KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 4 BY ayshay bee

KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 4 BY ayshay bee

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Har anyi Common entrance tun tuni amma haka Baffah ya je ya nemi alfarmar a karbe su, ya ko taki sa’a domin duka makarantar sun amince suje suyi common entrance in a gani.+

Hassan Gwarzo da ke kano aka nema wa Ummiy, Maijidda Islamic training center madallah a local government in Niger da ke gab da Abuja sai Zahrau Ulul Albab Science Secondary School Katsina.

Sunje sunyi common entrance, ba laifi dukkan su sun kai cutt off mark in da ake bukata, Wa’azin da Mami da Ammah su ka musu ne ya sa suka hakura su kayi jarrabawar da kyau amma da plan in su kiyi su kayi.

Da yake dab da bude schools su ka yi jarrabawar hakan ya sa su na koma wa aka fara musu shirye shiryen tafiya.

Tsab an gama musu shopping da komai da komai, washegari ko waccen su zata wuce. Daren ranar in ka gansu sai kace wasu marayu ma rasa gata jikin su duk yayi sanyi sun zama wasu abun tausayi sai kace basu da ke cika gidan da hayaniya don ko dukan su surutun ne dasu sai dai Ummiy ta fisu masifa ne, maijidda kuma ta fi kaifi wurin tsokanar fada Zahrau dai yawanci Tsoro ke Hana ta yin abubuwa don haka ta fi kaifi wurin surutun da kuma wasa.

Sun ci kuka kaman ba gobe a haka suka rabu suna karawa Aliyu Allah ya isa domin kuwa duk shi yaja musu wannan bala’in, Babban Yaya ne ya zo ya dauki Zahrau ya tafi da ita Abujan, Abbah ya kai Ummiy kano Baffah kuma ya tafi da Zahrau katsina.

Katsinan dikko dakin kara

Karfe daya dai dai na rana ya musu a kofar shiga katsina, a haka su ka shiga suna tafiya har su ka kai kan titin da zai kai su lungun da za a shiga makarantar, dai dai wurin wani gini mai kaman torch light da yan makarantar su ka ma lakani da faduwar gaba dalili kuwa da ka fara hango abun kasan ka iso schl din.

Iskar tayar su ce ta sace a wurin hakan ya sa drivern parking a gefen hanya yana Neman inda zai samu mai sa iskan. Zahrau naji iskan garin yana ta busowa sai dai abin mamaki zafi ne ke busowa maimakon sanyi, “ashe da gaske ne da aka ce katsina akwai zafi sosai? Lallai tana da aiki” ta fada a ranta.

Mai sa iskan suka samu ya sa sannan suka cigaba da tafiya, wani lungun gidan mai su ka Shiga su ka sha kwana sannan ta hango makarantar wani irin faduwan gaba ne ya ziyarce ta “shikennan yanzu nan za ta yi ta rayuwa?” Ta tambayi kanta.

Suna parking Almajirai su ka karaso domin taya su kwasan kayan su zuwa wurin bakin gate in shiga makarantar inda ake biyan schl fees da tela sannan a rubuta suna.

Admin block suka nufa wani office, sabbin dalibai ne cike a wurin yawancin yan JSS1 da SS1 ne a wurin.

A nan aka bata Class da Admission no sannan aka bata mattress, Wata malama ce ta hada ta da wata Senior yar SS2 domin ta kai ta hostel in Yan JSS1.

Last corner ta kai ta wurin kanwar ta da ita tazo JSS1 din. “Lah Yaya Safiyya Kawa kika samo min” Yarinyar ta fada tana murnar ganin Zahrau

“Ehm sunan ta Fatima ita ma kinga kin samu bonkiey sai ta zauna a down ki, ko kinfi son Up” ta tambayi Zahrau

Saurin girgiza kai Zahrau tayi “Sunana Fatima Yusuf Danbatta ke fa” ta fada tana mika mata hannu su yi musabaha.

“Fatima Al-ameen Turaki Amma ana ce min Zahrau” itama ta fada bayan ta mika mata hannu sun yi musabahan.

“Friends?” Fatima ta tambayan

“Friends” ita ma ta fada tana mata murmushi.

“Kije kiyi sallama da babanki sai ki dawo ko” Yaya Safiyyan ta fada ma Zahrau.

Can bakin gate in ta koma inda Baffah ke jiranta dake ba a barin maza su shiga girl section in in ba malamai ba

Wa’azi Baffahn ya fara mata akan ta maida hankali tayi karatu banda kawayen banza, wasu irin zafafan hawaye taji ya fara bin kumatun ta, lallashin ta Baffah ya fara yi yana share mata hawayen.

Sheshekar Kukan wata Yarinya da ta kankame babanta ne ya katse su, Baban ne ya karaso wurin Baffah su ka gaisa sannan yace “Yar ta ka ma JSS1 take?” Baffah ya amsa mai da Eh.

Jawo yar tashi yayi yana fadin “to Sumayya tashi kinga ga Kawa ma na miki”

Cikin sheshekar kukan nata ta dago ta kalli Zahrau sai kuma ta saki murmushi, Zahrau inma murmushi ta mata.

Nan dai Baffah da Baban Sumayya su ka musu nasiha sannan suka musu sallama suka wuce, kuka kam da ga ita har Sumayya sai da su ka yi shi sabanin Fatima da ko a jikinta ko dan taga akwai yayarta a schl dinne.

JSS1 Aisha aka ba Zahran ita da Sumayya, Fatima kuma Khadija. Komai banbarakwai ya zamar ma Zahrau kwanan kan bonk, zuwa dinning, bin Layin toilet da sauransu Dan ma Yaya Safiyya da kawayenta na taimaka musu.

Ba ta manta daren ranar da ta zo makarantar ganin sauro ya sa ta fiddo sabon Net inta Fatima ta taya ta suka daura jikin bonk in, a ciki ta kwana da safe ko da ta tashi fuskanta kaman garwashi haka take jin shi dalili kuwa net in sabo ne sai an wanke an shanya.

Da kyar ta gabatar da sallan Asuban, Ruwa ta debo a cup da handkerchief inta, tana sawa cikin ruwan sannan ta goga a fuskan ta unknown to her ruwan kara wa fuskan radadi yake, ta sha wuya ranar.

Da ke itan mutum ce mai saurin sabo ta saba da mutane dayawa ga ta kuma akwai son labari hakan ya karasa wa ta zama mai jama’a ko da yanayin shirin da suke da ita though Fatima da Sumayya daban ne tafi shakuwa dasu hakan ya rage mata kewan gida sosai.

A bangaren karatu kuwa sosai ta mai da hankalin ta musamman ganin kawayen nata masu hazaka ne, gaskiya schl in akwai karatu sosai ga kuma competition da ke both boys and girls ake hadawa a fidda result.

Kasancewar ta mai tsoro ya sa take taka tsan tsan da seniors, ko aike aka bata salin alin za tayi hakan yasa ba ta shiga case insu.

A hankali ta fara sabawa da rayuwan makarantar da duk wani schedules insu, sai karfe goma na dare ake tashi daga Qur’an class Wanda shi ne last activity in rana sannan kuma tun six na safe za a tashi morning prep, wurin karatu kam suna sha sosaiA kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Su Zahrau har sun kai JSS3 suna extension in JSSCE, Kowaccen su yanzu jin dadin makarantar da take take yi sosai, anyi kawaye kala kala.+

In ka gansu yanzu za ka sha mamaki in aka ce maka sune su kayi abubuwan da, yanzu kam basu da abinda su ka sa a gaba sama da Karatu, sosai su ke yin shi.

Duk Hutu ko tabbas sai sunje Kaduna wurin Anty Rukayya, sun saba da ita sosai ita ma ko tana ji dasu, ita ce uwar dakin su duk wani shawara da ita ake yi, Nanah ma kawance su yayi karfi sosai don ko basu je Kaduna ba zata je wurin su a Zaria.

Visiting ko raba shi ake yi kowa da Wanda zai je, Ummiy ce ma ta dan fi su morewa coz on weekend sometimes Anty Zee na zuwa ta duba ta.

***

Kwance ta ke akan gado da daurin gaba domin ta yi shirin wanka ne sai ta kwanta tana karanta wani Novel mai suna SON KOWA, Sosai ta ke jin dadin littafin hakan ya sa ta shagala da yin wankan.

Sumayya ce ta shigo kwanan da kulan Abinci da ta amso musu a dinning tana fadin “Zahra yanzu nayi waya gida su Yaya Abdoul sun dawo, sun ma ce zasu zo min visiting”

“Oh I will finally get to meet them” Zahrau ta fada tasan halin Sumayya in bata tanka ba ba zata barta ta cigaba da karatun ta ba.

  Dariya Sumayyan tayi, Yayyinta biyu ne da ke karatu a India suka dawo Hutu, sai dai dayan Cousin inta ne, suna shan labarin su kala kala gurin kanwar ta su, da alamun dai suna shiri Sosai.

Fatima ce tazo ta tadda su a kwannan, kallon Zahrau ta yi “wankan kenan, toh Albishirinka ruwa ya kare har an shiga rizaf”

Saurin ajiye littafin tayi tana fadin “bari mana, mu kadai a makarantar ma sai anyi rashin ruwa”

“Kar ki manta yan SS3 na nan, kince Sa’a naje naga ruwan ya na daf da karewa na ari bucket gurin Ummi na debo miki” Fatiman ta bata amsa

Ajiyar zuciya ta yi tana fadin “Amma gaskiya kin taimakeni, bari inje inyi wankan Ku jira in dawo sai mu ci Abincin” Soso da soap case ta dauka sannan ta nufi bayin.

***

Yau ne ranar Visiting insu, Ammah, Yaya deedat da Yusrah ne suka zo mata, taji dadi sosai musamman ganin Ya deedat domin yana ji da ita.

Sai karfe uku su ka tafi, kaman ko wani visiting sai da ta raka su har wurin inda malamai ke taru a kasan wani bishiya sannan ta juya.

Hostel ta koma, la’asar aka kira hakan ya sa ta fita Small tap dauro alwala domin ya fi kusa da hostel insu.

Tana shirin kabbara Sallah Sumayya ta shigo tana kwalla mata kira “Zahrau su Yaya Abdoul sun iso” haka kurum ta ji gabanta ya fadi, saurin kabbara Sallah tayi.

Ta so kin zuwa amma ganin yanda musamman Sumayyan ta jira ta ta idar duk yanda ta ke zumudin ganin yayyin nata ya sa ta hakura ta bita.

Zaune su ke akan fararen kujeru da aka tanada domin visiting in, itan kan tana nufu su taji bugun gabanta ya karu ta rasa dalilin hakan.

Sallama ta musu sannan ta gaishe su sabanin Sumayya da ta fada jikin su tana musu oyoyo.

Su Uku ne a zaunen ” ga kawata Zahrau” Sumayyan ta fada tana nuna ta.

Dukkan su murmushi su ka mata, daya daga cikin su ta ke ganin kaman ta San shi, shi ma kallon sanin ko yake ma ta. “Kaman na sanki” ya fada

“Zaria kike koh? Kinyi Therbow School?” Ya tambaya, Kai ta gyade mishi alamun eh.

“Baki ganeni ba koh princess? Kina primary one mu kayi relocating Kaduna, you used to be my little sister back then”

Sarai ta gane shi, ya ma za ayi ta manta Abdoul dinta Wanda idan Uncle Aliy ya basu assignment ya ke koya mata, amma ganin irin kallon da Sumayya ke mata ya sa tayi kaman ba ta gane ba, Sarai tasan halin Sumayya mutum ce mai kishin tsiya ballantana ta San yanda su ke da Abdoul din, farouk ne blood brother inta amma sun fi shiri da Abdoul, ta dade da sa wa relationship in question mark shiyasa gudun kar Sumayyan ta zargi wani abu tayi pretending ba ta gane shi ba.

Tun daga wannan visiting in Abdulrahman ke yawan kira wayan Ummi kawar su da sunan za su gaisa da Sumayya, zasu dade suna waya da Sumayya sannan yace ta bawa Zahrau su gaisa, ba wani hira ta ke tsayawa suyi ba zata ba Sumayya wayan saboda kar ta zargi wani abun.

Ranar hutu Abdou in ne ya zo daukan Sumayya, ganin ba a zo daukan ta ba yace ta zo su sauke ta, ta yi mamakin rashin zuwa daukan ta da wurin da aka yi domin ko irin haka bai taba faruwa hakan bai sa ta bisu ba saboda gudun sabani.

Fatima anzo daukan ta daga kano amma Zahrau shiru kake ji, har ta yanke shawaran kiran waya domin hakan bai taba faruwa ba.

Admin ta nufa gun wani teachern su zata shiga office in kenan ta hango Uncle Aliy da abokin sa Saleem. Gabanka ta ne ya yanke ya fadi don har ga Allah ta manta when last ta ganshi da sunji zai zo zasu tattara su tafi Kaduna.

Karfin halin karasa wa wurin su tayi “kaga gata nan ma kana ta mitan yanda za ayi muganta” Saleem  ya fada

Gaishe su tayi Saleem kadai ya amsa gogan naka kuwa ko a jikin shi, wurin form master ajin su suka nufa ta amshi news letter da ke extension tayi ba result, sai da suka jira Saleem ya ga gaisa da malaman su da ke shi ma school in ya gama sannan su ka tafi.

Ita kadai ke zaune a baya abinta ta kulla wannan ta saka wancan, ta saba duk tafiyan da za tayi sai tayi ciciye kala kala amma banda na yau da ruwa ma Saleem in ne ya bata amma Uncle Aliy ko a jikin shi sai danne danne waya kawai yake yi.

Ko da suka isa Zaria ta iske har an dauko Ummiy daga makaranta, Maijidda kam ta na Kaduna akan Babban Yaya zai zo Zarian washegari sai ya taho da ita.

  Banda harara ba abinda ke shiga tsakanin su da Aliyu ko abu yake so sai dai ya aiki Shahida ko Hamza tsabagen kin da yake musu.

Su ko zaman su a inda yake ma ba so suke ba hakan ya sa suka yanke shawaran bin Babban Yaya Kaduna in ya zo washegari domin sun takuru da kallon banzan da ake musu kallon tsana da kyamata.

Yanke shawara su kayi akan maijidda ta yi zamanta in yaso sa tafi mata da kayan ta. Da kyar Abbah da Baffah su ka amince da zuwa kadunan nasu Mami ce ta sa musu baki sannan aka barsu.

Washegari da safe sun gama hada breakfast suna karyawa a falon Ammah, Aliyu da deedat su ka shiga falon.

Sanin ce wa ko sun gaishe shi ba amsa wa zai yi ba yasa suka gaida Deedat kawai, hakan ba karamin fusata Aliyu yayi ba.

Wani matsiyacin kallo ya bisu dashi sannan ya ce “Ku wasu irin kazamai ne? Ko mai masu aiki za su muku koh? Da kun gama breakfast Ku tabbata kun share ko ina na gidan nan”

Haka ya sa su a gaba sai da su kayi aikin da su ka manta rabon da suyi shi bayan ga masu aiki kiri kiri ya hana su yi, ai ko Babban Yaya na iso jikin su har rawa yake su ka kimtsa kayan su da zai tafi su ka bi shi.

Shi kanshi Aliyun sai da ya fuskanci shi su ke gudu amman ko a jikin shi hasalima shi ma din ba son ganin su yake ba.Haka dai rayuwar ta su Zahrau ya cigaba da tafiya. Ko kadan ba alamun jituwa zai shiga tsakanin su da yayan nasu sai wasan boye da su ke dashi, shi ko kadan bai damu da su ba hasalima harkar gaban shi ya sa a gaba, zuwa yanzu ya NDA inda ya fito da rank in second lieutenant, Lagos aka fara tura shi course inda yayi kusan 2 months sannan port Harcourt.+

  Dawo wan shi jaji ne suka fara shirye shiryen auren abokin su Salim, su ne manyan abokai so duk wani hidima na bikin su ne a gaba. Sai dai duk wani harka da ya hada da mata su Umar ya bari da wannan bangaren shi yasa ba abinda ya hada shi da yan matan amaryar sai a wurin dinner.

Tsaye su ke a wajen hall in suna jiran isowan Amarya domin su ka rasa cikin hall in, shi kan a rayuwar shi yana matukar mamakin mata a ce komai sai sunyi African time tsabagen Nawa ya musu yawa, shikam da shine angon ba abinda zai hana yayi wa Amaryar fada ya tsani bata lokaci.

Wani siririn tsaki ya ja Umar da ke gefen shi ya juyo ya kalle shi “oh kai kam ina ga kafi angon kosawa ma coz tunda dazu na lura da matsuwanka”

“A gaskiya Umar mata na ban mamaki, a ce koman simi simi kaman basu da lakka a jikin su, for God sake tun yaushe mu ke jiran su a nan almost 40 minutes fa”

“Ya za muyi Aliyu sai hakuri” dai dai rufe bakin Umar din motan amaryar ya karaso haraban wurin, tuntuni daman sauran motocin sun karaso Amaryar ka dai ake jira. Kwafa Aliyu yayi shi dai Umar dariya kawai ya mai yana mai shakku anya Aliyu zai iya bin mace yanda take so kuwa?

Wata budurwa ce ta fito daga gaban motan kafin fitowan amaryar, wurin angwayen ta nufa tana smiling, “ina wunin Ku” ta gaishe su duk su ka amsa banda Aliyu da ko kallo bata ishe shi ba sai dai itan ma ba ta San yana existing ba ma gaba daya.

“Sorry yayana mun bata muku time koh? Wlh make up artist in tamu ce ba ta samu iso wa da wuri” ta fada da siririn muryanta tana kallon Salim.

“Haba Reeree a ce duk cikin Ku ba wacce za ta iya kwalliya sai make up artist ta zo” Salim in ya bata amsa coz shi ma he is provoked.

“No yayana nata is kind of special ne after all amaryarka aka fiddo ai” wacce ya kira da Reereen ta fada.

“Shknn ya na iya da ku farida…” Aliyu ne ya katse shi da fadin “wai Salim what’s the essence of all this surutu tunda dai sun iso a yi harama mana time is going”

Faridan ce ta bi shi da kallo ganin yanda ya katse musu magana, tsura mata ido yayi alamun kallon fah? Ita ma ko ta tabe baki sannan ta bar wurin.

Faridan aka kira ta ba couples in shawara, Sallama ta fara yi, tayi addu’an bude taro sannan ta yi wa Allah Godiya nuna musu rana irin wannan, Ayoyin Qur’ani ta fara jawo wa akan zaman aure tana bayani, wa’azi ta yi mai ratsa jiki kan zaman aure Wanda gaba daya yan hall din sai da su ka jinjina ma iliminta both Hausa, English da Arabic ba language da bata yi amfani dashi ba.

Sallama ta yi tare da godiya wa duk wadanda su ka halacci taron sannan ta koma wurin zamanta.

Kallon birgewa Aliyu ya bi ta dashi yana smiling, Umar ne ya tabo shi sai yayi saurin basarwa.

Allah ya gani ba karamin burge shi tayi ba, yana matukar burin ya samu mace mai ilimi ta kowanni bangare Wanda ba zai ji kunyan nuna wa a duniya ba sannan ya’ya’nshi su samu tarbiyya mai kyau. Da alamun wannan ta yi nisa a ko ina.

Haka aka tashi dinnern yana admiring inta. Bai kara ganin ta ba sai da za akai Amarya.

Daga gani ita ce best friend in Amaryar saboda she is always together with the bride, hakan ta kasance a yau hadda ita aka fito da amarya, Umar ne ke rike da key din motan da za a tafi da amaryar, a hankali Aliyu ya tabo shi ya juya kalle shi “pls Frnd canjan key za muyi”

“But why”

  “Please mana” Aliyun ya fada

Keyn Umar ya mika mishi yana fadin” halinka sai kai”

Shi dai amsa yayi bai ko tanka shi ya nufi motan. Yanda ko ya hara gaban motan ta shiga, yana driving yana Satan kallon ta shi dai haka kawai komai tayi burge shi yake, yanzun ma dadanna waya ta ke tana smiling, in bai yi karya ba sai yace bai taba ganin macen da murmushi ya ma face inta kyau ba irin Yarinyar nan da yaji an kira farida.

A bakin motan gidan amaryar yayi parking sannan su ka fita, bayanta ya bi da kallo tafiyan ta ma abin kallo ne komai a natse ta ke yin shi, she is just his dream girl…

A ranar aka yi komai aka gama aka bar Amarya da ango daga su sai halin su, duk an watse ta fito waje a rude tana duba time gaban ta ne ya fadi ganin irin yanda time ya ja tsoron ta Daddy ya San bata gida duk amaryar ce taje mata domin ita ta rike ta.

Amaryar ta kira a waya tana ma complain, hakuri ta bata akan za ta San yanda za tayi. Mota ta ga yayi parking a gaban ta yana mata hon, Salim ne ya fito daga seat in mai zaman banza yana fadin “Reeree zo ki shiga Ku tafi zai sauke ki”

“Thank you” ta ce mai sannan ta bude ta shiga.

“Sorry fa, na daura ma ka aiki”

“Ba wani abu” Aliyu ya amsa sannan ya fara driving car in.

“Ina muka nufa” ya bukata

“Malali kan Raba road ta bashi” ta bashi amsa.

  Har kofan gidan nasu ya kai ta, godiya ta mishi cikin rawan jiki ta bude kofan ta shiga cikin gidan, da alamun ta na tsoron daren da ta kai ne.

Yayi parking kenan zai karasa cikin dakin da su ke shi da Umar in suna Kaduna yaji wani ringing in waya na tashi cikin mota, hasken wayan ya bayyana mishi inda wayan ya ke har kiran ya katse.

Wani ringing in ne ya shigo a karo na biyu, Best Friend ya gani kan screen in, dauko yayi hade da sallama “sorry ta bar wayanta cikin mota na ne yanzu na sauke ta a gida” Amarya ce ta kira taji Faridan ta isa gida jin namiji ya dauko da kuma bayanin da ya mata ya sa ta mikawa Salim wayan.

  Bayani Aliyu ya mishi akan zai kai mata wayan gobe sannan su kayi sallama.

   

Karfe biyun dare a lokacin da kowa ya yi nisa cikin baccin shi amma hakan ya gagara ga Aliyu bawan Allah, sai juyaye juyaye ya ke yi yana rufe ido ko baccin zai dauke shi amma shiru kake ji kaman an aiki bawa garinsu, ga kuma gajiyan da ya saukan mi shi a dalilin hidimomin bikin da su kayi. Fuskar Farida ne ke ta fado mi shi shakka bbu yasan ya fada cikin kogin soyayyan da yake ji ana bashi lbr, bai San yawan tunani ba amma sanadin farida gashi ya sani, wayanta da ke gefen shi ya jawo, pic inta ne kan wallpaper in wayan rungume da teddy, kallon fuskan kadai ya yaye mishi damuwa. Akan abinda ya ke so zai iya yin komai haka in ba ya son abu ma. Bai kwankwanta Son Farida da ya shige shi cikin kwana biyu kuma in sha Allah zai same ta saboda da niyya mai kyau ya ke nemen ta gashi kuma tun farko addinin ta ne ya fara jan ra’ayin shi akan ta. Ganin karfe Uku yayi ya sa shi tashi ya gabatar da Sallahr nafila ya ne me rokon Allah ya biya mi shi bukatun shi na alkhairi. Cikin ikon Allah yana kwanciya wani bacci mai dadi ya dauke shi cike da tunanin Farida.

   Ko da ta shiga gida da daren wurin mahaifiyar ta nufa kafin ta tafi dakinta Allah ya taimaketa Daddyn nata bai neme ta ba. Sai da safe ta fara neman wayan ba ta ga alamun shi ba, Tabbas a hannunta ya ke ba ta sa shi cikin jaka ba, kila ta wurgar ne. Yayanta ta je ta sama a rude ta na bashi lbr, sabon waya ne mai tsada ko wata bai yi ba Daddyn ta ya kawo mata zuwan shi UK.

“Ke fa Allah kin cika careless, wa ma zai ga wayan nan ya mai do kawai ki rungumi kaddara Sisty”

“Kai big b Allah mu dai gwada kira a dace” ta fada cikin shagwaba

“Am not your boyfriend so stop all this your shagwaba its won’t help” Dialling numban na ta yayi

Karfe 9 na safe yana breakfast wayan Farida da ya makale sai kace nashi ya hau ringing, muryar namiji ne ke magana, dauko yayi ya mi shi bayanin komai hade da fadin anjima zai kawo mata wayan nata har gida. Godiya Adnan ya mi shi sannan su kayi sallama.

Karfe sha daya ya shirya zuwa gidan su Faridan, haka kurum ya ke jin wani farin ciki na daban. Numban yayanta Adnan ya kira ya fito su ka gaisa sannan ya mai iso cikin gidan. Ba musu ya bi shi domin shi ma ya dauri anniyar sauke abinda ke damun shi.

  Faran faran su ka gaisa da Adnan kaman sun saba da juna tun tuni, a hankali Aliyu ya sanar mi shi abinda ke tafe dashi, haka kurum Adnan ya ji ya yadda da shi but duk da haka sai da ya nuna mishi mahimmancin so tsakani da Allah, sun fahimci juna sosai sannan Adnan ya ce ya bashi numban shi in sunyi magana da Faridan zai sanar mi shi.

  Aliyu bai yi kasa a guiwa ba ya kara samin Salim ya sanar mishi, tsiya su ka yi ta mai shi da Umar kafin Salim ya yadda ya ma matar ta shi magana, ita da Salim in su ka same ta, da farko ma cewa tayi he acts rude sometimes but ganin yanda Salim in yayi ta mata sha’awar Aliyu ta San ba zai cuceta ba sai kuma gashi Yayanta ya same ta ya mata maganar, haka kurum taji ya burge ta ta yanda ya biyo abin shi.

Ranar da ya fara zuwa gun ta daga ita har Aliyu wani iri su kayi ta acting duk ba a saba ba Dan ma da Umar ya je kusan shi ya masa hiran, a hankali su ka fara sabawa da juna sannan suka kulla alaka mai karfi a tsakanin su, amma da iyaye su ka shiga maganar fir Daddyn na ta ya ce sai ta gama makaranta dalili kuwa so yake ya ga kamun kudin sojan zuwa lokacin saboda yanzu ya fara tarawan. 20th August, 2013+

                            5:30 pm

Da  sauri da sauri su ke tafiya sanadiyar hazon da ya mamaye sararin samaniya, shakka bbu ruwa na daf da sauko. Anty Rukayya su kaje amsowa a sauko a nan cikin kinkinau sai dai da dan nisa amma duk da haka sun zabi tafiyan a kafa, a cewarsu ana tafiya ana hira hakan ya fi dadi.

Wani irin guguwa ne ya fara tashi, da ke unguwan akwai wadataccen yashi, kasa ne ke tashi kaman ruwan sama. Dukkansu durkusawa su kayi domin kare idon su.

Kofan wani gida da ke wurin kwanar layin da za a je gidan Anty Rukayya su ka tsaya kafin kuran ya raguwa. Sai dai me kuran na tsayawa aka tsuge da ruwa kaman da bakin kwarya, duk da dai sun fake amma ruwan mai hade da iska ne yana iso su. “Oh mu yau daman sai da Anty ta fada” Maijidderh ce ta yi magana cike da nadaman fitan da suka yi a kafa duk da antyn ta gargade su. “Saukin ta ba mu fito da wayoyin mu ba” Nanah ta fada. “Mtswww” a tare su ka ja tsaki su duka ukun suna hararanta. Ummiy ce ta ce “ke dai wlh ina ga ba abu mai mahimmanci a rayuwar kaman waya”

“Da mun zo da wayan ma ai da ko malam Ado ma kira” Zahrau ta fada.

Sun dan jima a fake ganin ruwan ya dan tsagaita amma bai da alaman daukewa gaba daya ya sa su ka lallaba hakanan su ka karasa gida.

A bakin gate in gidan su ka hadu da wani saurayi ya fake a wurin sai faman rawan dari ya ke ga numfashin shi na neman seizing.

Sanye ya ke da 3 quarter ash colour, tsa tsaf ya ke amma kallo daya za ka mishi ka gane ya kwode dan har colour in ya fara fading, sai bakin riga mai guntu hannu ba laifi bai kai wandon kodewa ba. Kallo su ka bishi da shi kaman yanda ya bisu dashi.

“Ai da ka lallaba ka tafi malam dare nayi gashi kuma ruwan bai da alaman daukewa” Ummiy ta fada cike da rashin yadda.

“Ehm ehm Ummiy ki ka San nisan da yake dashi gashi unguwan nan ba a samun abin hawa da dadin rai, kuma daga ganin alama sanyin nan na mishi illa. Ina laifin ya shiga dakin IB in yaso ko shayi ya sha sai ya wuce din.”

 

  Kallon hankali dayaUmmiy da Nanah su ka bi Maijidderh da shi sabanin Zahrau da ta shiga ciki ta bar su a wurin don tun ainihi itan mutum ce mai jin sanyi sosai.

“Malam bismillah koh” Maijidderh ta fada tana mishi murmushi. Ganin da gaske ta ke yasa su Ummiy su ka shiga gida su ka barta a wurin.

Dakin IB mai gadinsu ta kai shi bayan ta ma IB din bayani, Wurin Anty Rukayya ta kara zuwa ta mata bayani ita dai bata ce mata komai ba.

Ruwan zafi ta tafasa hade da kayan shayi ta kai mai. Gogon naka kuwa daga kai kawai yayi yana kallonta da kyar ya iya bude baki yace “nagode” da ke ita Dan Allah tayi ba Dan godiyan na shi ba ko kadan hakan bai bata mata rai ba.

“Bara inje ko akwai abinda kake bukata?” Ta tambaya tana nufan kofan dakin.

“Man zafi” kawai ya ce mata yayi shiru.

  Man zafin ta je ta dauko mai ta same shi yana sallah, jira tayi ya idar sannan ta bashi ya amsa wannan karan ko arzikin godiyan ba ta samu ba sai da zata fita yace mata “Zan tafi, ina zan samu chemist”

“Eh akwai ba nisa IB Dan Allah raka shi mana”

“Toh” Ya amsa hade da mikewa

Saurayin ne ya juyo ya kalleta a hankali yanda za ta iya ji yace “Sannu fah  nima sunana Ibrahim, kin taimakeni da pneumonia ya tashi” sai kace dole yanda yake maganan

“Allah ya kara lfy am Maijidderh”

“Nagode Hauwa’u” ya fada cike da murmushi sannan ya bi IB su ka bar gidan.

***********************************

  Zahrau da Maijidderh ne a kitchen suna faman hada lunch, na yau din special saboda guest da Anty Rukayya ta ce musu zata yi ga kuma Sumayya za ta zo wurin zahrau, hakan ya sa suka zage wurin hada abinci na musamman, cuisines kala kala. Basu farga ba kayan salad ba sai da su ka gama dafe dafe su hakan ya sa suka yanke shawaran fita su siyo.

Daga nesa ta hango shi a gefe guda ear piece a kunnen shi yana duba jarida mutumin da Maijidderh ta taimaka jiya ne Ibrahim. “Wancan kaman mutumin ki na jiya” Zahrau ta nuna ma Maijidderh suna isa wurin mai sai da kayan Salad in.

“Ai ko shine” ta amsa

Kayan salad in da suka rage a wurin kadan ne kuma duk sunyi wani iri “Sannu Malam Dan Allah nace ba wani ne sai wadannan” Maijidderh ta tmby

“Yanzu za a kawo min daga kasuwa ko za Ku dawo nan da mintuna Ashirin” Mai saida kayan ya fada

“Kash Wlh da dan nisa ne anya Maijidderh ma zamu fasa ba kawai” Zahrau ta fadi tana ya mutsa fuska saboda nisan wurin da take gani.

“In ba matsala to Ku bar kudin mana inyaso wancan ya kawo muku Ku biya shi” ya fada yana nuna Ibrahim “sai kuje dashi yanzu ya ga gidan”

“Baba to shi kuma aikin shi kenan?”

Maijidderh ta bukata

“Allah sarki yarinya shi hanyan con abincin shi kenan, ya zo gari cirani bai San kowa ba da wannan yake Dan lallabawa kafin ya samu wani aiki mai dan karfi haka”

“Allah sarki” su ka fada a tare

Kiran shi tsohon yayi ya fada mishi aikin da zai musu, daga kai yayi ya kalle su sannan ya kalli tsohon yace “shikenan Babah na San gidan zan kai musu” gurin da yake zaune ya koma ko kara kallon su bai yi ba.

Ko da suka koma gidan har Sumayya ta iso. Da gudu su kayi hugging juna da Zahrau suna murnar ganin juna.

“Yaya Abdoulh yace in gaisheki shi ya sauke ni” Zahrau dai murmushi kawai ta Mata.

Tare su ka ciga da aikin suna hiran schl, har Ibrahim ya kawo Salad in, Dari biyar Maijidderh ta bashi wai ya dauka duka, godiya ya mata ya wuce abin shi don da alamu yana needing kudin.

Anty Rukayya ta sa su kai ma bakin nata abincin, was zasu gani? Uncle Aliy da abokan nashi wato Umar da Salim.

Bakin ciki kaman ya kashe Zahrau da Maijidderh haka su ka cije su kayi sallama “INA wuninku” su ka fada a tare. As usual su biyun ne suka amsa banda Aliyu.

  “Bismillah sauko ko kai ke ta babatun yunwa” Umar ya fada yana taba Aliyu.

Hararan shi yayi sannan yace “na maka kama da Wanda zai iya cin abincin kazaman yarannan? Ku dai da zaku iya Ku min sauri Farida na jira na”

“Eh lallai Aliyu kai mai budurwa wato ta maka girki ba za kaci na kannen ka ba ko?” Saleem ya fada cike da tsokana.

Su dai suna gama abinda ya kawo su su ka bar wurin su kaje suna ba Ummiy lbr takaicin wahalan da suka sha Ashe kan shi ne sunyi Allah ya isa ba adadi ita ko Ummiy har Sujjada tayi ta godewa Allah da bata sa hannu a girkin ba.

Suna falon su ka zo wa Anty Rukayya Sallama sannan suka wuce, ni ma nace Allah ya raka taki gona.1

  Da Yamma Abdulrahman ya zo daukan Sumayya, dukkansu su ka je rakata hadda ya’ya’n Anty Rukayya.

Duk a tare su ka gaishe ya amsa sannan yace “Aa Sumy haka kika yi jama’a ne?” Murmushi kawai su ka yi dukkansu tace “yaya Abdoulh kasan daman ni mai jama’an ne”

“Naga alama kam, Zahrau ba kirki ko? Ko Neman mutane ba kya yi”

Faking murmushi tayi tace “no ba haka bane”

Yace “to menene? I need ur number”

Wayan shi ya mika mata.

Ba musu ta amsa ganin yanda Sumayyan ke smiling ya sa ta rubuta mishi numban.

“Thank you” ya fada sannan su ka wuce.

  Anty Rukayya ce ta zo ta same su a falo suna hira ta musu complain akan malam Ado zai bar aiki nan da 2 weeks wai zai koma garin su. “To wa zai dinga kai su khalipha schl Anty” Ummiy ta tmby.

“Gashi kuma babban Yaya bai so kina driving” Zahrau ta kara

“Akwai wani sai dai bansan ko ya iya driving ba” Maijidderh ta yi saurin fada.

“Ina kika San shi Maijidderh” a tare duk su ka tmby

“Wanda na taimaka rannan”

  Anty Rukayya ta so hana Maijidderh yi ma Ibrahim magana amma ganin yanda ta dage ta na son taimakon shi ya sa ta barshi.

Ko da taje ta same shi bai mata boye boye ba yace mata shi bai iya driving ba amma Sam Maijidderh ta dage wai Malam Ado sai ya koya mishi kafin ya tafi.

Ba musu Ibrahim ya yadda saboda shi ma yana son aikin, a haka suka fara fita koyan tuki da Malam Ado kullum maijidderh sai ta ajiye mishi abinci hakan ya sa suka dan saba saboda shi ba mai son magana bane.

A cikin 2 weeks hannun shi ya dan fada saboda daman ba lokacin ya fara koyan mota ba a yanda ya fada kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page