JIRWAYE COMPLETE

JIRWAYE CHAPTER 2

 JIRWAYE CHAPTER 2

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tuqi yike suna ta hira, Fatima tana ta basa labarin childhood days dinta, shikuma yana ta sauraron ta yana dariya.+

“Habibi”. Ta kira sa kamar yadda ta saba.

“Yes dear”.

“Dan Allah mu shiga gun Hajjo kaji”. Juyowa yayi ya Kalle ta.

“Wai ke ya kike son gara ni ne haka”. Ya fadi ransa a dan bace.

“Toh naga muna kusa da layin su ne”. Ta fadi “Amma ba komi, mu wuce kawai” ta qara fadi. Shikuma yayi shuru bai ce mata komi ba. Can kawai yana tana fadi cikin wata iron murya da ta sosa mai ran sa

“Uwata ma yanzu hana ni ganin ta ake, in ban ganta ba yau waya san randa zan ganta”. Har da share dan kwallan ta duk sai yaji ba dadi, kamar bai mata adalci ba. Juyo kan motar yayi kawai ya shiga hanyar da zata sa da su da layin gidan iyayen Fatima.

Tafe suke ba me cewa kowa komi, sai radio da ke kunne. Suna isa wani makeken gida ya yi honking, ba tare da bata lokaci ba me gadi ya buda musu gate suka shiga. Da yayi parking sai ya fito ya buda mata qofa suka fara tafia hannayen ta a cikin nasa kamar yadda suka saba. Shiga suka yi cikin gida Hajjo ta tare su da fara’a. Suna zama masu aiki suka shigo musu da refreshments.

“Ai ba ma dadewa zamuyi ba, mun zo wuce wa ne nace mu shigo”. Fatima ta fadi wa Hajjo tana mata murmushi.

“Auu toh, Alhajin na nan ai, ku shiga ku gaisa”. Hajjo ta fadi cikin fara’a. Hajjo kamar yadda yaran ta ke kiranta ita ce mahaifiyar Fatima. Hajia Hajara ta kasance mace me kirki da haquri matuka, bata da hayaniya gashi tana daukar kowa tamkar nata. Bata kyamatar talakawa kamar yadda masu kudi ke yi, ita kowa nata ne. Fatima ita ce diyar ta ta uku, akwai maza biyu gabanta; ya Fu’ad wanda soja ne, sai kuma ya Abdul, shikuma engineer ne. A bayan ta kuma akwai maza biyu Muhammad da Mahmoud. Kasancewar ta the only girl ya sa aka fi ji da ita, fiye ma da yadda ake ji sa Auta Mahmoud.

A tsaitsaye suka gaisa da Alhaji sannan suka musu sallama suka wuce shopping mall domin siyawa Aryaman birthday present. Aryaman nephew din Fatima ne, yaron wan ta ya Fu’ad. Suna shiga mota ta Kalle sa ta saki wata murmushi wadda ya fito da dimples dinta.

“Thanks habibi, you always make my wishes your command”.

“The things we do for love”. Ya fada shima yana mata murmushi “yanzu dai kinga Hajjo dinki koh, hankalin ki ya kwanta”. Daga kai ta mai alaman eh hankalin ta ya kwanta.

Shopping mall din gidan bene ne me dauke da about 10 storeys. A nan ma suka shiga arguement.

“Gaskia elevator zamu shiga”.

“Haba dan Allah, kai wai baka ji abunda doctor yace mun bane rannan. Na dinga exercise sabo da cikin ya girma”.

“Toh ba muna strolling ba tare, gaskia Fatima I can’t take the stairs”.

“Shikenan, je ka shiga lift, ni zan taka stairs, mu hadu a 7th floor”. Ta fadi cikin bacin rai.

‘Duk na qosa ta haihu na huta da rigima’ ya fadi a zuciyar sa amma a fili sai ya jawo ta yana rarrashin ta.

“Aah haba habibty. Allah huci zuciyar ki. Muje mu yu exercise”. Ya hakura ya bi ta suka hau stairs ba wai dun ran sa ya so ba. A haka dai ya ta bin ta. Tun suna ma Aryaman shopping har Fatima ta koma side din cosmetics and body care products ta fara nata siye siyan shikuma yana gefen ta yana taya ta zabe.

“Ji mun wannan turaren, do you like the scent?” Ta tambaye sa.

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE