KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 5 BY ayshay bee

KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 5 BY ayshay bee

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wayar Zahra da ke gefen ta ne ya hau ruri, tana kallon call har ya tsinke wani ya kara shigowa still bata dauka ba har ya tsinke.+

“Ba dai kyau wulakanci” Nanah ta fada tana kallon ta.

“Kinsan Allah ba wulakanci bane kawai dai maganin kar ayi kar a fara” Zahraun ta bata amsa.

Ummiy ce ta tanka “wlh Zahrau ban San me ya sa kike wa Abdulrahman haka ba bawan Allah tun muna Nursery fa yake ji dake”

“Sumayya na son shi Ummiy, shi kuma naga take taken shi ya kira ni jiya da dare mun gaisa fa to gsky ni yau bansan me yake son in mishi ba”

“Ke kuma ke kika mishi kawai ta hakura” Nanah ta fadi

“Wai rufa min asiri” Zahrau ta fada tana rufe baki “ba ki San kishin Sumayya ba”

“Ke dai wlh anyi matsoraciya ” Ummiy ta kara fada

“Hmm ke ni ta karatu na ma nake duka duka SS2 fa zamu shiga”

“Ba sai kiyi candy marriage ba” Maijidderh da tun ta su ke maganan ba ta tanka ba sai yanzu ta fada.

Tsaki Zahrau ta ja hade da barin wurin.

Zaune su ke suna jiran babban Yaya ya dawo, yau za su koma Zaria saboda Hutu yazo karshe. Hira suke tayi ana raha amma banda Maijidderh da hankalinta gabadaya bai wurin su. Ummiy ce ta dafa kafadanta “Hajiya Hauwa tunanin barin Saurayin ki kike ne?” Hararanta Maijidderh ta yi sannan ta daure fuska.

Dariya su ka kwashe dashi dukkan su

“Nima naga alaman haka ai” Nanah ta fada cikin tsokana.

“Anty kin gansu dai ko” Maijidderh ta fada was Anty Rukayya dake dan nesa dasu amma tana jin duk abinda su ke tattaunawa.

“Ehm ehm kun ga dai Ku kyaleta ko, Taimako kawai ta yi kuma lada zata samu don haka Ku dai Ku bari” Anty Rukayya ta gargade su

“To Anty ki ce mata mu dai ba za mu kai Amarya ba in dai kauye za a” Ummiy ta fada.

“Kaniyanki kauyen ba mutane bane”

“Shi fa So ba ruwan shi da wannan, Ku muka San wa zaku So koh Maijidderh” Zahra ta fada ita a dole za ta kare wa Maijidderh

“Ce miki nayi ina son shi”

Nan fah su ka hau mata dariya wai an gwale ta.

Anty Rukayya ce ta shigo ta sanar dasu dawowan Babban Yaya, fidda kayan su suka yi.

Kaman kullum yana zaune kan benci a gefe guda yana duba jarida, kallon shi Ummiy ta yi ta girgiza kai “wai wannan me ya ke yi da jarida tsakini da Allah”

Dariya su ka kara yi Maijidderh kam ko tanka su bata yi don tasan ita su ke wa tsiya.

***                           ***                    ***

A gajiya su dawo daga shopping in makaranta dukkan su washegari za su koma School, a falon Mami su ka yada zango. Yusrah ce ta shigo da wayan Zahra a hannun ta tana gudu “Anty Zahra wayanki na ringing” ta mika mata.

Abdulrahman ta gani akan Screen in wayan, girgiza kai tayi hade da fadin “ikon Allah” karfin halin daukan wayan tayi kar ya ga kaman tana mishi wulakanci.

“Hello” ta fada a dakile

“Zahrau kina lfy”

“Lafiya kalau”

“Madallah na shigo Zaria ne pls ina son ganin ki in ba matsala”

“Ganina kuma? A ina kenan ” ta fada cike da mamakin request in shi

“Gidanku mana zan zo gun deedat, pls fa”

“Shikenan sai ka zo”

“Thank you” ya fada sannan yayi ending call.

Unguwar Alkali su kaje gaishe da yan uwa ba su samu dawo wa ba sai bayan la’asar.

Duba wayan ta Zahrau tayi taga Abdulrahman ya mata missed calls har 5, kwata kwata ta manta da yace mata zai zo gidan su. Call in Deedat ne ya shigo wayanta.

“Hello ya Deedat” ta fada cike da shagwaba

“Zahra na ina kika je ne, Abdulrahman ya ce min ke ya ke jira”

“Unguwan Alkali mu ka je amma mun dawo yanzu”

“To kiyi sauri ki zo he is on his way, ke ya ke jira”

  Veil ta yafa kan plain bakar doguwar da ke jikin ta ta nufi dakin Yaya Deedat in.

Sallama tayi a kofar dakin nashi sannan ta karasa ciki. Abdulrahman in kadai ta iske zaune kan single chair in da ke dakin yana danne dannen waya.

Yana ganin ta ya saki murmushi sannan ya ajiye wayan nashi a gefe. “Sannu da zuwa Zahra” ya fada cikin husky voice in shi da ya ratsa kunnen ta gaba daya.

“Kai ne da sannu kai da kazo daga wani gari”

“Allah ko? To ai ni na zama Dan gida”

Shiru kawai ta yi don ko bata da abin cewa. “Gobe za Ku koma school ko?”

“Eh” ta bashi amsa

“Okay, nima goben zan koma ke nazo wa sallama”

Dago kanta tayi cike da mamaki tana kallon shi, wani irin Kallo ya mata mai cike da ma’anoni dayawa daya sa ta saurin sadda kai kasa.

“Kina mamaki ne Zahra, ai kin wuce hakan a wurina”

“Kinyi shiru ” ya fadi still dai bata tanka din ba “ko kunyata kike ji princess”

Bata San sanda ta Saki murmushi ba hakanan ta tsinci kanta da jin dadin sunan daya kiratan, abin mamaki ba yau ya fara kiranta da hakan ba. “Aa” ta ce mishi tana wasa da yan yatsunta.

“To dago kai ki kalle ni” haka kurum ta ji nauyin hada idon dashi take.

“To Zahra bara in tafi yamma nayi ban son driving in dare”

“Okay Nagode” a hankali ta fada kaman mai rada

“Ni ke da godiya sai na kira ki”

Bayan tafiyan shi Deedat ya tsare ta sai ta fada mishi me ke tsakanin su da Abdulrahman din, ce mishi tayi mutunci ne kawai tsakanin su.

  Da dare kawai sai ta tsinci kanta da expecting call din Abdulrahman din Amma shiru kake ji kaman an aiki bawa garinsu. Wani sashe na zuciyan ta ne yace mata anya Zahra inda Amana ruwa ya dafa kifi, wannan yarinyar fa amana da yarda ya sa ta kwashi sirrinta ta fada miki in kika mata haka anya kin mata adalci? Saurin girgiza kai tayi hade dayin au’uziyya.

Washegari da sasafe suka dau hanyar katsina, tun a bakin gate wurin biyan school fees ta hadu da Fatima ta dawo , sunyi murnar ganin juna sosai Sumayya kam sai bayan Azahar ta iso.

Daukin SS2 su ke tayi yanzu ba su da seniors in da za su dinga takura musu dake ba a immediate bullying a girl section.

Wanki su ke a rizaf ita da kawayen nata guda biyu, Sumayya na basu labarin wani saurayi da tayi Al-ameen koma wansu Hutu, har waya su ke dashi a schl yanzun. Zahrau ce ta katse ta “Wai Sumy lafiyanki Yaya Abdoulh in fa, ya za kiyi dashi?”

“Hmm Wlh Zahra sosai nake jin Ya Abdoul a raina, sai dai Allah ma ya gani I can’t confess”

“Amma yanda kuke din nan ba kya ganin shi ma yana son ki” Fatima ta tmby

“Anya da kyar wlh, da fa na bashi lbr Al-ameen har shawara ya ke bani kinga ko ni ke haukana”

Ummi ce ta leko ta window din tana kwallawa Sumayya kira tazo ana Neman ta.

Kara ta buga tana “my Al-ameen ya kira ni”

“A nan zaki yi wayan ko, sai malama binta ta fito kija mana case gun malam Adams gobe a Assembly” Zahra ta fada

Fatima ta ce “wooh Zahra tsoro”

Maimakon yanda Sumayya ta yi tsammanin Al-ameen sai taji muryan Abdulrahman, sai farin cikin ma ya wuce na da tace “Allah sarki ya Abdoul yanzu mu ke lbrn ka da su Zahra”

“Lah Sumy gulma ko to me aka ce a kaina”

“Secret ne Yaya, ya schl”

Sun Dan Dade suna hira da kanwar ta shi kafin ya nemi ta ba Zahrau, da ke yasa tmbyn ta yasa bata kawo komai ba, cikin zumudi ma ta bata wayan.

Bayan sun gaisa ne ya nemi ya San secret in da Sumayya ta ce sunyi magana akan shi. Bata fada mishi ba duk nacin shi haka ya hakura, hira ya jata Wanda take amsa mai da ehm ko Aa ganin ta ki sakin jiki ya sa ya ce mata “shikenan princess gud nyt, ki kulan min da kanki pls” ba abinda ya fada bane ya tsaya mata a rai A’a yanda ya fadan ne ya mata dadi. Ita kam tana ga zata dena amsan wayan shi inba haka ba to tabbas zuciyan ta zai sa tayi betraying Sumayya, Wanda ko kadan bata fatan haka she can sacrifice everything for her love ones nd Sumayya is included.

Sumayyan ce ta nemi ta San me Yaya Abdoul ke ce mata su ka Dade a waya, ce mata tayi makaranta kawai ya ke tmbyrta. “Karfa Sumayya ta fara zargin wani Abu?” Ta fada a ranta dole ta yi yaki da zuciyar ta don ba shakka Abdulrahman ya fara samun wurin zama a wurin ta.Sumy zaune akan gadon ta suna waya da Abdulrahman, labarin Al-ameen ta ke bashi, shawaran Zahrau ne hakan a cewarta kila yaji kishi ya yi ma sumyn confessing. Sai dai maimakon hakan wani tunani na daban yake darsuwa a ran shi “Sumayya kenan na lura ko kunyata ma baki ji kike bani lbrn Saurayin ki ko” murmushin farin ciki Sumayya tayi a tunanin ta kishi ne ya sa Abdulrahman fadan haka kaman yanda kawayen ta suka fada.+

“Kai Ya Abdoul” ta fada cike da jin kunya.

Sun dade suna wayan yana mata nasiha akan ta dai mai da hankali kan karatun ta kar Namiji ya rinjayeta.

Tana gama wayan ta fita film show ita da wasu yan mate insu ta bar Zahrau na sana’ar karanta novel, novel in yaja ra’ayin ta sosai hakan ya sa tayi concentrating sosai akan shi, tana mamakin irin soyayyan da ke ciki, a kullum fatan ta Allah ya nuna mata namijin da zata so so na gsky da hakika kaman yanda ta ke karantawa kuma ta ke gani a Indian films. Ta sha imagining hakan ya faru she is just desperately waiting for the reality, ni dai nace ehm ehm Fatima ki dai bi a hankali…

“Zahra Zahra” daya daga cikin kawayen ta Amira ta shigo tana kwala mata Kira.

“Hey gani a kwanar hawwy” ta amsa

“Daman nasan kina nan ai” Amiran ta fada bayan ta zauna “wani ke nemanki a waya”

“Ehm ehm Kawa ba dai ni ba” ta fada cike da mamaki

“Ehmm tunda ba sunanki Fatima Al-ameen Turaki ba ko”

“To waye ne”

“Ina na Sani zai kara kira kila ma daga dayan barin ne” ta fada cike da tsokana

“Ke ma kin koyi iskancin Asiya kenan”

“Allah kuwa daman dayawa sun kai hari share su dai ake yi”

“Kyale su kinji, a dai yi mutunci kawai”

Wayan da ke hannun Amiran ne ya fara ringing, mika mata tayi sannan ta bar kwanar.

Sallama Zahrau ta yi bayan ta daga wayan.

“Wa’alaiki Salam” a ka masa

Muryar Abdulrahman ne ko shakku ba ta yi akan hakan.

“Abdulrahman ne”

“Na gane, ina wuni”

“Lafiya princess, ya makaranta?”

“Lafiya ya naka”

“Lafiya kalau nima”

Shiru su kayi dukkan su biyun sai bugun zuciyoyinsu

“Princess wani abu na ke so a gun ki pls”

“Ehmm menene” ta tmby cike da fargaba

“Za ki iya min?”

“In har bai fi karfi na ba kuma bai kauce wa addinin musulunci ba”

“Ba ko daya a ciki”

“Ina jinka”

  “Princessssss Zahraaaaa I luv you” ya fada cikin wani irin murya da shi kanshi bai San yana da ba.

Zahrau wani irin abu ne ya saukar mata a zuci jin Kalmar da ya fito daga bakin shi, ba yau aka fara fada mata ba amma na yau in sai taji ya bambanta da na kowani rana, har ga Allah bata San me zata ce mishi ba.

“Kinji” ya katse mata tunani

“Ehm” ta amsa

“Baki ce komai ba”

To ita me zata ce Har ga Allah ba ta San in tana Son shi ba ko akasin haka Abu daya ta Sani ba za ta ci amanar Sumy ba.

“Kingane nasan ba lallai kina feeling the same way ba, Amincewar ki kawai na ke bukata for now, just give me a chance please”

Daure wa tayi ta samo maganar da take ganin shine dai dai “Naji na kuma gode sai dai am sorry pls…”

Saurin katse ta yayi da fadin “No please princess Dan Allah kar ki bani hakuri, Wlh kunne na ba zai iya saurara ba, you don’t have idea how long am in love with you at least I deserve a chance”

Wani irin bugu taji Zuciyan ta nayi tana jin kalaman da ya fada na sauka a ko wani bangare na jikin ta, wani irin rawa jikin ta ya fara kaman mai ciwon zazzabi.

“Dan Allah kayi hakuri, I may also have my reasons” ta fada cikin rawan murya.

“Do you love someone?”

“No”

“Wlh Zahra wannan ne kadai reason in da Zuciyana zata iya amsa ta yi accepting kadarra amma banda wannan bazan iya ba, pls save a soul kinji”

Yanda ya ke maganan ma kadai ya isa ya karyar mata da zuciya, Ya Allah! Sumayya fa

“Kayi hakuri bazan iya ba” ta fada cikin wani karfin guiwa sannan ta yi saurin kashe wayan gaba daya.

Wani irin hawaye ta ji ya fara fita daga idanuwanta sai dai ta rasa na farin ciki ne ko bakin ciki ta ma rasa dalilin kukan nata.

Amira ce tazo amsan wayan ta iske ta tana kukan, ba irin tambayan duniyan da ba ta mata ba tace ba komai sannan ta ce mata ko an kara kira kar ta dauka ba yanda Amiran ta iya haka ta kyaleta.

Ranar dai da ciwon kai ta kwana saukinta ma washegari Saturday ne da dare kam ba ta yi bacci mai kyau ba sai bayan ta yi Sallar Asuba shi ma bana dadi ba kasancewar ta mutum mai saurin sa abu a rai.

Zuwa lokacin break Fatima da Sumayya sun zargi akwai abinda ke damun Zahrau amma fir tace ita kanta kawai ke ciwo, abinci ma kadan ta ci fatan ta Allah ya sa kar Sumayya ta Sani ne kawai, Novel in da take karanta wa ta dauka ta cigaba ko zai Kore mata damuwar ta ta ko yi nasara. Daga karshe ganin zaman class in ba zai fisshe ta ba ya sa ta tattara ta wuce class domin ida sa notes in dake gabanta da kuma Assignments. Nan ta hadu da wasu yan Class insu su na notes suna hira hakan ya sa damuwar ta tafiya.

***                           ***                         ***

Karfe goman dare  tana zaune gaban hostel suna hira da wata kawar ta da suke dan taba shiri Sumayya ta zo wurin ta “Dan zo kiji” ta fada tana kallon Zahra.

Karantar fuskar ta Zahrau ke so tayi amma ta kasa gane komai “ta so mana sorry sis one minute” ta fada ma wacce su ke hira da Zahrau.

Tasowa tayi Sumayya ta ja hannun ta suka dan yi gefe “Zahrau kenan naji abinda ya faru, nagode sosai kin kyauta, gashi za a kira pls ki dauka” Ta ajiye wa Zahrau a gefen ta ta wuce.

Kasa tantance mai Sumayya ke nufi Zahrau ta yi, haushin ta taji ko me? To gaya mata ma yayi ne ita dai bata Sani ba. Wurin kawar ta da suke hira ta koma ta iske ita ma ta tashi don haka hostel kawai ta shige.

Gaba daya ta rasa me ke mata dadi saboda rashin sanin manufar abinda Sumy ta mata, wayan da ta bata ne ya hau ringing ita har ta manta dashi.

Kin dauka ta so yi amma son sanin abinda Abdulrahman ya fada ma Sumyn ya sa ta karfin halin dauka.

Sallama aka mata sai dai kaman yanda tayi tunanin Abdulrahman ne sai taji akasin haka.

“Faroukh ne yayan Sumayya” ya fada mata kai tsaye.

“Oh ina wuni”

“Lafiya kalau Zahrau kin mana laifi fa”

Gaban ne ya fadi jin abinda ya ambata yana nufin tsakanin ta da Abdulrahman ko kuma kanwar shi.

“Me neyi” ta amsa muryar ta na rawa

“Au baki ma Sani ba? Kin bar mu da zaman jinya”

“Jinyan me” ta fada cikin faduwar gaba.

“Zahrau Serious Wlh Abdulrahman da zazzabi ya kwana ya wuni, yanzu haka tursasa shi nayi ya sanar da ni abinda ke faruwa, me ya sa kika katse waya kuna magana? Allah nasan waye Abdoul trust me ba karamin so yake miki ba tunda har ya iya furta miki, mutum ne shi mai Zurfin ciki”

Ita dai shiru ta yi tana sauraran shi don har ga Allah ba ta San me za ta ce mishi ba kuma har cikin zuciyan ta bata San miye mafita ba. Wani kewan su Maijidderh ta ji tana yi da suna nan da tuni sun nema ma ta mafita duk uncle Aliy na ya cuce su da suna wuri daya da duk ba haka ba.

“Yace min he is fond of you tun kuna therbow school, ranar da muka fara zuwa visiting tare ya gane yana son ki. Zahrau shekaru nawa kenan mutum na fama da abu daya, please save a soul”

“Wlh Ya Faroukh ban San me zance ma ba, ba zance maka INA son Abdulrahman ba ko ban son shi ni dai kawai na San ba zan iya dating in shi due to my reasons”

“Zan iya sanin reason in?”

“personal ne”

“Da za kiyi yarda da ni na dauke ki kaman Sumayya Wlh, fada min menene ni zan mi shi bayani in har reason in naki mai karfi ne”

“Nagode amma Yaya Faroukh ba zan iya fada ma ka ba, amana ne”

“Amana?” Ya tambaya sai kuma yayi shiru “OK na so in fahimce ki akan Sumayya ko? Sumayya na son Abdoulh right? “

Tayi matukar mamakin yanda Faroukh ya dago su amman da ta yi la’akari da shi in yana tare da su duka biyun sai taga ba abin mamaki bane.

“Aa Yaya Faroukh ba haka bane” ta fada cikin sarkewar murya

“Kul” ya katse ta “kar ki boye min komai abinda ma na Sani tun da dadewa. Baki son ki ci Amanar kawar ki Ko, maganan da na ma Sumayyan kenan ta nemi ta musa man that’s why na kyaleta nace ta hada ni da ke. Abdulrahman a matsayin kanwa ya dauki Sumayya Wlh, yana ji da ita sosai, caring and been nice to her. Ku matsalan Ku mata kenan da an nuna muku Kulawa sai zuciyan Ku ta rinjaye Ku. Abdoul in ma na sha fada mai abubuwan da yake ma ta yayi yawa kar ya sa ta wani tunani but ya ce min har lbrn Saurayin ta ta ke bashi. Ga abinda na ke gudu kenan, Ki barni da Sumayya za muyi magana kuma ban son Abdoul ya ji zance nan pls and wannan ba reason bane go and think pls”

“Shikenan Nagode”

“Ba matsala Sai anjima”5 days kenan da wayan Zahrau da Faroukh, tun daga ranar da ga Faroukh din har shi kan shi Abdulrahman din ba Wanda ya neme ta, in tace hakan bai dame ta ba to tabbas karya tayi ga kuma halin ko in kulan da Sumayya ke nuna mata tunda abin ya faru, ko abinci su ka zo zata ce sai anjima za ta ci nata, gaba daya ta dauke kafa daga kwanar su Zahrau haka class sabbin kawaye ma tayi a wurin su ta ke wuni, ko a hanya su ka hadu sai ta dauke mata kai. Hakan ba karamin kona ma Zahrau rai yayi ba at least they are friends inma tunani ta ke taci amanan ta ne ai sai ta same ta su yi magana. Har yan mate insu sai da suka fahimci da matsala tsakanin su, yan makaranta da tsegumi tuni aka hau kus kus.

Tests in Sciences gare su Week in da zai shigo, ganin class insu a cike ya sa Zahrau tafiya junior classes coz a can ba za ayi distracting inta ba. Essential biology ta ke duba, tayi nisa a karatun Fatima ta shigo tana Neman ta.

“Ke ashe nan ki ka gudo”

Murmushi tayi saboda kwanakin nan Magana ma wuya ya ke mata saboda halin damuwan da ta ke ciki.

“Zahrau please me ke damun ki kwana biyu” ta tambaya cike da kulawa

“Me kika gani” ta fada a takaice

“Abubuwa dayawa, farko ma me ya faru tsakanin Ku da Sumayya naji wasu maganganu marasa dadi”

“Hmm kina raba mutane da tsegumi ne”

“Aa amma Alamomi sun nuna gsky zantukan nasu, na lura wlh ko magana ba kwa yi”

“Wannan kuma daga ita ce ita ta share ni”

“Kalla Zahrau please fito ki gaya min meke faruwa, ban son haka matsalar ki ba matsala ta bace? In nice ai zan fada miki waton ni banda sirri ko?”

“Wlh Fatima ba haka bane Sumayyan ne ba zan ce miki ga dalilin da yasa ta share ni ba, a hankali ta warware mata duk abinda ke faruwa, 5 days kenan ba Wanda ya neme ni cikin su, kila ma shawara su kayi a share ni din”

“To ke kika neme su tun farko, kiyi hakuri komai zai warware amma let me ask you kina da interest akan Abdulrahman in?”

“Wlh ban Sani ba Fatima kawai nasan ban son Sumayya taga kaman naci amanan ta ne, wlh komai ya faru tsakanin su sai ta sanar dani shiyasa ma ban ga laifin ta ba ya dai kamata ta same ni muyi magana ne akan halin ko in kulan da take nuna min”

Jan ta Fatima ta yi su ka tafi hostel ganin lokacin light out ya kusa, sai da su ka biya ta class Fatima ta akiye books inta tana ganin su ta dauke kai dan takaici Fatima tsaki ta ja hade da fadin “Rashin aikin yi” don Sumayyan ba karamin kular da ita tayi ba.

“Fatima please kar ki shiga kinga za ta ga kaman kin fi so na ne since akan ta ba dadi” Zahrau ta fada tana rokon Fatiman.

Suna koma wa hostel sai ga Sumayya ta biyo su Fatima ta iske a gaban kwanar nasu tana tsaye “Fatima please dan ba Zahrau ana nemanta a waya” ta fada a cikin son barin wurin.

“Ai kin San inda take” Fatiman ta amsa sannan ta wuce ta bar hostel inma gaba daya ta bar Sumy tsaye a wurin.

Ganin ba sarki sai Allah ya sa ta shiga kwanar Zahrau na kwance ko jiyo ta kalle ta bata yi ba “Gashi ana son magana da ke” ta fada hade da ajiye wayan a gefen ta. Ta tashi za ta fita kenan Zahrau ta katse ta “Dan tsaya zo ki dauki wayan ki ba Wanda zanyi magana dashi”

Cike da mamaki Sumayyan ta juyo tana kallon ta, dauke kai Zahrau tayi ta gyara kwanciyar ta. Wayar ne ya hai ringing ganin da gaske Zahraun ta ki kallon wayan ma ya sa Sumayya dauka “Hello sorry Yaya Abdoulh tayi bacci” ta fada tana barin kwanar, tana jin ta tana fadin “No bazai yiwu in tada ta ba ka bari sai gobe” ita dai tabe baki tayi tana fadin “Ku kuka Sani”

Washegari suna breakfast sai ga Sumy ta kara dawo wa wannan karan ma har cikin kwanar su ta shiga ta zauna daga dai Fatima har Zahrau ba Wanda ya tanka mata, hira su ke dasu Aisha da Amina da ke opposite kwanan su. “Fatima wurin ki na zo” Sumyn ta fada tana kallon ta.

“Gani nan ai ina jinki”

“I want to see you for some minute please”

“No nan ma is alright ai”

  “Kiyi hakuri muje Dan Allah”

  Shiru Fatima tayi sai kuma can tace muje, mike tayi ta bita sun kai kusan Ashirin suna tattaunawa Sai ga Fatima ta dawo ita kadai da waya a hannun ta “Zahrau pls yi hakuri ki dauki wayan zan miki bayani”

“No Fatima bar su kawai na riga na yanke shawaran fita harkan su dukkan su”

“Ehm ehm kar ki yi hka please”

Ance mai hakuri bai iya fushi ba da kyar Fatima ta lallashi Zahrau akan in ya kira za ta dauka.

“Assalamu Alaikum” ta fada bayan ta yi picking call din

“Ke ma Amincin Allah ya tabbata a gare ki” Abdulrahman ya amsa

Shiru su ka yi dukkan su shine ya katse shirun da fadin “au ko ya jiki ba za kice min”

“Ciwo kayi?”

“Sumayya ba ta fada miki ban da lafiya ba”

“Aa, Sannu, ya karfin jikin?” Ta fada a lokaci daya

“Alhmdlh na warware, Princess ya maganar mu ne, Allah ina cikin wani hali, ko so kike zuciya ta bugu”

“Aa” kawai tace tayi shiru

“Princess ina miki son da ni kaina ban San irin shi, me zanyi ki tabbatar da gaakiyan lamarina ki yi accepting request INA” cikin marairaicewa yake magana hakan duk ya kashe ma ta jiki ba karya ya fara samun zama cikin zuciyan ta.

“In tambayeka”

“Ina jinki”

“Kace kana sona naji but why do you love me”

“Wlh in nace miki ga reason nayi karya kawai dai nasan tun kafin in san kaina kike burgeni na bar school inku sai kuma ranar da muka zo visiting Allah na gani ina ganin bayan na gane ke ce naji wani abu ya darsu a rai na, tun daga ranar da tunaninki na ke kwana dashi nake tashi, kullum kina raina”

“Burge ka nake with no reason how long zan cigaba da burgeka ba ka tunanin wata rana za ka iya tashi kaji komai yayi fading”

“Ba zan miki karya ba Zahrau don INA Neman Amincewar ki haka kuma ba zan miki alkawari ba saboda ba ni ke da kai na ba ko zuciyata ni dai nasan My intentions towards you are real and pure, kuma ina fatan in so ki har karshen rayuwa ta, ba passing time na ke so nayi da ke ba, I want to marry you, gab nake da gama degree na so I think I can make work it out”

“Naji na kuma gode sosai sai dai Shawara Abu ne mai kyau so zan so ka bari inyi shawara da wadanda ya dace da kuma zuciyana coz right now am asking myself am i even ready to starts a relationship, so zan so in samu natsuwa da amincewar zuciyana tukkun na”

“Shikenan na gode sosai sai mun kara magana”

***                          ***                        ***

Tana gama wayan ta daga kai tana kallon Fatima alamun ina sauraranki, tsaf Fatiman ta dago ta “Tace in baki hakuri Dan Allah amma ita haushin da taji da kika ki fada mata bayan da ita ce duk da ta San abin zai bata miki rai zata fada miki, ba za ta miki karyan cewa ba ta ji zafin abin ma amma Wlh ta yi kokarin yakice Abdoulh daga zuciyan ta just because of you, ayanda ta ce min ta fahimci ba karamin so ya ke miki ba hakan ya sa ta janye jikin ta daga wurin ki saboda gudun ta fara jin haushinki, sannan ta na neman Alfarmar ki yi accepting Dan uwanta Dan Allah in har saboda ita ne wlh ta hakura dashi sanin kanki ne ba zata taba nace ma namijin da bai son ta ba kuma sunyi magana da yayanta Faroukh shi ya ce ma ta same ki ta miki bayani ita kuma ta najin nauyin abinda ta miki amma pls kiyi hakuri, Forward as received” Fatiman ta karashe tana dariya.

Ita dai Zahrau murmusa wa kawai tayi sannan ta tashi ta fita saboda tana da abubuwa dayawa a gaban ta weekend in nan.

Da Fatima ta fara shawara saboda complain inda ta mata akan bata sanar da ita matsalar ta kaman yadda itan ta ke yi sannan ta nemi Maijidderh an ko yi sa’a domin duk maganar su ta zo daya akan ta bashi chance taga iya gudun ruwanta amma kafin nan ta yi addu’a tukunna in hakan ya kwanta mata a zuciya, Hakan ko aka yi domin tun daga ranar Zahrau ke addu’a akan abun har wasu lokutta da ta tashi Sallahr dare domin Addu’an biyan bukatun ta ta hada da shi, cikin ikon Allah ji tayi abin ya kwanta ma ta a rai ba shakka zuwa yanzu zuciyan ta ya gama yadda ta amince da batun Abdulrahman.

Sun ci gaba da kawancen su da Sumayya sai dai shirin ba kaman da ba coz daga Zahrau har Sumyn nauyin juna su ke ji Fatima ce ma ke kokarin ganin sun koma kaman da.Yau Sati daya cib da wayan su na karshe da Abdulrahman, haka kawai ta ke ji ta kaguwa ya kira ta domin nuna mishi amincewar ta. Anya kuwa ya damu da ke yau har sati daya bai neme ki ba? Wata zuciyar ta kimtsa mata, Saurin yi mishi uzuri tayi. Ai da tana gida yana yawan kiranta kila Dan yaga tana school ne.

  A wunin ranar ko ya kira ta da dare, har ga ranta ta yi farin cikin kiran amma kuma sai tayi kokarin fuskewa ba ta nuna hakan ba. Bayan sun gama gaisawa ne ya tambaye ta “Toh princess na kira inji Hukuncin da kika yanke”. Shiru ta yi domin ta na kunyan abinda zai fito bakin ta. Jin shirun na ta yayi yawa ya sa shi sake mata wani tambayan “Yadai? Kinyi shiru”.

  ” Ehmmmm ” kame kame ta fara yi “Shknn na Amince”

  “Ehm banji ba” Ya tmby domin ji yake kaman kunnen shi karya ya ke shiyasa ya ke son ya kara tabbatar wa.

  “nace maka na amince”

   “Dan Allah princess da gaske kike? Pls kar kice min wasa ne” har muryar shi canja tayi tsaban farin cikin da ya tsinci kan shi

  “Da gaske na ke na Amince” ta kara maimaitawa.

    “Alhamdulilah Allah kai ne abin godiya, Princess ina zuwa” Ya katse wayan, murmushi ta yi sannan ta ajiye wayan a gefe domin jiran kiran nashi.

  Alwala Abdulrahman yayi sannan ya gabatar da Sallah raka’a biyu domin godewa Allah da ya sa burin shi cika.

  Kiran ta ya sake yi, sun dade suna waya ya na nuna mata farin cikin Amincewar ta da yayi hade da tabbatar da ba son wasa ya ke mata ba. Ita dai bin shi ta ke da ehm ko Aa saboda hakan sabon abu ne a wurin ta sannan ba ta San abinda za ta ce mishi ba, ranar har Faroukh da wani abokin Abdulrahman din sai da su ka Kira su ka nuna mata jin dadin su haka Sumayya ma tayi ta murna duk da Zahrau tana ganin kaman Yake Sumayyan kawai ke ma ta ba Wai dan hakan bai kona mata rai ba.

***                         ***                        ***

Duk da dai ba wani waya su ke ba shakuwa ta shiga tsakanin su sosai, A ganin Abdulrahman zai takura mata in har yana yawan kiran ta a schl kar ma yayi distracting inta hakan ya sa yayi limiting kiran nashi. Zuwa yanzu sosai ta ke jin Abdulrahman ya shiga ran ta saboda yanda yake nuna mata kulawa da So.

  A haka har aka yi hutun schl, kaman ko wani hutu Sati daya kawai su kayi a Zaria su kayi wa Kaduna diran mikiya.

  Zuwa yanzu mutumin Maijidderh wato Ibrahim ya zama dan gida, Maijidderhn ta cigaba da kula da Alamarin shi kaman farkon zuwan shi gidan, su kam yan gidan mamakin ta su ke gani ganin yanda ta ke nan nan da Alamuran shi amma godiya wannan da kyar ya ke mata ba Wai dan bai jin dadin abubuwan da take mishi sai dan naturally haka ya ke miskili, bashi dai da karanta jarida kullum da ear piece a kunne, kullum da yamma ya kan Dan fita inda su ma basu San ina bane.

  A kule Maijidderh ta fito daga cikin gida saboda da haushin da yan uwan na ta su ka ba ta, Recharge card ta ke son siya urgently amma duk sun ki yarda su rakata gashi su khalipha na islamiyya, zaune ta iske shi akan kujera sai dai wannan rubuce rubuce ya ke maimakon jaridan da su ka saba ganin yana karantawa.

“Sannu da hutawa” ta fada hade da kutsa kai waje

Bai amsan sannun da tayi mishi ba sai ma tambayan da ya jefo ma ta “ina za ki je da ranar nan? Ko ke ba ki jinshi?”

  Kallon mamaki ta bishi dashi domin ba ta saba jin yayi dogon magana haka ba inba sako zai fada ba shi ma yanayi kaman matse bakin shi ake yayi magana.

“Kati zan siyo a shago” ta amsa mishi

“Kawo in siyo miki”

“No ka barshi kaga Abu kake kar in katse ka”

“Karki damu kawo”

“Allah ka bar shi nima tafiyan na ke ji”

Wani irin kallo ya bita dashi da ya sa ta sadda kan ta kasa ba shiri “Hauwa” ya fada cikin wata irin sigan murya da ta ke ji har cikin jinin jikinta “ki kawo nace ko, ban cika son musu ba”

Saurin mika mishi ta yi tana fadin “Nagode” ko kallon ta bai yi ba ya tattara littatafan shi sannan ya fita.

   Tana tsaye a tsakar gidan har ya siyo katin ya dawo “Da kin shiga ciki ai sai na aika a kira ki” ya fada yana mika mata katin. “Ba komai Nagode Sosai” ta fada bayan ta amshi katin. Shi dai murmushi ya mata hade da mika mata sauran canjin ta da ke hannun shi “ka bar shi kawai” Kallon ta yayi cikin idanu sannan ya ce “ayi haka?”

  “Allah ka rike ba komai”. ” Tohm Nagode ” ya fada a hankali sannan ya sa kudin cikin aljihu.

   Cikin gidan ta nufa haka kawai ya tsinci kan shi da bin ta da kallo yana murmushi “I think i got her” ya fada yanda shi kadai zai ji. Har za ta shiga kofan falo ko me ya zo kanshi sai yaji ya kira sunanta “Hauwa” ya fada da muryar shi da ke sa ta rasa natsuwar ta dan har cikin kwakwal war kanta muryar ke sauko sannan ya zaga ye jikin ta gaba daya. Juyowa tayi tana kallon shi kallon da ya bita dashi ya sa ta janye idonta “Abu na ke so na tmby ki” ya fada sannan ya sadda kanshi kasa kaman ba shi ya mata magana ba, tsintar kanta tayi da isa wajen ta kaman ita ke aiki a gidansu maimakon shi.

 

Dakalin da ke gefen shi ta yi ma kan ta matsugunni sannan ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta “Hauwa” ya kira ta, ta rasa dalilin da ya sa duk lokacin da ya kira ta sai ta ji wani Abu, ko dan shi kadai ke kiran ta da sunan bayan malaman ta na makaranta “Naam” ta amsa mai a hankali  “Shekarun ki nawa” ya bukata. Tayi mamakin dalilin da zai sa ya tambayi shekarunta amma hakan bai hana ta bashi amsa ba “am 16”.

” aji fa”

“SS2”

“Great Allah ya taimaka, zan so tambayanki me ye sa kika taimake ni baki sanni ba” Shiru tayi don har ga Allah ba ta da reason in da ya sa ta taimake shi kawai taji tan son taimakon nashi ne. “Kinyi shiru”

“Ban Sani ba kawai naji ina son taimakon na ka ne”

“Haka kawai? To in na cutar da ke fa ko yan gidan nan”

“Ni saboda Allah nayi ai kuma ya ga zuciya ta”

“Haka ne kam, toh Allah ya biya ki saboda ni ban da abinda zan biya ki dashi, Amma ga wani taimakon za ki yi min?”

“Matukar bai fi karfi na ba”

“Ko kadan just ki min alkawarin za ki min”

“In sha Allah”

“Ina ga mu bar shi zu wani rana, ki Shiga gida kar su neme ki”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page