ABAR SO CHAPTER 4 BY NAFISAT MA’ARUF SHEHU💋(WURARH)💋
ABAR SO CHAPTER 4 BY NAFISAT MA’ARUF SHEHU💋(WURARH)💋
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nadhira batayi la’akari da cewan hospital sukeyi bah ta kurma wata iriyan wawaiyan ihu ai basu hankara bah suka jita akasa+
Mumy kam mutuwan tsaye tayi sanadiyar hango big dady kwance akan gado
Su Maryam da Fatima ma kuka sukeyi kaman ba gobe
Dakyar aka fita dasu daga dakin while Nadhira aka dauko ta akan gado
Ward akayi da Nadhira inda su mumy suka mara musu baya cikin tashin hankali
Taimakon gaggawa aka shiga bawa Nadhira cikin sa’a kuwa ta farfado
Tana farfadowa tafara”Kukaini wajen big dady”
Allura aka tsikara mata nan da nan bacci ya kwashe ta sai uwar zufa dake tsatsafo mata akan goshi da hanci
“Zan iya magana dake hajiya?” Yatambaye ta ganin halin datake cikin
Gyada mishi kai kurum tayi tareda bin bayan shi aka bar su Maryam tareda Nadhira
Zama doctor yayi akan kujeran shi tareda nuna wa mumy wajen Zama da hannu
Zama tayi ita din mah, cire glass din idonshi yayi gyaran murya yayi yace” sannu Hajiya , wato dazu neh aka kawo mijinki rai a hannun Allah sakamakon accident din da yayi”
Hawaye mumy ta share da gefen khimar tareda da Jan hanci tace” amma inace baiyi wani muni bah?”
“Maganan gaskiya hajiya saidai ayi hakuri amma kafarshi guda daya tasamu matsala sosai don haka sa hannun ki kawai muke bukata anan sai muyi mishi aiki”yafada tareda mika mata wani farin paper mai dauke da sunan hospital din
Cikin dauriya mumy tace” dole neh sai an mishi aiki neh??”
“Gaskiya yana bukatan aiki cos a halin yanzu sosai kafan zai na takura mishi”
“Kuna da kayan aikin neh anan ko za’ayi referring din mu?”
“Erh akwai kayan aiki kuma a halin yanzu akwai visiting doctor akasa”
Wata iriyan huce ta fesar sannan ta dauke biro tareda signing pepern da ya bata
Fita tayi daga cikin office din tayi ward dinda aka shiga da Nadhira
Har lokacin baccin wahala takeyi sai ajiyar zuciya mai karfi take saukewa akai akai…
Dishi dishi take kallon ceiling,waro idonta tayi dakyau cikin son sanin inda take
Nan kuwa ta tariyo abinda ya faru , gefen ta ta kalla ta hango su azaune jugum kowa yayi tagumi sun lula duniyar tunani
“Alhmdllh”ta furta ahankali tareda sakin wata munafukar murmushi na jin dadi
Saisaita kanta tayi kafin takira mumy ahankali
Dada matsawa sukayi kusa daita ahankali tace”ina big dady nah yake??”
Cikin jarumta mumy yace” aiki za’ayi mai zuwa anjima”
“Aiki!???”
“Erh wai kafarshi ya samu matsala”
Acikin zuciyarta tace”Masha Allah One done two more left” afili kuwa tashin hankali neh ya bayyana afuskarta tace”pls mumy kukaini naganshi”
Inspector Nasir dinda tin da tafarka yake kallon duka reactions dinta yakaraso gurin su yace”hajiya zaki iya kaita taganshi”
Tsarguwa tayi da irin kallon dayake mata wanda yasa takusa rasa nutsuwar ta amma kasancewan ta shu’uma yasa ta waske
Ganin yanda tasha mur yasashi shan mamaki tareda dora shakku akanta
Agefen gadon zauna bayan sun fita yace”wace ita??”
“ABAR SO kenan”Maryam tafada
“ABAR SO kuma??” Ya tambaya cikeda mamaki ganin hakan ba ainihin suna bane
“Mind her not sunan ta Nadhira but ana kiranta da either ABAR SO or Babynmu”
Gyada kai yayi yace” Allah sarki maybe itace auta ma naga yanda tashiga tashin hankali dalilin ciwon dadyn ku”
“No yar kanin dady muce ita mata dadyn ya rasu”
Kura musu ido yayi yace”haba dai??”
Ya mutsa fuska Fatima tayi tace”kwarai dagaske kuma bata Jima da dawowa gidan mu bah amma abin mamaki tinda tashigo abubuwa marasa dadi suke faru agidan mu”
Gyara zaman yayi akan gado alaman he’s interested in hearing labarin su”bangane abubuwa marasa dadi bah?”
Ba bata lokaci maryam tafara zayyano mai abubuwan da suka faru”nikam in dady ya warke gaskiya zamu mishi magana akan yakoma gidan su
Dawowar su Nadhira neh yasa su yin shiru, ganin still wannan suspect look din nan nasamar fuskar Inspector Nasir yasa ta lumshe anime eyes nata wanda yayi daidai da gangarowan hawayen daga samar fuskan ta.
“Oh Babynmu kidaina kuka mana”mumy tafada daidai ta zaunar da ita daga inda Inspector Nasir ya tashi
Maimakon tayi shiru saita kara volume din kukanta tareda runtsa idonta dakyau
Ganin zakuwarta tayi yauwa yasa yace”Miyesa kike kuka? Pls kidaina kukan nan
Dago idonta tayi takalle shi wanda daman shine abinda takeson ji daga gareshi
Maganar ta sukaji tace” bangane miyesa nake kuka bah?? Kana nufin wannan ba abin kuka bane awajen ka?babana yan…Maganar ta sukaji tace” bangane miyesa nake kuka bah?? Kana nufin wannan ba abin kuka bane awajen ka?babana yana chan kwance babu lafiya and you said miyesa nake kuka?? So ridiculous”+
Shafa keyarshi yayi cikin son waskewa yace” amma a bincike nah he is not your father”
Jim tayi tareda kallon inda su Maryam suke ganin suna sunkuyar dakai yasa ta sanin su suka fada mai
“Amma uba yake awajena koh tinda shi wan ubana na neh” tafada cikin zafi cos Inspector yana son shiga abinda ba’a kasa dashi bah
Gyada kanshi yayi tareda duban ta for some seconds sannan ya dage kai
“Toh hajiya in bazaki damu bah pls kuzo station za’a muku wasu yen tambayoyi gameda accident din daya faru” yana gama fadin hakan yayi gaba abinshi
Da ido taraka shi har ya fice kafin ta dauke idonta sannan ta lumshe kaman mai bacci tareda lulawa duniyar tunani
Ganin tana bacci yasa suka bar Maryam zalla while su suka tafi dubo Maimuna…
Kiransu akayi akan za’a shiga da big dady theatre soboda doctorn dazaiyi aikin ya iso
Rankayawa sukayi zuwa kofar theatre room tareda Nadhira da ta dage ai taji sauki
Sauri yakeyi ya je ya shige theatre room din soboda baison su dade inda Inspector Nasir na daga gefenshi
Dago idon da zaiyi yayi daidai da lokacin da Nadhira take cewa wani doctor” pls doctor kuyi iya bakin kokarin ku ganin komai ya dawo daidai cos a halin yanzu dashi kawai muka dogara”
Harde hannayenta tayi alaman roko ga hawayen gulma sunfara sintiri afuskarta tace”in wani abu mara kyau yasame shi am very sure ciwon zuciya ce zata yi ajalina”
Rungumeta mumy tayi cikeda tausayin ta ganin yanda tayi magana da dacin murya
Kowa awajen mah saida tasa tausayin ta acikin zuciyan su ciki kuwa harda Inspector Nasir wanda iyanxu yafara nadaman zargin ta da yafara da farko
Amin kam takawa yayi hankali zuwa garesu tareda zare ta daga jikin mumy ya rungumeta ajikinshi
Jin kamshin Amin yasa tayi tsit tareda kokarin cire jikinta anashi
Tureshi tayi sannan ta saita mai jajayen Amine eyes dinta, wani irin yarr yaji tun daga saman shi har kasa
“Stop crying sunshine” yafada cikin sanyi
Hararan shi tayi tareda ficewa daga wajen da suke, girgiza kanshi yayi tareda shigewa cikin theatre room din…
Tsayawa tayi cakk dalilin hango yanda idanuwanta suka yi Jah tareda kankancewa ajikin glass din wani mota
Tsaki taja ta lumshe ido tace”kai pretence is not easy, in fact nothing is easy”
Bude idonta tayi tarr tareda fara waige waige kozata ga shago,tinawa datayi akwai shaguna awajen asibiti yasata fara tafiya
Batayi nisa bah taji an kwala mata kira, runtsa idonta tayi tana maijin haushi mai muryan cos tasan Inspector neh
Bude idonta yayi daidai da isowar shi gabanta
Kura mata ido yayi yace”Ina zuwa?”
Hadiye wani yawu tayi tace”need to be alone”
Gyada kanshi yayi cikeda gamsuwa cos yasan tana bukatan hakan yace”toh karki dade”
Rolling idonta tayi kurum tareda yin gaba tana mai addua karya sake tambayan ta wani abun
Cikin sa’a kuwa bai tambayeta komai bah,straight wajen masu kayan Miya tanufa naira dari ta ciro daga aljihun
“Abani albasa dankarami”
Albasa kanana guda 10 mai kayan miya ya zuba mata a leda sannan yabata
Karban ledan tayi tareda cire guda biyu sannan ta miyar mishi da sauran dake cikin ledan
“Biyu kawai ya isheni” tafada tareda yin gaba abinta
Turus taja ta tsaya tareda boye alabasan gudun karta hadu da wani a hanya amma cikin rashin sa’a har Inspector Nasir ya gani(nace kai Inspector kafara shiga gonan da ba naka bah fah, ba ruwan mu in Nadhira tasa karasa aikin ka😏)
Kura mata ido yayi harta karasa cos itakam ma batasan ya ganta bah
“Miye kika siyo mana neh??”
Afirgice tadago kanta dalilin jin muryan shi, waske wa tayi ta ciro albasa guda daya daga inda ta boye sannan tattaro jarumtar ta tace…