KASHE FITILA CHAPTER 6 BY BATUUL MAMMAN

KASHE FITILA CHAPTER 6 BY BATUUL MAMMAN

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

A hankali take taku kamar ba ita bace mai aiki da kuzari a asibiti. Tana taka kafarta a kofar falo taji ana kokarin kinkimarta. Dariya ce ta subuce mata domin da kyar ya iya rabata da kasa kafin ya ajiyeta yana maida numfashi da kyar bayan ya sanya hannuwansa duka biyu ya rike gwiwoyinsa a duke.+

“Wai fa irin dan surprise dinnan zanyi miki na dagaki sama na juya ina miki wakar i love you. Gaskiya nauyi ne dake matar nan…”

Tana dariya tace “kamar shari’a ko”

Sai kuma ta dan bata rai “yanzu ni irin daukan da maza ke yiwa matansu sai dai na gani a tv” zama tayi harda tagumi ita a dole bata ji dadi ba.

Kusa da ita ya zauna tare da sakala hannu a kafadarta “banda abinki wannan daukan da kike gani duk buge ne fa. Indai matar ba bugun fulawa bace katuwa a ido shafal a hannu to sai dai idan mijin kakkarfa ne jikan Antaru”

Dariya sosai Yana da Mujahid suke yi ta mike “bari naje na gaishe da Hajiya sai na dawo ka fada min nice bugun fulawar ko kuma kaine rago baka cikin jikokin Antaru”

Kamar yace ta dawo yadda suke nishadin nan haka yaji yana kallo ta fita ta zagaya bayan gidan bangaren mahaifiyarsa. Ajiyar zuciya yayi ya gyara kwanciya akan doguwar kujerar falon yana jiranta.

Da sallama ta shiga wata mata da zata girmeta sosai tana durkushe gaban Hajiya tana kwaba lalle a wata roba ta amsa. Hajiya kuwa dauke kai tayi ta cigaba da sakace hakorinta.

Yana ta durkusa ta gaisheta ta kara kawar da kanta gefe. Mai kwabin lallen wadda musamman yayar Mujahid ta daukota tana biyanta ta rinka taya Hajiya zama idan Yana ta tafi aiki tace Hajiya ana gaisheki .

Da ido daya ta kalli Yana ta tabe baki “anje an gama gantali da sunan aikin an dawo? To sannu da zuwa sarauniyar masu gida”

Murmushi tayi domin ta saba da halin surikar tata wadda ta kasance yaya ta uwa daya uba daya ga mahaifiyarta.

“Hajiya yaya gida da sanyi sanyin nan?”

Kin amsawa tayi sai ta janyo kafarta daga bangaren Laraba mai aikin nata ta dorawa Yana akan cinya saboda a kusa da ita ta durkusa.

“Kinga cire mayafin nan zakiyi ki saka min lalle.”

Laraba tayi saurin janyo robar daga hannun Hajiya mai shirin turawa Yana

“Haba Hajiya da ganinta yanzu ta dawo ki bari nayi miki ita taje ta dan huta”

Wata uwar harara Hajiyan ta doka mata sannan ta fizge robar lallen “aikinta ne dama ba don ta sawa zuciya kwadayi ta gagara zama tayi bautar aure ba me zaisa ma a daukoki. Ga gida har gida ana neman shekara biyu taje tana bankar tarkacensu na asibiti nasara ya hore musu kunne anki haifa min jikoki.”

Yana kanta a kasa ta soma shafa mata lallen a kafa idanunta fal hawaye taji Hajiyan ta cigaba da fada

“Ke nifa da ace ba Mujahid bane kadai namiji babu abin da zai kawoni gidansa. Yo gidane banda yahudanci da nasaranci babu abin da ake yi. Ni dai hadin zumunci baiyi min rana ba. Da bare ya aura mai halin nan da tuni tasan inda dare yayi mata. Yanzu kuwa ko me nayi sai ace babu kara babu zumunci. Ko ita uwar taki Yakaka ai tasan ina kokari”

Cikin siririyar murya tace “Hajiya kiyi hakuri”

Tsaki tayi tace ita dai a saka mata lalle kuma ta rinka yi daki daki kada wani wurin yafi wani kamawa.

Mujahid da yake daga wajen dakin yana jinsu ya koma bangarensu zuciya babu dadi. Samun mace irin Yana sai an tona. Matar da bata da burin da ya wuce ta kyautatawa mutane. Idan ya nuna rashin jindadinsa game da yadda Hajiya take yi mata ranar kwana take yi tana fushi dashi. A cewarta bazata taba jindadin rayuwa ba idan ta zama silar da mijinta yayi wasa da aljannarsa dalilin kin kyautatawa mahaifiya.

STORY CONTINUES BELOW

Zaman jiranta yayi sai bayan awa biyu ta dawo. Tana shigowa dundu tayi masa a baya tana fara’a kamar ba ita ba. Wanka suka yi sannan suka ci abincin da tayi musu kafin ta fita aiki. Suna gamawa aka kira magariba ya fita sallah ita kuma bayan ta idar ta gaggauta dora tuwo wanda ta gama kafin isha. Da ya dawo ne suna hira take bashi labarin Maamu da taji a wurin Rumana

“Yaya ba don cin fuska ba nake baka labarin nan amma gaskiya wasu matan basu iya samun wuri ba. Yanzu ita Allah Ya bata wadda zasuyi zaman fahimta ga zuria amma ta daukowa kanta balai da hannunta”

Hannuwanta ya rike tare da kokarin hada ido da ita “Kanwata don Allah kada naji kin shiga wannan case din. Nasan halinki na tarar aradu da ka. Amma har yau ban manta mutumin da kika taimaki matarsa akaje alkali ya kashe auren saboda dukan da yake mata. Kinfi sati ba kya fita daga gidan nan saboda fakonki da ya rinka yi. Ni kaina a tsorace na rinka fita kada a sabauta ni” ya kare da dariya

Jinsa kawai take yi amma ko kadan bata tsammanin yadda labarin nan ya shigeta zata dauke kai. Ita fa salihancinta daya ne a rayuwa gaban uwar miji. Daga nan kuwa bata ki a hau sama a rikito ba indai zata kwatarwa mutun yanci.

Yadda ya kula tana juya kai yasan maganar bata shigarta. Girgiza kai yayi don yasan aiki ya same shi.

*****

A gaggauce Awaisu yake ta shiri ya watso kaya daga wardrobe yana cusawa a karamin akwati. Takun Gimbi yaji gabansa ya fadi sai dai ya dake ya cigaba da zubawa amma a hankali. Kallonsa tayi tare da akwatin

“Indai kayan tafiyarka Lagos ne na hada maka tun jiya”

In’ina ya soma sannan da kyar ya iya saita kansa yace “nasan wancan kayan duka suits kika zuba. Ni kuma yanzu Fika zan tafi na fasa zuwa Lagos din.”

Duk da ta razana ta daure tace “bangane ba”

“Ashe tun daren jiya Yaya Harisu ke kirana Maamu tana kwance a asibiti. Bansan yadda akayi wayar ta koma silent ba sai da safe naga text dinsa”

Gimbi ta hade girar sama da ta kasa. Dama ita tayi silencing wayar da ta ga Harisu yana kira “yanzu don sun rainaka shine tun tafiyarsu baa nemeka ba sai yau zasu ce Maamu babu lafiya. Anya ba wani abu suke kullawa ba? Kayi tafiyarka Lagos din kawai Abban Haris ina zaton maganar da Amir ya fada min bayan dawowarsu daga Fika kwanakin baya gaskiya ne”

“Me ya fada miki?” Ya tambaya yana kokarin zuge karamin akwatin.

Shiru Gimbi tayi taki magana. Awaisu ya sake tambayarta sai kawai ta fashe masa da kuka. Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba domin kuka take mai cin rai. Duk yadda zatayi kada ya tafi sai tayi domin gudun bacin aikin boka. Zama yayi yana ta rarrashinta har zuwa lokacin da idea tazo mata sannan ta fara magana murya a dashe.

“Kasan tun bayan dawowar Maamu garin nan ka rage zuwa Fika.”

Kansa ya gyada yana cigaba da kallonta.

“Dasu Amir suka dawo shine yace min wai yaji Kawu Harisu da Baaba suna cewa yanzu ka rage basu kudi tunda Maamu tana nan. Wai zasu san yadda zasuyi ta koma Fika dole ka rinka zuwa”

Jin haka ya mike da sauri rai a bace “bari naje na sami Amir din naji gaskiyar zancen nan”

Kafin ya kai kofa Gimbi ta riko shi tana wasu hawayen “kada ka tambaye shi saboda ranar da ya fada min baka ga irin dukan da nayi masa ba nace bana son  gulma. Nace masa kuma yayi min alkawarin bazai sake zancen ba”

Hannunwanta ya zame daga jikinsa ya sake nufar kofa “ai ba wani zai fadawa ba sai ni.”

Har ta fara tsorata tace “amma Abban Haris baka ganin bata tarbiya ne hakan. Ni nace yayi alkawarin barin zancen kai kuma zaka sa ya fada. Kaga zai tashi da rashin sanin girman alkawari”

STORY CONTINUES BELOW

Har zuciyarsa yasan ko kadan bai gamsu ba amma kuma zuciyarsa tana ingiza shi akan ya hakura. Wani irin bacin rai ya rinka ji ya juya a fusace ya dauko jakar da ta zuba masa kayan zuwa Lagos ya fita. Wani  asirtaccen murmushi tayi a fuskarta kuwa tsantsar damuwa ce kawai take nunawa. Har waje ta biyo shi tana bashi hakuri akan kada ya dauki zafi da su Harisu ‘yan uwansa ne. Shi dai bai tanka mata ba ya shige bayan mota dreba ya ja.

Dakinsa ta koma ta daka tsalle tana murna. Su Harisu basu isa su dagula mata lissafi ba. Tasan duk ranar da hankalin Awaisu ya dawo jikinsa akwai rikici tsakanisu. To amma ko kadan bazata lamunce uwar miji ta rinka juya mata miji ta zama borar karfi da yaji ba. Aure tayi don taji dadi bata fatan irin zaman da wasu suke yi iyayen miji su mayar dasu tsumman goge goge. Mace ta kasa sakewa a gidanta saboda suruka me kenan akayi. Gara da tayiwa tufkar hanci taci karenta babu babbaka.

Awaisu kuwa tunda suka fita zuciyarsa take masa wasu sake saken banza. Har ayyana masa takeyi Harisu ya killace Maamu ne kawai don yaci kudinsa. Abin haushin shine duk nemansa saboda su da iyalinsa ne. Me ya ragesu dashi da zasuyi masa haka? Numbar Maamu yayi niyyar kira sai wata zuciyar ta hana shi. Tsaki kawai yaja ya lumshe idanunsa har suka isa bankinsu. Aiki zai dan rage kafin lokacin tafiyarsu airport yayi.

*****

Kwanaki biyu a tsakani Harisu ya cika fam da bacin rai. Ya sake kiran Awaisu wai shi yake fadawa ayyuka sunyi masa yawa yanzu ma yana Lagos. Harda cewa ya duba accout dinsa yayi masa transfer na dubu dari biyu su kara a kudin asibiti. Da wannan takaicin ya tafi asibiti yana zuwa Baaba take tambayarsa yaya sukayi da kaninsa ya daure fuska kuwa. Ganin haka Maamu ta soma hawaye. Bacin ranta ba na komai bane sai yadda danta ya juya mata baya. Harisu ya kula da haka ya dawo kusa da ita ya zauna yana murmushi.

“Maamu ki dena saka damuwa a ranki. Kina warkewa da kaina zanje Abuja na sami Awaisu. Yanzu kinga likitoci sunce baa son komai ya bata miki rai. “

Baaba ta kara da cewa kada ta damu tare zasu je sai wannan Gimbin ta gane bata da wayo. Ita dai jinsu kawai take yi tana yake don nuna musu bata damu ba.

Suna haka Dr. Yana ta leko dakin da fara’arta suka gaisa ta tambayi jikin Maamu. Bayan ta dubata ta ne ta dan kalli Harisu wanda a cewarta bata ga mutum mai karamcinsa ba.

“Uhmmm dama nace an kirawo mata Awaisun da take kira kuwa? “

Baaba Hure tace “amma wannan yarinya da fitina kike. Yanzun nan mun samu hankalinta ya dan kwanta zaki zo ki tada zance.”

Langabe kai Dr. Yana tayi tana kallon Maamu “ni wallahi tausayi take bani. Idan yaki zuwa ne wani ya bishi mana a fada masa bata da lafiya yazo kada Allah Ya raba ganawar”

Harisu ya dafe kai yana kallon yadda yanayin Maamu ya sauya tana neman kara rikicewa. Tsawa ya dakawa Dr. Yana yace ta biyo shi waje. A zuciyarta tayi dan murmushi bukatarta ta biya. Sumsum tabi bayansa suka koma can reception suka tsaya daga gefe.

Hannuwansa biyu ya hada a gabanta yana roko “don Allah likita ki tsaya a iya duba jikinta ki dena tado mana zantukan da zasu hanata warkewa da wuri. Idan da kinsan irin wahalar da tasha za ki tausaya mata ne”

Dr. Yana ta dago kanta ta gyara fuskarta alamun ba da wasa tazo ba.

“Tunanin hakan ne yasa nake ganin ya kamata duk yadda zakuyi ku taimaketa kuyi. Bazan boye maka ba gaskiyar magana wannan baiwar Allah da wuya ta tashi. Ka dubi yadda jikinta gabadaya ya bushe ga cututtuka sun hadu da tsohon kashi. Idan kuka tsaya dogon tunani rai yayi halinsa baku hadata da Awaisun nan ba ku kanku bazaku ji dadi ba”

So take ta sanar dashi tasan komai amma tana gudun yadda zai dauki abun. Tana kallo ya zurfafa a tunani tace “ko kasan ganinsa yana daga cikin abubuwan da zasuyi saurin kwantar mata da hankali ta sami sauki da wuri? Kuyi tunani akan shawarata. Indai yana da rai duk yadda zakuyi ku kawo mata shi ku kawo shi ko yaya ta saka shi a ido”

Tana kaiwa nan tayi gaba. Rumana dake tsaye a bayansu dauke da kwanakan abinci ta goge kwallarta. Ita da kannenta ne Abba ya kawo su. Ji tayi ta sake tsanar Uncle Awaisu sosai. A iya sani da fahimtarta kawai yayi kudi ne yake wulakanta mahaifiyarsa da danginsa.

Karasowa sukayi suka gaishe da Harisu sannan suka wuce. Maamu tana nan jiya iyau sai damuwa da ta karu. A cikin halin ciwo take sanar da Baaba Hure tana zargin akwai hannun Gimbi a wannan halayyar ta Awaisu. Abubuwa da dama da suka wakana a Abuja ta bata labari wanda itama Baaban ya kara tabbatar mata da zarginta na asiri ake yi masa. Hakuri ta kara bawa maamu da alkawarin Harisu zaije da zarar Awaisu ya dawo daga Lagos din da yace ya tafi. Da yake su kadai ne a dakin Maamu tana hawaye ta soma yiwa Baaba magana

“Baaba kada kiga ina nuna damuwa kamar babu kara. Idan kika zauna a gidan nan yanzu ko yini daya ne zaki gane danki baya cikin hayyacinsa. Ina tsoron in mutu duk wani sauran zumunci namu ya yanke. Abubuwan da kuka yi mana bani da bakin saka muku ko godiya. Nayi tunanin Awaisu zai fitar dani kunya ya kyautata muku da zuciya daya. Sai gashi ni da na haife shi ma….” kuka ne ya kwace mata sosai sai tari ya sarke ta.

Rumana tana daga waje duk ta gama jin abinda suke fada domin ta wuce sauran yan uwanta. Dama da kuka ta karaso na maganganun babanta da Dr. Barrister. Zantukan Maamu sun kara karya mata zuciya. Tana jin ta soma tari ta tura kofar ta shiga. Baaba ta gani rike da Maamu jikinta babu kwari tana ta tari. Dago kan da Maamu tayi daga cinyar Baaba sai jini suka gani yana fita ta bakinta. A razane suke duka su biyun Rumana ta soma kuka don tsoro ta kasa komai.1

Baaba Hure itama a tsoracen take tace “ki ruga ki kirawo min babanku da likita”

Ta juya a guje zata fita taji muryar Maamu tana cewa “ki fadawa Awaisu na yafe masa”

Bata jira jin karshen maganar ba ta fita. A hanya suka hadu da Harisu tana kuka ta fada masa Maamu na aman jini. Nan suka tafi shi da Abba kiran likita.

Dr. Yana tare da wasu likitoci biyu suka taho dakin cikin sauri. Suna isowa suka sallamesu daga dakin suka rufo kofar. Jikin kowa a sanyaye suka tsaya jiran tsammani.Bayan kamanin rabin awa aka bude kofar dakin. Tura Maamu suka ga anayi akan gado tana kwance ko kwakkwaran motsi bata yi. Kuka ne ya barke daga bakin matan da ke wurin domin duka matan Harisu da su Aunty Suwaiba sun iso. Baaba Hure ce tayi karfin halin hanasu a lokacin Harisu ya bi bayan likitocin. Dr. Yana tasan yana binsu shiyasa bayan sun daidaita Maamu a I.C.U ta fito ta same shi. Yanayin barkwancin nan duka babu afuskarta sai  tausayi. Ita ta soma magana da ta karaso inda yake tsaye hankalinsa a tashe+

“Mun samu jikin nata ya dan daidaita. Ta kusa samun heart attack ne dazu”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Dr yanzu menene abin yi?”

“Addu’a ita ce za’a cigaba da yi. Sannan gaskiya ku dena taruwa da yawa a dakin tana bukatar hutu. Wannan dakin bama bukatar kowa sai mutum daya itama kuma ba ciki zata zauna ba.”1

Godiya yayi mata ya juya ya tafi da niyyar hada kansu su tafi gida ta kuma tsayar dashi

“Awaisun nan da take kira har a cikin wannan tsananin ciwon addua take yi masa. Don Allah a karo na karshe kada kace na shiga abin da babu ruwana ku taimaka ku kawo shi. cuta ba mutuwa bace amma tana jin jiki.”

Jiki a sabule ya koma kofar dakin nan suka tsare shi da tambayoyi. Ya gama yi musu bayanin me likita tace yayyen Maamu maza suka zo da matansu har da su Tikeke da Bomai kanin baban Awaisu. Harisu yaso sakaya lalurar Maamu amma Baaba Hure tayi musu bayani dalla-dalla.

Nan wurin ya kaure da salati sai da security yazo yace duk su koma waje. A nan ma manyan suka hado aka yanke shawarar su wuce Fika ayi maganar a gida.

Mazansu da matansu manyan haka suka hadu a falon Harisu ana fadar abubuwan da suka faru. Baaba tasa aka kirawo Rumana domin shaida. Ita kuwa bata boye komai ba dangane da yadda  suka tsinci kansu a gidan Awaisu. Bomai da ake ganin yafi kowa shiririta ne ya soma magana bayan an sallami Rumana.

“Lallai biri yayi kama da mutum. Idan kun tuna zuwanmu gidan nan abubuwa marasa dadi sun faru. Kuma daga bayanin wannan yarinya Rammana duk mai hankali yasan cewa akwai wata a kasa”

Wanda Maamu take bi ya amshe “abin da ya faru ya riga ya faru sai dai mu kiyaye gaba. Dama Maamu ga zurfin ciki tazo ta hadu da bacin rai dole ya taba zuciya. Ni dai idan da mai zuwa ya kamataa gobe muje mu taho da Awaisu ko yana so ko baya so”

Kowa yayi na’am da wannan shawarar inda aka yanke cewa zasu tafi su uku harda Harisu da Bomai.

Can asibitin kuwa Aunty Baraka ce ta zauna ko da zaa bukaci wani makusancin Maamu.

*****

Da yake jirgin safe Awaisu ya biyu kafin azahar ya iso gida. Yana zuwa ya tarar Gimbi bata nan ga yara sun tafi makaranta. Rita ce ta fito da gudu tana yi masa maraba kamar zata rungume shi. Abin ya bashi tsoro ma yayi saurin matsawa baya sai tayi murmushi ta wayance da karbar jaka.

“Sir how was your trip?”

Fine yace kawai yayi gaba. Saurin shan gabansa tayi ta matso daf dashi tana karairaya “ga abincin na gama hada maka”

A gajiye yake baya son yin magana shiyasa ya wuceta kawai yana mamakin wannan abu da take yi kamar zata shige jikinsa.

Ita kuwa dariya tayi tana tunanin lokacin da nasu aikin zai fara aiki ta shigo gidan ayi waje da Gimbi. Dakinta ta koma ba jimawa taji ana buga kofa da karfi. Ita da Awaisu kusan karo suka yi suna sauri zuwa bakin kofar don jin ko lafiya.

Bashi hanya Rita tayi yana budewa suka hada ido da wata mace da jikinta duk ya motse ga fuskarta kamar ayi amai saboda lalacewar fata. Tana tsaye tana ta susa tana bige bige a jikinta. Maigadi yana bayanta yana son tabata ya fitar da ita amma kyankyami ya hana.

STORY CONTINUES BELOW

Ganin Awaisu yasa ta dan sakin rai “Awaisu fadawa wannan yaron gidan naka cewa nice Anti Bebi”

Sake kallonta yayi cikin rashin gaskata me take fada. Wannan matar da ko almajira bata kai matsayin a kirata dashi ba itace Anti Bebi. Yana cikin wannan tunanin yaga ta rike wuya tana ta kakari.  Da kyar ta saki wuyan tana haki

“Shegu yanzu kuma wuyana akace ku shake. Duk abinku ni Bebi nace dubu sai ceto”

Maigadi ne ya kuma yunkurin miko hannu sai suka ji horn a waje. Da sauri ya tafi ya fita duba waye ya bar Awaisu da Anti Bebi da Rita.

Anti Bebi ta dan nutsu ta soma magana “Awaisu ta inda aka hau ta nan ake sauka. Ka fadawa Gimbiya naji labarin komai daga wurin aljanun da tasa suke bibiyata kuma wallahi dani take zancen domib bata ci riba ba. Yadda tasa nake dandanar balai a rayuwata itama ta shirye gamuwa da nata. Nayi alkawarin ko zanyi yawo tsirara ne sai naga bayan Gimbiya”

Su Harisu ne suka shigo ta karamin gate din mai tafiyar kafa. Karshen maganar Anti Bebi kawai suka ji suka kalli juna.

“Nasan bata nan shiyasa na shigo amma idan na kuma shigowa sai nayi ajalinta” yawu ta tofa a kasa ta juya ta fita suna mata kallon mahaukaciya.

Sai a lokacin hankalin Awaisu ya kai kan bakin nasa. Da faraarsa ya taho yana musu sannu da zuwa. Bomai ya kalli Rita da kayan jikinta

“Yanzu Awaisu meye wannan a gabanka?”

Harisu yace “mai aiki ki”

Yayan Maamu ya daure fuska ya kalleta yace ta basu wuri. Awaisu ya nuna musu kofa su shiga ciki suka ce a’a.

Kawun nasa yace “ba zama muka zo yi ba Awaisu. Ana ta kokarin sanar da kai Maamu bata da lafiya kaki zuwa.”

Harisu ya kalla yayi wani murmushin takaici “yanzu abin harda su Kawu kuka hada a ciki? Me na rage ku dashi da har zaka kalawa Maamu cuta kawai don kuna son na zo Fika na baku kudi? Idan kana bukatar wani abu kafi kowa sanin cewa a shirye nake na baka”

Ba su Kawu ba hatta Harisu bai fahimci zancen ba sai da suka nemi yayi musu karin bayani. Nan ya fada musu abin da Gimbi tace Amir ya fada ya kara da cewa yasan bazata taba yi masa karya ba.

“Kazo ka dauke Maamu ka bar min mata cikin damuwa kawai saboda son abin duniya…”

Wani wawan mari irin wanda Awaisu baya jin an taba yi masa tunda yazo duniya Harisu ya kwada masa a kumatun hagu yana huci saboda  tsantar bacin rai.

“Ni Awaisu? Ni kake fadawa magana irin wannan?”

Bacin ransa da haushin Harisu wanda ya rasa dalilinsu ne suka kara tsanani a zuciyarsa har hawaye suka fara fita daga idanunsa ba tare da ya sani ba.

“Saboda na fadi gaskiya shine zaka mareni? da me na rageka da zaka sanya mahaifiyata cikin son zuciyarku kai da Baaba Hure”

Ran Harisu ya kara baci yayo kan Awaisu a harzuke. Kwalarsa ya kama da hannu daya da daya hannun kuma ya rinka marinsa shima kuma hawayen yake yi. Muryarsa tana rawa yake magana ga su Bomai na son ya saki Awaisun ya ki.

“Awaisu nine Harisu…ka dawo cikin hayyacinka ka kalleni. Yayanka ne wanda zaiyi komai domin farincikinka da rike amanar da Mahaifinmu ya dauka.”

Tamkar karamin yaro Awaisu yake zubar da hawaye ya ma dena kokarin kwacewa daga rikon da Harisu yayi masa. Kirjinsa ya dafe yana kallon dan uwan

“Yaya kirjina ne yake min zafi kamar ana hura wuta. Na rasa abin da yake damuna. Yaya ka taimaka min”

Harisu rungume shi yayi tsam a jikinsa yana shafa masa baya shima kuma yana hawayen.

“Allah baya bacci Awaisu. Ka roke shi zai kawo maka sassauci cikin lamuranka”

Bomai da Kawu suka ja gefe suna kallon wadannan ‘yan uwa. A hankali  cikin sigar lumana Harisu ya sake labartawa Awaisu ciwon Maamu sannan ya roke shi ya zo su tafi ya dubata. A ransa yana son zuwa amma zuciyarsa tana ta hura masa wutar kada ya yarda da yayansa. Ba karamin yaki yayi ba da tsananta karanta Hasbunallahu wa ni’imal wakeel da Lahaula wala quwwata illa billah sai ya sami kansa da amincewa.

Su Kawu suna murna Harisu yace yaje ya dauko kayansa su tafi yace zuciyarsa bata so ya shiga gidan.

“Yaya kullum da tsoron gidan nake kwana. Amma bari naje na dauko mukullin motar da wayoyina da wallet “

Su ukun suna waje kusan minti shabiyar sai gashi ya fito har da yar jakar kaya. Rita ta biyo bayansa tana tambayar ina zaije ya daka mata tsawa akan ta dena binsa. Wata jeep ya nufa ya kira maigadi ya dan gogeta suka shiga suka fice.

Rita duk ta kidime tayi ta kiran Gimbi shiru bata daukar wayar. Yau tasan gidan babu zaman lafiya.

*****

Daga saloon Gimbi ta fito taje anyi mata kananun kitso da karin gashi da dan mayafinta a rabin kai irin na Anti Bebi babu dankwali ta fito zata shiga mota.

Daga tsallaken titin tun daga nesa Mama ta hangota suna dawowa daga unguwa da Umar. Da sauri ta rinka dukan kafadarsa tana nuna masa Gimbi akan suje wurin da sauri kada ta tafi. Wata irin kwana yayi har suka kusa gwara motocin ta kuwa fito a fusace tana bambami. Mamaki ne ya isheta ganin Mama da kaninta ta dan murmusa. Ba karamin kewar mahaifiyarta tayi ba. Sai dai taji kunya sosai don rabonta da gida tun ranar da ta koma gidan Awaisu da kanta. Sannan ko waya bata taba yi musu ba.

“Idonki kenan Gimbi?”

Ta dan rausayar da kai “Mama nayi zaton kuna fushi dani ne shiyasa na kasa zuwa gidan. Yaya kuke da Alhaji?”

Kaninta ta kallo da ko fitowa daga motar baiyi ba bare tasa ran zai kulata ta murmusa ta leka ta window tayi masa magana kawai sai ya saka waya a kunne shina dole baiji ba. Abin ya bata mata rai sosai kuwa. Kwanakin nan ba karamin kewar ‘yan uwanta take yi ba da iyaye.

Mama tace “ban sani ba ko kin hadu da Bebi amma tazo min a kamanni na ban tsoro tana ikirarin ganin bayanki. Gimbi shawara ta karshe zan baki domin indai da rai baa fitar da rabon samun gafarar Allah. Ki tuba ki dawo daga rakiyar wannan mummunar rayuwa da kike yi. Ni da ‘yan uwanki babu mai zuwa gidanki wannan umarnin babanki ne. Amma ki sani yadda Bebi tauraronta ya haska har ki mutu bana jin zaki kamota. Yau ga Bebi duniya ta gwada mata ita budurwar wawa ce. Wanda duk ya kamu da sonta a sannu zata yaudare shi  ta karar da duk wani abin arziki a tare dashi sannan ta gudu ta barshi.”

Shiru Gimbi tayi tana tunanin su Mama basu san wanda ta kama ba. Bokanta na yanzu ba dai ta fadi bukata ba kafin kace kwabo zaka ga yadda kake so indai an kiyaye sharuddansa. Bata samu bakin magana ba Mama ta shige mota suka tafi suka barta a tsaye. Motarta ta shiga ranta a dagule ta kula da wayarta tana haske. Ko da ta duba missed calls din Rita sunfi biyar. Kiranta tayi don tasan babu lafiya. Ai kuwa ta bata mummunan labarin tafiyar Awaisu. Wani zagi ta rinka jerawa Harisu sannan ta tada mota tayi gida.

Kafin ta karasa Ovi tazo don a hanya tayi mata waya. Tambayarta shawara tayi akan me ya kamata tayi Ovi tace da safe ta hada kan yaranta su tafi Fika don kada tayi bakin jini

“Ki sani ko an fadawa boka babu yadda zaayi ace an rufe bakin kowa a cikinsu. Tafiyarki kawai itace mafita. Idan kinje ki san yadda zakiyi ki kwantar da kai a wurinsu sannan ko da Maamu ta fada musu wasu abubuwa ki karyata. Zani wurin boka gobe sai na fada masa a haukata ta idan yaso dole a yarda dake. Mijinki kuma kada ki damu shima zaa sake daure miki shi”

Ovi na fita Rita tabi bayanta “Sis yaya zaki bata shawara haka mu sai yaushe zamu fara namu aikin?”

Ovi ta dafa Rita ta rage murya “kada ki damu wannan shawarar babu inda zata kaita. Kuma bazani wurin Boka ba don gobe ma ni Enugu zamu tafi da wani sabon kamu da nayi “

Tafawa sukayi sannan Ovi ta fice.

*****

Awaisu ke tuki babu mai magana cikinsu har suka isa wani gidan mai suka tsaya yin sallah. Daga nan Harisu ya karbi tukin Awaisu ya zauna a gaba kusa dashi sai bacci. Yana baccin nan banda mugayen mafarkar babu abin da yake yi. A firgice ya farka ya cigaba da kallon titi.

Damaturu suka wuce suka nufi hanyar asibitin. Gaban Awaisu ne ya rinka faduwa akai akai tun kafin su karasa har Harisu yayi parking. Ji yake kamar bashi da laka ga mugun tsoro ya mamaye zuciyarsa. Hannunsa yaji Harisu ya kama suka nufi ICU.Har suka isa kofar dakin  Awaisu a tsorace yake. Dayake kofar ta glass ce ta wajen Harisu ya nuna masa Maamu kwance tamkar bata da rai. Wai a haka ma ta danji sauki kuma ta dan murmure ba kamar lokacin da aka kawota ba. A hankali ya taka ya leka inda Harisu ya nuna masa. Kafafunsa ne suka fara rawa sai gashi yana neman faduwa. Harisu yayi saurin tare shi sai dai yana mikewa ya fice daga cikin asibitin zuciyarsa tana matsanancin harbawa.+

Jikin motarsa yaje ya shiga ya rufe kofar sannan ya kifa kansa akan sitiyari. Kuka Awaisu yake yi sosai irin wanda rabonsa dashi tun kuruciya. Kukan da yake yi ba na halin da ya tarar da Maamu bane , kuka ne na tsananin nadama  da tausayin kansa. Idan ya mutu a yanzu ya tabbatar bashi da abin da zai kare kansa a gaban Mahallicinsa. Tambaya daya yake ta nanatawa a zuciyarsa. Shin yana ina Maamu ta kamu da ciwokan da Harisu ya fada masa ya daukota dasu? Wata faduwar 6gaba ya sake ji da ya tuna rabonsa da sata a ido tun wata waya da ya hadata da Harisun farkon komawar Rumana Fika.

Mahaifiyarsa abokiyar sirrinsa, abokiyar shawararsa ita ce a wannan yanayin kuma a cikin gidansa bai sani ba. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun yayi ta maimaitawa a ransa. Shi dai ba jahili bane. Ya san cewa wurare da dama a Al’Qurani Allah SWT Yayi umarni da bin iyaye da kyautata musu. Hadisai kuwa bazai iya kirga wadanda ya sani masu magana akan bin iyaye ba musamman uwa wadda ta sha wahalar ciki, haihuwa, raino da kula da ‘ya’yanta tun zuwansu duniya har sai ta dena numfashi. Uwa ko kana ganin kaiune maiyi mata komai na bukatun rayuwa baka taba girmaa idonta shiyasa ko a gidanka take bata fasa yi maka  tambayoyi kamar kaci abinci ko kana jin bacci.

Tunaninsa na karshe shine yanzu idan Maamu ta rasu a wannan yanayin yasan duniyarsa ta gama lalace, lahirarsa kuma dama ba’a magana. Share idanunsa yayi ya koma cikin asibitin.

Dr. Yana tana tsaye da su Harisu ana kokonto ko Awaisu tafiya yayi sai gashi ya dawo. Ganin likita a wurin ya roketa ta taimaka ta barshi ko na minti biyu ne ya shiga wurin Maamu. Harisu ta kalla da guntun murmushi a fuskarta

“Shine Awaisu?”

Shi ya amsa mata da kansa “nine don Allah ki bari na ganta”

Bude masa kofar tayi ta matsa gefe tana murmushi.

Maamu tana kwance tana tunanin yadda rayuwarsu ta sauya cikin dan lokaci. Ga kudi sosai Allah Ya basu amma Ya jarrabesu da mace irin Gimbi wadda ta kasa gane me ta tsare mata. Kamar a mafarki ta jiyo kamshin turaren Awaisu wanda ta dade da saninsa dashi. Tana ayyanawa a ranta wane likitan ne mai wannan turaren taji an kama hannunta an rike gam.

A hankali ta bude idanunta suka sauka cikim na Awaisu. Cikin wata irin murya mai rauni yace

“Maamu” sai ya kawai ya durkushe a gefen gadon yana kuka. Ita ma Maamun hawaye take fitarwa a hankali ta dora hannunta daya a kansa tana shafawa.

Sun dauki kusan minti biyar a haka wadanda suke wajen dakin harda Dr. Yana suna kallonsu wasu suna tayasu kukan.

Sake dago kansa yayi bakinsa har rawa yake yi. Maamu ta rame iyakar rama. Idanuwanta duk sun shige ciki ga uban baki da tayi.

“Ki yafe min Maamu. Don Allah kada fushinki ya zama katanga gareni da samun rahamar Allah.”

Murmushi tayi cike da jindadin addu’arta ta karba hankalin danta ya dawo jikinsa tasa hannu ta goge masa wasu sababbin hawayen da yake fitarwa a hankali

“Ban yi fushi da kai ba domin nasan baka san abin da kake yi ba”

Girgiza kai yayi “so nake kice kin yafe min Maamu. Nayi miki alkawari wallahi bazan kara saba miki ba. Daga yanzu har karshen rayuwata akan rokon gafararki da kyautata miki zanyi”

STORY CONTINUES BELOW

Lumshe idanu tayi a hankali “na yafe maka Awaisu. Allah Ya cigaba da tsareka daga sharrin mutum da aljan. Allah Ya yafe mana baki daya”

Yana kuka yana dariya ya rinka cewa ameen. Ji yayi wani sakayau jikinsa kamar an zare masa wata kaya mai sukarsa a zuciya. Daga shi har ita babu wanda ya sake magana sai lokaci zuwa lokaci su kalli juna suyi murmushi. Shi Awaisu ma har jin ya rinka yi kamar ya zama sabon mutum.

Kusan awarsa daya a dakin kafin Dr. Yana ta sake dawowa tace ya fito a bar Maamu ta huta. Ba don yaso ba ya fita yana jaddada mata cewa a kofar dakin zai zauna tare da su Baaba.

Haka ya fito yana tunanin dole ya koma Abuja ya fara processing kai Maamu asibiti a Egypt ko Saudiyya ko kuma duk inda aka tabbatar masa akwai manyan likitici da kyakkyawar kulawa.

Gaban Baaba Hure ya fara zuwa ya durkusa ya gaisheta. Itama neman ta yafe masa yayi tana kuka tace ta yafe. Daga nan ya gaishe da su Anti Baraka da sauran ‘yan uwa da suke zazzaune a wurin. Kallonsa suka rinka yi cike da tausayawa.

‘Yan Harisu da na ‘yan  uwansa mata da suke wurin suma duka suka gaisheshi banda Rumana. Ya kula suna hada ido wata muguwar harara ta jefa masa tare da dauke kai.

Dan murmusawa yayi ya matsa kusa da inda take zaune akan katon kafet din da suka shimfida a wajen.

“Umm Ruman babu magana?”

Ga mamakin kowa tsaki taja mai sauti kuwa ta tashi ta bar wurin. Bata yi nisa ba kukan da take boye ya fashe har suna jiyota. Mamanta ce ta kirata cikin fada tace wace irin dabi’a ce wannan.

Mama uwargidan Harisu ta janyota jikinta tana goge mata ido itama hararar Awaisun take yi ta kada baki tace

“ai dai baza’a daki mutum a hanashi kuka ba ehee. Kiyi hakuri kinji Rumana”

Awaisu ji yayi jikinsa ya kara sanyi ya matsa gefe wurin yayansa yana kara fada masa abin da ake ciki dangane da ciwon Maamu.

Ranar sai wurin shadayan dare suke kama hanyar Fika. Ba don an matsa masa ba nan yaso kwana a kofar dakin Maamu. Ita kuwa wannan ganin kawai da tayi masa ya sanyaya mata rai hankalinta ya kwanta.

*****

Har shabiyun dare babu wayar Awaisu balle text. Gimbi ta kalli wayarta a karo na ba iyaka tayi jifa da ita tana fada ita kadai.

“Wallahi Awaisu baka isa ka wulakanta ni ba. Don ka tafi garinku shine bazaka kirani ba?”

Har wurin biyun dare ta kasa bacci tunani ya isheta. Bata kula da lokaci ba ta kira Ovi a tsohon daren nan. Cikin magagin bacci ta dauka tana tambayar me ya faru.

A hargitse Gimbi take tace “babu lafiya Ovi. Kince kada na kira Awaisu boka yace aiki zai lalace. To amma kinga shiru yaki kirana. Ina tsoron fa kada su juyar masa da kai game da ni komai ya lalace.”

Ovi tayi siririn tsaki don ta ma manta da karyar da tayiwa Gimbi dazu sannan ta daure ta bata amsa

“Kamar yadda na fada miki gobe kawai ki bi bayansa . Gara kowa ma yasan cewa basu isa dashi ba naki ne ke kadai. Ki tafi ki taso shi a gaba ku dawo gida”

Cikin zakuwa Gimbi tace to.

A nasa bangaren ji yayi ko kadan baya so yana tunaninta don fargaba hakan yake saka masa. Sannan duk da bai fada mata ba yayi mamaki da har ta kai yanzu babu wayarta domin jin ina ya tafi. Wasu abubuwa game da zamansu da Maamu ya rinka tunawa abin yana daure masa kai. Zarginsa akan Gimbi ya kara karfi amma bazai dauki mataki ba sai ya tabbatar saboda wannan abu ba karami bane da za’a yanke hukunci da gaggawa. Da sassafe ko abinci bai tsaya ci ba yace asibiti zai tafi. Hakan yayiwa su Baaba dadi ya tafi shi kadai. Baaba tasa aka kira Antu Ummukulsum da ta kwana ranar akan cewa yana isowa ta tafi gida domin a bawa da da mahaifiya damar ganawa a nutse. Harisu da ta bawa sakon murmushi yayi yana jindadin hali irin na tasa mahaifiyar. Ba karamin jinjina mata yake ba domin ita ce tushen zaman lafiyar gidan.

*****

STORY CONTINUES BELOW

Kafin tara na safe Gimbi ta gama hada kayanta da na yara duka. Makaramtarsu tayi niyar fara zuwa sanarwa zasuyi tafiya.

Suna zaman jiran dreban ya iso Ovi ta kirata bayan sun sake shawara da Rita.

“Munyi magana da Boka yace kada ki kuskura kije garin nan sai yayi kwana biyar da rabi bai dawo ba. To daga daidai wannan lokacin sai ki hau hanya ki bi bayansa saboda sharrin makiya daga can garin nasu”

Gimbi ta danyi jim tana tunani. Gashi ance kada ta kira yanzu kuma kada taje. Anya bazata janyowa kanta matsala ba kuwa? Shirunta yasa Ovi gane me take tunani tayi saurin cewa

“Kada ki damu yace aiki zaiyi akan mijin naki da babat tasa yadda zasu tsani juna. Zuwanki yanzu zai bata masa aikin ne”

Sai a lokacin hankalinta ya kwanta tayiwa Ovi godiya sukayi sallama. Ovi ta kira Rita tace tayi maza taje ta fadawa bokan yadda sukayi da Gimbi koda zata zo kada ya karyatasu.

******

A rana ta biyar da tafiyar Awaisu Gimbi ta shirya tahowa Fika.

A can kuma Maamu tana ta samun sauki don har an mayar da ita amenity. Yanzu har hira anayi da ita kuma ta soma cikowa. Awaisu shanu biyu ya saya yasa aka yanka kullum ana sarrafawa a kawo mata. Suma jamaar gidan sun sami nasu rabon. Kaji da kayan lambu da na marmari kuwa wani na tarar da wani. Barin kudi yake yi kamar bai san ciwonsu ba. Burinsa kawai Maamu ta warke ya cigaba da kyatata mata.

Yau bayan ya dawo daga sallar azahar ya tarar da Dr.Yana a dakin. Wajen dakin ya biyota bayan ta gama duba Maamu da barkwancinta yace yana son fitar da ita waje yana bukatar takardun gwaje gwajensu domin tafiya dasu.

Dan daure fuska tayi “a haka kuke sawa muji babu dadi. Yanzu duk kokarin da muke yi kuma ciwon bai gagaremu ba shine zaka ce zaka fitar da ita?”

“Baki fahimceni bane, ina so ta sami kulaw ne sosai saboda wasu dalilai nawa”

Dariya tayi ganin yadda yayi da fuska da gaske yake.

“To don Allah ka bari ta kara samun sauki sannan ko fitar zakayi da ita sai kayi.”

Godiya yayi mata ya koma cikin dakin. Rumana wadda har yanzu bata kula shi tayi saurin mikewa zata fita.

Girgiza kai yayi ganin da gaske yarinyar nan fushi take yi dashi “Rumana ina zuwa?”

Kamar yayi magana da dutse ko girmansa bata gani ba tayi hanyar kofa. Ai kuwa manyan dake dakin suka hauta da fada ta fita a fisace tana hawaye. Tasan har abada bazata taba manta rayuwar gidan Awaisu ba. Idan ta kalli Maamu haushin kanta na barin gidan ita kadai take yi da kuma na Awaisu da ya gagara kula da ita.

Maamu na kallonta ta kalli yadda ya bita da kallo wai itama ta zama ‘yan mata ta iya fushi. Daga inda take zaune ana bata abinci tace ya bi bayanta ya rarrasheta.

Anti Suwaiba tace ya rarrasheta ko ya zane ta dai “yarinya taki sakawa ranta salama kullum fushi”

Maamu ta sake kallonsa “idan ka taba min ita zamu sa kafar wando daya da kai da yayar taka mai bada shawarar”

Anti Suwaiba na dariya ya fita yana cewa yanzu duk duniya ai babu da mai ladabinsa.

Ya dan wahala wurin nemanta kafin ya hangota can wurin ajiye motoci a durkushe tana share hawaye. Wurin ya karasa tana ganinsa ta kuma tashi sai dai kafin ta fita ya rufe hanyar. Dama tsakanin wasu motoci biyu ta zauna a wani dan tudu wanda bayansa fence ce babu hanyar fita. A tsiwace tace “zan wuce”

Yana kada kai yace “Rumana…”

Bai kare magana ba ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Idan da zata tona abubuwan da Maamu ta rinka dannewa a zuciyarta a zamansu a gidansa bata jin ko ruwa zai kara sha da dadin rai. Gabadaya komai ya sire mata har tsoro take ji kada itama ta girma duk yadda tasan Awaisu yana son Maamu ya koma haka itama ta zama hakan.

Tausayi ta bashi sosai ya mika hannu zai rungumeta sai kuma ya fasa. Wannan ba ‘yar karamar Rumanan nan bace. Shi bai san ma yana ina yarinya yar shekara goma sha shida ta zama ‘yan mata haka ba.

Da hannunsa ya nuna kansa ya dan rage murya “nine ko? Kiyi hakuri Umm Ruman Uncle Awaisunki bazai kara bari abin da ya wuce ya kuma faruwa ba”

Baki ta dan tsuke “ni ba Uncle Awaisuna bane”

“Har kin manta haka kike fada a gida kice naki ne ke kadai? Muje a tambayi su Baaba idan mun koma gida “

“To na fasa ba nawa bane”

Kwaikwayonta ya sami kansa da yi yace harda yin alamun kuka yace  “don Allah kice naki ne ko na fadawa Maamu”

Dariya yaso bata sai ta wani gimtse fuska wanda ya lura da hakan. Inda ta baro yace tazo su zauna ta fada masa duk abin da ke ranta ko zata sami sauki.

Dr. Yana da take tsaye a jikin motar Mujahid tun dazu ta sauke ajiyar zuciya ta shiga. Kallonta yayi yace sannu da shanya ta dan kwanto a jikinsa tana fada masa wani kyakkyawan gamo tayi wanda dole ma ta ga faruwarsa.Cikin kuka Rumana ta rinka zayyanawa Awaisu wasu abubuwan da suka faru dasu a gidan. Ciki wasu ya sani har yana mamakin sai yanzu da take fada yake jin haushinsu. Me yasa a lokacin baiyi yunkurin daukar mataki ba. Ita ce tambayar da yayi ta maimaitawa kansa. Zuciyarsa ba karamin nauyi ta kara yi masa ba. Ba don a gaban Rumanan bane babu abin da zai hana shi kukan bakinciki.+

A raunane yace “Abin da yasa kika dawo gida kenan? Me yasa baki taba fada min ba?”

Tambayar tasa ta biyu ce taji a kamar wani rainin wayo. Ita fa yanzu daga shi har matarsa tayi alkawarin dena ragawa kowa sai dai idan tayi a daketa ace mata mara kunya.

Wani kallo ta bishi dashi kafin tace “Uncle a gabanka fa yawanci ake yi”

Ajiyar zuciya yayi “haka ne….hmmmm…tashi ki koma ciki. Komai zai daidaita in sha Allah”

Mikewa tayi tana tafiya yabi bayanta da kallo. Hakuri yaso bata na kasa rikonta da yayi sai kuma ya fasa kada sauran girmansa ya zube don ya tabbatar yanzu ba wata kima gareshi ba.

Ita kuwa tana tafiya tana tuno wasu abubuwan da kunya tasa ta kasa sanar  dashi. Yaushe zata manta cewa a iya zamanta na gidan kafin tayi rabin shekara ta koma yin gunzugu na mutan da da dankwalayenta saboda rashin kudin siyan pad. Daga baya ne da suka shaku sosai da Yusra ta fada mata shine take bata a makaranta. Tsigar jikinta ce ta tashi da ta tuna yadda take kasancewa duk wata.

Awaisu bai bar wurin ba ya zurfafa a tunanin wannan rikirkitacciyar rayuwar tasa da ya kasa fahimtarta yaji wayarsa tana ringing. Kyalewa yayi sai da  yaji mai kiran ya nace ya dauka.

Muryar mace yaji tayi masa sallama a hankali ya amsa yana tunanin inda yasan wannan murya.

“Shuhada ce, ka gane ni ko?”

Ji yayi hankalinsa ya kuma tashi. Yaushe zai manta da ita, matar da Maamu ta dage sai ya aureta lokaci guda.

Jin yayi shiru yasa ta kalli Daddynta da yake zaune kusa da Mamansu wadda ta dawo sati biyu da suka wuce.

Alh Maitama ya mika hannu ya karbi wayar yayi masa sallama.

“Suna na Alh Maitama mahaifin Shuhada”

A mutumce Awaisu ya gaishe shi. A garin Abuja waye bai san wannan sunan ba. Tsoronsa daya ba dai maganar auren bace zasu sake tayarwa.

Daga daya bangaren yaji Alhajin ya soma yi masa magana.

“Malam Awaisu ina son haduwa da kai ne domin wasu maganganu masu mahimmanci “

“Shikenan” ya fada a ransa yana tunanin tabbas zancen auren ne. A zahiri kuwa ya sanar dashi baya gari kuma bai saka ranar dawowa ba yanzu saboda rashin lafiyar mahaifiyarsa.

Fatan samun lafiya yayi masa sannan yace “don Allah ka nemi ne idan ka dawo yanzu Shuhada zata turo maka nambar da zaka sameni. Ina kuma yi maka adduar yadda Allah Ya fitar dani kaima Ya fitar da kai lafiya. Sai naji daga gareka”

Yafi minti biyu yana kallon wayarsa yana kokarin gano me Alh Maitama yake nufi da maganarsa ta karshe. Daga karshe ciki ya koma ya sami wuri ya zauna kusa da gadon Maamu. Idan ta dago kai sai ta ga yana yi mata  kallo mai cike da tausayi. Murmushi kawai take yi tana ayyanawa a ranta ko yanzu ta bar duniya Alhamdulillah.

*****

Bayan sun gama wayar Alh Maitama ya mikawa Shuhada wayarta.

Mamanta Haj. Rahama ta ce “Daddy yanzu kana ganin zai yarda idan ka fada masa abubuwan da matarsa da Bebi suke yi?”

“Ni da na yarda a yanzu nasan ba komai bane illa karfin addua da ikon Allah. Gabadaya jina nake kamar rayuwar da nayi da ita a mafarki ta faru. Lokaci yayi da matan nan zasu fuskanci hukuncin laifukansu. Dubi Shuhada duk irin son da mijinta yake mata Bebi ta shata musu layi bazasu kara zama tare ba idan har ba wani auren ta kuma ta fito ba. Kina ganin akwai iyayen da zasu so a rinka kirgawa ‘ya’yansu aure ne?”

STORY CONTINUES BELOW

Haj Rahama ta girgiza kai. Ita kanta Allah ne Yayi da sauran zama tsakaninta da masoyinta uban ‘ya’yanta. Saki uku Anti Bebi tasa yayi mata daga shigowarta gidan. Fushin da tayi akan wannan sakin yasa tana gama idda tayi aure don ta nuna masa tana da sauran daraja. To da yake bata son mutumin zaman nasu yaki dadi ga kishiya can ma ta matsa mata. Auren bai jima ba ta fito.

“Waccan ledar yaya za’ayi da ita ne” ta nuna ledar da aka kulle da tarkacen layoyi, guraye, ruwa kala kala a robobi da kananun tukwanen kasa duka dauke da sunayen Alh Maitama da iyalinsa.

“Munyi magana da wani malami a islamiyar da su Shuhada sukayi. Yace zai zo karshen sati ayi addu’o’i sosai a gidan sannan a konasu.”

‘Yarsa ya kalla tana gefe tayi shiru sai ta kara bashi tausayi.

“Ki kara hakuri kinji ‘yar Daddy. In sha Allah da sannu Allah zai baki miji nagari. Jiya shima Tajuddeen nayi ta masa nasiha akan yayi hakuri ya fawwalawa Allah komai. Ni da kuka ganni duka abubuwan da suka faru kara min imani sukayi da sanin cewa lallai Allah Shi kadai Ya cancanci a bauta maSa.”

Sun jima suna hira wadda kusan dukkanta akan yanayin da suka tsinci kansu ne bayan zuwan Anti Bebi. Basu tashi ba sai da yayi musu alkawarin tafiya wurin Suhail cikin wata mai kamawa sai su jira ya kammala jarabawa su taho gida tare. Kudi kuwa ba kadan ya tura masa ba yace ya biya duk abubuwan da ake binsa na makaranta da bashin abokai idan yaci.

*****

Yau Harisu ya tsaya a daya daga cikin shagunansa sunyi lissafi da yaron wurin. Yana dawowa Baaba Hure dama a shirye take ta fito su tafi asibiti cikin Damaturu. Sun kusa fita daga layin gidan nasu ta hango ta yi saurin cewa Awaisu ya tsaya. Juyowa yayi yana kallonta ta waiga baya

“Wata na gani a motar can da ta wuce kamar Gimbiya”

Ransa har ya baci jin sunanta yace “Gimbiya kuma Baaba me zai kawota yanzu?”

“Juya mu koma gidan dai. Na tabbatar ita na gani”

Ba musu suka koma. Ai kuwa suka hadu da Gimbi da yaranta a waje suna fitowa daga mota.

Harisu da Baaba suka kalli juna ganin yadda ake ta fito da kaya daga boot. Kwalayen juice ne kala-kala da kayan abinci irin su shinkafa, maggi, taliya, mai da sauransu. Motar wata hadaddiya ce amma mai mazauni uku.

Tana ganinsu Baaba ta dena yamutsa fuska musamman ganin  yaranta sunyi wurinsu da gudu suna murna. Harisu yaji dadin ganinsu domin jinin Awaisu ne don yana kin babarsu baya jin akwai dalilin da zai sashi kin yaran.

Gimbin ma da sauri ta karaso wurin Baaba ta fada jikinta tana ta murna.

“Baaba mun sameku lafiya? Yaya gida ?”

“Da kin bari mun shiga ciki sai gaisa sosai” Baaba tayi gaba yaran na biye da ita.

Suna shiga ciki Gimbi ta nufi dakin Maamu tun a tsakar gidan take kwala mata kira kai kace ‘ya tazo ganin babarta ne bayan sun jima basu hadu ba.

A bude kofar take saboda an ajiye kayan wankinta da safe baa rufe ba. Ganin babu kowa kuma dama tasan babu din ta fito tana gaisawa da matan gidan. Su mamakin kayan da ake shigowa dasu sukeyi. Harisu ta kalla tana murmushi

“Yaya Harisu shine daga zuwa ka dauke mana Maamunmu ko? To kafata kafarta tare zamu koma kuma mu hada da Baaba Hure kaga mun koma ‘yan gata ko ta ina. Tana ina ne? Maamu???” Ta kare da daga murya tana kiranta.

Murmushi Baaba Hure tayi wanda Gimbi tayi zaton na murnar tace zasu tafi da ita Abuja ne. A zuci tace kwadayayyu. Ita kuwa Baaba Hure tsabar mamakin rashin kunyar Gimbi take da gogewa a kissa. Tana kallonta tace

“Su Makiru manya”

Gimbi a razane ta kalli Baaba ba dai da ita take ba ta dan hade rai da tsoron kada a dagota.

STORY CONTINUES BELOW

Baaba ta fahimce yadda fuskarta ta sauya ta daga kai tana kallon sama tana magana cikin kulawa da sassauta murya

“Makiru shegen tsuntsu, idan baka iya takunka ba da ranka da lafiyarka sai ya sunkuce maka da ya barka da ciwon zuciya. Tsuntsaye da dama tsoronsa suke yi. Gimbi kuna dashi a Abuja? “

Harisu ne yayi saurin magana saboda tsoron kada daga nan Baaba ta  fadi maganar da zata janyo rikicia take a wurin don bata da hakuri indai an taba nata bisa rashin gaskiya. Yafi so cikin ruwan sanyi su shayar da Gimbi mamaki akan abin da tayi.

“Babana ina Abbanku ne” ya dafa kan Mu’allim yana tambayarsa. Yayi sa’a babu kowa a wurin sai shi da Baaba kada wani yayi saurin cewa Awaisun yana nan.

Gimbi tayi saurin cewa yaran  “kai ku shige ciki”

Bayan taga shigarsu dakin Maman Rumana ta dan tabe baki “Yaya Harisu lamarin kaninka sai addua kasan yadda ayyuka suke masa yawa.  Tare muka so zuwa tun farkon tahowarku da Maamu sai aka tura shi Lagos. Na kasa hakurin jiransa ne nace bari na taho kawai kewar Maamu ta dameni. Shi kuma kwana biyar ban sami wayarsa ba ma, ina zaton aikin can din ne yayi masa yawa ko an sace wayar.”

Ikon Allah, wato da haka ta taho zata nuna bata san me yake faruwa ba kenan ta mayar da laifin kan mijinta. Girgiza kai yayi kawai yace “Allah Ya kyauta. Kuci abinci ku dan huta sai mu tafi Damaturu. Dama asibiti zamu je wurin Maamu muka ga shigowarku shine muka dawo”

Jakar hannunta mai mugun tsada ta saki a kasa ta dafe kirji “asibiti kuma? Me ya sameta?”

Bai kai ga bata amsa ba ta soma kuka harda daga murya. Nan da nan kuwa aka fara fitowa daga dakuna kallonta. Su Haris ta kira tace su zo su tafi asibiti Maamu babu lafiya.

Wadanda ke wurin manya mamakin diramar Gimbi suke yi yayin da ta zamewa yara abin kallo. Tare da Baaba suka sake fita ta shige tasu motar  da ‘ya’yanta wsu Harisu na gaba suka dauki hanya.

*****

Kana shiga dakin Maamu zaka san cewa akwai soyayya da shakuwa tsakanin ma’abota cikinsa. Maamu zuciyarta ta sanyaya har tana ganin ya kamata a sallameta ta karasa jinyar a gida. Ga su Anti Baraka da ‘yan uwanta ana ta wasa da zolayar juna. Lokaci lokaci sai ta kalli Awaisu wanda ya kasa dena yawan kallon Rumana.

Murmushi tayi domin bai dade da fada mata cewa yana tsoron dasa kiyayyarsa a zuciyarta ba duba da cewa yarinya ce kada abubuwan da suka faru su kasa gogewa a ranta. A lokacin Maamu cewa tayi kada ya damu indai Rumana ce zata hakura. Yanzu ma ganin yadda ciwo yaci karfinta ne yasa ta zama haka har take ganin tamkar laifinta ne na dawowa ita kadai. Da ta fada masa haka cewa yayi yadda ta bashi labarin abubuwan da suka faru a gidansa yasa jikinsa yayi sanyi. Yasan Girmansa ya fadi tana masa kallon wanda ya kasa rike mahaifiyarsa bai cancanci a ga girmansa ba.

Maamu gani tayi abin ba komai bane Rumana yarinya ce mai ladabi da hakuri komai zai wuce nan gaba. Amma yadda Awaisu yake ta jan maganar da nuna damuwa yasa tace masa to yasan yadda zaiyi ya dawo da kimarsa a idon Rumana tunda abin ya dame shi haka.

Jin ta fadi haka yasa shi saurin mikewa “Maamu  ba fa wani abu nake nufi ba abar zancen nan dai”.

“Dawo dai mu karasa sai ka fada min me kake nufi”

Matsar da kujerarsa yayi can gefe cikin ‘yan uwansa shi kadai namiji a cikinsu yana dariya. Sai dai duk motsinsa a idon Maamu tana kallon inda idanuwansa suke yawan sauka.

Wasu ne suka zo dubiya daga Fika dangin Baban Awaisu maza da mata dakin ya dada kaurewa da hayaniya da gaishe gaishe. Rumana da ta kasance karama duka dakin sai ta matsa can gefe bayan ta gaishesu.  Sallamar Babanta taji ta tashi karbar kayan da yake hannunsa idanunta suka sauka akan Gimbi. Nan take jikinta ya hau bari tsoro ya kamata ta kasa motsin kirki a wurin. Awaisu na ganin yadda ta tsorata don bai ma ga Gimbi ba ya taso yazo gabanta ya tsaya tare da rage tsaho ya hura mata iska a fuska.

STORY CONTINUES BELOW

“Umm Ruman are you okay?”

Hawaye ne taf ya cika idonta duk yadda ta rinka tsara rashin kunyar da zata yiwa Gimbi ranar da duk suka sake haduwa ji tayi abubuwa da dama sun dawo mata a lokaci guda sai matsanancin tsoro da fargaba.

Ledar da ta fara karba a hannun Harisu ya karbe ya ajiye a kasa yace mata ta wuce su fita daga dakin. Daga kan da zaiyi ya mikawa Harisu hannu su gaisa ya hada ido da Gimbi wadda tayi mutuwar tsaye.

A zuciye take da yadda ta ga yayiwa Rumana. Harda wani sabon salo wai Umm Ruman. Sunan da rabon da taji ya ambata tum farkon zuwansu Abuja kafin Wangesi ya fara aiki a kansa ita da Maamu ya manta da lamarinsu ballantana sunayensu. Kishi ne ba bala’i a cikin idanuwanta da suka kada sukayi jazur. Me yasa boka yace kada ta biyo mijinta washegari? Me ya faru a kwanaki biyar dinnan da ya dawo Fika?

Daga kan gadonta Maamu ta gama kallon komai tsaf ta kuma gano ta inda in sha Allahu zata nunawa Gimbi nata ikon na mahaifiyar Awaisu. Tun da ta fara samun lafiya ita da Baaba Hure suka saka shi a gaba da fada akan sakaci da azkar. Sun karfafa ko ma meye ya same shi da yadda ya damu da neman kudi kawai batare da yawaita yiwa kansa addu’ar neman tsari ba.

Yaransa ne suka rungume shi suna murnar ganinsa shima yayi murna domin yayi kewarsu. Gimbi da duk abubuwan da take yi tun zuwanta shawarwarin Ovi ne ta rasa me yake mata dadi saboda ganin da tayiwa Awaisu da Rumana yana nuna damuwarsa a kanta. Kenan asirinta ya soma  karyewa tunda har ya damu da wata karan kada miya Rumana. Kula da tayi dakin ita suke kallo yasa ta mayar da idanunta ga Maamu wadda kallo daya yasa ta gane ba karamin ciwo tayi ba. Kanta tayi da gudu har tana takawa Hindu matar Bomai hannu ta fada jikin Maamu tana kuka.

“Maamu me ya sameki haka? Ina can ni ban sani ba”

Tsigar jikin Maamu har tashi tayi jin rungumar da Gimbi tayi mata. Tsana da kyankyaminta take yi sosai saboda tasan ita ce silar wargajewar farincikinsu.

Ba Awaisu da yake da tabbacin ya sanar da ita rashin lafiyar Maamu har tace karya ne ta kara da yiwa su Baaba sharri kowa na dakin da yasan me yake faruwa mamaki ne ya kamashi na wannan karfin hali irin na Gimbi.

Da fuska cike da hawaye ta dubi Awaisu ta soma korafin me yasa bai fada mata ba shine ya taho shi kadai don ya sa tayi bakin jini. Wannan abu da take yi duk tuggun Ovi ne da tace mata a haka zata wanke kanta. Ita kuma sukuwa bata san bakin jini Ovi take son kara mata ba yadda asirinta zaiyi saurin tonuwa ta bar gidan Awaisu.

Baaba ce tayiwa Rumana alama da hannu  akan su fita ita da yaran. Sauran bakin ma duka suka fice don abin ya zama matsalar family.

Jikin Awaisu har wani tsuma yake yi saboda bacin rai wai shi Gimbi zata yiwa wannan rainin hankalin a bainar jama’a. Yunkurin karasawa gabanta yayi mata magana yayi Harisu ya girgiza masa kai. Cikin bacin rai ya kaiwa bango naushi zuciyarsa na kuna. Da wace irin mace yake zaune tsahon shekaru sai yanzu halayenta ke bayyana kansu gare shi.

Maamu tana kallonsa ga tausayi ya bata taji kwalla ta cika mata ido. Sanin cewa Gimbi bata jin yarensu kuma ita idan ta fada mata da hausa sakon bazai isa yadda take so ba yasa ta yafito Baaba da hannu. Magana tayi mata kasa-kasa yadda sauran bazasu ji ba. Baaba ko dogon nazari batayi ba akan maganar duk da tayi matukar mamaki ta dago ita da Maamu duk suna murmushi

“Awaisu jeka wurin Rumananka ka rarrasheta naga ta fita kamar zatayi kuka. Kaima a yadda ranka ya baci dinnan ganinta nasan zai sanyaya maka rai.”

Anti Baraka da kanenta duka suka bi Baaba da ido cikin rashin fahimtar inda zancen ya dosa. Shi kuwa Awaisu kamar jira yake yi ya fice daga dakin don yasan idan zai cigaba da zama yana kallon Gimbi tana wannan karyar kulawar zai iya kai mata hannu a yadda zuciya ke dibarsa.

Fitarsa tayi daidai da zare dukkan wani farinciki da yayi saura a zuciyar Gimbi sai nauyin da taji kirjinta yayi mata. Tsabar takaici ma kasa magana tayi ta rinka kallonsu daya bayan daya. Wai yaje wurin Rumanansa??? Kai kila kunnena baiji daidai ba ta fada a fili ba tare da ta sani ba.

Shi kuwa sai da ya kusa isa inda suke tare da su Daula sannan ya tsaya cak yana tunanin me Baaba tace. Rumanansa? Me take nufi da hakan? Daga ido yayi suka hada ido da Rumanan da yake tunani ta dan yi masa murmushin karfin hali a zatonta ko yaji haushin yadda ta nuna tsoron matarsa ne don tasan yana sonta sosai. Shi kuwa wannan murmushin jinsa yayi tamkar an *kunna fitila* a cikin zuciyarsa har abin ya bashi tsoro. Rumana ce fa ‘yarsa.

A cikin sakin kuma cikin yarensu Anti Ummukulsum ta tambayi Baaba me take nufi da Rumanan Awaisu. Nan tayi bata bayanin sunyi ne kawai don bata ran matarsa.  Maamu ta kafe Harisu da ido tace

“ni ba da wasa nake yi ba dana ka taimakeni ka kara yi min wannan alfarmar”

Baaba tayi saurin kallonta “Da gaske kike yi Awaisu kike son hadawa da Rumana?”

“Ba don na huce takaici ko bacin ran da matarsa ta saka min ba kawai na kula kamar shima yana son hakan”

A raunane take maganar ta rike Baaba Hure “kiyi hakuri idan na bata miki rai, ban ko yi tunani ba”

Baaba tace “da gaske kina son wannan hadin?”

Su Harisu duk suka zaro ido jin wannan maganar ta iyayensu. Maamu na cewa eh Baaba tace

“In sha Allahu anyi an gama alfarmar Manzon Allah SAW”

Dakin tsit yayi su Harisu an ma rasa me cewa komai. Gimbi tana tsaye suna yare bata fahimci komai ba sai dai zuciyarta ta bata akwai abin da suke kullawa jin an ambaci sunan Rumana da na mijinta. Wani zafi ta fara ji a jikinta tun daga tsakiyar kai har tafin kafa.Babu wanda ya kula ta sai ma Harisu da ya fita don ya rasa abin cewa. Awaisu ya hango ya kusa karasawa inda su Rumana suke yayi saurin binsa ya tare shi. Rasa abin fada yayi don jin wannan hadi da bai taba tsammani yayi ba daga sama. Sai kuma ya daidaita kansa yace ya kamata yaran suci abinci a mayar dasu gida saboda sun sha hanya, gashi suna isowa an sake tahowa dasu asibiti.

Awaisu yayi na’am da shawarar “ni zan zauna a nan waje har su gama don raina bazai jurewa karairayin Gimbi ba”

Kafadarsa Harisu ya dafa “kayi hakuri Awaisu ni bana son wata rigima ta tashi a asibitin nan ba mutumcinmu bane. Duk abin da zamuyi ka bari a koma gida”

Daga nan Rumana ya kira ya umarceta da zubawa su Amir abinci. A dan tsorace ta shiga dakin kai a kasa taki bari su hada ido da Gimbi wadda take sankame a gefe guda zuciyarta tana ruri kamar ana hura mata wutar bacin rai.

Ganin Rumanan sai ta dan saita kanta ta rungumota. Tamkar mazari jikin Rumana ya hau bari saboda tsabar tsoro.

“Oyoyo Rumana kin tafi kin barni da kewa ganin Maamu yasa ban kula babbar ‘yar Mummy ba.”

Yawu ma kafewa Rumana yayi ta kasa daga harshe tayi magana sai murmushin yake. Gimbi na kula da yadda ta tsure a ranta taji dadi yarinyar nan bata isa ta kawo mata raini ba don ta riga ta dasa mata dafi a zuciya. Hannunta ta kama tayi hanyar fita daga dakin da ita tana dariya

“Shine kika biyewa Abbanku baku fada min Maamu babu lafiya ba ko? Muje waje dai musa labule akwai labari”

Rumana ido yayi kwal-kwal da hawaye ta juyo neman agaji wurin iyayenta tana so wani cikinsu ya hana Gimbi fita da ita daga dakin. Anti Suwaiba ce tayi yunkurin tashi ta hana Baaba ta girgiza kai. Bayan fitarsu ganin cewa akwai su Haris a dakin ta sake magana da yarensu

“Ku kyaleta hakan da tayi ya tabbatar min tayi zargin wani abu game da maganganun da mukayi dazu. Ga dukkan alamu tsorata ta zata yi.”

“Kuma shine zaki hana a tsayar da ita? Kada ta cutar da Rumana” cewar Maamu tana sako kafarta kasa daga kan gadon.

Baaba ko a jikinta harda dariya  tace “nafi so ta cigaba da tunanin tayi nasara wannan ne zaifi kona mata rai idan taji an shafa fatiha”

Abinci ta zubawa yaran da kanta tace su ci a kama hanyar komawa Fika su huta. Su Maamu duka hankalinsu a tashe tace kada su damu da kanta zata fita ta dawo da ita. Tafi so dai ta bata damar da zata ji kamar babu wanda ya isa sai ita kadai.

Wani dan wuri da babu kowa Gimbi ta kai Rumana ta sakar mata hannu tare da hade fuska sosai

“Rumana kin fadawa su Abban Haris wani abu ne?”

Hadiyar yawu tayi da kyar “Mummy wane abu?”

“Au har kin manta na fada miki ni ba Mummynki bace? Da kika dawo gidan ubanki baki hadu da taki uwar ba?”

Bata ce komai ba hakan ya kara tunzura Gimbi amma dole ta daure tana wurin da dolenta tayi a hankali saboda ‘yan uwan Awaisu ne ko ta ina. Zaro idanu tayi tana mata kallon banza

“Akwai wani abu tsakaninki da Abban Haris? Naji ana ce miki Rumanansa”

Wannan karon ma kasa magana tayi sai ma tsoro da taji ya mamayeta tunda bata nan lokacin da Baaba ta fadi hakan.

Ta gama kidemewa karshe kamar daga sama taji muryar Awaisu ya kirata cikin sanyin muryar da ko kadan batayi kama da muryar da uba zai kira ‘yarsa ba. Ita kanta Rumana ba don rashin sabo ba da ta dago cewa Uncle Awaisu fa wani salon shagwaba yayi mata.

“Umm Ruman kije ki gani idan sun gama cin abinci ku fito mu tafi dare yana yi kuma nima yunwar nake ji baki bani abinci ba”

Tirkashi, zuciyar Gimbi ta kumbura suntum da bacin rai mara misaltuwa. Kallon Rumana tayi wadda ta kara shiga cikin duhu saboda rashin fahimtar meyasa yayi magana irin haka. Ita ina ruwanta da cin abincinsa? Ko da can ma ai ba ita take bashi ba. Yadda ya tsareta da kallo yasa ta cewa “bari na duba idan akwai saura sai na zuba maka”

STORY CONTINUES BELOW

Kamar zata bi iska don sauri haka ta bar wurin. Bayanta yabi da kallo kuma yasan tabbas Gimbi shi take kallo yayi dan murmushi yayi gaba yana jin yadda take kiransa hankali a tashe.

Sai da ya koma wurin Harisu yake fada masa me yaji Gimbi na tambayar Rumana. Dama tare suka hango fitowarsu Awaisu yayi saurin tahowa don yasan bazaa kulla alkhairi ba.

Ita kuwa Gimbi da zaa aunata a lokacin tabbas jininta ya hau. Ta rasa gane meye yake faruwa. Tunda tazo fa ko kalma daya bata shiga tsakaninta da Awaisu ba. Abubuwa ke neman rikecewa ta zaro wayarta daga jaka ta kira Ovi. Kuka ne ya taho mata ta danne don kada wani ya fito ya ganta ta zayyana mata halin da take ciki.

“Ovi please kije wurin Boka ki sanar dashi. Idan abubuwa suka cigaba a haka ina kyautata zaton komai zai lalace zuwa matakin da bazaa iya gyarawa ba.”

Ovi ta gimtse dariyarta tace “ki turo kudi yanzun nan zan tafi wurinsa. Ina muka ga ta zama ana neman bata shirin da aka jima ana yi. Dayan maganin nan dai da ya baki kiyi kokari ko ta wane hali ki shafawa maman tasa. Boka yace da kanta zata ce ya biyoki ku tafi kuma bata son kara ganinsa. Kinga daga nan kin huta”

Gimbi ta sauke ajiyar zuciya sai dai tana kokontan yadda zata iya shafawa Maamu magani babu wanda ya kula. Ta kula wani kallon tsana suke yi mata shiyasa take tunanin ko Rumana tazo ta fada musu irin zaman da sukayi. Sai kuma ta ga babu dalilin damuwa saboda idan boka yayi mata aiki a kansu babu wani wanda ya isa ya daga mata yatsa. A take ta turawa Ovi dubu hamsin sai dai tana jin faduwar gaba game da maganar Baaba Hure akan kiran Rumana ta Awaisu.

Tana nan tsaye suka fito tare da su Anti Baraka yau Anti Ummukulsum ce zata kwana. Babu wanda ya kulata taji jikinta ya danyi sanyi. Dakin ta koma tayiwa Maamu sallama harda alkawarin gobe da wuri zata zo don ita zata kwana da ita ma ta fita.

Motar Awaisu ta nufa domin tana son magana dashi akan abubuwan da ta gani daga zuwanta. Sai da Baaba Hure ta tabbatar nan ta taho har tana cewa su Haris su tafi motar da suka zo da ita kawai Baaba tace

“Rumana kin gaji ne haka kike tafiya da kyar? Awaisu bude mata gaba ta zauna kannenta sai su zauna a baya ku fara yin gaba”

Murmushi yayi ya bude kofar yana satar kallon yadda Gimbi ta kame kam a wurin tana kallon ikon Allah. Rumana itama tsayuwa tayi zata waiga ta ga yaya Gimbi tayi don tayi tunanin tare zasu tafi da Awaisu taji yace

“Shiga mana ko sai na dauke ki ne?”

Kunya taji tayi saurin shigewa yana yi mata dariya. Baaba Hure a zuci tace karen bana maganin zomon bana Awaisu kayi min daidai. Taji dadi da ta lura da yadda kalar fuskar Gimbi ta canja gabadaya.

Harisu dama ya riga ya tayar da tasa motar su Anti Suwaiba sun shiga. Baaba Hure suke jira ta tsaya ta karewa Gimbi kallo

“Kun zo mota a cike zaki koma ke kadai. Ko na dawo taku motar ne na tayaki hira?”

Duk yadda taso daurewa bata san sanda ta watsawa Baaba harara ba sannan tayi gaba kamar zata tayar da kura. Baaba tana dariya ta karasa motar Harisu suka tafi. Shima Awaisu jan tasa yayi yaransa suna ta yi masa hira yana amsawa cikin nishadi. Rumana kuwa shiru tayi jikinta ya kara mutuwa. Me zaisa ace ta shiga motarsa ga matarsa a wurin da ta gama bata tsoro dazu.

Gimbi na shiga mota sai hawaye ya balle mata. Tsawa ta dakawa dreban akan ya fita daga motar. Jiki na rawa ya fita tana kuka ta kira uwargijiyarta Ovi ta fada mata sabon lamarin da yake faruwa.

“Ovi cikin kankanin lokaci daga zuwana mutanen nan zasu kasheni da bacin rai. Ki fadawa Boka ko wane irin shiri suke yi ya wargaza zan bashi ko me ya bukata”

Kwantar mata da hankali Ovi tayi da kyakkyawan alkawarin cewa daga gobe idan taso duka gidan sai ta juyasu suga tsiya. Tayi wani mugun murmushin auno yadda zata fanshe bacin ran da Awaisu ya saka mata.

*****

STORY CONTINUES BELOW

Har gari ya waye bata ga Awaisu ba domin jiya sun rigasu isa Fika. Da suka iso kuma bata ma ga motarsa ba. Daki aka bata ta shiga tana tabe baki. Ta tsani zuwa garin nan domin a takure take jin kanta. Su Haris sun bi ‘yan uwansu maza yaran Harisu a dakinsu suka kwana. Daula uwar iyayi ma wurin Rumana ta zabi kwana suka bar Gimbi ita kadai. Da aka bata abincin dare cewa tayi bata ci saboda tunani yayi mata yawa.

Shiyasa da safe Anti Amarya taki aika mata da breakfast. Shiru Gimbi na jiran abinci don ba karamar yunwa take ji ba taji shiru sai hayaniyar yara. Nata ‘ya’yan da take ji kamar ‘ya’yan gwal babu wanda ya leko dakin. Takaici ya sake kamata.

Sai wurin karfe goma Awaisu ya shigo gaishe da Baaba kafin ya wuce asibiti. Bayan sun gaisa yana cin abinci tasa aka kira mata Harisu.

Nutsuwa sukayi a gabanta tace tana fatan sun amince da maganar da akayi jiya na auren Rumana. Awaisu ya dago kai da sauri

“Aure kuma Baaba karatunta fa? Saura watanni ta gama secondary. Daga dawowarta ko wata biyar bata yi ba ta sami miji ne?”

Sai a lokacin ta tuna baya dakin suka yi magana a asibiti.

“Aure ne zaa hadaku Awaisu ina fata bazaka watsa mana kasa a ido ba”

Harisu yayi saurin kallo shi kuma ya kawar da nasa kan saboda har yanzu bai san yadda zai kwatanta yaya ransa ya karbi wannan hadi ba.

Baaba Hure ta lura dasu tayi murmushi

“wannan hadi wanda bamu taba kawowa ko da wasa zamuyi shi ba ina so ku dauke shi a matsayin rubutaccen al’amari. Bansan me Maamu ta gani ba amma ni dai tunda ta fada zuciyata ta aminta ta kuma sami nutsuwa sosai akan hakan. Ina so a matsayinku na ‘yan uwa kuyi shawara da juna. Idan har wannan hadin zai taba muku zumunci kafin mu tafi asibiti yau ku yanke shawara ku fada min.”

Babu wanda yayi magana a cikinsu Baaba Hure ta tashi ta fita. Sai suka koma yiwa juna kallon kallo. Awaisu kunyar Harisu yaji ta rufe shi. Shi da kansa yana mamaki tun zuwansa Fika yake yiwa Rumana kallo na daban. Yarinyar da aka haifa a gabansa har ya saka mata suna. Wannan abu da kunya sai dai ya rasa gane dalilin da yasa shima zuciyarsa take kwadaita masa da ya amince.

Harisu ya gyara zama yana kallonsa  “nasan yadda nayi mamakin wannan magana kaima kayi. Ina so nace ban yarda ba domin Rumana ‘yarka ce amma bazan taba  yiwa iyayenmu musu. Abu daya zan tambayeka dan uwana….ka amince da auren nan da zuciya daya?”

Ya Ilahi sosai Awaisu yaji kunya musamman ganin yanayin Harisu ba yadda ya saba ba. Yasan ko shine zaiji kwatankwacin haka ko ma fi. Bai taba tunanin faruwar haka ba amma shima tasa zuciyar ingiza shi take yi akan kada ya cuci kansa.

Kansa ya sunkuyar “Yaya Harisu… ” sai kuma yayi shiru saboda nauyin amsar da zai bayar.

Tashi Harisu yayi batare da ya saurari amsar tasa ba ya fita. Bai dade ba suka dawo da Baaba a gabanta yace ya amince. Awaisu ya kasa kallonsu duka su biyun saboda tsananin nauyi da yaji. Harisu yasan cewa duka su biyun abin yazo musu a bazata kuma baya ganin laifin kanin nasa sai dai har ga Allah yana tausayin Rumana.

Nasiha sosai Baaba tayi musu akan zumunci da fatan wannan hadi ya zame musu alkhairi mai dorewa.

Awaisu ne ya fara fita Baaba ta cigaba da yiwa Harisu nasiha don tasan sai a hankali zai nutsu da maganar. Ba kuma don baya son Awaisu ba sai dai ko waye yaji zaiyi mamaki duba da alakar dake tsakaninsu.

Ranar Gimbi kirikiri taki zuwa asibiti wai bata da lafiya saboda Ovi bata kira ba. Abinci kuwa sai da rana ta take Anti Amarya ta aika mata. Ba don gudun batawa Harisu rai ba ma ai so tayi ta gasa ta yadda ta yiwa Maamu.

Da Maamu taji sun amince duka su biyun tayi ta saka musu albarka shi da Harisu. Sai kuma ta bawa Awaisu shawarar ya koma bakin aikinsa tunda suna sa ran nan kwana biyu a sallameta.

Dr. Yana taji dadin yadda Maamu take samu sauki sosai idan ta gama round har hira take zuwa suyi.

Washegari Gimbi ta sami kuzarin zuwa asibitin saboda Ovi ta kirata ta fada mata Boka ya kwana aiki akan Awaisu da duk wani wanda zai iya kawo mata cikas. Yaranta tun safe suka bi ‘yan uwansu da Abba ya cika a mota suka tafi. Rumana da yayyenta dake gidajen mazajensu suka tafi har yanzu ita da iyayenta mata babu wanda yake da masaniya akan hadin aurenta da Awaisu.

Hayaniya sosai suke yi a dakin Maamu kuma da ita ake hirar wani likita yazo yace ko su rage murya ko su fita. Harisu yace gara su zo su tafi kawai don hayaniyar tayi yawa. Yaran aka fara turawa suka tafi Rumana zata bisu Baaba tace ta zauna sai tabi Awaisu. Duk da tayi mamaki haka dai ta zauna.

Yayyenta basu kawo komai ba suka fita. Dakin ya rage Gimbi, Baaba da ‘ya’yanta duka su hudun da Awaisu. Hirarsu suke yi babu wanda ya sakata ga Maamu tana ta jan Rumana da hira tana biye mata suna dariya.

Gimbi ta auna taga wulakancin yayi mata yawa kuma dai an tabbatar mata Boka ya gama dasu. Awaisu ta kalla tana wani kada kai tace

“Abban Haris ya kamata mu fara shirin komawa Abuja ko”

A dakile ya amsa mata  “tare muka zo?”

Baaba tace ya kamata ya koma saboda aikinsa. Maamu ma tace dama tayi masa maganar jiya. A wautar Gimbi da mika wuya ga boka sai tayi tsammanin aiki ne ya soma ci shiyasa abin da ta fada duka suka bada goyon baya.

Tayi shu’umin murmushin nasara sannan ta kada kai ta kalli Harisu.

“Yaya Harisu ranar da nazo na taho muku da kayan abinci amma da kai da matanka babu wanda ya nuna ya gani bare ayi godiya. Ko ba komai nasan na rage maka wani nauyin”

Baki bude suka bita da kallon mamakin wannan furucin nata. Awaisu yaji ya mugun tsanar kansa da ya rasa matar aure sai Gimbi. Kafin yayi magana Anti Suwaiba rai a bace tace

“uban waye ya rokeki da har kike jiran godiya. Ke Gimbi! bari kiji in fada miki wallahi baki da arzikin da zaki kawowa iyayenmu abinci”

Baaba tace cikin bacin rai “Suwaiba bana son sakarci ki wuce ku tafi kawai ki kyaleta”

Dayake dama itama bata iya fushi ba sai ta kasa yin shiru

“Baaba wallahi shirun da ake yi mata ne yasa take tunanin ana jin tsoronta. Bayan kin kusa kashe Maamu da yunwa a gidanki shine don rashin kunya zaki zo ki taho da kayan abinci? Billahilzi Gimbiya idan zaki koma baki kwashe kayan nan ba sai na nuna miki ke karamar mara kunya ce. Ki dubemu da kyau gabadayanmu babu matsiyaci balle kice maula muke yi.”

Gimbi ta rasa abin yi jin wannan magana ta tabbatar asirinta yana daf da tonuwa sai kawai tasa kukan munafirci

“Yaya Suwaiba me yayi zafi haka”

“Munafuka kada ki sake kirana Yaya. Da can kina kiran sunayenmu ne ma, sai yanzu don gulma tunda kika zo kike cewa kowa yaya”

Anti Baraka ta kama hannun Suwaiba tace tazo su fita daga dakin ta kwace. Ana ta yi mata magana amma ranta ya gama baci taki sauraron kowa

“Ku barni na amayar mata da abinda ke raina. Gara ta sake shiri idan tana tunanin tayi nasara ne. “

Jikin gadon Maamu ta karasa ta dafa ta “dubi yadda kika mayar mana da uwa. Ba don tsahon kwana ba da tuni bakinciki da ciwukan da kika kwasa mata sunyi ajalinta “

Rumana gani tayi dakin ya kaure Gimbi na kuka ana ta kokarin Anti Suwaiba tayi shiru taki sai ta tashi ta fita tana kuka. Awaisu na ganin haka baiyi tunanin komai ba ya bi bayanta yana kiranta saboda yadda ganin hawayenta ya tayar masa da hankali.

Kukan karyar Gimbi ta dena ta bisu da kallo tana son gano ainihin me yake faruwa dasu biyun. Harisu da kansa yaja hannun Suwaiba tana ta fada yayi waje da ita sauran yan uwansu suka biyo bayansu. Baaba takaici ya isheta ta cewa Maamu bari taje ta tabbatar duka sun tafi yau ita zata kwana.

Tana fita Gimbi tabi bayanta sai ta tuna da maganin da aka bata. Lekawa tayi ta kallo hagu da dama ta tabbatar babu idon sani sannan ta dawo ta rufe kofar. Fitowar Baaba da leken da Gimbi tayi akan idon Dr. Yana wanda fuskar Gimbi ta kasance bakuwa a gareta. Saurin barin matar da take yiwa kwatancen dakin hoton kashi tayi ta taho dakin Maamu da sauri saboda alamun rashin gaskiya da ta gani a jikin mai leken. Tana bude kofar ta ga Maamu a tsaye tana matsawa baya ga Gimbi rike da wani abu kamar izgar doki tayi kanta tana kokarin shafa mata. Cikin zafin nama Dr. Yana tayi kanta…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page