DA KAMAR WUYA COMPLETE BY ZULAIHATIDRISMISAU

DA KAMAR WUYA CHAPTER 9 KARSHE BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

 DA KAMAR WUYA CHAPTER 9 KARSHE BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Very sorry, na jina shiru, kwana biyu. Sai dai nayi

Hadaddiyar walima su Hafiz omer suka hada na maza, a eat more restaurant.

Taran suna ya kayatar matuka, ta fannin hubby ma. Ta samu alkhairi da yawa, kamar me bude shop. Kawayenta da yan’uwa sun matukar taka rawar gani.+

Sunyi wanka sun kwanta, don huta gajiya. Hubby kam harda ciwon kai, sai da tasha magani tukun.

Hayder yayi musu sallama ya shigo. Gwaggo ce ta harareshi.  Smirk yayi mata yana kashe mata ido daya. Duk yadda gwaggo taso masa rashin mutunci yasan ta yanda zai zille. Mikewa tayi ta fita tana mita. Don ba karamin aikinsa bane ya mammatse mata jika a gabanta, yau bata shirya ganin wannan fitsarar ba, gara ta bashi wuri.

Hubby na tsaye jikin mirror tana tufke gashinta, da yasha gyara, sai kamshin da daukar ido yake. Murmushi tayi ganin drama din gwaggo da hayder.

” kafa takurawa gwaggo, bacci take son yi.” Hubby ta fada tana murmushi

Rungumota yayi jikinsa. ” dole tabari inyi sallama da iyalina.” Ya fada yana kai mata kiss a kumatu ” ya akaji da jamaa?” Shafa kansa tayi, tana murmushi ” alhamdulillah, sai ciwon kai dake damuna.”

Ido yadan fito dashi. ” kinyi takin medicine ko?” Ya fada cike da damuwa, yana Jan hannunta, zuwa bakin gadon, Ya zaunar da ita ” nasha.” Ta fada tana dan lumshe ido cike da shagwaba. Kan ya kama ya mata addua. ” Allah ya sauwake.” Amin” ta fada tana daura kanta akan kafadarsa.

” yaushe zaki koma gidanmu ne? Na gaji da takurarsu Hajiya. ” ya fada in his husky voice

” in 40days time. ” da sauri ya dago fuskarta yana kallonta. ” are u serious? ” ya fada cike da damuwa

Gira ta daga masa, tana murmushin mugunta.

Shiru yayi yana kallonta, can taga ya saki smirk, tare da mikewa, ya dauko bebynsa dake kwance a cikin gadonta tana bacci.

Kiss ya manna mata a goshi. Tare da rungumeta a jikinsa. Motsi tayi, tana son tashi, jijjigata ya fara a hankali. Hubby na zaune daga bakin gado tana murmushi. Sun burgeta matuka, hada ido sukayi, ya daga mata gira, yana mata alama da fuska ” what. ” yatsunta  biyu ta hada, alamar sun mata kyau.

Smirk yayi, ya tako zuwa inda take zaune.

” kana son ka tasheta, ta hanamu bacci ko?” Hubby ta fada cike da shagwaba

” that’s agric chicken beby ai!!” Ya fada yana smirk

” yanda na gajin nan, ta ce zata hanani bacci duka zata sha.” Ta fada

” don’t even try it.” Ya fada in serious tone

” like father like daughter. ” ta fada a hankali, a tunaninta baiji me ta fada ba.

Smirking yayi tare da hade fuskarsu, bakinta ta daura a kan nasa, kamar yana jira ya kamo harshenta. Kissing din juna suka fara, so romantic so fashionable. Beby na rungume still a jikinsa.

” balarabe koka fito, ko in taso Hajiya ta fitar min dakai, yara ba kunya.”

Gwaggo ta fada daga bakin Kofa tana huci.

Hubby tai saurin zare bakinta, tana dariya kasa- kasa. Tsaki yayi, ya kwantar da amatullah tare da mata manna mata kiss a kumatu.

Dawowa yayi, ya rungume hubb, kissing dinta ya fada, hannunsa na yawo a kirjinta, don yayi missing dinsu sosai. Gaba daya sun manta da gwaggo dake bakin Kofa tana huci.

” ai shi kenan tunda bazaka fitoba, bari inje in taso uwar taka.” A sama suka fara jin muryar gwaggo.

Da sauri hubby ta zare jikinta, ” good night. ” ya fada in husky voice yana mata blowing din kiss. Fuskarsa dauke da faraa ya fita.

Gwaggo ya hango da Hajiya, ai da sauri ya nufi Kofa ” Allah bamu alkhairi. ” ya fada yana barin dakin.

” Allah ka shirya, na rasa lokacin da hayder ya fitsare kafarsa haka.” Hajiya ta fada

Juyawa gwaggo tayi, ta nufo dakin. A kwance ta samu hubby. ”

Tana adduar bacci, bayan ta gama ma amatullah nata. Harararta gwaggo tayi ” ki ci gaba da biyeshi, sai ya kaiki ya baro, zakiyi bayani.” Shafa adduar tayi cikin shagwaba tace ” ni kuma me nayi da daddaren nan.” ” ban Sani ba.” Gwaggo ta fada cikin jin zafi.

” Allah baki hakuri.” Hubby ta fada

” kayane nade gammo ki dauka, da bakya biye masa, ai da ba haka ba. Amma ke dadi miji, jiki na rawa! Anga miji, ke zaki shiga uku randa ya kara dura miki wani cikin, yarinyarki batayi kwari ba.”

Ajiyar zuciya hubby ta ja, ta gyara kwanciyarta. ” ba amin ba, wallahi.” Ta fada a kasan ranta.

                *****************

Hubby da bebynta sunyi kyau sunyi bul-bul dasu saboda kulawa ta musamman da suke samu. Kwanan hubby 25 da haihuwa, Ummul khair ta sanbalo nata beby boy din. Zo kuka murna wurin su hubby, ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a abuja. Amma ba dama. Ranar suna yaro yaci sunan Yusuf, wannan karamci da mijin Ummul khair yayi musu, ya matukar musu dadi, da kara ganin kimarsa a idon daikacin xuriar zubair Oregon.

Bayan sunan bebyn Ummul khair, gwaggo ta koma kankiya, Hajiya ta ci gaba da kula dasu hubby, a lokacin tafiya ta kama hayder zuwa China, ya tafi cike da kewar iyalansa.

              *******************

Yau hubby ke shirin komawa dakinta, komai ya kammala na daga gyaran gida, da sauransu. Ta fannin gyaran jiki ma, baa cewa komai, don Hajiya zagewa tayi ta gyara ma auta matarsa tsaf. Ciki da waje, da taimakonsu Hajiya Balkisu.

Hubby a gidansu ta wuni a ranar, wanda daga nan zata wuce gidanta. Kayanta already sun riga sun isa. Hayder ma suna sa ran dawowarsa a ranar, ko washegarin ranar.

Mommy Hauwa ce, goye da amatullah da ranar take jin rikici da koke koken, Sai faman jijjigata take. Junaid ya shigo da sallama. Dariya yayi ganin yadda mommy Hauwa ke safa da marwa. ” lallai mommy, bakya kishi, ta kwace miki miji, ki tsaya kina lallashinta! Jiyafa naji daddy yana zuwa umran bana shida amatullah ne.”

Murmushi mommy tayi ” wane ita!!! Gadon ari sai ganna! Can dai.”

” an riga an gama, ta riga ta rushe gomnatinki a wurin daddy.” Junaid ya fada yana murmushi tare da mata wasa daga bayan mommy.

” anya ma mommy bake kika muntsineta ba? Amatullah ba ta rikici, yau daga zuwa gidanki ta rikice da koke koke.” Ya fada

” inda mintsinin na mata ai daba haka ba? Amma tunda kace haka, tana kara bude mana katon bakinta zan mazgeta.” Mommy Hauwa ta fada still tana jijjigata.

“Afuwan!!!! Ina katon bakin? Kina ganin yarinya zankaceceya, wanke hannu ka taba. Shiyasa daddy ya rikice ai.”

” nunan ranar?” Mommy ta fada tana tabe baki

” kala mai tsada” ya fada yana dariya

” nima in naga dama sai in siyo, tunda gashinan a shago ana siyarwa.” Inji mommy

Dariya sukasa gaba daya. Hubby dake zaune tana jinsu, Itama dariyar tayi.

” natural is far better than artificial. ” ya fada yana zama kusa da hubby

” sis how far?” Ya fada yana murmushi.

” fine!! Baka tafi ba Ashe?”

” yes!!! Sai next week.” Ya fada yana Sosa kai.

