MAFARI COMPLETE BY UMMU AZAMM

MAFARI CHAPTER 5 BY UMMU AZAMM

MAFARI CHAPTER 5 BY UMMU AZAMM

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin sati biyu da tarewar su yakaka a gidan madam saly ,sun zama ƴan gari a da’irar ta yadda yakaka ta san ɗakunan manyan kilakai da ƙananun karuwan da suke unguwar saboda aiken ta da madam saly take wurin su , a gefe ɗaya kuma ta zama ƴar ɗakin samy baby , wacce bayan dawowar yakaka gidan madam saly ta gama nazarin yarinyar tsaf , ta gane bata san ma mai kalmar bariki take nufi ba kamar yadda da tayi zaton yakakar ƙaramar karuwa ce , sai ta fahimci ashe yakakan neman abun sawa a bakin salati take tare da wajen da zata sanya haƙarƙarin ta , dan haka sai ta jaa ta a jiki ta maida ta mai gyara mata ɗaki tare da yi mata ƴan kananun aike da aiki , ita kuma tana bata ƴan kuɗaɗe bayan jibgin suturun ta da ta fitar ta bata kwance , tun yakakan tana ɗari-ɗari ganin abun da samy baby tayi mata a farkon haɗuwar su , har dai ta zo ta saki jiki da ita , sosai take kyautatawa samy baby da ta riƙa a matsayin uwarɗakin ta , wacce take samun alheri tare da sakewa a wurin ta , domin a lokuta da dama har ƴar hira samy baby take zama su yi da yaks ,

Aikin gidan madam saly kuwa tuƙuru yakaka take yin sa domin gwanintar da take nunawa ya faranta ran madam saly da take ganin ta a matsayin ginshiƙin su cikin duniya a yanzu , bata da wani lokaci nata na kan ta sai na aikin burkutu wanda ba’a sanya ba ma yi take kamar su wanke dawa , juya ruwan dahuwar burkutun da kuma tace shi wanke kayan madam saly da gyara mata ɗaki , tun safe idan ta kama aiki sai dare karfe sha ɗaya take samun hutu ,” wanda hakan ke matuƙar farantawa madam saly rai har take ganin wautar kan ta da farko,  da ta so korar su ashe dai maganar ɗan liti dutse ,

Ga falmata ma sai sam barka domin kuwa har ɗan kumatu tayi ta sake mul-mul , sakamakon cika mata ƙundu da ɗan liti yake da cimar daɗi kullum dare kafin su kwanta bacci , ga kuma labaru masu sanya nishaɗi da yake bata har bacci ya ɗauke ta ,bata zuwa ko’ina daga ɗakin ɗan liti da yake daga wajen filin rawa sai cikin gidan madam saly da take aikin wanke-wanke kofuna tare da farantan aikin burkutu tsawon yini a cikin gidan , bata da wata matsala saboda duk lokacin da yakaka ta ɗan zagaya zata taho bakin fanfon da take zaune din-din a gefen sa ta shafi kan ta koh kuwa fuskar ta , ta kuma tambaye ta bata da wata matsala koh ? Nan zata amsa mata cikin farin ciki da ita bata da wata matsala ,3

Haka zata sake komawa bakin aikin ta tana mai farin cikin sauyin rayuwar da suka samu , musamman farin cikin da take hangowa a fuskar ƙanwar ta wacce ɗan liti ya wadata ta da ƴan kayayyakin gonjo na ƴan matasan yara maza sa’annin ta fes-fes da ita hasken ƴar luwai ɗin fatar ta ruwan zuma yana bayyanuwa,

Ranar da suka kwana huɗu a gidan ɗan liti yayi mata kyautar kayan wanda daga ita har falmata kyautar bata wani faranta musu ba , saboda ƴan rigunan basu da wani girma kayan turawa ne , su kuma sun san kayan nan burguza burguza da falmata ke sanye da su sune rufin asirin su a kasantuwar falmata namiji saboda kayan ya boye ɗan tudun kirjin falmatan wanda suka fara tasowa tare da bunƙasa , 4

Da kƴar yakaka ta shawo kan falmata wacce da farko ta tubure akan shawarar da yakaka ta kawo na falmatan ta dunga sanya riguna biyu bayan ta tamke kirjin ta da ɗankwali ,saboda boye tudun tare da yi mata gargaɗi kada ta yadda ta sauya kaya a gaban ɗanliti duk juyin duniya , ta kan ce

    Kiyi hakuri falmata har mu ɗan tara abun da muka tara anan ɗin zuwa lokacin kuma mun san gari sosai idan ya so sai mu koma wani wurin da babu ƴan iska mu raɓa ki koma saka kayan mu na mata , kamar kowacce mace ina nan ina ware miki kayan ki cikin kayan da nake samu ,”2

STORY CONTINUES BELOW

Ranar da ta fara ɗaure kirjin ta yini tayi tana fama da ciwon kirjin , amma da ta kwana biyu sai ta saba ta daina jin ciwon ,1

Bata taɓa yin wanka sai sun tabbatar da ɗan liti ya bar da’irar wajen sannan zata yi wankan a gurguje yakaka ta raka ta ta sauya kaya tare da sake gyara mata ɗaurin kirjin ta wanda ya taimaka ƙwarai wurin boye halittun kirjin ta , sai dai salon takun tafiyar ta tare da tudun bayan ta ke sa samy baby tana yawan tsokanar ta da

“Kachallah me jikin mata ,”

   tafiyar ka sai kace ta hamshaƙan mata , koh kuwa tace shege kachallah da kai mace ne da anyi manyan kaya a wurin ka ,”2

Idan yagana tana wurin tayi ta sheƙa dariya ,wacce ita ma a yanzu sha’awar rayuwar su yakakan take , domin kuwa har kuɗi da suturu yakaka ta bata daga cikin wanda samy baby ta bata ,”

Haka kwanaki suka yi ta tafiya har suka samu wata guda da ƴan kwanaki a dafdalar wannan gidan , wanda zuwa lokacin yakaka tayi jazur wannan maɗaukakin hasken fatar ta ta ya sake bayyana dal tamkar fitila haka take a waje , ƴar kyakkyawar ƙaramar budurwa mai sanyi tare da yawan fara’a koyaushe cikin murmushi take , ko magana yakaka take haka zaka ga fuskar ta da yalwatattacen murmushi dasashin ta a waje , wanda hakan yake tasiri matuƙa wurin bayyana ƴan ƙananun kyaun ta wanda hasken da take da shi ya fi jaan hankalin mazan da suka fara ƙaraƙaina akan ta fiye da kyan nata ,”2

Zuwa lokacin samy baby ta fara jaan ɗamarar wanke yakaka daga dauɗar datti gami da ƙazantar ƙauye a cewar ta yakaka haja ce me matuƙar tsada , wacce sayan ta sai alhajin da ya rufu ya tada kai , ” sai ya so zama tamkar gasa a tsakanin ta da madam saly wacce ita ma take bada sumfurin tata kulawar ga yakaka domin ta farga gaba kaɗan yakakan zata zame mata hanyar samun arziki ,dan haka ta fara kokarin janye ta daga wurin samy baby da ta lura tana son kawo mata tsaiko domin kuwa ga alama so take ta fanɗarar da yakaka ta sanar da ita daɗin ƴancin kai kamar yadda ita take da nata ƴancin a hannu domin samy baby ba’a ƙarƙashin kowa take ba cikin magajiyoyin gidan , da karfin ta ta shigo bariki da kuma nawin aljihunta tare da gatan ta domin ba kukan yunwa koh na rashin wurin kwana koh kuwa na neman kuɗin zuwa asibiti zubda ciki ne suka kawo ta bariki ba , ƴar cikin ƙwaryar gari ce da gatan ta da kome iyayen ta ma manyan mutane ne sanannu , uwa uba bata da duhun jahilci domin kwalin digiri ke gare ta ,” sha’awar rayuwar barikin take tare da taimakon matar uban ta wacce take sake ingiza ta , uwa uba shaiɗan da yake tsakiyar kan ta yana buga ganga ,2

Gidan kakaf ba wata tsohuwar kilaki da take shakka , sai ma su da idan jarabar su ta busa sigari koh afa ƙwayoyi suka motsa , kuma suka laluba lalitar su suka ji wayam , su je wurin ta neman ƴan kuɗaɗe sanin da suka yi kaf cikin karuwan gidan ba wacce ta kai ta kama kuɗi , da kuma kyauta domin hannun ta a sake yake bata da rowa ,”

Ranar wata litinin da safe yakaka ta wayi gari da wani irin matsanancin ciwon mara wanda tun kwanaki biyu da suka wuce take jin sa kaɗan kaɗan amma ta daure ,3

Har zuwa yanzu da take kan hanyar ta ta zuwa ɗakin samy baby domin ta gyara mata ɗakin ,bayan ta gama kintsa na madam saly kamar yadda ta saba kafin su duƙufa aikin sana’ar su ,”

A dudduƙe da jaan ƙafa ta ƙarasa cikin ɗakin samy wacce take kwance tana sharar bacci daga ita sai ƴar ficiciyar rigar bacci kan gadon duk a hargitse kayayyakin ta tun daga kan rigar mama da ɗan kafai duk a wurge a kan gadon , tayi ɗai-ɗai da kafafu gashin dokin da yake kan ta ya baje akan filon da tayi matashin kai da shi ,” idan da sabo yakaka ta saba tadda ta a haka kullum .

Tana shiga ɗakin ta zube akan shimfiɗar kafet ɗin ta kwanta gami da dunƙulewa wuri guda tana murƙususu , dunƙulewar da tayi ta haɗe guiwar kafafun ta da kirjin ta sai ya sa taji rangwamen kartawa tare da murɗar da marar ta ke mata har ɗan wani bacci ta fara ji yana figarta saboda rashin bacci da tayi daren jiya a sakamakon ciwon cikin ,” bata ankara ba bacci mai karfi ya fisge ta , ta sake jiki sosai tana baccin ta ,

STORY CONTINUES BELOW

Samy baby ce ta farka bayan da taji baccin ya soma gundurar ta , ta daina jin dadin sa , doguwar hamma ta hangame baki ta jaa babu neman tsari daga shaiɗan babu salati , ta gantsare bayan ta ya bada sautin ƙaƙas , tana zira ƙafar ta ƙasa ta sauke akan yakaka wacce baccin ta yake kai mata karo har tsibirin keemala na ƙasar bankok,”

    Da farko ta firgita da ganin mutum kwance a gaban gadon ta sai dai fahimtar wacece a kwance ya sa ta ƙewaye ta gami da nufar kofar banɗakin da take ta cikin ɗakin nata , a ranta tana raya cewa gajiyar aiki da rashin bacci ne suka sa yakaka ta bingire anan ta na bacci , tare da sake aiyana niyyar taimakon yakakan har ta samu karfin tsayuwa da kafafun ta muddin yakakan zata yadda ta bi hanyar da zata ɗora ta ,” yo ina ma zata ƙi ?? Ai duk wanda ruwa ya ci shi idan aka miƙa masa takobi sai ya kama ,”1

   A firgice yakaka ta farka lokacin da samy baby take tashin ta , “cikin inda-inda ta fara bata haƙuri bayan ta gaishe ta,  tare da faɗa mata cikin ta ne yake ciwo amma yanzu ya lafa ,”ta daina jin ciwon sa sosai , sai dai lema-lemar da take ji ta ƙasan ta ya sa ta gaza miƙewa sai faman muskuɗawa take cikin ran ta tana Allah ya sa dai ba fitsarin kwance tayi ba , toh amma ai ita bata fitsarin kwance tun da ƙuruciyar ta bare yanzu da ta zama ƴar budurwa ,

Tunanin ta ya katse lokacin da samy baby tayi mata umarni bayan ta miƙa mata kuɗi akan ta sayo mata soyayyar   indomi da ƙwai tare da shayi haɗin murtuku ya ji sugar sosai ,”1

A sanyaye yakaka ta miƙa hannu biyu ta ƙarba tana mai taraddadin tashi kar samy baby ta ga yadda ta jiƙa mata kafet ,” amma ba yadda ta iya haka ta miƙe tare da nufar bakin kofa

Bin bayan ta da kallo samy baby tayi tana tunanin me ya sanyayar mata da jiki ?ko cikin ke damun ta saboda ta san a wurin aiki da aike yakaka bata da sanya ,” karaf idanun ta suka sauka a bayan yakaka inda shuɗin siket ɗin yadin da take sanya da shi duk ya baci ,”

  Ke yaks dawo nan wai ke me yasa kin cika gidadanci ne ?? Yanzu har yau baki yi wayewar da zaki saka pad a jikin ki idan kina menses ba ? Haba mana yaks meyasa kullum ina kai ki kina dawowa , yanzu ba dan na gani na ƙira ki ba da kenan haka zaki fita ?? Ta ƙarasa zancen tana balla mata harara ,”

Ƙasa da kan ta yakaka tayi tana me satar kallon wurin da ta tashi domin ita duk bata wani gane kalmar pad da menses ba , ga zaton ta faɗa samy baby take yi mata akan fitsarin da ta saddaƙar shi tayi a kwance “ɓacin rana”

, sai dai ga mamakin ta wurin da ta tashin ɗan alamun danshin kaɗan ne kuma bai wani fidda kala ba saboda kafet ɗin ruwan kunkumadi ne ita ma da kƴar ta hango danshin toh akan me samy baby take mata faɗa ?? Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji samy baby ta ce ,”

      Ki buɗe ƙaramin akwati na ki ɗauki sabon pant da pad ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki nan gaba kar ki sake zama babu pad alhalin kin san lokacin yin menses ɗin ki yayi kusa kina jin alamar sa ki tanadi pad idan ma baki da ita ki zo na baki koh kuma ki yi ƙunzugu da tsabatatatcen tsunma kin ji koh ,??

Da sauri yakaka ta gyaɗa kai tana rarraba idanu , domin ita har ga Allah ba wani fahimtar dogon bayanin samy baby tayi ba , koh ta so fahimta ma kalmomin da ta jefo guda uku da turanci sun hana ta gane kan maganar , dan haka kawai sai ta je ta durƙusa a gaban akwatin tayi zugui ,”

Fahimtar da samy baby tayi yakaka fa bata fahimce ta ba ya sa ta tashi ta zo ta buɗe akwatun ta tare da ciro sabon pant fil sai tashin ƙamshi yake  ( ku sani mata tsabtace undies tare da wanke shi da kuma goge shi wani babban sirri ne na sanya nishaɗi a gangar jiki tare da bada kariya na musamman daga kamuwa da cututtukan da suke addabar mata daga ƙasan su a zamanin yanzu ,ki kasance kullum cikin wanke tare da goge panties ɗin ki bayan kin shanya su a rana sun yi a ƙalla awanni shidda a rana ) da kuma ledar pad mai guda takwas ta danƙa mata,” ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki ,”

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri yakaka ta amsa da toh ,

   Kin iya amfani da shi koh ?

   Gƴaɗa kai ta yi sai kuma ta sake girgiza shi ,”

Samy baby wacce ta fara zowa wuya da gidadanci tare da jahilcin yakaka tace ,”

    Buɗe baki zaki yi kiyi magana ba ki dunga gƴaɗa min kai ya kadangaren gobara ba , kin iya amfani da shi koh na gwada miki ??

   A sanyaye ta amsa ban iya ba ,”

Karɓa tayi tare da nuna mata yadda ake amfani da shi ta ɗora mata da ,”ki wanke siket ɗin naki a banɗakin zan miko miki wasu kayan ,”

Ƙiris ya rage yakaka ta kurma ihu lokacin da ta ga yadda jikin ta ya ɓaci da jini ,”tashin hankali na shiga uku na lalace fitsarin jini na fara shikenan nima zan mutu na bi su abba wayyo Allah falmata waye zai kula min da ke ,”  wannan shine tunanin da yakaka take yi lokacin da take wanke jikin ta da kayan ta , tana yi tana sharar hawaye ,”3

Ido jazur ta fito bayan ta shirya kan ta cikin kayan da samy baby ta miƙa mata na wata koriyar atamfa riga da siket , sun zauna mata ɗas kasancewar ita ma samy baby ƴar madaidaiciya ce tamkar ta ,”

Sumi-sumi ta wuce tana share guntun hawaye ta nufi wurin aiken da aka mata ,’ samy baby ta bi bayan ta da kallo tana me jin tausayin yarinyar na zaunawa cikin ranta , ta fahimci yau ne ta fara tsintar kan ta a yanayi na al’ada saboda tashin hankali da damuwar da ta gani tare da yakakar wanda ba kome ya jawo hakan ba illa jahilcin addini da na boko saboda da tana zuwa makaranta kowacce daga cikin ta boko koh ta islamiyya a shekarun ta da take sha shidda da ƴan watanni ya ci ace ta san me wannan jinin yake nufi saboda ana wayar da kai a makarantu ,” nan take ta ji tana son tayi yunƙuri domin ganin yakaka ta ɗan samu ilmi ko kaɗan ne domin ita kan ta harkar da take son ɗora ta akai idan kana da ilmin boko kafi samun kasuwa wurin manyan wayayyun mutane irin wanda take yi wa yakakar yangen su , domin su basu cika harka da jahila ba ,” zamani ya zo da kome zaka yi domin cigaban kan ka sai kana da ilmin zamani ilmi shine gishirin rayuwa ,”1

Tana tafiya tana rarrakaɓewa ta jikin gini tafiyar kan ta ba yadda ta saba take yin ta ba tana tafe tana mammatse kafafu domin ji da take tamkar ƴar audugar da take jikin ta zata faɗo wacce rashin sanya ta a dai-dai ya sa take jin hakan ,” cikin ranta kuwa kalmomin wasiyyar da zata barwa falmata take haɗawa ,”

Yaks baby , yaks baby , ke yaks ji mana wai yane ina miki magana kina wani ƙara wuta tamkar baki ji na , zo mana magana za muyi ,”

Muryar babasho mai sayar da wiski da su matallah , zuwa kan taba sigari da sauran kwayoyin sanya maye a cikin ɗan shagon da yayi da tsoffin kwanukan rufi da katako ,ta katse mata tunani , babasho yayi masifar maƙalewa yakaka , yana bala’in son ta kamar zai yi hauka ,sai dai samy baby ta kasa ta tsare ta hana ya samu damar koh ɗan zantawa da yaks , duk kuwa da cewa kullum sai ya je rumfar saly baby ya sai burkutu dan kawai ya samu ya ga fuskar yaks ,” samy baby ta kan faɗa mata ,” ta wuce ajin babasho fintinkau , me zata yi da wannan sauran tabar ? Da duka-duka idan aka haɗa jarinsa da shagon nasa ba zai fice dubu goma ba ,??  Ai sama tayi wa yaro nisa tsakanin ta da ire-iren su babasho sai dai ta kira su ta aike su ,”amma ita kalar manya ce kalar hamshaƙan da suka ci suka tada kai da naira ,1

,” kar ki kuskura ki kula shi yaks bashi ma da isasshen hankali idan ya sha ta kai masa karo yana iya shaƙe ki ya kar ki ya kar banza atoh kiyi hankali,”

Ga yakaka kuwa ita ba ma babasho ba da take jin mugun-tsoron sa saboda chukurkuɗaɗɗan gashin sa da ya tara akai baya wani kula da shi duguzum-duguzum ya fenta kan kalar jaa shuɗi da kuma yalo , uwa uba faranta hannunsa zaƙo-zaƙo da suke cike taf da annakiyar dauɗa suna tsorata ta har su sanya ta hasashen yadda zai kafa mata farce a wuya idan ya shaƙo ta kamar yadda samy baby take faɗa mata , ita gaba ɗaya maza ma ƙarƙashin ranta tsoron su take , babu wani ɗa namiji da ta taɓa jin sa cikin ranta idan aka ɗauke dakta hamza wanda shi ma ta ɗauki tunanin sa da yake faɗo mata jifa-jifa a zuwan tana tuna sa ne domin taimakon da yayi a gare su ita da ƙanwar ta , bayan shi babu wani ɗa namiji da yakaka take ɗaga kai ta dube shi iyakar ta da su harkar cinikayyar su ta burkutu su , su zo saya ta je ta kawo musu ta karbi kuɗin ,” bata taɓa buɗe baki tayi tsiwa koh rashin kunya ga kowa ba duk kuwa da yadda suke kai mata wawura tare da maganganun banza da ita bata ma kai ga fahimtar wasu kalmomin su na batsa ba ,”ita dai ba’a raba fuskar ta da tsadadden murmushin ta , dan haka yanzu ma da babasho yake kwala mata kira koh kallo bai isheta ba haka ta cigaba da tafiyar ta ,’ shi kuwa ya bi bayan ta da kallo yana lashe leɓe tare da lanƙwasa ƴan yatsun sa cikin ransa yana fatan Allah ya kai damo ga harawa koh bai ci ba yayi birgima,”,1

STORY CONTINUES BELOW

Karo taji tayi da mutum wanda zurfin da tayi a tunanin ta ya sa bata ga tahowar sa ba ,” da sauri tayi baya ,tare da durƙusawa ta ɗauko masa makullin motar sa da ya faɗi a hannun sa ta sanya bakin gyalen ta ta goge ƙasan jikin ɗan makullin bakin ta ɗauke da kalmar ban hakuri ta miƙa masa mukullin ba tare da ta ɗago kan ta ba ,

     Miƙa wankakken hannunsa mai ɗauke da wankakkun fararen farata ƙal yayi ya karbi makullin agogon hannun sa na ta ɗaukar ido ,”hannun ta bi da kallo wanda kyaun sa da gogewar sa a tsafta irin wanda bata taɓa gani ba ya ɗauke hankalin ta , muryar sa ce ta dawo da ita daga shagalal da tayi cikin hausar sa ta bamarɗe yace ,”

  “, Ai ni ke da laifin ina gaugawa ban lura da ke ba yi mini afouwa ,”2

Da hanzari ta ɗago kan ta jin muryar sa da ta yi kamar ta san ta , tana ɗagowa yana gifta ta sai tashin mabuwayin ƙamshin sa da ta shaƙa wanda ya sa ta jin tsaftar sa ta burge ta har ta waiwaya tana bin takun sa da kallo ,”

Har ta je ta amso aiken da aka mata tana jin ƙamshin turaren sa cike taf da hancin ta ,” bayan samy baby ta ci indomie da soyayyen ƙwai ta cika cikin ta har ta barwa yakaka sauran ta cinye tas tare da wanke kwanon , ta tashi da niyyar fara gyaran ɗakin , samy baby ta dakatar da ita tare da cewa ta bata hankalin ta ,” nan tayi mata bayanin jinin haila da ta fara da yadda ake wankan sa , ta kuma jaa kunnen ta akan ta kula kar ta yadda wani ɗa namiji ya ɗirka mata ciki kar ma ta kula kowa a yanzu idan lokacin fara harkar ta yayi ita da kan ta zata kaita a bata maganin hana ɗaukar ciki ta yadda zata ji daɗin cin kasuwar ta ba tare da wata fargabar yin ciki ba , nan dai suka ɗauki lokaci samy baby tana mata huɗuba wanda mafi yawan su ba na kirki bane , idan aka cire wankan hailar da ta koya mata a taƙaice babu wani abun kirki cikin sauran shawarwarin da ta bata ,’

   Ki lura da kyau da lissafin kwanakin menses ɗin ki domin ta haka ne idan kin fara harka zaki gane lokacin da kike danger ɗin ki dan ki kiyaye harka a waɗannan kwanakin duk da dak zamu je a miki ƴan dabaru amma kau da bara sai ana haɗawa da zamiya ,”kin ga yau ɗaya ga wata kika fara duk inda wata ya kai shidda  takwas zuwa goma zaki iya gamawa toh kwanaki bakwai da zasu biyo bayan kwana uku na kammala jinin al’adar ki sune ranaku mafi hatsari gare ki idan kin fara harka domin tabbas kina iya samun ciki idan kika sake kika yi koh da wasa da lawurjen namiji ne ehee ,sai ki kiyaye kin ji koh ?2

Ba tare da yakaka ta fahimci mafi akasarin bayanan samy baby ba ta amsa da “toh” hankalin ta ya fi karkata ga son sanin wacce harka ce zata ɗora ta akai wacce har akwaj hatsarin samun ciki ?? Ita fa tana tsoron zancen ciki kowacce irin harka ce zata iya hakura da ita idan har zata iya yin ciki , toh amma tayaya ma ake samun cikin ?????? ( ta miƙa tambayar ga masu karatu 😂)4

Cikin sanyin jiki ta koma bakin aikin ta inda duk take a takure domin gani take kamar kowa ya san tana fitsarin jini bini-bini ta leƙa ta kalli bayan siket ɗin ta ,kou kuwa ta shiga bayi tayi tsarki , duk a matse take jin kan ta , sai dai tata damuwar ta kau koh kuwa ace ganin damuwa kwance ɓaro-ɓaro akan fuskar falmata ya sa ta daina jin ta ta sai wani sabon tashin hankali tare da damuwar da ta fi ta farko da taji ya mamaye ta , sam bata ƙaunar ganin falmata cikin damuwa

  Falmata nah ! faɗa min menene ?? wani ne ya zage ki ? Koh baki da lafiya ne , yunwa kike ji ?? Koh kina son wani abu ne ?? Koh jiya ɗan liti ya miki wani abun da ya ɓata miki rai ne  ? Gaya min dan Allah menene

    Ɗan guntun murmushin da daga ganin sa na ƙaƙale ne shi falmata ta ɗora a fuskar ta ,”

    Yakaka ni babu wanda ya min kome kuma lafiyata ƙalau , bana  jin yunwa ,”

      Toh meye ne koh kin tuno da su mama ne ??

   Da sauri falmata ta gƴaɗa kai tana me rushewa da kukan da tuntuni yake cin ta , sakamakon abun da ya faru da ita a wurin wani mutum wanda ɗan liti ya ɗauke ta jiya ya kai ta a matsayin shine ubanɗakin sa wanda yake bashi kayan daɗin da yake kawo mata tana cika cikin ta da shi ,”

Ita dai bata san ina ɗan litin ya kai ta ba domin a mota suka tafi ,

   Duk da cewa ba gani take ba amma ta fahimci gidan da ɗan liti ya kai ta gidan me hali ne , domin maɗaukakin sanyin da ta ji a parlour da suka tadda mutumin har zuwa kan lallausar abun da aka zaunar da ita akai kujera zata kira abun koh gado ?? Ita dai bata taɓa zama a makamancin abu mai taushin sa ba ga wani fitinannen ƙamshi da ya cika wurin , bata ji ta fara tsorata ba sai da ɗan liti ya ɗibo wani abu mai matsanancin sanyi ya cusa mata a baki da ya umarce ta da ta buɗe bakin ta zai bata wani abu wai shi “ice cream” anan ta ji ta tsorata domin kuwa dawo da abun tayi ta tofar da shi saboda bata taɓa shan abu mai tsananin sanyin irin sa ba ,”

   Mutumin da suka tara a falon ya buɗe ƙatuwar muryar sa marar daɗin sauti kamar fasasshiyar  gangar  ya dunga tuntsira dariya ɗan liti yana taya sa harda shewa ,”3

    Watau kachallah bai taɓa shan ice cream ba ?? Ai kuwa daɗi ya bar ka , toh liti bashi gasasshiyar kaza ya ci nasan dai koh daga kan dutse ya sauko ya san nama ,

Wata ƙatuwar cinya ɗan liti ya fisgo ya damƙawa falmata a hannun ta bayan ya miƙa mata kwalin lemun ,”five alive” a ɗaya hannun ,

    Maza ɗan kachallari ci kaza ka sha lemu yaro ai ka zo gidan arziki duk wasu kayan daɗi da nake kai maka kana ci kana lashe baki “ya tsohon kare nan ne tushen sa kaɗan ne daga cikin ire-iren kayan maƙulashen da suke jibge a gidan nan yaro saki jiki ka ci arziki ka bar shi a inda ka gan shi ,”1

    Cikin sanyin jiki falmata ta kai cinyar kazar bakin ta ta gutsuri kaɗan tana taunawa ,” zaƙin kayayyakin ɗanɗano irin na alfarma tare da zaƙin naman kazar suka haɗu suka sa kunnen falmata motsi har bata san lokacin da ta cinye wacce ɗan liti ya bata ba ,

    tana tanɗe baki ,  ɗan liti wanda suke kus-kus da wannan ɗan tsurut ɗin mutumin shi ya lura da ita ya sake fisgo ɗaya cinyar ya ɗangwala mata a hannu ,”

      ungo maza cinye har ƙashin ka tauna ka haɗiye , yau ta shiga ranakun tarihi a wurin ka ɗan kachallari ,”1

Miƙewa ɗan liti yayi bayan sun gama kitsa abun da suka kitsa ,”

    Ɗan kachallari ni zan ɗan je na dawo nan kusa ka jira…

   Koh kafin ya ƙarasa abun da yake nufin cewa falmata ta miƙe zuruf ta dangwarar da sauran naman hannun ta ”,

      Ah ah mu tafi tare nima zan bika ,”

Haɗa ido ɗan liti da wannan mutumin suka yi , mutumin ya yiwa ɗan liti alama da ido akan ya tafi kawai zasu yi waya ,”

   Saɗaf-saɗaf ɗan liti ya fita ya jaa musu kofar wanda ƙarar rufe kofar ya sa falmata wacce take tsaye tana jiran amsar ɗan liti ta farga da barin ɗan liti wajen ,”

     Kuka ta sa tare da fara taku tana nufar hanyar da ta ji motsin rufowar kofar da ɗan liti yayi lokaci ɗaya tana jera kiran sunan ɗan litin ,”

  Dariya ta ji mutumin ya kwashe da ita  kafin ta ji ya fara tahowa inda take yana cewa haba ɗan kyakkyawan yaro kachalla menene abun kuka yi shiru yanzu ɗan liti zai dawo aiken sa nayi , kafin ya dawo zo muyi wasa ,”kafin ta ankara ta ji ya sure ta sama yana cewa ,” A ɗaga sama anyi wa wada kwace 😂 ,”Tuƙuru ɗan tsamurmurin mutumin nan yake son danne falmata , sai dai lamarin ya faskara domin daga ya samu nasarar cillata kan gadon kafin yayi wani yunƙuri ta zabura ta mike , babu abun da ya fi fusata shi da har ya kai shi ga danna mata cizo a kafaɗa irin ihun da ta buɗe maƙogoro tana yi tun karfin ta , wanda hakan ba karamin tada masa da hankali yayi ba sanin da yayi matar sa tana nan a sashin ta da yake maƙotan nasa , zata iya jin ihun falmata kuma duk irin manyan alfashan da yake aikatawa matar tasa bata kai ga sanin wannan mafi muni daga cikin su ba watau ,”luwaɗi,” baya kuma son ta sani domin yana matuƙar son ta bai haɗa ta da kowacce mace ba cikin rayuwar sa ita take biya masa bukatar sa uwa uba ita ce silar arzikin sa tare da bazar ta yake taka rawa ,” neman yara maza da basu kai ga balaga ba da yake yi a duk daren lahadi wayewar litinin wani sirri ne cikin rayuwar sa ,”+

Dan haka a wannan karon cikin hakin da gajiyar kokawar da yake yi ya haifar masa , gami da tsabar mugunta ya ɗaga falmata a karo na takwas ya maka ta da kan katifar gami da sanya hannun sa ya danne mata baki , ya fara ƙokarin zare mata bujen ta da ɗaya hannun ,”

Bai ankara ba yaji ta gantsara masa wani fitinannen cizo a ɗan yatsan sa babba , wanda hakan ya sa shi sakin wani ihun azaba jin tana yunkurin gutsire mishi ɗan yatsa ,”

Da ɗaya hannun sa yayi amfani wajen kai mata maruka da duka ta ko’ina amma falmata ko gizau taƙi sakin ɗan yatsan da zuwa yanzu take jin gishiri-gishiri a bakin ta da ta tabbatar jinin sa ne ,” ƙara nutsa haƙoran ta tayi da ya sanya shi ba shiri ya daina dukan ta ya koma roko cikin kuka akan ta sakar masa yatsa ,”

Bata sakar masa da yatsan ba sai da ta tabbatar ta jikkata shi ta inda ko ta sake shi jinyar raunin da tayi masa zai fara sannan ta sakar masa yatsan ta miƙe da sauri tana tofar da jinin da ya zuba mata cikin baki,”

Tana sakin sa ya tashi da gudu ya buɗe kofar banɗaki da yake cikin ɗakin ,’

Tana jin tashin muryar sa tare da ihu lokacin da ya buɗe fanfo yana wanke yatsan ,”

Bin bango ta fara yi da lalube tana neman hanyar fita duk kayan jikin ta sun yamutse , tsumman da take ɗaure kirjin ta da shi ya zazzago wanda hakan ya bawa kirjin ta damar tasowa ,

Sai dai duk yadda ta kai ga lalubawa ta gaza gano kofar bare ta buɗe ta sai kewayawa take yi cikin hawayen tausayin kai da take yi ,” makanta mutuwar tsaye ,”

Ido jawur ya fito ya tsaya ta bayan ta yana kallon ta cikin ran sa yana aiyana irin azabar da zai ganawa yaron nan a daren yau ,”

Cigaba yayi da naɗe hannun sa da Bandage yana kallon yadda take ta laluben bango , chak ya tsaya da abun da yake lokacin da idanun sa suka fara bayyana masa ainahin surar ta ta ƴa mace ,’

Sosai ya ƙura mata ido yana kare mata kallo daga sama har ƙasa domin tabbatarwa ,”

Wata chafka yayi mata tare da haɗa ta da bango yana mai ɗaura hannayen sa akan kirjin ta ,

Zabura tayi ta angaje shi baya,

Dan ubanki daman ke mace ce ??

Shine aka kawo min ke a matsayin namiji ??

Kika bani wahala irin wannan har da yi min rauni ? ashe ma ungulu da kan zabo ce ? Me zanyi da macen titi ? Kuma ma ƙwaila ?

Dan uban ki yau zaki yabawa aya zaƙin ta , sai na wassafa ki ta yadda gaba baza ki sake yadda ayi haɗin baki da ke ba , ƴar yarinya da ke amma har kin san ta kan bariki , kin san yadda ake maguɗi ,

Bugun kofar falon da aka Fara yi da karfi shi ya sa shi dakatawa da maganar da yake yi ,tare da yin kasaƙe domin sauraro , ai kuwa ya tsinkayo muryar matar sa tana danna masa kira tare da cigaba da bugun kofar , wani irin zillo yayi cikin taraddadin riskar falmata da zata yi cikin ɗakin sa ,’

STORY CONTINUES BELOW

Diri-diri yayi yana neman abun yi ba tare da ya lura da falmata wacce ta fara kokarin kintsa kanta ta cikin shigar ta na maza ba,

Bugun yana tsananta tare da ƙarin fargabar sa juyowa yayi da nufin chafkar falmata ya tura ta cikin wardrobe Ya kulle domin ya san muddin matar sa tayi ido hudu da budurwa a ɗaƙin sa da daren nan kome zai faɗa mata baza ta yadda ba , bai kuma san wanne irin mataki zata ɗauka akan sa ba , da ya san ba mai sauki bane domin ya san kalar kishin ta na masifa dan haka ya gama yanke shawarar ko ta halin ƙaƙa sai ya rufawa kan sa asiri ko da kuwa zai kashe falmata ne,

Sai dai ga mamakin sa shirye ya ga falmatan tsaf yaro namiji kamar dai yadda ɗan liti ya kawo masa ita , wanda ya tabbatar a kallo ɗaya baza’a taba gane falmata ƴar budurwa bace ,

Wani ɗan sanyin daɗi ya ji cikin ransa ,

Dan haka ya matso kusa da falmatan

Dan uban ki ga mata ta ta zo tana buga min kofa , idan kika yadda kika yi wani abun da ya sa ta gane ke mace ce sai na kashe ki kin ji ko baki ji ba ??

Cikin sauri falmata take gyaɗa kan ta tana gwalalo ido jin kalmar kisa daga bakin sa wanda azabar da ya gana mata a cikin mintuna da suke ƙasa da talatin ya sa ta tabbatar tsaf zai iya sheƙe ta har lahira ,”

Ungo nan ya watso mata kayan sa masu datti da ya ciro su daga loƙo ,

ki riƙe su a matsayin garƙuwar ki da zata fidda ki gidan nan lafiya

Da gudu ya fita ya buɗewa matar sa da take tsaye daga bakin kofa tana ƙuta , tare da mamakin meye yake yi haka a ciki da bai jin bugun kofa kuma ta kira wayar sa bai ɗauka ba , ita ba kome ya kawo ta ba illah ihun da ta tsinkayo daga sashin nasa ,” ta ɗaga hannu da nufin sake buga kofar ,karaf ya buɗo kofar

Yanayin fuskar sa kawai ta duba ta san ba lafiya ba , lafiya kuwa baban sadiq?

ta tambaye shi ,

Subahananlahi ta furta hakan tana mai riko hannun sa da ta gani naɗe da bandage kafin ta ja shi ciki tana tambayar sa cikin tashin hankali akan meye ya same shi , ‘ shi kuwa sai faman yamutsa fuska yake cikin alamun nuna jin zafin ciwon ,”

Kwantar da hankalin ki my dear ɗan ciwo na ji da wuƙa ,ya furta hakan yana me satar kallon kofar ɗakin sa cikin ransa yana zagin falmata akan me ta tsaya yi masa kuma cikin ɗaki ?

Fitowar falmata rungume da kayan da ta naɗe su da kƴar cikin daya daga cikin rigunan nasa , shi ya maida hankalin matar sa kan falmata ,’

Bin falmatar tayi da kallo lokacin da ta ga ta doshi jikin bango gadan-gadan tana shirin cin karo ,”

Kai yaro kai kuma daga ina da daren nan ?

Chak falmata ta tsaya lokacin da ta ji kafar ta ta zunguri garu ,

Juyawa tayi ga mijin ta wanda yayi kicin-kicin da fuska ,

Baban sadiq kana ganin yaron da nake gani koh dai gamo nayi ?

Cikin bagararwa yace wane irin gamo kuma bilkisu ? Yaro ne ya shigo karɓan kayan wanki ,?1

Kayan wanki kuma ? A daren nan ?

Kuma naga kai kake kai kayan ka laundry da kan ka yaushe kuma ka koma bawa masu wanki , ? Tukun ma yaron baya gani ne naga yana bulunbutuwa ?1

Bagarar da sauran tambayoyin ta yayi ya bata amsar tambayar ta ta karshe almajiri ne kuma makaho ,” nuna masa hanyar fita daga falon , ya saki ƴar wata ƙarar da ke bayyana azabar da hannun sa yake yi ,da hakan ya tilasta bilkisu ta bar sauran tambayoyin ta tare da watsar da wasi-wasin da ya fara zuwar mata na ganin yaro a turakar maigidan nata har uwar ɗaki da dare ,’

Ta kama hannun falmata wacce tun da a garin neman hanya ta bige ɗan yatsan ta da kafar kujera ta raƙube ta tsaya daga wajen tana sauraran duk maganganun su ,cikin ranta ta gudurta muddin ta ga matar nan zata zalunce ta , zata fyaɗe mata biri har wutsiya ta faɗa mata gaskiyar zancen , idan ya so shi mijin nata ya kashe ta a gaban matar ta sa kamar yadda ya ce ,”

Ga hanya nan ka miƙe nan kar kayi kwana ,’

Ɗan turus tayi cikin kokonton

Kai yaro !

Chak falmata ta tsaya wacce har ta fara taku cikin sauri tare da hamdalar kubutar da ita da Allah yayi daga hannun wannan azzalumin mutumin da bata kai ga sanin sunan sa ba ,”

STORY CONTINUES BELOW

Waye ya kawo ka ? Ina nufin tare da wa kuka shigo gidan ?

Unn’umm’un tare tare da alhajin muka shigo shi ya kawo ni ,” cikin inda-inda kalaman suke fitowa daga bakin falmata ,’

Shikenan tafi,”

Babu ko waiwaye falmata ta miƙa hanya , bata yi wata tafiya mai nisa ba ta fara tsinkayo tashin muryar ɗan liti da yake hira da wani , yana ta faman sheƙa dariya cikin salon maganar sa ,” wata irin tsanar sa ta taso ta maƙure ta ,” macuci azzalumi ta ambata a ranta ,’

Hangon ta da ɗan liti yayi ya sa shi miƙewa daga inda yake zaune akan bencin mai gadi suna hirar su ta duniya domin zamu ce ta tadda muje mu ,( yaƙin ruwa ya ci sakaina ,) shi ma maigadin tsohon ɗan iska ne wanda duniya ta gama kare masa ba tare da ya farga ba , duk wasu tsiyatakun da ubangidan sa yake yi ya sani , ya kuma san ɗan liti kawalin ubangidan sa ne , dan kuwa duk lokacin da ɗan litin ya shiga da yaron da ya kawo , nan yake zama a wurin sa yayi jiran fitowar yaron ,’

A ah kaga ɗan kachallarin Alhaji har ka fito ? Iyeeh har da kaya haka alhajin ya baka ,?? Inji dai baka yi masa gardama ba ?? Ka saki jiki ka ci tsokokin nama ka kora da ruwan tatattun ƴaƴan itatuwa yadda ya kamata ? Toh albishirin ka ɗan kachallari ? Kafin ka ce goro kawo kayan na riƙe maka ya furta hakan yana mai karɓe kayan hannun falmata ,”

Sati mai zuwa iwar haka kana nan na sake kawo ka ka dangwali arziki kayi buroshi da zuƙa-zuƙan cinyoyin kaza ɗan kachallari fiye da yadda kayi a yau,’

Ni bazan sake zuwa ba , bazan sake bin ka ba , ka maida ni gida ,’ falmata ta furta hakan tana me rushewa da kuka

Wata ƴar iskar dariya ɗan liti ya kwashe da ita da ya sa falmata ƙaro sautin kukan ta wanda yake tabbatarwa da ɗan liti aikin gama ya gama a tunanin sa ,’

Tsawon dare falmata bata yi wani baccin kirki ba daga ta fara baccin zata ji ƙarar marukan da mutumin nan ya dunga yi mata , cikin ranta tana sake tsorata da mutane gaba ɗaya , abun da ta fahimta a ɗan ƙarancin shekarun ta shine mutane basu da kirki mafi yawan su azzalumai ne tana mace bata huta ba ta zama namiji ma bata tsira ba , sai dai cikin ran ta tayi niyyar boyewa yakaka abun da ya faru da ita domin ta huttashe ta shiga damuwa a dalilin ta , tasan daga lokacin da yakaka ta ji abun da ya faru baza ta sake samun nutsuwa ba har sai ta samo hanyar da take ganin ta bada kariya a gare ta , kwatankwacin wacce ta baro su daga sansanin su , a gare ta samun kwanciyar hankali tare da walwalar da take tsinkayowa daga muryar yakaka yafi mata kome , baza ta so tayi wani abu da zai Wargaza mata farinciki ba , hakan ya sa da a halin yanzun yakaka ta takura ta faɗa mata abun da ya sa ta kuka , taƙi bayyana mata haƙiƙanin gaskiya ta danganta kukan ta da tuno da mahaifan su da tayi ,

Kwanaki biyun da suka biyo baya sun yi su ne cikin takura , ita yakaka al’adar da take yi ita ta hana ta sakewa a matsayin ta na sabon shiga , dan haka duk a takure take jin kan ta gani take kamar kowa ya san halin da take ciki duk kuwa da cewa dai-dai gwargawdo samy baby ta wayar mata da kai tare da saya mata sabbin pad da pants,kuma zuwa yau da take kwanaki biyar da fara yi , ya fara jaa baya, ita kuwa falmata fargabar da take danƙare cikin ran ta akan irin matakin da ɗan liti zai ɗauka akan ta ne a lokacin da mutumin da ya kai ta wajen sa ya tabbatar masa da cewa ita mace ce ,

Sai dai a yau da ake kwana biyar da faruwar lamarin ta ɗan samu nutsuwar zuciya ganin har yau bata ji ko ganin wani sauyin da yake nuna mutumin nan ya gayawa ɗan liti wani zance ba, dan haka ta sake suka yi hirar su ita da yakaka da yagana waɗanda suke ɗan zagayowa su taya ta wanke-wanke , walwalar ta ta sauya zuwa taraddadi ne lokacin da ta ji muryar ɗan liti yana dannanawa madam saly kira ,

ahayye nanayee madam saly fito, fito , fito ki ji sabon bayani abun mamaki ciyawa da cin doki ,wai kamar mu a garin nan za’a nunawa barikanci , za’a yi mana ungulu da kan zabo ,? Chafɗijam , inji masu iya magana suka ce bar ganin ƙanƙantar allura karfe ce , yekuwa jama’a ku hallaro ku ji abun al’ajabi ango ya kwana da ƙunzugu ,5

STORY CONTINUES BELOW

Da ɗai-ɗaya hankali mutanen wurin ya fara dawowa kan sa saboda tsabar ƙwarmaton sa hatta masu cinikin madam saly da suke cikin rumfa sai da suka ji yo shi wasu ma har suka tsallako suka zo ganin dal ,”

Liti yaya ne ? Yaya ne ?ya da irin wannan kiran haka ? Ta samu ne ? Ko kuwa ta guntso ne zata fesar , ? Kunne na tarwai ina jin ka bamu mu sha ,” cewar madam saly wacce take ƙarasowa wurin tare da wasu daga cikin ƴan aikin gidan ,”1

To wallahi yaran nan yaks da ƙawar ta tare da munafiki koh munafukar ƙanwar ta zan ce ? Yo abun ne ya sauya , ninke mu baibai suka yi suka buga mana stamp ɗin sakarkaru na gaya miki, ”

Wani banzan kallo madam saly take sakar masa kafin ta jaa ɗan guntun tsaki ,

Ban gane ba ? Daman akan waɗannan yaran kake kwalla wa jama’a kira har da yekuwa ? , kai dai Allah wadaran ka dan liti3

Tsiya ta da ke wutar ciki madam saly , toh na rantse da Allah kachalla dai mace ce , macen ma luntsumemiya kuma nunanniya , shine dan iskanci da kuturun munafurci yaran nan suka ce wani wai namiji ne , aradun Allah ma ni ban yadda da su ba idan ba turo su ɗaukar rohoto aka yi ba , atoh ki dai bincika ki kuma san abun da kike ciki kar sai kin baje kafafu ki ji anyi ramm da ke anyi sama da duwaiwan ki atoh , zamanin nan na yanzu ko inuwar ka baka sakankance da ita ba dan zata iya harɗewa ta shige cikin na makiyin ka idan kuka jeru, ji min duniya mai abun mamaki wai ƴan waɗannan ƙuya-ƙuyan yaran sun iya dabo-dabo da rufa-rufa , toh dan uban uban ku yau asirin ku ya tonu ,”3

Duk maganganun da yake suna sauka a kunnuwan falmata wacce take duƙe a bakin fanfo da kuma yakaka wacce ta kawo kai domin shigowa ta karbi burkutu ta kaiwa abokan ciniki , dukkanin su tsam suka yi da jin kalaman ɗan liti , wannan fa shi ake kira an yanka ta tashi , take falmata ta fara yin hawaye , yayin da yakaka ta ɗaure ta cije tare da jaan ƙwanjin kare falmata ,”sai dai ayi wacce za’a yi wai bera ya zubda garin ƙyanwa ,”

Madam saly ce ta juya ga falmata bayan da ta gama jin zantukan ɗan liti ,

Kai kachalla zo nan

Sum-sum falmata ta taso tana laluben hanya ta sashin da taji tashin muryar madam saly

Haiyaratataa ni idan ba makantar taki ma ban yadda da ita ba , ni daman kullum ina shakkar waɗannan idanun naki da suke wural uwa na mujiya da tsakiyar dare ace wai bakya gani ??? Cewar ɗan liti wanda yake jijjiga ya dogare daga gefe ,”1

Kai kachallah meye gaskiyar maganar da ɗan liti yake faɗa akan ka ? Tambayar da madam saly ta jefawa falmata wacce take durƙushe a gaban ta kenan , “

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE