lafiya ƙawartata take ba, kawai itama sai tafashe da kuka, hakanan taji wani irin tausayin Zahrah’n yacika zuciyarta, rungumeta tayi da kyau a jikinta, ko kaɗan Khausar batayi yunƙurin hana Zahrah kuka ba, saida Zahrah tayi kuka sosai, kafun ta tsagaita, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya,, hanunta Khausar takama suka zauna akan katifar Zahrah’n,,

“Zahrah!” Khausar taƙira sunanta cikin sanyin murya, Zahrah bata iya amsa mata ba, sai ɗago idanunta da suka kumbura suntum tsabar kuka, tayi ta kalli Khausar ɗin,

Zaro idanu Khausar tayi, cike da tashin hankali tace “Zahrah maiyake faruwa ne, tun ranan nake ƙiran wayarki a kashe, nazo gida kuma bansamu kowaba, nazo yafi sau huɗu bana samun kowa acikin gidan, dan Allah ƙawata kifaɗamin maiyake faruwa ?” Khausar tayi maganar cikin damuwa.

“Rayuwata taƙare Khausar, yacuceni,ya yi mini babban illa, dakuma tabo wanda bazai taɓa gogewa ba, ya nakasamin rayuwata, ashe haka ƙaddara zata zomin mummuna? nayarda cewa kowani bawa da’irin tasa ƙaddaran amma ni tawa ƙaddaran tafi takowa muni, danasan haka zata faru dani, dana roki Allah daya kasheni kafun yanzu na….” Saurin toshe mata baki Khausar tayi, cike da ruɗani haɗi da tashin hankali, Khausar tace “Kada kiyi saɓo Zahrah, kinsani acikin duhu, kisanar dani maike faruwa dan Allah, gaba ɗaya kinsani cikin tashin hankali !” Khausar tafaɗa cikin ƙosawa,

“Za..i..d yayi min fyaɗe Khausar !!!” Zahrah tafaɗa tana maisake rushewa da kuka,,

Tamkar anwatsamata ruwan zafi haka Khausar taji ajikinta, lokacin da maganan Zahrah yadaki dodon kunnenta, “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Fyaɗe fa kikace Zahrah ?” Khausar ta tambaya cikin matsanancin tashin hankali, lokaci guda hawaye suka shiga sauƙa daga cikin idanunta, take jikinta yayi sanyi laƙwas,,

“Yacutar da rayuwata Khausar, ashe haka soyayya ta ke? rama alkhairi da cuta, ashe haka duniya take cike da azzaluman bayi? maiyasa yayi min haka Khausar? mainayi masa? yaruguzamin duk wani farincikin rayuwata, wayyo Allah na Khausar ki karɓi wuƙannan ki kasheni dashi ko da zansamu sauƙi da salama acikin zuciyata !!” Zahrah taƙare maganar tana mai miƙomawa Khausar wata wuƙa da ke aje gefenta,,

Matsanancin kuka Khausar tasanya, haɗe da jawo Zahrah jikinta, ta rungumeta ƙam, kuka suka shiga yi wiwi, babu mai lallashin ɗan uwansa…

((Agaskia banson abunda wasunku sukemin,musamman masu cewa naƙara musu yawan typing, inaso kusani cewa, banda wadataccen lokaci, inazuwa makaranta, inada miji, sannan kuma nima inada wasu uzururrukan, yakamata kuna hakuri, amma wasu har baƙar magana su ke ƙoƙarin gayamin don kawai shekaran jiya nayi muku typing kaɗan, hmm wlhy kunbani mamaki, ni bana neman faɗa da kowa, saboda banɗauki duniya komai ba, shekaran jiya a matuƙar gajiye nake saboda naje school, amma haka na lallaɓa nayi muku typing, a she duk da haka wasunku basu godeba, haka sukaita ƙananan maganganu, wata har cewa take wai tagaji da wayon danake yi,koda yaushe sai nace na gaji, yes dole nagaji tun da dai ni ba engine bace, da za’ace bazan gaji ba, kuma ina da abubuwanyi. kuyi haƙuri my real fans na zage inata faɗa, wlhy raina ne yaɓaci wasu komai kamusu baka burgesu.

Nadawo gareku sisters masu cewa Zahrah tasoma basu haushi sbd abubuwan da takeyi, yaka mata ace kufahimceta, bawai inabin bayan tabane, amma yana da kyau ku yi imagine akan ya mace za taji idan har akai mata fƴaɗe?dole za taji matsanancin ciwo, acikin zuciyarta, kuma dole ne abun zai zama babban tabo wanda bazai taɓa gogewa acikin zuciyarta ba, saboda haka kuyi hakuri kuyi mata uzuri. Kuyi haƙuri nayi mistake, ƙawar Zahrah sunanta Husnah ne ba Khausar ba, kamar yanda nasa a page ɗin baya, Husnah nakeson sawa, to bestyna saita tsayamin arai nasa sunanta,lol.)+

Kuka suka shugayi wiwi babu mai lallashin ɗan uwansa, da ƙyar Husnah ta’iya tsagaita kukanta,haɗe da daidaita nutsuwarta, duk da cewa zuciyarta bata daina bugu ba, tamkar ƴar uwa ta jini haka ta ɗauki Zahrah, saboda haka duk wani abu daya faru da Zahrah tamkar da ita yafaru, domin kuwa abokin kuka shi’ake gayawa mutuwa, wannan abotar tasu tasamo asaline tun suna yara, haka kuma sun ƙulla abotansu cikin gaskia da yarda da juna,,1

“Bazance miki kidaina kuka ba, Zahrah domin idan nace miki haka, banyi miki adalci ba, sai dai zan sake tunatarmiki cewa akwai Sarkin sarakuna, mai tausayi ga bayinsa, mai amsa addu’an bayinsa, mai basu, mai kuma hanasu, shi ishashshene akan dukkan komai, yanaji,kuma yana gani, sannan kuma shi ya wanzar da faruwar haka a gareki, tunkafun ya halicceki ya tsara, cewa hakan zai faru a kanki, kada kiyi jayayya Zahrah, domin kuwa babu wani bawa a duniya daya isa ruguza tsarin Allah, Allah baya bacci, yanasane da wanda sukayi cuta, dakuma wanda aka cuta, zaifi kyau ki miƙa al’amuranki garesa, haƙiƙa nasan cewa abun da Zaid yayi miki, abune mafi matsanancin ciwo acikin rayuwar ƳAMACE, amma kashe kai, ko kice a kasheki banaki bane Zahrah, rungumar ƙaddara ita tafi dacewa dake, haƙiƙa nasan cewa har gaban abada bazaki mantaba, amma inaso kiɗauki ƙaddaranki, kimiƙawa Allah lamuranki, da sannu zakiga sakayya, ke ba jahila bace, da iliminki na addini dana zamani, saboda haka inaso kiyi amfani da wannan ilimin naki wajen ɗaukar ƙaddaranki hanu bibbiyu, kada kice na faɗi haka ne don banasonki, wlhy inasonki ƙawata, inajinki tamkar jinin jikina, kawai dai hakan shine mafita !!” Husnah tayi maganar cikin tsananin tausayawa, yayinda ruwan hawaye suka gama wanke fuskarta…

A hankali Zahrah taɗago idanunta dasuyi jajur tamkar anwatsa musu garin barkono, ta kalli Husnah, sosai maganar Husnah yadaki zuciyarta, sai dai yazame mata dole shiga ƘUNCIN RAYUWA, da ace zata buɗewa mutane ƙirjinta suga, cikin zuciyarta, to tabbas da tayi hakan, domin tasan duk wanda yaga ciwon dake mamaye da zuciyarta, to tabbas dole ne zai koka mata, domin kuwa wani irin danƙareren ciwone yabaibaye zuciyarta, wanda batasa ran zata warke har gaban abada,

” Ashe babban kuskurene ɗaukar soyayya ka bawa wanda yafika? menene aibuna dan nafito a mace? me maza sukaɗauki mata ne? a she dan kana talaka shikenan kai bakomai bane? bakuma ka da ƴanci? ya ketamin haddina da ƙarfin tsiya, yanunamin ƙarfi da kuma fifiko, duk dan kawai ina mace, maiyasa ya tsalleke dukkan mata yazo kaina nida banda kowa sai Allah? nayi masa kuka, nayi masa magiya, na roƙesa amma ya toshe kunnuwansa, yacire duk wani imaninsa ya cutar da rayuwata, kigayamin miye laifina dan nafita cikin hayyacina ? ki faɗamin shin bancancanci in haɗiyi zuciya in mutu ba, f…ya…ɗ…e fa yayi mini Husnah!!!” Zahrah tafaɗi maganar cikin matsanancin kuka,

STORY CONTINUES BELOW

Duk yanda Husnah taso ta sake danne zuciyarta kasawa tayi, kawai sai ta sake sakin kuka haɗe da rungume Zahrah ƙam acikin jikinta,

Saida sukayi kuka sosai, kafun suka soma sakin ajiyar zuciya, take zuciyar Husnah tayi sanyi, amma banda ta Zahrah, domin babu wani sanyi daya ragewa zuciyar Zahrah.

A hankali Husnah tashiga shafa bayan Zahrah, wacce haryanzu sheshsheƙan kuka take,

” Ki tsaida kukanki Zahrah, kuka baya maganin komai, sai dai ya sanyamiki ciwon kai, addu’a ita kaɗai ce magani, nasanki Zahrah, inakuma da yaƙinin cewa baki kai kukanki ga Allah ba, kiji rani inazuwa ” Husnah tafaɗa tana me miƙewa tsaye, kaitsaye ficewa tayi daga ɗakin, yayinda Zahrah tafaɗa kan katifa taci gaba da kukanta,,,

Mintuna kaɗan Husnah tashigo ɗakin hanunta riƙe da wasu magungunan da likita ya kawowa Zahrah, wanda takarɓo wajen Inna,,

Ledan da tashigo dashi ta jawo, haɗe da ƙarasowa wajen Zahrah, tamkar ƴa da uwa, haka Husnah ta jawo Zahrah jikinta, cike da tausayi haɗi da rauni tace ” Kidaina kuka dan Allah Zahrah, kinga ko na tahomiki da abincin da kikafi so, Shinkafa da Kifi, Mom ce ta dafa ” Husnah taƙare maganar tana mai buɗe wni kula, wanda ta ciro a cikin ledan da tazo dashi,

“Nasan bakici komaiba, kuma koda nace kici ma, cemin zakiyi kin ƙoshi, amma dan Allah kici ko kaɗanne zanji daɗi Zahrah, baki da kowa sai Allah, amma kada kimanta nidake tamkar gudan jini muke, damuwarki damuwata ce ” Husnah tafaɗa tana mai zub da ƙwalla,

Kallonta Zahrah tashigayi, take kuma zuciyarta ta karye, sai kawai tafaɗa jikin Husnah, tashiga sauƙe ajiyar zuciya,,

Cike da lallami Husnah tashiga bawa Zahrah shinkafa da kifin da takawo, duk dacewa maɗaci yafi abincin daɗi a bakinta, amma hakanan ta daure takeci, badon komaiba sai don Husnah tacancanci tayi mata komai a rayuwarta, itace mace ta farko data fara bata kyakkyawan kulawa wanda tunda abunnan yafaru da ita babu wanda yabata, sai likita..

Duk da cewa bata wani ci mai yawa ba, amma zaiyi mata amfani, domin kuwa cikinta yajima ba’asa mai komai ba a cikinsa,,

Husnah nagama bata abincin, ta ɗauko musu Al’Qur’ani guda biyu, miƙawa Zahrah ɗaya taƴi, haɗe da buɗe mata fejin farko, cemata tayi su karanta a tare, duk da cewa da ƙyar muryarta yake fita amma sosai tayi ƙoƙari wajen karanta Al’Qur’ani,n.

Babu abun da yagagari Allah, Al’Qur’ani littafine mai cike da tarin haske, yana wanke zuciyar maikarantasa, yanasanya nutsuwa ga ma’abocin karantashi, take ƙuncin dake maƙare acikin zuciyar Zahrah yasoma ragewa, sunacikin karatun wani irin bacci ya yi gaba da’ita,, take ta kwanta a wajen tahau bacci,,

Murmushi kawai Husnah tayi haɗe da ɗaukar Al’Qur’ani’n, dake riƙe a hanun Zahrah ta aje gefe,

“Kayafe ma ta ya Allah! domin nasan tsananin tashin hankali da damuwa, su sukayi tasira a cikin zuciyarta, wajen mantar da’ita kai kukanta gareka!” Husnah tafaɗa tana mai kallon sama, gudun kada ta tashi Zahrah a bacci yasanya tasoma karatun nata ƙasa ƙasa…

((Ƙawaye: bawai nishaɗantarwa kaɗai shine amfanin muba, mu mata ne, kuma mu ƙawayen juna ne, yana da kyau, mu ƙaunaci junanmu, tsegumi, ƙyashi, baƙinciki, hassada, duk banamu bane, kamar yanda akace ciwon ƴa mace na ƴa mace ce, yana da kyau muɗauki hakan da matuƙar mahimmanci, du kanmu zamuso ace munsamu ƙawa kamar Husnah, to amma ta yaya zamu samu ƙawa kamar Husnah? dole ne mu tsarkake zuciyoyin mu, mudaina mawa junanmu ƙyashi da hassada, mudaina bawa junanmu mugayen shawara, mudaina zuga wasunmu sukai kansu zuwaga halaka, kada ki bata gurguwar shawara wanda zata cutar da’ita, wai don takawo kanta gareki domin kibata shawara, kada ki zugata akan cewa ta aika ɓarna, idan har bazaki faɗa mata alkhairi ba, to kada ki faɗa mata sharri, dukanmu mata ne, kuma dukanmu zuciyoyin mu suna da rauni, ta yarda dake, saboda kunyi shekara da shekaru kuna tare, hakan yasa ta ɗauki duk wani sirrinta ta zazzage miki, maiyasa tayi haka? saboda ta ɗaukeki ƴar’uwa, tunda ta sanar dake duk wani sirrinta, mai yakamata kiyi? saiki riƙe mata amana, ki tsare mata sirrinta, amma saiki kaje ki ka tona mata asiri a wajen mutanen duniya, idan kikayi haka kincancanci a ƙiraki da suna ƙawa? maiyasa muka ɓata kanmu ? mukaraba kan abotanmu ? saboda bama iya riƙe sirrin juna, kuma bamaso kowa ya ƙaru, ko ya samu buɗi, saimu kaɗai, yana da kyau muriƙe abotarmu da kyau, domin a matsayinmu na mata idan bamuyi abota da junan muba, da waye zamuyi? da maza? suda basusan yanda zasu magance mana matsalolinmuba, sirrin mace fa sai mace ƴar uwarta, please Sisters dan Allah muyi ƙoƙari wajen gyara zuciyoyinmu, domin mukasance abokai na ƙwarai, masu rufa asirin juna.))

STORY CONTINUES BELOW

Zaune yake a katafaren wajen shaƙatawa dake farfajiyar gidan, sanye yake da riga da wando na jamfa hadda hulansa, bakaɗan ba yayi kyau, kasancewarsa matashi mai jini a jika, sannan kuma dama akwai kyau ɗin tubarkalla, Wayarsace ƙirar iphone Xs Max riƙe a hanunsa yana faman latsawa da dukkan alamu abu mai mahimmanci yakeyi, ƙamshin turarenta ne yafara cika hancinsa, a hankali yaɗago kansa yakai dubansa zuwa gareta, sanye take da doguwarriga na atamfa wanda yakama jikinta sosai, yayinda ta saƙala wani ɗan ƙaramin vail a wuyanta, balaifi tayi kyau, tunda dama kyakkyawace.

cike da takun ɗaukar hankali taƙaraso wajen dayake zaune bakinta ɗauke da sallama,

Amsa mata sallaman yayi yana mai ɗauke idanunsa daga gareta, domin komai najikinta bayyane yake a fili.

Kujeran dake kusa dashi ta ja, ta zauna, cikin sauyawa murya amo tace, “Barka da zuwa Jarumi na”

Kai kawai yaɗaga mata alamar yaji, batare daya Kuma kallon taba, sake lanƙwasa murya tayi, takuma cewa “Yakamata mu’isa falon baƙi ai, sai nake ga kamar zaman mu anan baiyiba, kasan fa kai ɗin maidaraja ne baidace ace nabarka anan ba” taƙare maganar tana mai kaɗa idanunta, alamar yanga.

“Inaganin nan ɗin ma yayi ai basai munshiga ciki ba” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai gyara zamansa,

Harara Zabba’u ta ɓallamasa ƙasa ƙasa batare daya gani ba, a zuciyarta kuwa cewa tayi “Inbanda Allah yaɗigamin soyayyarka a cikin zuciyata, da mai zai sanyani tsayawa, har ka wulaƙantani “

Ɗago da kansa yayi ya kalleta, cikin muryan dakewa yace “Ni zan wuce “

“Haba Yaya Sadeeq maiyasa kakemin hakane wai ? ko minti 30 fa bakayi da zuwa ba, amma kuma kace zaka tafi ” taƙare maganar tana kwaɓe fuska tamkar wata ƙaramar yarinya, ko kaɗan kuma hakan baimata kyau ba, domin kuwa shekarunta ya wucewa abun da take ƙoƙarin yi, (wannan saimu nida bestyna jikar Hajiya sweet 19,lol)

Hanu yasanya a cikin aljihunsa yaciro kuɗi, aje mata yayi akan table ɗin dake gabansu, haɗe da tashi tsaye yasoma tafiya,, ganin haka yasa Zabba’u daɗa ɓata fuska, cike da ƙuncin zuciya, tarufa masa baya.

Mai gadi na buɗe masa gate yafice da motarsa, Zabba’u naganin fitansa, tasaki tsuka cike da takaici, wai ace kamar ita babbar yarinyar da maza suke mararin samunta, amma wai ita wani ke wulaƙantawa, kwashe kuɗin da ya aje mata akan table tayi haɗe da sakai tayi shigewarta gida…

Zahrah kuwa ba’ita tafarka daga wannan baccin da takeyiba, sai ƙarfe 6 na yamma, lokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, har zuwa lokacin kuma Khausar tananan bata tafi ba,,1

Koda ta tashi a baccin, ji tayi gaba ɗaya tayi sakayau da’ita, a cikin kaso ɗari na ƙunci da damuwarta, babu kaso talatin, Allahu Akbar haƙiƙa karatun Al’Qur’ani warakace ga duk wani damuwar zuciya, harma da ta rayuwa.

Matsowa kusa da’ita Husnah tasakeyi, cike da tausasawa takama duka hannayenta biyu,

“Bazan gajiya da faɗa miki ba Zahrah, yin imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, shi’ake so ga ko wani musulmin ƙwarai, kuma Allah baya ɗaurawa bawa abun da bazai iyaba, idan kika ƙara haƙuri ki kaɗau ƙaddaranki, to ina mai tabbatarmiki da zaki samu kyakkyawan sakamako awajen ALLAH, haƙiƙa nasan Zayd ya cutar da rayuwarki, amma Allah bazai barshi ba, da sannu Allah zai saka miki,kimin alƙawari bazaki na yawan kukaba, sannan bazakina yawan damuwa ba, duk da nasan hakan abune mawuyaci, amma idan kika daure zaki iya, sannan kuma kuka baya maganin damuwa, karatun Al’Qur’ani kaɗai zaki riƙa, insha Allahu damuwarki zata gushe, sannan kuma, kinyi kuskure Zahrah kinbari tarin damuwar da kika shiga, ya hanaki kai kukanki ga Allah, kin manta shine maikowa mai komai, dan Allah Zahrah kimin alƙawarin cewa zaki rage sanya kanki a damuwa, duk sanda wani tunani yake shirin zuwa miki, to ki gaggauta ɗaukan littafi mai tsarki, ki karanta hakan zai sanyamiki nutsuwa !!” Husnah tayi maganganunta cikin lumana dakuma son sawa ƴar uwarta ƙwarin guiwa,,

“Bansan mai zance miki ba Husnah, amma haƙiƙa kinwuce ƙawa ke ƴar uwace, kuma koda a cikin ƴan uwanma keɗin ta da bance, namiki alƙawari cewa zan maid komai nawa ga Allah, haƙiƙa rayuwata tana cikin ƙunci da kuma baƙin ciki, amma nasan babu a bunda yagagari Allah, kuma da sannu rayuwata zatayi haske, duk da banda tabbacin hakan !” Hawayene kawai ke tsiyaya daga idanun Zahrah, domin sosai takejin ciwon abun da Zayd yayi mata, yanzu tayarda cewa dama haka Allah yatsara mata, kuma zata rungumi Ƙaddaranta, har Allah yakawo ma ta mutuwarta,, amma dudduniya bata taɓa jin matsanancin tsana ga kowa ba bayan Zayd,,

Sosai Husnah tabawa Zahrah shawara masu amfani, wanda zasu taimaka wajen cireta a damuwa,, saida akayi sallan Isha kafun driver’n gidan su Husnah yazo ya ɗauketa…

Tiryan tiryan Baffa ya ɗebi ƙafa, har ofishin Alhaji Umar, gaba ɗaya abun da yafaru da Zahrah, Baffa ya kwashe ya faɗa masa, bakaɗan ba hankalin Alhaji Umar ya tashi, domin kuwa shi Zahrah tamkar ƴa yaɗauketa, saboda mahaifinta yayi masa taimako sosai, cikin faɗa da hargowa Alhaji Umar kecewa zai kai case ɗin koto, saurin dakatar dashi Baffa yayi, haɗe da yagyara zama, ban baki Baffa yashiga yi wa Alhaji Umar, akan cewa kada yakai case ɗin kotu, domin kuwa yaron yafi ƙarfinsu, sannan kuma idan har aka kai case ɗin kotu, tofa sunan Zahrah ne zai sake ɓaci, wanda basusan an ma ta fyaɗe bama zasu sani, sannan kuma zata rasa mijin aure, domin wasu zasuce ba fyaɗe aka mata ba, ita takai kanta, kuma dole su zasukwan a ciki, domin basu da kuɗi, a yanzu yanda rayuwar duniyar nan take, mai kuɗi shine sarki, kuma mai kuɗi shi kaɗaine mutum, haka wasu suka ɗauka, ko shari’a ake mai kuɗi shiyake nasara,, sosai jikin Alhaji Umar yayi sanyi, domin kuwa tabbas maganganun da Baffa yafaɗa haka yake, kuma yasan duk kuɗinsa bai isa yaja da wanda suka fisa ba, domin shi ɗan ƙaramin mai arziki ne akan wasu…

((Sau dayawa akan cutar damu ƴaƴan talakawa, amma bamu isa mu kai ƙara ba, mune da gaskia, amma mu’ake bawa rashin gaskia, maiyasa ? saboda mu bamu da kuɗi, wanda bashi da kuɗi kuma ba mutum bane a wajenku ko? anacin zarafin ƙananan yara dakuma ƴan mata, amma ba a iya ɗauka musu mataki, saboda kawai wanda suka aikata abun masu hanu da shuni ne, mukuma an maidamu ko’oho, Allah sarki Allah ka’iyar mana, kabimana haƙƙinmu gaduk wani wanda yazaluncemu Ameen.))A hankali yake tafiya da motarsa har yakawo ƙofar gidan, dai dai tsayawur motar tasa, Baffa ya fito daga cikin gida.+

cikin hanzari ya ƙaraso inda motar Dr Sadeeq ɗin ke fake, “A’a likita kaine da yammacin nan haka ?” Baffa yafaɗa fuska cike da annuri,

“Eh wlh nine Baffa, tun safe naso zuwa, to aikine yayimin yawa ” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin fitowa daga cikin motar tasa.

“To muje nayi maka iso zuwa cikin gidan ko, aikuwa mutumiyar taka tanacan ta kulle kanta a ɗaki, tana karatu “

“Karatu kuma Baffa? badai ta dawo normal ba ?” Dr Sadeeq ya tambayi Baffa cikin sakin fuska, domin har yaɗanji sanyi a cikin zuciyarsa daga jin maganan Baffan,

“Ƙwarai kuwa likita, ai yanzu duk wannan hargowan kukan ta dainashi!” Baffa yafaɗa dai dai sanda suka kawo cikin gidan,

Da fari’a Inna ta tarbi Dr Sadeeq, haɗe da baje masa tabarma a ɗan madaidaicin tsakar gidan nasu, shima cike da mutum tawa ya gaida ta.

Bayan sun gama gaisawanne yake tambayar ko Zahrah tana shan magungunanta ?

Take Inna tace yabiyota tayi masa iso zuwa ɗakin Zahrah’n,

Ba musu yabi bayan Inna duk da cewa yasan hakan baidace ba, amma bayida wani zaɓi sai hakan, domin kuwa shima yanason ganinta.

Zaune take akan katifa, yayinda hanunta ke ɗauke da wani ɗan ƙaramin Al’Qur’ani, tana karantawa ƙasa ƙasa, a hankali taɗago kanta jin muryar Inna abakin ƙofar shigowa ɗakin nata,

“Shigo mana likita ” Inna tafaɗa tana mai wangale ɗan yalolon labulen ɗakin,

Yanashiga cikin ɗakin, Zahrah tamiƙe zumbur daga zaunen da take, take jikinta yasoma rawa,

Ganin yanda yanayinta ya sauya alokaci ɗaya, yasa Dr Sadeeq tsayawa cak a inda yake, yana mai ƙare ma ta kallo, kallo ɗaya yayimawa idanunta, yafahimci cewa tayi kuka, take yaji ba daɗi a zuciyarsa.

“Zahrah!” yaƙira sunanta cikin muryar nutsuwa,

Kasa amsa masa tayi saima kau da kanta gefe da tayi tana mai rumtse idanuwanta, domin kuwa sosai Likitan yake mata yanayi da Zaid.

Cikin muryar nutsuwa ya kuma cewa “Kifito waje inason magana dake”

Yanakai ƙarshen zance’nnasa, yajuya yafice daga cikin ɗakin.

Tunyanasa ran fitowar Zahrah hardai yacire rai domin kuwa babu alaman zata fito ɗin.

Daga ƙarshe dai kayan marmari da kuma sauran magungunanta da ya taho mata dashi, sai Baffa ya bawa yace a bata, don yafahimci batason damuwa, kuma yafuskanci cewa tana matuƙar tsoronsa, baikuma san dalilin hakanba.

STORY CONTINUES BELOW

Tanajin ƙaran tafiyar motarsa ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, hakanan duk sanda ta kallesa takejin faɗuwar gaba, shigowar Inna cikin ɗakin shiyayi sanadiyar katsuwar tunaninta,,

Ƙatuwar ledan da Dr Sadeeq yakawo, wanda yake cike da kayan marmari Inna ta aje mata haɗe da watsamata harara gami dayin tsuka tafice daga cikin ɗakin, domin yanzu gaba ɗaya tsananin haushin Zahrah’n takeji.

Ko kallon ledan Zahrah batayiba ballantana ta duba miye a ciki, domin itakam yanzu anshata kuma haryanzu bata warke ba, don haka babu wani ɗa Namiji daya isa yasake yaudaranta, babu kuma wani Namiji da zata sake amincewa dashi a iya tsawon rayuwarta, tasan cewa ingancin rayuwarta yariga dayagama ƙarewa, domin kuwa tasan cewa babu wani namiji dazai aureta, bayan yasan cewa Zaid yariga da ya gama keta mata rigan mutumcinta.

New York City

Gudu sosai motar tasa keyi akan titi tamkar zai tashi sama, yayinda jami’an tsaron dake tsaron titi suke tayi masa magana amma bayako sauraransu, kai tsaye katafaren gidansa dake cikin New York ɗin ya nufa, tundaga fitowarsa acikin motar zaka gane cewa a matuƙar buge yake domin kuwa sai haɗa hanya yake gakuma zungureriyar kwalbar giya dake riƙe a hanunsa, yana shiga cikin katafaren falonnasa, yafaɗa kan kujera, haɗe da lumshe idanunsa,

“MY ZAHRAH!!” yaƙira sunanta cikin wani sweetness voice ɗinsa, sannan kuma cikin yanayi mai nuni da cewa mutum yana cikin shauƙi,, da ƙyar ya iya miƙewa yakai kansa zuwa ɗaki, yanashiga cikin bedroom, kaitsaye ya wuce bathroom saida ya amayar da gaba ɗaya giyan da yasha, kafun yasamu nutsuwa, amma duk da haka mayen giyan bai sake sa ba.

Buɗe drowern sa yayi, haɗe da fiddo wani irin ƙaton hoto wanda gaba ɗayansa aka rufesa da glass ma’ana akayi masa gidan glass, ba hoton kowa bane face hoton kyakkyawar fuskar Zahrah tana murmushinta mai burgewa.

Murmushi yayi haɗe da mannawa hoton kiss, cikin unique voice ɗinsa yace “Inakewarki My Zumata, haƙiƙa keɗin ta da bance, verysoon inanan dawowa gareki, har yanzu sha’awarki bata sakeni ba, banƙoshi dake ba babyna, kikulamin da kanki kinji Sweet Zahrah na!!” yaƙare maganar cike da tsananin shauƙi, domin kuwa wani irin feelings yakeji a ga me da Zahrah’n, yarasa maiyake damunsa akan Zahrah, aƙa’idansa idan yayi sex da mace sau ɗaya, to baya sake waiwayanta harsai idan ita tawaiwayesa, nan ma saiyaga dama ya amsa tayinta, amma yau gashi yana mugun kewar Zahrah saboda yasha zumanta mai daɗin ɗanɗano, haryanzu baisan menene so ba, sha’awa kawai yasani akan haka kuma ya dogara.

Haka Bacci yaɗauki Zaid yanata sambatu irin na mashaya yayinda yake rungume da hoton Zahrah akan ƙirjinsa, yana ji tamkar Zahrah’nce dakanta ya runguma a ƙirjinsa.

Washe gari bashine yatashiba sai ƙarfe 9 na safe, salati yasoma yi cike da ƙuncin rai, sam baisan maiyasa yake makara sallan asuba a kwana biyunnan ba, ( Nace Saboda Zina bata haɗuwa da ibada ) daƙyar ya’iya tashi yashiga bathroom domin gaba ɗaya jiyake jikinsa na masa ciwo,gashi kuma baida time ɗin da zaiyi gym, wanka yayi cikin mintuna ƙalilan, fitowa yayi sanye da rigan wanka ajikinsa, agurguje yamurza lotion ajikinsa haɗe da sanya hand dryer ya busar da gashin kansa, wata baƙar jallabiya yasanya haɗe da nufar inda darduma ke shumfuɗe, yatada kabbaran sallah, ko kunya bayaji.

(Tir da hali irinnaka Zaid, sallah da rana faɗe faɗe Allah yashirya)

Yana idar da sallah, ya buɗe ma’adanan clothes ɗinsa haɗe da zaro wasu riga da wando masu matuƙar kyaun gaske, koda yasanya kayan sosai suka amshi jikinsa kasancewarsu masu kalar fari, daga takalmi, belt harzuwa agogon dake ɗaure a hanunsa kalar maroon garesu, haɗaɗɗiyar rigar suit maroon colour yaɗaura akan kayannasa, take yafito a asalin Zaid ɗinsa, wato Abundance, Increase, Increment, Superabundance, Addition, Excess, Surplus, haƙiƙa Zaid kyakkyawane kuma cikakken namiji da ya isa ɗaukar hankali ko wacce irin mace ce afaɗin duniyar nan, haƙiƙa Zaid yana da kyakkyawar sura irinta cikakkun maza, haka kuma yanada matuƙar burgewa abubuwan da Zaid kedasu naburgewa suna da tarin yawa, tamkar yanda ma’anar sunansa ke da tarin yawa, shikansa yasan yayi kyau sosai, babu kuma abunda ke tashi a jikinsa sai tashin ƙamshi mai sanya nutsuwa da kuma sanya shauƙi,

STORY CONTINUES BELOW

Al’adarsa ce kullum kafun yafita saiya bawa hotonta kyakkyawan sumba (kiss), to yauma hakance takasance domin wannan hoton nata yaɗauko, ya manna mawa kiss, haɗe da maidashi ya aje, kaitsaye yafice daga cikin ɗakin, ko sauraran kayan breakfast ɗin da aka aje masa akan derny table baiyi ba yasakai yafice daga cikin Aljannar duniyar falon nasa,, yana fita yashiga cikin motarsa, kai tsaye yawuce babban hotel ɗin dazasu gudanar da meeting, domin yau sunada gagarumin meeting, zuwa yanzu gaba ɗaya duk an hallara a wajen shikaɗai kawai ake jira, domin shida ma’aikatansa ne zasuyi meeting ɗin.

Nigeria

Yau kimanin sati guda kenan tunda Dr Sadeeq yazo baisake zuwaba, ɓangaren Zahrah kuwa sosai takesamun sauƙi acikin zuciyarta, sakamakon karatun Al’Qur’ani da tariƙe babu dare ba rana, zuwa yanzu ta dangana komai nata ga Allah, tasan ko ba daɗe ko ba jima zai bi mata haƙƙinta.

Zaune take a tsakar gidannasu tazuba uban tagumi, amma a zuciyarta karatu takeyi, Inna ce kishingiɗe a gefenta, tana koran sauron dasuka addabeta kasancewar dare yasoma rufawa domin kuwa har an idar da sallan magriba,,

Baffane yashigo cikin gidan fuskarsa ɗauke da fari’a, Inna ce kawai ta amsa masa sallaman da yayi, kallon Zahrah yayi haɗe da cewa “tashi ki ɗauko hijabinki likita na jiranki a waje”

Wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, domin dudduniya a yanzu babu abun da zai ɗaga mata hankali kamar ace wai wani naƙiranta a waje, sam itakam tagama cire ƙauna da sake zuwa ƙiran wani, bata ƙaunarma koda sake fita waje ne,

“Wai ba magana nakeyimiki bane Zahrah kin shareni kuma bayan kinajina!” Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa,

Kuka Zahrah tafashe dashi haɗe da ɗago idanunta, ta kalli Baffa cikin muryan kuka tace “Baffa kataimakeni dan Allah, wallahi banso wani abu yasake faruwa da rayuwata !! “

“Ikon Allah, Malam kajita ko zata sake ɓarar mana da daman da muka samu na biyu, saikace akanta aka fara yin fyaɗe!” Inna tafaɗa cikin ɗaga murya,,

Da gudu Zahrah tajuya ta shige cikin ɗakinta haɗe da faɗawa kan gado tashiga rera kuka mai sauti, itakam batasan yanda zatayi da rayuwarta ba, batasan wasu irin iyaye bane Baffa da Inna, son zuciyarsu tayi yawa, kansu kawai suka sani, anya kuwa zasu rabauta da rahamar Allah ? cutar da maraya abune wanda ba kyau, kuma sunsani amma suke take saninsu, “Ya Allah kataimakeni !” tafaɗa cikin muryar kuka,

“Banni da’ita Salame nida itane, ai inbazata fita ba shi zaishigo cikin gidan ” Baffa yaƙare maganar yana mai nufar ƙofar fita daga gidan.

Dr Sadeeq ne tsaye a jikin motarsa yasha sky blue ɗin shadda sai tashin ƙamshi yake,

Baffa yafito fuska a sake kai tsaye yanufeshi, “Yauwa likita ka’iso saikuyi maganar acikin gida ko, kasan mutumiyar taka sai a hankali” Baffa yafaɗa still washe da baki, like namesake ɗina (fatiwasha lol), ba musu Dr Sadeeq yarufa masa baya suka shiga cikin gidan.

Yauma dai a tsakar gidan yazauna duk da cewa babu yawancin haske a tsakar gidan amma akwai hasken farin wata.

“Wai Zahrah bazaki tashi kije bane, nacemiki gashi yashigo har cikin gida, dan Allah Zahrah kada ki watsamana ƙasa a ido, kidubi girman mutumcin dayayi miki sanda kike ciwon hauka kitashi kije ” Inna tafaɗa cikin lallami.

“Ciwon Hauka kuma Inna?” Zahrah ta tambaya cike da mamaki domin dai ita a saninta batayi wani ciwon hauka ba,

“Ƙwarai kuwa kedai tashi kije kawai” Inna ta faɗa still cikin lallami, bawai don tasoba haka tasanya hijab haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.

Tun fitowarta a cikin ɗakinnata ya kafeta da idanunsa, har taƙaraso can gefe dashi ta zauna, haɗe da takurewa waje ɗaya tana matsan ƙwalla,

“Saiyaushe zaki daina kuka ne?” Dr Sadeeq yatambaya cikin tattausar murya,

STORY CONTINUES BELOW

Shiru tayi bata amsa masa ba domin jin kalamansa take tamkar zuban narkakken dalma acikin kunnuwanta,

“Matsowa yayi gaf da ita, har tana iya jiyo ƙamshin turarensa, babu wani tsoro kokuma ɗar ya sanya hannayensa akan kumatunta yashiga share ma ta hawaye, sosai jikinta yaɗauki rawa domin tayi matuƙar tsorata da hakan,

“Banason kukanki Zahrah, nasani dole kina buƙatar ayi miki uzuri, kinajin ciwo da damuwa a cikin ranki, kuma kinada buƙatar kyakkyawan kulawa, kidaina min kallon wani bare kokuma na daban, kiyi mini kallon ɗan uwanki, wanda zaki iya gayawa damuwarki, inaso kifaɗamin duka damuwarki kinji ƙanwata, nasan zakiji sanyi idan kika faɗi ko kaɗanne daga cikin damuwarki !!” Dr Sadeeq yayi maganar cikin lallashi dakuma tausasawa,

Kuka takuma sanyawa mai sauti, domin kuwa tabbas abun daya faɗa ɗin hakanne, tana buƙatar mai kulawa da’ita, tana buƙatar ɗan uwa mai ɗaukar damuwarta, saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, sakamakon jin hannayensa da tayi akan nata,

Kai ya jinjina mata batare da yace da ita komaiba, yana kallonta tayi kuka harta ƙoshi, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya, kofin ruwan dake gefensa ya ɗauka, haɗe da kawai bakinta, babu musu taɓuɗe baki ta soma sha, domin kuwa yanda zuciyarta ta bushe tana buƙatar ruwan,, saida tasha fiye da rabi kafun ta tsagaita da shan ruwan, sosai taji zuciyarta tasoma dawowa daidai nutsuwarta kuma yasoma sauƙa,,

“Yaushe zaki koma makaranta ?” Yajefomata tambayar kansa tsaye, kallon mamaki tabisa dashi, domin kuwa ko a wasan mafarki bata sake kawo sake zuwa makaranta acikin zuciyarta ba, itakam ai duk wani farinciki yawuce mata,

“Kada ki yarda da abun da zuciyarki takecewa, ba’akanki aka faraba, haƙiƙa abune mai ciwo amma idan kika daure zuciyarki, zaki iyayin rayuwar farinciki kamar kowa” Dr Sadeeq yafaɗa cike da son ƙarafafa mata guiwa,

“Kada kayi ƙoƙarin yaudarana domin kuwa sam banda wani sauran farinciki, yaruguzamin duk wani burina, to yanzu inaso kasanar dani shin menene amfanin karatuna bayan zuciyata cike take da ƙunci? kuma miye amfanin farincikina bayan rayuwata ke waye take da duhu ?, zanfaɗama damuwata domin nayarda dakai, inajin ciwo mai zafi a zuciyata bankuma san ranan warkewarsa ba, shin maiyasa zaka ce nayi farinciki bayan kasan cewa bazantaɓa samuba ?”

Ɗan gajeren murmushi yayi haɗe da matse hannayenta gam acikin nasa, “Saboda inada yaƙinin baki farinciki mai ɗorewa, amma saikin daina sakanki a damuwa “

Wani irin kallo tawatsa masa wanda yake nuni da cewa tana buƙatar ƙarin haske akan maganganun nasa.

“Zahrah ke yarinyace mai ɗauke da tarin ƙuruciya, kinaga yadace kibar rayuwarki tatafi a haka ?”

Dr Sadeeq yatambaya yana mai kafeta da idanu.

“Haka Allah yatsaramin, BAZAN BUTULCE BA, yadda da ƙaddara yana da kyau, NAYARDA DA ƘADDARA TA, saidai kuma bazan mantaba har abada, babu mai aurena, babu kuma mai tallafawa rayuwata, zanƙare rayuwata acikin ƙunci, idan har kaɗaukeni ƴar uwa kamar yadda kafaɗa, to inaso ka yi tunani shin wacce ta tsinci kanta acikin mummunar ƙaddara irin tawa akwai sauran farinciki da yarage mata?, ni yarinyace haryanzu bangama sanin rayuwaba, amma tabbas nasan mai kyau dakuma marar kyau, saboda haka rayuwata a gurɓace take, yariga daya ruguzata, bakuma zata taɓa kafuwa ta tsaya da ƙafafunta ba har abada, BANI DA ZAƁI likita amma akwai Allah ya isarmin komai!!” gaba ɗaya hawaye yagama wanke mata fuska, wannan karan ba iya zuciyarta bace tayi rauni hadda tashi zuciyar, lallai ƙaddaran Zahrah mummuna ce, amma kuma yazama dole yatsaya yakawar mata da duk wani duhu dake rayuwarta shi mai iya dawo mata da farincikin tane idan harzata amince, amma yasani Zahrah ta yanke ƙauna gaduk wani ɗa namiji,

“Likita ga abinci ko” Inna takatsemusu tunanin da sukeyi su dukansu.

Inna tana aje abincin tajuya tashige cikin ɗaki, kallonsa yamaida kan ɗan ƙaramin bakinta dake bushe, sannan yakuma maida kallonsa kan idanunta, a matsayinsa na mutum mai karantar yanayin ɗan adam, take yakaranci halin da take ciki, bayajin yunwa ko kaɗan domin saida yaci abinci kafun yafito, amma saboda dalili ɗaya yasa yajawo kwanon abincin gabansa, shinkaface ƴar gida jalof, ko mai batajiba ballantana albasa, amma haka ya share, yakai loman abincin cikin bakinsa, taunawar farko yaci karo da dutse amma haka dolensa ya basar (readers likitafa yagamu da girkin manya Inna, lol🤣).

“Zo muci” yafaɗa a taƙaice,

Saurin kallonsa tayi haɗe da girgiza kanta, domin ita yanzu abinci baya gabanta, damuwarta ma abincine a wajenta,,

Babu alamar wasa akan fuskarsa kaitsaye yanufi bakinta da hanunsa wanda yake ɗauke da ƙwayoyin shinkafa domin da hanu yakecin abincin,,

Saƙare haka tayi tanakallonsa domin wannan shine karo na farko a rayuwarta da wani ɗa Namiji ba muharraminta ba ya taɓa yunƙurin bata abinci a baki,

Kai tagirgiza masa alamar bataso haɗe da kawar da kanta gefe,

“Kinaso muyi faɗa kenan, kuma hakan nanufin baki ɗaukeni ɗan uwaba, nasan wunin yau bakisa komai a cikin kiba, sbd haka banason gardama, idan kuwa kikace bahaka ba, to akwai alluran da na taho da’ita, yanzu sainasa Baffa da Inna su riƙemin ke na yi miki har guda uku!! ” yaƙare maganar in a serious tone, aikuwa ya faɗar mata da gaba domin kuwa tsoron alluran da takeyi haryazarce tunanin mutane, “Haaaa” Dr Sadeeq yafaɗa still yana kusanta hanunsa ga bakinta, tamkar dai za abawa ƙaramin yaro abinci.

“Basaikabani ba zan iya ci!” Zahrah tafaɗa cikin raunanniyar muryarta,

“To ci ingani” Shima yafaɗa yana mai turo mata kwanon abincin gabanta, ahankali ta sa hanu ta tsakuri abincin, tamkar wacce akace ta tsakuro garwashin wuta da hanunta, daƙyar ta iya buɗe baki ta kai loman abincin bakinta, murmushi yayi haɗe da sanya hanunsa acikin kwanon abincin yasoma ci, duk da cewa ba daɗin abincin yakejiba, adole Zahrah take kai loman abincin bakinta bayanda ta’iyane kawai,,

Lomanta huɗu ta soma kwarara amai a wajen tamkar zata amayar da ƴaƴan hanjinta, miƙewa tayi daga tsugunen da take domin tasoma ɓata jikinta da amai, aikuwa wani irin jiri ne ya ɗe beta take ta faɗa kan Dr Sadeeq dashima yake yunƙurin tashi tsaye,, gaba ɗaya yatarota tafaɗa cikin ƙirjinsa, yayinda aman dake jikinta ya gogu ajikin kayansa,,

Da sauri su Inna da Baffa suka ƙaraso wajen domin tundaga ɗaki sukejin ƙaran amannata, “Lafiya likita maiyasameta kuma ?” duka suka tambaya cikin ƙosawa, da’alama dai sungaji da lamuranta.

” Bakomai inaga olsa (ulcer) ce kawai ke damunta ” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin shimfiɗeta a akan tabarman da suke zaune,

Saidai gaba ɗaya ba ƙarfi a jikinta, saboda haka duk ta narkemasa a cikin jiki, yayinda shikuwa zuciyarsa ke tsananta bugawa, addu’a yake a zuciyarsa Allah yasa ba abun da yake zargi bane ke damun Zahrah idan kuwa abun da yake zargine tabbas babban tashin hankali na gaba…

(Wani tashin hankali munbanu readers 😲, Allah yasadai bacikine da ita ba, da Zaidu ya yi aiki mai tsada 🤣 )A hankali Doctor ya kwantar da ita, cikin sanyin jiki yanufi motarsa don ɗauko jakarsa ta aiki, domin dama daga office yake yabiyo tagidannasu,, Allah yasa ba abun dayake hasashe bane yake shirin faruwa, lallaiko idan har ya zamana Zahrah ciki ne da ita, to fa shikansama yashiga tashin hankali, bawai ita kawai ba, domin yasan ɗan guntun tsarin daya shirya rugujewa zaiyi, to ina kuma ga Zahrah wacce bata gama warkewa daga ciwon dake jikinta ba, kuma ace taƙara faɗawa cikin azabar wani ciwon, tabbas yasan tashin hankalin da zata shiga sai ya take wanda tashiga a baya,, jiki a saluɓe haka Dortor Sadeeq yadawo cikin gidan, zuwa lokacin har Inna ta ɗauketa takaita cikin ɗaki.1

Tana kwance akan ƴar katifarta, sai faman sauƙe numfashi take a hankali, dagani kasan aman da tayi ya galabaitar da’ita sosai, zama yayi gaf da’ita, haɗe da kama hanunta, lokaci guda yaji jikinta yaɗau zafi sosai, kayan aikinsa dake cikin jakarsa ya ciro ya fara yi mata ƴan gwaje gwaje,

Wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe sakamakon gano abun dake damun Zahrah da yayi, duk da cewa baiyi mata gwajin ciki ba, amma a iya ɗan bincikensa da yayi ya gano cewa bata ɗauke da ciki, ulcer ce kawai tayi mata mummunan kamu, sakamakon yunwa daya samu mazauni acikin cikinta.1

Kallonsa yamaida kan Baffa haɗe da cewa ” Bawani babban damuwa bane ulcer ce, yanzu zanje na ɗauko wasu allurai a asibiti sainazo nayi mata, insha Allah komai zaiyi dai dai”

“To likita Allah yayi albarka muna godiya sosai !” Baffa yayi maganar cike da yabawa ƙoƙarin Dr Sadeeq.

Miƙewa Dr Sadeeq yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, yana fita su Inna ma suka mara masa baya.

Kwanciya tayi lamo tamkar wacce ruwa ya ƙare mawa a jiki, gaba ɗaya jinta takeyi bata da kuzari, gawani irin zafi da ƙuna da ƙirjinta keyi mata,,

Koda Dr Sadeeq ya ɗauko magunguna da Alluran da yakamata ace yayi mata, sai da ya biya ta wani katafaren wajen sai da kayan marmari yasaya mata dangin su apple da su inabi hadda abarba, bai tsaya anan ba hadda fresh milk saida yabiya ya saya, gudu yashiga sharawa akan titi, burinsa ɗaya shine yaje yabata taimako mai kyau, sosai yakejin tausayinta, saboda ta cancanci a tausaya mata, daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa idan yatuno da cewa ba ciki bane da’ita, sai yaji wani irin sanyi da nishaɗi na ratsa zuciyarsa, wanda ya alaƙanta hakan da cewa bayason tasamu ciki saboda zata sake shiga wani hali marar daɗi. (kuji shifa😏 wai hakane reaɗers?)

Mintuna ƙalilan ya iso ƙofar gidannasu.

Koda yanemi Inna da tayi masa iso zuwa ɗakin Zahrah’n, cewa tayi yashiga kai tsaye ai anzama ɗaya su yanzu ɗan uwa suka ɗaukeshi (hmm)

Yanda ya barta haka yataradda ita sai dai yanzu idanunta a lumshe suke, “Zahrah!!” yaƙira sunanta dai dai lokacin da yake ƙarasawa kusa da’ita.

A hankali ta buɗe idanunta tasauƙesu a kansa, ɗan guntun murmushi yayi mata, wanda yasanya gabanta mugun faɗuwa, domin kuwa murmushin nasa yatuna mata da murmushin Oga Babba (ZAIDU manyan maza, lol), take taji wani irin abu ya toshe mata maƙoshi, yayinda zuciyarta tayi ƙunci.

STORY CONTINUES BELOW

Aje ƙatuwar ledan dake hanunsa yayi, haɗe da zama akan katifarta ta, “Tashi ki zauna” yafaɗa yana mai kafeta da ido, kai kawai ta girgiza masa alamar bazata iya tashi ba, ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya ɗagota zaune, duk da cewa yana matuƙar jin shock idan yataɓa jikinta, amma babu yanda zaiyi dole hakan shine mafita.

Ledar daya shigo da’ita ya buɗe, haɗe da ɗauko apple guda ɗaya ya miƙa mata, kallonsa kawai tayi haɗe da kau da kanta gefe,

“Magani bazaiyi aiki a jikinki yadda ya kamata ba, harsai kinci abinci, idan kuwa kikasha magani bakici abinci ba zai wahalar dake sosai, dan Allah banason gardama Zahrah, nasan kuma kema kina buƙatar abinci, don haka ki karɓi apple ɗinnan kici, ciwon ulcer bazai taɓa sake kiba matuƙar kina zama da yunwa!!” yaƙare maganar cikin lallashi.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da ɓata fuska, sam batason cin wani abu daga garesa, amma yana ƙoƙarin tursasata dole, kuma yayi gaskia dayace tana buƙatar abinci, tabbas ita kanta tasan tana buƙatar abinci.

“Yauwa Zahrah nasan dama keɗin maijin magana ce, karɓa kici ko!” yaƙare maganar yana mai marairaice fuska, haɗe da kusanto da apple ɗin dai dai saitin bakinta.

Hanu tasa ta karɓi apple ɗin, a hankali take gutsuran apple ɗin kamar mai gutsuran magani, duk da kuwa cewa taji test ɗinshi a cikin bakinta,, tana cinye apple ɗin ya miƙo mata goran fresh milk mai sanyi.

“Ungo wannan ma ko kaɗanne kisha, nasan zai taimaka kuma idan kika sha bazanmiki allura ba!”

Saurin kallonsa tayi, don tabbatar da abun da ya faɗa, aikuwa idan dai har bazai yi mata allura ba idan tasha, to lallai zatayi ƙoƙari tasha ɗin,

“Ka tabbata bazakamin alluraba idan nasha?” tafaɗi maganar a sangarce, cikin kuma yanayi na marar lafiya,

“Bazan miki allura ba Zahrah, idan dai harkika sha, kuma koda zan miki ma kaɗan zanmiki kuma bamai zafi ba!” yaƙare maganar yana murmushi.

Take tasake turɓune fuska haɗe da turo baki.

“Nifa wasa nake miki bawata allura dazan miki !” Dr Sadeeq yafaɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

Karɓan goran fresh milk ɗin dake hanunsa tayi, haɗe da kafa kanta tasoma sha, tun asalinta ita mai son madara ce, haka kuma fresh milk yana ɗaya daga cikin abubuwan da takeso, sabo da haka sosai tasha har saida taji cikinta yacika, take kuma ɗan kuzari yasoma dawo mata, miƙo masa goran tayi alamar taƙoshi,

“Kishanye duka” yafaɗa a taƙaice,

“A’a naƙoshi” itama tabasa amsa ataƙaice,

“Okay to mai kikeson ci yanzu kuma?” yatambaya yana mai tsareta da idanu.

“Babu” ta basa amsa a taƙaice,

Kansa kawai yajinjina haɗe da ɗauko drugs ɗin daya taho mata dasu yasoma ɓarewa yana bata, sai ta rufe ido haɗe da ƙanƙame jiki sannan take iya sha, shiko dariyama take basa, bai taɓa ganin mai tsoron allura da magani kamarta ba.

Yana gama bata maganin yace ta kwanta, batayi ƙoƙarin musa masa ba, ta kwanta domin kuwa kafun yace mata kwantan, idanunta harsun fara rufewa,, “Zahrah!” yaƙira sunanta, shiru babu amsa kuma bata ko motsaba sai idanunta da suke buɗewa suna rufewa a hankali, da’alama dai yabata wani magani ne mai matuƙar kashe kuzarin jiki.

Dariya yayi ƙasa ƙasa haɗe da cewa “Yarinta da daɗi”

zuƙa zuƙan alluran daya taho dasu guda biyu, yaciro acikin ledan haɗe da haɗa komai da komai wanda ya kamata,

Riƙe alluran yayi a hanunsa haɗe da mai da kallonsa ga Zahrah wacce take kwance lamo, a hankali yasanya hanunsa ajikinta haɗe da juyata, saida ya rumtse idanunsa shima kafun ya’iya yi soka mata alluran, yana gamawa ya juyata ɗaya gefen ma yayi mata, sosai taji zafin alluran amma bata da bakin magana, sai dai hawaye da suka soma gangara daga cikin idanunta.

STORY CONTINUES BELOW

“kiyi haƙuri Zahrah ƴan mata, dolece tasa namiki alluran, inaso naga kinsamu lafiya ne!” Dr Sadeeq yafaɗi maganar cikin tausasa murya, bayan yashare mata ƙwallan dake sauƙa a gefen fuskarta, miƙewa yayi tsaye haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, bayan yatattara kayan aikinsa.

Bai taradda Inna a tsakar gida ba sai Baffa, don haka a gurguje yayi masa sallama, yatafi sbd dare yasoma rabawa.

Ɓangaren Zahrah kuwa tun kafun Dr Sadeeq yafita bacci yayi awon gaba da’ita, domin daga magungunan har alluran da yayi mata suna saka bacci.

A hankali yake tuƙin motar tasa, fuskarsa cike take da annuri, Situation ɗin Zahrah kawai yake tunawa, sosai komai nata yake burgesa, musamman ma tsoronta, hakanan yakejin kansa cikin nishaɗi idan yana tare da’ita, baikumasan dalilin faruwar hakanba.

Koda ya yi parking motarsa kai tsaye ɓangaren mahaifiyarsa ya nufa, domin yau ko gaisawa basuyi ba ya fice daga gidan,

Koda yashiga falonnata bai isketa ba, don haka kaitsaye yanufi bedroom ɗinta domin yanada yaƙinin cewa zai taradda ita acan.

Knocking ƙofar bedroom ɗinnata yashigayi a hankali, jin knocking ɗin ya tsananta ne yasa taba wa mai knocking ɗin umarnin shigowa, domin dama tana da yaƙinin cewa shiɗinne kasancewar taji ƙaran shigowar motarsa cikin gidan.

Zaune ya’isketa akan sallaya, da’alamu idar da sallan nafilanta kenan.

Harƙasa ya durƙusa ya gaidata cike da girmamawa, cikin sakin fuska itama ta amsa masa gaisuwarsa haɗe da cewa ” Ina kashigane yau tunsafe ?”

Ƙeyarsa yashiga sosawa a hankali, yayinda fuskarsa ke ɗauke da ɗan murmushi.

” Am Hajiya aikin office ne ya ɓoyeni, dana tashi kuma sai na biya ta gidansu Zahrah domin duba jikinta, to danaje sai nasamu batajin daɗi !” ya faɗi maganar fuskarsa ɗauke da alamar damuwa.

“Gidansu Zahrah kuma Sadeeq ?, to Allah ya sauwaƙa, a kwai a binci, a derny saika ɗebi iya yanda zaka iyaci, domin daganinka bakasa komai a cikin ka ba” Hajiya tafaɗi maganar cike da kulawa,

“To Hajiya zanci insha Allah” yaƙare maganar yana me miƙewa tsaye, sallama yayiwa mahaifiyartasa kafun yasakai yafice daga cikin ɗakin.

Yana fita Hajiya tasaki ƙwafa haɗe da cewa

“Nasan maganinka aure zanyimaka ko da baka shiryaba, natabbatar hakan zai sa ka rage yawan kaiwa dare a waje, kullum kai baka da hutu aiki tamkar engine, duk kuma rashin iyali shiya jawo hakan “.

Yana isa ɗakinsa yasoma rage kayan jikinsa, ɗan ƙaramin towel ya ɗaura haɗe da faɗawa bathroom yasakar mawa kansa shower, cikin zuciyarsa kuwa cunkushe take da tarin tunanuka kala kala, haƙiƙa yasan cewa yana buƙatar mace akusa dashi, domin dai shiba dutsi bane da zai zauna haka ƙiƙam ko da yaushe, dole yana buƙatar wacce zata na taimakawa wajen enjoying life ɗinsa, tun ba yauba yagane cewa yana ɗaya daga cikin maza masu yawan buƙata, amma kuma sosai yake ƙoƙari wajen shan pills wanda zasu sama masa relief, a gurguje yayi wankan yafito, wata brown ɗin jallabiya mai kyau yasanya bayan yatsane ruwan dake jikinsa, kulan abincin daya ɗauko a falon Hajiyarsa yajawo haɗe da buɗewa, jallof ɗin shinkafa ne sai coslow, kaɗan ya tsakura a cikin plate yasoma ci, gaba ɗaya tunanin Zahrah yacika masa zuciya wani irin feeling yakeji a kanta, idan yatunota sai yaji nishaɗi ya sauƙa acikin zuciyarsa, yanason komai nata, idan tana kuka tanayimasa kyau sosai, haka ma idan ta kwaɓe fuska bakaɗan ba take kyau, gaskia tana da abubuwan burgewa da yawa, da tunaninta yasamu ya kammala cin abincin duk da cewa baiwani ci mai yawa ba, saida yafita ya ɗanƴi exercise kafun ya dawo ya kwanta, domin a matsayinsa na likita yasan illan dake cikin kwanciya daga cin abinci..

Washe gari

Alhamdulillahi tatashi da ƙarfi a jikinta, sai dai ɗan abun da baza a rasa ba, tun tashinta da haushinsa ta tashi, domin jiya tanaji tana gani haka ya yaudareta yayi mata allura, bayan yagama kashe mata jiki da ƙwayoyin da ya bata, don haka bakinnan a ɗane yake ita adole tana fushi da likita.

Kasancewar yau Asabar babu aiki, yasanya bai tashiba harsai 9 na safe, wanka yayi yashirya cikin kaya masu kyau haɗe da baɗe jikinsa da daddaɗan turare, motarsa yanufa direct bayan yafito daga ɓangaren Hajiyarsa, JABI LAKE yanufa inda yayiwa Zahrah siyayya sosai.

(hmm readers kunaga zaƙewar doctor batayi yawa ba kuwa 🤔)

Yaukam har zauren cikin gidan yashiga anan yatsaya yasoma kwaɗa sallama, Cike da zumuɗi Inna dake zaune a tsakar gida tasoma amsa sallaman nasa, domin tasan bazai shigo hanu rabbana ba, sauran kayan maƙulashen da yasa yawa Zahrah jiyama ita tacinyesu.

“Iso mana likita, ai dakazo kawai ka iso, bawani nuƙu nuƙu nanma fa gidan kune !!” Inna tafaɗa fuska a sake,

Ɗan murmushi kawai Dr Sadeeq yayi haɗe da ƙarasa shigowa cikin gidan, akan tabarma ya zauna kamar koda yaushe,

Yana zama Zahrah tafito daga cikin banɗaki, daga ita sai ɗaurin zani a ƙirji sai kuma ƴar ƙaramar lufaya dake jikinta, kallo ɗaya zaka mata kasan cewa daga wanka take, saurin ɗauke idanunsa yayi daga gareta, yayinda ita kuma tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, sam bata zaci ganinsa ba awannan lokacin. Sumi sumi haka ta raɓa tashige cikin ɗakinta.

Bayan sungama gaisawa da Inna ne ya yayi shiru haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa, sarai Inna tasancewa wajen Zahrah’n yazo don haka kai tsaye tace masa yashiga yasamu Zahrah’n aciki.

Shikam harga Allah bayason shiga ɗakinta, domin kaɗaituwar mace da namiji a waje ɗaya hatsarine, amma ya ya’iya tunda yalura cewa iyayen riƙonnata ƙaramin tunani garesu.

Tsaye take atsakiyar ɗakin, saka rigarta kenan ko zip ɗin rigarma bata gama jaba, jin sallamansa yasa tayi saurin dawo da kallonta bakin ƙofar, harta fara zaton ko kunnenta ne yaji hakan ba sallamarsa bane, sai kuma taga yashigo cikin ɗakin, da sauri ta matsa jikin bango ta manne bayanta, domin gaba ɗaya bayanta a waje yake,

“Uh sorry nashigo kinasa kaya ko” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai kallonta.

Harara ta gallamasa haɗe da turo bakinta gaba, dagani kasan fushi take.

Dariya yasanya harsai da fararen haƙwaransa suka bayyana,

“Fushi kikeyi dani ko?, to ai balaifina bane, dolece tasa nayi miki alluran don ki samu sauƙi, yanzuma kuma wasu alluran nazo nayi miki” yafaɗa yana gimtse dariyarsa.

Kuka Zahrah tasanya haɗe da sake matsewa ajikin bango,

“Dan Allah kada kamin, banason allura kataimakeni!” tafaɗa cikin muryar kuka da tsoro.

“Shiiii kada kitaramana jama’a madam, ni ba allura zanmiki ba wasa nake miki ” Dr yafaɗa yana mai ɗaura yatsansa ɗaya akan laɓɓansa alamar tayi shiru.

“Ni bazansake yarda dakai ba, ai jiyama cewa kayi ba allura zakaminba, amma kuma shine kabani wani abu nasha kamin, ni bazan sake yarda dakai ba!” Zahrah tafaɗa tana matsar ƙwalla daga idanunta.

“Hahhh to ya’isa haka yanzu kam dagaske ba allura zanmiki ba, juyo na jamiki zip ɗin kinji ƴar ƙaramar ƙanwata !” Dr Sadeeq yafaɗa cikin tsokana,

“Dan Allah kafita banaso, zanzo na sameka, domin ni ba wani namiji da zai sake taɓamin jiki ehe !” Zahrah ta faɗa cike da shagwaɓa.

Wani irin zubawa tsikar jikinsa yayi, domin yanayin yanda tayi maganar kaɗai ya isa sanya jarumin namiji faɗawa cikin wani yanayi,

(Hahhhh likita bokan turai, to Zaid ma yafaɗa a wani hali, balle kai da bakasan salon mace ba 😂)

Nannauyar ajiyar zuciya Doctor ya sauƙe, haɗe da zura hannayensa a cikin aljihun wandon sa, “Shikenan to tunda kince haka, na baki two minute kacal kisameni a waje, idan kuwa bakifitoba zan dawo na sake iskeki, kuma wlh sai na danneki na jamiki zip ɗin da ƙarfin tsiya” dagajin yanda yayi maganar kasan cewa tsokana ce kawai.+

Kai kawai ta iya jinjina masa alamar cewa taji zata fito ɗin,

Ɗan gun tun murmushi Dr yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin.

Yana fita ta sauƙe nannauyar a jiyar zuciya, haɗe da sanya hanunta a bayanta, taƙarasa jan zip ɗin rigarta, zunbuleliyar hijabinta ta zura akan rigar haɗe da ficewa daga ɗakin, saboda tasan idan bata je bama tabbas zai biyota.

Zaune ta iskesa a cikin rumfar dake barandar gidan nasu, can gefe dashi ta zauna haɗe da kawar da kanta gefe domin kuwa ta lura gaba ɗaya idanuna akanta suke,

“Banason wasa matso kusa kisha maganinki !” yafaɗa babu alamar wasa akan fuskarsa.

Ɗan ƙaramin bakinta tacunno gaba haɗe da sake ɓata fuska, Allah ya sani ta tsani magani sosai da sosai, batama so ayi mata ko da zancen magani ne.

Batare da ya sake ce da ita komaiba yashiga ɓallo ƙwayan maganin daga jikin tablet ɗinsu, yana sawa a hanunsa, har sai da yagama ɓare iya wanda zatasha a yau ɗin, miƙo mata maganin yayi haɗe da bata goran ruwa,

Fuska a daƙune haka ta karɓi magananin saida ta rumtse idanunta sosai kafun ta iya haɗiye maganin, gashi dama irin magani mai ɗacin nan ne,

“Kishirya next week zaki koma makaranta ” Dr Sadeeq ya faɗa yana mai latsa wayar da dake riƙe a hanunsa, bakuma alamar wasa akan fuskarsa.

Saurin dawo da kallonta garesa tayi, haɗe da girgiza kanta, “A gaskia ni bazan sake komawa makaranta ba !” Zahrah tafaɗa cikin ɓata rai,

“Maiyasa ? ” Dr Sadeeq ya tambaya kai tsaye.

“Saboda babu amfanin hakan, ana karatune don a inganta rayuwa, to nikuma tawa rayuwar tajima da rugujewa, mai yasa zanɓata lokacina wajen gyara abun da bashi da kyau, bakuma zai gyaruba, na haƙura da komai zanjira mutuwata kawai !” Zahrah taƙare maganar cikin yanayi mai nuni da cewa zuciyarta tagamayin rauni,

” Idan ginin gida ya ruguje, ƙoƙari ake a sake gyarasa, akuma sabuntasa har yafi nada ɗin daya ruguje kyau, da kuma ƙawatuwa, shin kinsan maiyasa ake yin hakan? ” Dr Sadeeq ya tambayeta bayan yamai da gaba ɗaya nutsuwarsa gareta.

“A’a” tafaɗa a taƙaice.

“Saboda yanada matuƙar amfani gamasu shi, sannan kuma yana da kyau idan karasa dama ta farko, kasake neman wata damar, domin sau dayawa anasamun nasara ne a gaba, bawai a farko farko ba, idan kika ci gaba da kashewa kanki ƙargin guiwa, to zuciyarki zata zama mai tsananin rauni, babu amfani idan kikace bazaki inganta rayuwarki ba, amma inaso kisanar dani fa’idan yin hakan, nuna kin yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin mantawa da komai, idan kika zauna a gida, bazaki taɓa samun cigaba ba, nasan abun da Zaid yayi miki har yau yana cikin zuciyarki, kuma inada tabbacin cewa idan kinsamu wadataccen ilimi nan gaba, zaki iya yaƙi da azzalumai irin su Zaid, please Zahrah kada kicemin a’a, nayi hakanne saboda samamiki sauƙi, da kuma cireki a kaɗaici !” Dr Sadeeq yaƙare maganar cikin muryan tausasawa, dason ƙara mata ƙarfin guiwa.

STORY CONTINUES BELOW

Hawayen da suka shiga ambaliya akan fuskarta ta sanya hanu ta share

” Yar zuwa yau banajin akwai wani sauran farinciki daya ragemin a gaba, da wani ido mutanen duniya zasu kalleni? wasu zasu ɗauka cewa ni nakai kaina garesa, wasu zasumin dariya wasu ko zasumin Allah ya daɗa, babu wani namiji da zai tunkareni da sunan soyayya, rayuwata a yanzu tana gudana ne tamkar ruwan shayin da aka sa ma sa lipton amma ba asanya sugar da madara acikin saba, dan Allah kada ka matsa akan cewa lallai saina koma…..”

“Ya’isa haka Zahrah, banason yawan gardama, shin bazakiyi ƙoƙari ki inganta rayuwarki ba? haƙiƙa Zaid yacutar dake, amma hakan bawai yana nufi ya ƙarar da rayuwarki bane baki ɗaya, matan da akamawa fyaɗe suna da yawa a duniyarnan, amma kuma hakan bai sa sun tauyewa kansu wani nau’i na jin daɗin rayuwarsu ba, ke mai yasa bazaki yi haka ba ? inaso ki manta da komai, kuma daga yau ɗinnan nagama maganata, next week zaki koma school insha Allah, tun yanzu saiki fara shiri !” Dr yafaɗa fuskarsa babu alamar wasa.

Aikuwa yanayin yanda taga fuskar tasa a ɗaure tamau yasa takasa ce dashi komai, hakanan yake mata kwarjini a cikin idanunta.

Miƙewa yayi tsaye, haɗe da cewa “Kibiyoni waje inason muyi wata magana”

Saurin kallonsa tayi, domin ita rabonta da fita waje tun randa mummunar ƙaddaranta ya rusketa, wanda kuma da bazata taɓa mantawa ba.

Jiki a saluɓe haka ta rufa masa baya, suna zuwa bakin motarsa taja ta tsaya, haɗe da sake tamke fuska.

Murfin ƙofar mai zaman banza ya buɗe haɗe da fiddo wata ƙatuwar leda,

” Idan har kika kumamin musu to tabbas zamu ɓata dake, sannan kuma wlh allurai shida zan danneki na miki da ƙarfin tsiya bandamu ba koda ma sun karye a cikin jikinki, ke kikaso!” Dr Sadeeq yafaɗa cikin tsare gida, yayinda yake miƙo mata zungureriyar ledan dake hanunsa.

“Dan Allah kayi haƙuri kada kamin allura, amma a gaskia ni baxan iya karɓan komai daga gareka ba, ni bazan sake karɓan abun kowa ba, domin kuwa da haka Zaid yasamu ya cuci rayuwata yasamin babban tabo mai wahalar gogewa!” Zahrah tayi maganar cike da tsoro da kuma ƙunan zuciya.

“Alluran dai kikeso kenan, shikenan bana ɗaukosu dama nazo dasu kusan guda goma” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai niyar sake buɗe murfin motar.

A tamanin Zahrah ta ruga zuwa gida,

Dariya sosai Dr Sadeeq yashigayi, sosai yarintar Zahrah yake burgesa, haƙiƙa Zahrah yarinyace, domin kuwa kallo ɗaya zakai mata ka fuskanci cewa tsananin yarinta na damun ta sosai, akan allura gaba ɗaya ta ruɗa kanta.

Baiyi yunƙurin komawa cikin gidan ba, sai neman wani yaro yayi yabasa ledan yace ya kai cikin gidan, shikuwa key yayi mawa motarsa yayi tafiyarsa.

Zahrah kuwa tana shiga cikin gidan kaitsaye ɗakinta tawuce haɗe da banko ƙofar ta rufeta gam, faɗawa tayi kan katifarta tana mai sauƙe a jiyar zuciya, ko da taji ƙaran tashin motar Dr Sadeeq ɗin, wani sanyi taji a cikin zuciyarta, haka kawai yazo ya zurkuɗa mata wannnan maka makan alluran nasa, ai wlh bata saɓuwa…..

*New York City*

Kwance yake akan makeken gadon sa, daga shi sai ɗan wani 3 guater jeans, yayin da ya ware ƙafafunsa, duk da cewa akan gado yake, amma saboda tsabar iskanci irin na Zayd sanye yake da takalma (toms) aƙafarsa, yayinda hanunsa ke riƙe da wata zungureriyar kwalbar giya, gefensa kuwa wata kyakkyawar baturiya ce kwance tsirara bako ɗigon abun rufa tsiraici a jikinta, daganinta kasan irin cikakkun ƴan iskan nanne, gaba ɗaya ta tsare Zaid da idanunta, sai wani lasan baki takeyi tamkar tsohuwar mayya, bakomai yasa hakan ba, face yanda gaba ɗaya ta gama kwaɗaituwa da Zaid ɗin, amma kuma yaƙi amincewa ya kusanceta, gaba ɗaya wani irin muguwar sha’awarsa takeji, duk kuwa yanda ta nu namasa zallan karuwancinta a fili, yaƙi kusantar ta, saima sake je fata cikin kogin sha’awa da yayi,

Zaid kuwa da gangan yaƙi kusantarta, domin yanzu tsagwaran iskanci yake ji dashi, sai ya ɗauko mace yagama ƙwaƙuleta, yabarta batare da yayi sex da’ita ba, wayarsace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, har ƙiran ya katse Zayd bai ko kalli inda wayar take ba balle yasan wake ƙiransa,,

Cike da salo irin na ƴan bariki wanda ta yarda cewa idan hartayi masa zai kusanceta, ta sake matsowa daf dashi, a hankali ta zura hanunta acikin 3 guater jeans ɗinsa, haɗe da soma shafa kan mararsa a hankali, yayinda ɗaƴan hanunta ke kan faffaɗan ƙirjinsa tana shafawa slowly, ta yadda zaiji abun har tsakiyar kansa, cike da ƙwarewa tashiga murza ….

A hankali yaɗago idanunsa da suka soma sauya launi ya sauƙesu akan baturiyar, ai kuwa yayi kyakkyawan gani, domin kuwa fuskar Zahrah yagani ta bayyana akan ta baturiyar, bakomai yasa hakan ba face giyar da yasha da tasoma yi masa aiki, da ƙarfin gaske yajawo baturiyar jikinsa, haɗe da matseta ƙam a ƙirjinsa, take jikinsa yasoma ɓari,lokaci ɗaya yashiga bata kyakkyawan romance wanda yasanyata tafara nishin daɗi.

Gaba ɗaya baturiyar nan tadawo masa Zahrah acikin idanuwansa, baisan sai yaushene matsanancin sha’awar da yakemawa Zahrah zata sake saba, a kullum a ko wani daƙiƙa sha’awar Zahrah sake ninkuwa masa takeyi acikin zuciyarsa,

Hmmm duk jaraba irin ta wannan baturiya yau fa sai dai ta haƙura, domin kuwa Zaid tun kan abunnasa yagama shiga jikinta, yayi saurin tureta gefe, wani irin masifaffen ɓacin raine yazo masa, ƙarya ne yasani ba Zahrahn sa bace wannan, sharrin giyane kawai, idan har giya zata iya sanyawa yaga fuskar wata a matsayin Zahrah, to bata isa sawa ɗanɗanon wata yakasance tamkar na Zahrah’nsa ba, Zahrah da ban take komai nata na dabanne, cikinta a cike yake, bakamar sauran matan dayake mu’amala dasu ba, wanda su gaba ɗayansu a wage suke daga ciki har waje, ita kuwa Zahrah daga ciki har waje a haɗe take, bakomai yasanyashi ture baturiyar nan gefe ba face jinsa da yayi ya faɗa zuruf tamkar anzura ƙwallo a raga, bathroom ya wuce kaitsaye yasakarmawa kansa shower.

Itakuwa mayyar baturiyar dolenta ta maida ɗan fingilan rigarta ta fice daga cikin ɗakin, cikin matsanancin sha’awa, Zayd ya jangwalo mata bala’i.

Zayd kuwa a daddafe yayi wanka, domin kuwa wani irin ciwo marar sa ke yi, koda yafito a wankan a daddafe yasha tea da lamon tsami, kwanciya yayi lamo yana mai sauƙe numfashi akai akai, lallai yazame masa dole yakoma Nigeria kodan Zahrah ma, yazame masa dole yakomawa Zahrah domin kuwa bazai zauna sha’awarta ta kashe shi ba, amma ya ɗau alƙawarin cewa wannan karon bazai mata da ƙarfi ba, lallaɓata zaiyi tabasa kanta cikin sauƙi, da wannan tunanin bacci yayi awungaba dashi,

(Hmmm ayi bacci lafiya Zaidun Munubiya,lol).

Nigeria.

Yaune ranar da Dr ya shaidawa Zahrah cewa zata koma makaranta.

Don haka tun tashinta, tatashi tanajinta wani iri, gaba ɗaya ji take gabanta na faɗuwa, hakanan take tsarge, gani take tamkar kowa yasan maiyafaru da’ita, a daddafe tayi wanka, wata simple gown tasanya ajikinta, wanda bata da ado ko kaɗan, wata ƙatuwar lufaya ta zura wanda tsawonsa ya wuce guiwarta. Jin maganarsa a tsakar gidan, yasa taji ƙirjinta ya ɗan buga kaɗan, cikin rashin kuzari tafito daga cikin ɗakin.

Kamar yanda yayi mata kyau, haka shima yaga tayi masa kyau, duk da cewa babu ɗigon kwalliya akan fuskarta.

“Muje ko!” Yafaɗa a taƙaice, saurin ja da baya tayi haɗe da girgiza kanta, domin kuwa ko karen hauka ne ya cijeta, bazata yarda ta shiga motarsa ita kaɗai ba.

“Muje Baffa na jiranmu a waje” Dr Sadeeq yafaɗa domin yaga alamar a tsorace take,

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe haɗe da bin bayansa, domin kuwa tuni yariga da yayi gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page