DR TAHEER CHAPTER 7 BY UMMU ASHRAF

 DR TAHEER CHAPTER 7 BY UMMU ASHRAF

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kai tsaye ummi ta wuce da ita bathroom bayan ta hada mata ruwan wanka da kanta…tace”yi sauri kiyi wankan ki fito..ki tabbata kin wanke ko ina na jikinki”…Layla dai batace Mata komai ba..don gani take wankan ma sai ance ga yanda zatayi…ummi Kuma na fita ta janyo trolley da aka cikashi da some of kayanda zata fara amfani zasu tafi dashi..ta fiddo Mata kayanda zata sa da inner wears snn ta jiyesu kan gado ta sake rufe akwatin…tana nn zaune Nafisa ta shigo da kabbasa a hanunta tace”yawwa ummi gashi”…ummi ta Mika Mata kayanda Layla zata Sanya jikinta tace”amshi kiyi maza ki turarasu Nafee…bansan meya dauke hankalina baayi turaren ba tun dazu wlh..da yanxu yasha iska”…ba musu Nafisa ta mike tareda jona burner dake ajiye kan bedside a socket..ummi ta miko Mata turarenda zaayi amfani dashi ta zuba cikin burner din..in no time qamshin turaren mai sanyin dadi ya fara tashi a dakin…ta dauki kayanda ummi ta bata tareda dorasu kan kabbasa..ta ajiye burner din a karkashin kabbasan…ta lullube ko ina ruf ya zamana bata inda iska zai shiga ciki.. hakan shi zai sa turaren yaita hawa kan kayan…after ike 10 mins ta sake juya kayan snn ta Kara

turaren..nanma ta barshi Yana tayi…Layla kuwa Saida ta kwashi almost 11 mins snn ta fito daga bathroom…idonta ya kada yayi jajir don ba karamin kuka taci a cikin bayin ba…tana fitowa ummi ta mike tareda komawa bathroom din..wani ruwan ta sake hada Mata mai daukeda madarar turare kala kala..snn ta fito ta sake tura Layla kan ta dauraye jikinta dashi…ba musu Layla ta koma bayin tayi kmr yanda ummi tace…ita kanta taji yanda lokaci daya jikinta ya sake dumamewa da kamshi..bayan ta fito again ummi ta sake bata wani Humra nan ma tabi duk loko da saqo na jikinta ta shafeshi tass da Humra din…zuwa yanxu zaka iya jiyo kamshin da jikinta keyi ko baka kusa da ita…bayan Nafisa ta gama turara kayan ta mikama ummi tana fadin”ummi ga kayan an gama”…ummi ta amsa kayan tareda shinshinasu…Saida ta lumshe ido don jin kamshin dake fita jikin kayan…ba bata lokaci ta ba Layla kayan kan ta sa ajikinta…Layla da keta kokarin danne hawayenta ta amsa kayan…Saida ta fara sa pant da bra snn ta saka kayan…atampa ne blue da touches din yellow a jiki..dinkin riga da skirt ne daya zauna a jikinta das kmr a jikin aka dinka..ummi ta zaunar da ita gefen gado kafin a gama turara lafayan da zaa nadeta dashi…kawai saita fada jikin ummin tareda fashewa da matsanancin kuka…ummi ta shiga shafa kanta tana kakalo murmushi…ita kanta duk abunda takeyi dauriya kawai take..Allah ya sani ba karamin missing dinsu zatayi ba idan suka tafi…ta riga ta saba dasu tun suna kanana…tasan idan suka tafi dole kewarsu ya dameta…tabbas ba don aureba da babu abinda zai rabata dasu sai dai ko mutuwa..+

A bangaren ango kuwa tun yamma dama ya gudu daga gidan Yusuf bayan ya sallami some of abokanshi da suka koma…Sam baison wani rakiya da abokai sukema ango wurin amaryarshi..shi Sam hakan baiyi mai ba..haka nn kawai ka kwashi katti suje suyita kallema mata suna mgn da ita…ba dashi zaayi wnn kwadon ba Kam…a masallacin kusa da gidansu yai sallahn magrib snn yaci gaba da zama a ciki har akai Isha..bayan idar da sallahn yayi add’u’o’i sosae kan aurenshi da Layla saida ya idar snn ya nufi gidan don ganin wainar da ake toyawa.

Kai tsaye part dinshi ya wuce bayan ya hadu da some of family members dinsu dake nn compound sunata tsokanarshi…ya bude daki ya shiga snn ya maida kofan ya rufe..ya karasa tareda kwanciya kan three seater dake parlon..sai ya fada duniyar tunani…yana tunanin yanda zamanshi zai kasance da Layla ba tareda wani abu na aure ya shiga tsakaninsu ba..yanaso yai keeping distance dinshi as he promised amma Kuma yana tunanin how…Allah ya gani shi din ba wai ma’asumi bane snn Shiba karfe bane da zai iya rayuwa cikin gida daya da wadda yakema matsanancin So irin haka Kuma ba tareda ya aikata komai a game da ita ba…yana tunanin ta Ya zai iya coping if suna rayuwa da Layla under thesame roof ba tareda yayi messing  plan dinshi ba…yasan for sure zai iya kasa jurewa wani lokacin..amma Kuma baiso ya aikata abinda zai zama baiyi fulfilling promise dinshi ba..yanaso ne ya bata kulawanda bata taba tunani ba…yanaso ta tabbatar da ita din yake so bawai wani abu na jikinta ba..but how…a wani bangaren Kuma Yana tunanin rabuwa da ummi…yasan definitely zata shiga damuwa na rashinsu sosae..ta riga tayi sabo dasu na tsawon shekaru..gashi ita ba wasu yaran ke gareta ba..shi kadai Allah ya bata sai Layla…yanxu gashi aure zai nisantasu da juna..wnn shine dalilinda yasa ya dage kan umma ta dawo Abuja gaba daya…yasan idan tana nn ummi zata samu saukin kewansu da zatai…and shima zai riga kokari kullum yazo ya gaishesu as hakan zai rage Mata damuwa sosae..itama Layla sai Yana kawota tana ganinsu time to time…yayi nisa cikin tunani har baiji lokacinda wayarshi tai ringing ba..bai kumaji lokacinda umma ta shigo har ta zauna kusa dashi ba…Saida tasa hannu tadan jijjigashi snn ya mike zaune da sauri Yana rarraba ido…umma na mai kallon mamaki tace”tunanin me kake haka Taheer har nai maka 2 missed calls baka ganiba snn na shigo har na zauna bakayi noticing ba..are you alright”…Saida ya sauke numfashi snn yace”lfy Lou nake umma..kawai Ina tunani ne”…umma tace”ai dama ba bacci kaji nace kanayi ba…so nake inji tunanin me kakeyi haka”…ya saki dan smile snn yace”come on ba wani abu bane fa umma”…Yana rufe baki umma tace”tunanin Yaya kakeyi koh”…a hankali Taheer ya daga Mata Kai alaman eh…ita Kuma ta kamo hanunshi tace”kar ka damu kanka kan wnn.. InshaAllah zanyi iya bakin kokarina inga bata shiga wani hali sbd missing dinku ba..dukda nasan ban isa in hana taji kewan naku ba..but i promise bazan bari damuwa ya rabeta ba..she’s my sister afterall..so Nima tana Sona sosae baku kadai takeso ba”…umma ta karasa mgnr da murmushi a fuskarta..tanaso taga ya saki ranshi shima…saida yai Mata murmushi snn yace”na sani umma..nasan bazaki taba barin ta shiga damuwa ba…Allah ya saka maki da alkhairi umma for making everything here possible …thank you for getting me married to baby…without you this couldn’t have happened..so nagode nagode sosae umma…Allah ya saka maki da aljannah”…umma dake murmushi ta janyoshi jikinta ta shiga shafa bayanshi kawai…ita kanta tasan zatai kewansu.. especially shi da kusan duk problem dinshi itake solving…a hankali Taheer yace”am going to miss all of you umma”…still umma na shafa bayan nashi tace”and we are going to miss you both..Allah ya Baku zaman lfy da zuria dayyiba”… Taheer ya amsa da Ameen…cikin hikima umma ta shiga mai nasiha sosae kan zamantakewar aure…dukda tasan ya sani amma Yana dakyau a Kara tunatar dashi..nasihan nata ko na shiganshi sosae har ba karamin kashe mai jiki yayi ba.

STORY CONTINUES BELOW

A can wurin amarya kuwa..ummi da Nafisa nata Mata nasiha itama..Banda kuka ba abinda takeyi..sun dauki tsowon lokaci kafin su gama..Ummi ta dauki lafaya dinta yellow..wanda aka turara da turare shima snn ta nadeta a ciki…tana kallon Nafisa tace”ki kula da ita Nafee..bari inje in samu in Kira Taheer din..ban taho da wayn nawa ba”…Nafisa ta mike tareda karasawa inda Layla take ta zauna..ita Kuma ummi ta fita…Layla ta fada jikinta tana Kara sakin wani kukan…Nafisa ta rungumeta a jikinta cikin sigan lallashi tace”kukan ya isa haka Layla ko kinaso kanki ya fara ciwo ne..kiyi hakuri kinji duk wata mace da haka ta fara…ki nustu sosae Layla domin aure gareki yanxu…mijinki yana bukatar kulawarki sosae don haka kiyi kokari don Allah kiga kin biya mai duk wata bukatarshi…kiyi kokarin sauke duk hakkinshi dake kanki nasan shima bazai taba tauye maki hakkinki ba…sai ki dena wnn shashashancin don ke zaki kula da kanki snn ki kula da mijinki ma..ki zama jaruma Layla banda raki Banda gudun miji duk abunda yace kiyi kiyi mai Layla..duk abunda yace baiso ki bari kinji… InshaAllah zamuzo har gidan naku kafin mu koma..Allah ya Baku zaman lfy”…Layla najin duk abinda ta fada amma bata dena kukanta ba.

Ummi kuwa na fita ta wuce part dinta..Saida ta dauko wayanta snn ta shiga dialing number din Taheer…lokacin ya fito daga wanka..yana shiryawa Kiran ya shigo..yai picking tareda sallama a hankali…ummi tace”ka sameni part din abbanka yanxun nn”…tun kafin yai mgn ma ta yanke wayar…Yana kallon umma ya fada Mata abunda ummin tace…ita ta fara mikewa tace”kayi sauri ka gama ka fito..nasan an gama shiryatane”..Taheer Kai kawai ya iya daga mata..umma ta fita zuwa part din dad din nashi..shi Kuma ya karasa shiryawa snn ya fita.

Umma bata dade da shiga ba shima ya shigo..kanshi a kasa ya nemi wuri ya zauna…ummi na dubanshi tace”to ga Layla nan dai Taheer…ka dauketa ku tafi…I don’t have to remind you kan duk wasu hakkokinta dake kanka cox kai ba yaro bane…inaso ka riketa tsakaninka da Allah Taheer..karka cuceta Kuma kada ka bari wani ya cutar da ita… remember Amana ce yanxu a hanunka..sai kayi kokari kar Amana ya cika..Allah ya Baku zaman lfy ya kawo zuri’a dayyiba”…Taheer kanshi a kasa ya amsa da ameen a hankali…ummi ta mike tareda kamo Layla da har yanxu ke kuka jikin Nafisa…ta kama hanun Taheer din shima ya mike tsaye…kawai saita rungume su gaba dayansu tana hawaye… tasan tafi kowa farin ciki da wnn hadin nasu..da Layla da Taheer duk nata ne..ta Kuma San irin son da Taheer din ke mata bazai cutar da itaba…kawai she’s going to miss them…ta riga tayi sabo dasu gashi yanxu zasu tafi…a hankali Taheer yaji wasu hawayen tausayin mahaifiyar tashi sun zubo kan face dinshi…yasan su kadai gareta…Layla kuwa dama kukanta yafi na kowa…sundauki kusan 6 mins a haka kafin ummi ta sakesu a hankali snn ta juya tareda shigewa bedroom..Nafisa ta mike tabi bayanta da sauri…ita Kuma umma ta karaso inda suke ta rike hannayensu cikin nata snn suka fita daga part din…har bakin mota umma ta rakasu..bayan ansa akwatin kayan Layla a motan…Saida ya bude mota ta shiga snn shima ya shiga…Yana ganin umma na musu waving har suka fice daga gidan…shi kanshi gaba daya jikinshi a sanyaye yake…tausayin ummin yakeji sosae…yasan dole zataji ba dadi..dama shi kadai ta Haifa kwal..sai Laylan da aka basu…yanxu gashi duk sun tafi sun barta..

Har suka isa gidanshi dake Maitama..Layla bata dena kuka ba…gaba daya kukan nata ya dameshi…daurewa kawai yake…bayan ya shiga ciki yana gama parking ya bude motan ya fita…side din da take ya zagaya tareda bude kofan…bai tsaya yi Mata mgn ba kawai ya dauketa cak snn ya rufe kofan da bayanshi…Layla ta shiga wutsil wutsil tana fadin”daddy drop me..I can walk by myself”…Taheer baibi takanta ba ya nufi entrance din gidan…Saida yai unlocking kofan da key din dake hanunshi snn ya tura ya shiga ciki…Layla nata kuka tana ya ajiyeta amma yai Mata banza…Saida ya haura sama direcit to his bedroom snn ya direta kan gado…ta kwanta kan gadon tana Kara sautin kukan nata..Taheer ya dafe goshi tareda fadin”na shiga uku”..ganin da gske fa ba dena kukan zatai ba ya nufi inda take da sauri…ya dagota yana share Mata hawayen yace”so baby bakya tausayina koh..baki damuba duk halinda zan shiga right”…da sauri ta shiga girgiza mai Kai tace”daddy ummi…banaso mu barta daddy don Allah mu koma gidanmu”… yana girgiza kan shima yace”nan ne gidanmu baby..ummi Kuma i promise you ba abinda zai sameta..umma na tareda ita and na tabbata she’ll look after her..so stop crying..you know my heart aches for you…it aches whenever I see you in pain..so don Allah stop it”…ta gyada Kai a hankali…Taheer ya janyota jikinshi yanajin yanda jikin nata ke fitar da wani ni’imtaccen kamshi…sai ya janyeta da sauri yana fadin”now let me get you something to eat kafin mu kwanta koh”…Yana rufe baki tace”banajin yunwa”…yace”kinci abinci ne kafin mu taho”…da sauri ta daga mai Kai tana tuna uban kazan da ummi tasa Mata a gaba Saida ta cinye…bai sake cewa komai ba ya mike Yana cewa”alright muje kiyi changing I want to sleep”…ba musu ta mike tabi bayanshi..Saida ya fita ya dauko trolley din nata dake mota snn ya dawo tareda kulle ko ina..ya Kuma kashe bulbs din gidan snn ya haura sama…har yanxu Kuma Layla na biye dashi a baya kmr bindi…wata kofa taga sun shiga dake nn cikin parlon… corridor ne mai daukeda dakuna biyu…na farkon taga ya bude ya shiga…itama ta mara mishi baya…ya ajiye trolley din kan gado snn ya bude don nema mata sleeping dress…wata riga ya dauko ash color..jikinta cotton ne sosae…hanunta bai da wani girma can likewise tsawonta bazai wuce iya gwuiwa ba…ya ajiye gefe snn ya dauko daya daga cikin hulunanta na bacci shima ya ajiye gefe…ya juyo ya sameta tsaye tana binshi da kallo…Dan murmushi ya saki snn ya taka a hankali zuwa inda take…yasa hannunshi ya janyota jikinta…kafin ya shiga warware lafayan dake jikinta…itadai idanunta rufe ruf tanajin yanda yake warware lafayan…Saida ya gama wareta gaba daya snn ya shiga bin jikin nata da kallo…tayi mai kyau as always…a hankali ya dauko kayan dake ajiye kan bed din ya Mika Mata…idonshi a kanta”kinyi wanka kafin mu taho?..”…ta daga mai Kai alaman tayi…yace”ok ki cire kayan kisa wnn…nima zanje inyi changing”…yana rufe baki tace”ai tsoro nakeji daddy..nidai ka jirani pls”…bai sake cewa komai ba ya zauna gefen gado…har ta daga riganta zata cire a nn sai kuma ta fasa ta nufi bathroom…bayn mintina kadan ta fito sanyeda rigan da ya bata…ya sauke boyayyen a jiyar zuciya cikn ranshi yace”she always cute”…Layla ta karaso inda yake tace”na gama”…sai ya kama hanunta suka fita daga sakin zuwa nashi…ya zaunar da ita kan gado snn ya nufi closet tareda dauko pyjamas dinshi ya shiga bathroom…after like 6 mins ya fito…ya karasa inda Layla ke zaune har yanxu…kmr jira take ya zauna din ta matso tareda kwanciya a jikinshi…Taheer murmushi ya saki snn ya jata ya kwantar a kan gadon…ya rufa Mata duvet snn ya kwanta kusa da ita…Saida yayi addu’a ya shafa mata snn ya shafa ma kanshi…ya sauke wani nannauyan numfashi…this is what he has been praying for for…ya dade ya fatan Allah ya kawo ranan da idan yayi Mata addu’a zai kwanta kusa da ita kmr haka..ko bazaiyi komai da itaba he’s ok…ya lumshe idanu tareda fadin”Alhamdulillah”.

(Asuba ta gari amarya da ango😇)

Washegari…

They slept peacefully that har suka kusa makara sallahn asubah…lokacin da Taheer ya tashi har an fara sallah a masjid..ya mike zuwa bathroom ya dauro alwala da sauri snn ya fito..ya tasheta itama taje tayi alwalan ta fito…shi ya jasu jam’i sukai sallahn..don ko yace zai fita masallaci ba lallai ne ya samu sallhn ba..Saida suka fara raka’atainil fajr snn sukai subhi…bayan sun idar Layla ta mike tareda komawa kan gado ta kwanta…shi Kuma nan yaci gaba da zama yana add’u’o’inshi…Saida gari yai haske sosae snn ya koma shima ya kwanta.

10:45am

Daidai wnn lokacin Taheer ya fito wanka…ya tsaya gaban mirror yana tsane ruwan jikinshi da towel…su Layla ajebo kuwa har yanxu baa tashi daga bacci ba…bayan ya gama tsane jikinshi sai ya zauna kan stool yana shafa mai…Saida ya gama tsaf snn ya nufi closet ya dauko kayan da zaisa…ya shiga bathroom ya sa Kayan snn ya fito…yana combing gashinshi a gaban mirror wayanshi ya fara ringing…yai saurin maidata silent gudun kar karan ya tashi Layla…yai picking tareda kaiwa kunnenshi…muryan umma yaji tace”Ina ka shigane na Kira baka daukaba”… yace”ina wanka ne umma…Ina kwana”…umma ta amsa da”lfy lou..ya gidan”…yace”gida lfy umma..Ina ummi”…umma tace”gata nn bari in bata ku gaisa”…umma na gama mgn ta mikama ummi dake zaune kusa da ita wayan…ta amsa tareda yin sallama…Taheer ya amsa sallaman shima snn ya gaisheta…tace”duk muna lfy..ya gidan..hope dai ba wani matsala”…yace”ba komai ummi”…ummi tace”to Alhamdulillah..Ina Layla”…Taheer ya danyi shiru kmr bazai ce komai ba..sai Kuma yace”tana bacci”…ummi ta saki salati tana fadin”dama abinda nake gudu knn wlh..inba iskanci ba Taheer ya zaka bari tayita bacci har karfe 11…wane zaiyi Mata gyaran gidan toh”…Taheer na shafa Kai yace”calm down ummi..ai yanxu ta kwanta baccin…gidan Kuma ba abunda ya sameshi…ko Ina tsaf yake”…wani salatin ummi ta sakeyi tace”ka tasheta a baccin nn ko sai naci ubanka…wane irin gida a gyare yake bayan jiya duk anyi dabdala a cikinsa…yanxu  abunda zaka koya Mata knn”…murya can kasa Taheer yace”to bari in tasheta”…yana rufe baki ummi taci gaba da fadin”ka tasheta yanxu yanxun nn…tun sassafe Aisha ta damemu wai a kawo muku breakfast…Ni nace bazaa kawoba don nasan Kuna can Kuna baccin asara…gashi kuwa mgn na tabbata..Allah ya sawake muku wlh”…shidai bai sake cewa komai ba ya kashe wayar…ya ajiyeta nan kan mirror snn ya juya zuwa kan gadon…ya zauna a hankali yana kallon yanda take baccinta hankali kwance…harga Allah shidai ba son tashinta yakeyi ba…

A hankali ya Kai hannunshi yana cycling lips dinta dake matukar tempting dinshi…sai ta fara motsi…shi Kuma yaci gaba dayi har ta bude idanunta a kanshi…ta dan turo bakin tace”daddy plss mana…baccin bai isheni ba”…tana kokarin juya baya taci gaba da baccinta ya kamata ya zaunar kusa dashi…ta sake turo bakin tana kallonshi…Taheer ya dauke idonshi a kanta da sauri jin tsigan jikinshi ya tashi…sai ya mike daga kan gadon gaba daya snn yace”ki tashi kiyi wanka..ummi nason mgn dake”..Layla ta zaro idanu waje tace”na shiga uku…daddy kace mata Ina bacci ne”…a hankali Taheer ya daga Mata kai alaman ya fada Mata…sai ta sauko daga gadon a guje tana fadin”shknn..nasan wlh ummi tayita mun fada knn..Kuma ni wlh baccin bai isheni ba”… juyowa Taheer yai zuwa inda
take…ya kama hanunta suka fita daga dakin yace”muje kiyi wankanki ki shirya..babu fadan da zatayi miki InshaAllah”… itadai bata sake mgn ba as tana tsoron me ummi zatace…Saida suka shiga dakinta snn ya saketa…ya shiga bathroom ya hada Mata ruwan wanka snn ya fito…yana dubanta yace”go ahead and take your bath..na fada maki ba abinda zai faru’…jiki a sanyaye Layla ta nufi bathroom din ta shiga…shi Kuma ya shiga nema Mata kayan da zatasa…lokacin da ta fito har ya dauko mata wata English gown sea green..gown din is handless sai red top da zaa dora a Kai…tana daure da dan towel dinta ta karasa gaban mirror ta zauna…Taheer ya debo kayan shafan ta daya fito dasu yazo ya jera mata su gaban mirrorn…tana kallonshi da murmushi tace mai”thank you”…shima yayi mata murmushin snn ya koma tareda zama gefen gado yana kallonta with adoration…ita Kuma ta dauki lotion dinta ta fara shafawa…bayan ta gama ta dauki humra dinta ta shafa a jikinta sosae snn ta shafa powder…ta sanya kajal a idanunta sai dan chapette a lips dinta…ta mike daga gaban mirror din tana kallonshi…kafin tayi mgn ya dauki kayan daya fito mata dashi yana Mika mata yace”here you go”…ta amsa kayan a hanunshi snn ta juya ta shiga bathroom…tasa kayan a ciki snn ta fito…Taheer mikewa tsaye yai kawai yana kallon yanda gown din yai mata kyau sosae…a hankali ya shiga takawa har zuwa inda take tsaye..ya kama hanunta zuwa gaban mirror ya zaunar da ita snn ya dauko comb yana ware gashin kanta daketa faman sheki…ta bata fuska tana kallonshi ta mirror tace”daddy is it necessary”…saida ya fara taje mata gashin a hankali snn yace”yes it is..and karki kuskura kimin kuka”…ta turo baki kawai tana kallon yanda ya dage yana taje kan…shiko Taheer he is doing it with pleasure…wani irin laushi ke gare gashin nata…sai yaji baiki su kwana nn wurin yana combing Mata shi ba…in kaga yanda yake taje kan a hankali sai kace kan jaririya…Layla kuwa dadi takeji don kmr susa yake Mata…Saida ya gama snn ya daure Mata shi da ribbon a tsakiyar kan nata…yana kallonta da murmushi ta cikin mirror din..itama murmushin take tana kallonshi tace”it look nice daddy..kafi ummi iya taje min kai ita nata da zafi takeyi”…still Taheer na murmushi ya mikar da ita tsaye tareda juyo da ita tana fuskantarshi…ya lumshe ido snn ya manna mata peck a forehead dinta kafin yace”I love you so much baby…bari in duba naji kmr an danna door bell”…Yana gama mgn ya juya tareda ficewa daga dakin…ita Kuma Layla ta fada kan gado tana sakin murmushi…he really is a nice man.
+
Taheer na sauka ya bude kofan sai yaga driver ne ya kawo musu breakfast..ya amsa snn ya maida kofan ya rufe…ya ajiya basket din kan dinning snn ya sake haurawa sama…ya bude dakin nata ya sameta kwance tanata faman smiling…ya karasa ciki hanunshi rungume a kirji yace”to tashi muje muyi breakfast”…ba musu ta mike..shi Kuma ya sake kama hanunta suka fita daga dakin..bayan sun isa dinning yaja mata kujera ta zauna shi Kuma ya nufi kitchen don dauko plates da cups da zasuyi amfani dashi…yana daukowa ya dawo..sai ya shiga bude wormers din yana ganin abinda ke ciki…saida ya gama snn ya dawo da idonshi kanta yace”me kikeso a ciki”…maimakon ta amsa mashi sai ta mike tsaye tana duba wormers din daya bubbude…tayi pointing finger dinta kan Wanda ke daukeda fried plantain tace”one”…ta nuna Wanda ke daukeda pepper soup tace”two”…sai tea flask dake daukeda shayi da yaji different ingredients tace”three”…sai Kuma wani small one dake daukeda fried egg shima tace”four”…Taheer dake kallonta yana murmushi yace”is that all”…tana murmushin itama ta daga mai kai alaman yes…ya shiga zuba mata duk abunda ta lissafa din ita Kuma ta koma ta zauna inda take tanata aikin binshi da kallo…Saida ya gama ya tura Mata komai gabanta snn yace”oya Bismillah”…tace mai”thank you”..snn ta fara cin abincin…shima yai serving kanshi snn ya shiga ci a hankali…baya cikakken minti 2 bai dago ya kalleta ba..he don’t know why bai taba gajiya da kallonta…Sun dauki almost 30 mins snn suka gama…yana kallon duk abubuwan da tace zataci ba wanda ta cinye duka…duk Saida ta rage..yai murmushi tareda kada kai..snn ya kwashi duk abubuwanda suka bata yai kitchen dasu…da sauri itama ta mike ta dauki sauran da bai dauka ba tabishi kitchen din dasu…ta ajiesu cikin sink kmr yanda taga ya ajiye sauran…sai taga ya shiga nannade hanun rigarshi…ta kwalo idanu waje tana fadin”daddy me zakayi”…yana ci gaba da nannade hannun nashi yace”wanke wanke Mana”…ta karasa gaban sink din da saurinta tace”Ni zan wanke daddy…ai basa da yawa”…yana girgiza kai yace”no babu abinda zakiyi baby..just sit down and watch kinji…ba sai kinyi komai ba”…ta makale kafada tana cewa”nidai I want to do it daddy..Mami tace kar in yadda in ringa bari kana aiki da kanka..so bakai zakayi wanke wanken nn ba ni zanyi”…Taheer dake kallonta yace”I see…ita tayi miki wnn huduban knn koh”…Layla ta daga Kai da sauri…ya karaso inda take tsaye gaban sink din yana fadin”ok..tunda hakane let’s do it together”…yana rufe baki tace”to nine zanyi sabi sai kanayin dauraya”…ya daga Mata Kai alaman toh…ita Kuma ta dauko morning fresh dake ajiye a wurin ta hada kumfa sosae snn ta fara wanke wanke…tanayi yana daurayewa har suka gama..dayake ba wani abu masu yawa suka bata ba…Saida suka maida komai inda yake snn yaja hanunta suka fita yana ce Mata”now it’s time to look around the house..let’s start from outside”…Layla dai binshi takeyi har suka fita compound din gidan…Yana da girma sosae ga flowers da aka zagaye compound din dasu…car park na daga can gefe wanda 2 of his cars ke Parke a wurin…suka dawo cikin gidan nn ma katon parlor ne sosae..dake daukeda duk wasu abubuwa na more rayuwa…akwai bedroom mai daukeda toilet a nn cikin parlon snn akwai another toilet dake cikin parlor…sai dinnig area shima nada girma..daga gefenshi Kuma kitchen ne mai daukeda store a cikinshi…da suka haura sama nan ma it’s another parlor sai dai shi wnn bai Kai na kasan girma ba…babu abunda babu a ciki tun daga kayan kyale kyale har zuwa furnitures da sauransu…shima yana daukeda mini dinnig daga can karshe…sai kofofi guda biyu dake opposite to each other amma da akwai distance sosae a tsakaninsu…left one din suka shiga…Wanda shine na Layla.. corridor ne mai daukeda two bedrooms kowanne da toilet…shima dayan is the same da natan..Wanda shine na Taheer din…Layla sai baza ido take duk inda suka shiga tana kalla tana smiling har suka gama…nan parlon sama sukai branching ya kwanto ta jikinshi yana shafa jelar gashinta dake yawo tsakanin wuya da bayanta yace”so how do you see the house”…ta sake lafewa a jikinshi snn tace”it’s very beautiful daddy…I like it”…Saida yai kissing gashin nata snn yace”Alhamdulillah you like it”.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan Sati daya…
Cikin satin nan tana ganin zallar soyayya wurin Taheer…dukda ba wani abune ya shiga tsakansu ba amma yanda yake kulawa da ita is something she can’t ignore…ya nuna Mata ita din yakeso and nothing else…wnn dalilin yasa kullum she’s falling for him…his kindness is something da bata taba gani wurin wani ba…gaba daya week din nn sunyishi ne a gida…shi baije clinic ba don ya dauki hutu…itama bataje makaranta ba…sedai almost everyday sunayin karatu dashi a gida…she really loves him that ko kadan bata son matsawa daga kusa dashi sbd yanda yake taking very good care of her…she loves him so much abun har mamaki yake bata…one thing dake dan damunta is yanda taga kmr baida wani feelings a kanta…a yanda taji ana fada in mutum na sonka bazai iya resisting beauty dinka ba…amma it’s like daddy gaba daya ma baida wani feelings a kanta…har yanxu ba abunda ya taba hadasu banda peck da yake yimata wnn kam tana shanshi kmr me…in tayi tunanin ta fadama wani sai taga kmr ist not right..sai ta share batun kawai taci gaba da zuba mai ido.
Shiko Taheer a nashi bangaren yasan there’s a progress tsakaninshi da Layla and kullum cikin godiyan Allah yake… yana kokarin keeping distance dinshi sbd baison karya promise din da ya daukan Mata…but Allah ya sani he’s disturbed…yana cikin damuwa..these days ko baccin kirki bai samu…the moment yajita jikinshi yake loosing duk wani strength nashi…he really wants to have her amma yana tausayinta..and yana so yayi keeping promise dinshi…yasan a yanda yakejin Layla cikin zuciya da gangar jikinshi.. duk rananda ta shiga hanunshi ba karamin wahala zai bata ba…wnn ma yana daga cikin dalilinda yasa yake kokarin danne feelings dinshi…he believe komai nada lokaci and nasu time din na nan zuwa..so he won’t rush..he’s going to wait for the perfect time to come.
Yau ya kama Sunday shi da ita gaba daya suna gida…ita batada lectures yau…shi Kuma evening duty yake..so sai 2 zai bar gidan…Yana zaune parlon kasa yana wasu aiyuka cikin laptop dinshi…Layla ta sauko da gudu tana fadin”daddy nidai ka kaini in gaida su ummi yau plss”…Taheer ya dago idonshi yana kallonta…tana sanyeda dan riganta iya guiwa..gashinta da har yanxu ba kitso yana daure da ribbon a tsakiyar kan nata…saida ya saki smile snn ya dauke system dake kan laps dinshi ya ajiye gefe…yai balancing kan kujeran sosae yana dubanta da idanunshi da suka kankance yace Mata”come here”…ba musu ta karasa saukowa daga stairs din ta karaso parlon..zata zauna kusa dashi ya kamata ya zaunar kan laps dinshi…ya zagaye kugunta da hannayenshi yace”me kike cewa”…ta dan juya tana kallonshi baki a tunzure tace”I said inaso ka kaini in gaida su ummi yau..tunda evening zakai sai ka barni a can…in ka dawo daga clinic din sai ka biyo ka daukeni”…Taheer yasa hannu yana sake matseta a jikinshi yace”banji me kikace bafa baby..say it again”…wnn karon harara ta watsa mai tana fadin”nasan ka jini daddy…nidai don Allah ka kaini kaji”….Saida ya juyo da face dinta yai cupping da hannayenshi…yana kallon tsakiyar idonta murya can kasa yace”ni bazan iya driving ba baby…banida lfy”…ya karasa mgnr tareda kwantar da kanshi a chest dinta…Layla ta dan zaro idanu tana kokarin dauke kan nashi tace”to..to..na hakura daddy…ka sakeni sai in dauko maka magani”…cikin zuciyarshi yace”my medicine is only you”…sai Kuma a fili yace Mata”ni ba maganin da zansha…kawai idan Zaki iya driving din muje ki kaimu”…ta shiga girgiza kai da sauri..har yanxu kokari take ta dauke kanshi dake jikinta amma kmr magnet yaki tashi…saita dena kokawan da takeyi kawai tareda lumshe eyes dinta…shiko Taheer he’s far gone…lokaci daya mood dinshi ya canxa…gudun kar yai loosing control dinshi sai ya mike daga jikin nata…ya shiga kallonta yana kokarin kakalo murmushi yace Mata”bari in sake wanka idan naji zan iya sai muje”…bai jira cewarta ba ya mike tareda haurawa sama…Layla Kam binshi tayi da ido ganin yanda yake tafiya da kyar..da alama yanajin jiki sosae…mikewa tayi itama tareda haurawa saman…tayi hanyar dakinshi zata shiga wayanta dake hanunta ya fara ringing…sai ta fasa shiga snn ta koma zuwa dakinta…Saida ta rufe kofa snn tayi picking tareda fadin”babe how far”…a daya bangaren Hanna tace”ke zaa tambaya how fa ai amarya…ya gida ya amarci”…Layla na girgiza kai tace”Allah ya shiryeki”…da sauri Hanna tace”Ameen…amma bani lbri..ya rayuwar auren take..I mean kina jin dadinshi kuwa”….wani kasaitaccen murmushi Layla ta saki data tuna yanda Taheer ke mata cikin sati dayan nn…ta tabbata da haka kowane miji kema matarshi da baa samu marital problems ba…Saida Hanna ta sake cewa”hello”…snn tace”it’s really amazing…ban taba tunanin haka auren yake ba”…Hanna ta kwashe da dariya tana fadin”kice daddy ba daga nn ba…ko dayake ai dama daga ganinshi Majnoon ne…kinsan Layla da Majnoon fa kan soyayya suka mutu”…Layla dake sauraran shakiyancin Hanna tace”malama spare me wnn surutun naki…ya school”…Hanna ta danja tsaki tace”school wahala wlh Jakada..nima jiya ban samu shiga ba sbd banida lfy”…Layla ta dan zaro idanu snn tace”umh kodai kodai”…”ke ba wani kodai kodai wlh…fever ne kawai”… cewar Hanna knn…itakam Layla dariya ta saki kafin tace”ban yadda dakeba wlh…dama tun tuni na fara noticing changes a jikinki..so ba wani fever morning sickness kawai kikeyi hajiyata”…sai ta Kara sakin wani dariyan…daidai lokacin Taheer ya turo kofar dakin ya shigo…tai saurin cewa Hanna”babe Ina zuwa..zan kiraki ltr”…tanajin Hanna na fadin”Majnoon ya iso knn”…itadai ta kashe wayarta tana fatan Allah sa baiji abunda ta fada ba…ta daga ido tana kallonshi sai taga ya dauke kanshi gefe… muryanshi can kasa yace”ko kin fasa zuwa ne”…sai ta mike tana fadin”naga bakada lfy ne daddy…mu barshi kawai duk ka samu lfy sai muje”…tana rufe bakinta yace”don’t worry i can manage..kiyi sauri ki shirya zan jiraki downstairs”…Kai kawai ta iya daga mai…shi Kuma ya juya ya fita…ta bishi da kallo duk sai taji tausayinshi ya kamata..to ciwon mene ke damunshi haka..zata cigaba da mai addu’a Allah ya bashi lfy.(ji uwar gulma😏)
Bata bata lokaci wajen shiryawa ba ta sauka downstairs kmr yanda yace…yana ganinta ya mike ya fita…itama ta bishi a baya…Saida yai locking kofar snn ya nufi inda motarshi yake…yana karasawa ya bude ya shiga itama ta shiga…snn yai Mata key…mai gadi ya bude musu gate suka fita daga gidan….ko a kan hanya Layla sai Satan kallonshi take…duk ta damu da yanayin data ganshi ciki…dama shi bai iya rashin lfy ba…ba tareda ya kalleta ba yace”mu fara zuwa kici abinci ne sai mu wuce gidan?..”ta girgiza kai da sauri tace”aa idan munje can sai muci abincin”…bai sake cewa komai ba yaci gaba da driving dinshi.
Bayan sun isa gidan yayi parking ta bude mota ta fita…shima ya fita suka shiga ciki tare…ummi na zaune a parlor..sai Nafisa da itama bata komaba tana zaune kusa da ummin…da gudu Layla ta karasa ciki ta fada kan ummi tana fadin”I missed you so much Ummita”… murmushi ummi tai kafin tace”ke dawa haka da ranan nn Layla”…kafin Layla tayi mgn sai ga Taheer din shima…Saida ya samu wuri ya zauna snn ya gaisa da ummi…yana Shirin gaida Nafisa kawai yaji tace”Ina yini”…yai murmushi yana girgiza Kai shima yace”an yini lfy”…tace”lfy Lou..ya gida”….”gida lfy Lou…su Ramadhan sun koma koh”…tace”sun koma wlh..ai sbd school..nima jibi zan wuce InshaAllah”…yace”ok..Ina umma fa”…”tana kitchen”…Yana kokarin mikewa zuwa kitchen din Layla tace”yawwa umma kiyi ki gama girkin wlh yunwa nakeji”…sai ya juya yana kallonta da sauri…ummi ma kallon nata take kafin tace”ke uban me ya hanaki cin abinci kafin ki baro gidan naki”…ba tareda ta kawo komai a rai ba tace”kinsan ba iya girki nayi ba ummi..daddy yace zai siyo kafin mu tafi nace idan munxo nan sai muci”…shiru ummi tayi tana kallon Layla rai a bace…itama Laylan sai yanxu tasan tayi subutar baki…batasan lokacinda mgnr nn ya fito daga bakinta ba wlh..shknn yau mai rabata da ummi sai Allah.
Da mamaki sosae ummi ke kallonta kafin tace”me kika ce”…Layla na stammering tace”ba..ba…ba komai ummi…am sorry plss”…wani zagi ummi ta kunduma mata tana fadin”har wani abun alfahari ne rashin iya girkin da kike fada with confidence…shima Kuma tunda ba hankali ne ya ishesa ba ya biye maki kuketa sintirin siyan abinci a waje koh”…ummi ta maido kallonta ga Taheer dake sauri ya shiga kitchen wai don kar ta juyo kanshi…kawai sai yaji tace”dawo nn kaima”…jiki a sanyaye ya dawo parlon…ummi na dubanshi da kyau tace”yanxu abunda kakeyi kana ganin daidai ne knn…duk abubuwan da muka fadama yarinyar nn kasa tayi watsi dasu..don me zaka biye mata ka ringa fita siyan abinci… idan tana gwadawa ba a haka zata saba ba”…Taheer ya rausaya Kai yace”kiyi hakuri don Allah… InshaAllah zaa kiyaye”…daidai nn umma ta shigo parlon tana fadin”ah yaushe kuka zo son”…Taheer yace yanxu mukazo umma..Ina yini”…Saida ta zauna kusa dashi snn tace”lfy Lou..ya gidan”…ya sake cewa”lfy Lou”…umma na duban ummi tace”ke da qawar taki Kuma Yaya daga zuwa har anji kanku”…tsaki ummi taja snn tace”ai abun ne abun takaici wlh Aisha…har wani cemin take wani wai ita ba yin girki take ba..shima dan naki sbd shashasha ne yake biye Mata kullum yana gararin siyo musu abinci”…umma ta maida kallonta kan Taheer kafin tace”why son..ance fa ka dinga bari tana practicing watarana sai kaga tayi abunda akeso”…a takaice yace”to umma”…Saida umman ta mike snn tace”an gama abincin…sai ku tashi muje dinning”…ummi ce ta fara mikewa tai dinning din snn Nafisa..umma ma tabi bayansu…ya rage daga shi sai Layla dake matsan kwalla a parlon…ya karaso gareta da sauri ya zauna snn yace”tashi muje kici abincin toh”…tana share hawaye tace”ni na koshi”…yai shiru Yana kallonta for some secs snn ya sake cewa”to Fadi abunda kikeso inje in siyo maki yanxu kafin time din tafiyana yayi”…maimakon ta amsa sai ta riko hanunshi tace”daddy am sorry nasa ummi tayi maka fada”…yana girgiza kai yace”it’s not your fault okay..yanxu ki fadamin me kike son ci”…tana turo baki tace”ni na fasa zama a nan daddy…kaje dani clinic din kawai”…yace”bazai yiwu in tafi dake can ba baby..kiyi hakuri ki zauna a nn..zanyi mgn da ummi bazata sake yi maki fada ba”…shiru tai kawai tana kallonshi sai wasu sabbin hawaye ke fita a idonta…Taheer ya janyota jikinshi yana cewa”come on mene abun kuka Kuma..kiyi hakuri ki dena kuka naji zan tafi dake..are you happy now?..”…sai ta shiga share hawayen tana daga mishi Kai…nan suka cigaba da zama su kadai kmr marasa gsky😆
Umma ce ta fara dawowa parlon snn ummi…tana dubanshi tace”wai baza kuci abincin bane”…Taheer ya Dan saci kallon ummi snn yace”Ni dama banjin yunwa”…”ita Kuma Laylan fa”…umma ta sake fada tana kallon yanda Laylan ta wani lafe a jikinshi…Saida ya sake kallon ummi ta gefen ido kafin yace”ta koshi…dama ba yunwa takeji ba”…yana gama fadan haka ya mike Yana fadin”bari muzo mu wuce..dama clinic zamuje nace mu biyo ta nan”…umma na kallon Layla data mike tsaye itama tace”ba nan zaka barta ba?..”yace”no tare zamu tafi”…ummi ta watso musu wani kallo tana cewa”to bazaka tafi da itan ba..a nan zaka barta..sbd nayi muku fada wato ku baa isa a fada maku gsky ba knn”…da sauri Taheer yace”ummi ba haka bane..dama can banyi niyyar barinta a nn din ba”… strictly ummi tace”to ni nace ka tafi ka barta a nan..idan ka dawo sai ka biyo ka dauketa”…bai sake cewa komai ba ya juya yana kallon Layla da har ta fara hawaye…ya karasa inda take tareda kamata suka zauna…cikin lallami yace daita”kiyi hakuri ki zauna kinji.. InshaAllah bazan dade ba zan dawo”…Layla sai ta fada jikinshi tana fashewa da sabon kuka…umma da ummi kallonsu kawai suke baki bude…ummi ce ta kasa hakura Saida tace”ai saidai Allah ya kyauta Kuma..dududu satinsu daya da tarewa amma dubi yanda yarinyar nn ta sake tabarbarewa sbd Allah…zuwa nan gaba ban San me zai faru ba Kuma”…su dai basu kulata ba…Taheer ya mike rikeda Layla a jikinshi suka kama hanyar dakinta…ummi na duban umma tace”kingani koh..wato ga mahaukaciya na mgn”…umma na girgiza kai tace”ki rabu dasu kawai Yaya…ki dena ma shiga harkansu suje can su karata..in yaga dama ya maidata ciki ma tsabar soyayya”..
STORY CONTINUES BELOW
Taheer na shiga dakin da ita..ya zauna gefen gado itama ya zaunar da ita..hannunta cikin nashi yace”kiyi hakuri ki zauna baby..tunda ummi tace ki zauna kin San ban isa in tsallake umarnin ta ba..zanyi mgn da ita InshaAllah bazata sake yi maki fadan ba..yanxu ki fada me zakici inyi sauri in kawo maki kafin na tafi”…tana share hawayenta tace”no ba sai ka siyo komai ba..zanci a nan din”… yana dubanta yace”are you sure”…ta daga mai kai…saida yai kissing dinta a forehead snn yace”to bari inzo in wuce..take care of your self kinji”…tana murmushi ta daga kai alaman toh..snn tace”daddy kaima bakaci abincin bafa”…yace”idan na fita zan nemi abinda zanci.. promise me baza ki Kara kukaba in na tafi”..tace”I promise”…”that’s my baby..Allah ya maki albarka”..Taheer ya fada yayinda yake fita daga dakin….bai sake zamaba yai sallama dasu umma snn ya tafi.
Yana isa clinic din bayan ya shiga office dinshi sai ya shiga Kiran wayan umma…yanaso yace Mata ta bama Layla abinci kafin ya fito amma ganin ummi a wurin sai ya fasa… ringing kmr uku umma tayi picking call din…tun kafin tai mgn yace”umma don Allah ki bama baby abinci taci kinji..wlh tun safe bata karacin komai ba”… murmushi umma ta saki kafin tace”naji..bari in kirata sai ta fito taci”…cikin jin dadi yace”yawwa umma thank you…snn umma don Allah ki kulamin da ita Amana pls..ko wani abun tayi kice ma ummi a bari in na dawo sai a fadamin..ni zanyi mata fada da kaina..kinji umma”…wnn karon dariya umma tayi sosae kafin tace”saidai ka kirata da kanka ka fada Mata”…dariyan yayi shima yace”Tabb kinaso ta zageni knn umma”…”eh ni sbd ka rainani ai shiyasa ka fadamin..hadda wani cewa a riketa Amana sai kace Wanda muke gutsuran Naman jikinta munaci”…still Yana dariya yace”wlh ba raini bane umma..kawai ke kina fahimta na ne unlike ummi da slight mistake zata fara fada”…umma tace”to naji..yanxu bari in kirata taci abincin”…yace”yawwa umma i love you”… murmushi kawai take snn ta kaste wayan…Taheer dai kan Layla baida kunya Sam..
Tana shiga dakin ta samu Layla zaune waya kare kunnenta..daga yanayin yanda take mgnr umma ta gane Taheer ne…ta girgiza Kai cikin ranta tace”oh wnn yaron baida hakuri wlh..har ya kirata”…a fili Kuma tace”to ki fito kici abinci..yanxu aka gama bani amanarki”…Layla da ta gama wayan da takeyi yanxu ta mike suka fita tareda umma…ita ta zauna parlor umma Kuma ta zubo abinci ta kawo Mata…ba laifi ta danci abincin amma ba wani sosae ba…so take kawai daddy ya dawo su tafi gida abunsu…ita bai taba yi mata fada ba tun da sukaje amma yanxu ummi daga zuwanta ko 10 mins batayi cikin gidan ba ta fara Mata fada.
9 pm daidai ya shigo gidan…duk hankalinshi na kanta ko time din tashinshi bai karasa ba ya tafi…duk suna zaune parlor sai hira suke kmr ba abinda ya faru…a boye ya sauke ajiyan heart at least dai ba wanda ya sake Mata wani abun…Yana zuwa shima abinci kawai yaci snn suka tafi bayan ummi ta sake mai gargadi sosae kan lallai ya ringa Bari tana practicing girki ko yaya ne..yace Mata zaiyi ba don zai aikata din ba..ya fada ne kawai don a zauna lfy sbd ita ummi hukuma ce sai da lallashi😆
Washegari…
Karfe takwas daidai yayi dropping dinta a school don 8 zata fara lectures…yana ajiyeta ya koma gida don he’s still on evening duty.
Tun da ta shiga class yau bata samu fitowa ba..sallah kadai suka fito sukayi ko abinci basu samu daman ci ba suka sake komawa for another lecture..lectures din a jere sukayi su.
Karfe uku suna zaune cafeteria itada Hanna..ita tanacin abinci Hanna Kuma tace ita tafiya gida zatayi…Layla tai sipping drink dake hanunta tana fadin”wai saurin me kikeyi ne haka..idan kinje gidan ma me zakiyi da bazaki tsaya kici abinci ba”…Hanna tace”Habibi 4 zai tashi daga office..Kuma banaso ya dawo gida ban gama abinci..I want to go back on time so that in samu in gama girki kafin ya dawo”…Layla na daga Kai tace”ohk..you can go sai gobe”…Hanna tace”wait..ke bazaki koma kiyima daddyn naki abinci da wuri ba..ko ba da wuri yake dawowa ba”…Saida ta sake sipping drink dinta tana daga kafada tace”ni bana girki ai”…Hanna ta zaro idanu waje tace”ban fahimceki ba..don’t tell me tunda kukai aure baki taba shiga kitchen da sunan girki ba”…tana rufe baki Layla tace”come on mene kikayi haka da fuskanki toh..meye a ciki..ai ni ban iya girki ba dama”…Hanna ta saki salati tareda komawa ta zauna inda ta tashi…tana kallon Layla da mamaki tace”then me kukeci a gidan all this while”…”daddy ke fita ya siyo mana”..ta fada kanta tsaye…Hanna ta sake sakin wani salatin tace”wlh Jakada ban taba sanin you insane ba sai yau…how could you…kina zaune cikin gida allowing mijinki yana fita kullum siyan abinci a eatry..mene amfaninki…to let me tell you this..namiji da kike ganinshi bashida tabbas wlh..kina nn zaune kina tunanin he can die for you wata zatazo ta kwace maki shi a banza..duk kika kuskura ya gaji da fita siyan abinci to definitely aure zai Kara..kika bari mijinki ya karo aure sbd kina lacking wani abu kuwa kinyi asara..kinaji kina gani zaa maisheki bora a cikin gidan wlh..ko kinzo kinayi daga baya bazaki taba burgeshi ba”…tunda Hanna ta ambaci wata zata kwaceshi a hanunta taji gaba daya abincin ma ya fita a kanta…like how on Earth Hanna zata kawo Mata wnn mgnr…ya zaai tace daddy zai Dena sonta ya samu wata..no..that’s no possible..idan Kuma haka ya faru to tabbas zata iya mutuwa…Saida Hanna ta buga table din dake gabansu snn ta dawo daga tunanin data Lula…cikeda rudu tace”how could you say such a thing Hanna…kawai don ban iya girki ba sai daddy yace zai karo wata”….Hanna ta kwashe da dariya kafin tace”unbelievable..ba dai har kishi ya rufeki don kinji ance he might marry a second wife in future ba..to wallahi matukar baki tashi kin gyara rayuwar aurenki ba…I assure you ko daddy bai Kara aure ba watarana duk son da yake maki sai ya Dena..sbd bakida amfani a wurinshi…bakisan girki nada matukar muhimmanci wurin ‘ya mace ba koh..to duk macen da bata iya girki ba she’s an incomplete woman..ya zama lallai ki koyi girki nor matter what don ki gujema kanki dana sani a nn gaba”…zuwa yanxu Layla kuka takeyi wiwi…harga Allah she can’t stand seeing him with another..bazata iya sharing dinshi da kowa ba..it’s better ta koyi girkin kota yaya ne amma bataso daddy yace zai Kara aure ko ya Dena sonta…tana sheshsheka tace”I know you are right Hanna…nasan gsky kike fadamin amma ban iyaba..ya zanyi in koya don Allah”…Hanna ta matso da kujeranta kusada nata..ta riko hanunta snn tace”ba Abu bane mai wahala ai…Thank God akwai social Networkings…ba abinda bazakiyi da wayanki ba..for example idan kika shiga YouTube kikai searching zasu nuno maki different kind of girki da procedures dinsu..sai ki ringa downloading kina bin yanda sukayi kema kiyi…a hankali zakiga kin saba…snn akwai recipes da nake dasu..zanyi maki sharing ta WhatsApp sai ki duba..suma Zaki iya yinsu…and akwai online classes da akeyi shima Zaki iya joining..da akwai wata sis dina a kano take..so zata fara online classes dinta cikin week din nn..zanyi maki registration sai muyi tare..and the most important thing shine kisama ranki Zaki iya..ki cire son jiki ki ware kiyita practicing tun kina samun mistake zakiga kin kware…but kina zaune a haka kina cewa baki iyaba bazai miki amfani ba…yanxu Bari in tafi kinga sauri nake..zamu cigaba da mgn gobe..akwai wasu littafai duk na koyon girki ne zan kawo maki su gobe sai kiyita practicing..bye”…Hanna na gama mgn ta wuce ta tafi don sauri takeyi…ita Kuma Layla tabita da kallo tana share hawayen idonta… maganganun Hanna ba karamin tsoro suka bata ba wlh…ashe ummi gata takeyi Mata bata saniba..aiko zatai iya bakin kokarinta taga itama ta iya girkin nn..idan ta tuna yanda Taheer ke mugun bata kulawa sai ta sakejin wani tsoro ya shigeta..bazata iya jure yana treating wata kmr yanda yake treating dinta ba..she can’t.
Haka taci gaba da zama nan wurin tana jiranshi..time time tana share hawaye don da gske mgnr Hanna ya shigeta…bata taba tunanin haka take da kishi ba sai yanxu..a da idan taga mace na damuwa idan zaa Mata kishiya ko idan taga mijinta da wata… gani takeyi kmr basuda aikinyi…like mene zai kaita wani damuwa don kawai mutum yace zai Kara aure…bata taba sanin haka feeling din yake ba sai yanxu…yanxu ta gane dalilinda yasa wasu matan ke aikata abubuwa marasa dadi kan kishi…don inhar mutum bai iya controlling kishin shi ba…babu abunda bazai iya aikatawa ba…sbd gaba daya hankalin mutum gushewa yake..bazaka Kuma taba gane yanda yanayin kishin naka yake ba sai wani abun ya faru..
(Allah ka mana tsari da kishi mara amfani🙏🏻)
Taheer bai samu isowa daukanta ba sai wurin 4:30…aiyuka ne sukamai yawa sosae a office and he’s the only doctor around..
Yana gama parking ya shiga Kiran wayanta…har ya gama ringing Layla na duniyar tunani bataji ba…sai a na biyu ne taji vibration din wayan dake cikin bag dinta…ta daukota da sauri snn tayi picking…yace Mata ya iso…sai ta mike zuwa inda tasan zata sameshi…Taheer tun da ya hangota daga nesa ya fuskanci something is wrong with her sbd yanda take walking slowly…kafin ta karaso inda yake ya fito ya bude Mata mota…tana zuwa sai ta shiga cikin motan kawai…ya rufe kofan snn ya juya shima ya shiga…Saida suka bar haraban school din yace daita”baby are you alright..I mean what’s wrong with you”…tana kokarin dora murmushi kan fuskanta tace”ba abunda ke damuna mana daddy..gajiya ne kawai”….tana rufe baki yace”I don’t believe you baby… your eyes are swollen..am sure kuka kikayi”…tace”Allah daddy ba komai..gajiya ne kawai..kasan yau fa tun safe muke lectures ko abinci banci ba sai yanxu”…Yana murmushi yace”medicine din knn..har yanxu ma baku fara karatu ba baby..this is just an introduction”…tana dan turo baki tace”I think guduwa zanyi gsky”…ya saki dariya yana cewa”don’t be silly Mana..I know my baby is very intelligent..she can make it”…tana girgiza kai tace”aah fa daddy wnn compliment din nake won’t change a thing..ni na fara gajiya gsky”….dariya ya saki sosae don mgnr nata ba karamin dariya ya bashi ba..wai ta fara gajiya..to me akai da maza.
Suna isa gida kowa ya nufi yayi freshen up snn suka fito cin abinci don already ya siyo musu abinci…kememe Layla tace ita bazataci abincin ba wai ta koshi…haka nn ya rabu da ita don yaga da gaske bataci ba…shima sai ya samu kanshi da kasacin abincin…for sure yasan akwai abunda ke damunta duk sai yaji he’s not normal shima…bai son abunda zai daga mata hankali ko kadan..
7:45pm
Daidai wnn time Taheer ya dawo daga masjid…ya samu Layla zaune a parlon sama ta fada duniyar tunani…mamaki ya sake kamashi ganin   hankalinta na kan tv amma ba kallon takeyi ba…a hankali ya karasa ya zauna kusa da ita…ya dauki remote ya canxa channel zuwa Zeeworld don yasan tana sonta snn yace Mata”baby yau babu kallon Twist Of Fate ne”…dan girgiza kai tayi tana tabe baki tace”am not in the mood”… Taheer ya zaro idanu waje jin abunda tace…duk soyayyanta da Twist Of Fate yau tace she’s not in the mood dole akwai abunda ke damunta…ya janyota jikinshi aiko kmr jira takeyi ta kankameshi sosae…yana shafa kanta yace”baby yau su Abhi da Pragya ne bakison gani Kuma…tell me abunda ke damunki plss..kin sani a damuwa fa”….Layla na hawaye tace”I don’t want to loose or share you with another dady..I love you”…maganganunta sun bashi mamaki sosae don baisan abunda yai warranting such statement ba…ko dai wani ne yace mata she’s going to loose him…mgn irin wnn bai taba shiga tsakaninshi da itaba…to me a kawo mata wnn tunanin all of a sudden.
Hankali tashe Taheer ke share hawayen nata yace”baby what is it..and waya fada maki zakiyi loosing ko sharing dina da wata..you know I love you…I belongs to only you..so ki dena damun kanki kan such a minor issue”…Layla na girgiza ta sake cewa”an ce maza basuda tabbas”…wani mamakin ta sake ba Taheer don bai San duk me ya kawo wnn maganganun ba…yasan definitely wani ne zai fada mata wani abun ita Kuma ta yadda…ya dago kanta yana kallon wet face dinta yace”baby calm down mana..duk meya kawo wnn maganganun..idan ma wani ya fada maki haka bai kamata ki yadda ba baby..you know how much I love you…I can die for you baby and you alone…so ki dena wasting min precious hawayenki kan wnn mgnr”…maganarshi ba karamin sanyaya Mata rai yayi ba…ta shiga share hawayen nata shima Yana tayata…ta rungumo hanunshi a jikinta kafin tace”and daddy daga yau inaso ka dena siyo mana abinci a waje…zan na shiga kitchen Ina yi mana girki da kaina”…kallonta kawai yakeyi don he’s speechless…ita Kuma ta turo baki ganin kallon da yake mata tace”ni da gaske nakeyi fa daddy”…Taheer ya lumshe ido kawai sai ya sunkuyo yayi brushing lips dinshi a kan nata for like 2 secs snn ya sake rungumeta a jikinshi gam yana cewa”yaushe baby ta iya girki ban saniba”…still bakin a tunzure tace”am going to learn..ai kowama Saida ya koya snn ya iya”…Taheer na gyada Kai yace”naji..yanxu a Ina Zaki koya”….tace”zan na downloading videos Ina kalla..and zamu fara online cooking classes cikin week din nn”…yace”that’s a great idea..kice zamu fara shiga kitchen munayin girkinmu da kanmu”…Layla da harta fara smiling tace”yeah”…ya sunkuyo daidai kunnenta yace”tell me wa ya baki wnn shawaran”…ta sake turo baki tace”ba kowa”…bakin nata ya ja da hanunshi yana fadin”idan baki dena turomin lips din nn ba zakisha mamakina wlh”…sai Kuma tasa dariya tana boye face din nata a jikinshi…shima yana smiling yace”to yanxu me zakici”…ba tareda ta dago kan nata ba ta nuna goran fresh milk dake kan table tace”nasha wnn..so am ok”…ya Dora kanshi kan nata Yana shaqan daddadan kamshin dake fita a gashinta yace”so yanxu Zaki kalla Twist Of Fate din”…ta dago kanta still smiling tace”eh mana..9 ake farawa ai”…ya mike tsaye Yana fadin”to bari in dauko fresh milk din nima insha tunda kin hanani cin abincin”…batace mai komai ba..tanadai binshi da kallo har ya fita daga parlon..ta sauke ajiyar zuciya mai karfi kafin tace”in Allah ya yadda na kusa iya girki nima”+
Shiko Taheer har yanxu bai bar tunanin waya bata wnn shawaran ba…yasan dai haka nn bazatayi wnn tunanin ba..amma ko waye ya bata wnn shawaran ya kyauta kam…dukda rashin iya girkin nata ba wai yana damunshi bane amma sai yaji idan har zata koya din zaiso hakan…at least zasu huta da fadan da sukesha wurin umm.
Washegari da safe kmr yanda ta fada..da kansu suka shiga kitchen bayan tayi downloading different videos na lunch.. breakfast da dinner…tun daren jiya take aikin kallan videos din idan yaje karshe haka zata sake dawowa…cikin vidoes din ta samu very simple one.. Wanda sukeda engredients dinshi a gida tace shi zasuyi da safe…haka kuwa akai don daga ita har Taheer din suka shiga kitchen suna yin aikin tare…basu gama breakfast dinba sai wurin 8:30 Allah yasota ma yau 9 zata fara lectures ba 8 ba..
Bayan sun gama suka haura sama kowa yayi wanka ya shirya snn suka sauka don yin breakfast din…yau da kanta tayi serving dinshi snn itama tayi serving kanta…idanunta a kanshi lokacin da ya fara cin abincin tanaso taga reaction dinshi..gabanta sai faduwa yake don gani takeyi kmr baiyi dadi ba…shiko Taheer da yaci sai yaji abincin is not that bad…tayi kokari sosae a matsayinta na first timer dai…sai ya sakan mata smile tareda yi mata alaman jinjina da hannunshi…ta saki wani wawan ajiyan zuciya tana murmushi…at least dai baice abincin ba dadi ba…sai yanxu itama ta samu ta faracin abincin…itama din bataji irin rashin dadin nn ba sosae a bakinta…so sai ta karajin dadi tareda alkawarin zage damtse ta koyi duk wasu nau’i na abinci don ta na burge mijinta itama(umh su Maryama an shigo gari😅)
STORY CONTINUES BELOW
Ko a school yau saida ta ba Hanna lbrin girkin da sukayi…Hanna nata mata dariya wai ba sabon ba…kuma ta  tura Mata wasu recipes kala kala ta WhatsApp snn ta tabbatar Mata da cewa tayi Mata registration na online classes din data fada…nan dai Hanna ta cigaba da bata kwarin guiwa da kuma nuna mata indai bata zage ta iya girki ba to tana dab da rasa mijinta…wnn mgn har yanxu Layla ta kasa sabawa dashi…duk Hanna ta fada sai taji kmr ta kurma ihu don takaici.
Gab da zasu tafi gida Hanna ta ciro wani dan abu a kwalba ta mikama Layla tana fadin”wnn sunanshi saka mai gida sambatu…small mum dina ta aikomin dashi tun daga maiduguri…wlh idan kikayi amfani dashi Jakada zakisha mamaki…da kanki zakizo kina bani lbrin yanda daddy zai susuce”…Layla ta zaro ido tana kallon dan mitsitsin kwalban da Hanna ke miko Mata…saita shiga girgiza kai tana fadin”no ki rike abinki wlh..nagode”…Hanna tai sakato tana kallonta kafin tace”ban gane kin gode ba Jakada…kodai rainawa kikai”…ta sake zaro idon tana cewa”haba Hanna ya zakice haka…kema kinsan bazan taba rainawa ba kawai idan na karba ma it’s of no use so it’s Better in bar maki abinki”….Hanna tayi shiru tana sake sake cikin ranta…dukda Layla bata fada ba tana ganin da kyar idan wani abu ya taba shiga tsakaninta da daddy…amma meyasa…yanda taga yake son nn nata sai takega ma kmr bazai iya daga Mata kafa ba…tafi minti 5 a haka kafin ta dawo da dubanta kan Layla tace”it’s ohk tunda bazaki amsa ba…ni matsayin sister na daukeki…so duk advise da zan bama sister na zan baki…bawai inaso in San sirrin gidanki bane..no inaso in fada maki gsky ne..don naga ke rainonda akai maki na gata da shagwaba ne kawai…ya kamata kisan wasu abubuwan bayan wnn especially yanxu da kike da aure…Jakada bari kiji..duk namijin dake zaune da matarshi ta Sunnah…matarda ya aureta don kashin kanshi ba Wanda aka musu auren dole ba…Kuma suka cigaba da zama ba tareda wani abu na auratayya ya shiga tsakaninsu ba gsky cikin abu biyu dole a samu guda daya a tare dashi…it’s either bashida lfy..Ina nufin baijin sha’awan mace kwata kwata…ko kuma Yana samun biyan bukatanshi a wani wurin…bai yiwuwa kiyita zaune gida daya da mijinki Kuna kwana gado daya snn ace bai taba nemanki ba koda sau daya ne wai kiyi tunanin lfy Lou…mgnr gsky ya kamata ki binciki mijinki…shifa mutum ne ba dutse ba… especially ma shi daya jima baiyi auren ba…am sorry idan abunda na fada hurts you but that’s the fact”….
Layla shiru tayi kawai tana sauraron abinda Hanna ke fada…lokaci daya zufa ya fara keto Mata..itama tana wnn tunanin but Allah ya sani tasan daddy bazai taba aikata alfasha ba..sai dai idan ko baida lfy din..wnn kam zata yadda amma bazata taba yadda da zai iya neman matan banza a waje ba…no way…Hanna da taga yanda ta fara zufa sai tayi murmushi tareda dafa kafadanta tana cewa”hey relax…am not saying mijinki na neman Mata a waje..kawai dai inaso ki gyara rayuwar aurenki ne…your hubby loves you..Yana sonki sosae Jakada banso kiyi watsi da wnn Daman da kika samu…ba kowace mace Allah kema baiwan soyayyan miji kmr yanda mijinki ke sonki ba…you have to do something…inhar Zaki iya tambayanshi ki tambaya…cikin dabara Zaki fahimta idan ma baida lfy kinga sai ku fara neman mgni…dukda he’s a doctor ko akwai na asibiti  zaku iya neman traditional one”…cikeda gamsuwa Layla tace”nagode sosae Hanna…ban San da wani kalma zan maki godia ba… InshaAllah I will try my very best… thank you so much”..
Hanna ta saki dariya tana fadin”ni ki denamin godia…what are friends for”.
10:15pm
Daidai wnn time Taheer na zaune bedroom dinshi yanata faman aiki da system…Layla Kuma na kwance nan kusa dashi tana kallonshi…tun dazu takeson yimai tambayar nn amma ta kasa…batasan ta Ina zata fara ba…Allah ya sani tana son tambayanshi amma kunya takeji…tun da tabar school zuwa yanxu thought din nn bai bar mind dinta ba daidai da one second…kawai tunanin ta inda zata fara takeyi…tun dazu take attempting fada mai sai Kuma kunya ya hanata…haka tacigaba da saka da warwara har ya kammala abunda yakeyi ya kashe bulbs din dakin snn ya kwanta shima…sai a lokacin ta matso tareda shigewa jikinshi tana ayyana girman mgnr da zata fada din…Taheer yasa hannayenshi yana sake hadata da jikinshi…a hankali yaji tace”daddy”… idanuwanshi lumshe yace Mata”na’am”…tayi shiru kafin ta sake cewa”daddy”…Taheer ya sake amsa mata Yana fadin”what is it?..”a hankali ta sake cewa”I want to ask you something..but daddy don Allah kada kace banida kunya…”Taheer ya saki murmushi cikin duhun yana cewa”umhum inajinki…bazance bakida kunya ba…”shiru ta sakeyi na tsawon mintina har saida ya sake cewa”baby go ahead Mana”…ta sake kankameshi…tana kara boye face dinta a kirjinshi…idanunta a rufe ruf ta fara mgn a rarrabe “dan…Allah..daddy…are you… alright…I mean…lfynka…qlou?…”
Taheer yai shiru yanason gane me take nufi amma Sam tunaninshi baije nn wurin ba..sai yace daita”lfy na qlou mana baby..ance maki wani abu ya faru dani ne?..”Layla taja tsaki a zuci ganin duk abinda ta fada ma bai ganeba…still idanunta kulle tace”niba haka nake nufi ba daddy..ina nufin don’t you feel anything when am with you..”…tsitt Taheer yai kmr ruwa ya cinyeshi…he never thought abunda zata tambaya knn…wai wake koya Mata abubuwa ne haka…yasanta tun tana ‘yar mitsitsiyarta so ko baa fada mai ba yasan wnn mgnr ba yin kanta bane but who…jin yayi shiru Layla ta jijjigashi tana fadin”daddy am talking”…wani dan iskan smile ya saki yana mamakin wnn sudden change din nata…a hankali yakai hannunshi tareda dago fuskanta…ya tsurama cute lips dinta ido for some secs dukda ba wani haske sosae ke akwai dakin ba…ba zato..ba tsammani kawai taji bakinshi cikin nata…ta kwalo idanuwa waje tanajin bakon al’amarin daya ziyarceta…yanda yake Shan bakin nata dama kana gani zakasan a kusa yake…kunsan tuzurai fa dama sai a hankali…Layla ta shiga mutsu mutsu tanason kwatan kanta amma ta kasa…gaba daya ma gani takeyi kmr bai San me yake aikatawa ba…tunda take dashi bai taba kissing dinta irin haka ba…tsakaninta dashi dan peck ne..amma wnn is different…lokaci daya hawaye ya balle mata jin ba iya kiss din ya tsaya ba…sai tayi regretting yimai tambayan da tayi…shiko daddy Taheer is far gone…bai San me yake aikatawa ba bai Kuma San me itama takeyi ba…yayi nisanda ko sunanshi ka tambayeshi da kyar idan zai iya baka amsa…Abun nema ne dama ya samu…Layla ta shiga kuka sosae don yanda yake kissing dinta sai kayi tunanin tsinke Mata lips din zaiyi…dama tuni yayi da wurgi da dan rigan baccin dake jikinta…lokaci daya jikinta ya fara rawa kmr mazari..so take tayi mgn ko muryanta zai dawo dashi hayyacinshi amma yaki sakin mata bakin…kuka takeyi sosae tana kokarin kwatan kanta amma Inaa…kmr daga sama ya farajin dumin hawayenta a fuskanshi…a hankali Kuma ya fara dawowa hayyacinshi…har ya saki bakin nata da sauri…ya shiga binta da kallo yana zaro ido don baisan lokacinda ya cire mata rigan baccinta ba…ya dafa goshi ganin yanda take kuka…hannu kawai ya iya sawa ya kama hanunta cikin nashi..shi kanshi nashi jikin sai kakkarwa yakeyi kmr Wanda keda very high fever…gaba daya baisan yanda akai yai loosing control dinshi ba..ya dai san lokacinda ya hada lips dinshi da nata…sai ya lumshe ido daya tuno yanda taste din lips din nata suke…sai motsi yake da baki yanason yi Mata mgn amma ya kasa…lokaci daya maranshi ya kulle yayi wani irin murdawa da bai tabayin irinshi ba…abunda yake gudun ma kanshi knn dama..shiyasa all this while yake kokarin keeping distance dinshi amma inaa..ya lumshe ido yanajin yanda Heart dinshi ke bugawa da karfi…bai taba shiga irin wnn yanayin ba all his life…da kyar yai gathering sauran energy dinshi ya matsa kusa da ita…zuwa yanzu ta dena kuka sai hawayenta da suka ki tsayawa…ya kwanta kusa daita tareda janyota jikinshi..cikin muryanshi da bai fita sosae yace Mata”this is exactly dalilinda yasa nake daga maki kafa..ke kuma ashe kallona ma kike mara amfani…”murya can kasa itama tace”but I didn’t ask you to kiss me”…yace”you’ve asked mana..kuma sai na karasa yi…ba dai ni kikema kallon mara lfy ba…”yana rufe baki tace”dan darajan Annabi Muhammad SAW kayi hakuri…wlh bazan kara ba…”Taheer dukda yanayinda yake ciki Saida yai dariya ganin yanda dan wnn abun ya gigitata..duk rananda zaayi the real deal din bai san ya zatayi ba…ya tattara sauran karfinshi ya mike tsaye…yana tafiya da kyar ya shige bathroom…ya dan jima a ciki snn ya fito…ya bude first aid box dinshi ya nemo tablet din da zaisha..ya balla snn yai dispensing ruwa a water dispenser dake dakin..yasha maganin snn ya koma kan gadon ya kwanta…yana janyota jikinshi ta matsa da sauri…sai ya saki dariya yana ce mata”zanyi miki abinda kike gudun indai baki dawo ba…”tun bai rufe bakiba ta matso jikin nashi da sauri…Taheer kam wnn attitude din nata ba karami dariya yake bashi…dukda he’s in pain amma Saida ta sashi yin dariya…Yana jinta tun tana motsi har bacci yayi gaba da ita…shi kuwa sai ya kasa baccin…abunda yaketa gujema kanshi knn dama tuntuni.
Washegari daya tashi bai sameta a dakin nashi ba…har ya shiga wanka ya fito..ya gama shiryawa tsaf ba ita ba alamarta…sai ya fito don zuwa dakinta ya dubata…to his suprise bai sameta a dakin ba…ya fito daga dakin ya sauka kasa wondering Ina ta shiga at this time of the day…kawai sai ya jiyo motsi a kitchen…wani smile ya saki..ashefa ta koma chef ya manta…Kai tsaye ya nufi kitchen din shima…duk ta barbaje abubuwa a kitchen tayi kicin kicin tana girki…Taheer Saida yai da gaske snn ya danne dariyan dake son kufce mai…ya karasa ciki a hankali…sai ji tayi yayi hugging dinta ta baya…ta tsayar da abunda takeyi cak…ya sunkuyo kanshi daidai wuyanta yace”good morning sweetheart…”Layla ta wani turo baki kafin a takaice ta amsa da”good morning…”ya juyo da ita tareda hade goshinsu wuri daya..hancinshi na gogan nata..idonshi kuwa kirr kan bakin da take turowan yace”idan na kama bakin nn naki bazakiji da dadi ba baby…”da sauri ta tura lips din nata cikin bakinta…Saida ya sake yin dariya snn ya zagayo kugunta da hannayenshi yace”me kike dafa mana ne…”shiru tayi da bakinta don Allah Allah take ya saketa ya kama gabanshi…ganin kiris ya rage tasa mai kuka sai ya saketa…yaja gefe ya zauna yana binta da kallo… cikin kankanin lokaci ta gama abunda takeyi..dama ta kusa gamawa ya shigo…shi ya tayata suka gyara kitchen din snn suka jera abincin a dinning…da sauri ta haura sama tana cemai she’s coming…dauriya kawai take amma maranta ya fara Mata ciwo…tunda ta tashi yau dashi ta tashi…dama tasan date dinta ya kusa…tsoronta Allah tsoronta kar ya kwantar da ita don ko kadan batason yin fashin zuwa school…a gurguje ta gama shirinta snn ta sauka kasa…ta sameshi zaune a dinning din…tana zuwa tai serving dinshi kawai itama tayi snn suka faracin abinci…yau ma dai la ba’asa..girkin nata bazaace baiyi dadi ba don tana kokartawa sosae…
Suna gama ci Kuma suka fita…tun a hanya ya lurada ita kmr batajin dadi..bai dai ce Mata kala ba Saida suka isa makarantan..kafin ta fita a motan ya zaro drugs din daya fito mata dasu…don Yana sane period dinta na iya zuwa yau…Mika Mata drugs din yai Yana cewa”take..duk kikaji maranki ya fara ciwo sai Kisha..idan Kuma kinga bazaki iya zama ba just give me a call..sai inzo in maidaki gida…”ta sakin mai murmushi snn ta amsa drugs din…bayan ta fita daga motan tace”thank you”..shi Kuma ya daga Mata kai snn ta tafi…shima ya tada motan ya tafi..cikin ranshi ko har yanxu bai bar tunanin scene dinsu na jiyaba..kawai sai ya sake sakin smile Yana shafa gemunshi…ya tabbata ba don period dinta da yake expecting ba..da ba abunda zai hanashi angoncewa yau..but zai jira har zuwa time din da zata gama period din…he really can’t wait…
A can makarantan nasu kuwa..Layla bata bama Hanna lbrin yanda sukai da Taheer ba..itama Hanna bata tambayeta ba..don bincinke is not her thing…sukaci gaba da abubuwansu as they used to.
Bayan sun gama last lecture dinsu duk kowa ya gaji so kawai yake a tashi…sai lecturer din ya tsaidasu wai zai raba musu assignment da sukayi submitting tun last week…Layla na duban Hanna tayi kasa da murya tace”kiji mutum don Allah..kowa ba class rep yake ba assignments din ba.. meye shi zai wani tsaidamu wani wai zai raba mana assignment…”itama Hanna murya a kasa tace”ki rabu da gulmamme Mana..shegen rawan Kai ne dashi”..
Yayinda suke gulmarsu…shi Kuma lecturer din nasu mai suna AY Gambo yanata Kiran sunan mutane yana raba assignment din..kmr daga sama taji yana Kiran Maryam Taheer Jakada…Layla ta mike a hankali daga seat din da take…ta fita zuwa inda yake..dukda idanunshi na boye cikin galsses saida jikinta ya bata he’s looking at her…itadai kanta kasa harta karasa inda yake ta amsa abunta…abun mamakin Kuma..yana bata nata sai ya tattare sauran papers din yacema class rep dinsu ya karba ya karasa…da hanzari kuwa class rep din yazo ya amsa..su Kuma Layla da aka basu nasu sai suka fita daga class din.Suna fitowa Hanna ta wuce don already Habibinta na waje yana jiranta…Layla ta rakata suka gaisa dashi snn ta samu wuri ta zauna nn parking lot din tana jiran Taheer…zuwa yanxu maranta ciwo yakeyi sosae…bata taba tunanin she is this strong ba sai yau…bata dade zaune a wurin ba ta hangoshi yazo…ta wani kauda Kai ita a dole yayi mata ba daidai ba…tun kafin ya gama parking dama ya hangota..so yana yin parking din ya nufi inda take…Yana isa ya kama hanunta ta mike tsaye..still bata kalleshi ba…shi Kuma yai murmushi snn ya shiga janta har zuwa inda motanshi yake..ya bude tareda sata ciki snn shima ya zagaya ya shiga…bayan sun fara tafiya ya dubeta har yanxu bai dena smiling ba yace”come on talk to me mana baby..sorry for keeping you waiting”…yana rufe baki ta juyo tana kallonshi da idonta daya cika da hawaye tace”bani da lfy..tun daxu nake jiranka baka zoba”…ya kamo hanunta ya rike yace”to kiyi hakuri ki yafemin kinji…wasu mutane aka kawo emergency wlh..I can’t leave ba tareda na dubasu ba”…batace komai ba sai kifa kanta da tayi kan laps dinta tana cigaba da kuka don ciwo yake Mata sosae…Taheer na rikeda hanunta har suka karasa gida…ko parking din kirki baiyi ba ya bude motan ya fita…ya zagaya side dinda take ya dauketa cak yai cikin gidan da ita…Saida ya haura sama har dakinshi snn ya ajiyeta kan gado..ya lalabo injection da zaiyi Mata da sauri ya shiga withdrawing dinshi..yana gamawa ya karasa inda take ya dagota..yana share Mata hawaye shima kmr zaiyi kukan yace mata”baby kukan ya isa haka don Allah..bari inyi maki alluran..kinci abinci dai koh”…tana hawaye ta daga kanta alamar taci..shi Kuma Taheer ya mikar da ita tsaye snn a hankali yayi Mata alluran…Yana gamawa ta sake rushewa da kuka tana kokarin durkushewa a wurin ya kamota jikinshi da sauri…ya kwantar da ita kan gadon shima ya zauna gefe…hanunta cikin nashi yace”baby dan girman Allah kibar kukan nn haka..you have no idea of what am feeling right now..da ciwon naki zanji ko da kukan da kikeyi..or do you also want me to cry?..”ta girgiza mishi kai da sauri..ta sake rike hanunshi dake rikeda nata tace”to na dena daddy..amma fa ciwo yakemun inaji kmr zan mutu ne dad…tun kafin ta karasa ya katseta ta hanyar rufe Mata baki da hanunshi…ya janyota ya dora kan laps dinshi..yana kallonta da idanunshi da sukai jaa sosae kmr zaisa kukan shima yace”ki dena cewa zaki mutu don Allah baby..bakijin tausayina koh”…Layla ta sake lafewa a jikinshi tana sauke numfashi…shima ya gyara mata kwanciyan a jikinshi yana goge Mata hawayen yace”InshaAllah Zaki samu lfy kinji koh..bazaki mutu ki barni ba Bi’iznillah”…
+
Daren nn dai basu samu isashshen bacci ba…sai wurin karfe 3 ciwon ya lafa Mata shine ta samu bacci…shikam ji yayi bazai ma iya baccin ba…jiki a sanyaye ya mike zuwa bathroom ya dauro alwala snn ya fito ya fara sallah.
Da safe data tashi ta samu sauki sosae…ya dauketa da kanshi zuwa toilet din dakinta…ya hada mata ruwan wanka tayi..ya taimaka mata ta shirya snn yace bari ya siyo musu breakfast ya dawo..kememe Layla ta hanashi fita wai ita lallai bazai sake zuwa eatry siyan abinci ba..gashi Kuma ita bazata iya yin girkin ba..haka nn ya hakura ya dafa musu tea da kanshi snn ya soya kwai..ya dauko bread da jam..ya hada komai kan tray snn ya dauka zuwa sama..ya ajiyesu nan dinning din dake parlon snn ya shiga dakinta ya fito da ita…sai mita takeyi wai ita zata iya zuwa school ta samu sauki amma ya hanata…yace Sam bazai yadda ta bar gida ba sai ya tabbatar da she’s alright.
Bayan sun gama Breakfast din suka cigaba da zama nn parlon..ya kunna musu wani movie a system dinshi sunata kallo..tana lafe a jikinshi bacci ya dauketa…ya maidata zuwa dakinta ganin time din sallah yayi…yana fitowa ya daura alwala snn ya tafi masallaci…bai wani jima a masallacin ba ya dawo..don hankalinshi gaba daya yana kanta..baiso ta tashi daga baccin bai dawoba..yana haurawa sama sai yaga har yanxu bata tashi a baccin ba…ya zauna knn zai cigaba da kallon da yakeyi yaji ana danna doorbell…ya ajiye system din ya sauka kasa..yana tunanin wane bako sukayi ya isa kofan ya bude…sai ya zare idanu ganin Ummi da Umma tsaye a bakin kofan…ummi tace”ko mu koma ne naga ka wani tsatstsaremu da ido”…Taheer ya saki smile snn ya matsa daga hanyar suka shigo…yace”ummi ai banyi expecting dinku bane shiyasa..sannunku da zuwa”…bata amsa mai ba suka karaso parlon suka zauna…shima ya zauna kusada umma…bayan sun gaisa ya mike zuwa kitchen tareda dauko musu drinks da ruwa ya kawo parlon..bayan ya zauna sai ya kamo hanun umma cikin nashi yace”nayi missing dinki sosae ummata”…umma tai murmushi tareda shafa kanshi tace”and I missed you more”…ummi dake zaune gefe tana dubansu tace”Ina matar gidan takene wai..ko an tafi makarantan ne”…Taheer yace”yau bata samu zuwa makarantan bama ummi..batada lfy”…ummi ta zaro idanuwa tace”batada lfy Kuma..meya sameta ni Maryama”… maimakon ya amsa mata sai ya mike yace”muje ku ganta tana sama..bacci takeyi”…gaba dayansu suka mike tareda bin bayanshi zuwa upstairs…har dakin Layla suka shiga..tana kwance kan gado tana baccinta hankali kwance…ummi ta karasa kan gadon da sauri ta zauna..har ta Kai hanu zata tashi Laylan sai ta fasa..snn ta dawo da kallonta ga Taheer tace”kai kodai ciki garta ne..inba hakaba to wnn baccin dun na meye”…Taheer ya zare idanu yana kallon ummin kmr zaisa kuka yace”haba ummi ciki Kuma ana zaune qlou”…ummi bata sakebi ta kanshi ba ta shiga tashin Layla daga baccin…a hankali ya fara bude idanunta har ta saukesu kan ummin…sai ta mike zaune da sauri tana fadin”ummi yaushe kukazo”…maimakon ummi ta amsa mata sai tace”ke me yake damunki ne haka..ciwon me kikeyi”…a hankali Layla tace”marana ke ciwo ummi..jiya ko bacci banyiba kmr zan mutu wlh”…ummi tace”tooh ciwon mara Kuma..Kai ba ance ana dainawa idan anyi aure ba”…ta karasa mgnr idonta kan Taheer da har yanxu ke tsaye…ya dan dukar da Kai snn yace”ana denawa mana..itama zata nasan zata Dena kawai lokaci ne baiyiba”…umma dake zaune gefen gadon itama tace Mata”sannu Layla..Allah dai ya rabaki da wnn wahalan”…ummi tace”Ameen”..sai Kuma ta mike ta shiga bin dakin da kallo tace”to har yanxu dai banga datti cikin gidan naku ba…Ina sane nace Aisha kar ta sanar daku zamuzo don inaso inga wainar da kuke soyawa”…babu Wanda ya tanka ta acikinsu…suna gani ta bude bayi ta leqa snn ta sake fitowa ta fita daga dakin…umma girgiza kai tace”Hajia Yaya ikon Allah”…sai Kuma ta dawo da kallonta kan Taheer tace”zafa muyi mgn son”…Taheer na dubansta shima yace”to muje dakina umma”…bata sake mgn ba ta mike..shi Kuma ya karasa inda Layla take..yai kasa da murya yana ce Mata”koma kicigaba da baccinki baby..yanxun nn zamu dawo”…ba musu kuwa ta koma ta sake kwanciya..shi kuma hadda rufeta da duvet snn yabi bayan umma da har ta riga ta fita daga dakin…suna shiga dakinshi in a serious tone umma tace”fadamin tsakaninka da Allah.. yarinyar nn ajiyeta kawai kayi kana kallonta koh..har yanxu bakayi hankali ka dena cutar kanka ba koh”…dan murmushi ya saki yana shafa Kai..yasan dama da kyar idan umma bata ganoba…a hankali yace”umma ni tausayinta nakeji wlh..she’s too young for that..ko 18 fa bata karasa b…”tun bai karasa ba umma ta katseshi da fadin”rufemin baki da Allah..da can baka San she’s too young dinba sai yanxu..haka zaka ajiyeta kana kallo knn kai bazaka tausayama kanka ba..idan Kuma da gaske bakada lfyn sai ka fada a nema maka magani”…da sauri yace”wlh lfyna qlou umma..kawai banso tasha wahala ne”…this time muryan umma a hankali tace”ka gwammace Kai kayita Shan wahalan knn…wane irin so kakema yarinyar nn ne Taheer da baka ganin komai sai ita…ko kanka baka dubawa sai ita..wane irin abune wnn fisabilillahi sai kace shanyayye”…jiki a sanyaye ya Dora kanshi kan kafadan umma…murya can kasa yace”wlh umma ni kaina ban san irin son da nake Mata ba…inajin zuciyata kmr babu komai a ciki sai ita..duk wani abu da zai dameta yana daga mun hankali fiyeda yanda zakiyi tunani..shiyasa nake hakuri sbd bazan iya jure ganin tana Shan wahala ba umma”…ajiyar zuciya mai karfi umma ta sauke kafin a hankali tace”nidai duk da haka bai kamata ka ringa cutar da kanka ba Taheer..she is your wife afterall..ba wanda zaiyi questioning dinka kan duk abunda zai faru tsakaninku”…ya dago kanshi zaiyi mgn sai ga Layla ta shigo dakin…ya mike da sauri ya rikota yana fadin”meya fito dake baby..bakijin mgn koh”…ta lagabe kai tana cewa”naji sauki fa daddy..ummi ce take nemanku”…umma najin haka ta mike suka fita daga dakin…Taheer na rikeda hanun Layla suka sauka kasa…ummi dake zaune parlor tace”Allah ya taimakeku banga wani abun da ba daidai ba a gidan..yau da naci mutuncinku wlh”…Taheer na murmushi bayan sun zauna yace”baby fa yanxu har girki takeyi ummi”…wata harara ummi ta maka mai tace”yause ka maidani kakar ka ban saniba”…Layla ma dariya tace”Allah da gske yake ummi..ko jiya ma ni nayi girki na da kaina”..dan tabe baki ummi tayi tace”da yake girkin lokaci daya ake koyanshi ba”…Taheer yace”vidoes take downloading a YouTube tana gani ummi..Kuma sunayin online classes”…cikeda fara’a ummi ta kalli Layla tace”Dan Allah da gaske”… Layla ta daga kai itama tana murmushi…umma ma murmushin tayi kafin tace”to ko ku fa..amma ace mace ta zauna bata iya girki ba Kuma bazata koyaba ai da matsala”…tana rufe baki ummi tace”gane min hanya dai Aisha..da duk tasan da wnn din ta ringa yi mana iskanci..da kin zauna baki koya dinba kanki Zaki cuta ai..Allah na tuba mazan nn na yanxu da ba shedan su akeyi ba..kina zaune zaije ya dankaro maki kishiya tazo ta kwace maki shi”…Taheer ya rausaya kai yace”Kai ummi..yanxu hadda ni cikin Wanda bazaa sheda din ba”…”hadda Kai Mana..ko kai sunanka mace ne ba namiji ba..duk mazan yanxu halinsu daya ai..sai dai wani yafi wani amma gabaki dayanku ba tabbas garesku ba”…Layla taji gabanta ya Fadi da furucin ummi…idan bata manta ba irin mgnr da Hanna ma ta fada knn…kenan da gaske ne maza basuda tabbas din..ita kuwa idan daddy ya dena sonta ko ya Kara auren wata ai ta gama yawo..tasan har ta rasu bazata samu Wanda zaiyi Mata irin son da yake Mata ba..
STORY CONTINUES BELOW
A takaice dai nan su ummi suka karasa yininsu a gidan…sunsha hira sosae snn an sake yi musu nasiha na zaman aure…sai after magrib suka maidasu gida..
Saida Layla ta kwana uku snn period dinta ya dauke…sai yau ne Kuma zata koma makaranta don kiri kiri yace bazata jeba sai ta warke gaba daya…suna gama breakfast suka fita don shima da wuri yake son ya isa clinic yanada theatre karfe 10.
Yana dropping dinta ya tafi…ita Kuma ta shiga ciki…tana shiga class Hanna ta taso ta rungumeta tana fadin”babe nayi missing dinki sosae ‘yan kwanakin nn…ya jikin naki”…Saida suka karasa suka zauna snn Layla tace”jiki alhamdulillah na warke..Ina Habibi”…Hanna ta wani kashe ido tana cewa”Habibi na wurin aiki wlh..har kin tunomin dashi”…dariya Layla ta saki kafin tace”Allah ya shiryeki wlh..yanxu sai kixo ki koyamun abubuwan da akai bana nn”…da sauri Hanna tace”yawwa you remind me of something..kinsan tun ranar nn kullum sai AY Gambo ya aiko a kiraki baki nn..wai meya hadaki dashi ne”…Layla na kallonta da mamaki tace”waye AY Gambo Kuma”…tsaki Hanna taja kafin tace”AY Gambon ne baki saniba Kuma yau”…Layla ta zaro idanu don sai yanxu ta ganeshi…ta bude baki zatayi mgn sukaji Class Rep dinsu yace”Jakada kije AY Gambo na nemanki…kwanakin nn da baki zoba sai da na gaji da aiken a Kira mai ke wlh..kullum sai ya kirani a waya wai in turo mai Maryam Jakada”…lokaci daya Layla taji wani irin faduwar gaba ya risketa..to laifin me tayima AY Gambo Kuma..iyaka tunaninta bata gano laifinda tai masa ba..don haka sai ta dubi Hanna tace”babe bari inje in dawo..Allah dai yasa lfy”..Hanna tace”Ameen Ameen..be careful okay”…Kai kawai Layla ta iya daga Mata snn ta dubi Class Rep din nasu tace”Yana Ina?…”muje in nuna maki office dinshi”…cewar Class Rep din knn yayinda ya juya ya fita daga class din…a hankali Layla ke binshi a baya har sukazo office din…shi ya fara shiga snn itama tayi Bismillah ta shiga…Yana zaune bisa office chair dinshi yana dan juyawa…idanuwanshi rufe ruf kmr mai yin bacci…matashi ne Wanda akalla bazai haura 31 zuwa 32 ba a shekaru…yanada haske amma ba sosae ba..snn yanada tsayi haka Kuma bai da jiki sosae…Class Rep din ne yace”Sir gata na rakota”…ya bude idanunshi da sauri snn ya saukesu kanta…ya shiga binta da wani kallo kmr Wanda keson gano wani abu tattare da ita…ya kwashi almost 6 mins yana kallon nata kafin ya zaro kudi a aljihunshi ya mikama class rep din yace”you can go”…Class Rep na amsan kudin ya juya tareda fita daga office din…ya sake maido da idanunshi kan Layla dake tsaye kanta kasa..sai wasa takeyi da fingers dinta…a hankali taji yace”ki karaso mana ki zauna Madam..ba pepper soup din mutane nakeyi Ina cinyewa ba”…jiki a sanyaye Layla ta karasa ciki ta zauna…har yanxu idanunta na kasa tace”Good morning Sir”…shiko yai relaxing kan kujeran da yake Yana kare Mata kallo at the same time yana murmushi…Saida ta sake maimaita gaisuwan snn yace”good morning princess ya jikinki”…wani irin faduwa gabanta ya sakeyi jin sunan da ya kirata dashi..Allah dai yasa ba abunda take zargi bane…har yanxu bai bar kallon taba yace”I was very worried about you..har na fara tunanin ko gida zanzo in dubaki”…mamaki ya sake kama Layla..ya akai yasan gidansu toh..ko dai kawai ya fada ne…a hankali ta dago tareda yimai one second look kafin tace”Sir you called for me”…tana rufe baki yace”I know..inaso in fanshe kwanakin da ban kalleki bane”…wnn karon dubanshi tayi da kyau snn tace”ban gane me kake nufi ba Sir”…ya saki wani smile still Yana kallonta…Saida ya kwashi kusan 3 mins snn yace”from the very first time da nayi setting idanuna kanki na rasa sukuni…what have you done to me?..”Layla tayi tsitt tana jira ya kai inda za tace mai tanada aure and leave…”am asking you princess what have you done to me dana kasa dena tunaninki even for a second”…banza ta sakeyi dashi don she don’t have answer to his stupid talks…bai damu da shirun taba yai kasa da murya yace”well tunda bazaki fadi abunda kikai min ba let me tell you abunda ke cikin raina…I think I love you…I love you much more than you could imagine”…fuska daure Layla take dubanshi…dama inda takeso yazo knn Kuma yazo…cikeda bacin rai tace”Sir am sorry..Ni matar aure ce”…ya saki wani smile shima yace”Ma  am sorry..Ni mijin aure ne”…a kufule ta sake dagowa tana dubanshi..bata San Kuma me zata fada mai ba…yana kallonta shima yace”do you think wnn mgnr da kika fada zaisa ince na dena sonki ne..to ki kalleni da kyau da gaske nake sonki bada wasa ba..nasan Mata irinku dama sunada habit din cewa sunada aure in order to get rid of wadanda ke sonsu”…zuwa yanxu tsoro ne fal cikeda zuciyar Layla..ta fuskanci da gasken fa yakeyi kmr yanda ya fada..ya zama dole ta sashi ya yadda ce wa tanada aure..idan ba hakaba kuma zatasa kanta cikin matsala…a nutse tace”wlh Allah Sir ba karya nake maka ba..inada aure”…shiru yai yana kallonta..cikin ranshi ya kasa amincewa tana da aure..gani yake kmr raina mai hankali take…ita Kuma Layla ganin yayi shiru ta mike tsaye tana cewa”Sir I have to go kar a fara lecture ban koma ba”… wrist watch din hanunshi ya duba yaga time ya wuce Kam..ya mike tareda zagayowa inda take kafin yace”to muje in rakaki”…Layla ta sake zaro idanu tana girgiza kai tace”no thanks..ba sai ka rakani ba pls”… murmushi ya Kara saki kafin ya karasa bakin kofa ya bude mata..snn yace”to zo ki tafi abinki..inaso in Kara mgn dake before you leave”…bata sake cewa komai ba ta fice daga office din…gabanta har yanxu bai dena faduwa ba..ga wani tsananin tsoro daya baibayeta..idan daddy yaji wnn mgnr Allah kadai yasan abinda zai iya aikatawa…ta tuna yanda yakeda kishi a kanta…ko kallonta namiji ya fiya yi haushi yakeji inaga Kuma yaji mgnr wani na sonta..Kuma da aurenta… innalillahi wainna ilaihi rajiun…taketa maimaitawa har ta karasa class..Allah ya taimaketa tana shiga lecturer dinsu ta shigo…tai shiru kawai idanunta kan lecturer din daketa explanation amma hankalinta kaf baya wurin..tunanin abun daya faru kawai takeyi…har wani kuka kuka taji yana son taho Mata..ya zatayi da wnn masifa daya tunkarota.
Lecturer din na fita ta matso kusada Hanna tana hawaye tace”Hanna na shiga uku..kin San me mutumin nn ke cewa kuwa”…da sauri Hanna ta girgiza kai tace”Me ya fada maki”…Layla na kuka sosae tace”cewa yake wai yana Sona Hanna..just imagine”…idanu Hanna ta zaro before saying”and why didn’t you tell him that ke matar wani ce”…tana rufe baki Layla tace”Na fada mashi wlh..amma kmr bai yadda dani ba..ki taimakeni Hanna ban San zanyi ba wlh”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page