SHU'UMIN NAMIJI COMPLETE BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 2 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 2 BY FATYMA SARDAUNA

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

” Lafiya kuwa Zaid wakake nema ne ?” Bash yatambayeshi,, ɗan taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa ” bakomai kawai ina duba yanayin unguwar ne ” yaƙare maganar yana mai komawa cikin motarsa yazauna,,, sama sama Bash da Zaid sukayi magana, domin kwata kwata hankalin Zaid baya jikinsa, burinsa kawai shine idanunsa su sake yi masa to zali da wannar kyakkyawar fuska da jikin, daya gani…..+

Tunda Zahrah tafito daga gidan su Husnah tafuskanci cewa da akwai mai binta a baya, hakan yasanya taji wani irin tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, don haka ta ƙara ɗaga ƙafufunta, “Assalamu Alaikum !!” muryan Namiji mai cike da kamala ya doki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya da tafiyan da takeyi batare da ta juyo ba,, cikin takunsa na burgewa ya ƙaraso gareta, kyakkyawan saurayi ne, mai ɗauke da launin fata choculate colour, dogo ne amma ba har canba, yanada faffaɗan jiki mai burgewa, sannan yana da kwarjini ba laifi,, murmushi yayi mata haɗe da cewa “Ƴan Mata bazaki amsa sallaman nawa bane ?” saurin sunkuyar da kanta ƙasa Zahrah tayi haɗe da cewa “Wa’alaikassalam”

Lumshe idanunsa yayi domin kuwa bakaɗan ba zazzaƙar muryarsa tadaki ƙahon zuciyarsa ” Sunana JABEER, Idan bazaki damuba, inaso kibani adireshi’n gidanku, sai nazo, domin a matsayinki na mace mai mutumci baikamata natsaidaki a bakin hanya ba ” Jabeer yafaɗa hakan yana mai kafeta da idanu,, gaba ɗaya kanta ɗaurewa yayi don haka, batare da tace dashi ƙala ba, tacigaba da tafiya, da sauri sauri,, roƙonta Jabeer yashiga yi akan ta tsaya ta saurareshi, amma ina Zahrah ƙara ɗaga ƙafanta tayi domin ita tsoro ma yabata, ganin da Jabeer yayi cewa bazata tsaya bane yasanya shi ƙyaleta kawai tayi tafiyarta, amma a zuciyarsa ya ƙudura aniyar nemota komai daren da ɗewa ….. Zahrah tana komawa cikin gida kaitsaye ɗakinta tawuce, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa a kai akai tamkar wacce tayi gudu, idanunta da suke lumshe ta buɗe su ahankali, haɗe da da sanya harshenta ta lashi lips ɗinta na ƙasa, Allah yasani gayen ya burgeta amma kuma tanajin tsoro gaskia, domin bata saba tsayuwa da samari ba……

Birgima kawai yakeyi akan makeken gadonsa, kwana huɗu kenan daganinta amma da ya rumtse idanunsa, hoton kyakkyawar surarta yake gani, baisanta ba, baisan wacece itaba, amma wani irin sha’awarta yakeji, tabbas yazama masa dole komawa unguwar Suleja ko Allah zaisa yasake ganinta,, wayarsa dake ringing ne yakatse masa tunanin da yakeyi, DADY shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayara, ɗaukar wayar yayi a kasalance haɗe da karawa akan kunnensa “To” kawai naji yace haɗe da cilli da wayartasa gefe, tashi yayi daga kwancen dayake haɗe da ɗaukan rigarsa yasanya, ya fice daga cikin ɗakin…..

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE