RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 12 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

                Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Umma ta sunkuyar da kai, hatta danta kunyarsa take ji sosai. Shi kansa Abba ta kasa~ ganin fuska a wurinsa. Sultan ya nemi? wuri ya zauna, duk suka yi shiru a dakin. Ya dubi Hafsat ya ce, “Zan sa a kama Salim, sai ya dandani irin bakin cikin da yasa mu -ciki. Hafsat har yaushe kika yi wayewar bin saurayi gida? Ina. tunaninki yake? Ina iliminki da wayonki? To sai kin haife cikin kuma dole ya aureki, bayan ya gama shan wahala gidan yari.” Ya mike kawai ya fice ‘yana jinjina wai Umma ce ta makantar da Nasreen saboda tsabar Kiyayya.
Washegari Sultan suka wuce Abuja, kasancewar ya sami kiran gaggawa daga office

ZAMU TASHI 

A gida ya ajiye Nasreen ya wuce abinsa. Tana shiga ciki ta kama gyara ba tare da ta duba bangaren Zakiyya ba, komai ta shirya shi a ma’adaninsa tana jin tunanin mutumin da aka kira a matsayin mahaifinta yana ci gaba da addabanta. Har ta gama abincin bata bar tunaninsa ba. Ta rasa a tsakanin tausayi da tsanarsa wannene yafi tasiri a zuciyarta.
Yau shigar Kananan kaya ta yi, kasancewar garin da zafi. Zakiyya ta leKo dakin ta ci burin koma me ke cikin ran Nasreen akan kwana da miji, ita sai ta daKile hakan. Yana dawowa ya fada wanka ya dan kintsa sannan ya shiga bangaren Zakiyya yace ta zauna yana son magana da ita.


Babu musu ta zauna ya dubeta duba na tsanake ya ce, “Zakiyya na zo in yi maki magana ta Karshe daga haka kina iya wuce wa gidanku. Kin ganni nan? Bana son fitina, bana son tashin hankali, idan kika sake zagin yarinyar nan, ko! kika sake gaya mata maganar da Za ta sa ta kuka. Wallahi! Za ki tattara ki koma inda kika fito. Da kike yi mata gorin uba, ke waye yasan naki uban? Zan dauki mataki KwaKKwara akanki. Sai da safe.” Ya mike ya fice abinsa. – Www.bankinhausanovels.com.ng
Da shigarsa ta tare shi kamar wacce take jiransa. Rungume juna suka yi, ta saki ajiyar zuciya mai Karfi, “Namiji daya ne a gabana, amma yafi maza dubu. Kana da kima a idanuna, ina sonka, ina yi maka irin son da duk wanda ya tsaya kwatanta shi, bai san girman son ba ne. Yau zan yi barci irin wanda na jima ban yi irinsa ba.” Sultan ya shaki Kamshinta yace, “Allah na gode maka da na samu irin wannan tarbar a gurinki. Ban yi tunanin Kunci zai barki ki tarbe ni ba. Hakan yake nuna min ke matar Kwarai ce, mai danne damuwarta don ta faranta ran  mijinta.”
Ta ji dadin yabawan miinta, suka koma gado. Anan wasa ya sauya jin kansu, suke yi kamar wadanda suke dauke da Kishir ruwa. Ko da yake dukkan su makoshin su a bushe yake. Sun gama fita hayyacinsu suka ji ihun Zakiyya. Nasreen ta fara mutsu-mutsu za ta Kwace kanta, Sultan ya sake sauya salon wasansa, dole ta mance da wani ihun Zakiyya, a wannan dare Sultan ya tabbata ango, a wannan dare ya bambance budurci., da kuma_ rufa-rufa. A wannan dare ya fahimci dadin aure da yake yawan ji ana fada. Haka a wanann dare ya fahimci ashe lafiyarsa Kalau? Nasreen tasha albarka, hakan ya Kara mata juriya, sannan ta dage bata son duk wani dalili da zai batawa Sultan, ta rasa da me za ta saka masa irin wannan Kauna da ya nuna masu?
Da safe ta nemi yin Karfin hali, tana ta mike ta fasa Kara saboda wani irin zafi da ya ziyarce ta. Dole ya hana ta yin komai, ya fita da kansa ya kawo mata abinci, duk abinda ake yi Zakiyya tana nan zaune a falo ta ci kuka idanunta sun kumbura. Amma ko duban inda take bai yi ba. Cikin ikon Allah kafin dare ta fara tafiya da Kafafunta, sai dai jikin babu Karfi.
Dole Sultan ya dinga lallaba ta. A falo ya — ajiye su, Zakiyya ta dinga jin kamar ta shaKo Nasreen ta kasheta kowa ya huta. Sultan ya yi jawabi, ya kuma Kara da cewa yanzu ne zai yi kwanaki bakwansa, da tuntuni suka hana shi yi da matarsa, bayan kwana bakwan za su raba girki, kowa kwana bibbiyu. Ya Kara da jawowa Nasreen kunne akan ta rike Zakiyya a matsayin yayarta, duk da ita ce uwargida, yana son su mutunta junan su. Zakiyya ta dube su sosai, kawai ta kada kai ta bar dakin. ‘Nasreen ta dago cikin jin kunya ta dan saci kallonsa, ya aika mata da murmushi, yana sake ware idanunsa akanta, “Wai har yanzu kunyar ce? Ashe ban cireta gaba daya ba, ina zuwa.” Nasreen ta dago cikin nuna tsoro ta ce,Www.bankinhausanovels.com.ng “Wallahi babu kyau fa.” Ya yi murmushi yana jin natsuwa tana shigarsa. Hannunsa ya mika. mata ta noKe tana nuna masa-. hanyar dakin Zakiyya.
” Murmushi ya yi ya ce. “To mene ne?” . Girgiza kanta ta yi cike da son mijinta ta ce, “A’a idan ni ce na zo naga hakan ai sai na kwana _ ina yi maka kuka. Don”haka ina.amfani da hadisi, ina son wa kaina‘ abinda nake sowa dan ‘uwana.” Ta mike tana Kokarin guduwa, sai dai ba za ta‘iya ba, har ya cimmata ya dauke ta, tana mutsuU-mutsu, bai dire ta ko’ina ba sai kan gadonsu. Ya hada fuskarsa da nata yana dubanta sosai, sannan yasa hannu ya ja hancinta ya ce, “Haka Allah ke lamarinsa, shi ya hada soyayyar mu tun kafin ki fito duniya. Shi ya nuna min Anti ya ce, ga matarka can a cikin baiwar Allan can, maza jeka ka dauki abinka. Bana danasanin kasancewa da ke, ko da kuwa za ki dinga dibo wuta kina Kona min jiki da shi ne Zan ci gaba da sonki har in koma ga Mahaliccina, Kanwata ta jini kuma matata.”
Nasreen ta ware idanunta tana son kallon sa, sai dai kunyarsa ta hana hakan, don haka ta dan lumshe idanunta ta ce, “Ko da zan dauko bakin wuta da ninyar in Konaka bana tunanin zaka ji zafin wutan, domin babu komai a cikinsa sai ruwan sanyi. Bana jin wannan hannayen nawa Za su iya cutar da kai, bana tunanin idanuna za su tsaya kallon maKiyinka basu dauki mataki ba. Na tabbata ka haddace kalaman nan nawa, masu KanKanta amma kuma suna da kaifi, Ina sonka, Ina sonka.” Sai kuma ta rintse idanu’ tana jin hawaye suna zuba daga idanunta. Hannunsa yasa a bakinta, “Shiiii… Idan kika yi min kuka sai na fasa dan bakin nan.” Haka suka sake komawa cikin shaukKin soyayyarsu kamar Za su cinye juna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya dauki Nasreen da Umma da Naufal ya kaisu har gidan su Saudat. Iyayenta suna nan a raye, bayan sun karbe su né, Umma ta yi masu bayani, kafin su ankare*har mahaifiyar Justina ta shake Umma, “Shegu mugaye! Kun raba mu da ‘yarmu kun jawota cikin musulunci daga Karshe kuka kasheta. Haka addinin naku yake? Kuna cewa kuna da gaskiya kuna da tausayi, ina tausayin yake anan? Kune dukan mata, kune yi wa duk wanda ya musulunta gorin musulunci, ku ne Kyamatar mu, ga shegen saki a wurinku kamar kun mayar da matan riga. Tunda kun kasheta me kuke nema a wurin mu? Ku fita ku bar mana gida.”Baban Justina ya Kwace Umma daga hannun matarsa Rabeka, ya dubi su Umma ya ce, “Me ke tafe da ku?”  Umma ta nuna Nasreen da Naufal ta ce, “Wadannan ‘ya’yan sune Saudatu ta Haifa. Ina . nufin jikokinku ne.” Rabeka ta kafe su Nasreen da idanu, a lokaci guda Nasreen ta Karasa kusa da ita Www.bankinhausanovels.com.ng hawaye suna zuba, tana jin za ta fi yin alfaharida_ – su, fiye da mahaifinta. Ta rungume Rabeka ta saki kuka. Rabeka ta rungume Nasreen ta hada da Naufal. Gaba daya kuka suke yi. Sai bayan sun zauna ne Umma ta nuna Sultan, sannan ta gaya masu duk yadda aka yi. Sultan yasha albarka, haka sun Karyata maganar da ake fadi akan musulmai, sun tabbata a cikin musulman akwai na Kwarai akwai kuma bata gari. Sun yi alKawarin zuwa suga gidan Nasreen.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page