KASHE FITILA CHAPTER 8 BY BATUUL MAMMAN

KASHE FITILA CHAPTER 8 BY BATUUL MAMMAN

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kamar kada su tafi gida haka Awaisu ya rinka ji. Hanyar fita gari ya dauka Rumana ta dago kai a firgice.+

“Uncle ina zamu?”

“Kin fiye tsoro Princess. Abu zan saya miki”

Daga nan bai kuma magana ba har suka tsaya daidai wurin wani mai nama da yayi suna sosai a wurin. Murmushi tayi tana tuna lokutan baya kafin zuwansu Abuja. Babu zuwan da zaiyi garin bai tafi da ita da sauran ‘yan uwanta siyan gasasshiyar kaza a wurin ba. Har kurar Awaisu babanta yake kiranta sai gashi yau sun kuma zuwa amma tana matsayin matar Awaisu. Tunani ne barkatai suke ta zuwar mata akan wannan sabuwar rayuwa sai da yayi kusan rabin awa ya dawo dauke da ledoji. A baya a ajiye sauran sannan ya shiga mazauninsa ya ajiye mata daya akan cinyarta.

Zabura tayi tana kokarin mikewa tsaye ta ma manta a mota suke. Mamakin tashin nata yayi yace ta zauna. Cinyarta ya gani tana shafawa harda ‘yar kwalla

“Uncle ka kona min cinya” ta fada a shagwabe

“Subhanallah” yace tare da kai hannunsa inda yaga tana murzawa. Kayan jikinta material ne mai santsi shiyasa taji shiga zafin har kanta. Hannun nata ya dauke kawai sai ta ga ya duka daidai cinyar yana hurawa.

Tsigar jikinta taji ta tashi ta fara jan kafar yayi saurin rikewa.

“Kiyi hakuri don Allah na manta da zafi na baki don kici yanzu”

Ita dai so take ya kyaleta kawai tace “ya dena zafin ma”

AC taga ya kara sannan ya dan hade fuska babu alamun wasa “bari na janye skirt din kisha iska sosai kafin mu isa gida”1

“Iyyeeee, a janye me?” Ta fada tana zaro idanu a firgice.

Ya kama skirt din “nace ki bari yasha iska kuma na ga yadda wurin yayi. Kada yaja ruwa ko tabo”

‘Yar dariya ta soma yi wadda bata boye tsoron da yake bayyane a fuskarta ba

“Lahhhh ashe ka zata gaske ne naji zafi…to wasa nake yi kawai.”

Dariya yayi wai kamar shi zata yiwa wayo. Tsoron da ya gani tattare da ita yasa ya kyaleta. So yake ta soshi ba taji tsoransa ba.  Motar ya tayar suka kama hanyar gida yana satar kallonta tana sosa wurin. Da ta ga ya juyo sai ta dauke hannunta da sauri. Wani chemist ya tsaya ya sayi magani suka wuce.

Cikin kannenta ya kira wani mai suna Jamal ya bashi ledoji biyar manya cike da naman kajin nan yace ya kai ciki a raba musu. Shi kuma ya dauko leda uku a hannu ya zagayo bangarenta ya dauki nata.

“Muje na kaiwa su Maamu nasu sai na shafa miki magani”

“A ina? Wanne?? Maganin meye???”

“Bana son musu ki wuce muje kawai” ya fada tare da yin gaba.

Jikinta a sanyaye tabi bayansa. Ta yaya zai shafa mata magani a cinya. Shi ko kunyarta ma baya ji. Ita ce fa Rumana!

Dakin Maamu suka fara zuwa har tayi bacci. Ya bude fridge zai saka Rumana ta karbi ledar tace bari ta cire albasa da kabejin da yake ciki kada ya bata naman idan ya kwana.

Kamar yadda Hajiya Umma yayar Mama ta fada mata komai tayiwa mahaifiyarsa zai kara mata kima a idonsa haka ta kula da yadda yaji dadi sosai. Jiranta yayi ta cire sannan ta saka a fridge din suka tafi wurin Baaba.

Ga dukkan alamu itama baccin take shirin yi. Fuskarta a sake da ta gansu dadi ya mamaye mata zuciya.

“Awaisu kai da kake da tafiya a gabanka gobe shine baka yi shirin kwanciya ba?”

Leda daya ya ajiye mata yana murmushi “nama na tafi nema miki Baaba”

“A’a wannan kurar dai ta kusa da kai ka sayawa na sani.” Ta bude ta dauki daya tana dariya saboda Rumana tace ita ba kura bace.

STORY CONTINUES BELOW

“Yaya ya shigo ne?”

“Bai dade da tashi ba. Dama maganar tarewar Rumana ne. Kana ganin nan da sati hudu masu zuwa yayi maka? kada ta rasa da yawa a karatunta. ‘Yan uwanka suna son su kammala shirye shirye don ko tsinke ba’a fara tanadar mata ba”

Zama yayi sosai Rumana zata fita yace ta zauna itama. Baaba Hure ya kalla sai kuma ya dukar da kansa.

“Yanzu Baaba ni Yaya Harisu zai yiwa haka? Ko ban auri Rumana ba waye zaiyi mata kayan daki idan ta tashi aure?”

Baaba ta dan murmusa “kai ne.”

“To wallahi bana bukatar komai daga wurinsa. Ban isa na rama muku komai da kuka min ba Baaba. Bani da wannan niyar ma. Amma burina bai wuce na ga na kyautata muku iya yadda Allah Ya bani iko. Banda al’amura sun zo mana a haka Rumana a gida ya kamata ta zauna har aurenta. To kuma yadda nasan da hakan ta faru bazanso kowa yace zai shigar min kan maganar kayan daki da abubuwan da amarya take bukata ba yanzu ma bana so. Kawai ku saka mana albarka shikenan”

Baaba ta share kwalla “Awaisu meye baka yi mana ba? Yayanka da mazan yan uwanka mata babu wanda baka karawa jari ba. Yaransu duka babu wanda baici moriyar samunka ba. Duk wata aike baya yankewa tsakaninmu da kai ko da baka zo garin nan ba. Me zamu ce maka mu kuwa. Allah Ya kara yi muku albarka Ya rabaku da dukkan sharri”

Suka amsa da amin. Satar kallonsa Rumana tayi tana murmushi hannunta na daidai wurin kunar ta ma manta ta dan sosa wurin.

“”Ya soma kaikayi ne?”

Baaba tace meye yake kaikayi kuma. Cinyar Rumana ya nuna mata tare da bayanin me ya sameta. Saman wardrobe dinta ta nuna masa.

“Ga zuma can dauko ka shafa mata kada ya tashi. Kasan ba’a raina kuna.”

Rumana ta tashi har tana tuntube da kafar Awaisu.

“Bari na dauko naje daki na shafa”

Baaba ta wurga mata wata uwar harara “kin sami wuri kin zauna ko kuwa. Dauko kaji dan albarka” ta yiwa Awaisu murmushi.

Dariya yayi yadda Rumana tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka. Shima kuma da ya dauko sai ya kalli Baaba a dan kunyace ya mikawa Rumana kwalbar zumar. Duk abinsa da kunya ya kwaye mata cinya a gaban kakarta.

Baaba ta kada kai “Ahaf, abin da yanzu aka fara auren. Meye a shafa zuma mu da za’a kawo mana ‘yan dugwi-dugwi mu goya. Indai don nice ku kara gaba don ba fita zanyi na bar muku dakin ba.”

Kafin ma ta kai karshen maganar Rumana ta fice da sauri Awaisu ya bi bayanta yana dariya. Ita kuwa Baaba suna fita addua take Allah Ya kara hada kansu.

Da kyar ya kamota zata yi hanyar dakin mamanta.

“Wannan sauri kamar zaki tashi…ga wannan maganin shima na shafawa ne. Ki bara shafa zumar yau gobe sai kiyi amfani dashi. Ga naki naman kici kafin ki kwanta. Lastly kuma kada ki kashe wayarki zan kira”

Juyawa yayi ya tafi ya shige dakin Mama. Bata yi mamakin ganinta ba don taji sanda Baaba Hurw ke fadawa Maamu wai yaran yanzu basa lissafi. Ji dai Awaisu da Ummukulsum wai sun kai Rumana can gidan bayan a nan zaifi ganinta son ransa. Ko da suka fara zancen Mama fita tayi don kunya suka sa taji. Nata naman ne a gabanta tana ci tace yanzu aka raba aka kawo mata. Rumana duk kunya ta isheta ta shige uwar dakin ta dauko charger ta tafi nasu dakin bayan tayi mata sai da safe.

Wayar kusan awa daya sukayi kafin sukwanta duk da shine yake kaso casa’in na maganar.

Tun da tayi asuba bata koma bacci ba ta zauna gari ya danyi haske tayi wanka ta shirya. Takwas da mintuna kadan ya kirata yace ya shirya ta fito ya kaita gidan Anti Ummukulsum ya wuce. Sai a lokacin yake danasanin kin tahowa da drebansa.

STORY CONTINUES BELOW

Harisu ya fito sunyi sallama yaje wurin Maamu suka taba hira tace yaushe zai dawo yace Juma’a. Ai kuwa ta rinka dariya tana cewa ya hakura sai nan da wata biyu ita ta warke. Yadda yayi mata da fuska ya kara bata dariya.

“Wasa nake maka angon Rumana”

Ya dan sosa keya “Maamu harda ke a tsokanar”

“Nice ma kan gaba.” Ta gyara zama “Ka kula da amanar Rumana kaji ko. Kada naji ko na gani. Idan wancan karon tsautsayi ya ritsa damu sake faruwarsa sunansa sakaci daga gareka. A wannan lokacin kuma zan nuna maka fushina”

“In sha Allah bazan taba ganin fushin nan ba kuwa Maamu. Zan rike miki ita tsakani da Allah”

“Haka nake son ji. Allah Yayi albarka Ya tsare hanya Ya kaika lafiya. A kiyaye haram komai kyau da dadinta halaka ce”

Yaji dadin adduar sosai yayi sallama da kowa ya fita sannan Rumana ta fito don kunyar biyo bayansa take ji gaban mutane. Gaishe shi tayi sanna ta shiga ta zauna. Kallonta ya rinka yi tayi kyau duk da hijab ne ma a jikinta.

Sun fara tafiya taji hannunsa akan cinyarta.

“Kin hanani jinya bayan ni na jawo ciwon. How do you feel yau?”

Kunyarsa ta yau har tafi jiya saboda hasken gari yana ganinta sosai. Da kyar ta amsa masa. Bakin ATM machine ya tsaya ya ciro kudi suka tafi gidan Anti Ummukulsum.

Da sauri sauri suka gaisa don yace baya son tafiyar dare. Dubu dari ya bata yace tayi masa magana idan bai isa ba. Rumana ya nema har ta tafi wurin Iman aka kira masa ita.

Su biyu ne a falon da suka zauna jiya. Idonsa a kanta yace “kin tuna me ya faru a falon nan jiya?”

Wayyo tace a fili tana rufe ido. Haka zata zauna dashi yana sata jin kunya haka. Yaushe zata manta ita kuwa.

Tashi yayi tsaye “ban manta assignment din da kika bani ba. Ki shirya ina dawowa zaki cika alkawarinki kema”

“Bafa alkawari nayi ba Uncle”

“Har kin karaya kenan. To ki kwana da saninki ina dawowa zaki biya da abin da na fada miki jiya” ya dan daga kai ita kuwa sai ta juya gefe.

“Zan tafi Umm Ruman babu ko sallamar miji da zan samu? “

“Uncle Allah Ya kiyaye hanya Ya kaika lafiya”

“Amin amma sauran wannan”

Hannuwansa taga ya ware alamun tazo ya rungumeta. Sakin baki tayi tana mamaki.  Ko da wasa bazata iya ba.

Hannunsa ya kuma nuna mata da kansa yana jiranta.

“Zaki sa nayi dare fa. Ni fa babu inda zani sai kinyi min irin sallamar da nake so”

Tsaye take tana ta shawarar me zatayi. Uncle Awaisu ya sakata a tsaka babu mafita. Tana dago kanta suka sake hada ido ya kyabe mata fuska shi ya gaji. A hankali ta rinka takowa gabansa. Har ta kusa karasawa cikin hannuwansa yana murmushi sai kawai yaga ta zagaye ta bayansa ta rungume shi a hakan ta hanyar zuro hannuwanta ta karkashin nasa ta kwantar da kanta a bayansa. Motsin kirki Awaisu ya kasa saboda yadda yaji. Yatsunsa ya zura cikin nata masu dauke da jan lalle mai kyau yana ta murmushi ya kasa ce mata komai. Rumana ta gama masa komai ta shige ko’ina a cikin zuciyarsa. Tsoron abinda zai iya biyo idan ya kalleta yasa bai juyo ba sai hannunta da ya dan matse sannan yace

“Kamar kullum ki kular min da kanki. Ina yi miki son so Umm Ruman. Wannan new way of saying I love you ne”

Daga bayan nasa tayi wani kyakkyawan murmushi cike da kunya ta sake shi. Wai Uncle Awaisu yana sonta. Shima bai juya ba ya yi gaba yana  kara jin  sonta ya wuce.

******

Bayan tafiyarsa Anti Ummukulsum ta kirata daki. Plate ta miko mata ta kalli abin ciki ta kasa tantance ko menene.

“Daga yau kada na sake ganin kina cin komai sai abin da na baki kina jina. Wannan kasusuwan nake son rufewa kafin ki tare. Kuma kina bukatar kayan gina jiki don haka kada na kuskura wallahi na kamaki da kayan kwalamar da kuke ci da Iman.”

STORY CONTINUES BELOW

Rumana tayi murmushi “To Aunty meye wannan din?”

“Zogale ne na dafa na soya soya da albasa mai yawa da tumatir da kwai. Kici kisha wancan youghurt din” ta amsa mata.

Rumana ta ja plate tana kwasar dadi. Daga ranar Anti Ummukulsum ta dauki damarar gyaran ‘yarta. Kullum sai tayi mata farfesun kaji, kifi, kayan ciki ko nama. Ganye kuwa wasu ko sunansu bata sani ba haka take yi mata miyar  tuwo ko farar shinkafa. Ga maltina sai tasha gwangwani hudu a rana. cikin dan kankanin lokaci ta soma canjawa ita kanta tana ji a jikinta.

******

Washegarin komawar Awaisu yaje gidansu Gimbi ya sanar da iyayenta zai kawo su Daula na dan lokaci. Mama tace dama taso tayi masa magana tun ranar da yazo ma. Sun sanar dashi lokacin da ya tashi komawa Fika ya fada musu tare zasu je. Gidan nasa kuma a lokacin suka bi bayansa zasu taho da yaran su ga Gimbi.

Suna ta sallama ba’a amsa ba yana daga bayan Alh Mudi yace su shiga kawai yaran suna islamiyya ne. Mama kai tsaye dakin Gimbi ta wuce. Waya take yi ma bata ji shigowarta ba tana ta fada sai sakin kudi take yiwa su Ovi a kaiwa boka amma babu wani chanji. Ganin Mama yasa ta tashi da sauri ta katse wayar.

“Mama yaushe kika shigo?”

“Fito falo babanki yana jira”

Gabanta ne ya fadi. Rabonta da shi tun lokacin da Awaisu ya saketa taje gida. Dankwalinta ta janyo ta daura ta fito. Ganin Awaisu a wurin yasa tayi wani dan murmushi, wato ta nan ya bullo kuma.

“Alhaji sannu da zuwa, Abban Haris yaushe ka shigo?” Ta fada fuska a sake.

Alh Mudi ne ya soma magana “kinga bana son gulma ki zauna kawai muyi abin da ya kawo mu. Duk abubuwan da kikayi Gimbiya mun sami labari. Wallahi kin bamu kunya amma ki sani ba kowa kika cuta ba sai kanki.”

Kuka ta soma yi “Alhaji sharri yan uwansa suka kulla min don kawai basa sona. Zancen da nake muku fa ‘yar yarinyar nan da na rike suka aura masa”

Mama tace “Allah Yayi musu albarka da wannan hadin. Gimbi kada ki manta Bebi kanwata ce saboda haka idan ma kina shirin wani rainin hankalin ne ki nemi wanda zakiyiwa ba mu ba. Awaisu da danginsa bazasu miki sharri ba domin idanuna sun gani tun kafin ma Maamu ta dade a gidan nan kika ce min ba haka ba.”

Alh Mudi ya karba “Jiya muka dawo daga wurin Inna (babarsu Mama da Anti Bebi). Rokon su Amina gafara take akan yadda ta juya musu baya komai sai Bebi. Tayi rantsuwa bata san lokacin da take wasu abubuwan ba musamman danne musu hakki da Baba ya rasu da ta hada kadarorinsa da dama ta bawa Bebi a boye. Abin da ya rage aka raba daidai kuma da ita. Ke bari na takaice miki a yanzu Bebi da mahaukaciya fa bambancinsu bashi da yawa. Idan bazaki tub….  “

Murmushi yaga Gimbi tana yi wanda ya bayyana tsantsar farincikinta jin ance Anti Bebi ta zama kamar mahaukaciya. Abin ya konawa Mama rai ta kai mata duka. Haka suka zauna suna ta nasiha da fada yana bi ta bayan kunne. Da suka tafi ta tashi harda kade riga tabi bayan Awaisu.

“To me zuciyar yara a karo na karshe ina fada maka ka barni na fita daga gidannan kafin ka ga ba daidai ba”

Yana zare necktie dinsa yace “na nawa kuma. Kada ki damu kwana nawa ne zaki kara gaba”

Tsoro ne ya kamata don har mamaki takeyi wani azababben so da take masa yanzu. Duk wannan ruguntsimin da suke fama dashi son Awaisu karuwa yake a ranta kamar ana hura wuta ‘yan kwanakin nan. Da farko neman mafita take ko dai zamansu ya gyaru ko kuma ya saketa. Yanzu kuwa ido rufe gyaran take nema. Haka ta fita ba don taso ba. Har juma’a ta zagayo suna faman rigima tana son fita ga yaranta an kwashe sun koma gidan iyayenta. Wannan abu ma yayi mata ciwo. A cikin kwanakin bashi da nutsuwa sai idan yana waya da mutanen Fika musamman amarya Rumana. Daga banki sai gida yake zuwa. Bincike yake yi akan wadanda Gimbi ke muamalar zuwa wurin yan tsibbu tare dasu.

Abin da Gimbi bata sani ba shine kwanaki uku da suka wuce Anti Bebi da kyar da sidin goshi Wangesi ya yarda ya ganta. A nan ne take fada masa cewa tana zargin Gimbi domin aljanu har magana suke mata a kunne suce Gimbi tafi karfinta gashi sun jawo ana ganin kamar bata da hankali. Bayan dogon bincikensa na tsafi ya gano gaskiya ta fada. Fushi yayi mai tsanani har yaushe Gimbi ta isa tayi masa wasa da hankali. A dalilin haka yayi alkawarin ko me Anti Bebi take so ayi mata zaiyi. Shine ta rokeshi ya cusawa Gimbiya soyayya da kishin Awaisu na fitar hankali. Irin son da ko macen kuda bataso ta rabe shi. Ita kuma zata je ta tona mata asiri ya saketa. Tasan wannan son shine zai zamewa Gimbi masifa a duniya. Ko babu asiri mahaukacin son da take masa ne yasa bata son kowa ya rabesu musamman uwarmiji kada asa shi ya saketa.

*****

Dan sakin fuska  yau ta shiga dakinsa tana tsaye daga gefen mudubi shi kuma yana ta aiki “kasan dai ina da hakki a kanka ko Abban Haris. Yaushe rabonka da zuwa inda nake?”

Tafi ya rinka yi har ya isa gabanta “amma dai baki da kunya Gimbi. Wai hakkinki. To na karfine sai ki kwata ko kisa bokanki ya baki tunda dashi kika dogara.”

Ranta a dagule ta soma fada “nifa bazaka dokeni ka hanani kuka ba. Ka rufe ni a gida babu fita sannan ka tauye min hakki. Ga waccan shshh…..”

Babu yadda za’ayi ta karasa zagin don wani mugun kallo yake watsa mata.

“Kina iya fita gobe duk inda zaki kada ki wuce  karfe hudu ki dawo gida.” Taji yace

Anya kunnenta ya jiye mata daidai kuwa? Bata son jan zancen kada yace ya fasa tace to kawai ta fita. A baya ya bita yana jikin kofa yaji tana waya tana cewa zata zo gobe. Dariya yayi ya koma daki. Ya rasa yadda zaiyi ya dauki wayarta saboda balain yadda take kaffa kaffa da ita ko bandaki ta shiga idan ya duba dakin baya gani.

Ba dai haka yaso ba amma dole ya kira Rumana ya bata hakuri na rashin zuwansa a satin. Dama ita da take jin kunyarsa sai ta nuna bata damu ba har yana ta mita wai taki fara yi masa son so har yanzu yana so ta fara shiri tarbarsa sati mai zuwa.

Washegari kafin tara na safe Gimbi ta fita don ko ganinta baiyi ba. Yana fitowa daga daki da yaga bata nan ya koma yayi alwala tare da nafila raka’a biyu don neman kariya. Dakin Gimbi ya fara shiga ya fiddo kayanta daga wardrobe ya bincikesu. A ciki ya tsinci layu da guraye sunfi goma. Karkashin gado, kasan kafet har su toilet babu inda bai duba ba. Abubuwa ya rinka gani harda wasu irin ruwa masu kala a robobi. Jikinsa sosai yayi sanyi karshenta babu wanda baa zuba masa ba.

Yana gamawa da dakinta nasa ya koma shi kam har cikin pillow da kasan katifa akwai ajiyar layu. Haka ya wuni yana wannan aikin harda su kitchen, dakin Maamu da duka dakunan baki da na yaransa. Bayan ya gama hadasu ya fita duk inda babu interlock a gidan yace maigadi ya tayashi tonawa. Yawanci duk wuraren shuka ne amma sunyi sa’a babu komai a wurin.

Ciki ya koma duk yayi gumi ya watsa ruwa ya gyara dakinsa sannan ya kira cikin yaran shagonsa yace yazo yana nemansa.

Kayan gidan kaf banda na dakin Gimbi amma komai harda kayan kitchen yace a samo dillalai masu saya saboda da yawa basu tsufa ba. Kafin ya tafi suka shawarta ina zaije wurin kayan furniture masu kyau. Sunan wani shago ya bashi a wata babbar plaza. Zama yayi yayi dogon list na abubuwan da zai saya nasa da Rumana da yaransa. Kayan kitchen da su labulaye da komai ya gama tsarinsa. Kudi dai zasuyi ciwo amma yadda ya tsorata da kayan tsafin nan ko bai kara aure ba ya zama dole ya rabu da komai na gidan domin samun kwanciyar hankali.

Yaron shagon sai da yayi kusan awa daya ya dawo gidan tare da masu ganin kaya. Babu bata lokaci sukayi ciniki suka turo motocin dibar kaya.

Gimbi na dawowa wurin karfe shida ta ga gate a bude motoci biyu manya cike da kaya suna fita. A gigice ta shiga gidan ta sami Awaisu a falo ya zuba hannuwa a aljihu yana magana da wani cikin mutanen inda yace duk da yasan zasu chanja kujerun amma suyi hakuri ya farke dukkansu ta kasa. Kasa magana tayi jikinta na bari tana tunanin ba dai ya ga ajiyar da tayi masa a daki ba. Ko da ta shiga nata dakin haka ta  sami kayanta watse ko ta ina. Zama tayi jiki babu kwari ta dago jakarta tana tunanin ta ina zata zuba masa wannan maganin da akayi mata alkawarin karshen duk wata damurta yazo indai yasa shi a bakinsa.Aiki su Awaisu sukayi tukura ranar sai bayan isha suka tafi zasu dawo dibar sauran waahegari sannan shima zaije duba kayan da zai siyo.+

Dakinsa ya wuce babu komai sai barguna da ya shimfida a kasa don hatta pillowas yayi waje dasu. Kayansa kuwa da takardu wasu suna cikin akwatuna wasu ya turasu gefe a dakin. Wanka yayi ya kwanta bayansa har ciwo yake masa saboda tsabar gajiya. Yana jin yunwa amma baya tunanin zai iya fita daga gidan saboda ciwon jiki. Wayarsa ya dauko yana ta binciken aikin da Rumana ta bashi har yau ya kasa gane me take nufi. Zuwa yanzu ma dai gani yake ko kawai tsokanarsa tayi. Murmushi yake yi shi kadai idan ya tuna rabuwarsu. Bugu yaji a kofar dakin kamar daga sama ana yi da karfi. Sai lokacin ya tuna ya rufe dakin da mukulli da zai shiga wanka kada tazo ta saka masa wani abin a cikin kaya don ya tabbatar tunda ta fita babu abin da zai hanata dawowa da wani maganin. Tashi yayi ya bude mata ta kura masa ido. Yanzu komai nasa kyau yake mata fiye da yadda ta saba gani. Haushin kanta take ji sosai na wannan makauniyar soyayya da bata yi ba ko da can da kuruciya da ta tabbatar ta so shi sosai.

“Naga an fitar da kusan komai na gidan nan banda dakunan baki da nawa”

“Sababbi zan siyo ai kinsan nayi aure ko? To amaryar ce zata tare nan ba da dadewa ba” yana magana yana kallon hannuwanta da take kokarin taba shi dasu. Ja da baya yayi ya hade fuska ta sauke hannun ba shiri.

“Ba zuwa nayi ka fada min bakar magana ba mijin Rumana mai budurwar zuciya. Nazo yi maka tuni ne akan kayan fadar kishiya da ban ga kana da niyar yi min ba tunda kayan dakina banda hargitsawa ko tsinke baa dauka an fitar ba”

Yatsansa ta ga yana kadawa a gefen kansa “Gimbi kin fara shaye shaye ne? Ni kike tambaya kayan fadar kishiya? Idan har sai na baki zaki saka kaya to ki fara shirin yawo tsirara. Ke bari na fada miki wannan hannun da kika shafowa kayan tsibbunki idan kikayi gigin tabani dashi sai na karya shi. Sauran tarkacen da kika ajiye a lunguna da sakon gidan nan ma na konasu gabadaya kuma in sha Allah kin gama samun nasara a kaina da ‘yan uwana na.”

Borin kunya ne ya kamata amma dayake ta kware ta daga kai tana hura hanci “ni ba damuwa zanyi da sharrin da aka cusa maka yarda dashi daga gidanku ba. Idan ma ka tsinci wani abu baya wuce wanda aka bawa Rumana ta binne a gidan nan don ka aureta. Kuma gashi bukatarsu ta biya sai su zuba ruwa a kasa su sha”

“Kinga na gaji idan kin gama abin da ya kawoki sai anjima” kofar ya janyo ya rufe ya barta a tsaye daga waje.

Shu’umin murmushin da yanzu take yi idan ta sami nasarar aiki tayi ta juya ta tafi. Indai itace sai ya dawo bata hakuri don tun kafin ya bude kofar ta shafa maganin a jikin hannun kofar dakin. Fatanta idan ya taba yaje ya dauki wani abu yaci da hannun ta samu maganin ya shiga cikinsa.

Sai bayan wurin rabin awa da tafiyarta ya bude kofar ya fito rike da karamin towel jike da ruwa. Bismillah yayi ya goge kofar tun daga sama har kasanta. Duk da bai ganta ba amma yaji a jikinsa yanzu ko ta wane hali Gimbi zata yi kokarin hadashi da magungunanta. Ji yayi kamar ya saketa tun yanzu sai ya fasa. A kalla ta zauna ko na wata daya ne da Rumana ta kwashi guzurin bacin rai ta tafi dashi.

Rumana ya kira Iman ta dauka tace masa tayi bacci. Ya kula tana kwanciya da wuri shiyasa yake kiranta da farkon dare. Yau da bai kira ba ta sami kanta da jiran wayar tasa har bacci ya dauketa. Gashi ita kuma tana kunyar kiransa da kanta.

*****

Washegari Rumana da wuri tayi wanka saboda Mama tayi mata waya tace taje gidansu Hajiya Umma tana kiranta. Tana shiryawa Iman tazo ta zauna a kan gado

“Rumana kina kiran Uncle Awaisu kuwa?”

Ta madubi ta kalli Iman din “bangane ba?”

“Naga kullum sai dai yayi ta kiranki a waya. Jiya ma ya kira kina bacci. Ke ko dan text dinnan bana jin kina masa bare su chatting a whatsapp.”

STORY CONTINUES BELOW

Juyowa tayi da kyau ta kalleta “Iman, Uncle ne fa. Sai in yi masa text don rashin kunya.”

Dariya Iman din ta yi taje ta kamo hannunta suka zauna “Jiya Ummanmu ta tambayeni ko kina masa waya nace kuna waya dai don ban san dalilin tambayar ba. Shine tace in fada miki ki rinka sakin jiki dashi gidansa zaki koma. Kuma dai Rumana baki gani mu masu samari ma ko babu kudin kira mukanyi text balle ke da mijinki. Mijin ma kamar Uncle dan gayu dan boko”

Rumana tayi shiru jikinta ya danyi sanyi “tsakani da Allah ina son yi amma tsoro nake ji kada ya fassarani yace sonsa nake yi”

Wani mugun duka Iman ta sakar mata a baya saki kara tare da mika hannu tana shafa wurin. Iman tace “Wai kada yace kina sonsa. To da bazaki so shi ba bayan ya zama mijinki? Ko don kinga babba ne” ta kare da sanyin jiki.

Kuka Rumana ta soma yi mata ta  girgiza kanta  “kunyarsa kawai nake ji har cewa yake yana sona Iman. Idan ya fada sai naji har tsigar jikina na tashi. Wai ni yake so. Ta yaya zamu zauna idan aka kaini Abujan? Don bakiji yadda gabana ke faduwa ba.”

Duk da Iman ba wata babba bace amma tafi Rumana wayewa ta wannan fannin “ina jin fa kema kin fara sonsa ne tunda kike jin haka. Ki rinka yi masa text ko waya kice gaisheshi zaki yi zaiji dadi.”

“Idan nayi niyar yin abu sai naji tsoron kada yace bani da kunya ko kuma idan banyi ba yaji babu dadi. Shiyasa cikin biyun nake zabar rashin yin”

“Cikin kudin da ya aikowa Ummanmu da tace yace a baki ki karba kisa kati mana ki kirashi”

“Ya saka min kudi yafi 5000 a ciki shiyasa nace mata ta barshi bana bukata”

Harararta Iman tayi “kina da wannan kudin shine kika gagara kiransa. To yanzu kafin ki fitan nan tura masa text na gaisuwa kawai”

Da taimakon Iman ta rubuta text don duk wanda tayi sai Iman din tace baiyi ba. Karshe tambayarta tayi ko tana missing dinshi. Murmushi Rumana tayi ai kuwa Iman ta rantse sai ta rubuta tunda abin da ke ranta kenan. Tana turawa ta kashe wayar ta saka a yar jakarta. Bata ma son jin me zaice idan har yin text din laifi ne gashi Iman ta sakata rubuta abin da batayi niya ba.

******

Yanayin gajiyarsa ta jiya ya sanya shi tashi a makare. Shima wayarsa maigadi ya kira ya fada masa masu kwasar kaya sun dawo. Umarni ya bayar a bude musu gate yana zuwa. Alamun sakonni text ya gani da yawa ya dan bude ya duba sunayen wadanda suka turo ko akwai masu mahimmanci sosai ya fara cin karo da suna *SS* wanda a haka yayi saving din sunan Rumana wato son so. Cikin sauri ya bude saboda yau ce rana ta farko da ta taba turo masa.

_Uncle ka tashi lafiya? Yaushe zaka dawo ne? I miss you._

Ya karanta yafi sau biyar bakinsa ya kasa rufuwa saboda farinciki. Karshe dai screenshot yayiwa text din yasa shi a screensaver. Da ya kirata yaji a kashe yasan kunya taji shiyasa ta kashe.

A gurguje ya tafi wurin masu kwasar kayan aka ci gaba da gyaran gidan.

Gimbi na ganin shigarsa daki ta koma nata dakin tsabar murna harda tsalle tayi. Bokan Ovi bashi da wasa tasan indai anyi yadda yace bukata kuwa zata biya.

Rabuwa tayi dashi sai dare bayan ya dawo daga zabar kayan gida da zai saya ta shiga dakin tayi kwalliya tasha turaruka tana zuba kamshi.

Karar ruwa taji daga bandaki tasan wanka yake yi ta sami wuri ta zauna. Yana fitowa ya ganta. Dauke kai yayi ta danyi murmushi

“Kaga ba fada ne ya kawoni ba. Magana nake so muyi”

“Ina jinki”

“Ba wani jan zance zanyi ba yarinyar nan da ko sunanta bana son fada nake so ka saki”

Fuska ya saki ya ce “shikenan bukatarki?”

Bokan nan ba dai iya aiki ba ta fada a ranta “sauran komai mai sauki ne indai ka saketa”

STORY CONTINUES BELOW

“Miko min takarda da biro zaifi akan na tura text”

Jiki na rawa tana sauri ta dauko masa takarda da biron daga cikin jakar da yake zuwa office da ita. A kasa ya zauna yace ta matso ta rinka gani. Da ta tashi harda shigewa jikinsa.

_Ni Awaisu Kabir Fika na saki Gimb.._

Wata muguwar wawura Gimbi tayiwa takardar. Kafin ya farga ta nadeta ta cusa a baki tana tauna iya karfinta.2

Awaisu baiyi magana ba ta tashi a fusace ta fita harda buga kofar dakin da karfinta. Sai a lokacin yayi dariya don ya fuskanci abin nata ya soma zama hauka. Wato ta saka masa magani ne nan a tunaninta yayi aiki a kansa.

*****

A can Fika kuma da Rumana taje gidan kakaninta nasiha suka yi mata sosai da shawarwari akan zaman gidan miji tunda abu ne yazo musu duka babu shiri. Anti Umma tata shawarar harda yadda zata kula da kanta da kuma canza salon yadda take gabatar da kanta a gaban Awaisu domin kuwa yanzu mijinta ne shi kuma wannan matsayin ya danne duk wata alaka da ta san suna da ita a baya. Wasu abubuwan dai ji take sun girmi tunaninta musamman da yake ita ba mai kwashe kwashen kawaye bace bata tashi da lallai sai ta koyawa kanta ilimin da komai dadewar lokaci indai mace tayi aure zai zo gareta ba. Anti Umma tace mata lokacin kunya ya kare tunda an shafa Fatiha, yanzu sai karatun yadda za’ayi zaman. Ranar a nan ta wuni sai yamma likis ta koma gidan Anti Ummukulsum.

Bata jima da tafiya ba kayayyakin da dangin Mama suka tura kannensu biyu Kano su siyo suka iso. Yawanci kayan kitchen ne kuma sunyi kokari sosai don an mata siyayyar da ta dace duk da kurewar lokaci. Su Anti Umma ne suka kai kayan gidan Harisu a matsayin tasu gudummawar. Lokacin yake sanar dasu yadda sukayi da Awaisu akan yi mata siyayya.

Anti Umma tace babu yadda zasu aurar da ‘ya ko tsinke babu. Aure daban zumunci daban. Basa fata ko da wasa nan gaba wani abu ya taso gori ya biyo baya.

*****

A hankali kowane bangare ya cigaba da shiri. Rumana tana can tana shan gyara a wurin Antinta. Awaisu kuma ya wadata gidansa da duk kayan bukata don har fenti aka sake yiwa gidan. Kayan kitchen ne Harisu yace ya dakata har sai an kawo wanda gidansu Mama sukayi don sunyi rawar gani kada ayi ta asara wurin sayan wasu.

Gimbiya bata sake shiga sabgar Awaisu ba don ba karamin tsorata tayi da sakin da ya kusa auna mata ba. Yanzu jira take yi Rumanan ta iso gidan ai ba sai da Boka kadai zata iya sawa ta bar mata gida ba. Har nawa take da zata yi kishi da ita.

Yau alhamis Awaisu ya tashi daga wurin aiki ya wuce gidan Alh Maitama. Sun dade suna magana da shi akan halin da Gimbi da Anti Bebi suka sakasu.

“Babu abin da yake damuwa Mal Awaisu kamar kashewa Shuhada aure da tayi. Wallahi da mijin nata yazo gidan nan ya shiga wani irin yanayi. Kuma gashi saki uku ne”

Awaisu ya jinjina kai. Mutanen nan sunyi nisa. Yanzu dole sai dai ta auri wani anyi mata katanga da masoyinta. Shuhadan ya nemi gani bayan sunyi sallama da mahaifinta. Sun gaisa a mutumce har yake bata labarin abubuwan da suka faru da Maamu har zuwa aurensa da Rumana.

Baki da rike tana dariya “Kaga ikon Allah ko. Allah sarki Rumana yaushe zata tare muzo yiwa Gimbi dannar kirji?”

“Sai ki taho da yan sanda saboda na tabbatar bazaku rabu lafiya ba” shima yayi maganar yana dariya.

“Shuhada nagode sosai da taimakon da kika yi min duk da a lokacin ban san me yake faruwa ba. Kuma ina so don Allah mu cigaba da zumunci. In sha Allah har gidan nan zan kawo miki Rumana kafin kema Allah Ya kawo mana suruki musha biki. Alhaji yace akwai kaninki da zaku je gani ba don haka ba da na gayyaceki biki har garinmu”

Murmushi tayi “in sha Allah zumunci yanzu muka fara. Sai dai batun aure sai dai zuwa nan gaba. Yanzu dai masters zan nema in sha Allah”

*****

Ranar Juma’a yana ta murna zai je Fika da sun tashi sai dai wannan karon da dreba zaije saboda ya sha wahalar tuki wancan zuwan. Rumana tun da tayi masa text dinnan bata sakewa dashi sosai sai ya kyaleta yana jiran su hadu.

STORY CONTINUES BELOW

Yau ma baiyi nasarar gano aikin nan da ta bashi ba gashi har ya kusa tafiya Fikan. Yayi ta browsing akan sign language bai ci karo da wannan alamar ba. Hakura yayi kawai yace zai sa ta fada masa da bakinta. Idan tsokana ne kuwa yasan maganinta don ta bashi wuya.

Wurinsu Haris ya fara zuwa ya kaiwa su Mama kudi duk da basu karba ba yayi musu alkawarin yana gama gyaran gida zai mayar dasu. Sai dai ya kula suna jindadin gidan sosai kuma ga chanji sosai a yanayin tarbiyarsu. Daula ce mai tsiwa ya kula tafi kowa nutsuwa duk da ba wai ta dena wasa ko harkokinsu na yara ba.

Anti Ummukulsum ya fadawa tun safe yana hanya bayan ya tashi daga aiki amma yana so tasa Rumana yi masa girki duk da bai fada mata ya taho ba. So yayi ta ganshi kawai.

Da taimakonta Rumana ta dafa tuwon shinkafa da miyar taushe wadda aka sawa ganyen ugwu da alayyahu don tasan yana daga cikin abincin da yake so. Sai lemon kankana da apple mai dadi.

Anti Ummukulsum ta tafi amsa wayar maigidanta shima washegari zai dawo Rumana tana cin cingam ta ciro shi ta sake dandana miyar a karo na barkatai. Miyar tayi mata dadi sosai amma sai taji kamar da dan tsami wanda dandanon cingam din bakinta ya saka mata.

Fridge ta bude ta dauko soyayyen jajjagen attaruhu da albasa ta kamfata a cokali daidai yadda take jin zai daidaita miyar ta zuba cokali biyu. Ta sake debowa taji Anti Ummukulsum na tahowa tayi saurin ajiyewa don ita tace miyar tayi.

“Rumana ba dai karawa kika yi ba?”

A tsorace tace “yanzu zan zuba naji kamar da tsami”

“Ba dole kiji tsami ba kina ta fama da cingam mai tsami sosai. Kunfi so kuji miya ana ci ana shhhh da baki. Kije kiyi wanka ki shirya ina jiranki yanzu”

“Fita zamuyi?”

“Zamu je gida ne amma kiyi sauri kada yamma tayi”

Rumana ta tafi ta shirya tana saukowa ta ga Anti Ummukulsum ta hada kwanukan abincin a cikin wani kwando mai kyau. Kwandon tace ta dauko su tafi.

Suna zuwa gidan da murnarta ta shiga dakin Maamu don tayi kewarta sosai. A guje ta shiga tana kiran Maamun. Kamar yadda ta saba fadawa tayi jikinta tana tambayarta yaya jiki.

“Jiki da sauki Rumana ina maman taki?”

Sai a lokaci ta kula ita kadai ta karaso. Ashe Anti Ummukulsum din ta tsaya a falon Harisu inda suke hira da Awaisu yana masa fadan yaki cin abinci.

“Rabu dashi na amarya yake jira. Ta shige dakin Maamu bari nace ta kawo maka abincin”

Harisu ya kalla yana yar dariya “Yaya anyi min izinin tashi”

Harisu yace nan da sati biyu zaku bar min gida ni dai. Dafe kai Awaisu yayi ya fita yana dariya Anti Ummukulsum na tsokanarsu su biyun.

Rumana tana jikin Maamu tana bata labarin kayan dadin da take ci wanda yayi sanadiyar chanjin da Maamun ta gani a jikinta.

“Ta kyauta min kuwa zan aika da tukwici” inji Maamu.

Wayar Rumana ce tayi kara ta duba ta ga sunan uncle. Kasa dauka tayi wai kunyar Maamu ai kuwa ta rinka mata dariya wadda tasa ta fita ta tafi dakin Baaba Hure. Tana sa kafa suka hada ido dashi gabanta ya fadi yana zaune shima shigarsa kenan bayan ya kira bata dauka ba.

Kamar ta juya sai kuma ta daure ta karasa ta fara gaishe da Baaba sannan ta gaishe shi kanta a kasa. Wani irin dadi taji da ta ganshi kunya ta hanata nunawa. Shi kuwa kallonta yake duk ta chanja ta kara kyau. Baaba ta dan zungure shi.

“Nace ba, ai kana da daki a gidan nan ko? To ku tafi can ku gaisa sosai ba a nan ba. Kai ka kura mata ido ita tana satar kallonka kun manta ina dakin. Ni da dakina babu mai korata”1

STORY CONTINUES BELOW

Rumana ta tashi zata gudu Baaba tace “baki isa ba yarinya wuce ki bishi kuyi gaisuwar yaushe gamo kada kisa ya kasa komawa bakin aikinsa” ta kare da dariya.

Awaisu kansa kunya yaji ya tashi “daga zuwa gaisheki sai ki koreni ko Baaba”

Tace “a ranka kana shi min albarka ba…a tafi dai kafin nace tazo ta min tausa”

Yasan zata aikata hakan ya fita ta koro masa Rumana wadda kunya ta hanata tashi.

“Ina jiranki a daki ki kawo min abincin yunwa nake ji please” yace ya fara tafiya.

Sai lokacin ta gane ashe girkin da sukayi nasa ne Allah Yasa tayi kokarin ganin yayi dadi.  Da can tana zuwa kai masa abinci ko damunsa da hira dakin amma yanzu kunyar zuwa ma take yi. Dakin su Mama taje duka ta gaishesu sannan ta dauki kwandon abincin ta wuce dakinsa.

Zuciyarta na dukan uku uku ta shiga da sallama. Wata katuwar katifa ce a dakin shimfide da bedsheet mai quilt mai kyau. Wardrobe da dressing mirror. A kasan da karfet kalar labulen dakin sai akwatin kayansa a gefe da abin sallah. A gefen katifar yake zaune ta durkusa daga bakin kofa ta gaishe shi.

“Yau kuma tsorona kike yi? Gashi kuma kin shigo dakin nan kenan ke da fita sai da safe”

Idanu kamar su fado tace “kayi hakuri Uncle”

Murmushi yayi “to karaso mu gaisa wasa nake yi miki”

Baki ta dan turo “ai mun gaisa tun a dakin Baaba”

“Kina son kwana tare dani a dakin nan ne?”

“A’a don Allah”

Dariya ta bashi duk ta rude. Ba mamaki yasan dole iyaye zasu yi mata nasiha akan meye aure shiyasa take tsoronsa. Ai kuwa bazai bari hakan yayi tasiri a ranta ba.  Burinsa yanzu ta koyi sonsa kafin komai.

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta karasa inda yake. Hannun damansa ya mika mata ta saka nata ciki sukayi musabiha  sai dai bai barta ta tafi ba ya janyota ta zauna a kusa dashi.

A hankali ya soma magana “rannan naga text ance anyi missing dina amma nazo naga ba haka ba. Maybe daya yarinyar  ce ta turo ba naki bane don ke baki taba min text ba”

Da sauri ta dago ta kalle shi zuciyarta har tana bugawa da karfi “dayar kuma Uncle?” Ta fada a raunane

Farinciki da mamaki ne suka dirar masa. Lallai Rumana ta fara sonsa ko da bata sani ba sannan gashi har da alamun kishi yana gani. Hakan ya kara masa karfin gwiwar ya cigaba da nuna mata soyayya saboda baya son ta tare komai yazo mata wani iri saboda rashin sakewa dashi.

“Eh ke naga kamar baki damu dani ba”

Da shagwaba tace “nice na turo fa”

“Are you sure? Me kika rubuta a naki?”

Yadda ta haddace text dinnan ko cikin bacci ta tashi bazai mata wuya ba ta karanta masa yana bin bakinta da kallo.

“To kinyi missing dina? ” ya tambayeta idanunsa a kanta.

Kasa daga kai tayi sai kai da ta gyada a hankali.

“I miss you too Umm Ruman. Amma yanzu fara bani abinci”

Tana zubawa ta fada masa yau ita tayi girkin yace to bari yaci ya bata maki.

Cokalin farko da ya kai bakinsa zafin attaruhu ya kama masa harshe. Da kyar ya iya hadiyewa saboda yadda take kallonsa tana jira yaci yace da dadi. Runtse ido yayi tuwon nan yana sauka a cikinsa yaji ya mamaye ko’ina.

Kasa hakuri tayi tana murmushi tace “Uncle da dadi ko? Yanzu ina ta kara koyon girki a wurin Anti”

Kallonta yayi yaga murna take tayi masa abinci yace “yayi dadi sosai yau har kyauta zanyi miki”

Murmushin da tayi na jindadi har sai da hakoranta suka bayyana. Tace “cinye na kara maka kaga wannan malmalar karama ce”

A zuci yace tashin hankali. A daddafe ya kara loma hudu yaji bakinsa kamar ana hura wuta. Da kyar yake iya magana saboda yaji yace mata bari ya nemi yaro cikin kannenta  ya siyo masa batir din rediyo. Dakin ta kalla babu wata rediyo a ciki. Shima ya rasa me zaice mata ne ya dan fita don fankar kamar bata masa komai. Tashi yayi yace ta taya shi ci kafin ya dawo su cinye tare.

Ko kofa bai rufe ba ta dauki nama ta saka a bakinta. Ihu kawai yaji tayi yayi saurin dawowa harda rufe kofar don kada a ji daga ciki ta tara masa mutane.

Ido har ya fara ruwa ta rike baki “Uncle harshena”

Kamar yayi dariya yadda ta tashi tana dire  kafafu “Me ya sami harshen?”

Hawaye yaga ya zubo  sai ta bashi tausayi ” ya fita daga bakina”

Rikota yayi “yana ciki ki nutsu bari na zuba miki juice”

Jug din ya dauko kafin ya zuba a cup ta kafa kai a haka amma ko kadan harshenta bai dena radadi ba.

“Bai dena ba” tace tana wasu sababbin hawayen

“Bude bakin na gani” ya fada a hankali

Tana budewa ya soma kissing dinta sai da yaji a ransa duk nacin yajin nan dolensa ya ragu ko bai tafi ba duka ya kyaleta.

Kokarin hada ido ya rinka yi da ita  kunya tasa ta kasa daga kanta daga kirjinsa “yajin ya tafi ko na kara miki maganin?”1

Ji yayi ta sake rungume shi tana murmushi don bata san da wane idon zata kuma kallonsa ba

“Ya tafi”

“Ni nawa bai tafi ba yaya za’ayi kenan?”

Dagowa tayi kadan “in baka juice?”

“Saboda kirki yayi miki yawa? Wanda naci yama fi naki amma juice din bai korar miki ba sai ni zaki bawa…kuma ma dai nasha ya isheni”

“Yaushe?”

Lebenta ya rinka zanawa da karamin yatsansa “wanda nasha daga nan ya isa saura ayi min maganin yajin nan ko ki fada min me kike nufi da haka…”

yayi mata wannan alamar da hannu

“Ko kuma na fadawa Yaya Harisu irin wannan yajin da kika tura min. Zabi daya” ya mata murmushi ita kuwa  ta hadiyi yawu da kyar. Babu na zabe duk cikinsu”Ke nake jira fa” taji ya fada yana murmushi. Dubawa tayi ta ga babu zabin da yayi mata. Idan ya fadi yajin miyar nan yau mai rabata da Anti Ummukulsum sai Allah. Maganin yaji kuwa ko da wasa bata hango kanta tana wannan abin ba…karshen rashin kunya ma kenan! Zabi na uku kuma da wane bakin zata fada masa ma’anar abin da tayi da hannu. Wai waye ma ya aiketa tayi ne?+

Ya kula da yadda tayi zurfi a tunani  a ransa yace yau fa an hada mata da aiki. Hannunta ya riko

“Kin bani zabi?”

Rufe ido tayi bakin nan an dan turo shi  tana magana cikin sauri kuma can ciki a hankali yadda ba’a ji sosai tace “Dakayibakajiyajinyatafiba”

“Me kika ce?” Don shi ko kalma daya bai tsinta ba.

Sake maimaitawa tayi a hankalin yace bari kawai ya tashi ya fitar da food flask din da aka zuba miyar. Tayi saurin katse shi

“Uncle cewa nayi da kayi baka ji yajin ya tafi ba?”

Ya daga mata gira daya yana son yin dariya

“Da nayi me?”

“Abin mana” ta amsa tana kara turo baki.

“Wane abu nayi da bashi da suna Umm Ruman?” Ya gane me take nufi amma yana jindadin tsokanarta.

Kamar zata yi masa kuka tace “Uncle ka fa gane me nake nufi…ni dai don Allah ka hakura da wannan”

Shima irin muryarta yayi “ni dai don Allah bazan hakura ba”

Wani siririn hawaye ne ya gani ya fara bin kumatunta sa hannun ya goge shi “dadina da mutum shagwaba. To kiyi kukan idan aka tambayeki a ciki sai kice kiss mijinki ya nema kika kasa. Kuma kinsan ana ganin idonki za’a gane kinyi kuka ayi ta tambayarki sai kin fada. Gara ma ki tashi ki tafi babu ruwana”

Dankwalinta ta kwance ta janyo kasansa ta goge fuskarta tana murmushi “kukan wasa ne fa irin wanda mukeyi a makaranta idan bama son bulala”

Jinjina kai yayi “gaskiya ban yarda ba wannan wayo ne. Kin gama yiwa malamai fitinar ‘yan makaranta kuma nima kiyi min”

Dariya tayi “to ba kaine ba…”

Nishadin da yake ji a lokacin ya dade rabonsa da irinsa. Komai na Rumana yana burge shi musamman shagwabarta da kuruciya. Addua yayi a ransa Allah Ya bashi ikon kula da komai nata yadda bazata taba kaucewa hanyar da ta sabawa shari’a ba.

“To naji kinyi min wayo amma ba hakura zanyi ba. Kawai dai kinci bashin da zaki biya nan kusa. Saura na biyu me wannan yake nufi?” Ya sake hada yatsunsa yadda tayi.

Murmushi yaga tanayi harda dan sosa keya. Wannan dabi’ar kuwa yana kyautata zaton a wurinsa ma ta koya domin halinsa ne.

Ita dai yau ta shiga tsaka mai wuya daga wannan sai wannan. Dabara zata yi masa kawai don shima ya hakura

“A film din ‘yan Korea ne fa na gani ko ma’anarsa ban sani ba”

Dan fiddo idanu yayi  “baki san ma’anarsa ba amma kika yi min. Shikenan kila ma zagina kika yi. Zuwa zanyi na tambayi waye yake kunna miki gashi a kaina ya kare”

Gani tayi da gaske ya tashi tsaye bata san lokacin da tace

“I love you “

Wata irin juyowa yayi a hankali yana kallonta. Ita kuwa kamar ta nutse a kasa.

A hankali yace “Me kika ce”

“Uncle I love you yake nufi ba zagi bane” idanunta kamar su yo waje don ta tsorata.

Bata san yadda kalmomi ukun nan suka tsaya masa a rai ba tamkar wanda bai taba jinsu ba.

“Naji ma’anarsu amma da gaske kina yi min son so?”

STORY CONTINUES BELOW

Wannan karon ita ce ta tashi tana neman hanyar guduwa bazata iya jurewa wannan kallon da Uncle Awaisu yake mata ba.

Hannunsa ya ware “Give me a hug kafin ki fita please.”

Tsayawa tayi kanta a kasa tana wasa da hannuwanta.

“Kinga komai na tambaya bakya yi ga yaji kin hadani dashi”

“To ai kunya nake ji”

“Bari nayi miki yadda kika koya min”

Ta bayanta ya tsaya ya rungumeta yadda tayi masa wancan lokacin da zai tafi. Da yake ya fita girma da tsaho sai ya rufeta gabadaya ya mata rada mata a kunne

“Ke special SS dina ce Umm Ruman. Allah Yayi miki albarka”

Amin tace a zuciyarta. A zahiri kuwa tace “Uncle idan na fadi ma’anar SS din zaka taimakeni don Allah”

“Toooohhh wane irin taimako kuma. Ko me kike so fada kawai zakiyi”

Kwanukan abincin ta nuna masa.

“Idan na fita dashi fada za’ayi min kila harda duka ma”

“Maganin wannan kawai ki kwana a nan shikenan”

Dariyar da taga yana yi ce tasa ta gane tsokanarta yake yi. Ta tabbatar idan Mama ta ga wannan miyar ko bata ji a jikinta ba kunnenta zai bada labari don bayan fada idan ta kama shi ta murde bata da hanyar tsira.

“Don Allah kace ya zama assignment irin yadda na baka”

Yayi murmushi “Ya zama Umm Ruman, me SS yake nufi?”

Sai da tayi kamar mai tunani kada yace tayi saurin canka sannan tace “Son So”

Ya girgiza kai “sai hakuri ni Sabuwar Sarauniya nake nufi. Jeki kawai idan kinga zaayi miki fadan ki gudu nan” kan katifar ya koma ya dan kashigida. Hankalin Rumana a take ya tashi. Dama shi take tunanin zai rufa mata asiri gashi ta kula kamar bai damu ba.

Awaisu yana kallonta yana dariya.

“Jeki mana idan an gama ki dawo ina son magana dake”

Mamaki take yi amma kuma tasan dama can idan sunyi laifi baya cikin wanda zaka zo wurinsu ya hana a hukuntaka. Sai dai yayi rarrashi idan anyi hukuncin. Duk wanda ya hana a hukunta to fa sai dai idan ya tabbatar mutum bashi da laifi. Kanta ta dan rangwada gefe muryarta tana dan rawa “na tafi Uncle”

Yana danna waya yana dariya ciki-ciki yace “sai kin dawo SS dina”

Ta durkusa zata dauki tray din “yau tun safe kunnena na dama ke dan zafi gashi Mama ita kunne take murdewa. Uncle kana da panadol idan ta murde zazzabi ya kamani sai ka bani”

Wannan karon da kyar ya iya danne dariyarsa “idan kinje ki bata kunnen hagun tunda shi kalau yake maybe bazaiyi zafin da zaki yi zazzabi ba”1

Anya kuwa Uncle yana ma sonta ko da ba son so ba ta fada a ranta. Har wani dadi yake ji ga Anti Ummukulsum itama duk wasanta da yara ta iya duka.

Hadiyar yawu tayi da kyar ta tuna rankwashin da Antin ta yiwa Iman jiya saboda ta fasa mata plate. Harda sakin ajiyar zuciya ta sake cewa “bye bye Uncle”

“See you SS” yace daga inda yake.

Tafiya ta rinka yi kamar wadda kwai ya fashe mata. Ko dai kawai tayi tuntuben karya ne kwanukan su zube. Amma kuma masu kyau ne kila ma na baban su Iman Antin ta zuba abincin a ciki. Tana wannan tunanin har Awaisu ya kusa zuwa inda take bata kula ba. Tray din ya karba ya dawo da fuskarta daidai tata.

“Kin canka daidai Son So din Uncle Awaisu. Yanzu me kike so ayi da miyar nan kada a taba min mata”

Murmushinta kamar gonar auduga tace “zuciyata kamar ta fito don tsoro daurewa kawai nayi”

STORY CONTINUES BELOW

Hancinta ya ja “matsoraciya…jeki ki samo leda sai a juye miyar a ciki. Idan zan fita zan yar don bana fatan kowa yaci kada a kare a gadon asibiti”

“Yau ma tsautsayi ne amma next time me dadi zanyi”

“Ni kam tsoron girkinki ya shigeni Son So”

Dariya ya bata yadda yayi da fuska. Fita tayi ta tafi kitchen ta sami bakar leda har uku ta diba zata fita Mama ta shigo duba nama da take tafasawa.

“Ina zaki da ledoji haka kike sauri”

Da sauri tace “Uncle ne yace na kai masa”

Sanin halinta na rikicewa idan bata da gaskiya yasa Mama tunanin akwai abin da tayi.

“Zo nan Rumana” ta dan kaurara murya

Haba tuni ta karasa rikicewa “Mama don Allah kiyi hakuri tsautsayi ne.”

“Me kika yi?”

Har ta soma kwalla ta fadawa Mama yajin miyar. Jira take taji ta kama mata kunne sai ji tayi Maman ta sassauta murya alamar tausayawa.

“Jeki ki dauko min miyar”

Awaisu na jiranta yaga ta shigo a firgice. Flask din miyar ta dauka zata fita yace ina zata kai ta fada masa zata kaiwa Mama ne. Tasowa yayi don yasan halin Mamanta

“Muje na bata hakuri don Allah kada ta taba min mata”

“A’a Uncle idan dare yayi ma sai tayi fadan gara ma ayi yanzu kawai”

Tausayi ta bashi sosai amma kuma duk da yana aurenta yana ganin bai dace ya shiga komai tsakaninta da iyayenta ba kafin ta tare. Hannunta ya riko ya dan matsa “bana son kuka idan anyi miki fada gyara ne kinji ko”

“Uhumm” ta iya cewa jiki ba kwari ta fita.

Tana kaiwa Mama ta bude ta dandana da cokali “wai Rumana kamar wadda aka aika kama maye”

Har ta soma dariya ta gimtse ganin kallon da Mama tayi mata. Kabewa ta ga Mama ta dauko a store dama raba musu akayi har su Anti Ummukulsum din. Ta bawa Rumana ta fere ita kuma ta fita ta nemi yaro ya siyo mata alayyahu. Ga yamma bai samo da wuri ba.

Rumana tana kallo Mama ta hada markade na tumatir zalla da albasa nan da nan ta hada ruwan miya bayan ta dafa kabewar. Basu fita ba sai da ta gama nunawa Rumana yadda zata hada miyar taushen wadda ta kusa gama dahuwa da mai yajin sai ga dandanon yayi daidai saboda tasu ta gidan yawa ce kuma bata saka attaruhu ba ko kadan.

Rumana ta kalla Mama taji ta kara sonta.

“Idan girki ya baci dabara akeyi a gyara ba zubarwa ba. Maza basa son almubazzaranci duk da basu da dabarar kitchen irin tamu. Idan kinyi magriba ki zuba masa wannan miyar ki kai. In koma bazai ci tuwon ba sai kizo a dafa masa wani abincin”

“Mama bazaki fadawa Anti ba ko?”

Murmushi tayi mata “babu mai ji in sha Allah. Amma idan kika kara nida ke ne. Ki kiyaye cin abubuwa musamman tsami lokacin girki. Idan baki kware ba kina bukatar dandanawa. Kuma dole harshenki zai iya jin dandanon da ya bambanta da na ainihin abinci saboda tsami ko zaki”

*****

Sallah taje tayi Mama tasa ta dan shafa hoda sannan ta dauki miya ta fita. Addua Mama tayi mata don yanzu kam ta wuce duka ko murde kunne an zama matar aure.

Da taje kofar dakin tayi ta sallama bai amsa ba sai ta murda kofar. Dakin a bude yake amma yana can waje tare da Harisu dawowarsu kenan daga masallaci. Shiga tayi ta ajiye miyar ta dauko wancan plate din zata tafi dashi sai gashi ya dawo. Da murmushi tayi masa sannu da zuwa sannan ta duka gaban flask din.

“Mama ta koya min na sake wata miyar da waccan din. In zuba maka?”

Kirjinsa ya dafe yana tuna azabar da yasha dazu. Yau naga ta kaina.

STORY CONTINUES BELOW

“Ki bar tuwon kinji my sweet SS. Tea zan sha kawai ya isheni”

Bata ji dadi ba ta bude harda tura masa shi kuwa ya matsa yana mai fargabar sake zuba yajin nan a bakinsa don gaskiya bai yarda da girkinta ba.

“Wannan tayi dadi sosai kuma na dandana”

“Bakinki dinnan bana yarda dashi”

Cokali ta dauko ta debi miyar ta saka a baki tana kallonsa “ka gani da gaske wannan babu yaji”

“Sai na dandana nima zan yarda”

Diba ta sake da cokalin ya rike hannunta ya mayar cikin flask ya janyota tsaye

“Bude bakinki na tabbatar kin hadiye”

Tana budewa ya saka nasa. Ya kuma yi mata riko mai wuyar kwacewa. Dama abin da yake so kenan.

Da ya saketa ne yace “yanzu na yarda babu yaji zuba min yunwa har ta cinyeni”

Kasa kallonsa tayi saboda yadda yake mata abubuwan dake sakata jin kunya ta zuba masa abincin ta fita kafin ya ankara.

*****

Gimbi sai kai kawo take a daki duniya tayi mata zafi. Ta kira Ovi yafi sau goma ba’a daga ba.

A nasu bangaren Rita ta kalli Ovi ganin yadda take murmushin mxugunta.

“Sis wai me yake faruwa ne kinki daukar wayar Madam Gimbi”

“Kinsan a da naso ne ki auri mijinta saboda mu sami rabonmu a gidan. Amma Boka yace idan akayi auren nan daya daga cikinmu zata rasa ranta. Shiyasa nake ganin gara muci kudinta kawai muyi gaba. Ko maganin da ta karbo last a wurinsa ruwan datti ne kawai nace ya bata “

“Ba kya tsoron kada ta gane?”

“Zata gane amma sai mun gama da ita. Bani wayar naji me take so. Nasan yanzu haukane kadai batayi ba tunda aiki yake ta baci ga aure yayi”

Kafin wayar tayi Gimbi ta dauka rai a bace “Ovi kina kokarin cuta ta nr ko me. Yaya zanyi ta sakin kudi babu biyan bukata”

“Kiyi hakuri Madam Boka yace akwai inda aka sami kuskure wurin aikin da kikayi da maganin”

Da a gabanta take yadda ranta ke kuna kila sai ta kai mata shaka “sai kace wata sabon shiga zaku ce matsalar amfani da magani aka samu? Sau daya aka samu hakan da Maamu tana asibiti”

Ovi jin zata cika mata kunne da fada tace “haba ni nasan akwai inda aka kuskure. To boka yace ko waye silar bata aikin a wannan lokacin sune suke bibiyarki suka hanaki sakat”

Gimbi tayi shiru tana son tuna sunan wannan shegiyar likitar da ta hanata shafawa Maamu magani. Kwafa tayi taja tsaki “akwai wata likita da nake zargi don ta saka min ido lokacin. Ki fadawa Boka yayu min maganinta. A rabata da abin da tafi so duk duniya yadda ta taimaka wurin nesantani da mijina. Zan turo miki 200k yanzu ayi komai a gama da wuri. Ita kuma Rumana idan Awaisu ya dawo garin nan da igiyar aurenta Ovi zan baku mamaki. Bani da kirki ke kin sani. Shi kanshi ba don wannan azababben son da na rasa dalilinsa ba da bai isa ya sha daga hannuna ba”

Bayan sun gama waya Ovi ta cewa Rita ya zama dole wannan karon a biyawa Gimbi bukata saboda kada ta dena yarda dasu. A cikin daren babu fargaba bare tsoro suka tafi wurin Boka. Kayan tsafinsa ya dauko ya rinka surkulle wanda Ovi da Rita duj yawan zuwansu kullum tsoronsa suke yi.

Wata irin kibiya ya soka tun daga kai har tsakiyar wani mutum mutumi ya chake shi a jikin bango.

*****

Cikin barci Dr. Yana taji jikinta yana zafi kamar an hura wuta. Lokacin shadayan dare. tayi aiki ta gaji ga girkin da tayiwa Hajiya surukarta bayan ta dawo. Mujahid ta soma kira yana falo bai ji ba. Ido a rufe har lokacin ta ga Gimbi ta biyota da wuka ta soma kuka tana rokonta tayi hakuri. Shure shure take ta yi a kan gadon har ta fado ta bige da bedside drawer amma bata farka ba. Karar faduwar abu Mujahid yaji ya shigo ya ganta a wannan yanayin.

Duk yadda zaiyi taki bude ido amma ga hawaye yana ta zubowa. Fita yayi a guje ya kira Hajiya Allah Yasa idonta biyu.

Suna zuwa suka ji tana cewa “Gimbi! Gimbi!! Gimbi kada ki kasheni!!!!”

Hajiya ta daga kanta ta dora a cinyarta tana kuka don duk irin zamansu ba wai ta tsaneta bane ko don zumunci. “Yana bude idonki waye Gimbi?”

Jikinta  ne ya saki ta dena motsi sai ga jini ya biyo ta karkashinta yana zuba. Mujahid ya tashi ya fita neman key din mota ita kuma Hajiya tana duba jinin ta dafe kirji.

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun…Yana bari kika yi?”

Sai a lokacin Dr. Yana ta bude ido da kyar maganarta bata fita sosai saboda zafin ciwo “Hajiya kiyi hakuri niyata sai ya cika wata uku zanyi muku kyakkyawan albishir ashe ba me zama bane”

Wani abu ne ya tsaya mata a makwogaro tana tuna yadda cikin mafarki Gimbi kw fada mata sai ta rabata da abin da tafi so. Kuka sosai suke yi ita da Hajiya. Da taimakonta ta tashi ta dan gyara jiki a daren suka tafi asibiti. Sunyi kusan awa biyu sannan aka shawo kan matsalar don jini take zubarwa ba da wasa ba. Hajiya ce take yi mata komai cike da tausayawa tana jira ta sami kwarin jiki ta fada mata wacece ko waye  GimbiHajiyar Mujahid yadda taga rana haka taga dare wannan asabar din.  Tunani ne ya addabeta na son sanin alakar Yana da Gimbi da kuma barin da tayi daidai lokacin da take ambaton wannan sunan.+

Mujahid din ma a asibitin ya kwana. Bayan sallar asuba da ya shiga dakin Hajiya ta kasa hakuri ta tambayeshi wace ce Gimbi.

Dafe goshinsa da yake masa ciwo saboda rashin bacci da fargaba yayi “Hajiya ki bari ta tashi zata yi miki bayani sosai. Ni kaina abin da na sani game da matar kadan ne”

Hajiya tace “Allah Ya kaimu ta tashin. Wallahi ko wace ce bata isa ta kashe min jika ta kwana lafiya ba. Idan tana takama da hatsabibanci gidansa tazo. Ni har akwai wanda ya isa ya taba jinina ina raye ban dau mataki ba”

Tsoro ne ya bayyana akan fuskar Mujahid “Hajiya tun yaushe kika rufe wannan shafin don Allah akan barin nan kada ki koma abin da ya shude. Tsautsayi ne kawai da kaddara”

Tabe baki tayi “sai kuma kayi. Ka kira ‘yan uwanka ka sanar dasu tunda gari ya waye su kawo abinci kafin ta tashi”.

******

Karfe goma na safe ta wuce Maman Rumana ta shiga kitchen zata dora abincin rana saboda yara da wuri duk me girki take gamawa. Tray din da ta hada na breakfast din Awaisu ta gani nan inda ta barshi ba’a taba ba. Ranta kuwa yayi mugun baci ta rinka kwalawa Rumana kira. Jin bata amsa ba yasa ta zuwa dakin ‘yan matan. A kwance ta sameta ta rufa ido a rufe. Kanta tayi ta daka mata duka a baya wanda yasa ta tashi a firgice. Mama ta harareta

“Tun daren jiya ban fada miki da safe kije ki dauki abincin Kawunku Awaisu ba? Mutum yazo kin masa horon yunwa tunda bai sami abin arziki da zai iya ci da wuri ba sai bayan magariba. Sannan da safen ma shadaya na neman yi ko karyawa baiyi ba”

Idanun Rumanan dama a kumbure suke sai kawai ta soma kuka “Mama bani da lafiya ne”

Bata gaskata ba tace “wa kika fadawa a gidan nan?”

Tana share ido tace “kafata ce kuma su Hafiza duka basa dakin shiyasa ban fada ba”

Jiki a sanyaye Maman ta zauna tana shafa mata baya “sannu bari na dora ruwa sai a gasa kafar kiyi wanka. Allah Ya sauwake.”

Tana fita ta kira Sajid shima kanin Rumana ne na wurin Anti Amarya ta bashi tray din tace ya kaiwa Awaisu ya fada masa bata da lafiya shiyasa baa kawo da wuri ba.

Karo na biyar kenan da yake kiran wayarta bata dauka ya fara tunanin ko abin da yayi mata jiya ne yasa take gudunsa. Murmushi yayi yana tunanin idan ta tare akwai rigima kenan.

Sallamar Sajid ce ta katse masa tunanin yana zaune sanye da dogon wando brown da farar shirt. Ko yanayin aiki ne da baya samun isasshen hutu yasa bashi da wani jiki wannan sai Harisu.

Gaishe shi Sajid yayi kafin ya tambayeshi ina Rumana ya fada masa bata da lafiya. Hankalinsa ne ya tashi ya matso kusa dashi “me ya sameta? Tana ina?”

Sajid ya dan kada kai “ina jin ciwon kafar nan ne ya tashi. Uncle idan tana yi fa bata iya tafiya ranar ko bandaki zata sai an riketa”

Awaisu ya yiwa Sajid kallon rashin fahimta. Wane irin ciwo ne wannan yace a ransa. Tare suka fito sai dai kafin ya shiga kofar da zata sada shi da ainihin gidan ya dan tsaya. Kansa ya dan shafa ya fara tunani. Yana mamakin kansa da yadda yake jin nauyin iyayen Rumana yanzu. A da can Mamanta abokiyar shawararsa sannan bashi da na biyun Harisu. Amma yanzu darajar aure baya iya sakin jikinsa akan abu indai ya shafeta musamman da yake a cikin gidansu ne. Ya zama dole ginin da ya soma ya banzatar ya cigaba da yinsa saboda babu yadda za’ayi idan ta tare duk lokacin da zasu zo garin ya tare musu a gida shi ba yaro ba yana rabe-rabe idan zai ga matarsa.

STORY CONTINUES BELOW

Idan ya shiga tabbas akwai yiwuwar haduwa da Mama sannan idan bai je ba sai su iya tunanin bai damu da ita ba. Uwa uba yadda ya matsu ya sanyata a idonsa bazai barshi ba. Shiga cikin gidan kawai yayi ya gaisa da sauran matan gidan da ya gani suna fitowa daga kofar dakinsu Rumana.

Har yaje bakin kofar sai kuwa ya jiyo muryar su Baaba da mama. Maamu wadda bai san itama tana ciki  ba yaji tana cewa dasu Baaba

“Yarinyar nan duk wata haka muke fargaba idan ta kusa a gidan Kawunta. Saboda ciwo dama indai a gida ta fara ranar bata zuwa makaranta. Da yake babu wanda ya damu da lamarinmu lokacin haka zata ci ciwonta na kwana biyu sannan ta ware. Idan munyi sa’a kuma kwana daya take ta tashi “

Mama yaji tace “sai dawowarta muka san tana yi amma idan anyi mata allura tana dan samun sauki”

“Mata sai hakuri wai kafin ayi maganar ciki da haihuwa ma fa kenan. An fadawa mijinta?” Cewar Baaba.

“Ai kuwa a tura yazo maza-maza ya kaita asibiti idan tayi wanka. Sannu kinji Rumanan Maamu” Maamu ta fada tana tashi ita da Baaba.

Awaisu na jinsu ya dan ja baya don bazai shiga Mama tana ciki ba. Da suka fito gaishe su yayi ya tambayi mai jikin a ransa yana cewa mai yasa ta zauna a dakin da bazai sake ba. Baaba tace ya shiga tana ciki yayi saurin sake yin baya yana cewa zai dawo ya dubata. Murmushi tayi tace masa yaje dakinta ya jirata tana zuwa zasuyi magana ita kuma ta koma dakin.

“Rumana zaki iya tashi?”

Mama tace “tun dazu nima nace ta tashi ta kasa kafar taki daukarta”

Baaba ta fita ta kira Anti Amarya da kanta tace ta kama Rumana ta mayar da ita dakin ita Baaban saboda a nan hayaniya bazata bari ta huta ba. Suna fita ta mayar da hankalinta ga Mama wadda ta kasa fahimtar dalilin Baaba.

“Awaisu na gani a kofar dakin amma nauyi ya hana shi shigowa” tayi murmushi ganin Mama ta dan sunkuyar da kai itama sannan ta cigaba da magana

“Dama ina so nayi miki godiya da baki tayarwa mijinki hankali akan auren nan ba. Nasan dole zaki ji babu dadi kiga an hadata da mutum kamar Awaisu mai shekaru kusan arba’in. Amma kamar yadda na riga nasan kin sani kowane bawa yana da kaddarar da Allah Ya rubuta masa”

Mama tace haka ne. Baaba ta cigaba da cewa  “addua’armu bata wuce Allah Ya basu zaman lafiya da juna. Mu namu auren ma ko shekarunta bamu kai ba. Nasan wacece Rumana a tarbiya shiyasa banji komai ba na bada goyon baya ga bukatar Maamu. Abu na gaba da nake son jan hankalinki shine ko da nan gaba Awaisu ya nemi karin aure saboda yayi alkawarin rabuwa da Gimbi don Allah kada ki tada hankali ganin tana da kuruciya. Bai zo min da zancen ba amma kinsan yau da gobe sai Allah. Ko ba komai ina ganin tayi kankanta da daukar dawainiyar miji da yaransa wanda suka tashi kamar kannenta ita kadai.”

Mama da taji yar kwalla ta tarar mata saboda tausayin Rumana tace “Baaba kada ki damu in sha Allahu tsakanina da ita sai karfafa gwiwa da fatan alkhairi. Kuma ni a nawa ganin gara yayi aure idan yana da ra’ayi saboda nasan a yanzu kam wani lokacin sai yaji kamar ya zaneta” tayi dariya.

Baaba ma dariyar tayi “Yo wannan shirmen nata ai shi ne zai kara sawa ya sota. Ku yaran yanzu baku san komai game da soyayya ba. Misali yanzu da bance ta tafi dakina ba haka zaki barta a nan shi da yazo saboda ita haka zai juya gobe ya tafi. Dan irin wannan lokutan kamata yayi a barsu tare tunda matarsa ce. A haka zasu saba tunda ba wani lokaci sosai tarewa zatayi. Idan akayi tariya tana tsoronsa ko ta kasa masa kallon miji kinga babu kanta.”

Mama dai kunya taji sosai amma tasan halin Baaba. Ko a gaban waye duk mai girki cikinsu idan Harisu ya dawo ta rinka cewa bata son gulma a tashi a bi miji. Tun suna jin kunya har ya zama indai ya dawo ko tana wurin sai su tashi.

******

STORY CONTINUES BELOW

Awaisu yana zaune jiran Baaba amma hankalinsa gabadaya yana wurin Rumana da tunanin wane irin ciwo ne yake damunta haka.

Muryar Rumana yaji tana cewa bazata iya cigaba da tafiya ba Anti Amarya na cewa tayi hakuri saura kadan. Tasowa yayi ya fito Antin na ganinsa tayi murmushi “wato Baaba turo maka matarka tayi kayi jinya. To ni nayi nan ku karasa”

Hannun Rumana ta mika masa ya riketa ita kuwa ta juya tana tsokanarsa. Ko gama tafiya batayi ba Awaisu ya dauki Rumana tana ta mutsu-mutsu ya shige dakin da ita. Kan gado ya kwantar da ita fuskarta da sauran hawayen da take ta yi saboda ciwo.

Tausayinta yakeji sosai ya zauna a gefen gadon ya rike hannunta na dama.

“Me ya sami Son So dina?”

Ga ciwo kafafunta kamar ana sarawa ga kunyar an kawota dakin wurinsa ta rufe ido kawai. Matsawa ya sake yi kusa da ita kamar zai rungumeta kamshin turarensa ya mamaye wurin shi kadai take shaka.

“Naji Maamu tace duk wata kike yi. Period pain ne yake kama miki kafa?”

Wata irin kunya taji duk da ciwon da take ji ta soma sunne kai. Shi kuwa murmushi yayi yana tsareta da ido gashi yayi kusa da ita sosai

“Ashe dai ba kwaila na aura ba. Nana da shekara zaki shaifa mana babyn So”

Kunya ta kamata amma dayake ba wuya tayi dariya saboda kalmar kwaila da yace sai gashi tana yi a hankali amma taki kallonsa. Yaji dadi ganin ta dan sake dama tsokanarta yakeyi don ta saki ranta ta dena hawayen.

“Kada ki damu kin kusa denawa in sha Allah.”

Dan ware ido tayi “da gaske Uncle?”

Shan kunu yayi  “nima sunana Son So kema kuma sunanki kenan”

A hankali ta dago ta kalle shi amma bata yarda sun hada ido ba. Wani iri take ji a ranta game da Uncle Awaisu musamman idan yana mata irin wannan abin kamar yaro daidai da ita.

“Mace da namiji duk suna daya?”

“Mata da miji dai zaki ce”

Fuskarta ya gani ta chanja alamun tana jin jiki ya gyara zamansa sannan ya dago kafafunta ya dora a cinyarsa. Janyewa take son yi ya rikesu

“Ki bari idan ba kina so muyi rigima ba. Matsa miki zanyi ko zaki ji saukin ciwon.”

Dogon wandon bacci ne a jikinta rigar kuwa baya iya gani saboda hijab da tasa wanda ya sauko har  kusan cinyarta. Tausa ya soma yi mata a hankali yana matsa kafafun tana lumshe idanu.

“Tun yaushe kika fara ciwon nan?”

Bude ido tayi jin tambayar tasa sai kuma ta sake rufewa. Kamar bata son magana saboda kunyar magana irin wannan dashi tace da ta koma Abuja.

“Kenan duk zamanku a can kina wannan ciwon kafar kowane wata?”

Kanta ta daga tace eh. Yanayinsa gabadaya ya sauya zuwa takaicin irin zaman da yayi dasu a gidansa. Gimbi ya tuna a matsayin wadda ta zame masa shamaki ga sauke hakkokin da suke kansa yaji ya kara tsanar wannan mummunar dabi’a da ta fadawa a dalilin son zuciya.

Muryarsa a hankali cikin nutsuwa take fita yace “Son So bani labarin yadda kike managing a irin wannan lokacin”

Ya tabo abin da bata son tunawa ko kadan saboda yana cikin abubuwan da suka saka mata jin haushinsa a lokacin. Ta kwashi kusan minti uku yana kallonta kafin ta fara fada masa yadda suke kwana kuka ita da Maamu domin idan ta gaji da rarrashinta itama kukan take yi. Babu zancen magani sai dai ta gasa mata kafar tunda Allah Yasa kowane daki na gidan akwai heater ta bandaki.

Zuciyarsa ta karye sosai da tausayinsu. Da ace zai iya maida hannun agogo baya da ya mayar  ya gyara abubuwan da suka gabata. Godiyarsa daya ga Allah daga ita har Maamu duk suna raye da baisan yadda zaiyi ba. A lokacin kuka take yi sosai da ta tuna yadda lokutan al’adarta suka zama lokutan ciwo da kazanta a gareta.

STORY CONTINUES BELOW

“Uncle Awaisu yana so kiyi hakuri da dukkan abubuwan da suka wuce kinji. Sannan mijinki yayi miki alkawarin sauke duk wani hakkinki harda kari. Nasan kinsan komai game da abin da Gimbi tayi min amma duk da haka ba uzuri bane a ganina”

Hawayen da yake bin kumatunta yasa yatsansa yana gogewa a hankali. Akan abu da bai kai ya kawo ba Gimbi ta tarwatsa musu farincikin rayuwa. Tsoron kada uwarmiji ta koreta ya kaita ga aikata manya manyan laifuka da sunan soyayya.

Cigaba yayi ta matsa mata yana ja mata yatsun karfar daga ita har shi suna jin wani yanayi. Suna haka Hafiza tayi sallama ta shigo da kayan Rumana a hannu. Wai itama ‘yan mata harda rufe ido ganin Awaisu yana yiwa Rumanan tausa a kafa. Itama kunyar ce ta kamata tana ta kokarin dauke kafarta sai dai ya rike sosai gashi wani sabon ciwo da yafi na dazu take ji.

Dariya kunyar tasu ta bashi yace da Hafiza kayan waye ta kawo

“Maamu tace tayi wanka ka kaita asibiti ayi mata allura”

Rumana ta kwabe fuska “ni wallahi bana son allurar”

Hafiza dai ficewa tayi duk kunya ta isheta tana dariya. Ba jimawa ta dawo da ruwan zafi a bokiti ta shigar dashi bandakin Baaba ta sake fita.

Awaisu ya tashi ya miko mata hannu “taso kiyi wanka”

“Ni bazani asibitin ba. Allurar kara rike min kafa take yi”

Yayi murmushi “naji amma dai ya kamata kiyi wanka kafin na fara toshe hanci matata bata wanka”

Daga hijab din tayi batare da ta sani ba ta fara sansana jikinta. Shi kuwa sai dariya. Da taimakonsa ta tashi ta shiga toilet din. Sai da ta rufe kofar yaji tace

“Uncle amma zaka fita kafin na gama ko”

“Sai kin kirani Son So” ya bata amsa yana daga kayan da Hafiza ta ajiye. Riga da wrapper skirt ne na atamfa sai underwears da bodyspray. Wata leda ya gani ta pad ya tuna labarin da ta bashi dazu. In sha Allah kwalaye zai rinka ajiye mata a gida don kada ta taba nema babu.

“Uncle pleaseeeee”

“Son So pleaseeee” ya kaikwayeta.

Gaskiya bata so ta fito yana nan da ta sani ta kwashe kayanta ta shiga dasu.

Kamar mai rada yaji tace “Son So”

Shiru yayi ta sake fada yana jindadi sai a na ukun yace mata ya tafi.

Ta dade tana gasa kafafunta sannan tayi wanka ta fito kai tsaye daure da tawul.

Ganinsa tayi a zaune yana juya bra dinta a hannu yana dagowa suka hada ido yace “wannan ma acuci ce ko size din kenan idan na koma zan hada lefe. Nasan yanzu ance  mata komai kari kuke yi”

Mantawa tayi da ciwon kafar ta nufeshi gadan-gadan ta mika hannu zata karba saboda kunyar da taji da sauri shi kuma ya daga hannun sama yana kare mata kallo. Kula tayi da abin da yake yi ta kwasa a guje ta koma bandakin tana cewa

“Yau naga boni”

“Za dai ki ganshi yarinya har me akayi kike gudu tun yanzu”

Yadda ya saba jin farinciki idan tana wasu abubuwan haka yaji yanzu musamman idan ya tuna dan jikinta da ya gani. Tashi yayi don kada ta kasa fitowa ya dan jingina da kofar ta waje

“Fito ki shirya kinji zan jiraki a dakin Maamu”

Sai da ta dan kara lokaci ta leko don ta tabbatar ya tafi. A gaggauce ta shirya saboda kada ya dawo ta koma gadon ta kwanta tana zumbura baki yau gabadaya Uncle ya gama da ita.

*****

Hawayen da Dr. Yana take yi sune suka tabbatarwa da Hajiya cewa ta farka. Matsowa tayi kusa da ita ta dafa kanta.

“Sannun kinji Yana. Allah zai baki wani. Mutanen Maiduguri na hanya kada su iso kina wannan kukan ki karyawa kanwata zuciya”

STORY CONTINUES BELOW

Yana ta daga hannunta mara kwari ta share ido. Mafarkin da tayi da Gimbi tar take tuna shi kamar yanzu yake faruwa.

Mujahid na shigowa ta sake saka wani sabon kukan mai cin rai. Hajiya fita tayi ta barsu yana ta rarrashinta. Bayan kusan rabin awa Hajiya ta koma dauko  purse dinta da ta saka goro a ciki taji suna magana. Kara kunne tayi  sosai yadda zata ji da kyau.

“Shiyasa nace ki dena shiga sabgar mutane a asibitin nan”

“Yanzu sai na ga abu da idanu na na dauke kai don bai shafeni ko wani nawa ba?” Ta fada tana kuka

Rarrashinta ya koma yi “ba haka nake nufi ba amma kuma ba kowa ne zaki shiga lamarinsa ba haka kawai ya rabu dake. Wannan Gombo din din take ko Gimbo da bakinki kika ce an fada miki tana asiri. Infact da idonki kika ganta…”

“Da ban taimaka ba Allah kadai Yasan me tayi niyar yiwa tsohuwar nan. Ban taba nadamar taimakawa mutane ba domin kawar da kai da mukeyi idan abu bai shafemu ba shine babban rashin hadin kan da mukeyi a matsayin musulmi. Ya Mujahid idan har Allah Ya bani iko to duk inda naga rashin gaskiya zanyi kokarin taimakawa.”

Girgiza kai yayi “ban hanaki ba Yana amma ba kowane abu bane zaki shiga. Wanda yafi karfinki sai ki nemi mutanen da ya dace. Yanzu dubi yadda matar nan tayi mana sanadin zubewar cikin nan. Wallahi bazan yafe mata ba “

Yana ta dafa hannunsa “kayi hakuri in sha Allah zamu sami wani amma nima wallahi wannan matar sai na nuna mata kurenta”

Hajiya ce ta bude kofar dakin ta shigo tana kallonsu zuciyarta a hasale.

“Cikinku waye zaiyi min bayanin Gombo dinnan yadda zan fahimta”

Mujahid ya matso kusa da ita ta daga masa hannu.

“Wallahi kada ma ka soma cewa nayi hakuri don bazanyi ba. Yana ke nake saurare don wannan mijin naki babu abin da zai iya”

Ba don taso ba Yana ta bata labarin da ta samu a wurin Rumana da wanda idonta ya gani. Hajiya ta dan cije lebenta  na kasa

“Sai tasan ta taba gudan jinin Hajiya Fanta. Hatsabibanci gidansa tazo da kafarta”

Yana da Mujahid duka a tsorace suka fara rokonta tayi hakuri kada tayi abinda tayi niyya. Bata sauraresu ba ta dauki jakarta ta fita.

Hajiya Fanta mutuniyar Damboa ce a jihar Borno. Tun tana karama take fama da lalurar aljanu wanda da kyar aka rabata dasu. Su suka saka mata fitina, rashin hakuri da zafin nama wurin aiwatar da kowane irin aiki. Bayan tashon lokaci da aka diba ana nema mata magani an samu sun fita sai wata guda daya da ta nace wai bada magani take so Fanta tayi. A hankali ta zama wata karamar yar bori inda daga kallo daya zata iya fadin ciwon dake jikin mutum kuma ta fadi magunguna na gargajiya da zaayi amfani dasu a dace. Har tayi aure ta gama haihuwarta kowa yasanta da sana’arta. Wani babban malami ne su Mujahid da yan uwansa mata suka nema da kyar ya samu Fanta ta amince ta dena bada magani domin lokuta da dama abin yafi kama da wani nau’i na sihiri. Magani da wasu lakani babu wanda bata bayarwa. An rabata da aljanar da kyar amma kafin ta tafi ta nanata cewa duk sanda take neman taimakonta sunanta kawai zata kira tayi alkawarin share mata hawaye. Malamin nan ya nuna mata hanya ce kawai take nema ta dawo saboda haka duk runtsi duk wuya ta kai kukanta ga Allah shi kadai. Labarin Gimbi da abin da tayiwa jikanta da ko numfashi bai fara ba tayi sanadin zubar dashi ya tuna mata da cewa shekarun baya karyar mutum ya kara da ita. Aljanun ma bata shakkarsu balle wata Gimbi.

*****

Baaba da kanta taje ta koro Rumana tace suje asibiti. Ba yanzu ake ji ba sai dare yayi ne abin ke tsananta ta kwana tana kuka mai jinyarta ko rintsawa bazai sami yi ba.

Mayafi ta yafa fuskarta duk tayi fayau dama haka take yi tana dafa bango ta fito ta shiga motar. Baya ya bude mata yace ta kwanta sosai tace gaba zata zauna amma ya kunna mata AC zafi take ji.

Kujerar gaban ya kwantar mata yadda zata fi jindadin zaman ya kaita wani health centre dake kusa dasu. Sunyi sa’a da likita ya rubuta mata allura irin wadda ake yi mata tun dawowarta fika. Jikinta a sanyaye suka bi bayan nurse din da zatayi mata. Allurar ba karamin zafi gareta ba har wani dan tsayawa akeyi ruwanta ya shiga a hankali.

Nurse din tana  tsartar da ruwan allurar daga sirinji tana dan kada shi Rumana ta zuba mata ido wanda yake cike da kwalla . Awaisu ya kalleta duk ta bashi tausayi yace “kina so na rikeki?”

“A’a ka fita” sai ga hawayen ya sauko.

Nurse din tayi dariya “bazanyi miki da zafi ba. Hannuna kamar auduga yake wurin allura”

Tashi yayi zai fitan don yasan kila kunya take ji ayi mata a gabansa. Allurar ta sake kallo yana daf da fita yaji ta cakumo shi a gigici.

“Don Allah Uncle ka rikeni wallahi da zafi allurar”

Murmushi yayi “Suna na Uncle?”

Ta girgiza kai da sauri “Son So”

Nurse din ya kalla shima ba karamin tsanar allura yayi ba don ko ciwo yake aka rubuta allura baya zuwa idan ba yaji jiki ba.

“Yanzu dole sai anyi mata?”

Wani dadi ya kama Rumana tace “ina fa ba dole bane. Lokacin da ba’ayi min kwana daya nake warkewa”

Ya kama hannunta har lokacin nurse din yake kallo “to kinji ki bata magani kawai mu tafi”

Rumana sai gyada kai take yi har wani kuzari yana kara shigarta “bari na jira a mota ko Uncle idan ta baka sai mu tafi. Ni kaga bani da lafiya bazanyi ta tsayawa ba”

Shi kuwa yace ta tafi nurse din ta kwashe da dariyar yadda suke yi duk su biyun sannan tace idan har Rumana tana son lafiya ta bari ayi mata allurar saboda kada nan gaba kafarta ta sami matsala. Awaisu na jin haka ya janyota yace ta tsaya zai riketa.

Haba tuni hankalinta ya tashi ta soma kuka. Rungumeta yayi a hankali ya daga hijab dinta ya kuma janye rigarta kadan. Nurse din na dukawa da allurar  zata dan janye zanin kasa ya runtse nasa idon kamar shi za’ayiwa. Kankame shi da Rumana ta sake sosai tana kuka a hankali ya gane an tsira allurar shima ya kuma riketa sosai yana cewa tayi hakuri.

Nurse ta gama ta dago kai tana kallonsu. Shi da Rumana sai ka rasa wa akayiwa allurar idan ka kalli fuskokinsu. Kasa hakuri tayi ta tambayeshi yaya suke da Rumana.

Bai saketa ba har lokacin tana kuka yace  “matata ce Son So dina”

“Kun burgeni wallahi. Rumana zaki zama kawata daga yau ko?”

Zumbura baki tayi “bayan allurarki da zafi sosai”

“Tuba nake amarya bari na danna miki wurin kada ya tashi”

Kafin ta kai hannu Awaisu yasa hannunsa a wurin yana dannawa a hankali yana hura daidai kunnenta. Daga shi har Rumana babu mai magana Nurse din ta rike baki kafin ta fita ta rufe kofar tana cewa wannan sai ku makanta mutane ai. Kira taji daga bayanta

“Sister A’i maman hudu dagq ina haka?”

Daga hannu tayi ta rage murya sosai “hmmm soyayya na gani zata tayar min da tsohon tsumi”

Tafawa sukayi suna dariya ganin Awaisu ya fito rike da Rumana tana dingisa kafaKarkashin wata katuwar bishiyar umbrella fruit dake gaban gidan nasu Awaisu yayi parking din motarsa. Da yake babba ce sai ta yiwa wurin inuwa sosai don suna yawan zaman hira a wurin. Kuma yayi sa’a babu hayaniya sosai saboda yawancin mutane sun tafi cin kasuwar dake kusa dasu mai ci duk asabar. Kallon Rumana yayi tayi bacci sai layin hawaye da yake kwance a kyakkyawar fuskarta. Tunawa yayi da irin kukan da ta rinka yi masa a hanya wai ya bari anyi mata allura. Bata san ko a jikinsa akayi iyakar abinda zaiyi kenan ba saboda yadda shima yaki jinin allurar. Tana kukan yana rarrashi yaji shiru ashe bacci ne ya dauketa.

Yanzu da suka dawo yayi parking kallonta kawai yake yi yana kara jin sonta har cikin ransa. Bayan kamar minti goma aka soma kiran sallar azahar. Tunani yake me ya kamata yayi. Da gani tana jindadin baccin musamman da akace jiya kwana tayi tana fama da ciwo. Fita yayi ya zagaya bayan motar tasa hadaddiyar jeep navy blue ya dauko abin sallah. Tagar bangaren da take ya sauke kadan ya zira abin sallar ta ciki sannan ya mayar ya rufe. Sai yayi mata kamar labule babu yadda za’ayi rana ta dameta ko wani ya ganta idan ba gaban motar ya zagayo ba wanda kuma babu hanya don ta kusa taba bango. Sai da ya daidaita mata AC din ya kuma kwantar mata da kujera sannan ya fito yayi sa’ar ganin Sajid zai shiga gida. Kiransa yayi yace ya zauna a bayan motar ya jira shi ya dawo.

“Idan na dawo na samu ka tashi yayarka ni da kai ne. Kaga bata da lafiya ka barta tayi bacci”

Sajid ya dago kai a dan rikice jin yace zai gamu dashi “Uncle idan ta farka da kanta fa”

Hannu Awaisu ya dora a lebensa “shhhh da wannan surutun zaka tasar min ita.”

“Ita kadai ce taka Uncle mu kuma fa?” Sajid ya  fada fuskarsa na nuna rashin jindadi.

Murmushi Awaisu yayi yasan halin Sajid da tambaya idan ya biye masa zai iya makara sallah. Robar ribena daya ya dauko cikin wanda ya siyowa Rumana ya bashi ya fita daga motar yana nanata masa ya kula da mukullin da ya bari a jiki saboda AC da bai kashe ba.

Har ya dawo daga masallacin bata farka ba sai ma gyara kwanciya da ta kara yi. Gaba ya koma ya zauna ya cewa Sajid ya fita ya tafi gida. Yaro yayi kwal da idanu zaiyi kuka.

“Don Allah nima ka barni in sha AC bazanyi surutu ba”

Girgiza kai Awaisu yayi yana dariya ya daukowa kansa karfen kafa. Yadda yake da surutu yasan ko hannun Rumana ya taba sai ya kai rahoto cikin gidan. Wayarsa ya dauko kawai yana karanta labarai ba jimawa shima Sajid din ya bingere a bayan motar yana bacci. Sai bayan fiye da rabin awa ya farka ya fita wai zaiyi fitsari. Buga kofar da yayi da karfi ne ya tashi Rumana ta farka ta mike hannu tana mika ta kusa hadawa da fuskar Awaisu.

*****

Sajid na shiga tsakar gida ya hau bada labarin Uncle Awaisu yasa shi gadin Rumana yanzu ma tana motarsa tana bacci. Mama kunya ta rufeta ita kuwa Anti Amarya kan Sajid din ta make tana cewa bata son gulma.

“Uban surutu idan na kuma ji kana fadin abun da ba’a tambayeka ba sai na dirje maka baki”

Dakinsu ya tafi yana hawaye rai a bace an doke.

*****

Da sauri Rumana ta tashi tana waige gabadaya kanta ya juye ta kasa gane ina take. Awaisu kuwa hannun da ta miko gaban fuskarsa da tana mika ya damke.

“Kwashe min fuska zakiyi Son So?”

Rufe ido tayi a kunyace tana cigaba da waige ta gano ina suke “yi hakuri kaina ne ya juye”

“Har kinsa na fara jin tausayin kaina” yayi maganar yana son hada ido da ita. Kallonsa tayi ta tambayeshi meyasa yake tausayin kan nasa suka hada ido bata ankara ba. Sassauta murya yayi yana mata murmushi “saboda haka zaki rinka bugeni akan gado idan kina bacci”

STORY CONTINUES BELOW

Zaro idanu tayi “La ilaha illallahu….”

“Muhammadur rasulullah SAW” ya karashe mata.

“Ni dai babu ruwana wallahi” ta turo baki a rude

“Ni kuma da nawa saboda haka kema da naki. Wai me kike zaton ina nufi har kin wani tsorata?”

Baki na rawa tace babu komai. Dariya yayi yana cewa tayi ta gama tsoron da firgicewar zata dena ne.

Wata irin yunwa taji ta kamata don tun jiya rabonta da abinci. Cikin ta dafe ta kama kofar zata bude taji ta a rufe .

“Uncle don Allah zan shiga gida yunwa nake ji”

Wani irin kallon yayi mata ta kuma gane dalilinsa taki yin abin da yake so saboda kunya ta sake cewa tana jin yunwa.

“Babu inda zaki idan baki gyara sunan da kika kirani ba”

A hankali tace “ssssooonnn” don shi dai banda harafin *s* bai iya gane komai ba sai sautin da bakinta ya fitar. Matso da kunnensa yayi daidai bakinta kamshin turarensa ya kara shiga hancinta.

“Banji me kika ce ba fa”

Dagewa tayi ta saita bakinta a kunnensa da karfi tace ” *SON SO* “

Da sauri ya daga ya hau dukan kunnen don ji yake kamar ya zama kurma. Rumana ta rinka kyalkyala dariya allurar da aka mata tasa ta manta da ciwon kafa saboda saukin da ta samu.

Harara ya sakar mata amma fuskarsa ta fallasa murmushin da yake yi “so kike yi na kurmance zaki kashe min dodon kunne. Zo ki fita kafin ki sa na rasa na ji”

Dadi taji yadda yake yi kuma yace ta fita. Bude kofar tayi ta sauka sannan ta juyo tana kallonsa

“Uncle na iya maganar kurame fa sai na koya maka”

Hannu ya miko kamar zai kamata yace “ki kiyayi zuwa hannuna?”

Tayi saurin rufewa ta fara tafiya. Bata yi nisa ba ta sake juyawa

“Uncle ka gani” ta fada da dan karfi.

Lokacin abin sallar yake cirewa daga window din. Yana dago kansa yaga tayi masa wannan alamar da hannunta na dama fuskarta dauke da murmushi. Bata san yadda yaji dadin hakan ba har kasan zuciyarsa. A hankali yace “Allah Yasa kiyi min Son So tsakani da Allah ba don babu yadda zakiyi da aurena ba Umm Ruman”

Yadda tayi da hannun shima yayi mata ta sake jin kunya ta shige gidan a guje.

A ransa yace lallai lafiya ta samu. Kafin ya shiga shima drebansa yazo yana bashi hakuri wai ya zagaya ganin gari ne ya manta bai tambayeshi ko zasu fita ba.

“Kada ka damu sai anjima zan sake fita amma ni zan tuka kaina. Kai dai ka shiryawa naka tukin na gobe”

*****

Wanka ta fara yi sannan ta zauna taci abinci. Tana gamawa kamar jira wani baccin ya sake dauketa. Dama haka take idan anyi allura ta wuni bacci washegari ta tashi garau.

Awaisu tare da Harisu suka ci nasu abincin sai ya shiga babban falon gidan ya tura aka kira masa uwargidan Harisu. Tsokakanarsa ta gama sannan ta zauna ya dauko kudade masu yawa ya bata yace gashi nan na hidimar biki. Godiya sosai tayi masa da addu’a ta tashi tace zata kaiwa Harisu.

Sai da suka dawo daga sallar la’asar Harisu ya nuna masa ko kadan baiji dadin wannan kudi da ya bayar ba.

“Awaisu sai kace wanda ya auri wata bare zaka bada kudin hidimar biki” ya fada rai a bace yana mika masa kudin.

“Yanzu Yaya menene a ciki don na bayar. Bani da abin da zan iya biyanka ko na saka maka yawan alkhairan da kayi min”

“Ni dai bana so. Addu’ata kawai ku zauna lafiya shikenan”

STORY CONTINUES BELOW

Awaisu yaji dadi kuma yana yiwa kansa kallon wanda yafi kowa sa’ar ‘yan uwa.

“To don Allah ka bar mata kudin sai su kara a na lefe da zan bawa Anti Baraka”

Harisu ya rasa me zaice karshe dai yace “hmmm wannan shine ba mage ba miyau din. Nace bana son na biki kana zancen lefe. To wallahi kada ma ka fara. Idan tazo gidanka ku kare kalau. Amma yanzu kam ko sisinka bana so kuma bazan karba ba”

Awaisu ya dage shima “Yaya lefen nan dangi zasuyi ta zuba ido kuma kaga ga dangin uwa”

“Shine zaka biye musu ka dorawa kanka nauyi? Kayi gyaran gida ga kayan daki ga wannan zirga-zirga. Babu wani lefe da zaka yi na soke”

“Kada muyi haka da kai Yaya” ya dan rage murya.

“Mun riga munyi ma. Bari kaji tunda haka kake so a matsayina na mahaifin Rumana nace bazan karbi lefen ba”

Dariya maganar ta bawa Awaisu “Yaya harda fidda kokon usuli. To naji amma a matsayina na kaninka dolene na taka rawar gani a bikin Rumana”

Wannan karon Harisun ne yake dariya “akwai wata rawar ganin ne bayan sadakinta da ka bayar. Idan ma akwai rawar sai kayi mata idan ta tare”

Zuwa yanzu duka su biyun dariya suke yi sosai amma haka suka tashi Harisu ya kafe akan baya bukatar komai.

*****

Da sallama Haj Fanta ta shiga zauren Malamin suka gaisa a mutumce.

Tarin littattafai ne a gabansa ya sallami yaron da yake wurin suka sake gaisawa da ita.

“Ashe Damaturu kika koma wurin Mujahidu, rannan muke maganar da kaninki Maina. Ina fata kowa dai lafiya”

Haj Fanta ta dago kai idanunta suna nuni da tsantsar bacin rai “Ina fa lafiya Malam, wata shaidaniyar yarinya ta sako min iyali a gaba. In takaice maka dai haihuwar da nake ta jira daga matar Mujahid ta samu ta zubar da cikin. Ba yadda zanyi ba shiyasa ma ka ganni a garin nan babu shiri”

Mal Ridwan ya murmusa sanin hali da rigimar da suka sha da Haj Fanta a baya ya nemi tayi masa bayanin komai a nutse. Duk abin da Yana ta fada mata game da Gimbi ta sanar dashi tare da dan karin gishiri duk don ya amince Gimbi bata kyauta mata ba.

“Shine nace wai ko yau daya dai ya halatta na kira Gogojiya ta daukar min fansa.” Tana maganar tana kwantar murya saboda bata so yaki yarda.

Wani murmushin ya sake yi “Haj Fanta kada fushi ya saka ki yin shirka mana. Har kin manta gwagwarmayar da aka sha shekarun baya? Ko kinsan ba karamin lada kike samu ba da kika hakura da ayyukan da zasu nesanta ki da Allah duk yadda kike jindadinsu. Me akayi akai aljani ke da kika yi imani da Ubangijin aljanun da mutane”

Fuskarta tuni ta nuna rashin jindadin kalamansa na farko sai dai maganarsa ta karshe ta daki zuciyarta.

“Haka ne Malam ni kaina babu aljanin da zai ban tsoro balle wata karamar alhaki nan. Yanzu meye abin yi. Kada kace na hakura na riga nayi rantsuwa sai na rama. Idan ban dauki mataki ba zuciyata tana iya bugawa cikin dare a rasa me ya kashe tsohuwa”

Wannan karon murmushin da yayi sai da hakoransa suka fito. Haj Fanta rigimammiya ce ajin karshe. Ba don karfin addu’a daga iyalinta da imanin da take dashi ba yana kyautata zaton itama da bokar zata zama irin hatsabiban nan.

“Babu abin da yake faruwa da bawa batare da sanin Allah ba. Ki tafi gida kiyi kwanciyarki nayi miki alkawari duk wani sihiri da surkullen da matar nan ta taba yi sai ya karye. Addu’a zamuyi babu dare babu rana gani ga almajirai na. Kuma daga naku bangaren kada kuyi sake. Allah Ya azurtasu da samun rabo mai amfani duniya da lahira”

Sai yanzu tayi murmushi “Amin, Amin Malam nagode sosai. So nake ayi kaikayi koma kan mashekiya” ta saka dariya.

“Ki barwa Allah Shi Yasan ta inda zai kamata. Mu namu addu’a ne kawai.”

*****

STORY CONTINUES BELOW

Karo na shida kenan Gimbi tana son kiran Mama taji muryar ‘ya’yanta amma ta kasa. Tasan dayan biyu ne zai faru idan ta kira. Ko dai Maman tayi mata fada ko kuma ta rinka mata kallon ta ciki na ciki. Rasa mafita tayi ta jefar da wayar tana jin wani daci a wuyanta. Ta yaya ma za’ayi Awaisu ya kwashe mata yara. Duk da gidan iyayenta ne amma dai yaro sai uwarsa. Ranta har wani suya yake yi bata ga dalilin da zai sa idan kowa ya juya mata baya ba a hada har da yaran da babu wanda yasan wahalar zuwansu duniya da rainonsu sama da ita. Hawaye taji ya sauko mata tasa hannu ta share a fusace. Awaisu da duka danginsa basu isa ta sake musu kuka ba. Sai dai kuma tana gogewa wani na sauka. Haka ta kifa kai akan gadon tana kuka kamar ranta zai fita.

Gajiya tayi da kukan ta sake dauko wayar ta kira Ovi. Kamar jira take tace ta samar mata hanyar fita daga gidan zasu jirata a gidan Ovi din tazo suje wurin Boka.  Sosai taji dadin shawarar Ovi ta tashi ta dauko mukullin motarta. Dubawa tayi bata da isassun kudi ta bude kit dinta ta dauko daya daga cikin sarkokin da Awaisu ya saya mata tun kafin zuwan Maamu. Sarka ce hai hade da zobe da dankunne da awarwaro biyu. Seti ne mai masifar tsada don a lokacin da ya bata bayan tasha matukar wahalar haihuwar autanta Mu’allim ne har an fidda rai zata tashi. Jefashi tayi a jaka ta shiga kitchen dinta da yake fayau babu kayan arziki sannan ta fita waje tana yiwa maigadi kallon daidai.

*****

Rumana ta tashi daga bacci ta sake yin wanka saboda yadda jikinta ke baci sosai a irin wannan yanayin. Gyara jikinta tayi sosai sannan ta amsa kiran Harisu da ya tura a kirawo masa ita.

Tana daga labulen kofar falon nasa idanunta suka sauka akan Awaisu. Wata irin faduwar gaba taji da bata taba ji ba game dashi saboda kwarjinin da yayi mata. Zaune yake a kasa ya jingina bayansa da kujera kafarsa daya ya mike dayar kuma ya dan lankwasa ta yana shan fruit salad wanda ya dauko daga dakin Maamu.

Harisu ke zaune a kujerar dake kusa da tashi ta shiga ta sami gefen kujerar dake bakin kofa ta zauna a kasa tana gaishesu.

Bayan sun gama gaisawa Harisu yace ta dawo kusa da Awaisu ta zauna. Kamar kwai ya fashe mata a ciki haka ta tafi gefensa ta zauna a kunyace.

Harisu yayi gyaran murya sannan ya dubeta “Umm Rumana meye matsayina a wurinki?”

Kanta a sunkuye tace “mahaifi”

“Madalla, shi kuma Awaisu fa?”

Tun da ta shigo ta kula ya dauke idonsa daga kanta har taji babu dadi ko tayi masa laifine. Shi kuwa basarwa yake yi kada ya kunyata kansa a gaban suruki.

A dan karkace ta kallo Awaisu tayi sa’a suka hada ido sai cewa tayi “Son So…”

Allah Yasa irin maganar nan ta ciki tayi ko kadan Harisu bai ji ba shi kuwa Awaisu bowl din fruit salad din ya kusa saki don rudewa zata kunyata shi.

Harisu ya sake maimaita tambayarsa ta kuma bude baki har lokacin tana satar kallon Awaisu da dan karfi tace “Son….”

Bai san lokacin da ya kai hannu bayanta yana bubbugawa ba da sauri “Ruwa kike *so*, sannu kwarewa kika yi”

Dariyar da ya bata ce ta saka ta soma tarin dole harda hawaye. Ga Harisu da baisan me suke yi ba yayi zaton kwarewar gaske ya tashi yana cewa akwai ruwa a cikin dakinsa bari ya dauko mata.

Yana shiga Awaisu ya kura mata ido dariyarta tana bashi sha’awa kamar ya dauketa a lokacin “kinci bashi yarinya ki kuka da kanki ranar da zance ki biya”

Ita kuwa yadda taga ya rude baya son Babanta yaji wannan sunan ne yake kara bata dariya.1

Kallon mamaki sosai tayi masa kafin ta fara magana kamar zatayi kuka

“yanzu Uncle sai kace sai na biya idan naci bashinka? Kuma ni yaushe na karbi bashi a wurinka”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page