KOMIN HASKEN FARIN WATA COMPLETE BY ayshay bee

KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 2 BY ayshay bee

KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 2 BY ayshay bee

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Asubancin barin Zaria Aliyu yayi coz ba zai iya zama yana ganin abin takaici ba. Fisabillilahi upon all matan duniya a rasa da wacce za a hada shi sai daya daga cikin yaran nan, yaran da basu San mai ke musu ciwo ba kai at all ma shi ba ajin su bane, yaushe su ka girma duka duka ma ko ishashen hankali da ilimi he don’t think su na dashi da har zasu iya mu’amala da mutanen shi. Shi Mutum ne mai hulda da manyan mutane shiyasa tun farko yana mi wayyayar mace wacce ba zata bashi kunya ko kadan ba duk bayan wadannan ma Zahrau ba choice in shi ba ce ko kadan ba ta cikin irin maccen  da yake so.1

   Shi dai Umar hakuri ya dinga bashi da kuma bashi shawaran yayi biyayya ga iyayen shi sai ya ga alkhairi da bai taba expecting ba.1

 

••••••••••••

Cirkowa suka yi gaban Zahrau da ke ta rawan dari, zazzabi ne mai zafin gaske ya rufe ta lokaci daya sai sambatu ta ke yi. Ummiy ce ta kalli Zahrau ta girgiza kai “gashi nan ai tun ba a kai ko ina ba, ni ban ga dalilin da yasa za a fara irin tunanin nan ba”

“Zuwa zanyi kawai in kira Mami ta zo ta gane wa idonta abinda ke faruwa in kuma sun shirya rasa ta ne fine” Maijidda ta fada tana share guntun kwallan da ke idonta. Har ta kai baki kofa Nanah ta yi saurin tare ta “Haba Dan Allah wai Ku me ke damun Ku ne, yanzu ke kika je kika fada musu da wanne kike so suji, kar fa ki manta halin da Abbah ya Shiga a dalilin abinda mahaifin Farida ya musu suna kuma ganin su samu solution sai kije ki kara daga musu hankali? Gani zasuyi sunyi failing ta a matsayinta na yar su shi ya sa ba za ta iya musu

biyayya ba. Kuma ita ma kamata yayi Ku kwantar mata da hankali ba Ku dinga daga mata ba wai shi Uncle Aliyn annoba ne ko kuma makiyinta ne. After all yanda zazzabin nan ya rufe ta tausayinta ya kamata kuji ba Ku kara dagula mata lissafi ba” Ummiy ce ta katse ta “Ba gwara Annoban da kika kira ba akan Uncle Aliyn, Nanah kina ganin shi ne kawai Allah kadan ya San iya tarin muguntan da ke cikin shi. Wlh auren nan ba alkhairi a cikin shi ko kadan Dan kawai cutan ta za ayi”

“Subhanallah shin Ummiy ke ke da ikon Allah ne ka kuwa da zaki yi rantsuwan nan”

“Ai juma’ar da zata yi kyau tun daga laraba ake iya gane ta, mu ba zamu yadda muna kallo a kai ta ajalin ta ba”

Maijidda ta fada tana hararan Nanah

“Ehmm tun da kuka haife ta ba” Nanah ta fada cikin fushi dan zuwa yanzu sun fara kai ta bango.

   Hayayako mata su kayi tayi banza da su ta Shiga baya debo ruwa a wani roba da towel. A kai tazo tana shasha fa mata ko taji saukin ciwon.

************

Mami na zaune da Ammah suna tattauna hidimomin bikin wayanta ya dau kara. Aliyu ne daman ta San dole yau sai ya neme ta shiyasa ta share batunsa da ya zo da safe shaida masa batun komawarsa Abuja.

 

   “Mami an wuni lfy?” Shiru mami tayi tana nazarin muryar shi daga ji ta San yana cikin damuwa

  “Aliyu lafiya naji ka haka?”

   “Mami Dan Allah wani Alfarma nake nema a wurin ki”

“Ince wa Abbah ba ka son auren ko?”

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE