KASHE FITILA CHAPTER 7 BY BATUUL MAMMAN

 KASHE FITILA CHAPTER 7 BY BATUUL MAMMAN

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Gimbi bata ankara ba taji an damki hannunta ana kokarin kwace abin da take niyar shafawa Maamu. Damkewa tayi iya karfinta ta dage ta ture Dr. Yana sannan ta boye abin da sauri. Mikewa Dr. Yana tayi ta tafi ta riko Maamu wadda ta gama tsorata jikinta sai rawa yake yi. Kirikiri Gimbi ta nufota da abin har tana fadin wasu kalmomi da bata gane ba. A tsorace tace da Dr. Yana ta fitar da ita daga dakin gida zata tafi. Duk yadda Dr. taso kwantar mata da hankali tace ita dai fita zatayi kawai. Saboda jikinta bai gama kwari ba dafata tayi suka fito waje tana cewa su Harisu suna nan wajen suyi sauri kafin su tafi.+

A bakin mota suke tsaye Baaba sai fada take yiwa Anti Suwaiba. Awaisu da ya rasa inda Rumana tayi ya hango Maamu da Dr. Yana ya nufo su yana tunanin me ya fito dasu. Kafin ya karaso sun kusa zuwa wurin motar Harisu. Gimbi suka gani ta taho cikin mugun sauri har tana haki kafin duka suyi magana ta iso tare da yiwa Dr. Yana kallon banza.

“Ke wace irin likita ce zaki shigo daki haka kawai ki fitar da mara lafiya batare da wani bayani ba?”

Su Harisu sanin halin Dr. Yana sai suka fara tunanin ko wani salon shiga rigimar nata ne. Gimbi ta cigaba da magana tana kallon Maamu da tausayawa

“Maamu kinji tsoro ko? Ai in fada muku kuna fita wani abu ne ya shigo mana a guje na kasa ganewa ma  bera ne ko mage. Shine na samo abu zan kore shi ganin Maamu ta tsorata kawai sai wannan matar ta shigo ta fito da ita. “

“La ilaha illallah muhammadur rasulullah sallallahu alaihi wa sallam” Dr. Yana ta fada tana tafa hannuwa saboda tsabar mamakin wannan matar.

Kallonsu tayi duk sun zuba mata ido ta fada musu abin da ta ga Gimbi tana shirin yi a dakin.

Gimbi ta dafe kirji rai a bace “anya kina da hankali kuwa, uwarmijina ce fa kike cewa zan shafa mata wani abu. To a chajeni idan kun yarda da abin da take fada. Maamu fada musu gaskiya”

Wani irin kallo Maamu ta yiwa Gimbi wanda ya tsorata ta sannan ta kada kai ta bude mota ta shige ta zauna. Gimbi ba karamar makira bace. Gara su tafi gida kawai ayi wadda za’ayi gudun kada suyi abin fadi a asibitin.

Baaba tace “likita mungode miki bari mu tafi da ita kawai tunda dama gobe ne sallama.”

Dr. Yana tace “ku tsaya kawai Baaba bari na kira security yaje ofishin ‘yab sanda mafi kusa yayi report. Ni nafi so ayi komai a gama yanzu. In ga abu da idona mata ta nemi raina min hankali”

Tsoro karara ne ya bayyana a  fuskar Gimbi kada ayi binciken da gaske yasa ta fara masifa baji ba gani tana  cewa itama gida zata tafi ta fuskanci basuyi maraba da zuwanta ba shiyasa suke yi mata haka gashi abin ya hada da zargi kuma. Dreban da ya kawota ta kira yazo ta shige mota ko waige babu don tsoron kada a nemi ta fito ma suka tafi rai a bace wannan shegiyar likita ta cuceta domin damarta ta karshe kenan wurin amfani da wannan maganin kuma ta rasa.

Tana tafiya Dr. Yana tace ya kamata wani cikinsu ya tsaya karbar magungunan Maamu da takardar sallama sannan ta kara jaddada musu lallai a binciki Gimbi ba karya take ba. Awaisu yace to su tafi zaije yayi settling komai.

Su Baaba duka motar Harisu suka shiga suna al’ajabin halin Gimbi.  Anti Baraka  ce ta leko ta taga tace ko dai ta fito ne ta taya shi hada kayan da suka baro a dakin.

“Ki barshi kawai Rumana sai ta hada kafin na gama da wurin karbar maganin”

Dariya matan suka soma yi masa harda zolaya sannan suka tafi. Dr. Yana ya tsayar yanayin fuskarsa babu alamun wasa yace ta fada masa abin da ta gani.

Tana fada masa yanayin fuskarsa ya sauya zuwa bacin rai sosai yace idan babu damuwa yana bukatar numbarta saboda zai yiwu ya nemeta shaida. Kafin ya gama magana ma ta fada masa numbar. Katinsa ya zaro ya mika mata sannan yace zai fara zuwa dakin ya duba ko Rumana ta koma don bai ganta a waje ba.

STORY CONTINUES BELOW

Yana zuwa kofar dakin suka kusa karo da ita ta fito da gudu. Ganin Awaisu yasa ta dan dakata amma hankalinta a tashe yake

“Uncle ban ga su Maamu ba kowa ya tafi”

Dan sakin fuska yayi saboda ganinta kawai yaji ransa ya soma sanyi.

“An sallameta ne yanzu suka tafi.”

“Sallama kuma Uncle ba ance sai gobe ba. Ko wani abu ya sameta ne?” Ta fada ido yana kawo ruwa gabanta na tsananta bugu.

Rage tsaho yayi ya kura mata ido ba shiri taja baya ganin ya matso da fuskarsa kusa da tata.

“Maamu lafiyarta kalau. Ki hada kayan kafin naje nayi settling bills sai mu tafi”

Bata san lokacin da tace “mu kadai?”

“Eh mana, Uncle da Umm Rumanansa”

Baki ta bude jin me yace shi kuwa ya juya ya fita. Ita fa ta kasa gane meyasa yake yi mata magana yanzu a wani irin yanayi daban ba yadda ta saba ba. Duk da ita take ce masa Uncle Awaisun Rumana a da yanzu idan ya fada kunya ma take ji.

Kusan minti talatin yayi kafin ya dawo suka kwashe kayan suka kai mota. Dr Yana har bakin motar ta rakasu sukayi sallama da Rumana.

Sun fara tafiya shiru sai lokaci lokaci da ta kula yana yawan kallonta. Ta rasa me yake damun Uncle Awaisu yan kwanakin nan.

Katse shirun yayi ta hanyar yi mata tambaya.

“Saura sati nawa ku koma school?”

“Bai kai sati biyu ba”

“Yayi kyau ana komawa sai SSCE ko”

Ta gyada kai fuskarta na nuni da farincikinta.

“Idan kika gama zaki yarda ki dawo Abuja?”

Da saurinta tace “Allah Ya kiyaye”

Awaisu yayi murmushi. Ai dole ta tsani Abuja to kuma gashi a nan yake aiki

“Ba kya son zama dani ne?”

Ta hau girgiza hannu “A’a ina so mana, amma dai ….”

“na gane kada ki damu aure zan kara sai ki zauna da amarya”

Murna yaga tayi sosai harda juyawa ta fuskance shi da kyau “Allah Uncle, ashe zamu sha biki”

“Sai na fadawa Gimbi kina murna zaayi mata kishiya”

Gimtse dariyarta tayi  ta sunkuyar da kai tana yi kasa kasa. Allah Ya kara tace a zuci har taji tana kwadayin zama a gidan ko na kwana daya ne ta ga Gimbi da kishiya.

“kema ance tunda kika dawo kike ta tara samari. Kuma wanda ya fada min bazai miki karya ba”

A raunane tace “ayya Uncle dan abokin Baba ne na bayan gida kuma nace bana so. Sai wani malamin English a makaranta sannan yayan wata yar ajinmu. Duka fa nace bana sonsu”

Hannu daya ta ga ya saka ya danne kirjinsa bangaren hagu yace “wayyo zuciyata”

A rikice tace “yi parking a gefe Uncle me ya sameka? Ina wayarka na kira Baba”

Kashe mata ido yayi yana dariya “kishi ne dama kuma ya koma tunda naga an damu dani”

Matsawa tayi kunya ta rufeta bata san lokacin da tace “wai Uncle sai ya rinka yi min abu kamar budurwa da saurayi”

Dariyarsa ce ta tabbatar mata da cewa yaji me tace ba shiri ta rufe fuskarta da mayafinta ta shiga kogin tunanin chanjawar Uncle Awaisu. A hankali yaji numfashinta ya sauya jikinta ya dan saki. Mayafin ya ja a hankali ya bude mata fuska ya ga ashe bacci ne ya dauketa.

STORY CONTINUES BELOW

A daidai wannan lokacin yaji wata irin soyayyar Rumana ta shiga ransa. Tabbas da farko yaji ransa ya kwadaita masa amsarta a matsayin mata kuma komai tayi yanzu yana burge shi. Amma a yanzun nan da ya kalleta soyayya ce ta kamshi wadda ta bashi mamaki shi kansa. Rumana bata cikin jerin matan da ko a mafarki ya taba tunanin wani abu makamancin wannan zai shiga tsakaninsu.

Allah mai iko. Mutane biyun da Gimbi ta sanya masa fita harkarsu ya manta da lamuransu sune a yanzu cikin dan kankanin lokaci yake jin zai iya komai indai bai sabawa shariah ba domin  ya faranta musu.

Har gama parking bata farka ba kuma dole ya tasheta don har kannenta sun fito daukar kaya daga motar. Rasa yadda zaiyi ya tasheta yayi sai yayu saa Daula ta fito yace ta tasheta su shiga ciki.

Ranar har dare yayunsu mata suna gidan ana shawara game da matakin da zasu dauka akan Gimbi. Maamu ta tabbatar musu da zancen Dr. Yana gaskiya ne tace tana rokon alfarmar su gaggauta hukunta Gimbi kafin ta bar Fika. A lokacin Awaisu ya kira Alh Maitama ya roke shi akan ya fada masa idan abin da yake son fada ya dangan ci asiri da Gimbi da Anti Bebi sukayi. Alh Maitama bai boye masa komai ba har yadda aurensa da na ‘yarsa ya mutu. Ya tausaya musu sosai kuma ya sanar da su Baaba yadda suka yi.

******

Kamar sun san haka zata faru dama tun jiya Harisu da Awaisu sun sanar da kawun nansu na kusa batun hada aure da Rumana. Duk da sunyi mamaki amma kowa ya basu hadin kai a ganinsu hadi ne na kara dankon zumunci a tsakaninsu. Shiyasa tun wurin karfe tara na safe Harisu ya tura Abba ya sanar dasu dalili yasa dole a daura auren nan a yau bayan sallar Juma’a. Shi kanshi Abba da aka aika yayi mamaki matuka.

A cikin gidan kuma tun daren Harisu ya sanar da matansa. Mama da Anti Amarya murna sukayi sosai. Maman Rumana kuwa ta kasa magana har suka fita daga dakin da yake girkinta ne. Kuka ta sawa Harisu tace tana tsoron kada Gimbi ta sabauta mata ‘ya. Kusan kwana yayi yana rarrashinta da ban baki. Shima akwai wannan tsoron a ransa amma shawara ce da iyaye kuma yasan ko da aure ko babu Awaisu mai rike masa iyali ne bisa amana ba don ya hadu da hatsabibiya Gimbi ba wadda bata san wainar da ake toyawa ba. Tun da ta dawo daki ta shige ta hada kayanta da zummar zata bar garin da safe.

Ganin basuyi mata maganar abin da tayiwa Maamu ba yasa tayi tunanin wayar da tayiwa Ovi daga can bangaren boka ya rufe musu baki kamar yadda ta bukata

Ita kuwa Rumana bata san me akeyi ba don kitso ma tayi tafiyarta makota.

*****

Duka iyalin gidan tun daga kan su Baaba, Harisu da matansa, su Anti Baraka, Awaisu da Gimbi ne zaune a falon Harisu na karbar baki. Da Awaisu ya hana Gimbi tafiya yace ta jira zasuyi magana bayan masallaci bata yi tsammanin haka zata shigo ta tarar da wurin a cike ba. Gabanta ne ya fadi sosai ta sami wuri ta zauna a can gefe.

Kawun nansu da suka shaidi daurin auren Rumana da Awaisu a masallacin Juma’a duka Harisu ya sallamesu akan cewa sai washegari zai sanar da jama’a ayi walima a kofar gida. Yau  suna da abu mai mahimmanci da zasuyi shi da Awaisun.

To gasu duka a falon Baaba ce ta soma magana tana kallon Gimbi ido cikin ido..

“Ba tare da dogon zance ba Gimbiya wannan zaman naki ne. Bisa amana mijinki ya dauki mahaifiyarsa da ‘yar dan uwansa ya kai gidanki kin nemi halaka su. Bansan me zuciyarki ta ayyana miki ba a lokacin da kike azabtar da surukarki da yunwa. Babu ci babu sha sannan kin hana dan cikinta shiga lamarinta “

Mikewa Gimbi tayi a fusace saboda indai ba borin kunya ba zatayi asirinta ya riga ya gama tonuwa.

“Awaisu kana ji kana gani yadda ‘yan uwanka suka saka ni a gaba da sharri tun da na sa kafa a garin nan. To wallahi ni bazan yarda ba ai nima ina da gata ba daga sama na fado ba.”

Da yake yana kusa da ita wani wawan duka ya kaiwa bakin a take ya fashe sai ga jini. Baaba kuwa ta hau shi da fada tace ya tashi daga inda yake.

Bayan ya matsa ya kalleta cikin bacin rai “Gimbi kin cutar dani kin sanya mahaifiyata zubar da hawaye a dalilin juya mata baya da nayi”

Idonta da hawaye tace “kada ka yarda sharri suke son yi min”

“Nafi kowa sanin halinki Gimbi. A lokuta da dama sai kiyi abu raina ya baci sosai amma na rasa dalilin da yasa ko kallon banza bana iya yi miki. Allah sai Ya saka min gwargwadon hawayen da mahaifiyata ta zubar saboda bakinciki. Kuma ki sani yadda kika yi abin da kike so a lokacin da kike so nima yanzu lokacina ne. Gimbi sai na soya miki gyada a hannu kinyi nadamar aurena”

A gabansu ta dauko waya zata kira Ovi saboda tashin hankalin da ta shiga na maganganun Awaisu. Haka ‘yan uwansa kaf suka ci mata mutumci tasha Allah Ya isa babu iyaka akan halin da tasa Maamu.

Tunawa tayi da inda take ta fasa kiran wayar amma ranta  ya kololuwar baci. Idanunta jazur tana kumfar baka tace

“Awaisu idan ka cika dan halak ka sakeni. Meye a cikin auren naka wanda bazan iya samu ba idan na auri wani?”

Murmushinsa da take masifar so a da yayi mata “aure ni dake yanzu muka fara. Yanzu dai ki tsaya a kawo miki amarya ki karbi amana. Idan kuma kinfi so ku hadu a Abuja babu damuwa”

Komai na jikinta ne ya tsaya a lokacin da ya ambaci amarya. Jikinta na rawa tace “aure kayi Awaisu? Ni zaka wulakanta kayiwa kishiya. Wace shegiyar ce take jin zata iya zaman kishi dani?”

Magana take kamar zata zare ransu fes duka da ganin ko babu komai sun soma ramawa. Maamu ce tace “kada ki sake zagar mana ‘ya”

“Auuuu wani munafukin ne yazo ya bashi ‘ya ya aura?  To mu zuba ni daku wallahi baa isa a daura auren ba idan har ina numfashi”

Su Anti Baraka sai dariya Gimbi ji take kamar tayi hauka don takaici. Ledar goro Anti Suwaiba ta jefa mata

“Yau dai bokanki yayi karya domin an riga an shafa Fatiha tun dazu. Awaisu ya zama angon Rumana”

“Jakar uba, Rumana??? Rumana fa kika ce?” Kafin su ankara tayi kan Awaisu a gigice zata kaiwa wuyansa shaka.Fincikota taji anyi ta juya a fusace ta ga waye ya rikota taji saukar mari. Anti Baraka ce da wannan aikin halin Gimbi ya kaita makura duk da kasancewarta mafi hakuri a cikin ‘yan uwanta.+

Kumatunta ta rike don ba karamin shigarta yayi ba kalli Awaisu dake tsaye ya rasa yadda zaiyi. Kunyar ace matarsa ke wannan aika-aikar da bacin ne suka cika zuciyarsa.

Idanunta babu hawaye ko kadan tunda shima kuka wuri yake samu

“Abban Haris yanzu ka yarda da abin da nake fada maka ko? Mutanen nan sam basa kaunarka shine saboda sun rasa yadda zasuyi su rinka tatsarka suka hadaka da Rumana….wai Rumana yarinyar da ba haihuwarta ba uwarta ma a kan idonka aka aurota.”

“Gimbi kada ki kure hakurina wallahi. Ban taba sanin cewa akwai ranar da zanyi nadamar watsawa Yaya Harisu kasa a ido a lokacin da ya nema min matar aure na bijire ba sai yanzu.” Cewar Awaisu yana daga murya.

“Dama har wata matar ya taba sama maka? Hasashena bai zama kuskure ba da nace kudinka suke nema. Wato yaso baka wadda zata rinka sata ta kawo maka”

Hannu ya kai zai daki ko ma ina ya samu a jikinta Harisu ya rike “Awaisu kada kayi abin da nan gaba zakayi dana sani. Ka tuna akwai rabo a tsakaninku bai dace ka daketa ba”

Har wani huci yake yi ya dubeta tana kallon kowa daidai

“ki tashi ki kama hanya ki koma Abuja ki jira sauran abin da zai biyo bayan cin amanar da kika yi min na hadani da ‘yan tsibbu”

Ga mamakin kowa durkusawa tayi a gaban Maamu zata dafata tayi saurin janye jikinta sai ga wasu zafafan hawaye suna ambaliya kamar famfo a idanun Gimbi

“Maamu don Allah na tuba ki yafe min duk abubuwan da ake zargin nayi miki. Naji na karba amma ki yafe min. Indai don wannan ne aka sa ya auri Rumana ni ko me kike so daga yau na dauki alkawarin yi miki indai zai saketa”

“Mutuwa ce kadai zata rabani da Rumana kisa wannan a ranki Gimbi” Awaisu ya bata amsa

Tashi tayi tana share hawaye “wannan cin mutumcin da kayi min na rantse maka sai na rama. Yau ba don Rumana ka aura ba da ko kaki ko kaso sai ka sakeni. To amma abin kunya ne a gareni aurena ya mutu akan wannan yarinyar da bata gama zama mace ba. Banda son zuciya irin naka da na iyayenta ina zaka kai ta”

Baaba Hure ce wannan karon ta daka mata tsawa wanda yasa ta fita daga falon ranta yana kuna. Dakin da ta sauka ta shiga ta harhada kayanta cikin sauri ta janyo akwatin tsakar gida.

Budar bakinta ta soma kiran yaranta “Har….bari mu koma gida ko me zan yanka domin canja maka suna sai na canja don bazaka taba tashi da sunan makiyana ba”

Daga falon suka ji tana kiran ‘ya’yanta Awaisu ya taso da sauri. Tare suka taho da sa’aninsu na gidan saboda dama wasa sukeyi a can baya.

“ku wuce ku dauko kayanku tafiya zamuyi.” Ta fada fuskarta babu alamun wasa.

Amir ne yace shi dai a nan zaiyi hutunsa. Ai kuwa Gimbi ta surfa masa na maguzawa zata huce haushi a kansa. Awaisu ta gani yace yaran su koma ciki.

“Ni da ‘ya’yana ta yaya kake so na barsu a gidan nan?”

Ganin suna kallonsu da fargaba a idanunsu yasa Awaisu cewa “Haris ku tafi tafi ciki kunji. Mummy is very sick. Irin zazzabin da Mu’allim ya taba yi yana ta surutu ne ya kamata. Yanzu zamu je asibiti daga nan a mayar da ita Abuja. Mu kuma ranar sunday sai mu tafi tare ko “

Da tausayin mahaifiyar tasu Haris da kannensa suka koma har suna yi mata sannu.

Bude baki tayi zata fara masifa Awaisu yayi mata wani irin kallo duk rashin kunyarta sai ga bakin hangame a iska ta kasa furta koda kalma daya. Matsowa yayi kusa da ita harda daukan akwatin saboda yaransa da basuyi nisa ba sannan ya rage murya yadda zata ji

STORY CONTINUES BELOW

“Kada kiyi yunkurin daga murya a gidan nan wallahi zan baki mamaki. Ki duba ciki da waje baki da mai kwatarki idan kika shigo hannuna domin kin gama bata rawarki da tsalle a idanunsu”

Bata iya sake tanka masa ba ta bi bayansa har mota. Dreban ya kira gefe ya ja masa kunne sosai akan cewa kada ya kuskura ya tsaya ko ina sai Abuja. Sannan ya kara da cewa idan sun isa ya karbi mukullin motar Gimbi yace zai sha mata mai. Idan ta bayar ya hada da na motar da suka zo ya tafi kada ya dawo gidan sai ya neme shi da kansa. Dreba mamaki ya ishe shi amma baice komai ba. Dama ba dadewa yayi a gidan ba bai san meye tsakanin ma’auratan ba.

Baya Awaisu ya zauna kusa da Gimbi ya zaro kudi ya damka mata.

“Ga wannan ki rike ko bukata zata taso miki kafin na dawo. Sannan naji labarin za’a fara wahalar mai nace Gambo ya tafi da motarki ya sha miki mai idan kun isa. Sannan bana so kina tada hankalinki don kinsan bana jindadin ganinki a haka. Ki tafi kafin nasan yadda nayi na kawar da matsalolin dake son rabamu”

Bacin ranta taji ya fara sauka kadan saboda a tunaninta ko akwai sauran asirin da yake aiki a kansa. Ba dai tace komai ba don burinta kawai ya fita daga motar ta kira Ovi. Sallama yayi mata harda sakin fuska ya koma cikin gidan.

Yana fita ta kira Ovi ta juya harshe da turanci tana kuka tana fada mata me ya faru. Ovi dama a speaker tasa wayar ita da Rita sukayi dariya mai isarsu sannan tace zata jirata idan ta dawo su koma wurin Boka. Har tuna mata takeyi  tasan dai aikinsa babu wasa kaifi daya ne. Gimbi taci kukanta dai kafin su isa. Kamar yadda aka umarci dreba ya karbe mukullin motarta da na wadda suka zo yayi tafiyarsa.

*****

Da Awaisu ya koma ciki sun cigaba da tattaunawa inda ‘yan uwansa mata suka nuna tsoron kada Gimbi ta koma wurin da take karbo kayan asirinta. Nan ya fada musu umarnin da ya bawa Gambo dreba da kuma kashedin da yayiwa maigadin gidansa a waya kan cewa kada ya bar kowa ya shiga ko fita daga gidansa har sai ya dawo.

Baaba tace duk da haka sai ya tashi tsaye sosai da ibada saboda ta nan bangaren yayi raunin da aka sami galaba akansa duk da tasan cewa asiri gaskiya ne. Bayan nan suka ce ya kamata aje har gidansu Gimbi a fadawa iyayenta abubuwan da suka faru.

Awaisu yace dama yayi niyar idan ya koma yaje

“Ba’ayi haka ba. Wannan ba maganar mutum daya bace. Idan ka tashi tafiya sai mu tafi tare har da Harisu ko wani cikin kawunnai domin su dauki zancen da mahimmanci” inji Anti Baraka.

Maamu da Baaba ne sukayi ta saka musu albarka sannan suka tashi domin yin sallar laasar. Kafin su fita Mama uwargidan Harisu tana dariya tace “akwai fa amaryar da bata san an aurar da ita ba.”..

Tsokanar Awaisu suka fara har suna cewa ya tsaya su gaisa da surikinsa suna dariya. ita dai maman Rumana ficewa tayi. Ko ita bazata iya kishi da Gimbi ba bare Rumana. Auren nan don dai kawai anfi karfinta ne. Amma tana jin tsoron yadda zaa zauna gashi bai saki Gimbin ba kamar yadda yace zamansu tare ya rama abubuwan da tayi masa shine kawai zaisa ya huce.

Kowa ya fita daga dakin ya rage Awaisu da Harisu. Wani nauyin yayan nasa yake yi. Harisu ya kula dashi ya dawo kujerar kusa da tasa

“Menene yake faruwa Awaisu?”

Iska ya dan furzar “Yaya don Allah hankakinka ya kwanta da auren nan? Wallahi bana son abin da zai zo ya taba zumuncinmu ko kadan”

Zulumi da fargaba ya gani a cikin idanun kanin nasa. Da farko shima auren nan bai wani kwanta masa ba amma yanzu yaji dadin wannan hadin.

“Awaisu abu daya kawai nake so ka fada min shine dalilinka na saurin amincewa da auren”

Abin mamaki ga Harisu gani yayi kanin nasa ya dan dukar da kai kafin ya bashi amsa “Abin da ban taba tunani bane ko a mafarki Yaya shine jin soy….uhmmm…soyy”

STORY CONTINUES BELOW

Shiru yayi ya dafe goshi ya dago kamar zaiyi kuka  

“kunyarka nake ji”

Harisu ya kwashe da dariya irin wadda Awaisu ya dade bai ga yayi ba

” kaima yadda akace shiru ko kunya a wurin budurwa amincewa ne to kaima kunyarka ta cire min duk wata damuwar da tayi min saura. Nasan Awaisu a matsayin kani kuma dan uwa nagari. Fatana ka zamewa Rumana abokin rayuwa nagari. Na sani ko babu ni iyalina bazasy taba tagayyara ba idan kana raye. To menene abin fargaba idan kana auren ‘yata.”

Shi dai Awaisu godiya yayiwa yayan nasa sosai suka tafi masallaci.

*****

Wurin biyar da rabi na yamma Rumana ta dawo daga gidan kitso. Ana mata fadan dadewa tace kawayenta na primary ta hadu dasu a gidan suka tsaya hira. Sai da taci abinci aka kirata dakin Maamu. Bata kawo komai ba ta tafi. Da shigarta ta fada jikin Maamun tana murnar ganin kara samun lafiyarta. Baaba tace to ta tashi dai kada ta karyata.

Baaba tace “Rumana kin tuna duk wahalhalun da kuka sha da Maamu a Abuja ko”

Tace eh yaushe zata manta.

“A dalilin haka kawunki ya kara aure yau dinnan kuma muna fatan wannan karon in sha Allah an dace da matar kwarai” Baaba tana magana tana kallon yanayin fuskar Rumana.

Murmushi tayi mai nuni da farinciki  “dama jiya ya fada min zai kara aure ashe abin ya matso haka. Yeeyyy zamu sha biki….” tashi tayi zata fita tayiwa ‘yan uwanta shela Baaba tace ta dawo ta zauna.

A dofane take don sauri take ta samu ta fita ta kai musu labari. Dole suyi shagali wallahi ko don ta konawa Gimbi rai saboda bata san Gimbin ta tafi ba.

“Nasan bazaki so Maamu ta sake zama irin na da  ba a gidansa ita kadai da Gimbi..”

Rumana ta firfito da idanu tana kallon Baaba kafin ta dafe kirji a dan tsorace “Ba dai Abujan kuke so na kara zuwa ba. Ni wallahi bazan koma ba”

“Wane irin zance ne haka ina magana kina cewa bazaki koma ba?” Baaba ta fada cikin fada. Kafin ta kara cewa komai Rumana ta tashi tana bubbuga kafa ta fita daga dakin. Ko dukanta Baba zaiyi bazata yarda ta koma Abuja ba. Wa yasani ma ko matar tafi Gimbi iya mugunta.

Maamu ta kalli Baaba tace “gashi nan kince na bari ki fada mata har ta fita baki fada ba sai kara hargitsa mana ita da kika yi”

Rike baki Baaba tayi “to ni dai babu ruwana kuma iyayenta su karata. Wannan yarinya da gani zaayi daru da ita”

*****

Tun da ta shiga daki take ta kumburi taki fita falo. Bayan isha kanwarta Hafiza ta sanar da ita babansu yana kiranta a dakinsa. Tashi tayi da kudurin ko me zaice zata dage bata koma Abuja ba.

Mamanta ta gani a gefensa fuskarta babu wata walwala.  Zama tayi ta gaishe shi.

“Rumanan Baba kuna magana ashe dazu dasu Baaba baki gama ji ba kika tashi”

Kuka ta soma yi masa. Dama plan din da tayi kenan tayi ta kuka tana rokonsa ya barta a nan.

“Baba bana son sake zuwa Abujan ne”

“Naji Rumana amma ai baki tsaya sunyi miki cikakken bayani ba. Dazu auren dake aka hada”

Zama tayi dabas daga dan durkusun da tayi “Baba ni me nayi kuma zaka min aure? Shi wannan dan Baban bayan gidan Allah bana sonsa. Kuma ko makaranta ni ban gama ba”

Kuka ne ya kwace mata ta tashi ta fita muryarta har ta soma karade gidan ta shige dakinsu ta kuka.

Harisu ya kalli mamanta “ko sunan mijin ban fada ba kinga ta tashi”

Da alamun rashin damuwa don ita fa auren nan baiyi mata ba ta tabe baki “ni meye nawa a ciki?”

Kusa da ita ya koma ya rungumota “kinsan ina alfahari dake saboda saukin kai “

“Shiyasa zaka cutar min da ‘ya” ta amsa mai da hawaye

“Kiyi hakuri. Nasan ko ba Gimbi yake aure ba dole abin nan yazo mana wani iri. Amma ki kyautata zato ga Allah in sha Allah auren nan alkhairi ne”

Wayarsa ya dauka ya kira Awaisu ya fada masa yadda sukayi

“Ka tura a kira maka ita kayi mata bayani da kanka”

Awaisu ya kalli su Baaba da suka gama fada masa ya suka kare da Rumana dazu. Allah gani gareKa yace sannan ya fita ya ce a fada mata ta same shi a falon Harisu.

Kukanta ne ya fara sanar masa da isowarta ta shiga ko sallama babu.

Wuri ya nuna mata a kujerar kusa da wadda ya zauna. Ta zauna idanunta a kumbure ta sake fashe masa da wani kukan

“Uncle aure akayi min” ta fada murya na rawa.

Tausayi yaji ta bashi “kiyi hakuri, kinsan komai nisan lokaci dama wata rana zakiyi aure”

Bakinta ta turo tana wani hawayen “to kuma ni sai ayi min auren dole ko karatu ban gama ba. Kuma ko sonsa banayi”

Awaisu yayi murmushi “indai karatu ne zan barki kiyi ta yi har sai kin gaji don kanki”

Dagowa tayi suka hada ido yaji wani sonta ya kara shigarsa. Ita kuwa murmushi ta danyi “Allah da gaske zaka yiwa ko waye mijin magana ya barni nayi karatu? Daga nan ma ka roke shi ya sakeni kawai.” Ta dan cije lebe cikin takaici “nasan ba kowa bane mai nacin nan sai wannan dan abokin Baba da na fada maka”

Dariya Awaisu yaso yi jin tace mai naci.

“Bana fatan ki fito daga gidan mijinki indai ba da sunan zuwa unguwa ba. Ko kin yarda zaki bini Abujan?”

Duka biyun babu wanda yayi mata. Amma idan ta tuna yadda ta tsani yaron nan mai naci sai taji gara Abujan

“To amma don Allah uncle idan anje Abujan ka damka ni a wurin Anti Amarya”

“Umm Ruman kenan, wato Anti Amarya ko don iya dadin baki” yayi dariya yana kallon yadda ta hade fuska ita da gaske take.

Goge hawayenta tayi ta tashi “to yaya sunanta?”

“Umm Ruman Harisu Sa’ad”

Idanunsa ya kafeta dasu yana kallonta babu alamun wasa. Jikinta tuni ya fara wani irin rawa “Ni Rumanan?”

Sai da ya tashi tsaye ya rungume hannuwansa a kirjinsa sannan ya gyada kai “ke Rumanan”

Wai me yake fada ne. Kanta ta nuna da hannu tana masa kallon rashin fahimta “Uncle ni ka aura? Innalillahi”

Kafin ya ankara tayi hanyar fita daga falon. Da saurinsa ya isa bakin kofar ya rufeta da kafarsa tare da riko Rumanan. Kuka ta fashe masa dashi tana kokarin kwacewa. Rungumeta yayi yadda bazata iya kwacewa ba tana kuka tana maganganun da baya fahimta sosai “Uncle bazan iya ba. Ka rufa min asiri. Wayyo Allahna. Kalli ka gani fa nice ‘yar karama dani…”

Hannu yasa akan bakinta yace “shhhh Umm Ruman everything will be okay I promise.”

Tun tana kokawa dashi na son kwacewa daga jikinsa har ta gaji ta dena. Ji yayi ta dena kokarin kwacewa sai ajiyar zuciya da take yi lokaci-lokaci.

Tausayi Rumana ta bashi sosai sai dai kuma baya jin zai iya rabuwa da ita a yadda yake jin soyayyarta a ransa. Cikin ‘yan kwanakin nan komai nata burge shi yake yi.+

Hannunta ya kama suka koma wurin kujera amma da kyar ya samu ta zauna kanta a kasa taki dagowa.

“Dago ki kalleni” yace yana leken fuskarta.

Maimakon ta dago sai ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta gabanta yana tsananta bugu. Abu ne kamar a mafarki wai Uncle Awaisu ya zama mijinta.

Kyaleta yayi don baya son takura mata.

“Ki dena kukan nan kada ki fita ido a kumbure. Just calm down idan kin sami natsuwa ki shiga ciki”

Zumbur ta mike suka hada ido tayi saurin kawar da fuskarta. Idanunta banda kumburi sunyi ja sosai. Kafin ya sake mata magana ta fice da gudunta don ma kada ya sake tsareta. Komawa yayi ya zauna yasa hannu yana matsa gefen kansa da yake masa ciwo. Abubuwan da suka faru dashi a tsukin kwanakin nan sun daure mishi kai haka kuma dasu yake kwana yake tashi.

Rumana na fita dakin Maamu ta tafi suna tare da Baaba. Tana shiga ta fada jikin Baaban ta fashe da wani irin kuka. Bayanta Baaba tayi ta shafawa tana rarrashinta. Maamu itama rarrashin take yi. Ta dauki lokaci a haka kafin ta dago kanta

“Baaba don Allah kuce ya sakeni. Ta yaya zan auri Uncle don Allah” wani hawayen ke bin kumatunta ta rinka bin kakaninta da ido.

“Kul Rumana kada na sake jin zancen saki a bakinki” cewar Baaba

“Ni wallahi bana son aure yanzu. Yanzu sai ayi ta cewa na auri kanin Babana. Kuma ma ko sonsa banayi”

“A’uzubillahi” Baaba ta fada tana doke bakin Rumana. Bare baki ta sake yi Maamu ta janyota jikinta.

Maamu tace “Rumana ba kya sonsa? To babu maiyi miki dole “

Dan kunya taji “ina sonsa mana Maamu amma ba son so ba”

Dariya suka so yi su biyun sannan Maamu tace “to wanne kike masa.? Bansan meye son so ba”

“Ina nufin ina son shi amma ba na soyayya ba” ta kare a hankali muryar ma bata fita sosai saboda yadda taji kunyar abin da take fada.

Baaba ta rike haba, gaskiya akwai rigima don tayi zaton Rumana tafi haka wayo sai gashi ta gane har yanzu tana da sauran wauta. Wai son so, saura son ki.

Rarrashinta suka rinka yi da ban baki don ranar a dakin ta kwana.

Washegari ko alamun Awaisu bata gani ba ashe ya tafi gaishe da dangin Maman Rumana tunda basu san da auren ba shi kuma lahadi yake son komawa. Da kanin Malam Saad babansu Harisu da kuma kanin Maamu suka je sanar da kakan Rumana na wurin uwa domin fita hakkinsu tunda abin yazo babu shiri basu sani ba. ‘Yan uwanta sunyi mamaki sosai amma sunsa albarka tunda an riga an daura sai fatan zaman lafiya.

*****

Gimbi ta gama shirinta da sassafe ko ruwa bata iya sha ba ta fito tana neman keys din mota sai dai babu ko daya. Tunawa tayi ta bawa Gambo dreba ta fita ta tambayi maigadi ko ya bashi da ya dawo da motar don ta ganta a cikin gidan.

Maigadi yace ai bai ma fita da ita ba tun a jiyan. Abin ya bata haushi ta kira wayarsa yafi a kirga amma yaki dauka. Matarsa har cewa tayi ya dauka mana matar oga ce yace umarnin ogan yake ba.

Iyakar kulewa Gimbi tayi gashi tun a hanya take kiran Ovi da Rita bata samu. Data dawo gidan bata ga Rita ba duk ta damu. Shiyasa duk irin gajiyar da ta kwaso ko runtsawa bata sami yi ba saboda tunani.

Tsaki  taja ta nufi gate tana ta masifa. Isarta ke da wuya tace maigadin ya fita ya nema mata taxi ya dan sunkuyar da kai

“Oga yace kada a bari ki fita har sai ya dawo”

STORY CONTINUES BELOW

Kallon rainin hankali tayi masa sannan ta daka masa tsawa

“Zaka bude min ko sai nasa an koreka a yau dinnan?”

Matsawa yayi ya bata wuri taje taji kofar garkame da kwado. A fusace ta koma ciki tana ta kai kawo. Da ta gaji ta sake dawowa ya kuma tabbatar mata bazai bude ba. Suna haka tana ta sauke masa kwandon zagi suka ji bugu. Tambayar ko waye yayi Rita ta amsa.

Gimbi har ta soma jindadi zai bude ta samu ta fita sai ta ga ya koma kan kujerarsa ya zauna.

“Kai malam baka ji ana buga kofa ne?”

“Oga cewa yayi babu shiga babu fita” ya amsa mata.

Kallon mamaki tayi masa “ina jin baka ganeta ba. Rita ce mai aikina”

“Hajiya kiyi hakuri ko ki kira shi a waya. Ni dai abin da ya fada min kenan”

Jikinta har tsuma yake yi don bacin rai ta kira Awaisu. Lokacin tasowarsu kenan daga wurin kakan Rumana zasu tafi wurin da ya ajiye mota. Sai da ya bari ta kira sau biyar a jere sannan a na shidan ya dauka.

“Ina jinki” ya fada muryarsa na nuni da baya maraba da wayar.

“Abin da zaka ce min kenan bayan jiya ka yaudareni kasa na bada mukullin mota ko. Wallahi baka isa kaci mutumcina ba kaima ka sani”

“Meye dalilin kiran naki yanzu I am busy?”

“Sannu agogo sarkin aiki. Ba wani abu bane kasa maigadinka ya bude min kofa na fita “

“Babu mai fita ko shigar min gida sai na dawo”

Bacin ranta ne ya karu “to kace ya budewa Rita ta shigo”

Dadi yaji ashe matar da baisan daga ina ta samota ba bata gidan.  Murmushi yayi kafin yace “wani abu ne haka Rita din?”

Wulakanci! Lallai Awaisu bai santa ba har yau. Danne bacin ranta tayi domin burinta ta fita da kanta taje wurin Boka. Daga shi har dangin nasa sai ta mayar dasu waina don juyasu zata rinka yi.

“Awaisu kaga na shanye duk wani abin da ‘yan uwanka suka yi min. Ka barni naje gidan iyayena mana…”

Shiru taji na dan lokaci bai amsa ba sai kuma taji yayi yar siririyar dariyar da take matukar so a wurinshi. Kashe murya taji yayi yana magana kasa-kasa “ashe haka kike da rigima my little princess, don kina son tausa sai kin haye min cinya”

Hannun da Gimbi ta rike wayar dashi ne taji ya fara karkarwa kafin duka jikinta ya dauka. Wayar da kanta ta subuce ta fadi a kasa ta tarwatse. Kunnenta ta kaiwa duka tana son tabbatar da abin da Awaisu yace….runtse idanu tayi tana hango Rumana akan cinyar Awaisu. Wani irin ihu ta saka na tsananin bacin rai “Awaisuuuu, karyarka ka hadani da wannan afiruwar. Rumana tayi min kadan sai dai nayi da uwarta. Dani kuke zancen duka, sai na baku mamaki.”

Da kyar ta iya jan kafarta ta koma cikin gidan bayan ta hada wayarta. Rita ta dannawa kira tana bata sako zuwa ga Ovi da bokansu

Shirun da yaji daga bangarenta yasa shi kwashewa da dariya har idanunsa na kyalli. Mara kunyar karya ya fada yana komawa wurin motar ya shiga. Dama wadanda suka zo har sum shige ganin yana waya. Gidajensu ya kaisu tare da godiya da alkhairin da ya saba musu.

******

A daki Rumana ta wuni har dare taki cin abinci. Mamanta tayi fadan ta gaji ta fita harkarta amma duk ta damu. Gashi tun baaje koina ba ta wani fige ina ga ta fara zama da Gimbi.

Da daddare Awaisu da Harisu shawarwari suka yi da iyayensu mata akan yadda zasu gabatar da komai na lamarin Gimbi. Da sassafe zasu tafi Abuja tare da Harisu da Anti Baraka.

Yaso ganin Rumana amma baya son zakewa duba da rashin walwalarta tun bayan ta sami labarin shine mijin. Ajiye komai zaiyi yanzu sai ya koma Abuja yayi ‘yan shirye shirye da bincike akan Gimbi.

STORY CONTINUES BELOW

Ranar lahadi karfe takwas na safe sun gama shiri yaransa suma sunyi wanka sunci abinci ana ta fitar da kaya mota. Awaisu yana son ganin Rumana amma yayi wuri.

Dakin Baaba yaje yi mata sallama yayi sa’a Rumana tana kwance akan gado ta kudundune jiki da bargo. Yasan me yiwuwa Baaba na tare da Maamu ya danyi murmushi sannan ya karasa  bakin gadon ya zauna.

Yana zama yaji alamun Rumana ta dan matsa baya yayi murmushi wato taji shigowarsa. Ashe tun kafin ya shigo idonta biyu baccin karya tayi saboda shi. Kamshin turarensa ya mamaye dakin a hankali ya bude bargon saitin fuskarta da take kallon bango ta juya masa baya. A saitin kunnenta har tana jin numfashinsa taji ya soma magana a hankali

“Ki kular min da kanki sai nan da wata daya zan dawo in sha Allah. Idan kina bukatar wani abu kada ki tambayi kowa ki kirani”

A takure take sosai ga wani sabon yanayi Uncle ya wani zauna kusa da ita haka. Hannunta ya lalubo ya dora mata waya mai kyau.

“Akwai kudi a ciki kuma na saka miki numbers dina. Zan jira wayarki ta tambayata yaya hanya.”

Ji tayi kamar ya sake kwantowa jikinta ta kuwa runtse ido tam. Wani murmushi yayi ganin yadda tayi masa kyau. Ya cigaba da magana “a hankali zan koya miki yi min son so kamar yadda nake yi miki idan kin dawo Abuja”

Bata san lokacin da ta bude ido ba tana mamaki ko su Baaba ne suka fada masa. Kamar ya karanci me take tunani yace

“Indai bazaki rinka yi min magana ba to duk wanda kika yi hira dashi zan roka ya fada min tunda kina min rowar muryarki. Na tafi”

Wani gwauron numfashi ta saki da ya tashi. Sake juyowa yayi “Babu yiwa miji addua? Kina wasa da ladanki da kin magana Princess”

Bargon taja ta rufa har kanta sannan kamar bazata yi magana ba yaji tace “Allah Ya kiyaye”

Fita yayi yana murmushi shi kadai yana cewa “soon Umm Rumana, very soon zan koya miki karatun da ni kadai ya dace na koyar dake.”

Ita dai bata fito ba har taji ana ta sallama dasu sannan taji alamun duka an watse daga tsakar gidan. Tashi tayi jiki babu kwari don babu wani abin kirki a cikinta ta daga wayar tana kallo. Waya ce mai kyau ta zamani. Murna ta fara sai da ta tuna batun auren ta cusata a kasan pillow ta koma ta kwanta.

Wurin karfe uku Mamanta ta leko kiranta. Har yanzu Baaba bata dakin gata ko wanka bata yi ba ita tana fushi anyi mata auren dole. Dakin Maman taje tana shiga ta ga Umma yayar Mama dake aure a Lagos. Da yake sun dade rabon da su hadu saboda zamanta a Abuja a kunyace ta gaisheta.

Umma ta dagota tace “yata kamar ba amarya ba duk kin rame”

“Babu abin da take ci sai kuka Yaya” inji Mama

Umma ta bata fuska “wai haka Rumana?”

Bata jira amsarta ba ta dauki plate daga kayan abincin da Mama tasa aka kawo mata ta zuba abinci sosai a kai ta saka cokali biyu tace suci tare. Rumana zata fara gardama Mama ta soma mata fada. Umma tace ta tashi ta barta da ‘yarta. Ba musu ta fita ranta duk a bace.

Bayan ta fita ya rage su biyu kawai. Da nasiha Umma ta samu suna ci tare tana fakewa da hira Rumana ta cinye fiye da rabinsa Umma na tsakura. Dama wayo taso yi mata. Suna gamawa tasa taje tayi wanka ta shirya sannan tayi sallar laasar.

Can yamma Umma tasa Hafiza ta dama mata kunu ta shanye sannan da daddare suka ci tuwo tare. Sai da suka gama Umma ta kirata cikin uwar dakin mama tace ta zauna magana zasuyi.

“Rumana kinga da yanayin da aure yazo miki ko”

An tabo inda keyi mata kaikayi ta soma sharar kwalla

“Ba kuka nace kiyi ba. Rumana ki daga hannu ki godewa Allah. Ko kinsan mata nawa ne da kyau da ilimi da komai na tarbiya Allah bai basu mazan aure ba? Duk hukuncin Allah ga bawa alkhairi ne sai dai idan bawan ya bijire “

STORY CONTINUES BELOW

Shiru tayi tana sauraron Umman.

“Rumana naji labarin komai a wurin Binta kuma na tausaya miki Allah Yasa anyi bayan nazo gari. Sai dai ki sani damuwar nan da kike yi ita tasa mamanki ta kasa kwantar da hankalinta. Wanda hakan ya janyo ta kasa hakura yadda babanki yake ta bata shawara. Shin kina son zama sanadiyar kawo sabani cikin rayuwar iyayenki?”

Da sauri ta girgiza kai. Umma tace “ki koyi hakuri tunda girma ya hau kanki. Aure daraja ce da rufin asiri ga maauratan”

A hankali tace “ko da mijin babba ne Umma”

“Da babba da yaro basu da bambanci matukar sun iya kula da tattalin iyalinsu. Ina so ki nutsu ki sani cewa yanzu ke ba karamar yarinya bace saboda haka ki ajiye duk wata wauta da shirme a gefe. Gimbi da zaki zauna da ita idan kika tafi a haka zaki kwashi kashinki a hannu”

Rumana me zatayi in ba dariya ba da jin wannan maganar. Umma taji dadin ganin ta sake ta hau bata shawara da kwantar mata da hankali. Daga karshe tace

“Binta tace wai sai kin gama secondary nan da kusan wata biyar zaki tare amma mijinki yace a can Abujan yake so ki karasa. To nidai nasan a da ne ake irin wannan auren har ma a shekara amarya lafiya kalau. Yanzu kuwa indai ba so suke a kaiki da ciki ba gara ayi abin da ya sauwaka ki tare kawai”

Gaban Rumana ya fadi ta hau zare idanu. Ita ta manta ma ana tarewa idan anyi aure. Shikenan sai su zauna da Uncle Awaisu……ita kam bazata iya ba.

Umma ta katse mata tunani “Rumana ki sani Allah baYa dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Saboda haka ki kwantar da hankalinki ki fuskanci sabuwar rayuwarki. inaso ki kiyaye idan an kaiki ko ruwa kada Gimbi ta baki kisha, addua kuma kada ki kuskura kiyi wasa da ita. Sannan ki sani cewa kina da babban makamin jan hankalin miji wato kyautatawa mahaifiyarsa. Ina mai tabbatar miki tunda Gimbi ta wulakanta masa uwa yanzu ko pure water kika bata wallahi sai kin kara shiga ransa. Ina fada miki don kada ki sakankance wai  baya sonta ko abu makamancin haka. Tsakanin mata da miji sai Allah. Sai kiga mace da mugun hali ko kazanta miji yana korafi amma ya saka rabuwa da ita saboda aure rai gareshi”

Maganganun suna ta shigar Rumana har inda Umma tace ta cire zancen saki a ranta ta karbi kaddararta hannu biyu. Idan tayi haka da zuciya daya to lallai zaa wayi gari ta kamu da son mijinta. Abin da kamar wuya take ji amma yadda Umman lagos take ta rarrashinta da bata baki yasa taji zata yi kokari ta daure ta zauna dashi. Amma fa a ajiye maganar aure a gefe ita kam bata girma ba gaskiya nauyinsa take ji.

*****

Su Awaisu sun isa ido na ganin ido. Yara suna ta murnar ganin Gimbi amma taki kulasu ko fitowa daga dakin ta kasa. Sai da suka fada mata da su wa suka zo ta fito babu shiri.

A falo suka hadu Awaisu yana cewa Anti Baraka ta shiga daya daga cikin dakin baki zai kawo musu abinci su ci. Gimbi karasa fitowa tayi ta rinka jan tsaki tana harararsu. Babu wanda ya kulata sai Haris da yake kallon yadda take yiwa yayyen babansa yana jin babu dadi.

Ganin Awaisu yayi hanyar dakinsa suma kowa ya tafi masaukinsa ta bishi dakin sai dai tana zuwa taji ya rufe da key. Wanka yayi ya fito ba dadewa Gambo ya kawo abinci mai rai da lafiya da Awaisu yace ya siyo musu sannan ya bashi mukullan motocin. Duk yadda taso yi masa magana yaki. Gashi bata son basu fuskar ganin yana mata wulakanci.

Shi da yaransa dasu Harisu suka ci abincin suka koshi sannan kowa yaje ya kwanta. Washegari kafin shabiyun rana sun fita Gimbi tana ta tunanin uban me ya kawosu gidan.

Gidansu Gimbi suka je sunyi sa’a iyayenta duka suna gida. Bayan gaishe gaishe Alh Mudi bai boye musu mamakinsa na ganinsu ba saboda baiyi zato ba.

Anti Baraka ita ce tayi musu bayanin dalilin zuwan nasu. Domin shaida harda hoton Maamu a asibiti ta nuna musu. Mama tana gani sai kuka. Idan kaga Maamu a lokacin da cuya kace zata yi rai ma. Shi kanshi Alh Mudi idanunsa ja sukayi yana mai bakincikin Gimbi tsatsonsa ce.

“Alh Harisu wallahi na baku wuka da nama duk abin da kuka ga ya dace kuyi mata domin huce wanan bakincikin kuyi. A matsayina na mahaifinta kuma nayi alkawarin zamuje fika dubo maamu kuma mu basu hakurin bata musu zuria.”

Mama kuka ne kawai yaci karfinta ta shige daki ta barsu. Allah Ya isa Bebi.

Alh Mudi ya jajanta musu sosai karshe dai sun tsayar da magana akan Awaisu zasu je har gidan su yiwa Gimbi fada. Mamakin dalilinsa na kin sakinta ma sukayi. A ransa yace idan har ya saketa wallahi taci bulus karawa gaba zatayi wani mai rabon wahalar ya dauka.

Washegari da safe su Harisu suka kama hanya suka koma.

Duk bakin nacin Gimbi fita ta gagara. Ga kudi ta turawa Ovi masu yawa sunce an karbo magunguna amma babu damar kawowa gidan. Gimbi tayi haukan tayi borin duk a banza. Shi tsoro ma yake kada ta bata masa yara.

*****

Yau kwanansu Awaisu biyar da komawa Abuja Rumana tana cin kosai bayan tayi buda baki na azumin nafila da takeyi ranar litinin da alhamis taji wayarta tana ringing. Tun da ya bata wayar bata bawa kowa number ba kuma bata kira ba. Ajiyarta take yi kawai.

Uncle taga an rubuta tayi saurin yin baya kamar shine da kansa. Mama tana kula da yadda tayi ta dan sha kunu tace ta shiga daki ta dauka mana.

Gabanta yana faduwa ta dauka ta kara a kunnenta a dan tsorace.

“Assalam alaikum”

Wani sanyi yaji ya ratsa masa zuciya ya danyi murmushi a ransa yana mamakin yadda yake jin Rumana.

“Princess baki nemana ko? Har yanzu baki fara yi min son so din bane”

“Ina wuni” ta gaishe shi zuciyarta tana ta bugu.

“Ba amsawa zanyi ba tunda baki nemeni da kanki ba. Dama kira nayi naji ko kina da bukatar wani abu”

Murya can kasa tace “babu komai”

“I miss you”

Wani irin faduwar gaba taji shima kuma sai da yaji kunyar abin da ya fada mata. Amma sai ya sami kansa da son jin amsarta

“Baki ji me nace ba?”

Tunawa tayi Umman Lagos tace mata ta karbi kaddararta kuma tayiwa Awaisu biyayya. Budar bakinta sai cewa tayi.

“Uncle I miss you too” kit ta kashe wayar ta dafe kirji tare da kurma ihu. Ita wallahi kwatantawa taso yi a zuciyarta taji ko nan gaba zata iya fada.

Mama ce ta shigo dakin da sauri tace me ya sameta. Rumana dafe da kirji tace

“Babu komai”

Tsaki Maman tayi ta fita daga dakin.

Awaisu kallon wayar ya rinka yi cike da mamaki kafin ya tashi ya bude wardrobe dinsa. Fika zaije gobe tunda zai kama asabar ya dawo lahadi kawai don ya ga Rumana.Bayan Awaisu ya gama hada kayansa sai kuma ya fara tunanin me zai cewa su Harisu idan yaje. Kullum suna waya, karewa ma Harisu ne mutum na karshe da ya kira kafin ya kira Rumana. Kuma bai ce masa zai je ba. Dan tsaki yayi tare da jifa da jakar yana murmushi. Wai shine yau yake kunyar Harisu mutumin da kafin Gimbi ta fara gwara masa kai baya boye masa komai. Da ‘yar wani ya aura har shawara zai nema wurinsa akan yadda zai shawo kanta, amma yanzu babu hali. Can kamar an mintsine shi ya tashi da saurinsa ya dauko waya yana dariyar samun mafita.+

Anti Ummukulsum ya kira. Duk gidan idan aka cire Harisu to bashi da ta biyunta cikin ‘yan uwansa.

Tana daki ‘autarta cikin mata wadda ta kasance tsiransu da Rumana babu yawa don bai kai shekara ta bawa Rumanan ba ta kawo mata wayarta da ta bari a kitchen.

Ganin sunan Awaisu ta dauka ta soma tsokanarsa.

“Ango kasha kamshi”

Dariya yayi suka gaisa cikin barkwanci. Dan shiru yayi kamar tana wurin ya dan sosa kai

“Yayata ta kaina alfarma fa nake nema”

“Dama wannan waya cikin dare ai nasan ba a banza ba. Me kake so?”

“Ina son tahowa ne gobe…” dan dakatawa yayi domin jin me zata ce.

Anti Ummukulsum ta nunawa Iman kofa alamun ta fita.

“Awaisu kada ka sami matsala a wurin aikinka fa. Yaushe ka koma har zaka dawo.”

“Kwana daya zanyi. Ranar lahadi da wuri zan tafi in sha Allah”

Dan tsoro taji “ko dai wani abu ya faru?”

“Ko daya. Zancen gaskiya amaryata nake son gani”

Dariya sosai ta rinka yi masa tana tsokanarsa wai ya zama sabon shiga. Shi dai bai kula ba ya roketa akan ta san yadda zatayi Rumana ta wuni a gidanta gobe yadda idan ya iso zai taho nan su hadu saboda yana kunyar Harisu.

“Kinga daga tafiyata a ji na dawo bansan yadda zan hada ido dashi ba. Kuma gaskiya ina son ta saba dani a matsayin miji kafin ta tare”

Anti Ummukulsum tace “Da gaskiyarka amma tarewar nan fa naji ana shawarar ko nan da sati hudun da kace zaka tafi da ita tayi karatu zata tare kawai.”

Murmushi yayi saboda ko kadan bai so ba da matan Harisu suka dage wai sai ta gama makaranta zasuyi biki. Shi ko me suke bukata zai basu idan ta taho karasa makaranta ta tafi kenan ita da Fika sai ziyara.

Yaji dadi yadda yayar tasa ta bashi hadin kai zata aika Rumana tazo da wuri. Shima cewa yayi yana asuba zai taso

“Amma me yasa baka taho yau ba bayan kun taso aiki?” Ta tambayeshi

” ‘Yar taki akwai mulki. Sai yau tayi min kiran da dolena nazo” ya kare yana dariya.

Ji yayi Anti Ummukulsum ta dan dake murya “Ba kayi min dadin baki zan dauko maka matarka ba, wallahi kada kasa naji kunya nan gaba, ka dai san me nake nufi…”

Dariya yake yi sosai harda rike ciki. Sannan yayi mata alkawarin bazaiyiwa Rumana komai ba. Tace gara dai ko meye idan tazo gidansa su karata amma ba da ita ba. Cikin nishadi sukayi sallama ya dan kashingida akan gadon yana danna waya daidai sunan Rumana kamar ji yake kamar ya sake kira.

Gimbi ce ta turo kofar fuskar nan a hade tazo ta tsaya masa a ka. Ko dagowa baiyi ba bare ya nuna mata cewa ya ganta. Hannu tasa ta  daki gefen gadon.

“Malam ina da magana”

Har lokacin bai dago ba ta fizge wayarsa tayi jifa da ita can karshen gadon. A daidai lokacin Abba yana yiwa Rumana downloading applications na karatu a wayarta yaga kiran. Sai da ya daga sannan ya mika mata ya tashi yace idan ta gama ta kai masa daki ya karasa. Hannunta har rawa ya rinka yi ganin sunan wanda ya kira. Ita da take jin kunyarsa me zaisa ya kuma kira. Haushi Abba ya bata don da ita ce da kyar idan zata daga wayar. A hankali kamar tana tsoron zai kamata ta dan kara wayar a kunnenta. Muryar Gimbi da taji yasa tayi kokarin kawar da wayar da sauri sai kuma ta fuskanci ba da ita take maganar ba.

STORY CONTINUES BELOW

Yadda tayi masa jifa da waya haka ya tashi ya janyo hannunta ya wurgata kan gado yana daga tsaye ya dora kafarsa daya a kan gadon tare da dan rankwafowa.

“Koda wasa Gimbi kada ki kara taba min waya bare har kiyi min jifa da ita”

Wata muguwar harara ta sakar masa don bata tsoron ko me zaiyi mata.

“Woooooo ka dai ji kunya ka rasa wadda zaka aura sai ‘yar cikinka. Iyayenta kwadayi kai kuma son zuciya. Don kana waya da shegiyar yarinyar nan zaka tsareni da ido kace kada na sake taba maka waya. Idan na taba ka kasheni sai nasan cewa kaji haushi”

“Kin gama?” Ya tambayeta yana kara matsowa kusa da ita.

“Gamawata shine ka barni na fita daga wannan kurkukun saboda auroni kayi ba zaman prison nazo ba”

Tana rufe baki yasa hannu ya kamo labbanta a tsakanin babban yatsansa da manuni ya matse iyakar matsa. Kokarin cire hannunsa tayi saboda azaba har tsakar kanta shi kuwa ya damke hannuwan da hannunsa dayan. Fuskarsa ce ta birkice babu alamun wasa ko kadan.

“Ina so wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da zaki zagar min mata. Idan baki sani ba to ina mai sanar dake wallahil azim a cikin abin da bai kai sati biyu ba Rumana ta shiga raina ina yi mata son da bana fata wata mace ta sake samun gurbi a zuciyata irin yadda ta samu. Aurenki Gimbi *kashe fitilar* rayuwata ne ya sanyani cikin duhu. Aurenta kuwa tun a yanzu nasan daidai yake da *kunna fitila* na ga haske a rayuwar da kika mayar bakikkirin”

Yana magana yana murje mata labbanta radadi na shiga ga zafin maganganunsa gareta. Idonta ya cicciko zata yi kuka ya girgiza kansa.

“Kada ma ki fara yi min kuka don baki ga komai ba. Ina fatan ko daidai da rabin son da nake yiwa Princess dina na samu daga gareta. A lokacin ne zakiyi kuka Gimbi. Nayi miki alkawari sai na baki mamaki kamar yadda kika sa kafa kika take soyayyata gareki kika nemi hallaka min mahaifiya.”

Sakar mata bakin yayi da yake tana da hasken fata bakin nan yayi jawur tasa hannu tana shafawa tana hawaye. Awaisu tayar da ita yayi yace ta fitar masa daga daki. Wani irin kallo take yi masa mai wuyar fassara. Yayi kama da kallon idan na sami dama sai na rama….

Sai da ya bari ta kusa kofa yace “nayi mantuwa”

Gimbi ta juyo idanun nan sun kada sosai.

Awaisu kwanciya yayi a kan gadon ko kallonta baya yi yace “wai dama ma’anar shegiya da kika kira min mata zan fada miki. Kinga wannan kalmar a tawa fahimtar ba ta ‘yar da aka haifa a titi bace . Kalma ce ta matan da basa ganin darajar iyayensu balle suji maganarsu. Irin matan nan da suka fahimci aure a matsayin juya miji da ganin bayan suruka. Irin wannan matar Gimbi itace ta dace da kalmar. Saboda haka the next time da kika ji kina neman wadda zaki zaga da wannan kalmar to ki nemi mudubi ki kalla. Duk fuskar da kika gani itace she….  “

Wayarsa ya hango tana haske kuma lokaci yana tafiya. Alama dai ta cewa ko dai an kira shi ya daga ko kuma shi ya kira. Bai karasa fadin abin da yayi niyya ga Gimbi ba ya daga wayar ya saka a kunne yana adduar Allah Yasa bata ji me suke cewa ba.

Tun da Rumana ta dauki wayar ta soma kuka da taji maganganun da Gimbi ta yaba mata da iyayenta. Duk da taji sanyi a ranta saboda Uncle ya wanke Gimbi sosai amma a tsorace take. Me zai kaita gidan wannan mata a matsayin kishiya???

“Rumana kada ki kashe min waya magana zamuyi.” Yasan indai bai hanata ba tabbas kashe wayar zatayi don ta gigita da taji muryarsa kuma yana jin sautin kukanta.

Ajiyar zuciya kawai take saukewa saukinta ma ita kadai ce a wurin. Gimbi kuwa buga kofar tayi iya karfinta ta fita domin cigaba da tsayuwarta a dakin zai sa zuciyarta ta buga.

Kwantar da murya yayi sosai ya fuskanci wayarsa ya manta da wata Gimbi

“Banda abubuwan da suka faru dake da Maamu kinga irin rayuwar da Uncle dinki yake yi a gidansa. Umm Ruman don Allah kiyi min son so ko yaya ne domin na samu sauki a rayuwata.”

STORY CONTINUES BELOW

Rasa abin fada tayi ta share ido kawai tana jinsa. Abu daya ke yi mata yawo a zuciya shine ta bar jin tsoron Gimbi. Zata yi kokarin danne zuciyarta ta dena nuna tsoro a gabanta ko don ta tsira a gidan.

“Yanzu haka zamu zauna dake kullum babu magana. Kuma bayan nasan kinyi missing dina” yayi maganar a sigar wasa.

Da sauri kamar wani zai rigata tace “wallahi banyi ba dazu ma subutar baki ce”

Tamkar yaro zaiyi shagwaba taji yace

“Ayya Umm Ruman maganar nan kamar saukar tafasasshen ruwan zafi a tsakiyar watan March haka najita”

Yana ji Rumana ta soma dariya harda kyakyatawa. Dama haka take ba wuya tayi murmushi ko dariya. Rayuwar gidansa ce ta canjata daga yarinya mai kazar kazar da yawan fara’a zuwa shiru shiru.

Shima dariyar yayi sannan yace “Ina yi miki son so Rumana, don Allah kada ki bari na dade ina jira kema ki yi min irinsa. Nayi miki alkawarin baki dukkan kulawa kinji Princess dina”

Maganganunsa sunyi mata nauyi dadinta daya ma a waya ne kila da ta tashi babu shiri. Shima Awaisu da yasan ya soma janyo hankalinta kyaleta yayi yace taje ta kwanta amma kafin nan ta yawaita addua.

*****

Karfe goma na safe Anti Ummukulsum ta kira Maman Rumana tace don Allah ta turo mata ita tana nemanta. Mama tasan neman baya wuce nasiha game da aurenta tace zata taho nan da azahar. Anti Ummukulsum tace a’a yanzu take bukata don Allah saboda tana da uzuri a gabanta. Haka tayi ya ‘yan dabaru dai Mama ta turo Rumana harda kaya set biyu wai kwana zata yi.

Kafin shabiyu ta isa gidan Anti Ummukulsum tasa Iman rakata gidan kunshi nan kusa dasu. Bayan sun dawo Iman tayi mata kitso shiku kananu duk bisa umarnin Antin. Rumana dai bata san dalili ba tunda anyi mata lallen bati shikenan.1

Kafin tayi alwalar laasar Anti Ummukulsum din ta sake cewa tayi wanka. Iman ta kalla tana son tambayarta ko tasan dalili ita kuwa sai dariya take kasa-kasa.

*****

Biyu da rabi a Fika tayiwa Awaisu. Yaran Harisu na ganinsa sai murna. Ihunsu ya sanarwa su Baaba zuwansa.

Da ya shiga ciki Harisu baya gida yaje dakin Maamu ya gaisheta. Kamar ba ita ba ta kara cikowa ta murmure. Abinci ne mai rai da lafiya da fruits ake bata kullum banda su madara, nama da kwai. Duka sunji dadin ganinsa. Bai jima ba ya tashi ya tafi dakin da yake sauka. Mama uwargidan Harisu ke da girki har tana mita bai fada musu zai zo ba da tasa an gyara dakin. Wanka yayi ya kimtsa cikin kyakkyawar shiga ga kamshin da baya rabuwa dashi yana tashi.

Da hularsa a hannu ya shiga daki wurinsu Maamu yace zai fita.

“Daga zuwa kamar ana korarka zaka fita” inji Maamu.

Dan sunkuyar da kai yayi “gobe zan tafi ne shiyasa nake son gama komai a yau”

Baaba tace “har menene ya taso ka duk nisan tafiyar nan a yau kuma ka juya gobe?”

Anti Amarya tana dakin ta tuntsire da dariya ganin yadda  kunya ta hana shi sukuni. Babu wanda yasan Awaisu da kunya irin wannan sai fa yanzu da ya auri Rumana.

Tana ta dariya tace “Don Allah ku barshi ya tafi. Yazo bai ga amaryarsa ba yaushe  zai zauna”

Maamu ta hau tafa hannu “da gaskiyar Haj. Umma da tace gara ayi bikin da wuri.. Baaba kinga ikon Allah yaran zamani”

Baaba dadi taji har ranta Awaisu ya nuna da gaske yake son Rumana tace “tashi ka tafi kaji. Tana gidan Ummukulsum duk da dai yanzu zuciyata ta bani hadawa kuka yi kai da ‘yar uwarka aka ce Rumana taje can”

Godiya yayiwa Baaba wai ta taimake shi da ta sallame shi da wuri. Maamu ta jefeshi da lemon hannunta tana cewa babu mai kai Rumana gidansa sai ta gama makaranta. Shi dai fita yayi yana dariyar rigimar da yaji sun fara ita da Baaba akan tarewar Rumanan.

STORY CONTINUES BELOW

Yazo fita Maman Rumana kuma zata shigo gidan. Rasa me zasuyi duk su biyun sukayi. Da can barkwanci ke tsakaninsu yanzu kuma matsayi ya canja. Da hular tasa a hannu dai ya durkusa harda sunkuyar da kai

“Mama ina wuni”

Ai kuwa Mama ta rikice tana cewa ya tashi shi kuma yana cewa sai ta amsa yanzu ita babarsa ce. Karshe dai ya tashi suna dariya yace

“Daga yau irin gaisuwar da zan rinka yi muku kenan don gaskiya kunyarku nakeji”

“Ka rufa min asiri don Allah kada ayi mana dariya”

“Nagode da kika amince da auren nan. In sha Allah zan rike miki Rumana amana”

Dan hawaye ne ya taho mata “dama can amanarka ce. Allah Ya baku zaman lafiya. Amma idan ka kara durkusa min kararka zan kai”

Daga nan ta shige tana godiya ga Allah da Ya bawa ‘yarta miji kamar Awaisu. Fatanta su zauna lafiya. A nasa bangaren sai yanzu ya sami kwanciyar hankali saboda baya so ko kadan ya zauna da Rumana wani cikin iyayenta baya so.

Mota ya shiga ya sanar da Harisu isowarsa amma yanzu zai fita. Harisu shima yaji dadi domin ya fahimci zuwan na waye yace sai ya dawo zasuyi magana.

Abinci da kayan sha Iman da Rumana suka kai falon mijin Anti Ummukulsum suka jere. Zasu fita ta dan ja hijabin Iman.

“Yaya babba wai don Allah me yake faruwa ne? Naji kunce Abbanku yana Kaduna waye zai zo? Ko bako zakiyi?”

Iman tace “hajiyar dadin baki ni dai bazan fada miki komai ba idonki zai gane miki.”

Gabanta ne ya fadi suna fitowa tana hada ido dashi. Idanunsa a kanta ta fara rawar jiki kamar wadda tayiwa sarki karya. Dauke kansa yayi suka gama gaisawa da Anti Ummukulsum sannan ta ce da Rumana ta shiga dashi falon ta zuba masa abinci. Hannun Iman tayi yunkurin kamawa ita kuwa ta zille ta matsa gaba ta gaishe shi ta shige ciki.

Idanu kamar zatayi hawaye ta kalli Anti Ummukulsum sai ta ga tana girgiza mata kai ta dan sha kunu kada ma ta soma kuka. Tana kallo itama ta shige ciki aka barta da Uncle Awaisu a wurin.

Gani yayi ta kasa motsi ya tako gabanta yazo ya kama hannunta ya shiga falon da ita. Bata san yadda zata kwatanta me taji ba da ya rike mata hannun. Shi kuma bai saketa ba sai da ya je gaban kujera ya dafa kafadunta ya zaunar da ita.

Kasa kallonsa tayi ga kunya ga mamakin ganinsa a Fika a lokacin da bata yi tsammani ba.

Gabadaya tayi masa kyau. Fuskarta dauke da kwalliya daidai misali ta saka riga da skirt sai karamin mayafi da ta yafa maimakon dankwalin kayan.

“Wai me zanyi ki rinka yi min magana ne? Baki san musamman na taho wurinki kawai don kice min *I miss you* ba. Ko mun girmi wannan sai dai a fadi na gaban” ya kashe mata ido yana dariya.

Hannuwanta tasa ta rufe fuska tana girgiza kanta “ni dai Uncle kunyarka nake ji”

Zama yayi a kujerar dake kallonta ya duku kadan “nima fa kunyarki nake ji Princess. Yanzu sai muyi tunanin maganin kunyar tunda dai da bama ji ko”

“Eh” ta ce a hankali.

“To ki fara da yimin sannu da zuwa. Ance yana rage kunyar mata da miji”

Murmushi tayi masa wanda ya kara mata kyau ta turo baki “Uncle nifa ba ‘yar yarinya bace zaka yi min wayo”

Tasowa yayi daga kujerar da yake ya zauna kusa da ita. Ta ganin haka ta matsa shima ya matso. Sake matsawa tayi taga ya kuma matsarta. A karo na uku ta kai jikin hannun kujerar shima ya   matso ya zama babu wurin gudu. Mikewa tayi ya janyota tare da sakale hannuwansa ya zagaye kafadunta.

A kunnenta yace “Ina zaki gudu kuma ke da zaki nuna min girmanki”

Ji take kamar ta shige kasa ta rufe idanunta  “Wasa nake yi Uncle yarinya ce ni ….sannu da zuwa. Yaya hanya? Ya su Amir?”

Kansa ya dora a kafadarta yana murmushi cike da nishadi

“Ni ban yarda ba gaskiya kin girma. Matan da suka girma kinsan da yadda suke tarbar mazansu ma kuwa?”

Haushin kanta taji me ya kaita cewa ita babba ce. Gashi yana mata maganar manya duk kunya ta hanata sakat.

“Ki juyo na fada miki yadda manya matan suke yi” ya fada yana kokarin juyo da fuskarta.

Maganar wata malamarsu a Abuja ‘yar Kano ta tuna a rude  tayi saurin cewa “Wallahi da gaske ban girma ba. Malamar mu ta Civic education tace mu duka ‘yan ajin kwailaye ne kuma wai kwailaye yarane”

Duk da ta iya Hausa amma akwai kalmomin da suke kasancewa baki gareta irin wadannan.

Dariya sosai Awaisu yayi har lokacin kuma bai saketa ba. Fuskarta ya rike da tafin hannuwansa ya matso da ita kusa da tashi.

“Allah Ya faranta miki yadda kika faranta min. Ke kyauta ce gareni daga Allah. Allah Ya bani  ikon rikeki amana kinji. Yayi min gata da yawa Ya kara min da Umm Ruman”

Kokarin sauke kanta kasa take yi ya hana

“Kada ki hada rowar magana da rowar ganin fuskarki. Wannan malama gaskiya idan mun koma ya kamata kije ki fada mata mijinki yace ke ba kwaila bace”

” Da gaske Uncle?”

Daidai kunnenta ya matsa ya fada mata wace ce kwaila

Ihu ne kawai Rumana bata yi ba saboda tsabar kunya tamkar ta shige cikim kujerar. Shi kuwa Uncle Awaisu yadda take yi ne ya kara sanya masa nishadi a zuciyarsa ya kallon shirmen yarintar Rumana yana dariya.Hanyar fita ta soma nema yace ta dawo ta zuba masa abinci. Haka nan ta dawo ba don taso ba ta zuba ta mika masa plate din. Hanata tafiya yayi yasa ta zauna jingine da kujera da plate din a cinyarta shi kuma ya zauna daga gabanta yana ci. Duk lokacin da ta dago kai sai sun hada ido sai yayi murmushi.+

“Kin iya girki?” Tambayar tazo mata a bazata.

“Uhm” kawai tace

“Duk abinki sai kinyi min magana yau….kwaila kawai”

Mayafinta taja ta rufe fuskarta a kunyace “haba don Allah Uncle”

Yayi dariya “indai ba ita bace lissafa min abubuwan da kika iya dafawa”

Dan kallon sama tayi kamar tana lissafi “tuwo, shinkafa, taliya, indomie, macaroni, suyar kwai da abubuwa da yawa”

“Idan na sake dawowa abincinki nake so naci.”

Nan fa ake yinta. Girki yanzu take kokarin sake kwarewa. A da can tana koya a gida don har tana yi ma. Zuwanta Abuja da aka shata mata layi da kitchen yasa bata wani girki. Wanda ta iya dinma duk ta dan manta su. Dawowarta Fika ne Mamanta kamar tasan aurenta da wuri zai zo ta sa ta kullum shiga kitchen. Samun kanta tayi da tsoron kada yazo yaci abincinta taji kunya.

“Uncle ba fa sosai na iya ba”

“Ni dai zanci a haka sai na tantance. Gobe ta nan zan biyo kafin na wuce in sha Allah. Ki hada min breakfast  da kanki please”

Tuni kwakwalwarta ta fara laluben me zata dafa. Ko dai tayi shiru ne kawai ta bashi na gidan tayi sai tace masa ita tayi?

Hannunsa ya dan kada a gaban fuskarta  ta dawo daga duniyar tunanin. Plate din ya karba ya ajiye sannan ya kama hannuwanta duka biyu ya rike sosai a cikin nasa. Wani taushi yaji har baya son saki.

“Jiya kinji duk yadda mukayi da Gimbi a waya ko?”

“Kayi hakuri Uncle Allah na zata kaine ka kira” ta fada a dan tsorace don yana daga cikin abin da ya hanasu tun suna kanana yana zuwa gidan. Yace jin hirar wasu da bai shafeka ba babu kyau.

“Na sani Umm Ruman. Amma idan kika sake jin irin haka kiyi saurin kashe wayar. Kinga jiya da kyar na iya bacci saboda nasan kinyi kuka”

Bai ma gama ba yaga idon ya cika da hawaye.

“Kada kiyi min kuka mana Princess.” Ya girgiza kansa.

Hawayen ne kawai ya zubo ba shiri Awaisu ya tattarota gabadaya ya dorata akan cinyarsa yana shafa saman kanta. Bakinsa dai bazai iya fassara yadda yake ji ba a lokacin. Itama duk da bata gama gane me take ji akan Uncle Awaisu ba kunya mara misaltuwa ce ta kama ta.

“Nayi zaton Umm Ruman dina jarumar mace ce wadda abu irin wannan ba zai sa naga ragwantarta ba”

Hawayen ya goge mata da yatsansa ta rinka sunkuyar da kai. Suna haka wayarsa tayi ringing. Kamar ya share don baya son komai ya shigar masa dan lokacin da yake dashi tare da Rumana. Sake kira akayi yaga sunan Harisu ne sai ya dauka.

Rumana tayi ta kokarin zamewa daga jikinsa ganin hankalinsa ya tafi kan wayar yayi mata wani riko da hannu daya wanda yasa dole ta hakura. Tsoronta kada wani ya shigo ya gansu a haka. Ina zata saka kanta idan haka ta faru.

Bayan ya gama wayar yana rike da ita suka mike tsaye amma fuskarsa ta canja.

“Zan je gida Yaya yana nemana. Bansan dai ko menene ba amma yace min kowa lafiya yake”

Yadda yake magana Rumana ta gane hankalinsa a tashe yake. Gabanta har yana faduwa ko Maamu ce. Shima ya kula nata hankalin ya soma tashi yace ta kwantar da hankalinta babu komai in sha Allah.

STORY CONTINUES BELOW

“Uncle ko na raka ka?” Tayi maganar da karamar murya. Tausayinsa take ji amma bata son fadin abin da zai zama tayi rashin kunya. Tasan dai da bata aure shi ba zata dage sai ta bishi ne.

“Kiyi zamanki zanyi kokarin dawowa anjima don bamu gama hirar ba”

Fitowa yayi yayi yayarsa sallama ya tafi ita kuma ta kwaso kwanukan da yaci abincin.

*****

Dakin Maamu ya wuce kai tsaye. Zuciyarsa ba karamin bugu take yi ba kafin ya karaso gidan ko jikinta ne. Yana daga labulen dakin wani mummunan wari ya daki hancinsa. Hannu yasa ya rufe hancin yana kallon su Harisu dake zaune a wurin kowa ya toshe hanci.

Da kyar ya iya hadiyar yawu yace “warin meye wannan Yaya?”

“Ka tuna ranar da Maamu ta dage a sallameta da Dr. Yana tace ta kama Gimbi zata shafa mata wani abu?”

“Eh” ba sauraren Harisu yake sosai ba tunda idanunsa suka gane masa abin dake warin. Wani abu ne kamar izgar doki amma daga kasansa yana da kauri sosai. Ta wurin kaurin ne wani irin ruwa mai wari ke fita.

Abba da yake dakin ya daure ledar ya fita da ita sannan Harisu ya cigaba da fada masa ko menene abin.

“tun safe Dr. Yana ta kirani wai idan ina da lokaci naje asibitin. Nace bani da halin zuwa to sai Allah Yasa Abba bashi da komai a makaranta yau shine na tura shi. Wannan abin da ka gani shine Gimbi taso shafawa Maamu kwanaki. Wai kwana biyu kenan suna jin wari daga harabar dakin da Maamu ta kwanta an rasa ko meye. Sai da safe yau wani mai shara ya gano shi da alama ta taga aka jefa.”

Gaban Maamu Awaisu yaje ya zauna ya rungumota yana hawaye itama tana yi. Wace irin masifa ce Gimbi take bibiyarsu da ita. Wato har a gadon asibiti bata kyale masa uwa ba. Duk wani dan guntun tausayinta da yake tunanin akwai ko zai iyaji a gaba a take ya fice masa daga rai kamar sauke dutse mai nauyi.

Baaba ma kukan take yi bare ma da suka ga sunan Maamu barobaro a daidai inda warin yake fitowa. Abba  da ya fita da abin Harisu da Awaisu ya jira suka fito suka tafi dashi can bayan gida aka kona.

Haka Awaisu ya karasa wunin jiki babu kwari. Tare da Harisu suka yi sallar Magriba da Isha. Bayan sun dawo daga sallar Isha Baaba ta kira shi.

“Awaisu wannan damuwar fa bazata chanja komai ba sai dora maka ciwo. Kayi hakuri tunda Allah Ya taimakemu bata sami nasara ba”

“Baaba yanzu fa da ta tabata dashi kila ko kallon Maamu bazan sake ba. Wai me Gimbi take nema ne a tare dani? Babu abin da na rage yi mata saboda zuwan su Maamu Abuja”

Baaba tayi dan murmushin takaici “baka san mata ba kenan. Wasu a rayuwarsu su gansu da miji sai yadda suka ce shine babban burinsu. Akwai matan da suke kishi da surukansu. Kaga mace na kishi da matar da ko ita matar dan ta sa ido lallai duk abin da zakayi nata yafi na mahaifiyarka. Zamani ne yazo yanzu ayyukan sa6o sun yawaita. Wani abin idan kaji sai ka rasa ina hankulanmu suke tafiya. Saboda abin duniya da jindadi na takaitaccen lokaci sai mu koma tamkar jahilan farko. Ga addini amma bama aiki dashi”

Kansa ne yaji har ciwo yake masa saboda tunani da damuwa yace “to ni yanzu yaya zanyi da su Haris? Gimbi mahaifiyarsu ce ina tsoron kada abubuwan da take yi suyi tasiri akansu su fara koyi da ita”

Baaba tayi saurin daga hannu “Allah Ya kiyayemu mugun ji da mugun gani. In sha Allah Allah zai tsare musu imaninsu. Amma ina tunanin me zai hana ka kaisu gidan Alh Mudi kafin asan yadda za’ayi da uwar.”

Shawarar Baaba tayi masa yace in sha Allah zaiyi magana da iyayen Gimbi. Don har zuciyarsa baya so yana fita yana barita dasu. Su Maman Gimbin ma sun kira Harisu zasu zo ranar laraba.

“Wai bazaka tashi ka tafi wurin matarka bane?” Baaba ta fada masa tana kallonsa da tausayawa. Duk ya zabge ma tun da aka fara case din.

Agogonsa ya kalla ya dan dukar da kai “Baaba dare yayi ne. Kinga har tara saura. Wallahi abin nan ne duk ya tsaya min”

STORY CONTINUES BELOW

“Allah Sarki idan damuwa tayi yawa ai babu inda ya dace da mutum sai wurin masoyinsa” tana magana tana dariya.

“Da safe zan biya kafin na tafi” ba dai haka yaso ba shi da yazo musamman saboda ita.

Dan daure fuska Baaba tayi “ai ni bansan dalilin da yasa kuka kulla tafiyarta gidan Ummukulsum ba. Banda ragon azanci tunda a nan zaka kwana ai sai ka fi samun lokaci tare da ita. Kira min yayar taka muyi magana. Sauran ma zamu hadu dasu su tsara yadda za’a danyi taron biki cikin wata mai zuwa ta tare”

Wayar ya mika mata bayan yaji ta shiga. Tana dauka ta fara mitar me ya hana shi dawowa. Baaba ce ta soma labarta mata me ya faru sannan tace maza Rumana ta shirya yanzu zaizo ya dauketa. Ummukulsum tace ta yarda amma don Allah da safe a dawo da ita don akwai shirin da zata fara. Dama Awaisun ma ganin mijinta baya gari bai dace yayi musu zuwan dare ba haka shiyasa yaso hakura.

Cikin minti shabiyar yayi saurin watsa ruwa ya shirya cikin kananun kaya ya fita.

A can gidan Anti Ummukulsum kiran Rumana tayi tace maza taje tayi wanka tayi kwalliya amma ba mai yawa ba.

“Anti wanka a daren nan kuma?” An katse mata kallon da suke yi da ‘yan uwanta.

“Maza ki shige kuma wallahi banda jika-jika. Kwalliya kuma yar kadan ta isa. Mijinki zai zo mayar dake gida amma gobe zai dawo dake kafin ya wuce.”

Ji tayi ana neman kulle mata kai. Ance tazo ta kwana yanzu kuma ta tafi ta dawo. Ba dai tayi musu ba taje cika umarni.

Har Awaisu ya iso Rumana bata gama shiri ba. Shi da Anti Ummukulsum suka zauna yana bata labarin abin da ya faru. Itama ta kara jin tsanar Gimbi tunda bata ji kunyar idanunsu ba tazo raba da da mahaifiya. Dama tana son ganinshi game da Rumana. Dazu da zata ci tuwo ta kamata ta gutsira shi ta soya mai da yaji wai a haka zata ci. Dama gata ba wani jikin arziki ba musamman ga yadda yunwa ta kassarata. ‘Yan sinadaran gina jiki duk babu isassu ga aure daga sama. Shawara ta yanke dole ta gyara ‘yarta don wanda ya zauna da Gimbi sai mace tayi da gaske zata iya zama da mijinta. Magunguna da ake sha kuma ba wani tasirin arziki zasuyi ba matukar babu cima mai kyau.

“Ango don Allah ina bukatar ‘yan kudi na gyara amarya”

“Kuna cewa angon nan kunya nake ji” yayi dariya.

“tunda kunya kake ji to tashi ka tafi na fasa baka ita.”

“Tuba nake ranki ya dade. Yanzu dai nawa kike bukata?”

“Duk abin da ya samu…amma fa ka saki bakin aljihu gyaran gaske zamuyi”

Alkawarin taho mata da kudin da safe yayi domin a lokaci bashi da cash da zai isa ya bata.

*****

Da sallama Rumana ta shiga falon. Ganin Anti Ummukulsum yasa tayi saurin juyawa zata gudu.

“Dawo ke muke jira dama. Sai da safenku bari na shiga ciki.”

A bakin kofa ta rabe har Antin ta fito a hankali tace ta saki jikinta mijinta ne fa. Murmushi kawai tayi ta kutsa kai cikin falon suka yi karo da Uncle Awaisu yana fitowa.

Janyota yayi da sauri ganin tana neman dafa bango kada ta fadi.

“Gaskiya akwai matsala. Haka kike ba nauyi, yar wannan turewar tana neman kayar min dake”

“Matsawa fa nayi don kada kace na tureka amma baka ji nauyina ba….”

Sama taji yayi da ita maimakon su fito ya koma cikin falon da baya yana dauke da ita.

Salati ta soma yi sai kuma ihu ya biyo baya saboda yadda taji yana neman juyawa da ita ta kankame masa wuya. Yadda take tsoron hajijiya saboda jiri shiyasa bata ko son ta ga anayi.

STORY CONTINUES BELOW

Ihun nata da bai gama fita daga bakinta bane ya makale sakamakon bakinsa da taji akan nata.

Wani irin yanayi suka shiga bare ma Awaisu wanda yaji gabadaya komai ya tsaya masa. Baya tunanin komai sai Rumana da soyayyar da yake yi mata.

Da kyar ya iya kyaleta ya kalli fuskarta ta rufe idanu kamkam jikinta har wani rawa yake yi saboda tsananin faduwar gaba. A hankali ta bude idonta suka sauka cikin nashi tayi saurin kuma rufe su da taga kansa ya sake dukowa gareta. Wannan karon peck ya mata a goshi.

“Kinji kunya ne Princess? Kada ki damu muna nan dake idan kika fara yi min son so da kanki zaki….”

Duk da bata san me zaice ba amma bata son ji don ko da wannan kunyar ya barta tana ganin zata shekara bata dawo daidai ba a gabansa. Hannu tasa ta rufe masa bakin har lokacin yana dauke da ita. Shi ga tsaho ga jikinsa ba’a kira shi mai kiba ko siriri ba ita kuma ga kankanta ga rashin kiba.

Wannan karon a tafin hannun taji ya sake mata wani kiss din ta cire da sauri tana salati.

Dariya yayi ya sauketa yana rike mata hannun “Allah Ya hadani da ustaziyya”

Hanyar fita yaga tayi yabi bayanta batare da ya saki hannun ba. Suna fitowa Anti Ummukulsum ta leko ta sama don taji shiru kamar basu fita ba ta gansu. Dadi ne ya cika mata zuciya tana addu’ar Allah Ya kara musu so da fahimtar juna. Rumana abar tausayi ce matsawar Gimbi tana gidansa sannan ga kuruciya bata san komai ba. Shiyasa dole ta gyarata don ta kara mata daraja a idon miji.

*****

Da kansa ya bude mata ta shiga sannan ya shiga ya tayar da motar. Dan kallonta yayi duk ta takure kamar mai jin tsoronsa. Ya tallabo kansa yana kare mata kallo

“Yau fa na janyowa kaina dama da kyar ake yi min magana gashi yanzu ko sannu da zuwa ban samu ba” muryarsa a karye irin abin tausayi dinnan.

“To ba kaine ba…”ta turo baki kamar zata masa kuka.

“Allah Sarki Princess nine nayi miki ki……”

Hannuwanta tasa ta toshe kunnuwanta “don Allah kada ka fadi sunan”

Ya daga gira daya “Au ashe ma kinsan ko meye “

Cikin sauri tace “a’a ban sani ba”

Dariya yake mata sosai yadda ta rude

“To ki bari na fada miko ko da next time kina so kinsan me zaki ce min”

Tace “Na sani”

ya sake daga gira

“Ban sani ba” tayi saurin gyarawa shi kuwa sai dariya yake yi mata ya manta fiye da rabin bacin ransa. Kafadunta ya dafa

“I love you so much Umm Ruman. Duk da abu ne da wata uku da suka wuce ban taba tunanin zan wayi gari naga rana irin ta yau ba. Amma nasan cewa Allah ne Ya bani ke domin samun sassaucin laifukan da na aikata muku musamman Maamu da bani da tamkarta. Aurenki shine hanyar da tafi cancanta na faranta muku ke da ita. Please Princess ko yaya kiyi min son so dinnan kinji. Yanzu ni mijinki ne. Miji kuma yana taka rawa daban daban a wurin matarsa. Ni uba ne, aboki sannan masoyi gareki saidai na biyun da na ukun bazan iya nuna miki su sosai ba sai kin karbeni a sabon matsayin da Allah Ya hadamu”

Idanunta cike da hawaye saboda maganganun sun shigeta muryarta can kasa tace

“Uncle me ya sameka?”

Yadda take turo baki haka shima yayi “yanzu na ajiye kunya na gama fada miki ina sonki shine zaki ce me ya sameni?”

“Gani nayi kamar kana cikin damuwa lokacin da da na shigo kuna tare da Anti Ummukulsum”

Mamaki ta bashi sosai. Yana rainata ashe wayonta ya wuce yadda yake gani.

“Kin kawar min da damuwar tun dazu. Saura amsata “

Ta rasa menene yake saka mata faduwar gaba yanzu a tare dashi. Tasan dai bata kinsa ko kadan amma wanna matsayin nasa na da yasa ta kasa sakewa har ta fuskanci me zuciyarta take ji game dashi. Gani take yi kunya da nauyinsa da wuya su barta. Amma bata so yaji kamar bata damu dashi ba. Dubi yadda ya rama mata zagin da Gimbi tayi musu. Wannam kadai ya zama matakin farko na canja yadda take ji game dashi.

Yatsunta biyu babba da manuni ta hade tare da dunkule sauran ukun ta daga hannun a tsakiyarsu tana murmushi “In sha Allah”

Ya kalli hannun ya kalleta “Umm Ruman me kenan?”

Aha yau ta kure masa bai san me take nufi ba tace a ranta. Dariya ta soma yana binta da kallo cike da jindadi. Da kyar ta tattaro karfin hali tace

“Uncle idan ka canki me haka yake nufi ….”

Ya sake kallon hannun ta katseta “me zaki bani?”

Dadi duk ya cikata ta sake sosai yau tayi abin da tasan da matukar wuya ya gano.

“Abinci me dadi”

“Kin ma isa…wannan aikin naki fa ba mai sauki bane da gani.”

“To me kake so?”

Bakinsa ya nuna mata yana dariya a hankali.

Shi da ba gwanin kallo ba saboda rashin lokaci tana ganin kamar bazau taba gane wani salo ne na cewa *I love you* ba da take gani a series din Korea da suke gani a dakin Abba.

Karamin yatsanta ta daga shima ya biye mata ya saka nasa yatsan a ciki yace

“Deal! yarinya ki shirya shan mamaki”

Lumshe ido tayi harda dariya tana ganin tayi nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page