” rashin mutunci da kukaje kukayi kenan ashe? Yaushe zaku girmane?” Ta fada in serious tone

Murmushi junaid yayi. ” wannan ba rashin kunya bane, kwatar yanci ne.”

Mommy Hauwa hubby ta kalla. ” mommy yanzu abinda sukayi, da gaske ya dace?.”

Murmushi mommy tayi ” sun burgeni gaskiya, da ana haka da an zauna lafiya.”

Ido hubby ta zaro, cike da mamakin maganar mommy Hauwa

” to ni meye nawa? Mijinkine ya gayyacemu, mukuma muka amsa kira, so in ma rashin mutuncinne shi zakiyiwa not me.” Inji junaid

” Allah ya shiryeku daga Ku har shi.” Hubby ta fada

” amma sis kema akwai daukan dumi. Kiga yanda dan banzan nan ya mayar da fuskar Anty samira, ya zage ya bugeta, kamar ya samu kato sa’ansa. Kodon albarkacin ya’ya ai ko mai ta masa ya hakura, ko yabi ta wata hanyar ya rama, ba ya zage ya doketa haka ba, abin haushin ga ciki, Allah yasa ma anyi saurin kaita hospital da Allah kadai yasan yadda abunda zai faru.” Ya fada cike da takaici

” koma menene, ai ita tajawa kanta.” Inji  Hubby

“Duk da haka!!! Amma hakkinsa ne, ya kare martabar yayyensa da kannensa. Don na tabbata da kece, zanyi abinda yafi haka. Sai kinga idon dan banza.” Junaid ya fada yana dariyar mugunta

Mommy da ta fito daga wantar da amatullah da tayi bacci, ta samu wuri ta zauna. ” ban labari ya akayi, kasan jiya daga sama na tsinci maganar.” Inji mommy Hauwa

” hayder daya je hospital yaga halin da take ciki, hankalinsa ya matukar tashi. Ritsata yayi, kan saita gaya masa gaskiyar abinda ya hadasu, don kar ya dau mataki, daga karshe a samu itace batada gaskiya, tunda yasan halinta. Ashe wai kanwar mijin ce taga Abdul Karim, tace nan duniya shi take so, ke kuma Anty samira kika mata alkawarin duk runtsi zakiyi yadda zakiyi, Abdul Karim ya aureta. Wannan shine babban dalilin da Anty samira tashiga ta fita, tayi kutin kutin dinda aka fasa auren hubby da Abdul Karim. Saboda ta cika wannan alkhawari data dauka. Rashin jiyuwan daya shiga tsakaninta da Abdul Karim bayan rashin aurensa da hubby, shiya haifar da rashin cika wannan alkawari data dauka. Sai ya zama tun daga auren Abdul Karim zuwa lokacin babu jituwa tsakaninta da dangin mijin, don sun san da maganar. Ranar kanwar tazo wai tayi mata rashin kunya, tare da gaya mata maganganu marasa dadi, shine ta mareta, daga nan sai fada ya tashi, dakyar aka rabasu. Shi kuma yana dawowa, bajin baasi ya hauta da duka, saboda daga can gidansu an ce mai samira ta fara dukanta, tana aibatata, harda cewa itama kaddara ce ta sata auren dan uwanta, in ba haka ba har yaushe zata hada jini dasu, da har zatayi marmarin kara hada zuria dasu.

So muna gidansu Hafiz, hayder ya kiramu, kan kowa yayi shirin kwallo, mu sameshi a main house. Ni, Hafiz, amir, sai abokinsa aminu.

Daga main house gidan Anty samira muka nufa, kallonsa muke cike da mamaki, kasa hakuri nayi na tambayeshi. ” wani zamu dan koyawa hankali, gobe ko kanwarsa ce bazai sake daura hannunsa a kan taba.”

Nan ya mana bayanin komai, duk jikinmu yayi sanyi. Ko da mukaje kin fitowa yayi, ni da aminu muka shiga har gidan muka fito da shi ta karfin tsiya, zuwa farfajiyar gidan.

Hayder na zaune a saman matar da mukazo da ita. Cike da shan kamshi ya tambayeshi ” me yayata tama ka mata irin bugun nan kamar ka samu jaka? Sannan an kaita hospital yau kwana daya baka samu zuwa kaga a halin da take ba? Bayan kasan akwai kwanka a tare da ita?” Rarraba ido ya fara musamman ganin yadda muka zagayeshi ba hanyar tsira, don maigadin ma kulleshi a dakinsa mukayi.

” wannan ba maganar yara ba ce! Da manyanka zanyi magana.” Ya fada yana cika, duk da alamun tsoro ya bayyana a tare dashi.

Smirk hayder yayi. ” good. ” ya fada yana kallona, but na nufa, na dauko dorina guda hudu, na dawo na mikawa kowa dai dai, naja na tsaya.

Kallon dorinar yayi, ya bimu da kallo cike da firgici da tsoro, wanda zuwa lokacin ya tabbatar ba wasa ya kawomu ba.

Durowa hayder yayi ” zamu daku dani da kai, wanda ya ba wani kashi shikenan! In kuma kaga hakan bai yi ma ba, to ka kwanta salin alin kasha dorina. Kaga gobe ko kudi aka baka baza ka kara marmarin tabamin yaya ba, don kasan akwai masu rama mata. Daga nan sai mu karasa wurin manyan da kace su karasa nasu hukuncin.”

Kallon hayder yayi, maji karfi, jikinsa a mummurde, ya kalli sharbebiyar dorinar dake hannunsa, yana hadiye miyau, da Jan numfashi. ” duk abun bai kai haka ba, nasan nayi kuskure, dama yanzu nake son in shirya inje in bada hakuri,” ya fada cikin rawar murya

” ka makara ai, tunda har nazo.”

Bansan hayder mugu bane sai ranar. Yarda bulalar yayi yahau kilansa, saida ya masa lis, dakyar muka janyesa. Mota ya koma ya dauko paper da pen ya dawo. Dagoshi yayi ya zaunar dashi, tare da mika masa ” oya!! Rubuta mata takardarta, don baka can can ci, mijin da zata ci gaba da zama dashiba, mijin da baisan darajar matarsa ba, da kimarta, baya la’akari da zuriar da suke tsakaninsu, ya iya mata wannan tozarcin da cin fuska. Meye anfanin ci gaba da zama?.”

Ai sai ga mutuminki kuka shabe- shabe, shi yana son matarsa bazai iya rabuwa da ita ba, tsautsayine kawai ya gifta, Runtse ido hayder yayi kafin ya bude su a kansa. ” wannan ya zama last warning a gareka, duk randa hannunka ya kuma gigin kaiwa kan yar’ uwata, wannan ba komai bane, akan abunda zai faru. ”

Mota muka shiga muka bar gidan. Kallon hayder nayi ” dud daya rubuta sakin ya xakayi? Da alama Anty samira na sonsa sosai?.”

Tsaki yayi ” I have the feeling bazai iya sakin nata ba, they love each other, ga children, saki ba abin wasa bane, nayi hakan ne don ya kara sanin girman gargadina a gareshi.”

” karfa ya debo mana police? Kunga mu mukaje har gidansa.” Hafiz da tunda ake abun sai lokacin yasa baki

Hararsa hayder yayi ” matsoracin banza. Mu dashi waye abin kullewar, just dunduma masa jiki kawai nayi, sister dina fah dake kwance gadon asibiti, mu me yasa bamu kira masa police din ba?”

Dariya aminu yayi ” yanzu wannan dukan kake kira da just. Wannan in ni kama shi, ai nima gadon za’a bani.”

” na tausaya masa ni kaina wallahi.” Na fada

Sallar magrib muka wuce, bayan anyi isha’i muka nufi hospital duba Anty samira. Abun mamaki a can muka sami gogan. Sai wani sun sun kuyar da kai yake.

Kasa fadawa kowa yayi, har aka musu sulhu, ta koma. Ba Wanda ya Sani daga Hajiya sai Anty samira. Sai jiya da nake ba su jabir labari, bayan ya bamu labarin abokinsa da yayi aure 5 months ago, sun rabu, saka makon dukan shan gishiri da ya mata, kan abunda bai taka kara ya karya ba. Kuma yanzu yana nema  kome.”

” abinda kukayi Baku kyauta ba, ko baici albarkacin kowa ba, yaci na ya’yansa. Da baku ta bashi ba.” Hubby ta fada cikin rashin jin dadi

” sunyi dai dai, ai ba lokacin ya fara dukanta ba, fadane batayi.” Mommy Hauwa ta fada

Cike da mamaki hubby tace ” Allah ya kyauta. Dama ita da Anty abida ne masu problems, sai yanzu aira dake fama da kishiya.”

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE