JIRWAYE COMPLETE

JIRWAYE CHAPTER 10

JIRWAYE CHAPTER 10

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zainaba kam tunda maganar auran Mahmoud da Laylah ya iso ta ta rasa sukuni. Duk ta bi ta rasa kwanciyar hankali, ba kadan hankalinta ya tashi ba dun ta san Laylah is a strong competition. Duk abunda take tunanin tana dashi Laylah ta fi ta dashi. Dun haka ita da mahaifiyar ta da kawaye aka ta shige da fice gidan bokaye da malamai, neman asiri har Maiduguri, duk dun a fasa biki amma ina Kullum sai Matsowa kusa time yike, ga shirye shirye ana ta yi ba dare ba rana. Tsohon gidan da suka zauna Mahmoud yayi renovating ya dawo kamar sabo, daidai standard din wanda suke ciki a yanzu, a nan Laylah zata zauna. Unguwar ba nisa da unguwar da zainaba take. Da ka gansa yanzu kaga hutu da kwanciyar hankali, dun kusan Kullum in ya tashi aiki sai ya bi gun Laylah kan ya shiga gida kuma tafi basa kulawa fiye da matar sa da ke gida wanda ba abunda da ta iya daga gulma da kawaye sai kallon zeeworld and telemundo, going from one wedding to another, aikin kenan Kullum. Batawa cikin ta ta ci ba, bata yi wa yaran ta sun ci ba bare wani miji. Koh su yaran suna jin dadi in Baban su yace zai kai su weekend gun auntie dinsu because tana basu full attention dinta, tana bata su sosai. Kan a maida su gida sai ta tabbata an sake musu sabon hair do, an gyara su tas. Hakan nayi wa Mahmoud dadi matuka.+

Ita kam zainaba sabon mota ya sake mata ya mata alkawarin kujerar hajj duk wai cikin compensation da ake ba mata in zaa yi fadin kishiya banda kaya da siya mata amma duk wannan didn’t calm her down, ita kawai a fasa bikin shine burin ta.

Wata ranar Monday very early, after tayi dropping yara a school kawai tayi zooming off to GRA inda gidansu Laylah yike. Bakin gate ta dinga manna wani mahaukacin honk har sai da security man din ya buda mata gate ta shiga. Bata ma tsaya ta gyara parking ba ta fito daga cikin mota sai ihu take tana approaching main entrance din gida. A makeken living room inda ke downstairs ta tsaya tana ta fuming sai Ummati ta shigo cike da damuwa a fuskar ta tana lafia?.

“Ina take, ina wancan Shegiyar Karuwar take!”.

“Subhanallah! Me zan ji haka ni Rabi’atu”. Ummati ta fadi tana mamakin wai zainaba ce ke fadin haka.

“Dallah rufe mun baki tsohuwar banza, har da ke ai. Shegiya baqar munafuka! Ni din da kike fadin kin dauke ni tamkar diya shine zaa hada baki dake a cutar da ni dun iya shege. Ban barin gidan nan yau wallahi sai na ci wa wancan Karuwar diyar take mutunci. An je an gama yawon karuwanci an kwaso cuta zaa zo a liqa mun….. inaaa bazan yarda ba”. Zainaba ta dinga, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

Shima Abba hayaniyar da ya ji yayi yawa ne yasa yace wa yaron da ke kula dashi in Ummati bata kusa ya tura wheelchair sa zuwa main living room din gidan yaji dalilin wannan hayaniya da sanyin safiya. “Ke Baiwar Allah Meya faru”. Ya tambaya a hankula.

“Dallah rufe mun baki, tsohon banza. Shiyasa a haka zaka dawwama akan kujerar guragu. Mutane ne ba abunda kuka sa gaba sai kwadayi da cin amana toh wallahi sama tayi wa yaro nisa. Duk na sha karfin ku, sai ma na hadu da wancan annamimin, baqin munafiki mai halin ýan wuta, sai kace ba da shi aka zo neman aure na ba amma yanzu dun gulma ya dau gwalgwajin kanwar sa ya jonawa mijina, kun rasa yadda zaku yi da ita kawai zaku liqa masa. Waya ce muku shi bola ne da kowa zai iya watsar da sharan sa?”. Ta dinga, Ummati dai tana tsaye tana ta kallon ikon Allah.

Laylah kam hayaniyar da ta ji yayi yawa ne ya tashe ta, miqewa tayi ta zauna kan gadon ta ta rasa reason for the noise so early. Da taji shuru noise din sai qaruwa yike kawai ta dau dan karamin hijaab dinta ta sanya ta fito. Koh da ta sauko taga masu aikin gidan sun taru ga iyayenta nan, ga kuma zainaba sai maganganu take fadiwa mahaifiyar ta. Cikin hanzari ta qaraso.

STORY CONTINUES BELOW

“Toh bari in fadi miki…..”. Zainaba ta fadi tana nuna Ummati da dan yatsa. Bata gama fadin abunda take ba Laylah ta kamo dan yatsar ta dinga murdawa tana kallon yadda zainaba ke flinching in pain.1

“Me zaki fadi mata? Fadi mu ji”. Laylah ta fadi still tana murda mata hannu. “Uwar ki bata koya miki girmama na gaba da ke ba koh?”. Ta kuma fadi in a very calm tone, koh kadan bata bari bacin ran ta ya nuna ba “Now I see why mijin ki ke buqatar wani auran. Empty vessels sure make the loudest noise”. Ta fadi tana mata flinging da hannu.

“Banza, ballagaza, shara, bola dake har zaki buda baki ki wa mahaifiya ta rashin kunya? Toh wallahi kiyi hattara da ni. Ki ji tsoron randa zan shigo gidan Mahmoud, dun daga ranar ya tashi daga sunan naki, like as I said before in me wuri ya zo sai me tabarma ya nade ya tattara ya san Inda dare ya masa”.

“Ke!…”. Bata gama magana ba Laylah ta watsa mata mari, koh gama farfadowa daga zafin marin bata yi ba Laylah ta qara mata wani a dayan kumatun. Gaba daya ta sa hannayenta kan kumatu tana sosawa dun tsananin zugi da both cheeks ke yi, ga hannunta da ke mata dan karan zafi, from all indications Laylah ta mata targade.1

“Tsohuwar banzan can da kika bari Girei ita ce ke ba ni ba. Ni Badejo nike, yarinya ýar halal. So next time call my name with respect dun wallahi very soon zaki fara zuwa guna neman permission din yin abubuwa ke da gidanki. Yes that’s how much control I’ll have over the household. Mara hankali da tunani kawai. Go home and start counting your days”. Laylah ta fadi mata. Without warning kawai ta riqo mata hannunta daya ta jawo ta har bakin qofa ta tura ta waje kan ta jawo qofar ta rufe tana fadin a gayas.

Zainaba kam jiki ba sauran karfi ta wuce ta shiga motar ta, sai lokacin ta tuna cewa ta bar baby dinta cikin mota, yaro har yayi kuka ya gaji ya kama yatsa yana ta tsotsa har yayi barci. Tana fita daga harabar gidan tayi parking mota gefen titi ta duqar da kai, kawai sai kuka ta fara tana sosa kumatun ta. Laylah ta girgiza ta ba kadan ba. Tsoro ne ya da da cika ta duk ta rasa abun yi. Da kyar ta samu ta tuqa kanta zuwa gida. Tana isa ta kira kawar ta da ta bata advice din zuwa gidansu Laylah yin cin mutunci tana fadi mata yadda tables din suka yi turning.

Laylah kam on her own side haquri ta shiga ba iyayenta akan cin mutuncin da aka musu saboda ita tana gama haka ta hau sama zuwa dakin ta ta dau waya ta kira Mahmoud da niyyar yi masa tatas. Da ace insult din kan ta ya tsaya da Laylah bata damu da kiransa ba amma dun cin fuska har iyayenta baa bari ba. Aikam yana daukar waya ta fadi masa cewar ya ja wa matar sa kunne koh tsayawa sauraron sa bata yi ba ta katse wayarta. Yana ta kira shuru, kawai yaji hankalinsa be kwanta ba dun be san irin damage inda matar sa tayi ba dun haka kawai excuse ya dauka, yayi cancelling class inda yike dashi ya wuce gidansu Laylah. Koh yadda yaga iyayenta sun gaida shi jiki a sanyayyaye told him everything, yasan all is not well. Koh da ya zauna jiran Laylah ta fito, Addu’ar sa daya; kar ta zo masa da bad news. Kada yarintar zainaba yasa suce sun fasa.

Sai da Laylah tayi wanka ta shirya kan ta fito zuwa Majlis din. Kan ta wuce ta shiga kitchen ta bada orders wa masu aiki da su kawo mata breakfast dinta Majlis din, and su kawo da extra plate. Tana shiga ta dan yi masa murmushi, bata bari emotion dinta yayi getting best of her ba. Ta shiga bata dade ba aka kawo breakfast din, kayan tea aka kawo da toast. A hankula tayi spreading butter on some toasts kan ta hada black tea ta ije masa gabansa. Kamar ta san koh breakfast be yi ba. Sai da ya gama cin abinci kan ta fara mayar masa da duk abunda ya faru from A to Z bata boye masa komi ba, har marin da ta wa zainaba. Shikuma kunya ya ji yayi ta bata haquri yana fadin he’ll look into the matter. Be tafi ba sai da ya shiga cikin gida ya ba su haquri suka ce masa ba komi, Allah dai ya kiyaye.

Daga gidansu Laylah, Mahmoud gidansa ya wuce direct be koma office ba. Yana shiga kam ya sama zainaba zaune da kawayenta sai hira suke ana shewa, tun daga bakin qofa yike jin muryoyin su sai habaici suke ta yi. Koh da yayi sallama ya shiga ba wacca ta ansa masa a cikinsu. Shima rai bace ya shiga ciki ya kira zainaba kan ya wuce bedroom. Ita kam kamar ba da ita yike ba ta zauna suka cigaba da shewarsu, sai da ya jira ya gaji tukun ya kuma kiranta a waya.

“Koh kin manta ina jiranki ne”. Ya fadi tana daga wayar.

“Na sani ai amma abu nike”.

“Abu kike? Abu kike?”. Ya maimaita kalamanta.

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE