RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 14 BY Fateeyzah mbs✍️

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 14 BY Fateeyzah mbs✍️

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

 ….Gidan da muke  zaune yana *Maitama* ne, yayin da daddy da matarsa suke a *Asokoro*, gidanmu babban gidane gari guda, mai d’auke da gate har 4, inkin shigo gate na farko, parking space ne mai d’auke da canopies na mota har goma sha biyu(12), kowacce canopy tana d’auke da tsala tsalan mota  guda biyu, yayin da suke dauke da Alon da aka rubuta *TURAKI* da manyan bak’i wanda aka yi kuma numbering dinsa from 1 to 12, dai² adadin yaran gidan, first born dinmu bro suleim shi keda canopy mai d’auke da Alon *TURAKI1* haka abun ya tafi har kaina last born  da nawa ke d’auke da *TURAKI12*, hatta numbobin motar haka suka kasance, daga d’ayan b’angaren kuma part d’in masu gadine da sauran ma’aikatanmu maza, anan kuma zaki kuma shiga wani gate d’in na biyu, shi kuma nan d’akunan mazan suke, flat takwas ne shi kuma suna d’auke  da Alo shima kamar na canoping mota, sai dai su flat hudu na kallon

sauran h’udin, flat na farko na bro suleim ne da yake aiki a ministry of finance, at the same kuma yana *PHD* d’insa a jami’ar Abuja, Sai na biyu shine na Bro safwan, shi kuma yana aiki a ministry of Agriculture, at tge same time shima yana *PHD* d’insa a *Base university Abuja*, sai na ukun Bro Salim, shi kuma yana aiki a ministry of water resources, yayin da shima yake *masters* d’insa a *Base university Abuja*, sai na  hud’un Bro Salman, shi naya aiki, amma yana *masters* d’insa a *Alhikma University Ilori*,  sai na biyar Bro saif, shima tare suke da Bro Salman a *Alhikma*, sai na shidda Bro Sadeeq wanda shine silar lalacewa ta, shi kuma yana *masters* d’insa ne a *Oxford university*  da take *America* , sai na bakwai  Bro Sa’eed, shi kuma yana *first degree* d’insa ne a *Nile university Abuja* , sai na takwas Bro Sameer, shima yana *first degree* d’insa a  nan *Nile university*. Kowannensu parlour ne, sai two bedroom, study room, da kitchen.

Daga nan sai gate na uku, wanda nan mu kuma matan muke, Katon parlour ne sai dinning area da kitchen, gefen kitchen akwai corridor wanda anan d’akunan mu suke mu hud’u, d’akin Sis Salma ne a farko, tana aiki a *NDIC* ta gama *masters* d’inta, sai na Sis Safwa, yana kallon na Sis Salma, ita kuma masters take a nan *Base university*, sai nawa a gefen na Sis Safwa, sai na Sis Subai’a yana kallon nawa, ita kuma tana *first degree*  d’inta ne  a *A.B.U ZARIA*,  mu kuma namu Single Room ne, sai Toilet da Study Room, daga part d’inmu sai na Masu aikinmu mata, gate na hud’u kuma garden ne, sai swimming pool.

Kamar yanda na fad’a muku, rayuwace muke yi ta ‘yanci, kana iya kwana biyu ba kaga d’an uwanka ba, sai dai duk weekend tare muke wuni a garden ko anan parlour.

Daddynmu yana da wani ra’ayi ko ince wata d’abi’a wacce itace silar lalacewarmi, don dukkanmu babu wani na kirki, ke hatta musulunci sunan mu musulmai ne, amma bamu da wani sani ko ilimi na musulunci, d’abi’ar tasa kuwa itace………..

*Laifin dadi, karewa*

 _Saura k’iris in kammala part one((1) na wannan littafin mai suna *RAYUWAR CAMPUS* don son jin labarin har k’arshe sai ku biyoni a part two(2), wanda ya kasance na kudi, biya don ki karanta._ 

 _Zaku iya fara biya don kar a fara badda ku, zaki iya biya ta katin waya ko kuma account number_ 

 *Domin shiga paid group* 👇

 *_Single #200_* 

 *_VIP #300_* 

 *_Document #400_* 

 _Zaku biya ta wannan hanyar👇_ 

 *08161734851(katin waya) tare da turo da shaidan turawa.* 

 *Account number* 

 *0796627818* 

 *Fatima sani Muhammad* 

 *Access bank*

 _Ina masoyana na asali ,ku garzayo ku biya, don kara samun damar karanta sabon littafina mai suna *MATAR BAHAUSHE*_

 *Comment*

 *Like*

 *Vote*

 *Share*

 *_Fateeyzah mbs ce_*✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page